|
|
| |||
Daga: Muhammad Awwal Bauchi IRIB-Tehran - I.R.of Iran awwalubauchi@yahoo.com ________________________ Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata da Manzonsa da dukkanin Alayensa. Allah Ya yi gaskiya a yayin da ya ce: "Sa'an nan karshen wadannan da suka aikata mugun aiki ya kasance mafi muni, saboda sun karyata ayoyin Allah, kuma suka kasance suna izgili da su". (Surar Rum:10). Ya Yazid, shin kana tsammani ka kwace kasa da sama ne daga gare mu don ana yawo da mu kamar yadda ake yawo da fursunoni, sannan kuma mu wulakantattu ne a wajen Allah kai kuma mai daukaka? Saboda wannan nasara ta zahiri ne da ka samu ya sa kake alfahari da dagawa, kana mai tsammanin ka sami wata kyauta ce ta duniya kuma lamurranka sun daidaita haka nan kuma mulkinka ya dawo hannunka. To amma ka dakata kadan, kada ka yi farin ciki. Shin ka mance da fadin Allah Madaukakin Sarki ne cewa: "Kuma kada wadanda suka kafirta su yi zaton cewa, lalle ne, jinkirin da Muke yi musu alheri ne ga rayukansu. Muna yi musu jinkirin ne domin su kara laifi kawai, kuma suna da azaba mai wulakantarwa". (Surar Al'Imrana: 178). Ya kai dan sakakku! Shin wannan shi ne adalcinka, ka bar 'ya'yaye da kuyanginka cikin sutura amma ka sanya ana yawo da 'ya'yan Manzon Allah titi-titi cikin mawuyacin hali a matsayin fursunoni. Ka ci mana mutumci ta hanyar bayyanar da fuskokinmu. Sojojinka sun dinga yawo da mu daga gari zuwa gari, dukkan nau'oi na mutane, mazauna duwatsu da bakin teku suna kallonmu. Na kurkusa da na nesa, wulakantattu da madaukaka dukkansu suna kallonmu alhali kuwa muna cikin wani irin hali da babu wani namiji tare da mu da zai taimaka mana ko ba mu wata gudummawa. Ya Yazid, duk wani abin da ka aikata yana nuni ne da tawayenka ga Mahalicci da kuma rashin imaninka da Manzo (s.a.w.a), Littafin Allah da kuna Sunnar da Annabi ya zo da ita. Lalle ayyukanka ba za su kasance abin mamaki ba, don kuwa duk mutumin da kakanninsa suka ci hantar tsarkakakkun bayi, wanda namansa ya ginu daga jinin shahidai, wadanda suka yaki shugaban dukkan Annabawa, ba abin mamaki ba ne in ya wuce dukkan larabawa wajen kafirci, aikata sabo da kuma kiyayya da Allah da ManzonSa (s.a.w.a). Ka tuna fa wadannan munanan ayyuka da ka aikata sun samo asali ne daga kafirci da kuma kullin da kake da shi saboda kakanninka da aka kashe a Badar. Hakika duk mutumin da ya sanya idanuwan kiyayya da gabansa a kanmu ba zai yi kasa a gwuiwa wajen aiwatar da wannan kiyayya a kanmu ba. Lalle ya tabbatar da rashin imaninsa da kuma bayyanar da shi da harshensa lokacin da ya ce cikin farin ciki: "Na kashe 'ya'yan Manzon Allah da kuma mayar da iyalansa fursunoni" da kuma fatan da kakanninsa sun rayu su ga wannan nasara da ya cimma don su ce 'Ya Yazid, kada hannayenka su rasa wannan karfi, lalle ka dau mana fansa a madadinmu'. Ya Yazid, shin kana dukan lebban Imam Husain ne da sandanka a gaban jama'a bayan kuwa Manzon Allah (s.a.w.a) ya sha sumbantan wadannan lebba, amma duk da hakan kana cikin farin ciki da annashuwa. Na rantse da Allah, lalle ka kara mana zafin ciwonmu da kuma cutar da mu gaba daya ta hanyar kashe Shugaban matasan Aljanna, dan shugaban larabawa (Ali) kana kuma tauraron iyalan Abdul-Mutallib mai haske. Ta hanyar kashe Husain bn Ali (a.s), lalle ka kusa isa ga makoman kakanninka marasa imani da Allah. Kana bayyanar da wannan aika-aika da ka aikata cikin alfahari da kuma fatan cewa idan kakannin naka suka ga aikin naka za su yarda da shi da kuma yi maka addu'an kada hannunka ya raunana. Ya Allah, Ka karbo mana hakkinmu, Ka dau mana fansa akan wanda ya zaluncemu, Ka nuna fushinKa ga wanda ya zubar da jininmu. Ya Yazid! Ka aikata duk abin da kake so, amma ka kwana da sanin cewa ka yanka jiki da namanka ne da kanka gunduwa-gunduwa. Nan gaba kadan za a gabatar da kai gaban Manzon Allah (s.a.w.a), lalle nauyin mummunan aikinka na zubar da jinin iyalansa da kuma wulakantasu zai gagare ka dauka. Za a kaika inda za a kaika ne a idanuwan iyalan gidansa, inda za a dau fansa kan azzalumai da kuma azabtar da makiya, "Kada ka yi zaton wadanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne. A'a rayayyu ne su a wajen Ubangijinsu, ana ciyar da su. Suna masu farin ciki saboda abin da Allah Ya ba su na daga falalarSa..", (Surar Al'Imrana: 169-170). Hakika Allah ya isa ya hukumtaka, Manzon Allah kuma ya kasance mai husuma da kai kana Jibrilu kuma shi ne mai taimakonmu. Lalle da sannu wadanda suka dora ka akan musulmi da kuma wahalar da su za su ga abin da ke jiransu, kuma lallai makomar azzalumai ta munana ta zama makoma. Ya Yazid! Ba wai ina maka wadannan maganganu da kuma nusar da kai irin azabar da ke jiranka don ko ka yi nadama kan abin da ka aikata ba ne, a'a, don kuwa kai kana daga cikin mutanen da zukatansu suka kekashe, wadanda rayukansu da jikkunansu suka tarbiyyantu da sabon Allah, wadanda kuma suke karkashin la'anar Manzon Allah (s.a.w.a). Lalle kai kana daga cikin mutanen da Shaidan ya yi musu tambari a kan zukatansu, ba abin da suke haifarwa in ban da sharri. Babban abin mamakin shi ne kisan gillan da 'ya'yan sakakkun masu sabo suka yi wa bayin Allah, 'ya'yan Annabawa da wasiyyai. Hannayensu sun zubar da jininmu kana kuma namanmu ya kasance musu kalace. Lalle muna jin zafi ga wadanda aka bar gawawwakinsu a yashe a fagen daga ba tare da an bisne su ba. Kai Yazid, idan har kana tunanin cewa wannan abin da ya same mu a matsayin wata nasara gare ka, to lallai za ka dandana kudanka kan hakan a lokacin da ba abin da za ka gani face abin da ka aikata, don kuwa Ubangijinka ba ya zaluntar bayinSa. Allah Shi ne abin dogaronmu kuma Shi ne kawai muka mika burinmu gare Shi. Ka yi dukkan makircin da ka ke iyawa, sannan ka yi dukkan kokarin da za ka iya, amma dai wallahi ba za ka iya shafe ambatonmu ba da kuma dushe haskenmu, haka nan kuma ba za ka kawar da wannan wulakancin da kake ciki ba. Shin akwai wani abin da ya rage wa kalamanka in ba rauni ba, haka nan kuma ranakunka face 'yan kididdigaggu ba. Lalle ka kiyaye ranar da mai sanarwa zai sanar da la'anar Allah a kan azzalumai.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, Wanda ya cika wa na farkonmu da sa'ada da kuma gafara, kana na karshenmu kuma da shahada da rahama, muna rokon Allah da ya cika musu da lada Ya kuma kara musu Ya kuma kyautata mana halifanci, don kuwa Shi Mai rahama ne, kuma lalle Allah Ya isar mana kuma madalla da wakilcinSa(1)".
____________ (1)- Maktal al-Husain na Abdurrazak al-Musawi al-Mukarram, shafi na 358 da 359. |
||||