 |
Maganganun Manzon Allah (s) Kan Azumi
-
Manzon Allah (S) Ya ce wa Jabir bn Abdullahi:"Ya Jabir, wannan wata na
Ramalana ne, duk wanda ya azumci ranansa, sannan kuma ya mike (don ibada) da darensa, ya kiyaye cikinsa
da farjinsa, sannan kuma ya kiyaye harshensa, to ya fita daga cikin zunubi kamar yake fita daga watan(1).
- Manzon Allah (s) Ya ce: "Hakika watan Azumi wata ne mai girma, Allah Ya kan
rubanya kyawawan aiki a cikinsa, kana kuma ya shafe munana, Ya kuma daukaka darajoji. Duk wanda ya yi sadaka
a cikin watan Ramalana, Allah Zai gafarta masa, haka nan kuma duk wanda ya kyautata wa abin da hannun damansa
ya mallaka (bayi) a cikin watan, Allah Zai gafarta masa, haka nan ma duk wanda ya kyautata ayyukansa a cikin
watan, Allah Zai gafarta masa, haka kuma wanda ya hadiye fushinsa a cikin watan, Allah Zai gafarta masa, sannan
kuma wanda ya sada zumunta, Allah Zai gafarta masa"(2).
- Manzon Allah (s) Ya ce:"Hakika wannan watan naku (watan Ramalana) ba kamar sauran
watanni ya ke ba: Don shi idan ya zo muku, ya kan zo ne da albarkoki da kuma rahama, idan kuma zai tafi, ya kan
tafi ne da zunubanku da kuma yi muku gafara....(3)".
- Manzon Allah Ya ce:"Mafi girman aiki a cikin wannnan wata shi ne kamewa daga abubuwan
da Allah Ya haramta(4)".
- Yayin da aka tambayi Manzon Allah (s) cewa: 'Mene ne ya ke nisanta Shaidan daga gare mu, sai Ya ce:
"Azumi don Allah, ya kan bakanta fuskansa, sadaka kuwa ta kan karya kashin bayansa, haka
nan kuma soyayya don Allah da kuma da kuma kula da ayyukan kwarai sukan lalata asalinsa, haka nan kuma neman gafara ya kan
yanke jijiyar jininsa(5)".
- Manzon Allah (s) Ya ce: "Duk wanda ya azumci watan Ramalana, ya kiyaye farjinsa da harshensa
ya kuma kiyaye cutar da mutane, to Allah Zai gafarta masa zububansa wanda ya yi da wanda ya jinkirta Ya kuma 'yantar da shi
daga wuta ya kuma halalta masa gidan dawwama (aljanna),.....(6)".
- Manzon Allah (s) ya ce: "Watan Ramalana, wata ne da Allah Ya wajabta muku yin azuminsa, duk wanda
ya azumce shi yana mai imani da burin samun lada, za a shafe masa zunubinsa kamar ranar da mahaifiyarsa
ta haife shi(7)".
- Manzon Allah (s) ya ce: "Babu wani mumini da zai azumci watan Ramalana don neman lada, face Allah
Madaukakin Sarki ya wajabta masa wasu abubuwa guda bakwai:
- Zai fitar da haramun din da ke jikinsa
- Ba za a nisanta shi daga rahamar Allah ba.
- Zai kasance ya yi kaffara wa zunuban Babansa Adamu.
- Allah Zai saukaka masa zafin mutuwa.
- Zai kiyaye shi daga yunwa da kishirwan ranar lahira.
- Allah Zai kare shi daga wuta.
- Allah Zai ciyar da shi da abincin Aljanna(8)".
.
- Manzon Allah (s) Ya ce: "Mai azumi yana cikin ibada ne koda kuwa yana barci ne a kan gadonsa, matukar
dai bai ci naman (giba) musulmi ba(9)".
- Manzon Allah (s) ya ce: "Aljanna tana da wata kofa da ake kira Rayyan babu wanda zai shiga (aljannan)
ta wannan kofar sai masu azumi(10)".
____________
(1)- Wasa'il al-Shia, na Hurul Amuli, juzu'i na 4, Mujalladi na 7, Kitab al-Sawm, Shafi na 227.
(2)- Kamar na sama, shafi na 226.
(3)- Kamar na sama.
(4)-Kamar na sama, shafi na 228.
(5)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 69, shafi na 403.
(6)- Wasa'il, mujalladi na 7, Kitab al-Sawm, shafi na 174.
(7)- Kamar na sama, shafi na 177.
(8)- Miftahul Janna, na Muhsin Amin, mujalladi na 3, shafi na 117.
(9)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 96, shafi na 247.
(10)- Kamar na sama, shafi na 252.
|