An ruwaito cewa a lokacin da mutum ya ga sabon watan Ramalana ya kama,
sai ya daga hannunsa sama ya karanta wannan addu'a ta kasa:
-

RABBI WA RABBUKALLAAHU RABBUL A'ALAMEEN. ALLAAHUMMA
AHILLAHU A'LAYNAA BIL-AMNI WAL IMAANI WAS SALAAMATI
WAL ISLAAMI WAL MUSAARA-A'TI ILAA MAA TUHIBBU WA
TARZ'AA. ALLAAHUMMA BAARIK LANAA FI SHAHRINAA HAADHAA
WAR-ZUQNAA KHAYRAHU WA A'WNAHU WAS'RIF A'NNAA
Z'URRAHU WA SHARRAHU WA BALAAA-AHU WA FITNATAHU
Ubangijina da Ubangijinka Shi ne Allah Ubangijin Talikai.
Ya Allah Ka sanya wannan wata ya kasance mana kariya, (abin kara)imani da
kuma cikakkiyar mika wuya gare ka, da kuma tafiya akan abin da Kake so
kuma Ka yarda da shi. Ya Allah Ka albarka ce mu a cikin wannan wata, Ka arzurtamu
da alherinsa da kuma taimakonsa, sannan kuma ku kare mu daga cutarwarsa,
sharri, bala'i da kuma fitinarsa.
|