Cin abinci ko abin sha don yin Suhur yana da matukar muhimmanci
da kuma lada mai yawa ga mai azumi. Akwai ruwayoyi daban-daban da suke
kira da yin suhur koda da ruwa ne kawai saboda muhimmancinsa. Ga kadan
daga cikin irin wadannan ruwayoyi da suke magana kan Suhur:
Manzon Allah (S) yana cewa: "Allah da ManzonSa suna
salati ga masu neman gafara da masu yin suhur a lokacinsa. don haka ku yi
Suhur koda da ruwa ne"
Manzon Allah ya ce: "Suhur albarka ne, don haka kada
ku bar suhur koda kuwa da gutsuren dabino ne".
Haka nan kuma Imam Sadiq (a.s) ya ce Manzon Allah (s) ya ce: Ku yi Suhur
koda da (kofin) ruwa ne, Lalle amincin Allah ya tabbata ga masu yin Suhur
Haka nan kuma a lokacin Suhur din an so a karanta wasu addu'o'i da aka
ruwaito daga Manzo da Alayensa (a.s). Daga cikin wadannan addu'o'i akwai wannan addu'a ta kasa:

Niyyar Daukan Azumi.
Niyya dai ba wata aba ba ce face dai kawai mutum ya kudura cikin zuciyarsa cewa zai
yi azumi don neman kusanci da Allah Madaukakin Sarki, ba lalle ne sai ya furta da fatan bakinsa ba |