 |
Maganganun Jagora- Ayatullah Khamene'i (H)(1) Kan Azumi
- Ayatullah al-Uzma Khamene'i: "Azumi ya kan sanya kofofin hikima a zukata. A lokacin
da hikima ta kasance jagoran zuciya, to hasken sani da yakini zai kasance tare da mutum...kuma hakan zai saukaka
wa mutum dukkan wahalhalun rayuwa.....
- Ayatullah al-Uzma Khamene'i: "Azumi komawa ga Allah Madaukakin Sarki ne, kuma irin
zikirori da addu'o'in da ake yi a wannan wata, wadanda kuma a lokuta da dama zuciya ta kan koma gare su, suna daga cikin
taburman shiriya ta Ubangiji, don haka ku yi kokarin amfanuwa da wannan taburma don ku shiryar da kanku.
- Ayatullah al-Uzma Khamene'i:"Watan Ramalana wata dama ce da take ba wa mutum karfin gwada
nesantar sabon Allah. Hakika rashin aikata zunubi yana bukatuwa da wani karfi da kuma kudura, kuma daga cikin zunuban da
dole ne mai azumi ya nesance su har da giba da bata sunan sauran mutane.
- Ayatullah al-Uzma Khamene'i: "Hakuri da yunwa, kishirwa da kuma nesantar soyace-soyacen zuciya
a watan Ramalana na daya daga cikin nau'o'in yarda, wacce take ba wa dan'Adam ikon gudanar da nauyace-nauyacen da suka
hau kansa.
- Ayatullah al-Uzma Khamene'i::"Ya abin kauna ta! muna cikin watan Ramalana ne; ku dage da addu'a,
ku san girman addu'a, haka nan kuma ku san girman lokaci, ku ba da himma wajen damuwa da manya-manyan bukatu, bukatun al'umman
musulmi, bukatun kasashen musulmi, bukatun al'ummarku, bukatun ku kanku, duk wadannan ku nemi su a wajen Allah Madaukakin Sarki,
cikin kaskantar da kai da mika wuya gare Shi.
____________
(1)- Allah Ya kare shi Ya kuma kara masa tsawon rai.
|