SHARUDDAN WAJIBCI DA KUMA INGANCIN AZUMI


Mene ne hukuncin' yan matan da suka isa shekarun balaga to amma yin azumi na yi musu wahala zuwa wani haddi? Kuma shin shekarun balaga ga mata shi ne shekara tara?
A bisa mashahurin magana shekarun balaga a wajen 'yan mata shi ne shekara tara, na kamariyya to a wannan hali wajibi ne su yi azumi, kuma ba ya halatta su bar azumi dan kawai wasu uzuri, to amma da azumin zai cutar da su ko ya zama kunci a gare su, to ya halatta su sha ruwa.
Da mutum zai tsammani sama da kashi hamsin bisa dari kana kuma bisa ga wani uzuri mai karfi cewa azumi bai wajaba a gare shi ba dan haka sai ya ki yin azumi, to amma sai daga baya ta bayyana masa cewa azumin nan fa wajibi ne a gare shi, to mene ne hukuncinsa dangane da ramuwa da kaffara?
Idan dai har ya sha ruwan ne saboda kawai tsammanin cewa azumi bai wajabta a gare shi ba, to a nan wajibi ne ya yi ramuwa kuma ya yi kaffara a kamar yadda yake a tambayar to amma idan har ya sha ruwan ne saboda tsoron cutarwa kuma tsoron nasa abin karbuwa ne a gurin masu hankali, to babu kaffara a gare shi sai dai kawai zai rama azumin ne.
Mutumin da yake da azumin wajibi a kansa sai ya kuduri aniyar rama azumin, to amma sai wani abu ya bijiro masa da zai hana yin azumin, kamar tafiya ta same shi bayan ketowar alfijir inda ya yi tafiyar to amma bai dawo ba sai bayan azahar kana bai aikata komai daga cikin abubuwan da suke karya azumi ba, sai dai kawai lokacin yin niyyar azumin wajibi ya wuce masa, kuma wannan ranar tana daga cikin ranakun da yin azumi mustahabi ne a cikinsu, to shin ya inganta ya yi niyyar azumin mustahabi?
Idan dai har yana da azumin wajibi a kansa to azumin mustahabi ba ya inganta a gare shi ko da kuwa bayan wucewar lokacin yin niyyar azumin wajibi ne.

>