Would you like to make this site your homepage? It's fast and easy...
Yes, Please make this my home page!
ADDU'O'IN RANAKUN RAMALANA (1-5)
|
 |
Rana ta Farko ta Watan
Ramalana
|

Ya Allah Ka sanya azumina a cikinsa (watan ramalana) ya zamanto
azumi (dominka), Haka nan kuma tsayuwa ta (don salla) ta zamanto tsayuwar
masu tsayuwa, Kuma ta farkar da ni a cikinsa daga barcin gafalallu, Ka
gafarta min, Ya Ubangijin talikai, Ka yi min afuwa, Ya Mai yafe wa masu
laifi. | | |
 |
Rana ta Biyu ta Watan
Ramalana | |
 |
|
 |

Ya Allah Ka kusantar da ni zuwa ga abin yardarka a cikin wannan wata,
sannan kuma Ka nesantar da ni daga abin da ba Ka so da kuam fushinKa a cikinsa,
Kuma Ka bani damar karanta ayoyinKa a cikinsa, da rahamarka, Ya Mai rahaman
masu rahama. | | |
 |
Rana ta Uku
Ta Watan Ramalana | |
 |
|
 |

Ya Allah, Ka arzurtani, a cikinsa, da hikima da kuma fadaka,
kana kuma ka nesantar da ni, a cikinsa, daga wauta da rashin sanin ya kamata,
Ka arzurta ni da rabo na daga dukkan alherorin da Ka saukar a cikinsa, da
karimcinKa, Ya Mai yawan karimci. | | |
 |
Rana Ta Hudu ta Watan
Ramalana | |
 |
|
 |

Ya Allah, Ka karfafani, a cikinsa, da karfin yi maka biyayya, Ka
dandana min, a cikinsa, zakin ambatonka, Ka arzurtani, a cikinsa, da daman
gode maka, da karimcinKa, Ka kiyaye ni, a cikinsa, da kiyayewanka da kuma suturcewanKa,
Ya Mafi ganin masu gani. | | |
 |
Rana Ta Biyar Ta Watan
Ramalana | |
 |
|
 |

Ya Allah, Ka sanya ni, a cikinsa, daga cikin masu gafara, Ka
sanya ni, a cikinsa, daga cikin bayinKa salihai masu tsantsaini, Ka
sanya ni, a cikinsa, daga cikin waliyanka makusanta, da tausasawanka,
Ya Mai yawan rahama. | | |