ADDU'O'IN RANAKUN RAMALANA (26-30)
Bismillah
Rana ta Ashirin da Daya ta Watan Ramalana

supplication

Ya Allah! Ka nuna min, a cikinsa, hanyar isa ga yardarka, Kada ba wa Shaidan, a cikinsa, daman cin nasara a kaina, Ka sanya aljanna ta kasance makoma da kuma abin huta gare ni, Ya Mai biyan bukatun masu bukata.

Rana ta Ashirin da Biyu ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka bude min, a cikinsa, kofofin falalolinKa, Ka saukar min, a cikinsa, da albarkokinKa, Ka taimakamin, a cikinsa, zuwa ga tafarkin yardarKa, Ka zaunar da ni, a cikinsa, cikin aljannarKa, Ya Mai amsar kiran mabukaci (wanda ke cikin damuwa).

Rana ta Ashirin da Uku Ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka wanke ni, a cikinsa, daga zunubai, Ka tsarkakeni, a cikinsa, daga aibi (nakasa), Ka gwada zuciyata, a cikinsa, da takawar zukata, Ya Mai rufe ido kan zunuban masu zunubi.

Rana Ta Ashirin da Hudu ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ina rokonKa, a cikinsa, da abin yardarKa, sannan kuma ina neman tsarinKa, a cikinsa, daga abin da ke sanya Ka fushi, Kuma ina rokonKa, a cikinsa, samun nasarar yi maka biyayya kana kuma kada in saba maka, Ya karimi ga masu bukata.

Rana Ta Ashirin da Biyar Ta Watan Ramalana
Bismillah

supplication

Ya Allah! Ka sanya ni, a cikinsa, mai kaunar waliyanKa mai adawa da abokan gabanKa, mai bin sunnar AnnabinKa na karshe, Ya mai shiryar da zukatan Annabawa.