An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: "Misalin Mutanen gida na a cikin ku misalin jirgin Annabi Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya ki (hawa) to ya halaka". Hakika sanannen abu ne cewa a zamanin Annabi Nuhu (a.s) bayan da yayi addu'an Allah Ya halaka al'ummansa saboda irin sabon Allah da suke yi da kuma kin karban addinin da ya zo musu da shi, Allah Ya saukar da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye duk duniya, ta yadda dukkan al'umma suka halaka sai dai wadanda suka yi imani da shi kana kuma suka hau wannan jirgi nasa, su ne kawai suka tsira daga halaka.

Don haka wannan magana ta Ma'aikin Allah (s) da kuma misalta Mutanen gidansa da wannan jirgi na Nuhu, ya na nuni ne da cewa riko da Mutanen Gidan Manzon Allah shi ne kawai tafarkin tsira, kana kuma kin yin riko da su kamar kin hawa wannan jirgi na Nuhu ne kuma sakamakonsa shine halaka, Allah Ya kiyashe mu.