ADDU'O'IN RANAKUN RAMALANA (6-10)
Bismillah
Rana ta Shida ta Watan Ramalana

supplication

Ya Allah Kada Ka kama ni, a cikinsa, saboda wuce gona da iri cikin sabonKa, kuma kada ka buge ni da bulaliyar azabarKa, Ka nesantar da ni daga abin da zai kai ni ga fushinKa, don tausayawanka da kuma karfinka, Ya gayan masu tsammani.

Rana ta Bakwai ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka taimakeni, a cikinsa, da ikon yin azumi da kuma tsayawa (don ibada), Ka kuma nesantar da ni, a cikinsa, daga kura-kurai da kuma zunubai, Ka arzurtani, a cikina, da dawwamammen ambatonKa, Da taimakonKa, Ya Mai shiryar da wadanda suka bata.

Rana ta Takwas Ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka arzurtani, a cikinsa, da taimako da tausayawa wa marayu, da ciyarwa (ga mabukata), da yada zaman lafiya, da kuma zama da mutanen kirki ma'abuta mutumci, Ya matsugunin masu buri.

Rana Ta Tara ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka bani, a cikinsa, rabona na daga rahamarKa wacce take fadadda, Ka shiryar da ni zuwa ga bayyanannun hujjojinKa, Ka ja ni zuwa ga yardarKa wacce ta hada kome da kome, Saboda kaunarKa, Ya Makomar masoya.

Rana Ta Goma Ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka sanya ni, a cikinsa, daga cikin masu dogara (tawakkali) da Kai, Ka kuma sanya ni daga cikin wadanda suka sami nasara daga gareka, kuma Ka sanya ni, a cikinsa, daga cikin makusantanKa, da kyautatawanKa, Ya gayan masu bukata.