Idan mutum yana azumi sai jini ya fito masa a bakinsa, to hakan ya bata masa azumi ? Hakan ba ya bata azumi, to amma wajibi ne ya kare wucewar jinin zuwa makogwaronsa. Wata rana na kasance cikin azumin watan Ramalana to amma bayan suhur sai ban wanke bakina da man goge baki ba to sauran abincin da ya saura a baki na ya wuce zuwa cikina, ba da so na ba to shin wajibi ne a rama azumin wannan rana? To idan har ba ka san da kasantuwar sauran abincin a jikin hakwaran naka, ba ko kuma ba ka san zai wuce zuwa cikin naka ba, kana kuma ba da gangan ka hadiya ba, ba kuma tare da mai da hankali ba to ba komai a gare ka dangane da wannan azumi naka. Muna bukatar ka yi mana bayani kan hukuncin yin allura yayin da mutum yake, cikin azumin watan Ramalana? Babu wata matsala ga yin allura sai dai in allurar ta kasance ta sanya wa maras lafiyan abinci ne, to bisa lhtiyati wajibi ne a nesance ta yayin da ake azumi.