|
| |||
________________________
Mu'awiyya ya kasance gwamnan Sham (Siriya) na kusan tsawon shekaru goma sha shida, don haka ya kasance yana ta kulle-kulle da amfani da duk wata damar da ya samu wajen ganin ya samu damar darewa kujerar halifanci da jagorantar
al'umma. Don haka bayan kashe halifa Usman, sai ya zamanto ya sami gagarumar dama wajen yin tawaye wa halaltacciyar hukumar da al'umma suka zaba karkashin jagorancin Amirul Muminina Ali (a.s) da kafa tasa hukumar, yana mai cewa yana son daukan fansar jinin
Usman din ne, duk da cewa babu wani abin da ya yi a lokacin da Usman din yake neman taimako. Face ma dai yana dakon a kashe shi yake yi don yin amfani da hakan wajen cimma burinsa. Don haka kashe Usman din ke da wuya sai ya mike da ikirarin cewa sai ya dau
fansar jininsa.
A bangare guda kuma, al'ummar musulmi, bayan kashe Usman, sai suka taru a bayan Ali (a.s) suna masu bukatansa da ya zama shugabansu (halifa), duk da cewa saboda wasu dalilai ya ki amincewa da hakan da farko, amma dai daga karshe ya amince. Don haka sai al'umma
suka yi masa mubaya'a da kuma kafa gwamnatinsa a Madina, inda dukkan lardodi da garuruwa na duniyar musulmi suka amince da shugabancinsa da kuma yi masa bai'a in banda mutanen Sham karkashin jagorancin Mu'awiyya, yana mai cewa Ali (a.s) na da hannu wajen kashe
Usman. Don haka ya tara runduna ta mutane da nufin yakan halaltaccen halifa.
Ganin irin wannan yanayi da Mu'awiyya ya haifar da kuma hakkin da yake da shi na kawo karshe duk wata fitina da kuma ladabtar da duk wani mutumin da yake son haifar da fitina tskaanin al'ummar musulmi, Imam Ali (a.s) a matsayinsa na halifa, ya yi ta kokarin bin hanyar
sulhu ta hanyar aikawa da wasiku zuwa ga Mu'awiyya da ya janye wannan tawaye da yake yi don gudun zubar da jinin musulmi, amma ina Mu'awiyya ya ki amincewa da haka.
Don haka sai duka bangarorin biyu suka shirya sojojinsu don fuskantar juna. Sojojin share fage na Imam Ali (a.s) dai suna karkashin jagorancin Malik al-Ashtar su kuwa na Mu'awiyya suna karkashin jagorancin Abul Aawar Salmi ne. Da farko dai
sojojin Mu'awiyyan sun kai hari ga sojojin Imam Ali (a.s), to amma sun fuskanci gagarumar tirciya daga wajen sojojin Ali karkashin jagorancin Malik, inda suka tilasta musu komawa da baya. Ganin haka sai jagoran sojojin Mu'awiyya ya bukaci sojojin nasa da su mamaye bakin kogin
Furat don hana sojojin Malik shan ruwa. Ko da Mu'awiyya ya iso wajen ma ya ji dadin hakan, inda ya kara adadin sojojin da za su yi gadin bakin ruwan. Wannan ya sanya sojojin Ali (a.s) cikin tsananin wahala saboda ruwan da suke da shi ya kare. To sai dai a daidai lokacin da Mu'awiyya
yake farin cikin wannan mataki da ya dauka, Amr bn al-Aas, daya daga cikin na kurkusa da Mu'awiyyan bai amince da hakan ba saboda wasu dalilai da za mu gani nan gaba. Ba a jima cikin wannan hali ba sai ga Imam Ali (a.s) da kansa ya iso wajen, ganin
halin da ake ciki sai ya aiki Sasaa bn Sauhan al-Abdi, daya daga cikin sahabbansa, da wasika zuwa ga Mu'awiyya yana mai ce masa:
"Mun zo nan ne da nufin kokarin sasanta tsakani da hana zubar da jinin musulmi, muna fatan za mu magance sabanin da ya shiga tsakaninmu cikin ruwan sanyi ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna. To sai dai mun ga kai da mutanenka kun fara amfani da makamai kafin amfani da sauran
hanyoyi, kuma ka hana mutanena ruwa. Ka umarci (sojojinka) da su janye, don mu fara tattaunawa. Duk da cewa idan ba abin da kake so sai yaki, to mu fa ba mu tsoron hakan".
Bayan samun wannan wasika, sai Mu'awiyya ya kira jami'ansa don shawarar abin da ya kamata. Kusan dukkansu dai sun yi amanna da cewa su yi amfani da wannan dama da suka samu kuma su yi kunnen uwar shegu da wannan wasika. Mutum guda ne kawai ya ke da wani ra'ayi na daban, shi ne kuwa
Amr bn al-Aas, yana mai ce musu yin hakan kuskure ne don kuwa Ali ba ya so ne ya fara yaki da kansa, don haka ne suka yi shiru da kuma aiko da wannan wasika. Kada ku yi tsammanin za su janye don kun mance da wannan wasika da kuma ci gaba da hana su ruwa, don idan suka fara yaki sai sun kore
ku daga bakin tafkin cikin wulakanci. To sai dai ina mafi yawan jami'an sun yi imanin cewa ci gaba da hana sojojin Imam Ali (a.s) ruwa zai raunana su da tilasta musu janyewa, wannan ma dai shi ne ra'ayin shi kansa Mu'awiyyan. Koda wakilin Imam Ali (a.s) ya bukaci amsar wasikar da ya
zo da ita sai Mu'awiyya ya ce masa ya ci gaba da dakatawa yana kan tunani ne, inda kuma ya ci gaba da umartan sojojinsa da su kara kaimi wajen gadin bakin tafkin.
Ko da Imam Ali (a.s) ya ga dai wadannan mutane ba a shirye suke su amince da batun tattaunawa ba, sai ya tsara gaba ga mabiyansa yana mai umartansu da su tashi su karbo hakkinsu, yana mai ce musu:
"Wadannan mutane dai sun fara wuce gona da iri, sun bude kofar fitina da kuma tarbarku da gaba. Suna cikin kishirwan yaki da jinananku. Sun hana ku ruwa. Don haka ya rage muku ku zabi guda daga cikin wadannan hanyoyi guda biyu, wanda ba na uku: Ko dai ku yarda da wulakanci da zalunci
da ci gaba da zama cikin kishirwa, ko kuma ku shayar da takubbanku da kazamin jininsu don ku kawo karshen wannan kishirwa taku da ruwa mai zaki. Mutuwa dai ita ce rayuwa cikin wulakanci; kana rayuwa kuma ita ce ka yi nasara ko da kuwa mutum zai ba da jininsa ne. A hakikanin gaskiya dai
Mu'awiyya ya tara wasu jahilan mutane ne, kuma yana amfani da wannan jahilci nasu don sanya kawukansu cikin hatsari".
Wannan jawabi na Ali (a.s) dai ya motsa zukatan sojojin nasa, don haka sai suka fito suka fuskanci sojojin abokan gaba, inda suka kore su da kuma kame gurin.
Ganin haka sai Amr bn al-Aas (wanda tuni daman ya fahimci hakan zai faru) ya ce wa Mu'awiyya 'A halin yanzu idan Ali da mabiyansa suka saka muku da abin da kuka yi musu me za ku iya yi? Shin kuna tsammanin za ku sake iya kwace gurin ne?. Sai Mu'awiyya ya ce masa 'To me kake tsammain Ali zai yi
da mu? Sai Amru ya ce masa: 'Lalle na san ba zia hana ku ruwa ba, don kuwa bai zo nan don haka ba'.
Daga nan sai sojojin Ali (a.s) suka bukaci umarninsa da su hana abokan gaba ruwa kamar yadda suka yi musu. Amma ina Ali (a.s) ya ki amincewa da hakan yana mai cewa hakan ai aikin jahilai ne. Ya ci gaba da cewa zai yi ta kokarin ganin an yi sulhu, idan kuwa sun ki to zai yake su.
Hakan kuwa ya faru, don sai ga sojojin Mu'awiyya nan suna zuwa wajen don diban ruwa da yin amfani da shi ba tare da wata tsangwama ko gori ba.
|
||||