 |
Maganganun Imam Ali (a.s) Kan Azumi
-
Amirul Muminina Ali (a.s) ya ce:"Barcin mai azumi ibada ce, shirunsa ma tasbihi ne, addu'arsa
karbabbiya ce, haka nan kuma za a rubanya ayyukansa. Hakika akan amsa kiran mai azumi a ya yi buda baki(1).
- Amirul Muminina Ali (a.s) Ya ce: "Allah Ya farlanta azumi ne don jarraba ikhlasin bayinSa(2)".
- Amirul Muminina Ali (a.s) Ya ce:"Azumi shi ne nesantar abubuwan da Allah Ya haramta, kamar yadda kuma mutum ya ke
nesantar abinci da abin sha(3)".
- Amirul Muminina (a.s) Ya ce:"Azumin (hana) zuciya daga tunanin aikata laifi, shi ya fi daga azumin ciki daga cin abinci(4)".
- Amirul Muminina Ali (a.s) ya ce: "Azumin zuciya ya fi azumin harshe, haka nan kuma azumin harshe ya fi azumin ciki(5)".
- Amirul Muminina Ali (a.s) Ya ce: "Azumin jiki shi ne kamewa daga abinci, cikin son mutum da yardarsa,yana mai tsoron azaba da kuma
kwadayin lada, haka nan kuma azumin ruhi shi ne kamewan hawasai guda biyar daga dukkan sabo, da kuma tseratar da zuciya daga dukkan hanyoyin sharri(6)".
- Amirul Muminina Ali (a.s) Ya ce: "Ina gargadinku, a cikin watan Ramalana, da yawaita addu'a da istigfari. Don ita addu'a (a wannan wata)
ta kan kawar muku da bala'i, shi kuwa istigfari ya kan shafe muku zunubanku ne(7)".
____________
(1)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 93, shafi na 360.
(2)- Nahjul Balagah, hukm na 252.
(3)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 96, shafi na 294.
(4)-Gurarul Hikam na Imam Ali (a.s).
(5)- Kamar na sama.
(6)- Kamar na sama.
(7)- Wasa'il, juzu'i na 4, shafi na 223.
|