An wajabta azumi ne don musulmi su sami daman samun kusanci da Ubangijinsu Madaukakin Sarki wanda shi ne koluluwan burin dukkan kowani cikakken mutum. Mafi giman hanyan da ake samun wannan kusanci kuwa shi ne ta hanyar jin tsoron Ubangiji, wato aikata dukkan abin da ya yi umurni da shi da kuma hanuwa da dukkan abin da Ya hana, kamar yadda muka gani a karshen wannan aya da muka kawo a sama. Don haka azumi dai yana nufin, kamewa daga ci da sha tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwan rana. To sai dai kuma malamai sukan yi karin bayani cewa ba wai kawai kamewa daga wadannan abubuwa shi ne kawai azumin ba, face dai kamewa daga dukkan abubuwan da Allah Ya haramta, na daga kallo, ji da dai sauransu. To duk wanda ya yi hakan, ya kuma mika wuyansa kacokam ga Allah Madaukakin Sarki, ya cika azuminsa cif-cif. An samo hadisi cewa: Duk wanda ya ke azumi, to amma bai kare harshensa daga fadin karya ba, bai hana kansa aikata munanan abubuwa ba, to ba abin da ya yi face jin kishirwa. To kenan dole ne mu kiyaye irin wadannan abubuwa yayin da muke azumi. Baya ga haka kuma, bisa la'akari da cewa a cikin wannan wata ne aka saukar da Alkur'ani Mai Girma ga Manzon Allah (s.a.w.a), akwai bukatan mai azumi ya kula wajen karanta wannan Littafi don samun karbuwar aiki da kuma haskaka zuciya. Ruwayoyi da dama sun bayyana irin falaloli da ladan da ke cikin karatun Alkur'ani a cikin wannan wata mai alfarma. Wasu hadisan ma sun ce karanta aya guda ta Alkur'ani a wannan wata, daidai ya ke da karanta dukkan Alkur'ani cikin wani wata wanda ba wannan din ba. Don haka wannan wani garabasa ce da aka yi wa al'umman Annabi (s.a.w.a) da babu wata al'umman da aka yi mata. Abin da kawai ya rage mana shi ne mu yi amfani da wannan dama wajen kalato wannan garabasa da kuma ribantuwa da ita. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya amfanar da mu cikin wannan wata, kuma ya sanya mu cikin bayinSa da zai 'yanta a cikin wannan wata mai alfarma. |