Maganganun Sauran Ma'asumai (a.s) Kan Azumi

  1. Nana Fatima al-Zahra (a.s) ta ce: "Allah Ya farlanta azumi ne don tabbatar da ikhlasi(1)"..
  2. Nana Fatima al-Zahra (a.s) ta ce: "Wani amfani mai azumi zai samu daga azuminsa, matukar dai bai kare harshensa, jinsa, ganinsa da kuma gabobinsa (daga abubuwan da aka haramta) ba(2)"..
  3. Imam Hasan (a.s), yana gaya wa wani mutum cewa:"Ya Aba Harun, duk wanda ya azumci watanni goma na Ramalana a jere, zai shiga aljanna(3).
  4. Imam Husaini (a.s), yayin da aka tambaye shi dalilin da Ya sa Allah Madaukakin Sarki Ya farlanta azumi wa bayinSa, ya ce: "Don masu arziki su ji zafin yunwa, don ta hakan kuma su taimaka wa mabukata(4).
  5. Imam Muhammad Bakir (a.s) ya ce:"Allah ba Zai tambayi bawa akan salla ba in ban da ta farilla, haka nan kan wata sadaka in ban da zakka, haka nan kuma kan azumi in ban da na watan Ramalana(5)".
  6. Imam Sadik (a.s) ya ce:"Komai yana da zakkansa, to zakkan jiki shi ne azumi(6)".
  7. Imam Sadik (a.s) Ya ce:"Hakika watan Ramalana farilla ne daga farillolin Allah Madaukakin Sarki(7)".
  8. Imam Sadik (a.s) Ya ce: "Azumi kariya ne daga wuta(8)".
  9. Imam Sadik (a.s) ya ce: "Mai azumi yana da farin ciki gudabiyu: Farin ciki yayin buda baki, da kuma farin ciki yayin saduwa da Ubangijinsa(9)".
  10. Imam Ridha (a.s) ya ce: "Hakika an umurceku ne da yin azumi don kusan zafin yunwa da kuma kishirwa. Kana kuma don mai azumi ya kasance mai tsoro, kaskantar da kai, zalili, mai neman lada, masani kana mai hakuri kan abin da ya same shi na yunwa da kishirwa, don ya samu lada daga kamewan da ya yi daga abin sha'awa, sannan hakan kuma ya zamanto musu wa'azi da kuma kwadaitarwa zuwa ga aikata abubuwan da suka hau kansu, kuma mai shiryarwa zuwa ga ajali, kuma su san zafin hakan akan fakirai da marasa shi, kuma su fitar da abin da Allah Ya umurce su da su fitar daga dukiyarsu(10)"..
  11. Imam Ridha (a.s) ya ce: "Lalle watan Ramalana wata ne na albarka, wata ne na rahama, wata ne na gafara, wata ne na tuba kana kuma wata ne na komawa (zuwa ga Ubangiji), don haka idan ba a gafarta wa mutum a cikin wannan wata ba, to a wani watan ne za a gafarta masa?!(11)"..





    ____________
    (1)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 96, shafi na368.
    (2)- Kamar na sama, shafi na 295.
    (3)- Wasa'il al-Shia, na Hurul Amuli, juzu'i na 4, Mujalladi na 7, Kitab al-Sawm, Shafi na 176.
    (4)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 96, shafi na 387.
    (5)- Wasa'il, mujalladi na 7, Kitab al-Sawm, shafi na 177.
    (6)-Kamar na sama, shafi na 3.
    (7)- Kamar na sama, shafi na 176.
    (8)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 96, shafi na 256.
    (9)- Man la yahdhuruhul Fakih, juzu'i na 2, shafi na 45.
    (10)- Wasa'il, mujalladi na 7, shafi na 4.
    (11)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 96, shafi na 341.