ADDU'O'IN RANAKUN RAMALANA (11-15)
Bismillah
Rana ta Sha Daya ta Watan Ramalana

supplication

Ya Allah!, ka sanya ni, a wannan rana, in so kyautatawa (abu mai kyau), Ka sanya ni, a cikinsa, in ki fasikanci da kuma sabo, kuma Ka haramta mini, a cikinsa, fushi da kuma wuta (Jahannama), da taimakonKa, Ya Mai taimakon masu neman taimako.

Rana ta Sha Biyu ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka yi min ado, a cikinsa, da sutura da kuma tsarkaka, Ka suturtani, a cikinsa, da suturan tabbaci da wadatuwa, Ka sanya ni, a cikinsa, in riki gaskiya da adalci, kuma Ka kare ni, a cikinsa, da dukkan abin da nake tsoronsa, da kariyarKa, Ya Kariyar masu tsoro

Rana ta Sha Uku Ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka tsarkake ni, a cikinsa, daga dauda da datti, Ka kuma sanya min, a cikinsa, hakuri da jurewa abubuwan da aka kaddara, kuma Ka arzurtani, a cikinsa, da takawa da kuma zama da mutanen kirki, da taimakonKa, Ya Masoyin marasa shi.

Rana Ta Sha Hudu ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Kada Ka kama ni, a cikinsa, da kuskuren da nayi, Ka kuma sanya ni, a cikinsa, in kasance mai rage kura-kurai, Kada kuma Ka sanya ni, a cikinsa, mattataran bala'i da annoba, da daukakanKa, Ya Daukakan Musulmai.

Rana Ta Sha Biyar Ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka arzurtani, a cikinsa, da biyayyan masu tsoro (Allah), Ka fadada, a cikinsa, kirjina da neman gafarar masu daukaka, da tsaronKa, Ya Matsugunin masu tsoro.