GANGANTA ZAMA CIKIN JANABA

Idan mutum ya zauna cikin janaba (saboda wasu wahalhalu) har aka kira sallar asuba, to shin ya halatta ya yi azumi a wannan ranar?
Babu wata matsala ga azuminsa idan dai azumin ba na Ramalana ko ramakonsa ba ne, to amma a azumin Ramalana ko ramakonsa, idan har ba zai iya wanka ba to dole ne ya yi taimama, idan har ya bar taimama, to azuminsa ba ya inganta.

Idan ya yi azumi na wasu raneku alhalin yana cikin janaba, ba tare da ya san cewa tsarki daga janaba yana daga cikin sharadin azumi ba, to shin wajibi ne ya yi kaffaran wadannan raneku da ya yi azumi a cikinsu da janaba, ko kuma ramakonsu kawai ya wadatar?
Idan mutum ya wayi gari da janaba-alhali yana sane da cewa yana da janaba-to amma ya jahilci wajibcin yin wanka ko taimama (kafin fitowar alfijir), to wajibi ne a gare shi bisa ihtiyati ya yi kaffara bayan ramako, sai dai idan jahilcin nasa ba'a sakacinsa ba ne to a nan ba wajibi ba ne ya yi kaffara, ko da yake ihtiyat ne yin kaffarar.

Mutum ne ya tafi bakunta cikin watan Ramalana, to cikin tsakiyan dare sai ya yi mafarki, to dan saboba shi bako ne ba shi da wasu tufafi, dan haka sai ya kuduri aniyar yin tafiya washe gari dan gudu daga azumin, to bayan kiran sallar asuba sai ya fito dan yin wannan tafiya ba tare da aikata wani abin da ke bata azumi ba, to tambaya a nan ita ce: Shin kudura anniyar tafiya a wajen wannan mutum yakan sauke masa yin kaffara ko kuwa?
Kudura anniyar tafiya cikin dare kawai ba ya wadatarwa haka kuma yin tafiya da rana bai wadatarwa wajen kaffara daga gare shi idan har ya wayi gari cikin janaba-tattare da cewa ya san yana da janabar- ba tare da ya gaggauta yin wanka ko taimama kafin fitowar alfijir ba.

Shin ya halatta ga wanda ba shi da ruwa ko kuma dai wasu uzurorin na daban da suke hana wankan janaba (banda kurewar lokaci) da ya yi janaba da gangan cikin watan Ramalana?
Hakan yana halatta a gare shi idan har abin da ya hau kansa shi ne taimama, kana kuma yana da cikakken lokaci na yin taimamar bayan da ya yi janabar.

Mutum ne cikin watan Ramalana ya farka gabannin kiran sallar asuba, to amma bai san cewa ya yi mafarki ba, sai ya koma da barcinsa, to sai yayin da ake kiran sallar asuba ya gane cewa ya yi mafarki kuma ya tabbatar da cewa mafarkin nasa ya yi shi ne kafin kiran sallar, to mene ne hukuncin azuminsa?
Idan har bai gano hakan (wato janabar) ba kafin kiran sallar asuba din, to azuminsa ya inganta.

Idan mutum ya farka daga barci bayan kiran sallar asuba na watan Ramalana to sai ya ga ya riga ya yi mafarki, to amma sai ya ci gaba da barcinsa har zuwa bayan fitowar rana (ba tare da ya yi sallar asuba ba) ya jinkirta yin wankan har zuwa lokacin sallar azahar sannan ya yi wanka ya yi salla to shin mene ne hukuncin azuminsa?
Azuminsa ya inganta, jinkirta yin wankan har zuwa kiran sallar azahar ba ya cutarwa.

Idan mutum ya yi shakka kafin kiran sallar asuba na watan Ramalana kan cewa shin ya yi mafarki ko kuma, a a sai dai bai kula da wannan shakka tasa ba, ya ci gaba da barcinsa, to sai dai da ya farka bayan kiran salla sai ya ga ashe ya yi mafarkin kuma kafin kiran sallar, to mene ne hukuncin azuminsa?
Idan har a farkawar tasa ta farko bai ga wata alama na mafarki ba, kawai tsammani ne yake yi, ba tare da ya tabbatar ba to, azuminsa ya inganta, ko da kuwa daga baya ya bayyana masa cewa mafarkin ya yi shi ne kafin kiran sallar.

Idan mutum ya yi wanka da ruwa mai najasa a cikin watan Ramalana, to sai bayan sati guda sai ya tuna cewa ruwan da ya yi wankan da shi mai najasa ne, to mene ne hukuncin azumi da sallarsa cikin wannan lokaci?
Sallarsa batacciya ce wajibi ne ya sake ta, to amma azuminsa ya inganta.