KAFFARAR AZUMI

Shin bayar da kudi gwargwadon mudu na abinci ga fakiri dan ya sayi abincin da kansa (yayin kaffara) yana wadatarwa?
Idan har yana da nitsuwa kan cewa wannan fakirin zai wakilce shi ya sayi abincin da wannan kudi daga bisani ya mallaki abincin a matsayin kaffara, to babu wata matsala ga hakan.

Macen da aka dauke mata azumi saboda rashin lafiya, kuma ba ta samu daman rama azumin ba har watan azumi na gaba ya iso, to a irin wannan hali shin kaffarar yana kanta ne ko kuma yana kan mijinta?
A irin wannan hali wajibi ne gare ta ta ba da mudu na abinci a madadin kowace rana, kuma hakan bai hau kan mijinta ba.

Mutum ne yake da ramakon azumi na kwanaki goma, to sai a rana ta ashirin na watan sha'aban ya fara azumi, to shin a irin wannan hali zai iya karya azumin da gangan kafin "zawali" ko kuma bayanta? Kuma idan ya karya, to shin mene ne gwargwadon kaffararsa idan da ya karya azumin kafin zawali ne ko kuma bayansa?
A irin wannan hali ba ya halatta ya karya azumin da gangan, to amma idan ya karya da gangan, idan kafin "zawali" ne to babu kaffara a gare shi, idan kuwa bayan "zawali" ne, to kaffara ta hau kansa, wato ciyar da miskinai goma, idan kuwa hakan ya gagara, to sai ya yi azumin kwanaki uku.