 |
Maganganun Imam Khumaini (r.a) Kan Azumi
- Imam Khumaini (r.a): "Ya Allah! Ka ba mu daman zamantowa bakinKa da suka dace su
zama bakin naKa a cikin wannan wata da Ka ke kiran mutane zuwa bakuntanKa.
- Imam Khumaini (r.a): "Abin da yafi komai shi ne mutum ya yi kokarin gyara kansa
cikin wannan wata na Ramalana, hakika mu muna bukatuwa da gyaran kai, muna bukatuwa da tsarkake zukatanmu, lalle
har zuwa karshen rayuwarmu muna bukatuwa da hakan.
- Imam Khumaini (r.a):"Mu yi kokarin banbance wannan wata (na Ramalana) da sauran
watanni, mu yi kokarin mu yi abin da InshaAllah za mu samu daman ganin Lailatul Kadri.
- Imam Khumaini (r.a): "Wannan wata mai alfarma (na Ramalana) takun farko ne na
Lailatul Kadri, wanda ya tara dukkan gaskiya da ma'anoni a cikinsa.
- Imam Khumaini (r.a):"Matukar dai mu ka san girma da kuma ba da muhimmanci wa
Lailatul kadri da kuma lokacin da Mala'iku suke sauka a wadannan darare, to za mu samu daban saukaka
dukkan matsalolinmu.
|