Da dama daga cikin 'yan siyasa da kafafen watsa labaran duniya suna ganin Juyin Juya Halin Musulunci na Iran da Marigayi Imam Ruhullah al-Musawi al-Khumaini (r.a) ya jagoranta a matsayin mafi girman lamarin siyasa a karni na ashirin. Hakan kuwa bisa la'akari ne da cewa babu wani juyi, a wannan zamani namu, da tasirinsa ya jima tsakankanin mutane kamar wannan juyin Musulunci na Iran. Baya ga hakan kuma wannan juyi na al'ummar Iran yana da wasu siffofi na musamman da ya kebanta da su sauran juye-juyen da suka faru ba su da shi. Wadannan siffofi na musamman dai su ne za mu yi dubi cikinsu a nan da kuma kwatantasu da na sauran juye-juye.
Tarihin manyan juye-juye da aka samu a wannan duniya tamu suna nuni da cewa mafi yawa daga cikin jagororin da suka jagoranci wadannan juye-juye sun juya sun zamanot 'yan mulkin kama-karya wadanda ba su ba da wani muhimmanci ga ra'ayi da kuma mahangan al'ummarsu da suka taimaka wajen haifar da wadannan juye-juye. To amma sabanin haka, Imam Khumaini (r.a), mu'assasin Juyin Juya Halin Musuluncin na Iran, ba abin da ya fi ba shi muhimmanci kamar ra'ayin al'umma, don kuwa kasa da watanni biyu da samun nasarar wannan juyi nasa ya kirayi al'umma da su fito su ba da ra'ayinsu kan irin hukumar da suke so ta mulke su. Inda jama'a suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka zabi tsarin Musulunci (Jamhuriyar Musulunci) a matsayin tsarin da suke so ya mulke su. A takaice dai Imam Khumaini (r.a) ya ba da umarnin a gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kan irin tsarin da suke so a watan Aprilun 1979, inda ya gabatar wa duniya da wani sabon tsari na ba da muhimmanci ga ra'ayin al'umma a tsarin gudanarwa. Alhali kuwa duniya dai (musamman a wannan zamani namu) ba ta taba ganin wani Jagora na wani juyi da bayan samun nasara ya nuna damuwarsa ga ra'ayin al'umma kamar yadda Imam (r.a) ya nuna ba, face ma dai babban hadafin sauran jagororin shi ne samun mulki da kuma tabbatar da karfinsu. Don haka ana iya cewa Imam Khumaini, a matsayinsa na jagora kuma malamin addini, ya haifar da wani juyi da kuma yadda ake gudanarwa ga duniya, wato a bangare guda ya jaddada wajibcin gudanar da tsarin Musulunci a bangare guda kuma ya tabbatar da muhimmancin da mutane suke da shi a tsarin Musulunci wajen ayyana irin tsarin da siyasar da suke so.
Baya ga wannan matsayin mai girma da al'umma suke da shi a wannan juyi na Musulunci, shakka babu wata siffa ta musamman kuma da wannan juyi ya ke da shi shi ne haifar da wani sabon abin koyi a bangaren alakar kasa da kasa da ya ginu bisa asasin 'ba Gabashi ba Yammaci' (La Sharkiy wa la Garbiyyu), wato 'ba mu yarda da tsarin gurguzu na Tarayyar Sobiyeti ko kuma tsarin jari hujja na Amurka ba'. Wannan take na 'Ba Gabashi Ba Yammaci' na daga cikin take da wannan tsarin da wannan juyi ya dauka don nuna wa musulmin duniya cewa su ma fa suna iyawa ba tare da sun dogara da kasashen Gabashi ko Yammaci ba. Kafin wannan take da kuma nasarar wannan juyi na Musulunci dai, duk duniya, hatta kasashen musulmi, sun yi amanna da cewa babu yadda za su yi face bin daya daga cikin wadannan tsarurruka guda biyu (gurguzu ko jari hujja). Saboda haka ne masu kula da al'amurran yau da kullum na kasashen yammaci wadanda suke sa ido kan abubuwan da suke gudana a Iran da kuma wannan juyi suka yi imanin cewa lalle wannan juyi ma dai dole ya bi daya daga cikin wadannan tsarurruka guda biyu. To amma a aikace, wannan juyi na Musulunci ba wai ma kawai bai dogara da daya daga cikin wadannan tsarurruka ba ne wajen samun nasara, face ma dai bayan samun nasarar juyin ya kaddamar da wannan take na 'Babu Gabashi Babu Yammaci' a matsayin asasin siyasarsa na waje (na kasa da kasa). A hakikanin gaskiya wannan ma dai na daga cikin siffofin da wannan juyi na Musulunci ya ke da shi da ya banbanta da sauran juye-juye.
Wata siffa kuma da wannan juyi na Musulunci ya kebanta da ita ita ce riko da 'yantacciyar siyasa a daidai lokacin da manyan kasashe masu karfi na wancan lokacin ba abin da suke kokarin yi in ban da samun kutsawa da mayar da kasashen duniya bayinsu. Duk da cewa dai tun kafin nasarar Juyin Juya Halin Musulunci ake ta magana kan samun 'yanci na siyasa da kuma kubuta daga irin bakar siyasar kurayen duniyan nan biyu na wancan lokacin (Amurka da Tsohuwar Tarayyar Sobiyeti), to sai dai kuma duk wadannan maganganu sun kasance ne kawai a rubuce ba a aikace ba. Daya daga cikin wannan kokari dai shi ne kirkiro kungiyar Kasashen 'Yan Ba Ruwanmu da nufin samun 'yanci na siyasa daga wadannan manyan kasashen duniya, to sai dai kuma idan muka duba za mu ga cewa manyan jagororin da suka kirkiro wannan kungiya, irinsu Jamal Abdunnasir, Nehru, Sakarno da dai sauransu ba su tsira daga dogaro da daya daga cikin wadannan kasashe biyu (Amurka da Rasha) ba. Duk da cewa hakan dai ba wai yana nufin su wadannan shuwagabanni ba su da karbuwa a wajen mutanensu ba ne ko kuma wai ba sa girmama al'ummansu ba ne, face dai abin da ake iya fahimta shi ne cewa a lokacin babu wani tsari da ya iya tseratar da kansa daga bin siyasar yammaci ko gabashi ba. Don haka babban abin da ya iya sanya Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma Juyin Juya Halin Musulunci na Iran din ya tseratar da kansa daga dogaro da gabashi ko yammaci shi ne cewa tun farkon-farawa dai tsarin ya dogara ne da tsari da kuma koyarwa ta Musulunci.
Wata siffa kuma da wannan juyi ya kebantu da ita ita ce riko da musuluncin juyin da kuma hadin kan da ke tsakanin bangarori daban-daban na al'umman Iran. Dangane da hakan ne ma Marigayi Imam Khumaini (r.a) yake cewa:
"Asasin wannan juyi dai shi ne Musulunci, hakan kuwa yana nufin cewa ne mu dai babu wani abu babu wani umarni da za mu karba in ba na Musulunci ba…..abin da dai al'ummar Iran suka zaba shi ne Musulunci. Lalle babu wata kasa ko wani karfi da zai iya tilasta wa wata al'umma mai mutane miliyan 35 (adadin mutanen Iran a 1979) bin wani tsari ko wata hanya da ya tsara. Don haka matukar dai ba a samun wannan hadin kai ba tsakanin al'umma, to makomar wannan juyi za ta kasance kamar makomar sauran juye-juye da suka faru a tarihi, wato faduwa kasa warwas".
A mahangar Imam (r.a) dai abubuwa uku, wato addinin Musulunci, hadin kan al'umma da kuma jagorancin malamai, su ne ummul aba'isin din nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, ci gaban juyin da kuma matsayin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi a idanuwan al'ummomin duniya. Kuma a hakikanin gaskiya wannan juyi na Musulunci ya samu nasara ne ta hanyar dogaro da wadannan abubuwa guda uku, kuma rashin daya daga cikin wadannan abubuwa lalle zai kasance babbar barazana ga juyin, wanda zai iya kawo faduwarsa.
To amma dai har ya zuwa yanzu, bisa la'akari da tsayin dakan Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na yanzu Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i, wajen ganin an tabbatar da kuma kiyaye wadannan abubuwa guda uku, suna dada tabbatar wa al'ummomin duniya cewa lalle wannan juyi zai ci gaba da kasantuwa da kuma ci gaba da yardar Allah.
Mai karatu wannan dai kadan kenan daga cikin irin siffofi da wannan juyi ya ke da su da sauran juye-juyen da aka samu a duniya suka rasa ko kuma ba su ba su muhimmanci ba abin da ya sanya suka samu kansu cikin kwandon sharan tarihi.
Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah.