Tun dai daga lokacin da Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya yi nasara ranar 11 ga watan Fabrairun 1979 zuwa wannan lokaci da ake bukukuwan shekaru 25 da wannan nasarar, juyin ya fuskanci al'amurra da matsaloli daban-daban. Wasu daga cikin wadannan matsaloli kuwa, idan aka lura da irin girma da yadda suka bijiro, sun isa su kawo karshen wata gwamnati ko kuma wani juyi. To sai dai kuma bisa dogaro da Ubangiji da karfin al'umma, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu nasarar kawo karshen irin wadannan matsaloli da suka taso mata.
Yanzu bari mu yi dubi cikin wasu daga cikin wadannan matsaloli:
Daya daga cikin manyan abubuwan da suka faru jin kadan bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci shi ne mamaye 'Ofishin Jakadancin' (ko kuma mu ce ofishin leken asiri) Amurka a Tehran da kame ma'aikatan ofishin da wasu dalibai mabiya tafarkin Imam suka yi. Su dai wadannan ma'aikata na 'ofishin jakadancin' Amurkan sun fake da kariya ta diplomasiyya da suke da ita, inda suka mai da wannan ofishi zuwa wajen leken asiri da kuma kokarin yin zagon kasa wa jaririyar gwamnatin Musulunci da dawo da tsohuwar gwamnatin kama karya da aka kawar. Wannan kame 'ofishin jakadanci' dai da daliban suka yi ya samu goyon bayan al'ummar Iran da kuma shi kansa mu'assasin Juyin Juya Halin Marigayi Imam Khumaini (r.a). Kamar yadda kuma al'umma sun kara nuna goyon bayansu bayan da daliban suka nuna abubuwan da suka samu a ofishin da ke nuni da irin ayyukan leken asirin da ake gudanarwa a wajen. Duk da cewa dai Amurkan ta ta barazana da kuma matsin lamba wa Iran kan ta sako wadannan 'yan leken asiri da suka sanya rigar diplomasiyya, to sai dai Imam da al'ummar Iran sun tsaya kyam wajen ci gaba da tsare su, suna masu kafa wa Amurkan wasu sharudda kafin a sako su. Hakan kuwa ya faru don sai da Amurkan ta amince da wannan sharadi na cewa ba za ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Iran ba kafin aka sako wadannan 'yan leken asiri.
Haka nan kuma, a daidai lokacin da ake cikin tsakiyar wannan rikici tsakanin Amurka da Iran a karshe-karshen shekarar 1979, sai kuma ga wata matsalar kuma a hankali a hankali ta fara kunno kai, ita ce kuwa matsalar kungiyar 'Mujahidin Khalk' ko kuma kungiyar da aka fi sani da 'Kungiyar Munafukai'.
Ita dai wannan kungiya, saboda irin karkacaccen tunani da 'yan kungiyar suke da shi da kuma son rai da ya mamaye su, sun yi kokarin dawo da komai gare su da kuma kame dukkan al'amurran gudanarwa a Iran, don haka ne ma suka goyi bayan shugaban Iran na wancan lokacin da daga baya aka tsige wato Bani Sadr don cimma burorinsu. Irin wannan tunani na 'yan wannan kungiya dai bai samu goyon bayan Imam al'ummar Iran ba, face ma dai al'umma din suna ganinsu ne a matsayin munafukai wadanda suke kokarin mai da hannun agogo baya. Kai a takaice ma dai da wannan suna na munafukai suke kiransu, wannan ya sa sun gagara cimma nasara. Wannan rashin nasara da suka samu ya sanya 'yan kungiyar gudanar da ayyukan ta'addanci da jami'ai da malamai a wancan lokacin, inda suka samu nasarar kashe da dama daga cikin jami'an gwamnati da kuma malamai masu riko da hukumar. To sai dai kuma ba su jima suna yi ba, don kuwa irin kyamar da al'umma suke musu da kuma fuskantarsu da suke yi a duk lokacin da suka hadu da su ya tilasta musu gudu daga Iran da samun mafaka wajen wasu kasashe da suke adawa da gwamnatin musuluncin musamman ma daga tsohon shugaban kasar Iraki Saddam Husaini.
To sai dai kuma babu shakka mafi girman matsalar da Juyin Juya Halin Musuluncin ya fuskanta kana kuma ya iya gamawa da shi, shi ne kallafaffen yakin shekaru takwas da gwamnati kama karya ta Saddam Husaini ta kallafa wa Iran. Idan dai ana iya tunawa, a shekarar 1980 ne Saddam, bisa umarni da goyon bayan Amurka, tsohuwar Tarayyar Sobiyeti da kuma da dama daga cikin kasashen Turai da na larabawa, ya kaddamar da gagaruman hare-hare a kan Iran da nufin ganin bayan gwamnatin Musuluncin da aka kafa, a daidai lokacin da ba wani shiri na azo a gani da Iran din take da shi sakamakon makirce-makircen makiya da kuma irin rikon sakainar kashin da tsohuwar gwamnatin zalunci ta 'ya'yan gidan Pahlawi suka yi da kuma mika kai ga makiya.
Da farko da Saddam da iyayengijinsa sun dauka cewa cikin ruwan sanyi za su gama da Iran, to sai dai kuma wasa-wasa sai wankin hula ya kai su dare, sakamakon irin karfin jagoranci na Imam Khumaini (r.a) da kuma goyon bayan al'umma, sannan kuma ga kariya irin ta Ubangiji Madaukakin Sarki. A wannan lokaci dai dubun-dubatan matasa sun fito fili kusan hannu rabbana wajen fuskantar makiya wadanda suke da dukkan nau'oi na muggan makamai, inda daga karshe dai jaruman al'ummar Iran suka samu nasara a kan abokan gaba da fatattakansu.
Ko shekara guda dai ba a yi ba da kawo karshen wannan kallafaffen yaki, kwatsam sai ga wani babbar matsala kuma ta fuskanto wannan juyi. Wannan matsala kuwa ita ce rasuwar Mu'assasi kuma Jagoran wannan juyi, Marigayi Imam Khumaini (r.a) a ranar 4 ga watan Yunin 1989, wannan rasuwa dai ba wai kawai ga al'ummar Iran ba face ma dai dukkan al'ummar musulmi da raunanan duniya ta girgiza su matukar girgizawa. Makiya wannan juyi dai da man shekara da shekaru suna jiran faruwar wannan lamari da kuma samun wannan dama, suna tunanin cewa rasuwar Imam dai za ta kawo karshen wannan juyi da kuma faduwar Jamhuriyar Musuluncin da ya kafa.
To amma ta Allah ba ta su ba, don kuwa sai ga shi miliyoyin al'ummar Iran sun fito wajen jana'izar Imam da kuma jaddada mubaya'arsu ga wannan kira na Imam da kuma yin alkawarin kare manufofin Imam har karshen rayuwarsu. Wani abin da kuma ya kara sa makiyan suka yanke kauna daga cimma wannan manufa ta su, shi ne zaben Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i da Majalisar Kwararru Mai Zaben Jagora ta yi a matsayin wanda zai gaji Imam (r.a). Wannan zabe dai ya tabbatar wa al'umma da kuma makiyan cewa tafarkin Imam dai na nan daram kuma za a ci gaba da shi, hakan kuwa saboda masaniyar da suke da shi cewa Ayatullah Khamene'i dai na daga cikin daliban Imam na kurkusa ko kuma ma mu ce wanda ya fi dacewa da wannan matsayi saboda tsoron Allah, hangen nesa, ilmi, sanin madafan gudanarwa da dai sauran siffofin da ya ke da su.
Wannan rasuwa da kuma zaben da aka gudanar hakika ya yi kama da abin da ya faru a lokacin Manzon Allah (s.a.w.a), wato lokacin rasuwarsa. Inda tuntuntuni kafirai suna jiran dakon rasuwarsa ne da cewa lalle rasuwar tasa za ta kawo karshen Musulunci, to amma ina lokacin da suka ji ya zabi kaninsa kana kuma dan baffansa Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib (a.s) a matsayin wanda zai gaje shi (hakan kuwa ya faru ne a Ghadir Khum lokacin hajjin ban kwana), sai kafiran suka yanke kauna daga cimma muggan manufofin da suke da shi. Kamar yadda ya zo cikin fadin Madaukakin Sarki cewa: (Çáíæã íÆöÓó ÇáóÐíä ßÝÑæÇ ãäú Ïíäößãú ÝáÇó ÊÎÔæåõãú æÇÎúÔóæúäí) "A Yau Wadanda Suka Kafirta Sun Yanke Kauna Da ga Addininku. Saboda Haka Kada Ku Ji Tsoronsu, Ku Ji TsoroNa…" (Suratul Ma'ida; 5:3).
Har ila yau kuma, daya daga cikin matsaloli da barazanar da Juyin Juya Halin Musulunci ya dinga fuskanta kuma ya ke ci gaba da fuskanta ita ce barazanar gwamnatin Amurka a bangarori daban-daban na siyasa, tattalin arziki, tsaro, farfaganda da dai sauransu. Amurka dai tun bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci da kawar da gwamnatin kama karyar Shah, ta rasa haramtattun manufofinta a Iran, don haka ne ta dau wannan mataki na barazana don ganin ko za ta iya kawar da gwamnatin Musulunci. Daga cikin matakan soji da Amurkan ta dauka a kan Iran har da kokarin shirya juyin mulki wa gwamnatin Musulunci, wadanda kuwa suka fito fili daga cikin irin wadannan makirce-makirce, su ne, kokarin juyin mulkin shekarun 1980 da 1983, to sai dai kuma da taimakon Allah da kuma tsayin dakan al'umma, an samu nasarar kawo murkushe wannan makirci.
Takunkumin tattalin arziki ma dai na daga cikin hanyoyin da Amurkan ta bi wajen matsa wa Iran lamba, wanda ya faro ne tun daga farko-farkon nasarar Juyin Juya Halin har zuwa wannan lokaci kullum zai dada karuwa yake yi, to sai dai shi ma wannan makirci, kamar sauran makirce-makircen bai sa Iran din ta mika wa Amukawan kai ba.
Wata hanyar kuma da Amurkan ta ke bi wajen bakanta wannan juyi da kuma kasar Iran din ita ce hanyar farfaganda da yada karairayi. Daga cikin irin wadannan karairayi har da ikirarin take hakkokin 'yan'Adam, goyon bayan ayyukan ta'addanci da kuma kokarin mallakan makaman kare dangi. Batun take hakkokin 'yan'Adam da goyon bayan ayyukan ta'addanci dai batutuwa ne da suka jima suna yawo da su, to amma su ma dai ba su sami karbuwa a wajen da dama daga cikin al'ummomin duniya ba, musamman ganin yadda Amurkan ta ke take hakkokin bil Adama a cikin da wajen Amurkan da kuma yadda ta ke goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda irinsu Haramtacciyar Kasar Isra'ila da dai sauransu. Ganin cewa dai ba su cikakkiyar nasarar da suke so ba a wannan bangaren, yanzu kuma cikin 'yan watannin nan sun fara maganar Iran tana kokarin mallakan makaman kare dangi, wannan kuwa ba wai don cewa Iran din tana kokarin mallakan wadannan makamai ba ne face sai dai don Amukan ta yi kafar ungulu wa kokarin da Iran din take yi na mallakan ilmin makamashin nukiliyya don amfani na zaman lafiya, wanda kuwa yin hakan ba haramun ba ne a bisa dokokin kasa da kasa. Amurkan ta yi ta kokarin tura wannan batu zuwa ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da nufin samun daman bakin magana da tsoma baki cikin harkokin Iran, to sai dai kuma a wannan karon ma dai ba su samu sun yi nasarar ba, don kuwa sanya hannun da Iran ta yi kan yarjejeniyar karin bincike ya kawo karshen wannan makirci na Amurka.
Wadannan dai kadan kenan daga cikin matsalolin da Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya fuskanta cikin rubu'in karni (shekaru 25) na wannan juyi.
Ko ba a fadi ba dai yadda Juyin Juya Halin ya samu damar magance matsaloli masu wahalan gaske da ya fuskanta yana nuni ne da karfin da tsarin Musulunci ya ke da shi wajen magance matsaloli. Daya daga cikin dalilan da suka sanya samun nasara da ficewa daga cikin matsalolin da aka ta fuskanta cikin wadannan shekaru 25, babu shakka, shi ne jagoranci. Don kuwa duk cikin wadannan shekaru muna iya ganin rawar da jagoranci ya taka wajen magance kusan dukkan matsalolin da aka fuskanta. A bisa tsarin mulki na Iran dai, Jagora dai, baya ga masaniya, sanin al'amurran gudanarwa, sanin ya kamata, dole ne kuma ya kasance mutum ne ma'abucin tsoron Allah da sanin haddodin Ubangiji. Don haka ne a duk lokacin da wata matsala ta kunno kai, jami'ai da sauran al'umma sukan mika al'amurransu ga jagoranci don magance ta.
Wani rukuni kuma na gwamnatin Iran din wanda shi ma ya taka rawa nesa ba kusa ba wajen magance matsalolin da aka shiga, shi ne karfi na al'umma. Don kuwa ta hanyar goyon bayan al'umma ne wannan juyi ya samu nasara, sannan kuma ta hanyar goyon bayan al'umma din ne aka samu nasarar magance matsaloli daban-daban irinsu kallafaffen yaki, rasuwar Imam da kuma barazanar yau da kullum na Amurka, a irin wadannan lokuta dai al'umma din sun kasance tare da jagoransu da kuma sauran jami'an gwamnati wajen fuskantar wadannan matsaloli.