RASHIN LAFIYA DA KUMA HANIN LIKITA

Wasu likitoci 'yan ko a kula sukan hana marasa lafiya yin azumi wai saboda cutarwa, to shin maganar irin wadannan likitoci hujja ce?
Idan har likita ba amintacce ba ne, kuma maganarsa ba ta haifar da nitsuwa ba, kana ba ta sa an ji tsoron aukuwar cuta ba, to ba'a lura da maganarsa.

Wani likitan ido ya hana ni yin azumi inda yake ce mini ba ya halatta ka yi azumi saboda ciwon idon da yake tare da kai, to amma duk da haka sai na fara, to amma na dinga samun matsaloli kala-kala, ta yadda a wasu ranakun zan yi azumin ba tare da jin wani ciwo ba, a wasu lokutan kuma na kan ji ciwo da yamma, to amma tattare da taraddadin da nake da shi kan ko in bar azumin ko kuma in hakura da zafin ciwo na kasance na kan wuce da azumi har faduwan rana, to tambaya a nan ita ce, shin tun farko ma wajibi ne in yi azumi?A ranakun da nake yin azumi a halin ina kokwanton zan iya kaiwa har faduwar rana ko ba zan iya ba to zan ci gaba da azumi ko aa? Kana kuma yaya niyyata za ta kasance?
Idan har ka sami nitsuwa da kuma yakini kan maganar wani likita mai rikon addini, amintacce na cewa azumi zai cutar da kai, ko kuma ka zan kana tsoron cutarwa ga idon naka saboda azumi, to bai wajaba a gare ka ba, kai bai ma halatta ka yi azumin ba, kana ba ya inganta ka yi niyyar azumin idan kana tsoron zai cutar da kai, to amma idan ba ka tsoron wata cutarwa to babu matsala ga hakan, to amma kuma ingancin azumin naka ya ta'allaka ne da rashin cutarwar a hakika.

A shekarar da ta wuce wani kwararren likita ya yi min tiyata a koda ta biyu inda daga baya ya hana ni yin azumi har zuwa karshen rayuwa ta, to amma a halin yanzu ba ni jin wata matsala, ina ci ina sha kamar da, ba na jin wani ciwo, to mene ne ya wajaba a gare ni?
Idan har kai kanka ba ka jin wani tsoron cewa azumin zai cutar da kai, kana ba ka da wata hujja ta shari'a a kan hakan to wajibi ne ka yi azumi.

Idan likita ya hana mutum yin azumi, to shin wajibi ne ya lizimtu da wannan magana tasa? Tattare da cewa wasu likitocin ba sa da masaniya kan hukunce-hukuncen shari'a.
Idan har mutum ya samu nitsuwa da wannan magana tasa cewa azumi zai cutar da shi, ko kuma a sanadiyyar maganar likita sai ya ji tsoro kan cewa azumin zai cutar da shi, ko kuma hakan ya samu (wato tsoron cutarwa) daga wani sababi wanda masu hankali suka yarda da shi, to a wannan hali azumi ba wajibi ba ne a kansa.