ADDU'O'IN RANAKUN RAMALANA (16-20)
Bismillah
Rana ta Sha Shida ta Watan Ramalana

supplication

Ya Allah! Ka sanya ni, a cikinsa, samun nasarar (zama da) mutanen kwarai, Ka kuma nesantar da ni, a cikinsa, daga ashararai, Ka shiryar dani, a cikinsa, da rahamarKa, zuwa ga makoma ta har abada, da UbangijintakanKa, Ya Ubangijin talikai.

Rana ta Sha Bakwai ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka shiryar da ni, a cikinsa, zuwa ga ayyuka na kwarai, Ka biya min, a cikinsa, bukatuna da kuma burace-buracena, Ya wanda ba Ya bukatuwa da bayani da tambaya, Ya Masanin abin da ke cikin kirazan talikai, Ka yi salati wa (Annabi) Muhammadu da tsarkakan Iyalansa.

Rana ta Sha Takwas Ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka farkar da ni, a cikinsa, saboda albarkar asuba, Ka haskaka zuciyata, a cikinsa, da annurin haskensa, Ka sanya dukkan gabobina zuwa ga bin tasirinsa, da haskenKa, Ya Mai haskaka zukatan masana.

Rana Ta Sha Tara ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

YA Allah! Ka ninka min albarkar da ke cikin wannan rana, Ka saukaka min hanyar isa ga alherorinsa, kada kuma Ka haramta min karbar ayyuka a cikinsa, Ya Mai shiryarwa zuwa ga bayyananniyar gaskiya.

Rana Ta Ashirin Ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka bude min, a cikinsa, kofofin aljanna, Ka kuma rufe min, a cikinsa, kofofin wuta, Ka kuma arzurtani, a cikinsa, da karatun Alkur'ani, Ya Mai saukar da nitsuwa a cikin zukatan muminai.