Would you like to make this site your homepage? It's fast and easy...
Yes, Please make this my home page!
ADDU'O'IN RANAKUN RAMALANA (21-25)
|
 |
Rana ta Ashirin da Daya ta Watan
Ramalana
|

Ya Allah! Ka nuna min, a cikinsa, hanyar isa ga yardarka, Kada
ba wa Shaidan, a cikinsa, daman cin nasara a kaina, Ka sanya aljanna ta kasance makoma da
kuma abin huta gare ni, Ya Mai biyan bukatun masu bukata. | | |
 |
Rana ta Ashirin da Biyu ta Watan
Ramalana | |
 |
|
 |

Ya Allah! Ka bude min, a cikinsa, kofofin falalolinKa, Ka saukar min,
a cikinsa, da albarkokinKa, Ka taimakamin, a cikinsa, zuwa ga tafarkin yardarKa, Ka
zaunar da ni, a cikinsa, cikin aljannarKa, Ya Mai amsar kiran mabukaci
(wanda ke cikin damuwa). | | |
 |
Rana ta Ashirin da Uku
Ta Watan Ramalana | |
 |
|
 |

Ya Allah! Ka wanke ni, a cikinsa, daga zunubai, Ka tsarkakeni, a cikinsa,
daga aibi (nakasa), Ka gwada zuciyata, a cikinsa, da takawar zukata, Ya Mai rufe ido
kan zunuban masu zunubi. | | |
 |
Rana Ta Ashirin da Hudu ta Watan
Ramalana | |
 |
|
 |

Ya Allah! Ina rokonKa, a cikinsa, da abin yardarKa, sannan kuma ina neman tsarinKa,
a cikinsa, daga abin da ke sanya Ka fushi, Kuma ina rokonKa, a cikinsa, samun nasarar yi maka
biyayya kana kuma kada in saba maka, Ya karimi ga masu bukata. | | |
 |
Rana Ta Ashirin da Biyar Ta Watan
Ramalana | |
 |
|
 |

Ya Allah! Ka sanya ni, a cikinsa, mai kaunar waliyanKa mai adawa da
abokan gabanKa, mai bin sunnar AnnabinKa na karshe, Ya mai shiryar da zukatan
Annabawa. | | |