Tuka da Warwara Game da Shaci-Fadin
Akida Dangane da Bayyanar Mahadi.


Lalle sakamako mai ma'ana game da abinda ya gabata na tabbatar da rudu da tuka da warwarar shugabannin Masanan Turai game da cewa al'amarin Mahadi (A.S.) shaci-fadi ne a karshen zamani. Domin kuwa tatsuniyar da Imani ke yadawa da irin wannan kamar, babu shakka ta zare hankulan masu imani da ita. To ta yaya aka yi ya auku cikin al'umma wadda ta fi kowace al'umma a duniya kamar yadda su Masanan Turai 'yan a bata suka yi ikrari da kansu.
Abin al'ajabi ne cewa masu fadin haka suna ikrari da ci gaban rayuwar Musulunci da daukakarta a tsakanin tsarurrukan rayuwa na duniya baki daya kuma ba sa musa gudummawar musulunci wajen gyara zukatan musulmi daga sauran bidi'o'i da tatsuniyoyi da al'adu tsofafi da ke dushe zukata kuma hankula ke kin su. Kuma ba su waiwayi cewa al'umma kamar wannan ba zai yiwu ta yi ittifaki a kan imani da tatsuniya ba, kuma yawancin abin da wadannan Masanan Turai 'yan a bata suka zata yayin da suka sami akidun magabatansu sun cika da tatsuniyoyi da bata sai ya zamanto ya yi musu nauyi su yi rubutu game da Musulunci wanda ya fi zinariya tsarkaka ba tare da sun gwamutsa shi da wani abu na daga kufensu ba, don haka ne suka siffanta abinda ya zo ta hanyoyi daban-daban daga Annabi (S.A.W.A.) dangane da bayyanr Mahadi a karshen zamani da cewa wannan yana daga tatsuniyoyi.
Ainihin Musibar ma ba a nan take ba domin mun riga mun san abinda Alkur'ani ke fada game da su cewa:


( 23 )


Saidai babbar musibar ita ce wadda ke cikin rubuce -rubucen wanda ya sanya wa kansa rigar Sayyid Jamaluddin Afghani, da Shaikh Muhammad Abduh da makamantansu daga masu jagorancin kawo gyara abiinda ya taimaka wajen boye hakikaninta, da gaskiyarta wadda babu abinda ya zamanto illa fakewa a karkashin inuwar abokin husuma da neman shiriya daga wanda ya riga ya dulmuye a cikin kogin bata, ba tare da tunanin da ake bukata ba, kuma ba tare da mai da hankali ba zuwa ga abinda ke yin barazana ga gadon da addinin musulinci ya bari ba har kuma yake neman rusa asasin musulunci!
Daga nan ne ya zama wajibi a yi taka tsantsan da wadannan da wadancan, da kuma kiyaye abinda za a watsa, ko a yada, kafin bayyanar dalili mai karfi game da akidar musulmai dangane da Mahadi a fasalolin wannan binciken.
Allah na shiryar da wanda ya so ga hanya madaidaiciya.


( 24 )

FASALI NA DAYA.

MAHADI A ALKUR'ANI DA SUNNA

Ayoyi Dangane da Mahadi: Ba boyayye ba ne cewa Alkurani da sunna tagwayen juna ne daga Mai shari'a guda. Kuma akidar musulmi game da Mahadi a jejjere ta zo ta hanyoyi daban-daban daga Annabi (S.A.W.A.) babu shakka kuma babu rikitarwa - kuma Alkur'ani ya riga ya karfafa su da ayoyi da dama wadanda masu Tafsiri da dama suka danganta su ga Mahadi da aka yi bushara game da bayyanarsa a karshen zamani.
Idan kuwa har wani abu ya zo daga Annabi (S.A.W.A.) ta hanyoyi dabam-daban a jejjere to kuwa babu yadda za a yi Alkur'ani ya yi masa rikon sakainar kashi koda kuwa hankulanmu ba su fahince shi ba saboda fadar Allah Ta'ala:
"Kuma Mun saukar da Alkur'ani gare ka bayani ga dukan kome". (Surar Nahli: 89.)
Saboda fito da wannan akida daga ayoyin sun ta'allaka ne ga wanda ya fahimci Alkur'ani fahimta ta gaskiya. Babu shakka cewa Ahlul Bait (A.S.) Su ne tagwan Alkur'ani da nassin "Hadis, saklaini wato hadisin Abubuwa Biyu masu nauyi wadda aka ruwaito ta hanyoyi daban-daban a gurin dukkan Musulmi, don haka abinda ya tabbata daga gare su (A.S.) wato Ahlul Bait a dangane da Mahadi babu makawa a karbe shi a amince da shi.


( 25 )


Dangane da haka mun gano hadisai da dama daga Ahlu Bait (A.S.) wadanda suke fassara ayoyi da dama da Imam Mahadi (A.S.). Kuma ba za mu ambato daga cikinsu ba sai wadanda malaman Tafsirin Sauran Mazhabobi suka tabbatar da su, da sauran ruwayoyinsu.
1- Daga cikinsu akwai wadanda za mu share fagen mukaddama da su da cewa: Lalle makiyan addinin nan daga Ahlil kitab da Munafukai da mushrikai da Mabiyansu: "Suna nufin dushe hasken Allah ne da bakunansu amma Allah ya ki sai dai ya cika haskensa koda mushirikai sun ki." (Surar Taubat: 32.)
Wannan aya mai ban al'ajabi ta bayyana mana cewa halin wadannan kamar halin wanda yake son ya hure haske ne mai yawa wanda ya yadu a kusurwoyi, da bakinsa, Allah kuma yana son ya kai shi kololuwar cika a haske da haskakawa. A cikin wannan maganar akwai matukar kaskantarwa gare su da wulakanta la'amarinsu da raunana makircinsu domin hurar bakin za ta iya dushe haske mai rauni ne kawai - Wato kamar hasken fitilar aci fal fal-, sam ba za ta taba iya hure hasken Musulunci mai girma mai karuwa ba.
Wannan yana daga cikin al'amuran ban al'ajabi game da bayanin Alkur'ani, kuma yana daga zurfafan surantawar abubuwa daga Ubangiji, saboda abinda ya kunsa na kawo misali na kwarewa ainun wanda ya kai koli a bayani, ba za'a taba samun makamancinsa ba a wanin Alkur'ani.
Sa'annan sai Alkur'ani ya biyar da bayani gare mu bayan wannan misalin cikakken nufin daukakar wannan addinin kome kinsu kuwa, Allah Ta'ala ya ce:- "Shi ne wannan da ya aiki Manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya domin Ya fifita shi a kan addini dukkaninsa koda Mushirikai sun ki." (Surar Taubat: 33)


( 26 )


Fadar Allah Ta'ala: "Domin Ya daukaka shi a kan addinai baki daya" wato ya taimake shi a kan dukkan addinai, lamirin nan da ke cikin "li yuz hirahu" wato domin "Ya daukaka shi." Yana komawa ne ga addinin gaskiya a gurin Manyan mafassara da mashahuransu kuma sun sanya shi a matsayin abu mafi saurin bayyana a lafazin ayar.
Wannan bushara ce mai girma daga Allah Ta'ala ga Manzonsa (S.A.W.A.) da taimako ga wannan addinin da kuma daukaka kalmarsa, wannan bushara ta hadu da ta'akidi a kan cewa manufar makiyan addini ta dushe hasken musulunci ba za ta taba rinjayar iradar Allah Ta'ala ta fifita addininsa madaidaici a kan sauran addinai ko da Mushirikai sun ki ba.
Fifiko a wannan ayar babu abinda ake nufi da shi face galaba da daukaka. Razi ya ce a Tafsirinsa: "ka sani cewa daukaka ko bayyanar wani abu a kan wani yana iya zamantowa da hujja, kuma yana iya zama da yawan adadi da taruwa, kuma yana iya kasancewa da galaba da fifiko. Kuma sananne ne cewa Allah Ta'ala ya yi bushara da haka kuma bai halatta a yi bushara da abu ba sai abinda zai zo nan gaba wanda bai auku ba, daukakar wannan addini da hujja abu ne tabbatacce kuma sananne, don haka abu da yake wajibi shi ne daukar sa a daukaka ta yin galaba."(13)
Abu ne da ba zai boyu ba cewa wannan galabar a kan sauran addinai ta tabbata a Zamanin Annabi (S.A.W.A.) kuma mafificin dalili a kan haka shi ne cewa sun bayar da jiziya ga Musulmi da hannunsu suna kaskantattu kuma ba zai boyu ba cewa wannan galabar da nasarar ta kasance ne da abin da ya dace da zamantowar musulunci a matsayinsa na addini Mai karfi, wanda ke da garkuwa ko ta wane gefe.

____________
13-Tafsirul Kabir na Fakrur Razi Juzu'i na 16 shafi na 40.


( 27 )

Sai dai halin da muke ciki a yau ba haka yake ba, wadanda suka ba mu jiziya ajiya yau sun kankane mana abubuwan da muke tsarkakewa, makiya kuma sun yi mana kawanya, an yake mu a cikin gidajenmu, tare kuma da abinda ake gani a saran na yada addinin Ma'abuta hittafi, (yahudu da Nasara) kuru-kuru.
ldan han mun kasance mun yi imani da cewa Alkur'ani Shi ne kyautuwar yau da gobenmu, shin ma'anar bayyana da fifitar wannan addinin a kan sauran addinai ta yi daidai da hahn da musulunci yake ciki a yau alhahi yana kusa da zamantowa a kayyade da kungiyoyin musulmi da siyasoshinsu?
Abu guda da ya tabbata a busharar nan shine kawai ganin mutane masu yawa da ke danganta kansu da musulunci a yau duk kuwa da abinda ke cikinsu na sabani da tuka da warwara da bam-bancin akida da hukunce -hukunce? Wannan kuwa duk da cewa abinda aka ruwaito daga katada ta game da fadin Allah Ta'ala: "Domin ya fifita shi a kan addinai dukansu" ya Ce: "SU ne addinai guda shida: wadanda suka yi imani, da wadanda suka yahudaance, da sabi 'awa da Nasara da Majusu da kurna wadanda suka yi shir ka. Don haka duk addinai za su shiga karka-shin addinin Muslunci shi ma kuma musulunci ya shiga wani sashe daga cikinsu, dan haka Allah ya zartar da hukunci kuma ya saukar da cewa zai daukaka addininsa. a - - kan addinai dukkaninsu koda mushirkai sun ki"(14)

____________
14-Durrul Mansur iuzur'i na4 shall na176.


( 28 )


A Tafsirin ibm Jazziy kuwa: "Daukaka shi kuwa: shi ne sanya shi mafi daukakar addinai kuma mafi karfinsu har ya game Gabashi da yammaci."(15)
A Durrul Mansur: "sa'id bin Mansur da ibm Mansur da - Baihaki a sunani daga Jabir (R.A) game da Fadin Allah Ta'aia Cewa". Domin daukaka shi a kan addinai dukkaninsu ya Ce: "Ba zai Zamanto haka ha liar sai ya zamanta babu Bayahude ko Banasare mai wani addini sai musulunci.(16)
Daga Mikdad Bin Aswad ya Ce: "Na ji Manzon (S.A.W.A.) yana cewa: Babu wani gidan Marrnara ko kankare da zai saura a hayan kasa face kaimar Musuiunci ta shige shi, ko da daukaka madaukaki ko kuma da kaskanci mai kaskantarwa. Ko ya daukaka su sai Allah ya sanya su cikin Ma'abutansa su daukaka da shi ko kuma ya kaskan tar da su su yi addini da shi."'7
Daga nan ne kuma ya zo a hadisi daga lmam Bakir (A.S.) cewa ayar tana Bushara ne game da bayyanar Mahadi (A.S.) a karshen Zamani, kuma cewa da taimako daga Allah -zai daukaka addi-nin kakansa a kan sauran addinai har ya zamanto babu wani mushiriki da zai saura a bayan kasa, wannan shi ne maganar Siddiy malamin(18) tafsiri.
Kurtubiy ya Ce: "Siddiy ya ce wannan lokacin bayyanar Mahadi ke nan, babu wani wanda zai saura face ya shiga musulunci."(19)

____________
15- Tafsiru Ibm Jussiy shafi na 252
16 -Durril Mansur 4:176.
17-Majma'uI Bayan 5: 35.
18 -Majma'aI Bayan 5:35.
19-Tafsirun kurtabiy 8:121, da Tafsirul kabir 16: Ho, da Majma'uI Bayan 5:35.


( 29 )


2- Daga cikinsu akwai: Fadin Allah Ta'ala:
"Kuma da za ka gani yayin da suka firgita, to babu kubuta sa'an nan aka kama su daga gun makusanci." (Surar Saba'i: 34 -51)
Tabari ya kawo a tafsirinsa daga Huzaifah Bi~ul yaman tafsininta a kan sojojin da za a kife kasa da su, bayanin abinda zai nuna cewa wannan kife kasar bai auku ba tukuna zai zo nan gaba da kuma ruwaito da aka yi daga littafa ingantattu da Madogarai amintattu, kuma da cewa yana daga cikin alamun tashin duniya da ke hade bayyanar Mahadi ba tare da wani sabani ba.20
Da kuma abinda Tabari ya kawo wanda kurtubi ya ambata shi a littafin "Tazkirah" kai tsaye daga Huzaifah Binul yaman, kuma da shi Abu Hayyan ya bayyana a saran a Tafsirinsa, da kuma Makdisi Basha-fi'e a littafin Akdid Durar, da kuma suyuti a Al-Hawiy lil Fattawiy, kuma Zamakhshani ya kawo shi a Tafsininsa kasshaf daga ibm Abbas, Tabnisi ya ce a Majma'ul Bayan: Sa'alabiy ya kawo shi a Tafsininsa, mutanenmu ma sun kawo makamancinsa a hadisan Mahadi (A.S.) daga Abiy Abdillah (A.S.) da Abiy Ja'afar (A.S.).2'
3- Daga cikinsu akwai Fadin Allah Ta'ala: "Kuma lalle shi tabbas wani ilimi ne na sa'a, sabida haka kada ku yi shakka game da ita kuma ku bi ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya." (Surar Zukhruf: 61)
Bagawiy ya bayyana karara a tafsirinsa, da kuma Za makhshariy, da Razi kurtubiy, da Nafsiy, da khazin, da Tajuddinil Llanafiy, da Abu Hayan da ibm kasir, da Abu Sa'ud, da Haisamiy, cewa ayar kebantacciya ce game da

____________
20-A duba karin bayani a fasali na ukuna wannan littatin.
21-Majma'ul Bayan 4: 398.


( 30 )

saukowar Annabi isa dan Maryama (A.S.) a karshen Zamani.22
A Durrul Mansur Suyutiy yayi ishara ga abinda Ahmad Bin Hanbal da Ibm Abi Hatam da Tabaraniy, da Ibm Mundawayhi, da Faryabiy, da sa'id bin Mansur, da Abdu bin Humaid suka kawo daga hanyoyi da bam-daban daga ibm Abbas eewa ita ta kebanta da abinda Muka ambata ne.23
Alkanjiy As-Shafi'iy ya fadi a cikin littafinsa Al-Bayan cewa: "Mukatil bin Sulayman da wanda ya bi shi daga masu Tafsiri Sun ce a Tafsirin Fabdin Allah kuma lalle tabbas 'shi wani ilimi ne na sa'a." Shi ne Mahadi (A.S.) Zai kasance a karshen Zamani bayan bayyanarsa tashin duniya da alamunta za su zo."24
Za ka iske kwatankwacin wannan bayanin karara a gurin ibm Hajar Haitamyi da shabalanjiy As-shafi'iy, da Saffariniy Ai-Hanbaiiy, da kanduziy Al-Hanafiy, da Sheikh sabban.25
Babu sabani a tsakanin wadannan da wadancan domin saukar Annabi isa (A.S.) za ta kasance ne hade da bayyanar Mahadi (A.S.) kamar yadda ya zo a sahih Bukhari da sahih Muslim da sauran Iittafan Hadisai kamar yadda za mu bayyana a fasali na uku na wannan bayanin. Dogaro da isharorin wasu da muka ambata wadanda suka

____________
22-Ma'alimut TanziI, Al-Bagawiy 4: 444 /61 da Kasshaf 4: 26, Tafsirul Kabir 27: 222 da Tafsirul Kurtabiy, 16: 105, Tafsirun Nafsiy mai Hashiya da Tafsirul Kazan 4:108-109, da Durural Lakit 8: 24, da Baharul Muhit 8: 25, Tafsiriu ibm Kasir4: 142 Tafsiru Abis Sa'ud 8: 52, Mawaridud Dhaman hadisi na 1758.
23-Tafsiru Mujahid: 2/ 583.
24-AI-Bayan fi Akhbari Sahibiz Zaman: 528.
25-Durrul Mansur: 6/20.


( 31 )

fayyace haka a saran sun kawo daga tafsirin Sa'alabi cewa shi ya kawo a tafsirin wannan aya daga ibm Abbas da kuma daga Abu Huraira da katadata, da Malik Bin Dinar da Dahhaku abinda ke nuna cewa dangane da saukowar Annabi isa dan Maryama (A.S.) tare kuma da nunawa a saran game da samuwar Mahadi (A.S.) da kuma Cewa Zai yi saila a bayan Mahadi (A.S.).
4-Daga cikinsu akwai fadar Allah Ta'aia: "Ba sai Na yi rantsuwa da taurari Masu tafiya da baya-da baya ha, Masu gudu masu buya." (Surar Takwi:8 1:15)
Ya zo a hadisi daga lmam Bakir (A.S.) cewa ya ce: "lmam yana boyuwa shekaru dan biyu da sittin sa'an nan ya bayyana kamar walkiya yana haskaka dare mai duhu, idan han ka riski zamaninsa to idonka zai yi sanyi."26
Ba zai boyu ba cewa wannan hadisi ne gagara ba dau wanda AhiuiBaiti (A.S.) suka same shi daga Annabi (S.A.W.A.) wanda shi kuma ya same shi ta wahayi daga Allah mabuwayin sarki.
Za mu wadatu da wannan gwargwa-do haka saboda cewa shaikh kanduziy ya kawo ayoyi da dama da lmaman Ahlul Bait (A.S.) suka fassara su da lmam Mahadi (A.S) da kuma bayyanar-sa a karshen Zamani. [Yanabi'ui Mawadda 3: 76-85 a Babi na 71].

Nazarin Hadisai Game da Mahadi (A.S.)

Nazani ko da sau daya a kan hadisan da suka zo a littafan Musulmi game da mahadi (A.S.) zai gamsar da

____________
26-UsuluI Kafi Juzui na 1: 341/ 22, Kamaluddin 2: 324, B. 23 hadisi na 1, kitabul Gaiba Shaikh Tusi: 101, Kitabul Gaiba Nu'umaniy: 149 B.10 hadisi: 1, Hidayatul Kubra Al Hadhini: 88, Yanabi'uI Muwadda Juzu: na 3: 85, Babi na 71.


( 32 )

kasancewarsu cewa sun Zo ta hanyovi dabam-daham daga mutane dabam-daban daga Annabi (S.A.W.A.) ba tare da jin wani shakku ba. Da yake wannan bincike ba zai iya wadatar, wa mu kawo dukan hadisan da aka ruwaito a littafan Musulmi game da Mahadi (A.S.) ba saboda tsananin yawan da suke da shi don haka za mu takaita a kan ambata abinda ke ba da tabbacin ruwaito hadisan mahadi (A.S.) daga Annabi (S.A.W.A.) kamar haka:-

Na Farko: Wadanda Suka kawo Hadisai
Game da Mahadi (A.S.)

Fadin cewa babu wani malamin hadisi daga Malaman hadisin Musulunci face ya kawo wasu hadisai da ke albishir game da bayyanar lmam Mahadi (A.S.) a karshen Zamani ba zai Zama karin gishiri ba, har ma sun ware iittafa da dama a kcbe27 game da lmam Mahadi (A.S.).
Amma dangane da malamai da masu hadisan da suka kavw hadisan lmam Mahadi (A.S.) ko kuma suka ruwaito su daga wadanda suka gabace su a bisa salon kafa hujja da ita kamar yadda muka ga haka a littafansu su ne kamar haka:-lbin Sa'ad Mai Littafin Tabakatul kubra (Wanda ya yi wafati a shekara ta 230 Hijiriyya) da ibm Abi shaybah [Wanda ya yi Wafati a shekara ta 235 Hijiriyya], da

____________
27-A salinsu dai shi ne Malam Au wanda ya sanya kimanin littafan Ahulus Sunna talatin a Iiffafinsa mai suna lmam Mahadi (A.S.), alhali shi kuwa AIIama Zabihullah Muhallati Ya kai adadinsu zuwa Iittafa arba'in, kuma ya sanya da sunayensu da sunayen marubutansu a Iittafin Mahadin AhluI Baiti (A.S.) shafi na 18-2 1 har ha yau kuma a cikin wannan Iittafin da aka ambata ya ambata jerin sunan wasu littafan daga bangaren Shi'a dangane da Imam Mahadi (A.S.) inda ya kai adadinsu zuwa daruruwan gomomi akwai Iittafa da dama game da Mahadi (A.S.) wadanda ha ambata a wadannan Iittafa biyun ba.


( 33 )

Ahniad bni Hanbal [Wanda ya yi wafati a shekara ta 241 Hijiriyya] da Bukhriy [Wanda ya yi wafati a shekara ta 256 Hijiriyya] ya ambata Mahadi (A.S.) da siffa ne ba da suna ba, Muslim ma (wanda ya yI wafati a shekara ta 261 Hijiyya) ya aikata kamar yadda ya yi a littafinsa Sahihu muslim kamar yadda Za mu bayyana a Fasali na uku a wannan littafin, da kuma Abubakar Askafiy (wanda ya rasu a shekara ta 260 Hijiriyya) da ibm majan (wanda ya rasu a shekara ta 273 Hijiriyya) da Abu Dawud (wafatinsa shekara ta 275 Hijiriyya) da ibm kutaiba Ad-dainawari (wafatinsa 276 Hijiriyya) da Tirmizi (wafatinsa shekara ta 279 Hijiriyya) da Bazariy (wafatinsa shekra ta 292 Hijiriyya), da Abu ya'aia musiliy (wafatinsa shekara ta 307 Hijiriyya) da Tabariy (wafatinsa shekara ta 310 Hijiriyya) da Akiliy (wafatinsa shekara ta 322 Hijiriyya) da Na'im Bin Hamid (wafatinsa shekara 328 Hijiriyya) da shaikhul Hanabila, wato shugaban 'yan Hamba-liyya a zamaninsa, Barbahriy (wafatinsa shekara ta 329 Hijiriyya) a littafinsa sharhus sunna da kuma ibm Habanal Bastiy (wafatinsa shekara ta 354 Hijiriyya) da makdisiy (wafatinsa shekara 355 Hijiriyya) da Tabaraniy (wafatinsa shekara ta 360 Hijiriyya) da Abu Hasan Abiriy (wafatinsa shekara ta 363 Hijiriyya) da Darul kutuniy (wafatinsa shekara ta 385 Hijiriyya) da khattabiy (wafatinsa shekara ta 388 Hijiriyya) da Hakim Naisaburiy (wafatinsa 405 Hijiriyya) da Abu Na'im isfahaniy (wafatinsa shekara ta 430 Hijiriyya) da Abu Amrud Daniy (wafatinsa shekara ta 444 Hijiriyya), da Baihakiy (wafatinsa shekara ta 458 Hijiriyya) da khatib Bagdadiy (wafatinsa shekara ta 463 Hijiriyya) da ibm Abdulkarim mäiikiy (wafatinsa shekara ta 509 Hijiriyya)da A1-Baghawiy (wafatinsa shekara ta 510 ko 516 Hij iriyya) da A-kali iyadh (wafatinsa shekara


( 34 )

ta 544 Hijiriyya) da khowari Zaniiy A1-Hanafiy (wafatinsa shekara ta 597 Hijiyya) da ibm Jauziy (wafatinsa shekara ta 606 Hijiriyya) da ibm Arabiy (wafatinsa shekara ta 638 Hijiriyya) da muhammad bin Taiha As-Shafi'iy (wafatinsa shekara ta 652) da Aliama sibti ibm Jawziy (wafatinsa 597 Hijiriyya) da ibm Abil Hadid A1-mu'utaziliy A1-Hanafiy (wafatinsa shekara ta 655 Hijiriyya) da A1-munziriy (wafatinsa shekara ta 656) Hijiyya) da A1-kinjiy Al-shafi'iy (wafatinsa shekara ta 658 Hijiriyya)da kurdubiy A1-malikiy (wafatinsa shekara ta 671 Hijiriyya) da ibm khalkan (wafatinsa shekara ta 681 Hijiriyya) da muhibbuddin At-Tabariy (wafatinsa shekara ta 694 Hijiriyya) da Aliama ibm manzur (wafatinsa shekara ta 711 Hijiriyya) a lafazin HADIYA na lisanal (Arab) da ibm Taymiyya (wafatinsa shekara ta 728 Hijiriyya) da Ala'uddin Bin Balban (wafatinsa shekara ta 739 Hijiriyya) da Juwiniy As-Shafi'iy wafatinsa shekara ta 730 Hijiriyya) da waiiyuddin A1-Tabriziy (wafatinsa shekara ta 741 Hijiriyya) da A1-Maziy (wafatinsa shekara ta 739 Hijiriyya) da zahbiy (wafatinsa shekara ta 748) da ibm Wardiy (wafatinsa shekara ta 749 Hijiriyya) da zarandi Ai-Hanafiy wafatinsa shekara ta 750 Hijiriyya) da ibm kayyim Ai-Jawziy (wafatinsa shekara 751 Hijiryya) da ibm kasir (wafatinsa shekara ta 774 Hijiriyya) da Sa'aduddin Taftazaniy (wafantisa shekara ta 793) da Nuraddin A1-Hisamiy (wafatinsa 807 Hijiriyya) da ibm khaldun Ai-magribi (wafatinsa shekarata 808 Hijriyya) shi ne wanda ya tabbatar da ingancin hadisai hudu game da Mahadi (A.S) duk da matsayinsa da aka sani wanda kuma zamu kawo bayaninsa a Fasaii na uku, da kuma shaikh muhammad Jawziy Ad-Dimashkiy As-Shafi; iy (wafatin shekara ta 833 Hijiriyya) da Abubakar busiriy (wafatinsa


( 35 )

shekara ta 852 Hijirjiyya) sakhawiy wafatinsa shekara ta 902 Ilijiriyya) da suyutiy (wafatinsa shekara ta 911 Hijiriyya) da sha; araniy (wafatinsa shekara ta 973 Hijiriyya) da ibm Hajar A1-Haitamiy (wafatinsa 974 hijiriyya) da muttakiy A1-Hindiy (wafatinsa 974 Hijiriyya) da dai sauransu, daga cikin malaman baya-bayan nan kamarsu shaikh mar'iy A1-Hanbaliy (wafatinsa shekara ta 1033 Hijiriyya) da Muhammad RasuL A1-Barzanjiy (wafatinsa shekara ta 1108 Hij iriyya) da Zarkaniy (wafatinsa shekara ta 1122 Hijiriyya) da muhammad ibm kasim A1-Fakihi A1-Malikiy (wafatinsa shekara ta 1182 Hijiriyya) da Abil Ala A1-lrakiy A1-Magribiy (wafatinsa shekara ta 1183 Hij iriyya) da SaHariniy A1-Hanbaliy (wafatinsa shekara ta 1188 Hijiriyya), da zabidiy Al-Hanafiy (wafatinsa shekara ta 1205 Hijiriiyya) a littafin (Tajui Arus) gurin kalmar "Hadiy", da shaikh sabbari (wafatinsa shekara ta 1206 1Iij iriyya) da muhammad Amin AS-Swidiy (wafatinsa shekara ta 1246 Hijiriyya)da shaukaniy (wafatinsa shekara ta 1250 Hijiriyya) da Mumin shabalanj iy (wafatinsa shekara ta 1291 Hij iriyya) da Ahmad zainiy Dahlaniy A1-Fakih wal muhandi's As-Shafi; iy (wafatinsa shekara ta 1304 Hijiriyya) da Sayyid muhammad Sadik A1-Kanuj iy Al-Bukhariy (wafatinsa shekara ta 1307 Hijiriyya) da shuhabuddin A1-Halawaniy As-shafi'iy (wafati shekara ta 1308) da Abil Barakat Al-Alusiy A1-Hanafiy (wafati shekarata 1317 Hijiriyya) da Abi Tayyib muhammad shamsul Hakk Alzimabodiy (wafati shekara ta 1329 Hijiriyya) da kattaniy A1-malikiy (wafati shekara ta 1345 Hijiriyya) da mubarakFuriy (wafati 1353 Hijiriyya) da sheikh mansur Au Nasif (wafatinsa bayan shekarar 1373 Hijiriyya) da shaikh muhammad khidr Husain A1-Misriy (wafati 1377 Hijiriyya


( 36 )

da Abi Faiz Gamari As-shafihiy (wafati shekara ta 1380 Hijiriyya) da Fakihi Al-kasirn Binjid shaikh muhammad Bim Abdil Aziz A1-mani'u (wafati shekara ta 1385 Hijiriyya) da shaikh muhammad Fu'ad Abdul Bakiy (wafatisa shekara ta 1388 Hijiriyya) da Abul Aa'la rnaududiy da Nasiruddin A1-Albaniy zuwa illa masha Allah na daga cikin malaman wannan zamanin, idan kuma muka kara malaman Tafsiri daga Ahlussunna kamar yadda ishara ta gabata a kan haka to ya rage naka ka kintata gwargwadon ittifakin da ake da shi a kan ruwaito hadisai game da lmam mahadiy (A.S.) da kuma kafa dalili da su.
Dangane da malaman shi'a da masanan hadisansu da masu fassara wadanda suka kawo hadisai game da Mahadi (A.S.) za a samu damar ambata sunayensu ne kawai saboda kasancewar yin imani da bayyanar lmam mahadi daga cikin jiga -jigan, akidunsu.

Na Biyu: Wadanda suka ruwaito
hadisan Mahadi (A.S.) daga cikin
Sahabbai:


Lalle sahabban da suka ruwaito hadisai game da Mahadi daga manzon Allah (S.A.W.A.) ko kuma wadanda suka kasance hadisansu sun takaitu da su kawai amma hukuncinsu hukuncin isa har zuwa ga Annabi (S.A.W.A.) ne, -saboda ba zai dace da hankali ba a ce su suka yi hukuncin kansu a wannan, -suna da yawan gaske, idan har ruwaitowa ta tabbata daga kashi daya daga cikin gomansu to, tawaturanci, wato yawan hanyoyin ruwaitowa ta tabbata babu shakku kuma babu rikitarwa, kamar yadda ya zo a madogaran Ahlussunna kawai su ne:-


( 37 )

Fatumatuz zahrara (A.S) (wafati shekara ta 11 Hijiriyya)da mu'azu Bin Jabal (wafati shekara ta 18 Hijiriyya) da Katadata Bin Nu'aman (wafati shekara ta 23 Hijiriyya) da Abu ZaruL Ghifariy (wa?ati shek~ra ta 32 Hijiriyya) Abdullahi Bin mas 'ud (wafati shekara ta 32 Hijiriyya) da Abbas Bin Abdul mutallib (wafati shekara ta 35 Hijiriyya) da salmanul Farisiy (wafati shekara ta 36 Hijiriyya da Talha Bin Abdullah (wafati shekara ta 36 Hijiriyya) da Ammar Bin yasir (wafati shekara ta 37 Hijiriyya) da lmam Au (A.S.) (wafati shekara ta 40 Hijiriyya) da Tamimud Dariy (wafati shekara ta 50 Hijiriyya) da Abdurrahman Bin Sumra (wafati shekara ta 50 Hijiriyya) da lmran bin Hasin (wafati shekadra ta'52 Hijiriyya) da Abu Ayyub Al-Ansariy (wafati shekara ta 52 Hijiriyya) da Sauban Fansar Annabi (S.A.W.A.) (wafati shekara ta 54) da kuma UmmiL Muminina A'isha (wafati shekara ta 58 Hijiriyya da Abu Huraira (wafati shekara ta 59 Hijiriyya) da lrnarn Husain (A.S.) (shahada shekara ta 61 Hijiriyya) da Ummu Salama (wafati shekara ta 62) da Abdullahi Bin umar Binulkattab (wafati shekara ta 65) da Abdullahi ibm Amr Binul As (wafati shekara ta 65 Hijiriyya) da Abdiliah Bin Abbas (wafati shekara ta 68 Hijiriyya) da zaidu Bin Ar kani (wafati shekara ta 68 Hijiriyya) da Awf Bin malik (wafati shekara ta 73 Hijiriyya) da Abu sa'iduL khudriy (wafti shekara ta 74 Hijiriyya) da Jabir Bin sumra (wafati skekara ta 74 Hijiriyya) da Jabir Bin Abdu,illahil Ansariy (wafati shekara ta 78 Hijiriyya) da Abdullahi Bin Ja'afar At-Tayyar (wafati shekara ta 80 Hijiriyya) da Abu Hamamatal Bahiiiy (wafati shekara ta 81 Hijiriyya) da Bashar Binul Munzir Binul Jarud (wafati shekara ta 83 Hijiriyya) an yi sabani a kansa, an ce mai ruwaya ne kuma kakansa shi ne Janidiy Bin Amru (wafati shekara ta 20


( 38 )

Hijirin) da Abdullahi BinuL Hans Bin Jaz'uz zubaidiy (wafati shekara ta 86 Hijiriyya) da sahal Bin sa'adus sa'idiy (wafati shekara ta 91 Hijitiyya) da Anas Bin Malik (wafati shekara ta 93 Hi da Abut Tufail (wafati shekara ta 100 Hijiriyya) Da sauransu wadanda ban samu ainihin tarihin rasuwarsu ba kamarsu Ummu Habiba, da Abil Jahhf, da Abi salma makiyayin manzon Allah (S.A.W.A.), da Abi Laila, da Huuzaifa Binul yaman, da Harsi Binu Rabi'u Abi katadata da zarry Bin Abdillah da zurara Bin Abdillah da Abdullahi Bin Abi Awfa da Ala'a, da Alkamata Bin Abdillah da Aliyul Hilaliy da kurrata Bin Ayas.
Na uku: Hanyoyin Hadisan Mahadi (A.S.) a littafan sunna A Dunkule:sayyid Ahmad Bin muhammad Bin sadik Abul Fai z A1-Gamariy Husain As-shati'i v Al'-magribiy malamin Al-Azhar (wafatinsa shekara ta 1380 Ilijir,yya ya kokarta kuma ya amfanar a !itta-finsa muhinmi; mai suna "lbrazul wahmil maknun mm kalami ibm khaIdun" wata "Bayyana wahamin da ke Akwai amaganar ibm khaldun" inda ya tabbatar da hanyoyin ruwaitowar hadisin lmam Mahadi (A.S.) ta yadda babu wani daya gabata da haka kafin Shi,wannan kana ya yi shi ne ta kure raunin lb in khaldun da wasu daga cikin malanian da suka yi zamani da shi kamarsu Ahmad Amin daga masar da farid wajadiy da sauransu suka fake da shi. A nan babu laifi mu dan tsawaita kadan. a kan hanyoyin hadisan Mahadi (A.S.) a littafan sunna da akabayyana filIa-fihia a wannan littafin, wanda ke bayanin kwarewa wajen binciken hanyoyin ruwaya da madogarar hadasai game da lmam Mahadi (A.S.) daga littafan Ahlussunna farawa daga kan sahabbai sa'annan Tabi'ai sa'an nan


( 39 )

Tabi'an Tabi'ai da kuma sarwa zuwa kan wanda ya fito da wannan hadisi daga cikin malaman hadisi.
Abul Faiz ya ce: "Ba zai boyu ba cewa al'ada ta hukunta koruwar daidaituwar jama'a da adadinsu ya kai talatin zuwa sama shi ne abinda ya iso gare mu kuma muka iya tabbatar da shi a hahn yanzu, kuma mun rigaya mun sainu hadisin mahadi (A.S.) ya zo daga hadisin Abi Sa'idul Khudriy, da Abduhlahi Bin Mas'ud, da Ahiyu Bin-Abi Talib, da ummu salama, da Sauban, da Abduhlah Bin Taz'i Bin Harisuzzabidiy da Abi Huraira, da Anas Bin mahik, da ummu Habiba, da Abiy umama, da Abduhlah Bin Amru Binul As, da AmmarBin yasir da Abbas Bin Abdulmutalhib, da Husain Bin Au da Tamimud Dariy, da Abdur Rahman Bin Awf, da Abduhlahi Bin umar BinuL khattab da I'alha da Ahiyul Hilaliy, da lmran Bin Hüsain da Amru Bin marratal Jahaniy, da mu'az Bin Jabal, daga cikin mursal kuwa wato wa-danda suka dakata a kan maruwaitan su ya su, akwai:shahu Bin Haushan. Wannan abinda muka amkbata marfu'i ne kawai bamu ambaci maukufi da maktui ba wanda su ma a wannan babin tamkar marfui su ke.


( 40 )


To idan da za mu bi laIle da mun ambaci adadi mai yawa daga ciki, saidai kuma muna ganin cewa marfui da muka anibata ya wadatar.28
Na Ce: Na ambata wannan ne kawai saboda a San cewa abinda ya tsere wa sayyid Abul Faiz Gamariy daga cikin sunayen sahabban da suka ruwaito hadisan Imam Mahadi (A.S.) ya fi yawan adadin da ya ambata domin ya ambata ashirin da shida ne kawai daga sahahbai a ciki har da Bin Haushabs bai ambata ashirin da takwas ba wadanda su ne:
Abu Ayyubal Ansariy da Abu Jahhaf, da Abu zarrilghifariy,da Abu salmiy Ra'iy Rasululluh (S.A.W.A.) da Abu wa'ih da Jabir Bin sumra, da Jarud Binur Rabin da Imam Hasan (AS.) da zuran Bin -Abdullah da zurara Bin Abdullah da zaid Bin Arkam da zaid Bin sabit da sa'ad Bin malik, da salmanul Farsiy, da sahal Bin sa'adiy, ~la Abdurrahman Bin sumrata da Abdullahi Bin Ja'afarut Tayyar, da usman Bin usman, da AIa'u da Alkamata Bin Abdullah, da Umar Binul khattab, da Auf Bin malik, da majma BinJariya, da mu'az Bin Jabal kuma shi yana daga cikin sahabban Farko da suka ruwaito hadisan Mahadi (A.S.) kuma shi ya rasu ne tun shekara ta goma sha takwas (18) Hijiriyya ko ta hahn kakadai, shi dai Abul Faiz Al-

____________
28- Littafin Ibrazul waharnil maknuti shafi na 437. Wannan kenan, bui Faiz yana da wani dan'uwa da aka kzdaya shi a cikin malamai ma'abuta FaIala a kasar maroko wanda ake yi wa Alkunya da Abut Faizul Gamariy shi ne kuma maeubucin Iittafin "Imamul Mahadi" kuma ya kara a binda dan'uwansa ya ambàta a Iittafin Ibrazul waharn da sunaye uku daga sahabbai da kuma biyar daga Tabi'an da suka ruwaito hadisan Mahdi (A.S.) sa'an nan ya tabhatar da Iafiizzan ruwa-yoyin wanda ya ambacc su daya bayan daya har sal da ya wamnan ya cike abinda ya cike fiye da rabin shafukan Iittafin 55.


( 41 )

Gamariy As-shafi'iy ya bibiyi hadisan Mahadi (A.S.) wanda sahabbai sama da talatin suka ruwaito yana bayyana wadanda suka ruwaito daga cikinsu da kuma wanda ya kawo su daga cikin malaman hadisai; tare da dukkan tantancewa da fayyacewa.
Kuma da sannu za mu takaita a kan abinda ya fada game da hadisin Abi Sa'idil Khudriy kawai, wanda shi ne sahabi na farko da Abul Faiz ya ambace shi, sa'an kurna ka auna sauran hadisan sahabban.
Ya Ce:
Amma hadisin Abi Sa'idi Khudriy ya zo daga gare shi ta hanyar: Abi Nazrata da Abis Sadikil Najiy da Hasan Bin Yazid As-Sa'adiy.
Amma hanyar Abi Nazarata:
Abu Dawud ya kawo shi da Hakim, kuma dukansu su biyun daga ruwayar lmran kattani, daga gare shi kuma muslim ya kawo shi a littafin Sahih muslim daga Sa'id Bin Zaid da kuma daga ruwayar Dawud Bin Abi Hind kuma duka su biyun daga gare shi. sai dai a sahih muslim an ambata shi ne da sifa ba da suna ba kamar yadda zai zo.
Amma I-Ianyar Ahis siddikun Najiy daga Abi sa'id kuma:
Abdurrazak ya kawo shi da Hakim daga ruwayar Mu'awiya Bin Karrah daga gare shi, kuma Ahmad da Tirrnizi da ibm majah da Hakim sun kawo shi daga ruwayan zaydil Arniy, daga gare shi. Ahmad da Hakim sun fito da shi daga ruwayar mataru Bin Tahman da Abiy-Llaruna Abadiy duk su biyun daga gare shi. Ahmad ya kawo shi kawai daga ruwayaa rnatar Bin Tuhman shi kadai daga gare shi. Har ila yau kuma ya kawo shi daga ruwayar Ala'a Bin Bashir Al-mazaniy daga gare shi kuma har ila yau ya kawo shi daga ruwayar matraf daga gare shi.


( 42 )

Hasan Bin Yazid Kuwa:

Tabaraniy ya kawo shi a A1-Awsat daga ruwayan Abi Wash Abdu Bin Hamid daga Abis saddikun Najiy daga gare shi".29
Na Ce: ldan da za ka koma ga tarihin ibm khaldun Lalle da ka same shi cewa bai san wadannan hanyoyin hadisin Abi Sa'id ba sai kadan, balIantana ma abubuwan da ya ban daga tarihin sahabbai.
Ba zai boyu ba cewa gwargwadon abinda aka hadu a kansa a dukan hanyoyin nan zuwa kan hadisin Abi Sa'idul khudriy kawai banda sauran da ba shi ba, abinda aka hadu a kai, shi ne bayyanar Imam mahadi (A.S.) a karshen zamani, kuma babu shakka cewa duba dukan hanyoyin da suka zo da hadisan Mahadi (A.S.) daga dukan sahabbai na tabhatar da tabbaci da kuma jejjeruwar abinda Annabi (S.A.W.A.) ya yi albishir da shi kai hatta ma ko da mun kaddara cewa ta hanya daya ce aka ambata ga dukan sahabban to ta wadatar wajen tabbatar da yawan maruwaitansa kuma ya rigaya gabata cewa adadinsu ya fi hamsin. Na Hudu: lngancin HadisiGame da Mahadi: A nan za mu ambata wasu daga cikin masanan Ahlussunna ne wadanda suka bayyana ingancin hadisai game da Imam Mahadi (A.S.) kamar yadda muka samu a rubuce rubucensu, kuma ba wai manufarmu ita ce kididiga ba sai dai kawai ba da misalan abinda aka yi imani da shi kamar haka:-

____________
29- Ibrazul waharnil rnaknun. Shafi na 433.


( 43 )


1- Imam Tirmizi (wafati shekara ta 297 Hijiriyya) ya ce game da hadisai uku dangane da Imam Mahadi (A.S.) wannan Hadisi ne rnai kyau ingantacce"30
2- Hafiz Abu Ja'afar Akiliy (wafati shekara ta 322 Hijiriyya) ya kawo hadisi rarrauna game da Imam Mahadi (A.S.) sa'an nam ya ce:-"Game da Mahadi kuma akwai hadisai kya-wawa ba ta wadannan fuskar ba sabanin wannan lafazin." 31
3- Hakim Naisaburiy (wafati shekara ta 405 Hijiriyya) ya ce dangane da hadisai hudu, wannan hadisi ne mai ingantaccen isnadi amma ba su fito da shi ba.
4- Dangane da hadisai uku kuwa: "Wannan hadsi ne mai inganci a bisa sharadin muslim amma ba su fito da shi(32)
Dangane da wasu hadisai guda takwas kuwa ya ce: "Wannan hadisai ne ingantattu a bisa sharadin Buhari da muslim amma ba su fito da shi ba."33
Imam Baihakiy (wafati shekara ta 458 Hijiriyya) ya Ce: "Kuma hadisai game da bayyanar Imam Mahadi su ne mafiya ingancin isnadi."
5- Imam Bagawiy (wafati shekara ta 510 ko 516 Hijiriyya) Ya fito da hadisi game da Mahadi (A.S.) a fasalin sihah da kuma wasu hadisan kuma guda biyar dangane da shi. a Fasalin Hasanat daga littafin "Masabihus Sunna".

____________
30- Sunan Tirmizi Juzu'i na 4 shafi na 505 hadisi na 2230da na 2231 da Juzu'i na 4 shafi ha 506 hadisi na 2233.
31- mustadrakul Hakim iuzu' I na 4 Hadisi na 457, 465, 553, da 558.
32- mustdrakul Hakim Juzu'i na 4 had isi na 450, 557, 558
33- Mustadrakul Hakirn Juzu'i na 4 hadisi na 429 da 442, da 457, da 464, da 502, da 520, da 524, da 557. 4210-4213-da 4215.


( 44 )


6- ibm Asir (wafati shekara ta 606 Hijiriyya) A littafin, (Nihaya) ya kawo a lafazin "Hada" kuma daga ciki akwai hadisi: Sunnar Halifofi shiryayyu masu shiryarwa Mahadi: Wanda Allah ya shirye shi zuwa ga gaskiya kuma anyi amfani da shi a sunaye har sai da ya zamanto kamar yawancin sunaye kuma da shi ne aka sanya Mahadi wanda manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi albishir game da shi cewa zai zo a karshen zamani.34
Wannan magana ce da ba za ta zo ba sal daga wanda yake ganin ingan-cin hadisai game da Mahadi kai hatta ma zuwansu ta hanyoyin ruwaya da dama dabam-daban a bisa batu mafi inganci.
7- Kurtubi maliki (wafati shekara ta 671 Hijiriyya) yana cikin masu ikrari da kawo wannan hadisin ta hanyoyi dabam-daban. Abu mai muhimmanci a gare mu a nan shi ne cewa game da hadisin Mahadi daga ibm majah cewa ya yi: "lsnadinsa ingantacce ne." ya kuina bayyana a saran cewa "Mahadi daga cikin zuriyata ne daga 'ya'yan Fatima kuma shi ne ya fi hadisin muhammad Bin khalidul Jundi wanda za mu daldale shi daga bisanx.
8- lbin Taimiyya (wafati shekara ta 728 Hij iriyya) ya ce a littafin minhaijus sunna: "Lalle hadisan da yake kafa hujja da su -wato Allama Huh-game da bayyanar Mahadi hadisai ne ingantattu."35
9- Hafiz zahbi (wafati shekara ta 748 Hijiriyya) ya yi shiru game da dukan hadisan da Hakim ya tabbatar da ingancinsu a hittafin mustadrak dinsa dangane da hadisan Mahadi yana mai bayyana ingancin hadisai biyu, ya kuma yi raddin a kan wasu daga cikin wadanda Hakim ya

____________
34- An-Nihaya fi Garibul Hadis wal Asar na ibm Asir Juzu'i na 5 shafi na254.
35- Minihajus sunna na ibm Taimiyya shafi na 211 iuzu' i na 4.


( 45 )

tabbatar da ingancinsu daga hadisai game da abinda Hakim ya ingantar yana fassara yardarsa game da ingancin haka.
10- A1-Kinji Shafi'i (wafati shekara ta 658 Hijiyya) ya ce game da hadisin da Tirinizi ya kawo kuma ya inganta shi game da Mahadi (wannan Hadisi ne sahihi) dangane da wani kuma makamancinsa ya ce game cia hadisin "Mahadi daga gareni yake mai hasken fuska" "wannan hadisi ne tabbtacce mai kyau kuma ingantacce."36
11- Hafiz ibm kayyim: (wafati shekara ta 751 Hijiriyya) ya yi ikrari game da ingancin wasu daga cikin hadisan Mahadi da kuma game da ingancin wasunsu daban bayan ya kawo wani daki daga cikinsu, ibm kayyim kuwa yana daga cikin masu tabbatar da tawaturancin hadisai masu yawan hanyoyin ruwaya, kamar yadda zai zo nan gaba.
12- ibm Kasir (wafati shekara ta 774 Hijiriyya) ya ce game da isnadin wani hadisi game da Mahadi "wannanciro isnadi ne mai karfi ingantacce."37 Sa'an nan kuma sai ya wani hadisin daga ibm majah ya ce wannan hadisi ne mai kyau kuma an kawo shi ba ta fuska daya ba daga Annabi (S.A.W.A.)".38
13- Taftazani (wafati shekara ta 793 Hijiriyya) ya ce game cia bayyanar Mahadi a karshen zamani "Lalle hadisai ingantattu sun zo game da wannan Babin."
14- Nuruddin Haisami: (wafati shekara ta 807 Hijiriyya) ya kawo wasu adadin hadisai game da Imam

____________
36- AL-Bayan Fi Akhbari Sahi buz Zaman shafi na 486.
37- An Nihayatu FiL Fitani wal malahim na ibm kasir iuau i na 1 shafi na55.
3S- An-Nihayatu flu fltani waI malahim Juzu-i na 1 shaft na 56.


( 46 )

Mahadi (A.S.) sa'an nan ya yi ikrari game da ingancinsu da yarjewa da maruwaitansu.
Ya ce game da dayansu "Tabarani ya ruwaito shi a Al Ausat da kuma littafinsa na Rijal wato "Rijal" na Sihah".
Game da waninsu kuma ya Ce: "Na ce Tirmizi da kuma waninsasun ruwaito shi a takaice sosai Ahmad ma ya ruwaito shi da hanyoyi, da kuma Abu ya'ala a takaice matuka, kuma mazajensu amin-tattu ne."
Game da na uku kuwa cewaya yi: "AL-Bazaru ya kawo shi, maruwaitansa kuwa ingantattu ne."
Game da na biyar kuma ya Ce "Tabarani ya ruwaito shi a A1-Awsat, mazajensa kuma amintattu ne."
15- Suyuti (wafati shekara ta 911 Hij iriyya) ya yi wa wasu hadisai da aka ruwaito game da Mahadi (A.S.) alama da (Sah) wato ma; ana Sahihi, ga wasunsu kuma (h) watO hasanun ma'ana mai kyau ne!
16- Shaukani (wafati shekara ta 1250 Hijiriyya) kanuji ya kawo daga gare shi da batunsa game da ingancin hadi~an Imam Mahadi (A.S.) kai hatta ma da tawaturanei" ya gabata cewa ya rubuta littafi game da tawaturanCin Mahadi (A.S.).
17- Nasiruddin Albani: Ya ce a wata makala tasa mai suna: "Game da Mahadi wanda nassinsa shi ne". "Amma al'amarin Mahadi to lalle a sani cewa game da bayyanarsa akwai hadisai ingantattu yanki mai girma daga cikinsu isnadinsu ingantattu ne. "Kuma shi Albani yana daga masu bayyana tawaturancinsa39."
Za mu wadatu da wannan gwargwadon saboda takaitawa kana cewa wasu daga cikin masu bincike sun tabbatar da ikrarin malamai da masu nazari da dama game da ingancin hadisai game da Mahadi wadanda adadinsu ya kai ikrari sama da sittin.


____________
39- HawIai Mahadi na Albaniy

( 47 )

Na Biyar: Furucin Malainai game da
Tawaturancin Hadisan Mahadi:


Malaman ilimin hadisi da dama da kwararru a kan ilimin hadisi da koyarwa sun ambata a saran game da tawaturancin hadisan Mahadi a littafan Ahiussunna da Sahihai da lsnadai da wasunsu saboda la'akni da yawan da suke da shi za mu takaita ne kawai a kan wasunsu su ne:-
1- Al Barbahariy shaihin 'yan mazhabar Hanbaiiyya kuma babbansu a zamaninsa (wafati shekara ta 329 Hijiriyya) shaikh Hamud Tawijiri ya kawo daga gare shi a cikin littafin sa mai suna:
"AL lhtijaj bil Asar ala man ankaral Mahadi AL-Muntazar" shafi na 28 cewa ya ce a cikin littafinsa (sharhis sunna) "Al-lmanu bi nuzuii isa Bin maryam (A.S.): Zai sauko ya yi salla a bayan Ai-Ka'im daga zuniyar muhammadu (S.A.WoA.) kuma ha zai boyu ha cewa lmani yana nufin kudurcewa a zuciya, kudurcewa kuwa ba a gina shi a kan hadisin yan daidaiku.
2- Muhammad Binul Husainil Abiriy As-Shafi'iy: ya ce a cikin littafinsa manakibu shafi'i: "Ya zo a jejjere ta hanyoyi dabam-daban a hadisai kuma maruwaitansu da dama sun ruwaito daga Mustafa (S.A.W.A.) dangane da zuwan mahadi cewa yana daga zuriyar gidansa ne (S.A.W.A.) kurna zai yi mulki na tsawon shekara bakwai kuma zai cika duniya da adalci, kuma Annabi isa (A.S.) zai bayyana tare da shi ya taimake shi a kan kashe Dujal."
Kuma ya kawo wannan ma daga kurtubiy malikiy a littafin Tahzibil kamal 25: 146 da 181a littafin maruwaita na Muhammad Bin Khalid Ai-Jundiy, da kuma lbinul


( 48 )

Kayyim a littafin A1-manarul munif: 142/ 327 da dai sauransu.
3- Kurtubiy malikiy (wafati shekara ta 671 Hijiriyya) ya kawo maganar A bariy wadda ta gabata kuma ya karfafa shi da abinda ya kawo na daga hadisai game da Mahadi (A.S.) ya kuma kafa hujja da maganar lmam Hafizul Hakim Naisaburiy, "Hadisai daga Annabi (S.AW.A) game da bayyanar Mahadi (A.S.) da kuma cewa daga cikin zuriyarsa ne kuma daga 'ya'yan Fatima ne tabbatattu ne.40"
A cikin Tafsirinsa kuma (Jami'ul Ahkamul kur'an) ya ce "Hadisai ingantattu sun zo ta hanyoyi dabam-dabam da dama dangane da cewa Mahadi daga zuriyar manzo (S.A.W.A.) ne41."
4- Hafiz mutkin Jamaluddin maziy (wafati shekara ta 742 Hijiriyya) ya kafa hujja da maganar Abiriy wanda ya ~bata dangane da zuwar hadisan ta hanyoyi dabam-daban game da Mahadi (A.S.) bai kuma kawo wani abu da ke nuna wata tababa game da su ba ya dai kawo su ne kawai ~. zube abinda ke nuna cewa al'amari ne da aka sallama game da shi42."
5- lbinul Kayyim (wafati shekara ta 751 Hijiriyya) ya karfafa shi da maganar Abiriy da ta gabata dangane da hadisan Mahadi da suka zo ta hanycyi dabam-daban ya yi haka ne kuwa ta hanyar rarraba hadisan game da Mahadi ne zuwa kashi hudu sahih, ingantacce da kuma Hasan,mai kyau, da Gara'ib ababan al'ajabi da kuma maudhu'at,

____________
40- At-Tazkira Juzu'i na 1 shafi na 701.
41- Tafsirin kurtabiy Juzu'i na 8 shafi ne 12 1-122.
42- Tahzibul kamal 25: 146 /5 18.


( 49 )

wadanda aka(43) kaga kuma ba zai zama boyayye ba cewa tarin sahihan da kyawawan na daga cikin abinda ya kai matsayin mutawatir wato wanda ako ruwaito ta hanyayi daban-daban da dama, wanda shakku ba ya zuwa masa saboda yawansu da kuma kakkawo su.
6- ibm Hajarii Askaianiy (wafati 852 Hijiriyya) ya kawo maganar dangane da tawaturan-cinsa da wasunsa, sa' an nan ya karfafa shi da maganarsa cewa: "Acikin sallar Annabi isa (A.S.) a bayan wani mutum daga cikin wannan al'umma tare da ka-sancewarsa a karshen zamani kuma kusan lokacin tashin duniya-akwai nuni ga ingancin maganar cewa kasa ba ta rabuwa da wani tsayayye na Allah da hujj a.44"
7- Shamsuddin Sakhawiy (wafati shekara ta 902 Hijiriyya) wasu daga malamai sun bayyana a saran cewa sakhawiy na daga cikin masu bayyana a saran dangane da tawaturancin hadisan mahdi (A.S.) daga cikinsu akwai: Aiiama shaikh muhammad Arabiy Fasiy a littafinsa makasid, da kuma ma' abucin bincike Abu zaid Abdurrahman Bin Abduikadir Ai-Fasiy a mubhijui kasid, a kan abinda ya kawo daga Faizul Gumaniy. Daga cikinsu akwai Abu Abdillah muhammad Bin Ja'afar kataniy (wafati 1345 Hijiriyya) a littafin Nizamu imutanasir minal Hadisil mutawatir: 226 I 289.
8- Suyutiy (wafati 911 Hijiriyya) ya bayyana kasancewar Hadisai game da Imam Mahadi (A.S.) cewa mutawatirai ne a cikin iittafin "Al-Fawa'idul mutakasira flu Ahadisil mutawatira da kuma takaitac-censa da ake

____________
43- Tahzibut Tahzib 7:125 I 20.
44- Fatahul Bariy Fl sharhi sahihi I Bakhariy Jazu': na 6: 385.


( 50 )

kira: A1-Azhaarul mutanasira, da wasunsu daga cikin littafansa a bisa bayanin Al-Gumariy A1-shafi'iy.
9- ibm Hajaril Haisaniiy (wafati she-kara ta 974 Hijiriyya) yana kariya ga akidar musulmai da bayyanar Imam Mahadi sau dayawa ta hanyar bay-yana ruwaito hadisan ta hanyoyi dabam-daban.45
10- Muttakiy Hindiy (wafati shekara ta 975 Hijiriyya) wato marubucin littafin kanzul ummal, shi muttakiy Hindiy ya yi kariya kwarai ga akidar Imam Mahadi (A.S.) yana dogara da hujjoji da dalilai a cikin littafinsa: Al -Burhan Fi Alamati Mahdi Akhiriz Zaman".
La'alla mafi muhimmancin abinda ke cikin wannan Iittafi shi ne fatawoyi hudu kebantattu game da wanda ya karyata bayya-nar Mahadi: Fatawoyin su ne: Fatawar lbin Hajaril Haitamiy As-shafi'iy da kuma Fatawar sheikh Ahmad Abis surur Binus saba AI-Hanafiy, da kuma fatawar sheikh yahya Bin muhammad Bin Hanbaliy.
Muttakiy ya kawo nassi a kan cewa su wadannan malaman su ne ma-laman mutanen makka kuma malaman mazhabobi hudu, kuma duk wanda ya duba fatawoyinsu ya sani sani na yakini cewa su sun yi ittifaki a kan cewa hadisan Mahadi mutawaturai ne, da kuma cewa wanda ya karyata su ya wajaba ya sami horo sun ma bayyana a saran cewa wajibi ne a masa bulala a kuma ladabtar da shi a muzanta shi han ya koma zuwa ga gaskiya ko ba ya so kamar yadda suka bayyanaidan ba haka ba to a zubar da j ininsa.46
11- Muhammadu Rasulul Barzanji (wafati shekara ta 1103 Hijiriyya) ya bayyana tawaturancin hadisan Mahadi

____________
45- Sawa'ikul muhrika shafi na 122-126 Fasali na lBabi na 1.
46- Alburhan ala alamatil mahdi Akhiriz Zaman shafi na 178 -183.


( 51 )

(A.S.) a saran yana cewa: "Hadisai game da samuwar Mahadi da kuma bayyanarsa a karshen zamani da kurna cewa daga zuriyar manzon Allah (S.A.W.A.) yake daga' ya' yan Fatima (R.A.) sun kai gwargwadon mutawatir, wandaaka ntwaito ta hanyoyi dabam daban masu dama, a ma' ana kuma babu wata ma' ana dangane da musa
12- Sheikh Muhammad Bin kasim Bin muhammad Jasus (wafati 1182 Hijiriyya) kattaniy ya kawo a littafin NazmuL mutanasir ya bayyana cewa mutawaturi ne.48
13- Abul Ala'l lrakiy Al Fasiy (wafati shekara tal 1183) yana da littafi game da Imamul Mahadi, kuma ya kawo a cikin littafin Nazmil mutanasir cewa hadisai game da Mahadi mutawaturai ne.
14- Shaikhul Safariniy Al-Hanbaliy (wafati 1188 Hij iriyya) Al-kanuj I ya kawo daga gare shi cewa shi yana daga cikin masu cewa hadisan Mahadi (A.S.) mutawaturai ne, a lattatinsa mai suna Allawa'ih49.
15- Shaikh Muhammad Bin Au Al-sabani (wafati shekara ta 1206 Hijriyya) ya kawo batun mutawaturanci daga ibm Hajar a littafin As-sawa'ik da wasunsa ya kuma nuna cewa shi ma na daga maganarsa.50
16- Asshaukani: (wafati shekara ta 125 Hijiriyya a shahararren iittafinsa (Al-taudhi fi tawaturi maja'a flu muntazar wad Dajjal wal masih) ya wadatar wajen tabbatar da matsayinsa game da tawaturanci Hadisai game da Mahdi (A.S.).

____________
47- Al lsha'a Ii ashratus sa'a Al-Barzanji shafi tm 87.
48- littafin da ya gabata 226-289
49- Al-lza' atu na Al-kanuji shafi na 146.
50- As'a furragi bin, 145, 147 da 152.


( 52 )


17- Mumin bin Hasan bin mumin As-shabalanj i (wafati shekara ta 1291 Hijiriyya) ya bayyana a saran cewa hadisai game da Mahadi (A.S.) mutawaturai ne kuma shi daga cikin AhIul Bait yake.5'
18- Ahmad Zainiy Dahlani mufti shafiiyya (wafati shekara ta 1304 Hijiniyya) ya bayyana a saran kan cewa Hadisai game da Mahadi (A.S.) na da yawa kuma ya ce "(kuma yawan wadanda suka kawo shi yawan sashe na karfafa sashe har ya kai ga darajar da ke ha da ma' anar hujja tabbatacciya) kuma ba zai boyu ha cewa matsayin tabbatac-ciyar hujja a hadisai na samuwa da tawaturanci.
19- Sayyid Muhammad sadik A1-kanuci A1-Bukhaniy (wafati shekara ta 1307) ya ce game da hadisarn Mahadi (A.S.) "Hadisan da aka ruwaito game da shi duk da sabaninsu suna da yawa matuka sun kai matsain mutawaturai."
20- Abu Abdillah Muhammad Bin ja'farul kattani Al-maliki (wafati shekara ta 1345 Hijiriyya) ya kawo magana game da tawaturanci daga wasu da muka ambata su har ya Ce: "kuma abinda yake tabbatacce shi ne cewa hadisan da suka zo game da Mahadi da ake saurara mutawatirai ne"52
Da dai sauransu wadanda wannan bayani takaitacce ha zai wadatar ha mu kawo dukan maganganunsu kuma wasu masu bincike sun hi diddiginsu tun daga kami na uku har zuwa wannan zamanin.
A nan babu makawa mu rubuta muhimmiyar kalmar malam Badiuz zaman sa'id An-Nurisiy -wanda yana daga cikin manyan malaman Ahlis sunna a farkon karni na goma sha hudu Hijiriyya, ya ce:

____________
5'- AL-Futuhatul Islamiyya .Juza' I na 2 shafl na 211.
52- Dafa'u anil kafiy na samir umai diy Juzu'i na I shafi na 305-343.


( 53 )


"A duniya baki daya babu watajama'a mai asali mai albarka mai daukaka da ke daukaka zuwa ga darajar Ahlul Baiti da matsayinusu, kuma a cikinta babu wani taro ko wata jama'a mai haske da t~ fi hask~kawar jama'ar Ahlul Bait da mutanensu. Na'am lalle zuriyar Ahlul Bait wadanda aka ciyar da su ruhin hakikana Alkur'ani kuma sun shayu daga mabubbugarsa, kuma sun haskaku da hasken daukakar Imanin Musulunci don haka suka ketare zuwa ga kamala, suka samar da daruruwan gwaraje madaukaka, kuma suka kaddamar da dubban ja-goran kyautata zukata doinin ja-gorancin A1'umma, babu makawa cewa su suna bayyana wa duniya adalci cikakke da ja-goransu mafi girma A1-Madi A1-Akbar, da kuma hakkinsa na raya shari'ar Muhammadiyya da Kuma hakikanin Furkani Mai rarrabe tsakanin karya da gaskiya, da sunnar Ahmadu da aiki da ita da gudanar da ita.
Kuma wannan al'amari yana cikin matukar abubuwa na hankali ballantana kuma na matukar cikin lazimai da kuma larurai barna haka ba kawai a'a haka ka'idar dokokin rayuwar zamantakewa ya hukunta,


( 54 )

FASALI NA BIYU


Wane ne Imam Mahadi (A.S.)?


Ya bayyana Daga bayanan da suka gabata haduwar musu~mi da imanin su game da bayyanar Mahadi a hadisai mutawa-tirai daga Annabi (S.A.W.A.) kuma a nan babu makawa ga musulmi ya tambayi kansa ya Ce:
ldan dai har hadisan Mahadi da suke bushara da bayyanarsa a karshen zamani sun kai haka a matsayi da bayyana a saran a gurin malaman musulunci har ma kuma sun tabbatar da ingancinsu kuma suka bayyana a saran cewa mutawatirai ne to don me wasu ruwayoyin suka sassaba dangane da nasabar Mahadi (A.S.) kuma mai yi wuwa ne ma wasu daga cikinsu sun kai ga matsayin warware juna da zama kishiyoyin juna? To wane ne shi Imam mahadi din shin yana yiwuwa a cikin inn wannan sabanin a bambance shi ta yadda ba zai zamanto akwai koda shakku dan kadan wajenjuyar da lakabin (Mahadi) daga aihihin wanda aka sanya wa sunan alal hakika? Domin amsa wannan babu makawa a yi bayanin inn nau'in abinda ke tarnake da ke aukuwa wajen ayyana nasabar Imam Mahdi (A.S.) duk kuma da cewa ya yi imani game da bayyanarsa a karshen Zamani, amma wajibi ne kafin bayanin haka a yi takidin cewa wanda yayi imani da bayyanar mahdi amma bai ayyana gare shi wane ne shi mahadin ba to misalinsa kamar wanda ya san


( 55 )

tabbacin wajibcin salLa ne amma yajahulci ruku-nan duk wanda ya zaina haka kuwa to ba za a ce shi mai salla ne ba to haka hahn wanda ke jiran bayyanar mahadi yake alhali bai san shi ba,kamar yadda za mu ~abbatar da shi ko ta hahn kaka dai warkar da duk wata matsala game da nasabar Imam mahadi wannan fasalin ya dauki nauyinsa idan kuwa har mai karatu ya biyo mu tiryan-tiryan to zai sami yanki cikakke na amsar tambayar: Wane ne mahadi da aka yi alkawari kuma ake jiran bayyanarsa? Kuma muna masu yi masa alkawari eewa za mu raba kanmu da duk wani abinda zuciyarrnu ta sakankance da shi tun tuni. Domin kada ya zamanto shi ne mai ja-garantar dalilin ma-tukar kaiwa ga gaskiya ita ce manufa sawa'un gaskiyar ga ribar mu ne ko kuma nba a kanmu mai hankali kuwa shi ne wanda tsakaninsa da gaskiya babu ada-wa, tunani a kan maganarmu zai shaide mu da gaskiya a kan abinda muke lada wajen magance sarkiyar ayyanawa a bayanin da ke biye:-
Abin da muke nufi da sarkiyar ayyana-war hadisai wato hadisan da daga nesa za a ga kamar cikinsu akwai sabanin juna da junansu wanda zai yi waha-la ga mutane musamman ma wadannan da ba su da sadarwa da ilimin hadisai da warware su, abinda ke saukakewa kwarai- da auku-war mai raunin lmani daga cikinsu wajen hada kai da wadanda ba su yarda da mahadi ba sawa'un suna daga cikin wadanda ake yi wa suna da musulmi ne ko kuma wadanda ke bayyana kiyayyarsu a saran ne ga wannan addinin.


( 56 )

Hadisai Game da Nasabar
Imam Mahadi (A.S)

Mahadi daga kinana, Bakuraishe kuma daga Bani Ilashim yake. Makdisi As-shafi'iy ya kawo hadisi a littafin Akdud Durar, da kuma rnakarnancinsa da Hakrm ya kawo a mustadrak wanda yake danganta Imam mahadi (A.S.) ga kinana sa'annan kuma ga kuraish, sa'an nan kuma zuwa ga Bani Hashim kuma shi yana daga cikin ruwayoyin katadata daga Saud Bin Musayyib, ya Ce: na ce wa Sa'id Binul musayyib: "shin mahadi gaskiya ne" ya Ce: gaskiya ne Na ce daga wa yake? Ya ce daga kinana. Na Ce: Sa'an nan daga wa? Ya cc daga kuraishawa. Na Ce. kuina daga wa? Ya cc daga Bani Hashim... zuwa karshen Iiadis~n" sa'an nan kttma ya cc Imam AbuI I Iusaiii Ahmad Bin Ja'afar AI-manawiy ya kawo shi irnarn Abu Abdullah Na'im Bin Hammad ma ya kawa shi.5~ mai yiwuwa ana iya kintata cewa hadisin yana warware kansa da kansa, saboda wani lokaci ya hada nasabar Imam mahadi da cewa daga kinanata yake sa'an nan kuma ya Ce daga kuraish yake wani Iokaci kuma ya ce daga Bani Hashim yake Amsa kuwa ita Ce: babu bam-banci a kan haka dukkanin sa, domin dukan wani Bahashime to daga kuraishawa yake, dukan Bakuraishe kuwa daga kinanata yake domin kuraish shi ne Nadhra Bin kinana kamar yadda masana nasaba suka yi ittifaki a kai.

____________
53- Akadud Durar: shafi na 42-44 Babi na fatko, mustadrakul Hakim Jusu'i na4 shafi na 553 da rnajma'usz Zuwa'id iuz'i na 7: 115.


( 57 )

Hadisin Cewa Mahadi (A.S.) daga
'Ya'yan Abdul Mutallib ne:

Shi ne wanda ibm Majah da waninsa suka ruwaito daga Anas bin rnalik ya Ce: "Manzon Allah (S.A.W.A.) ya Ce: ~U 'ya'yan Abdulmutallib shugabannin 'yan Aljanna ne, ni da dan'uwana Aliyu da Baffana Hamza, da Ja'afar da Hasan da Husaini da mahadi sa'an nan ya cc: Jama'a daga shugabannin masana hadisai sun kawo shi a littafansu, daga cikinsu akwai "irnam Abu Abdullah muhammad Bin yazid Bin majah Al-kazwini a sunan dinsa da Abul kasim A1-Tabaraniy a mu'ujam dinsa, da kuma Abu Na'im lsfahaniy da wasunsu.54 Wannan hadisin baya warware abinda ya gabata sai dai ma ya kayyade abinda yake kafinsa ne domin babu sabani cewa Abdulmutallib kakan Annabi (S.A.W.A.) da ne ga Hashim, don haka ya'yan Abdulmutallib tilas Hashimawa ne sahoda haka Mahadi daga 'ya'yan Abdulmutallib Bin Hashim Bakuraishe Bakinane ne.
Hadisin cewa Mahadi daga 'ya'yan Abi Talib ne wannari hadisin shaikh mufid ya kawo shi a littafin lrshad, da kuma makdisi Asshafi'i a littafin Ikdud Durar kuma yace: Na'im Bin Hammad ya kawo shi a littafin fitan. Shi hadisin kuma yana daga ruwayar Safar Bin Umair ya Ce: Na kasance a gurin Abi Ja'far mansuri sai ya fara da ce mini: ya saifu Bin umair, babu inakawa wani mai kira zai yi kira daga 'ya'yan Abi Talib, sai na ce masa a sanya ni in zama fansa gareka ya Amirul muminin kai ma kana ruwaito wannan? Ya Ce: Na rantse da wanda raina ke hannun sa kunnena ne ya ji shi: sai na ce ya. Amirul mumi.nin lalle wannan ha disin ban taba jin sa ba kafin

____________
54- Aksdud Durur shefi iia 195 Babi na Bakwai.


( 58 )

wannan lokacin. sai ya Ce: ya saifu lalle shi gaskiya ne, idan kuma da ya kasance to mu ne farkon wanda zai arnsa shi an-ima wannan kiran ga wani ne daga 'ya'yan baffanmu. Sai na Ce: mutum daga 'ya'yan Fatima? Sai ya Ce: E, ya saifu idan da ba don naji shi daga Abi Ja'afar muhammad Bin Aliyu yana ba ni labarinsa ba, kuma mutanen bayan kasa baki daya suka ba ni labarinsa to da lalle ban karbe shi daga gare su ba sai dai kuma muhammad Bin Aliyu ne."55
Wannan hadisin ma yana kayyade wanda ya gabace shi ne domin duk wanda ya hadajini da Abi Talib babu makawa ya hada da mahaifinsa Abdulmutallib. Tare da runtse ido game da Furuci a saran da ya zo game da wannan hadisin na cewa mahadi daga 'ya'yan Fatima (A.S.) yake kamar yadda za mu kawo wasu hadisan nan gaba. Don haka sakamakon zai zamanto cewa laIle shi mahadi da aka yi bushara da bayyanarsa a karshen zamani tabbas shi daga 'ya'yan Abi Talib dan Abdulmutallib Bin Hashim bin kuraishi bakinane ne.
Hadisan (mahadi daga 'ya'yan Abbas ne.)
Babu shakka inn wadannan hadi-san suna zaniantowa rikitau game da fayya ce ko wane ne mahadi sosai domin 'ya'yan Abbas ba 'ya'yan Abi Talib ba ne saboda haka babu makawa a yi nazarin wannan nau'in hadisan Don haka muke cewa:-
Za a iya raba hadisan biyu: Na Farko: Hadisan da wannan ma'anar a dunkule suke: su sun takaita ne da hadisan tutoci daga cikinsu akwai wadanda Ahmad ya kawo a musnad dinsa daga saub?n daga manzon Allah (S.A.W.A.) cewa ya Ce:

____________
s5- Irshad, na mufid iuzu'i na 2 shafi na 370 -371 da Akdud Durar shafi na 149 Babi na hudu.


( 59 )


"ldan kuka gano tutoci bakake sun fuskanto ku daga khurasan to ku zo gare su ko da kuwa da rarrafe ne a kan kankara, domin lalle a cikinta akwai mahadi Halifan Allah.56
Hadisin ibm majah a sunan57 dinsa ya yi kusa da wannan. Kamar kuma yadda Tirmizi ya ruwaito da isnadinsa daga Abu Huraira daga manzon Allah (S.A.W.A.) cewa ya Ce:
"Bakaken Tutoci za su fito daga khurasan babu wani abu da zai iya juyar da su har a kafa su a Iliya'i"58
Wannan hadisan ko da yake a cikinsu ba a bayyana a saran ba cewa Mahadi daga 'ya'yan Abbas ne amma wasu na iya fahimtar haka daga hadisan bisa bayanin cewa wadannan tutocin bakake na iya zamantowa tutocin nan da Abu muslim khurasani daga khurasan ya kafa daular Abbasawa da ita don haka wadannan hadisan ke nan sal su zamanto suna nufin Mahadin Abbasawa ne.(59)

Raunin Hadisan da Kuma Rashin
Ishararsu ga Mahadi:

lbinul kayyim a littafin "Al-manarul munif" sa'an ya ce "kuma wannan wato hadisin -na lbin majah -da kuma wanda yake kafin shi babu wani nuni a cikinsa da ke cewa Mahadin da ya gabata daga Banil Abbas shi ne wanda zai bayyana a karshen Zamani."60

____________
56- Musnad Ahniael Jusu'i na 5 shafi na 277.
57- Sunan ibm majab iuzu 'I na 2 hadi si na 1336 14082.
58- Sunan Tirmizi juzu'i na 4 shafi na 531/ 2269.
59- LaIIe shi hadisin musnad Ahmad, da na sunan ibm majah rauninsa a gurin malarnai ba gada daya ha ne, daga cikinsu akwai
60- Sunan Tir mizi Juzu'i na 4 shafi na 531 hadi si na 2269.


( 60 )


Kuma daga cikin abinda ke nuna haka shi ne cewa wancan mahadin na Abbasawa ya riga ya mutu a shekara ta 169 Hijiryya, kuma a zamaninsa an ga kutsawar mata cikin al'amuran hukumarsa.Tabariy ya ambata tsomuwar khiziran matar shi khalifa mahadi Abbasi din cikin hukumarsa da kuma cewa ta yi kane-kane a kan al'amura a zamanin dansa Hadi61 wanda al'amarinsa zai zamanto haka ta yaya za a ce shi halifan Allah ne a bayan kasarsa.
Wannan kari ne a kan cewa shi mahadi Abbasiy da ma halifofin Bani Abbas baki dayansu basu kasance a karshen zamani ba kuma babu wani da ya yi kwadayin dukiya kamar kwadayin daya daga cikinsu kuma ba a yi musu bai'a a tsa-kanin Rukni da makama lbrahim ba ba su kuwa yaki Dujal ba, Annabi isa (A.S.) bai sauko don ya yi salla a bayan mahadinsu ba kuma ba a kifar da hamada a zamaninsu ha, kurna wata alama rnafi karancin alama daga alamon~in bayyanar mahadi bata bayyana ha a zamaninsu.
Amma dangane da hadisin Tirmizi kuwa ibm kasir ya riga ya sifanta shi da cewa hadisi ne bako. Sa'annan ya Ce:
"Wadannan tutocin bakake ha su ne wadanda Abu muslim khurasaniy ya zo da su ya hambare hukumar Bani umayya a shekara ta dan da talatan da biyu ha, sai dai bakaken tutoci ne na dabam wadanda za su zo tare da Mahadi..., wato abin nufi Mahadi sha yabo wanda aka yi alkawarin samuwarsa a karshen zamani fitowarsá da bayyanarsa za su kasance iie daga yankin Gabas"62 Ina cewa: Ba zai gagara ba masu kira ga Abbasiyawa su yi amfani da wannan hadisin domin yada al' amarinsu. kamar kago hadisan da suka yi game da wannan ma'anar a

____________
61- Tarikhi Tabariy Juzu'i na 3 shafi na 466.
62- Annihayatu Fil Fitani wal malahim na ibm kasir Juzu' i na I shafi na 55.


( 61 )

sarari kuma za mu kawo nan gaba a wannan bayanin, idan kuwa ba haka ba to aF amari ne mawuyaci kwarai a musanta hadisan bakaken tutoci wadanda ha sa nuna kome Fiye da bullowar dakarun sojoji masu taimakon Mahadi daga kusurwar Gabas, saboda ruwayarsa ta hanyoyi da dama wadanda Hakim ya iriganta wasunsu a bisa sheradin Buhari da Muslim.(63)

Na Biyu: Hadisai da Suka Bayyana
Wannan Ma'anar a Sarari

1- Hadisin: "Mahadi daga 'ya'yan Abbas baffana yake." Suyuti ya kawo shi a Jami'us Sagir ya kuma Ce; "Hadisi ne rarrauna."64
Manawi As-Shafi'i ma ya ce cikin littafin Faizil kadir "Darul kutniy ya ruwaito shi a Afrad. lbinul jauzi ya ce: cikinsa akwai Muhammad Binul Walid Mukarriy, yace ibm udaiy yana kaga hadisi kuma yana sadar da shi, yana kuma satar isnadai da matanai. Ibm Abi ma'ashar ya Ce: shi makaryaci ne, samhudiy ya ce: abinda ya ke bayansa da wanda ya ke kafinsa ya fi shi inganci amma wannan kuwa akwai muhammad bin walid a cikinsa., kuma mai kirkire ne."65
Suyuti ya raunana shi a littafin A1-Hawiy, da kuma Ibinul Hajar a littafinsa Sawa'ik da Sabbanu a littafinsa Is'af da Abul Faiz a littafin Ibrazul wahamil maknun kuma

____________
63- Mustadrakul Hakim Juzu'i na 4 shall na 502.
64- Jami'us Sagir iuzu'i na 2 shall na 672 hadisi na 9242.
65- Faidul kadir sharhin iami'us sagir Juzu'ina 6 shafi na 278 hadisi na 9242.


( 62 )

kuma sun kawo kalmomi da dama da ke bayyanawa a saran cewa kaga shi aka yi.66
2- Hadisin ibm umaar: "Wani mutum zai fito daga 'ya'yan Abbas" kuma ya riga ya ruwaito shi a littafin kharidatul Aja' lb kai tsaye daga ibm umar kuma daga kansa ya tsaya67 wannan kuwa kari ne a kan rashin isnadin abinda ke kara tabba-tar da raslhin ingancin hujja da shi kan cewa bai fito karara game da Mahadi a cikinsa ba, don haka abinda ya fi shi ne hada shi da bangare na farko wanda yake a dunkule koda kuwa an ambata sunan Abbas karara a cikinsa.
3- Hadisin ibm Abbas daga Annabi (S.A.W.A.) cewa ya ce ga baffansa "Lalle Allah ya fan musulunci da ni kuma ya ce ga baffansa "LaIle Allah da sannu zai cike shi da yaro daga 'ya' yan ka kuma shi ne wanda zai gabaci l~a dan maryama"
Khatib Bagdadiy ya ruwaito shi kuma a isnadinsa akwai muhammad Bin mukhallad shi kuma ibm mukhallad zahabiy ya raunana shi ya kuma yi al'ajabi game da rashin raunana shi da ibm khatib ya yi, ya Ce: "ya ruwaito shi daga muhammad Bin mukhallad Attar abin al'ajabil ne cewa khatib ya ambace shi a tarihinsa amma hal raunana shi ha tamkar ya yi shiru game da shi ne don keta hahn sa. "68
4- Hadisin ummul Fadhhi daga Annabi (S.A.W.A.) "ya Abbas idan shekara dan da talatin da biyar ta yi to wannan

____________
66- AI-Hawiy na Fattawiy Juzu'i na 2 shafi na s5 da As-sawa'ikul murika shafi na 166 da Is' afur R~gibin shafi na 151 da Ibrazul wahmal maknun shafi 563.
67- Tarilh Bagdad iuzu' i na 3 shafi na 323 da Juzu' i na 4 shañ na 117.
68- Mizanu'I I'Itidal iuza'i na 1 shafi na 89 hadisina 328.


( 63 )

taka ce da 'ya'yanka daga cikinsu akwai saffah, daga cikinsu akwai mansur daga cikinsu akwai mahadi" wannan hadisin ma khatib ya kawo shi da kuma ibm Asakir daga ummul Fadhli.69
Zahabiy ya ce game da shi: "A isnadinsa akwai Ahmad Bin Rashid Al Hilaliy, daga Sa'id Bin Khaisam, da hadisi batacce game da ambaton 'ya'yan Abbas daga Maruwaitan Khaisam, da Hanzala har zuwa inda ya ce daga Ahmad Rashid- shi ne wanda ya kago shi da jahiici."70
Ina cewa: Zahabiy ya yi ishara da wannan gajahilcin Ahmad bin Rashid a wajen kaga hadisi domin hukuncinsu ba a shekara ta 135 ya fara ba hukuncinsu ya fara ne a shekara ta 132 Hijiriyya kamar yadda aka yi ittifaki, wannan na daga alamun jahilcinsa game da hukuncin Bani Abbas.
5- Kwatankwacin wannan ne kuma abinda Suyuti ya kawo daga ibm Abbas a littafinsa A1-la'ali Masnu'a I'il Ahadisil maudu'a kuma ya Ce: "Kagagge ne da ake zargin Gullabi7' da shi."
Ibn Kasir ya kawo shi a littafin Albidaya wan Nihaya daga ruwayoyin Dhahhaku, daga Ibm Abbas kuma ya Ce: "Wannan Isnadinsa mai rauni ne, kuma Dhahhaku bai ji wani abu daga Ibm Abbas ba a bisa abu sahihi, don haka yankakke72 ne."
Kamar kuma yadda Hakim ya kawo shi ta hanyar da Isma'il Bin Ibrahim Bin Muhajir73 yake cikinta kuma Abul Faiz A1-Gumariy As-Shafi'i ma ya ruwaito daga Zahabiy

____________
69- Tarikhu Bagdad Jizu'i na 1 shfi na 63. Da Tarikhu Dimashk4: 178
70- Mizanu'I I'tidal iuzu'i 1:97.
71- AlaliyaI Masnu'a iuzu'i na 1 shafi na shafi na 434-435.
72- Al-Bidaya wan Nihaya Juzu'i na 6 shafi na 246.
73- Mustadrakul Hakim iuzu'i na4: 514.


( 64 )

cewa Isma'ila an yi ittafaki a kan rauninsa, Amma Kuma Babansa ba haka yake ba.74
Wadannan su ne hadisan da wasu ke iya ruduwa da su su dauka cewa shamakai na gaskiya ne a gaban fayyace dangantakar Imarn Mahadi (A.S.) Kuma ya riga ya bayyana cewa sakamakon karshe game da dangantakar Imam Mahdi cewa shi daga 'ya'yan Abi Talib yake gaskiya ne tare da kasancewar hadisin da ke cewa Mahadi daga 'ya'yan Abbas ne kagagge iie tare da rashin nunin hadisin tutoci akan wani abu sabanin wancan sakama kon. kuma da sannu tarin hadisari Mahadi wani daki dabam za su zo. da ke yanke cewa Mahadi ba daga 'ya'yan Abbas ba ne tabbatacce.

____________
74- Ibrazul Wahamil Maknuii shell tia 543.


( 65 )

HADISIN MAHDI DAGA 'YA'YAN
ALl (A.S) YAKE

To da yake Abu Talib yana da 'ya'ya masu yawa sal hadisai suka zo dornin su ayyana abinda ake nufi kurna su nuna cewa wanda ake nufi cikin 'ya'yansa shine Amirul Muminen Au bin Abi Talib (A.S.) domin Mahdi ya zama daga 'ya'yansa wato sayyidina Au, to hadisai sun zo da wannan ma'ana, karnar cewa da All bin Abi Talib (A.S.) yayi "shi mutum ne daga gareni""
Saidai bai buya ga wani ba cewa imarn Au yana da 'ya'ya masu yawa saboda haka sal an samu karin bayani kafin asan wanda ake nufi to wannari bayani kuwa samunsa mai sauki iie domin kuwa daga ruwayoyi da suka yi rnaganar dangantakar imam Mahadi sun ce Mahdi na daga AhluI Bait wasu kuma sun ce Mahdi daga zuriyar Manzo yake sa'annan akwai wadan da suka ce Mahdi daga Annabi yake, kurna dukan wadannan hadisai ingatattu ne kuma rnutawatirai.
To kuwa babu shakka cewa babu wanda aka sansu da cewa su Ahlu Baiti ne kurna zuriyar rnanzo ne kuma ya'yan manzo ne, face 'ya'yan imam Au ta hanyar Fatimatuz zahra (A.S.), to ga wasu hadisai dake nuna haka:

____________
75- AL-fitan INa'im bin I-larnrnad 1: 369 /1034 AL-Tashrifbil Minan Isayyid bin Tawus: 17'6 /238 babi na 19.


( 66 )

HADISAN MAHDI DAGA AHLUL-
BAIT YAKE (A.S.):

(1) Hadisin da yake cewa "kwanaki ba zasu kare ba kuma zamani ha zai tan ba, har sai wani mutum daga Ahli baiting ya mallaki larabawa, sunansa yana daidai da sunana."
Wannan hadisin Ahmad ya ruwaito shi a musnadinsa daga ibn Mas'ud, ta hanyoyi dabom-daban. Abu Dawud shi ma ya ruwaito shi a sunan nasa, Tabrani shi ma ya ru'vaito shi a Mu'ujamul kabir. Tirmizi da kanji na shafi'awa sun inganta shi. Bagawiy kuwa ya kirga shi a cikin hadisai masu kyau.76
(2) Hadisin da yace "da dai zamani bai saura ha face yini daya, to da sai Allah ya aiko daga Ahlul Bait wani mutum zai cika kasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci."
To wannan hadisin shine wanda aka ruwaito daga irnam Ali (A.S.) daga Manzon Allah (S.A.W.A.). Ahmad ya ruwaito shi a Musnadinsa da kuma lbn Abi shaiba da

____________
76- Musnad Ahmad 1: shafi na 376 da 377 da 430 da 448. Sunan Abi Dawud 4: 107/ 4283. Mujamul kabir na Tabrani 505/2230. Al Bayan fl Akhbar sahbi zaman: 481 babi na 1. Masabihus sunna 3: 492 142 10


( 67 )

Abu zar da Baihaki. Tabrasi a cikin Majma'ul Bayan yayi ishara,(77)ga ittifakin shi'a da sunna akan ruwaito shi. Abu Faiz Al Gimari dangane da wannan hadisin yace "ingantacce ne babu wani shakka ko kokwanto".(78)
(3) Hadisin dake cewa: "Ba za a yi tashin kiyama ba har sai wani mutum daga Ahlu Baitina yayi shugabanci sunansa daidai da sunana".
Wannan hadisi lbn Mas'ud ya ruwaito shi daga manzon Allah (S.A.W.A). Ahmad da Tirmizi sun fito da wannan ruwayar daga lbn Mas'ud, sa'annan Tabrani ya ruwaito shi daga hanyoyi da, yawa. Kanji da shaikh Tusi suma sun ruwaito shi kuma sun ce ingantacce ne.
Abu Yu'la at Musiliy shirna ya ruwaito shi a Musnadinsa daga Abu Huraira79. A cikin Durrul Manthur kuwa ga abinda ya zo: "Tirmizi ya fito da shi daga Abu Iiuraira, kurna yace ingantacce ne'XSO
(4) Hadisin da yace "Mahdi daga mu Ahlul Baiti yake madaukaki kuma mai hasken goshi, zai cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda aka cika ta da zalunci da ja'irci".

____________
77- Musnad Ahmad na I shafi na 99. AI-Musannafna Ibn Abi shaiba na 15 shafi na 198/ 19494. Sunan Abi Dawda na 4 shafi na 107/ 4283. AI-ITIKAD na Baihaqi shafi na 173. Majma'ul Bayan na 7 shafi na 67.
78- lbrazul Wamil Maknun shafi na 495.
79- Musnad Ahmad na I shafi na 376. Sunanu Tirrnizi na 4shafi na 505/3231. Mu'jamul kabir na Tabrani na 10 shafi na 165/10220 da 10221 da kuma na 10 shafi na 167 hadisi na10227. Al Bayan na kanji shafi 481. Kitabul zaiba na Tusi shafi 113. Musad Abi yu'la Musiliy na 12 shafi na 19 /6665.
so- Durrul Manthur na 6 shafi na 58.


( 68 )


Wannan kuwa yana daga hadisin Abu sa'id al khidriy daga Annabi (S.A.W.A). Abdur Razzak ya fito da shi daga gareshi. Hakim kuma yace sahihi ne a bisa sharadin Muslim. Arbilliy shima .ya kawo shi a kashfil Gumma.(18)

____________
81- Al-Musannaf na Abdul-Razzak Iittai na 11 shall na 372 / 20773. Mustadrakul Hakim na 4 shafi na 557. Kashful Gumma na 3 shafi na 259.


( 69 )

HADISAN MAHDI DAGA ZURIYAR
MANZO (A.S.) YAKE

Hadisai da dama sun zo da wannan ma' ana amma zamu zabi daya daga cikin su, shine hadisin Abu sa'id al khidriy daga Manzon Allah (S.A.W.A) cewa yace:
"Tashin kiyama ba zai zo ba har sai kasa ta cika da zalunci da shishshigi sannan sai wani mutum daga Ahli Baitina ko daga zuriyana - wannan shakku daga wanda ya ruwaito ne-ya fito ya cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda aka cika ta da zalunci da shisshigi"
Ahmad da lbnu Habban sun fitar da shi. Hakim shima ya inganta shi akan sharadin Buhari da Muslim. Safi shima ya kawo shi a cikin Muntakhabul Athar.82
Abu faid al Gimari asshafi'iy bayan yayi bincike cikakke ga hanyoyin wannan hadisin da kuma bin halayen maruwaitansa, sai yace "Hadisin nan ingantacce ne a bisa sharadin Buhari da Muslim kamar yadda Hakim yace".(83)

____________
82- Musnad Ahmad na 3 shall na 36. Sahih Ibn habban na 8 shall na 290/ 6284. Mustadrakul Hakim na 4 shafi na 557 Muntakhabui Athar shafi na 148/ 19.
83- Ibrazul Wahmil Maknun shall na 515.


( 70 )

HADISAN MAHDI DAGA 'YA'YAN
ANNABI (S.A.W.A) YAKE:

Daga cikinsu akwai hadisin da Abu Sa'id AL khidri ya ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.A).
Mahdi daga gareni yake mai hasken goshi mai kyan hanci zai cika kasa da adalci da daidaito kamar, yadda aka cika ta da zalunci da ja'rci, zai yi mulki na tsawon shekaru bakwai ."
Wannan hadisin Hakim yace ingantacce ne ak,an sharadin Muslim. Hakanan kanji Bashafi'e da suyuti da sheikh Mansur Au Nasif a cikin Tajul Jami'i lii usul da Abul faiz.84
To dukkansu sun inganta hadisin. Bagawiy kuma yace yana daga cikin hadisai masu kyau lbnul kayyim kuwa yace tafarkin ruwayar mai kyau ne.85
Wadanda suka fitar da shi daga Abu sa'id sune Abu Dawud da Abdur Razzak da khatabiy a cikin Ma 'alimul

____________
84- Mustadrakul Hakirn na 4 shafi na 557. Albayan na kanji shafi na 500. Jami'us sagir na 2 shafi na 672/ 9244 Tajul Jami'i lii usul na 5 shafi na 343. !burazul Wahmil Maknun shafi na 508.
85- Masabihus sunna na 3 shafi na 492/4212. AL Manarul Munifna Ibnul kayyim shafl na 144/ 330.


( 71 )

sunan. Daga shi'a kuwa sune sayyid lbnu Tawus da lbnu Batrik.86
Sa'annan har yanzu daga ciki akwai hadisin Amirul Mumuneen (A.S.) daga Manzon Allah (S.A.W.A) yace: "Mahdi daga 'ya'yana yake boyuwa zata zama tare da shi da demuwa wanda al'urnmu zasu bata a cikinsa, zai zo da taskar Annabawa (A.S.) sai ya cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda aka cika ta da zalunci da ja'irci"
Wannan hadisin sheikh saduk ya fitar da shi a kamaludden. Juwaini Bashafi'eya kafa hujja da shi a fara 'idus simtain da kanduzi Bahanafe a yanabi'ul Mawadda.87
To da wannan bayanin ya fito fill a saran cewa Mahdi ba makawa daga 'ya'yan Au (A.S.) daga wajen FATIMATUZ ZAHRA (A.S.) yake. Kuma hakan ya zo a bayyanc kamar yadda yanzu za mu ambata:

____________
86- Sunan Abu Dawud na 4 shafi na 107/ 4385. Al Musannaf na Abdur Razzak na 11 shafi na 372/ 20773. Ma'alimul sunan na 4 shafi na 344. Al Tashrifbil Minan shafi na 153/189 da 190 Babi na 159.Hakana daga lbn Hammad a Al fitan na 1 shaf na 364/ 1063 da 1064. Umda na lbn Batrik Al Hilli shafi na 433/ 910.
87- Kamalud-deen na lshafi na 287/ 5 Babi na 25. Fara'idus simtain na 2 shafi na 335/ 587. Yanbi'ul Ma wadda 3 Babi na 94.


( 72 )

HADISIN MAHDI DAGA 'YA'YAN
FATIMA (A.S.) YAKE

Yana daga ruwayoyin Ummu Salaina daga Manzon Allah (S.A.W.A) cewa yace: "Mahdi gaskiya ne kuma yana daga 'ya'yan Fatima".
Abu Dawud da lbnu Majah da Tabrani sun fitar da shi daga ummu salarna. Hakim kuwa ya fito da shi daga hanyoyi biyu. Hudu daga Malaman Ahlus-sunna sun fito da shi daga sahih Muslim.88
Sauran kuma wasu sun yadda da ingancinsa da kuma kyan tafarkin da aka ruwaito shi, bil hasali ma wasu sun fada a saran cewa hadisi ne mutawatiri.89

____________
88- Sunan Abu Dawud na 4 shafi na 107/ 4284. Sunan lbnu Majah na 2 shafi na 1368/ 4086. Mujamul kabir na Tabrani na 23 shafi na 267/ 566. Mustadrakul Hakim 4 shafi na 557. lbnul Hajar a sawa'ikul Muhrika shafi na 163 babi na 11 fasali na farko, Muttaki al Hindi a kanzul umma na 14 shafi na 264/ 3866 2, sheikh Mahammad bn All as - sabban a cikin lsaful-Ragibin shafi na 145 da shaikh Hasan at Adwiy at Hamzawi Bamalike a cikin Mashaikul Anwar shafi na 112 to wadannan mutum hudu dukkansu sun fito da hadisin daga sahih Muslim kuma sun yi ititfaki cewa yana nan a sahih Muslim, amma a yau da zaka duba sahih da aka hugo, to ba zaka samu a ciki ba:
89- Kanji a cikin AL Bayan shafi na 486 babi na 3 yayi hukunci da ingancin hadisin. Suyuti a Jarni'us-sagir na 2 shafi na 672/ 024, ya tabbatar da ingancinsa Hakana a karin bayanin Tajul iami'I Ill Usul na 5 shafi na 343. Bagawiya cikin Masabihus sunna na 3


( 73 )


Na'im bn Hammad ya ruwaito shi da tafarkinsa daga All (A.S.) cewa yace: "Mahdi mutum ne daga garemu daga 'ya'yan fatima".90
Kamar yadda ya fitar d4a zuhri cewa yace: "Mahdi daga 'ya'yan fatima yake."9'
Kaab ya ruwaito irinsa.92
Wannan ke nan, kuma wani hadisin wanda ya game yawancin hadisai da suka gabata ya zo wanda shine aka ruwaito daga katada, kamar yadda ya gabata. "yace: na ce wa Sa'id: shin Mahdi gaskiya ne? yace: E gaskiya ne na ce daga wa yake? Ya ce daga kuraish na ce daga wace kuraish? yace: daga Bani Hashim na Ce: daga wa ce Banu Hashim? yace: daga 'ya 'yan Abdul Muttalib. Na ce : daga wasu 'ya'yan Abdul Muttalib? Yace: daga 'ya 'yan fatima".93

____________
shafi na 492 hadisi na 4211 ya kirga hadisin daga cikin kyawawan hadisai. Abu fais a cikin Ibrazul Wahmi shall na 500 bayan ya binciki tafarkin hadisin sal yakawo go cewa hadisi ne ingatacce kuma cewa dukan wando suka ruwaito shi adilai ne tabbatattu. Albani ya yarda da kyan tafarkin hadisin kamar yadda ya zo a Akidatu Ahlis sunna da Athar fi Mahdil Muntazar na sheikh Muhsin bin Hamdil lbad shafi na 18. Kamar yadda kuma muka gabatar cewa kurtubi da wasu sun ce mutawatir ne rka duba can.
90- AL fitan na Na'irn bin Hammad na I shafi na 375/ 1117. Kuma daga gareshi a kanzul Ummal na 14 shall na 591/ 39675.
91- AL fitan na Na'im bn Harnmad na I shafi na 375/ 1114. Kuma daga gareshi a cikin Tashrif bil Minan shall na 176/ 237 babi na 189.
92- Fitan na Na'im na I shafi na 374/ 1112. Kuma daga gareshi a Tashrifbil Minan shafi na 157 /202 babi na 163.
93- Ikdud Durar shall na 44 babi na 1 fitan na Na'im na daya shafi na 368-369 Daga gareshi sayyid bn Tawus a Tashrifu Minan shafi na 157/ 201 babi na 163.


( 74 )


To koda yake mun kusa mu sami amsar tambayar nan da take cewa: shin wanene Mahdi da aka yi alkawari, ake kuma sauraro? Saidai har yanzu akwai abu guda dangane da ayyana nasabarsa daga 'ya'yan Fatima (A.S.) yanda ha za a samu wani kokwanto ba, domin kuwa a saran yake cewa wannan nasabar idan aka bar ta a haka to za ta kare ne zuwa ga Hasan (A.S.) da Husain (A.S.).
Saboda haka zamu fuskanci ra 'ayoyi uku sune:
(1) Mahdi ya zama daga 'ya'yan Imam Hasan (A.S.) yake.
(2) Mahdi ya zama daga 'ya'yan imam Husain (A.S.) yake.
(3) Ya zama yana daga cikin 'ya'yan Hasan da Husain dukkaninsu.
Ra'ayi na uku dai baya bukatar wani dogon nazari kafin a yarda da shi ko a ki yardo da shi domin a abinda ya gabata mun ga hadisai da suke karfafa ra ayin farko da na biyu.
To kuma ace akwai wani ra'ayi na hudu wanda ke nuna cewa Mahdi ha daga 'ya'yan Hasan da Husaini ha ne, wannan ko kusa ha daidai ha ne, kuma hankali ha zai karbe shi ha domin kuwa ga hadisan da ingancinsu ya tabhata da kuma kasancewarsu mutawatirai da suka nuna cewa Mahdi daga AhluI Baiti (A.S.) yake kuma daga 'ya'yan Fatima (A.S.).
To don haka ha abinda ya saura sai yin hincike kan ababen da suke tabbatar da ra 'ayin farko da na biyu. Saidai wajibi ne mu fadakar kafin nan cewa idan ya tabbata cewa ra ayin farko karya ne to kenan hamu bukata ko kadan mu nemi yin bincike akan abinda ke tabbatar da ra'ayi na biyu domin kuwa zai tabbata kai tsaye cewa shine na gaskiya wanda aka sakainkance da


( 75 )

shi kuma ya dace da hadisai. Musamman idan muka yi la'akari da abinda muka gabatar na cewa babu yanda za ayi duka ra ayoyi, biyun su hadu su zama karya Yanzu zamu zage damtse mu yi bincike kan abin da ke tabbatar da ra'ayin farko, kamar haka:


( 76 )

HADISIN MAHDI DAGA 'YA'YAN
IMAM HASAN (A.S.) (JIKAN MANZO)
YAKE:

Ban samu inda aka nuna cewa Mahdi wanda aka yi alkawari kuma ake sauraro daga 'ya'yan imam Hasan (A.S.) yake, 1)a a cikin littattafan Ahlus sunna face hadisi guda daya kacal kuma watakil duk littattafan musulmai idan ha wannan hadisin ha to babu waninsa, hadisin kuwa shine wanda Abu Dawud sajistani ya fitar a cikin sunan dinsa, to ga yanda yake:
Yace: an bani labari daga llarun binil Mugira, yace: Umar bin Abi kais ya bamu labari daga shu'aib bin khalid daga Abu ishak, yace: Au (A.S.) yace -sai ya kalli dansa Hasan - sa'annan yace: "Hakika da na wannan shugaba ne kamar yadda Annabi (S.A.W.A.) ya ambace shi, kuma wani mutum zai fito daga tsatsonsa wanda ake kira da sunan annabinku. yana kama da shi a dabi'a amma ha ya kama da shi a halitta". Sannan sai ya ambaci labarin cewa zai cika kasa da adalci'X94

____________
94- Sunan Abu Dawud na 4 shafi na 108 /4290. Kuma ya fitar daga gareshi a iami'uI usul na 11 shafi na 49-50/78 14 da kan~uI ummal na 13 shall na 647/ 37636. Na'im bn Hammad shima ya fitar a kitabul fitan na 1 shall na 3 74-375/ 11/3.


( 77 )

BACIN HADISIN DAGA JIHOHI
BAKWAI

Daga bincike da zaa yi a tafarkin hadisin da rna'anarsa sa'annan da auna shi da za'a yi tare da hadisan dake cewa Mahdi daga 'ya'yan imam Husain (A.S.) yake, to da wannan mai bincike zai gane lamarin wannan hadisin. hakan kuwa z~i mu vi ~hi t~c ta tiiskoki bakwai.
Na daya:
Sabanin abinda aka ruwaito daga Abu Dawud a wannan hadisin domin kuwa Jazri Bashafi'e (rasuwarsa 833 Hijiriyya) ya kawo wannan hadisin da hanyarsa daga Abu Dawud da kansa amma a ciki akwai sunan (Husain) maimakon (Hasan) sai yace: mafi inganci shine cewa daga zuriyar Husain bn Au yake saboda fadin haka a saran da Amirul Mumineen Au (A.S) yayi a cikin ruwayar da sheikh Umar bn Hasan al Rikkiy ya ruwaito, yace: Abul Hasan bn Bukhari ya bamu labani,umar bn Muhammad Darkazi, ya bamu labari, Abu Badr al karkhi ya bamu labari, Abu Bakr al khatib ya bamu labari, Abu umar al Hashimi ya bamu labari, Abu Au a! li'ulu'iy ya bamu labari, Abu Dawud al Hafiz ya bamu labari yace: An bani labani daga I-larun bn Mugira, yace: umar bn Abu kais ya bainu labari daga shi'aib bn khalid daga Abu lshag, yace, All (A.S.) yace: sal ya kalli dansa Husain sannan yace: "Hakika da na wannan shugaba ne kamar yadda Annabi ya ambace shi, kuma wani mutum zai fito daga tsatsonsa

( 78 )

wanda ake kira da sunan Annabinku, yana kama da shi a dabi'u amma ba ya kama da shi a halitta".
Sannan ya ambaci labarin cewa zai cika kasa da adalci. Haka Abu Dawud ya ruwaito shi a cikin sunan nasa sai yayi shuru akai"95 Daidai lafazinsa ya kare.
Hakanan Makadisi Bashafi'e ya fitar da shi a cikin lkdu Durar shafi na 45 daga babi na farko a ciki akwai sunan (Hasan) sai mai bincike yayi nuni a wurin karin bayani cewa akwai wani bugun da ya zo da sunan (Husain). Kuma wani abinda ke karfafa cewa akwai wannan bugun shine cirowar da sadrud Deen sadr yayi daga gareta yayin da ya kawo hadisin daga Ikdu Durar, kuma a ciki akwai sunan (Husain).96
To wannan sabani ya kore nuna fifikon wani daga cikin sunayen akan dan uwansa, idan ha ya sami wani dalili dà ya karfafa shi ha koma bayan wannan hadisin, kuma inn wannan dalilin babu shi akan (Hasan), amma akwai shi cewa (Husain) shine ke da fifiko a tsakanin sunayen biyu.
Na biyu:
Hanyar hadisin a yanke yake don kuwa wanda ya ruwaito shi daga Au (A.S.) shine Abu ishag abin nufi da shi shine As-sabiy'iy, shi kuwa bai taba ruwaito ko da hadisi daya daga Au (A.S) kai tsaye ha ~vato bai tabajin koda ruwaya daya kacal da kunnensa ha daga Au (A.S.), kainar yadda,97
Munziri ya bayyana a sharhin wannan hadisi, kuma lokacin da Au (A.S.) ya yi shahada shekarunsa bakwai ne

____________
95- Asma Manakib fi Tahzibi Asna MataI~b na Jasri Dimashkiy shafi'i shafi na 165-168/61.
96- AL Mahdi na sayyid sadrud Deen sadr shafi na 68.
97- Mukhtasar sunan Abi Dawud na Munziriy Iittafi na 6 shafi na 162 /4121.


( 79 )

kawai domin an haife shi kafin karewar halifancin Uthman da shekara biyu, kamar yadda lbn Hajar ya fada.9S
Na uku:
Tafarkin ruwayar majhuli ne, domin Abu Dawud cewa yayi: "an bashi labari daga Harun bn Mugira" amma ba a san wanene ya bashi labari ba, kuma bisa ittifaki dania ba'a lura da hadisi majhuli.
Na Hudu:
Hakika wannan hadisin da aka ambata, Abu salih al salili wato daga malaman Ahlus sunna ya fitar da hadisin da tafarkinsa daga imam Musa bn Ja' afar daga mahaifinsa Ja' afar bn Muhammad As-sadik daga kakansa Au bn Husain, daga kakansa Au bn Abi Talib (A.S.) a ciki akwai sunan Husain (A.S.) ba Hasan (A.S.) ba99.
Na Biyar:
Wannan hadisin ya ci karo da hadisai da dama wanda suka zo daga hanyoyin Ahlus sunna dangane da cewa Mahdi daga 'ya'yan Imam Husain yake Daga ciki akwai hadisin Huzaifa bn yaman yace: Manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi mana huduba sai ya ambata mana abubuwan da za su faru, sa'annan yace: da duniya ba ta saura ba face kwana guda, to da Allah ya tsawaita shi wannan kwana guda har sai ya tada wani mutum daga 'ya'yana, sunansa daidai da sunana sai Salman al- Farisi (R.A) ya tashi tsaye yace: ya Ma'aikin Allah daga wane

____________
98- Tahzibui Tahzib na 8 shafi na 56/ 100.
99- Tashrif bit minan na sayyid bn Tawus shafi na 285/ 413 babi na 76 ya fito da shi daga fitan na saliliy amma da sabani dan kadan.


( 80 )

'ya'yanka? Yace: daga da na wannan sai ya buga hannunsa akan Husain."100
Na shida
Akwai jin cewa kuskure aka yi wajen rubutu wato maimakon a rubuta (Husain) sal aka rubuta (Hasan) a ruwayar Abu Dawud dalili kuwa shine wannan sabani da aka samu a hadisan biyu. To koda ba a tabbatar da wannan kuskure ba, to wannan hadisi khabar Wahid.(101) ne wanda shi dama ba ya iya tsayawa gaban khabar mutawatir kamar yadda za mu yi bayaninsa dalla - dalla nan gaba.

____________
100- Al Manarul Munif na Ibnul kayyim sliafi na 148/ 329. Fasali na 50 daga Tabrani a Ausat lkdud Durar shafi na 45 daga babi na farko a ciki ya zo "Hafiz ya ciro shi wato Abu Na'im a cikin siffar Mahdi 11. Zakha'irul ukba na Tabari shafi na 136 ya zo a ciki "to sai a fassara dukkan abinda ya gabata da wannan ma'ana" fara'idus simtain na 2 shafi na 325/ 575 babi na 61. Al kaulul Makhtasar na lbn Hajar na 7 shafi na 37 babi na 1. Fara'idu fawa'idul fikr na z babi na 1. Seeral Halabiyya na I shafi na 193. Yanabiul Mawadda na 3 shafi na 63 babi na 93. Kuma akwai wasu hadisan daugane da wannan a Maktal Imam Husain na kharizmi Bahanafe na 1 shafi na 196 da faro'idus simtain na 2 shafi na 310-315 hadisi no 561-569. Da yanabi'ul Mowadda na 3 shafi no 170/ 212 babi na 93 da 94. Daga Iittattafan shi'ah kuwa ka duba: kashful Gumma na 3 shafi na 259 da kashful yakin shafi na 117 da Ithbatul Hudat na 3 shafi na 617/ 174 babi na 32. Da Hulyatul Abrar na 2 shafi na 701/54 babi na 41. Gayatul Maram shall na694/ 17 babi na 141. A cikin Muntaknabul Athar akwai da yawa daga wadannan hadisai wadanda aka ruwaito daga tafarkin shi'a da sunna, to ka duba can.
101- Shine hadisin da mutum guda ko kuma wasu mutane suka ruwaito amma ba a samu yakini akansu ba.


( 81 )


Na Bakwai:
Akwai alamun cewa wannan hadisin kaga shi aka yi kuma abinda ke karfafa wannan shine cewa Hasaniyyin wata zuriyar Imam Hasan dasu da magoya bayansu da mataimakansu sun raya cewa Muhammad bn Abdullah bn Hasan al-Muthanna bn Imam Hasan (a.s) jikan Manzon Allah (s.a.w.a), sun raya cewa shi Muhammad Mahdi ne shi kuwa Muhammad an kashe shi ne a shekara ta (145 Hijiriyya) a lokacin shugabancin Mansur na Abbasawa, kamar yadda su ma Banu Abbas suka raya cewa Muhammad bn Abdullah AL Mansur, khalifan Abbasi da aka yi wa lakabi da (Mahdi) (shekara 158-169) shi ma cewa suka yi shi Mahdi ne, ba don komai ha sal domin su cimma wasu bukatu na siyasa wanda ha zasu same su ta sauki ba face ta wannan hanya da suka kaga.


( 82 )

HADISIN BAI YI KARO DA HADISAN
"MAHDI DAGA 'YA'YAN HUSAIN
(A.S.) BA

Idan muka dauka cewa wannan hadisi ingantacce ne duk kuwa da alamomi bakwai da muka ambata, to koda mun karbi ingancinsa, saidai za mu iya cewa babu sabani a tsakaninsa da sauran hadisai da suka fito karara suka nuna cewa Mahdi daga 'ya'yan Husain yake. Saboda za a iya hada su wato shi wannan hadisin da wadancan hadisan, kamar haka, sai ya zama ana nufin cewa imam Mahdi ta wajen mahaifi daga zuriyar imam Husaini yake, a ta wajen mahaifiya kuma daga zuriyar irnam Hasan yake. Dalili kuwa shine cewa matar imarn Au bn Husain bn Au bn Abi Talib (A.S.), mahaifiyar imam Bakir Muhammad bn Au bn Husain (A.S.), ita ce fatima 'yar imam Hasan Al Mijtaba (A.S.) dan imam Au bn Abi Talib.
To bisa wannan imam Bakir (A.S.) sai ya zama daga zuriyan Husaini (A.S.) yake ta wajen mahaifi, a ta wajen mahaifiya kitwa daga zuriyar Hasan (A.S.) yake, kenan zuriyar a hakika ta zama dagajikokin Manzon Allah su biyun duka.
Wannan hada hadisan nan da muka yi yana da tushe daga Alkur'ani rnai Girma, Allah Madaukaki yana cewa:
"Sai Muka bashi lshak, da yakubu dukkansu mun shiryar kuma Nuhu mun shiryar kafin nan kuma daga zuriyarsa akwai Dawuda da sulaimanu. .da Isa da llyasu dukansu daga salihai suke" suratul An'am aya ta 84-85.


( 83 )


To Annabi isa (A.S.) ya shiga cikin zuriyar Annabawa ta wajen mahaifiyarsa Maryam (A.S.) ne, to don haka ba laifi zuriyar imam Bakir ta shigo cikin na imam Hasan ta hanyar mahaifiya.
Wannan hada hadisai dai bai kamata wani shakku ya shigo ciki ba idan da dai hadisin Abu Dawud ingantacce ne, koda yake dai wannan hadisin Abi Dawud bai inganta ba daga ta fuskoki dabam - daban kamar yadda ya gabata.
To zuwa nan ya bayyana a garemu a saran cewa ra'ayi na biyu wato wanda ke nuna cewa imam Mahdi daga 'ya'yan imam Husaini (A.S.) yake, shine ra'ayi na gaskiya wanda ya zama daidai koda kuwa mun yarda da ingancin hadisin da yace Mahdi daga 'ya'yan Hasan (A.S.) yake ballantana idan ha a yarda da ingancinsa ha.
ldan mun yarda da ingancinsa to babu sabani a tsakaninsu bil hasali ma wannan hadisin yana karfafa sauran ne, idan kuwa bamu yarda da ingancinsa ha wanda hakan shine gaskiya idan muka yi Ia'akani da fuskoki bakwai da suka gabata. Wato kenan komai ya fito fiji ba a bukatan wani dogon bayani, domin kamar yadda muka fada ne a baya cewa idan aka tabbatar da rashin gaskiyar daya daga cikin ra ayoyi biyun to hakan zai tabbatar da gaskiyar daya ra ayin da ya saura, kai tsaye, saboda babu dama, wato ba zai taba yiwuwa ba ace dukansu biyu karya ne, domin kuwa muna da yakini cewa Mahdi wanda aka yi alkawarin zuwansa, shi daga 'ya 'yan fatima (A.S.) yake tabbas.


( 84 )

ABINDA YA ZO A HALIN YA CI KARO
DA CEWA MAHDI DAGA 'YA'YAN
HUSAIN (A.S.) YAKE

Hakika ya bayyana daga binciken da muka yi na hadisai' daban - dabam dangane da nasabar imam Mahdi, cewa babu makawa shi daga 'ya'yan imam Husan (A.S.) yake, to sai dai kafin mu bayyana ababen da ke tabbatar da wannan lamari wanda akidar shi'ah Imamiyya ta ke kai na cewa imam Mahdi shine na tara daga tsatson imam Husain (A.S.), kuma cewa an haife shi tabbas wanda shine Muhammad bin Hasan A1-Askari (A.S.) to kafin wannan, lallai ne mu dan dakata kadan mu duba abinda ya zo sabanin haka a cikin wasu ruwayoyi daga hanyar Ahlus -sunna wanda suka nuna cewa sunar mahaifin imam Mahdi shine "Abdullah" wanda wannan ya sa wasu sun yi i'itikadi da cewa Mahdi shine Muhammad bin Abdullah kuma wai ba'a haife shi ba tukuna saidai wai za'a haife shi ne a karshen zamani yayin da yayi kusan bayyana.
To tim da yake an sami hadisai masu tawaturi akan zuwan Mahdi guda ba biyu ba, ashe kenan daya daga cikin wadannan jama'a biyu, ya na sauraron zuwan Mahdi ne wanda babu shi (wato ba'a yi shi ba, ba kuma za'a yi shi ba)! To don haka wannan abu ne wanda zai sa kowace jama'a ta sake duba dalilanta da jin cewa watakila kuskurene, na wajen watajama'ar shine gaskiya, ko kuma a'a nata shine gaskiya na wajen watajama'ar shine kure. To koda yake wannan abu ne mai wuya saidai kuma sauki


( 85 )

gare shi a wajen manemin gaskiya koda kuwa yaya yake, tun kafin kurewan lokaci.
Domin sanin daidai daga sunan mahaifin imam Mahdi, cewa shin Hasan ne ko kuma Abdulla"1 ne sai mu Ce:


( 86 )

HADISAN "SUNAN MAHAIFINSA
DAIDAI DA SUNAN MAHAIFI NA"
(ABDULLAH) YAKE.

Yana da kyau mu yi ishara anan zuwa ga cewa wasu malaman shi'ah sun kawo wasu daga cikin wadannan hadisai duk da cewa sun saba wa mazhabar su ha don komai ha sai don rikon amanarsu da kuma kiyaye shi kamar yadda su ka same shi a littafan Ahlus-sunna ha tare da sun shafe shi ko kuma sun yi masa wani gyaran fuska ha kuma sabila da suna ganin yiwuwan tawilinsa ta yadda ba zai saba wa mazhabar Ahlul Baiti, ha sannan daga bisani kuma su bayyana abinda ya dace game da fassarar hadisan.
To wadannan hadisai su ne:
1- Hadisin da lbn Abi shaiba ya fitar da shi da Tabrani da Hakim, dukkansu daga hanyar Asim bin Abin Nujud daga zar bin Hubaish daga Abdullah bin Masu'ud daga Annabi (S.A.W.A.) cewa yace: "Duniya ba za ta gushe ha liar sai Allah ya aiko wani mutum, sunansa yana daidai da sunana, kuma sunan mahaifinsa daidai da sunan mahaifina."(102)

____________
102- AL-Musannaf na lbn Abi shaiba 15: 198/ 19493. AL-Mujamul kabir na Tabrani 10: 163/ 10213 da 10: 166/10222. Mustadrakul Hakim na 4 shafi na 442. Majlisi Malamin shi'ah yà kawo a Biharul Anwar na 51 /21, DAGA kashful aumma na Arbili na 3 shafi na 261 shi kuma daga kitabul Ar ba'in na Abu Na'im.


( 87 )


2- Hadisin da Abu Amr Ad-dani ya fito da shi da shi da khatibul Bagdadi dukkansu daga hanyar Asim bin Abin Nujud daga zar bin Hubaish daga Abdullah bin Mas'ud' daga Annabi (S.A.W.A.) cewa yace: "Ba za a yi tashin kiyama ba har sai wani mutum daga Ahlu Baitina ya mallaki mutane, sunansa daidai da sunana, sunan mahaifinsa kuma daidai da sunan mahaifina"(103)
3- Hadisin da Na'im bin Hammad da khatib da lbnu Hajar dukkansu su ka fitar ta hanyar Asim har yanzu daga zar daga lbnu Mas'ud daga Annabi (S.A.W.A.) cewa yace: "Mahdi sunansa yana daidai da sunana, kuman 'suna mahaifinsa yana daidai da sunan mahaifina"(104)
4- Hadisin da Na'im bin Hammad ya fito da shi da tafarkinsa daga Abu Tufail yace: "Manzon Allah (S.A.W.A.) yace: "Mahdi sunansa daidai da sunana yake kuma sunan mahaifinsa yana daidai da sunan mahaifina"(105)

____________
103- Sunan Abi Amr Ad-Dani shafi na 94-95. Tarikhu Bagdad na I shafi na 370 amma babu wani da ya ruwaito shi daga shi'ah.
104- Tarikh Bagdad na 5 shafi na 391. Kitabul fitan naNa'im bin Hammad na 1: 367/ 1076 da 1077 a ciki Ibnu Hammad yake cewa "kuma na ji shi ha sau daya ba,ba ya ambaton sunan mahaifinsa" kanzul ummal na 14268 / 386 78 daga Ibn Asakir. Tashirfbil Minan na 156 / 196 da 197 babi na 163 daga fitan na Ibn Hammad. Haka na Ibn Hajar ya kawo shi a kaulu Mukhtasar 40/4 babu sadarwa.
105- AL-fitan na Na'im bin Hammad na I shafi na 368 hadisi na 1080. Daga gareshi sayyid bin Tawus a cikin AL Tasbrif bit Minan ya ruwaito a shafi na 257 hadisi na 200.


( 88 )

HAKIKANIN WANNAN SABANI DA
KUMA DARAJARSA A ILMANCE:

Wadannan sune hadisan da aka sanya su tsani domin a zabi Muhammad bin Abdullah a matsayin Mahdi na karshen zamani, kuma duk wadannan ruwayoyi basu isa hujja kan wannan zabi ba, ka dai ga cewa ruwayoyi uku na farko dukkansu sun kare ne zuwa wajen lbn Mas'ud daga ta hanya daya wato hanyar Asim bin Abin Nu jud.
To da sannu za mu kawo maku abinda ke cikin wanna~ tafarki dalla-dalla.
Amma ruwaya ta hudu, to hanyarsa raunanna cc kuma an yi ittifaki akan haka saboda zuwan Rishdinu bin sa'ad al-Mihriy wanda shine Rishdinu bin Abi Rishdinu wadda dukkan malaman Ahlus-sunna su ka yi ittifaki akan rauninsa a tsakanin maruwaita.
Ahmad bin Hanbal yana cewa: Ba a damuwa da ruwayar da ya ruwaito koma daga wanene. Sannan Harb bin lsmail yace: "Na tambayi Ahmad bin Hanbal dangane da shi wato Rishdinu, sai ya raunana shi. Yahya bin Mu'in kuwa ance ba ya rubuta hadisinsa. Daga Abi zar'a kuma yace: shi mai raunin hadisi ne. Abu Hatim kuwa yace: shi mai musun hadisai ne. Jauzjani kuma yace: Akwai ruwayoyi wanda suke raunana kuma wanda ba karbabbu ba a wurinsa. Nisa'i kuma yace: ~hi Rishdinu wanda ake barin hadisinsa ne ba'a rubuta hadisin sa.
A takaice ni ban samu wanda ya inganta ruwayarsa ba ko guda daya face Haisam bin Naja ya inganta shi a wata


( 89 )

majalisa inda Ahmad bin Hanbal ke zaune sai kuwa yayi murmushi yana dariya, wannan kuwa abu ne da zai nuna maka daidaituwansu akan rauiiinsa )06
Kuma babu shakka cewa wanda dai hal insa ya zama abinda ka sani yanzu to babu yadda za ayi a karbi inn wannan gagarumin lamari daga gareshi.
Amma hadisai uku na farko kuwa, to ba hujja ha ne daga ta kowane fuska, kuma daga cikin abinda ke tabbatar da rauninsu da rashin karbuwansu shine cewa lafazin "sunan mahaifinsa daidai da sunan niahaifina" babu wanda ya ruwaito shi a cikin manyari rnahaddata da maruwaita bil hasali ma abinda ya tabbata a garesu shine "kuma sunansa yana daidai da sunana" kadai, ha tare da an kara waccan iafazin ha, kamar yadda za mu kafa dalili akai. Wannan kenan tare da kuma faden wasu Malaman Ahlus-sunna a saran bayan sun hi diddigin hanyoyin Asim bin Abin Najud sun fada cewa wannan kanin babu shi, kamar yadda za ku ga bayaninsa dalla-dalla nan gaba.
Saboda haka tafarkin wadannan hadisai uku duka sun kare ne zuwa wajen lbnu Mas'ud shi kadai, yayin da kuma abinda aka ruwaito daga shi lbnu Mas'ud da kansa a cikin Musnad Ahmad da kuma sauran wurare shine, cewa "sunansa daidai da sunana"107 Kadai. Hakana yake a wajen Tirmizi shima, domin ya ruwaito wannan hadisin ba tare da wannan karin lafazin ha sa'annan ya kara da cewa abinda aka ruwaito daga Au (A.S.) da Abi sa'idil khudriy da Umm salama da Abu Huraira to shima an ruwaito shine da cewa:

____________
106- Ka duba Tahzibul kamal na 9:/191/1911 da Tahzibut Tahzib na 3 shafi na 240. Domin a cikinsu akwai dukkan abinda aka ambata a game da Rishdinu bin Abi Rishdin.
107- Musnad Ahmad na 1:376 da 377 da kuma 430 da 448.


( 90 )


"Sunansa daidai da sunana", sai kuma yace bayan ya ruwaito hadisin daga lbn Mas'ud da wannan lafazi sai yace: "A cikin babin daga Au da AN sa'id da umm salama da Abu Huraira, kuma wannan hadisi ne mai Kyau ingantacce."'08
Kuma haka yake a wajen yawancin mahaddata. A misali Tabarani ya fitar da hadisin daga lbnu Mas'ud da kansa daga hanyoyi daban masu yawa, kuma da lafazin "sunansa daidai da sunana", kamar yadda kuma ya zo cikin r~iwayoyin Mu'jam nasa masu lamba 10214, 10215, 10217, 10218, 10219, 10220, 10221, 10223, 10225, 10226, 10227, 10229da 10230.
Har ila yau Hakim ya fitar da wannan hadisin a cikin Mustadrark nasa daga lbn Mas'ud da lafazin: "Sunansa yayi daidai da sunaria" kadai, sannan yace "Wannan hadisi ne ingantacce a bisa sharadin shaihunnai biyu amma ha su fito da shi ba."'09
Zahabi shi ma ya hi shigen abinda Hakim yayi hakana Najdul Bagawi a cikin Masabihus-Sunna shima ya ruwaito wannan hadisin daga lbn Mas'ud ha tare da waccan kari ha sannan yace hadisi ne mai kyau."O
Makdisi ha shafi'e ya fada fihla-fihla cewa waccan karin, imaman hadisai ba su ruwaito shi ha, sai yace: bayan ya kawo hadisin daga lbn Mas'ud ha tare da karin ha yace: "Wata jama'a daga imaman Hadisai sun fitar da shi a littafan su, daga cikinsu akwai imam Abu isa AL-Tirmizi a cikin Jami'insa da imain Abu Dawud a sunan nasa da Hafiz Abu Bakr AL-Baihaki da sheikh Abu Amr

____________
108- Sunanut Tirmizi na 4: 505 /2230.
109- Mustadrakul Hakim na 4 shafi na 442.
110- Masabihus-Sunna 492 / 4210.


( 91 )

Ad-dani dukkansu haka su ka ruwaito shi""' Wato ma'ana babu Iafazin "sunan mahaifinsa daidai da sunan mahaifina". Sannan sal ya fitar da wasu hadisai wanda suke karfafa hakan kuma ya ainbaci wadanda suka ruwaito shi daga imamai mahaddata kamarsu Tabarani da Ahmad bin Hanbal da Tirmizi da Abi Dawud da Hafiz Abi Dawud da Baihaki, daga Abdullah bin Mas'ud da Abdullah bin Umar da Huzaifa.112
Dada da abinda ya gabata daga isharar da Tirmizi yayi na cewa an fitar daga Au (A.S.) da Abu sa'idil khudriy da umm Salama da Abu Huraira dukkansu da lafazin "Sunansa daidai da sunana" kadai. To kuma dai hankali ba zai yarda ba ace dukkan wadannan imamai mahaddata sun hada baki ne domin su shafe wannan, karin (sunan mahaifinsa daidai da sunan mahaifina) idan dai a hakika an ruwaito shi daga tafarkin Asim bin Abin Nujud, bama haka ba, ai baya taba yiwuwa ace su hada baki akan su shafe shi don ganin muhimmanci da yake da shi na koli domin ganin za a iya kore abinda wata mazhabar ke kira gareshi ta hanyarsa.
Daga nan ne za mu gani a fili cewa waccan karin an yi shi ne akan hadisin lbnu Mas'ud ta tafarkin Asim ko ta hanun mabiyan Hasani yyun da magoya bayansu domin su yada akidar Mahdi da suka jingina wa Mohammad bin Abdullah bin Hasan AL-Musanna, ko kuma ta hanun mabiyan Abbasawa (Abbasiyyun) da mataimakansu domin raya akidar Mahdi da suke yi akan Mohammad bin Abdullah wato Abu Ja'afar AL-Mansur na Bani Abbas.

____________
111- Ikdud Durar 51/ Babi na 2.
112- Ikdud Durar 5l-56/Babina 2.


( 92 )


Wani abu kuma da zai karfafa wannan magana wato na cewa kari aka yi wato kagawa aka yi, shine idan muka san cewa na farko daga cikin wadannan mutum biyu yana da dauri a harcensa wanda hakan ya sa magoya bayansa sun kago karya suka lika wa Abu Huraira sai suka ruwaito daga gareshi cewa yace:
"Mahdi sunansa shine Muhammad bin Abdullah a harcensa akwai dauri""3
To da yake hadisai uku na farko daga ruwayar Asim bin Abin Nujud daga zar bin Hubaish daga Abdullah bin Mas'ud, sun saba ma abinda mahaddata suka ruwaito daga Asim a dangane da imam Mahdi kamar yadda ya gabata, to don haka AL Hafiz Abu Na'im AL lsbahani ya bi tafarkunan wannan hadisin daga Asim a cikin littafinsa (Manakibul Mahdi) har sai da ya kaima tafarki talatin da daya amma babu daya daga ciki da aka riwaito cewa "sunan mahaifinsa daidai da sunan mahaifina", bil hasali ma dukkansu sun daidaita akan ruwayar "sunansa yana daidai da sunana" kadai shi kuwa AL-Hafiz Abu Na'im ya rasu ne a shekarar 430 Hijiriyya AL-Kanji ba shafi'e (wanda ya rasu a shekara ta 638 Hijiriyya) ya ciro cikakken maganar AL Hafiz Abu Na'im sannan sai ya bi bayan maganarsa da cewa "Kuma wani ya ruwaito shi koma bayan Asim, wanda ya ruwaito din shine Amr bin Huna daga Zar, kuma dukkan wadannan sun ruwaito "sunansa daidai da sunana" face abinda aka ruwaito daga Ubaidullah bin Musa daga Za'ida daga Asim domin yace a ciki "sunan mahaifin sa daidai da sunan mahaifina". Kvma mutum mai hankali ba zai yi kokwanto ba kan cewa wannan karin babu kima gareshi saboda haduwan

____________
113- Wannan hadisi kagagge an ciro shine a Mu'jamu Ahadisil imam Mahdi daga Makatilul Talibiyyin shafi na 163-164.


( 93 )

wadannan irnamai abisa sabaninsa har zuwa inda yace magana mai rarrabewa anan shine cewa: imam Ahmad tare da lura da kiyayewarsa ya ruwaito wannan hadisin a Musnadinsa a gurare da dama da lafazin "sunansa yana daidai da sunana."(114)
To daga nan zamu san cewa hadisin "sunan mahaifinsa daidai da sunan mahaifina" akwai rauni a cikinsa sosai ta yanda ba za a taba dogaro akai ba wajen sanin mahaifin Mahdi na kusa.
Saboda haka hakika duk wanda yake jiran Mahdi da sunan (Muhammad bin Abdullah) to lallai shi a bisa hadisan da ake da su a Iittattafan musulmi, yana jiran kawalwalniya ce wanda masujin kishi ke zaton ruwa ne!
Don haka ne zamu tarar cewa ustaz AL-Azhari sa'ad Muhammad Hasan ya fada karara cewa hadisan "sunan mahaifinsa daidai da sunan mahaifina" hadisai ne wanda aka kago su, saidai wani abin al'ajabi a maganarsa shine ya danganta kagen ne ga shi'ah imamiyya, wai domin su karfafa ra'ayinsu da shi, kamar yadda yace!"5
To ya bayyana daga abinda ya gabata cewa sakamakon bincike cikin riwayoyi game da nasabar imam Mahdi ya kate ga cewa imam Mahdi daga 'ya'yan imam Husain (A.S.) yake domin raunin sauran hadisai da suka saba ma wannan sakamakon gami da cewa ba' a sami wani dalili wanda ke karfafa ingancinsu ba, bil hasali ma an sami dalilai cikakku wanda suka nuna cewa ba daidai suke ba.

____________
114- AL-Bayan fi Akhbari sahibiz Zaman na AL kanji Bashafi'e shafi na 482.
115- AL-Mahdiyya fit Islam-AL uataz aI-Azhari sa'ad Muhammad Hasan shafi na 69.


( 94 )


Idan muka koma ga sakamakon bincike a cikin hadisai da suka gabata zamu tarar cewa ruwayoyin da musulmi ke da su Mutawatirai su na karfafa wannan sakamakon.

ABABEN DA KE KARFAFA KASANCEWAR MAHDI DAGA 'YA'YAN IMAM HUSAIN (A.S.) YAKE Akwai ruwayoyi da yawa a wajen shi'ah imamiyya wanda suka ayyana imamai goma sha biyu da sunayensu daya bayan daya daga kan imam Au har zuwa kan imam Mahdi (A.S.), tare da wasu hadisai din wadanda a cikinsu kowane imami da ya gabata ke aniibaton sunan imami da zai zo bayansa. Sannan akwai kuma hadisai a wajen Ahlus-sunna wanda suka ambaci adadin imamai a saran kamar yadda ya zo a cikin Manakib da wasunsu, baicin wadannan akwai kuma wasu hadisai da aka yi ittifaki akan ingancinsu wanda suke nuna cewa Mahdi yana da rai matsawar an sami mutum biyu da suka saura a cikin mutane to dayansu imam Mahdi ne, to wannan ba zai zama daidai ba saidai idan mun fassara da cewa shine na tara daga 'ya'yan imam Husain (A.S.). To mu kuwa ba zamu taba ambaton inn wadancan hadisan ba, face wadanda aka kafa hujja da su a littattafan bangarorin biyu wato shi'ah da sunna. HADISIN SAIKALAIN (NAUYAYA BIYU) Babu shakka Ma'aiki (S.A.W.A.) ya koma ga Allah amma a yayin nan ba'a rubuta hadisai da dukkan bayanansu dalla-dalla ba a zamaninsa. Ma aiki ya tsarkaka ga barin kawo tawaya a sakonsa wanda aka kaddara ya saura har zuwa tashin kiyama, kuma ya tsarkaka ga barin kin maida hankali ga al'ummarsa alhali shine wanda aka sani da tsananin tausayawarsa ga alumarsa, to ta yaya za~ mai da su ga AL kur'ani mai Girma kadai alhali a cikin Al-kurani akwai ayoyi muhkamat (bayyanannu) akwai kurna Mutashabahat (masu fuskoki da suka yi kama) saxman a cikin ayoyin AL-kur'ani akwai Mujmal (takaitattu) akwai kuma Mufassal (dalla-dalla), akwai kuma wanda ya shafe wani (Nasikh) sannan akwai wanda aka shafe (Mansukh), ga kuma fuskoki da ra'yoyi da aka yi amfani da su domin a kafa hujja akan ababe da suka sha bamban kamar yadda muke gani kuma muke ji daga shuga bannin rnazhabobi da kungiyoyi na rnusulunci! Gami kuma da cewa Ma aiki (S.A.W.A.) ya san cewa an yi masa karya tun yana raye ballantana kuma bayan fakuwarsa, dalili kuwa shine abinda Manzo (S.A.W.A.) yace a cikin littafan ruwayoyi wanda lafazinsa ya zama mutawatir, yace: "Wanda yayi. mani karya da gangan to yayi tanadin makomarsa a wuta". To saboda haka ba abu ne da hankalin dan Adam zai yarda ba ace Annabi (S.A.W.A.) ya bar shari'arsa kara zube domin mutane su yi ta yin ijtihadansu ba tare da ya ayyana masu wata makoma ha wanda ta san abinda ke cikin kur'ani sani na hakika, kuma sunna ta zama sananne dalla-dalla a wurinta. Wannan shine abinda ya dace da kare sako da kiyaye shi domin ganin ci gabansa ya tabbata a aikace kuma a rike tafarkinsa a rayuwa. To daga nan ne muhimmanci hadisin sakalain (wato kur'ani da Ahlul Bait) ya fito flu da kuma amfanin komar da al'umma zuwa ga Ahlul Baiti domin su koyi addini na gaskiya daga garesu, don haka ne ma zaka ga Annabi (S.A.W.A) ya yi ta maimaita shi a gurare dabam-daban da lokuta dabam-daban daga ciki akwai na ranar AL-Gadeer na karshen kuwa shine a rashin laflyarsa ta karshe. Daga zaid bin Aslam daga Manzon Allah (S.A.W.A.) yace: "kainar an kira ni kuma na amsa, ni mai bar muku nauyaya biyu ne dayansu ya fl daya girma: littafln Allah da Etra -Ahlu Baitina, to ku duba yanda zaku rike su a bayana, domin ha zasu taba rabuwa ba har sal sun riske ni a tabki, Allah shine majibinci na, ni kuma shugaban kowane mumini ne, duk wanda na kasance shugaba a gareshi to Aliyu shugabansa ne, ya Allah ka so wanda ya so shi, kuma ka yi gaba da wanda yayi gaba da shi.""6 Kuma daga Abu sa'id AL khudri daga Annabi (S.A.W.A.) yace: "Ni mai ban a cikinku ne ababen da idan kuka rike su, ha zaku taba bata a bayana ha, dayansu ya fl daya girma: littafln Allah igiya cc mikakkiya daga sama zuwa kasa da kuma itra na Ahlu Baiti na, kuma ha zasu 116 - Mustadrakul Hakim na 3 shafi na 109. taba rabuwa ba har sai sun riske ni a tabki to ku duba yanda zaku rike su a bayana.""7 Wannan kenan banda kuma maimaitawa da Manzo (S.A.W.A.) yayi ta yi a kullum na cewa a yi koyi da itrarsa Ahlu Baitinsa da kuma bin shiriyarsu, da tsoratarwa da yake yi daga saba masu ta yanda yake sanya su kamar Jiragen tsira, ko kuma Aminci ga AL'umma, wani lokaci kuma tankar kofar zubar da zunubi. Hakika sahabbai a lokacin ha su bukatar tambaya da neman bayani daga ma' aiki dangane da cewa menene ake nufi da Ahlul Baiti, alhali sun ga lokacin da ya fita zuwa ga Mubahala (Tsinuwa) babu kowa tare da shi face Ashabul kisa (ma'abuta Borgo) yana mai cewa: "ya Allah wadannan sune Ahalina" kuma sahabbai sune suka fi kowa sanin abinda wannan magana ta kunsa kuma sun fi kowa fahimtar ma anarta duk da kasancewarta takaitacciya. Ldan kuwa ha haka ha to wata tara lbnu Abbas ya bada labarin cewa Ma'aiki har tsawon wadannan watanni yayi yana tsayuwa kofar fatimatuz-zahra kowace safiya yana karata ayar: Hakika Allah yana nufin ya tafiyar maku da kazanta ya ku Ahlul Baiti, kuma ya tsarkake ku tsarkakewa""8, to 117- Sunanu Trimizi na 5: 662 /-3786. Kuma hadisin sakalain an ruwaito shi daga sahabbai fiye da talatin sannan adadin maruwaitansa yanzu haka bayan tsawan karnoni ya kai daruruwa. Ka duba Iittafin Hadisus sakalain -Tawaturuhu-Fikhuhu na sayd AL aI Husaini AL-Milani shafi na 47-51 ya ambaci maruwaita a ciki. 118- AL Ahzab sura ta 33 aya ta 33. Kuma ka duba ruwayar data nuna cewa Manzo (S.A.W.A.) yana tsayuwa a kofar fatimatuz-zahra alhali yana karata wannan ayar-Tafsiru Tabari 22 /6. lalle kuwa wannan abu ya isa ya sanar da dukkan jama'a cewa menene ake nufi da Ahalul Baiti (A.S.). Saboda haka babu bukata sahabbai su tainbayi Annabi (S.A.W.A) dangane da wadanda zasu kare al'umma daga bata bayan Ma'aiki liar zuwa ranar tashin kiyama, idan dai al'umma suka rike su tare da AL-kur'ani. Bukatar AL'umma da bukatar sahabbai bai fi su san farkon Ahlul Baiti ba, domin ya zama shine makoma wanda zai fara aikinsa bayan Annabi (S.A.W.A.) domin yayi aikin kare al'umma daga bata, kuma shi wannan na farko idan aka san shi to shi zai ayyana wanda ke biye da shi a wajen yin wannan aiki, da haka liar a zo kan na karshen mai kare al'umma daga bata tare da AL-kur'ani liar kuma a riski Annabi (S.A.W.A.) a tabki. To idan mun san cewa Aliyu (A.S.) ruwayoyi da yawa wanda babu adadinsu sun ayyana shi wanda daga cikinsu akwai hadisiii sakalain, ashe kenan ba lallai bane Annabi da kansa ya dau nauyin ayyana wanda zai jibinci al'amuran al'umma da sunansa a kowane zamani da kuma cikin kowane mutane, wannan bai zama laIlai ba idan ba dai wasu ababe ne za su wajabta hakan ha. To don haka ma~ aunin sanin imamin kowane zamani, ko ya zamanto ayyana su da aka yi kai tsaye tun tashin farko, ko kuma Imami da ya gabata ya ayyana wanda zai biyo bayansa., wannan kuwa shine ma' auni wanda aka saba da shi wanda Annabawa da Wasiyyai su ka saba anifani da shi, kuma shine ma~ auni wanda mutane su ka san shi a siyasarsu tim zamani dadadde liar ya zuwa zamamnmu na yanzu. ldan muka koma ga lamarin Ahlul Baiti (A.S.) zamu tarar cewa ga hadisai nan cunkus ta hanyoyi biyun nan da muka ambata, kuma wanda yayi bincike mai zurfi a tarihin rayuwarsu zai sani, sani na sakankancewa akan sun yi ikrarin cewa su lmamai ne duk kuwa da cewa akwai shugaba na zamanin, kuma sun bayyana kansu kamar yadda miliyoyin mabiyansu su ka rike su cewa su lmamai ne kuma sun yi shugabanci ga masu yin hamayya da hukumomin da ke ci a zamainisu saidai kuma cikin lumana. Tare kuma da shiryarwa da kowane lmami yayi wa mutanensa zuwa ga wanda zai rike lamarin lmamanci bayansa, to a bisa haka rayuwarsu ta gudana, sai suka kasance wadanda ake sa masu ido sosai daga hukumomin lokacin, kuma su ka zamanto ana daure su a kurkuku abinda ya kai ga shahadar wasu daga cikinsu, wasu kuma aka sa masu guba, wani lokaci kuma ka same su a fagen yaki (jihadi) su na fafatawa da hukumomi. Kuma koda ace wani daga cikinsu bai ayyana wanda zai rike lamarin lmamanci a bayansa ga mabiyansa ha, to tun dà yake shi dama hadisi ya ayyana shi, to haka na nufin cewa ~vannan imam luff abada yana tare da AL-kur'ani a cikiii kowane lokaci don kuwa hadisin da yace "ha zasu taba rabuwa ha har sal sun riske iii a tabki" yana nuna cewa a kullum akwai lmami daga AhluI-Baiti a dukkan zamani kamar yadda yake akwa kurani a kowane zamani wannan kuwa a flu yake. To saboda hakane ma lbnu Hajar ya cc: "kuma a cikin hadisai da suka yi umurni ga riko ga Ahlul Baiti akwai nuni ga cewa AhluI Baiti ba za su taba yankewa ha har ranar kiyama domin ayi riko garesu kamar yadda AL-kur'ani mai girma shima ya zama haka, don haka ne su ka zamanto aminci ga mutanen da ke kasa kuma wannan hadisin na tabbatar da haka: "A cikin kowace jama'a a al ummata data zo bayan wata to a cikin kowace daya daga cikinta akwai adilai daga Ahlu Baitina"."9 119- As-sawa'ikuI Muhrika shafi na 149. HADISIN: "WANDA YA MUTU BA TARE DA YA SAN IMAMIN ZAMANINSA BA." An rubuta wannan hadisi da lafuzza dabam-daban wanda babu makawa za su koma ga ma'ana daya da kuma manufa guda, a cikin muhimman littafan hadisai na sunna da shi'a. To daga Ahlus-sunna ya wadatar mu ambaci ittifakin Bukhari da Muslim akan ruwaito shi."'20 Daga shi'ah kuwa akwai kulaini da saduk da Mahaifinsa da Himyari da saffar su ma sun yi ittifaki akan ruwaito shi.'2' Da yawa kunia sun fitar da wannan hadisin ta tafarkuna wanda mutum zai gaza kai karshensu.'22 120- Sahihul Buk han juzu'i na 5 shafi na 13 Babin fitan. Sahihul Muslim juzu'i na 6 shafi na 2 1-22 / 1849. 121- UsuIul kafi juzu'i na 1 shafi na 303 /5,juzu'i na I shafi na 308 hadisi na I da na 2 da na 3 da kurnajuzu'i na I shafi na 378 / 2, da Raudatul kafi na 8 shafi na 129 / 123. Kama!ud-deen na 2 shall na 412-413 hadisai na 10 ii, 12 da 15 babin 39 AL lmam~ wa Tabsira shafi via 219 hadisai via 69, 7Oda 71. Kurbul lsnad: 351 / 1260. Basa'irud Darajat: 259, 509 da 510. 122- Ka duba Musnad Ahmad via 2 shafi via 83 da na 3 shafi na 446 da na 4 shall na 96. Musnad Abi Dawud AT TIYALISI shall na 259. Mujamul kabir na Tabarani na 10 shall na 350 /10687. Mustadrakul Hakim na I shall na 77. Hulyatul Auliya na 3 shall na 224. AL-kuna wal Asma na 2 shall na 3 sunanul Baihaki via 8 shall via 156 da 157. Jami'ul usul na 4 shafi na 70. Sharhin sahih Mustadrak via zahabi via farko shall via 77 da 177. To don haka wannan hadisin babu ta inda za a yi kokonton tafarkinsa, koda yake sheikh Abu zuhra yayi wahami sal ya kirga shi daga cikin ruwayoyin AL-kafi a~23 Wannan hadisin kuwa kamar yadda ka gani wajen fitar da shi za a iya cewa mutawatir ne, kuma hadisi ne wanda ba ya karban tawili ba kuma za a iyajuya ma'anarsa ba wanda ya fito flu karara dangane da wajibcin sanin Imami na gaskiya akan kowane musulmi da musulma, idan kuwa ba haka ba to makomarsa ko ita abu ne mai ban tsoro kwarai. Wanda kuwa yace abin nufl da Imami wanda idan ba a san shi ba za ayi mutuwar jahiliyya shine shugaba ko haikimi ko Mai mulki da sauransu ko da kuwa fasiki ne azzalumi!! to ya wajaba.akansa ya tabbatar mana da cewa sanin Azzalumi, fasiki shin addini ne ma tukuna ko kuwa Sa annan ya bayyana wa masu hankali inn fa'idar da ke rataye da wajibcin sanin azzalumi, fasiki, har yanda ya zarnanto idan mutum ya mutu ba tare da ya san shi ba to yayi mutuwar jahihyya. To ko ta kaka dai wannan hadisin yana nuni ga cewa akwai Imarni na gaskiya a kowane lokaci kuma a eikin kowace jama'a, wannan kuma ha zai cika ha saidai idan muka yarda da cewa akwai Imam Mahdi wanda kuwa gaskiya ce babu tantama ciki, kuma yana daga 'ya'yan Nana fatima (A.S.) kamar yadda ya gabata. Daga ababen da ke karfafa shi kuma shine: Majma'uz zawa'id na Haisamijuz&i na 5 shafi na 218 da 219 da 223 da 225 da 312. Tafsiru lbnu kasir na 1 shafi na 517, kamar yadda kashiy ya fitar a cikin littafin Rijal nasa shafi na 235 / 428 a tarjamar salim bin Abi Hafsa. 123- AL-lmamus-Sadik na Abu zuhra shall na 194. HADISIN: "HAKIKA KASA BA TA WOFINTA DAGA TSAYAYYE GA ALLAH DA HUJJA:" Wannan hadisin shi ma sunna da shi'ah sun kafa hujja da shi kuma sun ruwaito shi daga tafarkuna masu yawa.'24 Hakika kumail bin ziyad An-Nakha'iy ya ru~vaito shi daga Amirul Mumineen (A.S.) kamar yadda yake a Nahjul Balaga, yace (A.S.) bayan yayi magana mai tsawo: "ya Allah haka yake! Kasa ba zata wofinta ba daga tsayayye ga Allah da hujj a". 124- AL-lskafi na Mutazilawa ya kawo wannan hadisin a cikin AL-Miyar wal Muwazana shafina 81. Da Ibnu kutaiba a cikin uyunul Akhbar shall na 7 da yakubi a tarihinsa na 2 shall na 400. Da lbnu Abdi Rabbuh a Ikdul farid na 1 shall na 265. Da Abu Talib AL-Makkiy a kutul kulub fi Muamalatil Mahbub na 1 shall na 227 da Baihaki a Mahasin wal Masawi'i shall na 40: da khatib a Tarihinsa na 6 shafi na 479 a tarjamar Ishakun Nakha'i. Da khawarizmi AL Hanafi a Manakib shall na 13 da Razi a Mafatihul Gaib na 2 shall na 192 da Ibnu AbiI Hadid a sharhin Nahj kamar yadda zai zo. Da Ibnu AbiI Bir a Mukhtasar shall na 12 da Taftazani a sharhul Makasid na 5 shall na 24 da lbnu Hajar a fathul Ban sharhin Bukhani na 6 shall na 385. Kulaini ya fitar da shi daga hanyoyi daga Amirul Mumineen (A.S.) a Usulul kafi na 1 shall na 136 / 107 da 270/ 103 da 274 /3. Da saduk a kamalud-Deen na 1 shafi na 287/ 4 babi na 25 da dajuzu na I shafi na 289-294 / 2 babi na 26 dajuzu'i na I shall na 10302 babi na 26. (A.S.): -ya Allah haka yake! Kasa ha za ta wofinta ha daga wani wanda zai tsaya ma Allah da hujja, ko ya zamanto a flu sananne ko kuma ya zama boyayye suturtacce, domin kada hujjojin Allah da dalilan Sa su zama sun baci"'27 To don haka ne ya zo a hadisi ingantacce daga Husain bin Abil Ala AL-khaffaf yace: "Nace wa Abu Abdillah (A.S.) shin kasa ta na iya zama babu lmami a cikinta? Yace: A'a zuwa karshen ruwayar."'28 To idan muka jingina wannan hadisin zuwa ga Hadisin sakalain da Hadisin wanda ya mutu bai san Imam na zamaninsa ha, da Hadisin "Halifofi guda goma sha biyu ne" wanda zamu kawo, to idan muka yi haka zamu san cewa hakika da dai Imam Mahdi bai zan an haife shi ha hakkan to da ya zama wajibi wanda ya gabace shi ya zama rayayye har zuwa ranar kiyama, to saidai babu wani daga cikin musulmi wanda yake cewa akwai wani lrnami rayayye banda Imam Mahdi (A.S.) wanda shine Imam na Goma sha hiyu daga cikin Ahlul Baiti, kuma sune wadanda littattafan Manakib suka bayyana sunayensu. 127- Nahjul Balaga sharhin sheikh Mohd Abdu na 4 shafi na 692 / 85. Da sharhin lbnu Abil Hadid na 18 shafi na 351. 128- UsuIul kafi na I shafi na 136/ Babin "innal Arda Ia takhlu mm Hujja." Kuma tafarkin Hadisin ga yanda ya ke: "Adadi daga Ashab daga Ahmad bin Mohd bin Isa daga Mohd bin Abi umair daga Husain bin AbiI Ala daga lmam sadik A.S.". HADISAN: "KHALIFOFI GOMA SHA BIYU NE". Bukhari ya fitar daga Jabir bin sumra yace: "Naji Annabi (S.A.W.A.) yana cewa: "za ayi shugabanni goma sha biyu", sai ya fadi wata magana da ban ji ta ba, sai mahaifina yace: hakika cewa yayi "Dukkansu daga kuraish suke"'29 A cikin sahih Muslim kuwa "Kuma addini ba zai gushe ba yana tsaye har zuwa tashin kiyama kuma ya kasance akwai khalifofi goma sha biyu akanku dukkansu daga kuraish."'30 A Musand Ahmad kuma da tafarkinsa daga Masruk: yace: "Mun kasance muna zaune a wajen Abdallah bin Mas'ud, shi kuwa yana karatun AL-kurani yayin nan, sai wani mutum yace masa: ya kai baban Abdur-Rahman! Shin kun tambayi Manzon Allah (S.A.W.A.) khalifofi nawa ne za su mulki wannan al'umma? Sal Abdullah yace: Tun da na zo lrak babu wani mutum da ya tambaye ni dangane da haka kafin kai, sa annan yace: E, hakika 129- Sahiul Bukhari na 4 shafi na 164 kitabul Ahkam Babin AL-Istikhlaf. Saduk kuma ya fitar daga sumra a cikin kamalud-deen na I shafi na 272 / 19 da AL-khisal na 2 shall na 469 da 475. 130- Sahih Muslim na 2 shall na 119 kitabul lmara Babin An-Nasu Taba'un Ii kuraish. Ya fito da shi daga tafarkuna tara. mun tambayi Manzon Allah (S.A.W.A.) sai yace: Goma sha biyu kamar adadin shugabannin Banu lsra'ila"'31 To wasu fa'idodi da za'a iya samun su daga wadannan ruwayoyi sune kamar haka: 1- Hakika adadin shugabanni ko khalifofi bai shige guda goma sha biyu ba kuma dukkansu daga kuraish ne ba tare da sabani ciki ba. Kuma wannan adadi yayi daidai da wanda shi'ah suka yi i'tikadi da shi na adadin lrnarnai kuma dukkansu daga kuraish. Ta yiwu ace ambaton su da aka yi da cewa su "shugabanni ne ko kuma su kahlifofi ne" bai yi daidai da hahn lmarnai ba, to amrna amsar wannan magana a saran take domin kuwa Annabi (S.A.W.A.) yana nufin shugabanci da kuma khalifanci ne bisa cancanta, kuma Annabi ya tsarkaka da yayi nufin irinsu Muawiya da yazid da Marwan da sauran makarnantansu wadanda suka yi facaka da kadaronin al'ulmma iya ganin damansu. Abin nufi da khalifa shine wanda ya sami izinin shugabancinsa daga Allah Ta'ala koda kuwa shugabancin bai shigo hanunsu ba a sandiyyar galaba da wasu suka yi akansu. Don haka nema ya zo a cikin "Aunul Ma'abud fi sharhi sunan Abi Dawud" kamar haka: "Turbashti yace: tafarki madaidaici a wannan hadisin da abinda ya biyo bayansa a wannan ma'ana shine a fassara shi da masu adalci daga cikinsu, domin kuwa sune suka cancanci sunan khalifai ~ hakika, ba lallai bane ace shugabanci na hanunsu, koda kuwa sun samu zama shugabanni a wani lokacin, domin 131- Musnd Ahmad na 5 shafi na sliafi na 90 da 93 da 97 da 100 da 106 da 107. Kuma saduk ya fito da shi daga Ibnu Mas'ud a cikin kamalud deen na 1 shafi na 270 I 16. kuwa abin nufi shine wanda aka kira su da haka koda ba su zama ba-haka yake a cikin Mirkat".'32 I -Hakika wadannan Goma sha biyu sune wadanda aka yi nufinsu da lafazin hadisin don haka ne aka kamanta su da shugabannin Bani lsra'ila, Allah Ta'ala yace: "Hakika Allah yayi alkawari da Bani lsraila, sai ya tada shugabanni Goma sha biyu daga cikinsu".'33 2- Wadannan hadisai sun nuna cewa kasa ha zata wofinta daga Goma sha biyun gaba daya ha, kuma cewa dole ne a saxni daya daga cikinsu matsawar akwai addini har zuwa ranar tashin kiyama. Kuma hakika Muslim ya kawo a sahihinsa daga wannan babi din, abinda ya zama a bayyane sosai game da wannan a yayin da ya zo a ciki: "Wannan lamari ba zai gushe ha yana cikin kuraish matsawar mutum biyu sun saura a cikin mutane". Kuma wannan dai a bayyane yake kamar yadda ka gani cewa yayi daidai sosai da abinda shi ah ke fadi na cewa lmami na Goma sha biyu (wato Mahdi) yana da rai a hahn yanzu kamar yadda sauran rayayyu suke, kuma cewa lallai zai bayyana a karshen zamani domin ya cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda aka cika ta da zalunci da ja'irci bisa ga yadda kakansa Annabi Muhammad Almustafa (S.A.W.A.) yayi bushara. Kuma dai bai buya ga wani ha cewa Ahlus-sunna basu taba yin ittifaki ba koda sau guda akan fadin sunayen wadannan mutum Goma sha biyu har ma saida lamarin ya kai ga wasun su sun shigar da sunan yazid bin Muawiya da Marwan da Abdul Malik da ire-irensu har suka zo kan 132 -Aunul Ma'bud na 11 shafi na 262. Sharbin ruwaya ta 4259. 133 - Surar Ma'ida: 5 aya ta 12. Umar bin Abdul-Aziz, domin cika adadin Goma sha biyu! ! '34 Alhali kuwa wannan fassara ce wanda ba daidai ba tabbas, ba ta dace da lafazin ruwayar ba. Domin, kenan duk sauran zamanin da ya biyo bayan su Umar bin Abdul Aziz to babu wani khalifa a ciki kenan, baicin dama abin nufi shine cewa addini ba zai gushe ba yana tsaye daram a sanadiyyar su har zuwa tashin kiyama. Hakika hadisan: "khalifofi Goma sha biyu ne" zasu saura babu fassara idan har bamu fassara su da wannan ma'ana ba, domin kuwa kuraishawa da adadinsu ya nunka wanda aka ambata a hadisannan, sun yi shugabanci na zahiri sannan kuma dukkanin su sun mace bugu da karl kuma babu daya daga cikin su wan da hadisi ya ambaci sunansa daga Bani umayya ko Bani Abbas abisa ittifakin musulmai. To game da wannan ne kanduzi Bahanafe yake cewa: "Wasu masu bincike sun Ce: hakika hadisai da suka nuna cewa khalifofi bayan Annabi (S.A.W.A.) su Goma sha biyu ne, sun shahara daga tafarkuna, to tare da shudewan zamani gami da kuma kasantuwan abubuwa da kuma canjin lokaci, an gano cewa abinda Manzo (S.A.W.A.) yake nufi daga wannan hadisi nasa "shine lmamai Goma sha biyu daga Ahlu Baitinsa, da zuriyarsa" domin kuwa ba dama a fassara wannan hadisin da sahabbansa kawai 134- Ka duba maganganunsu a Iittafin: "As-suluk Ii Ma'arifati duwalil Muluk" na Makrizi juzu'i na farko shafi na 13-15 daga ban na daya. Da fafsir Ibni kathin na 2 shafi na 34 a tafsirin aya to 12 na suratul Ma'ida. Da sharhul Akidat Tahawaiyya na 2 shafi na 736. Da sharhin Hafiz lbnul kayyim akan sunanu Abi Dawud na 11 shafi na 263 sharhin hadisi na 4259. Da Hawiy Ill fatawa na 2 shall na 85. saboda karancinsu daga sha biyu, kuma babu dama a fassara shi da Masu mulkin Bani Umayya domin kuwa adadinsu ya zarce sha biyu saboda kuma zaluncinsu da yayi yawa saidai Umar bin Abdul Aziz kuma sabila da su ba daga Banu Hashim suke ba, don kuwa Annabi yace: "Dukkansu daga Banu HASHIM suke" a ruwayar Abdul Malik daga Jabir, kuma boye murya da Annabi (S.A.W.A.) yayi a wannan yana nuna gaskiyar wannna ruwayar da fifikonta domin su basu iya kyan khalifancin inn na Banu Hashim. Har wa yau kuma babu dama mu fassara shi da masu mulkin Bani Abbas domin sun zarce adadin da aka ambata, kuma da karancin lurarsu da maida hankalinsu Dada kuma wani abinda ke karfafa fassarar wannan ruwayar da cewa abinda Manzo (S.A.W.A.) yake nufi shine lmamai Goma sha biyu daga Ahlu Baitinsa, shine ntwayar Hadisin sakalain."'35 Kuma abu ne da bai buya ga kowa ba cewa hadisin "khalifofi Goma sha biyu ne" ya gabaci zuwan lmarnannan Goma sha biyu daya bayan daya, kuma an kiyaye shi a littattafan sihah da wasunsu tun kafin su wadannan lmamai su tabbata, to saboda haka wannan hadisi ba wai yana fadin abinda ya rigaya ya faru ba ne, a'a bil hasali wannan wata hakika ce ta ubangiji wanda, mutumin da ba ya furuci bisa son zuciya ya furta shi sai yace: "khalifofi baya na su Goma sha biyu ne" domin waiman ya zama shaida ne kuma abin gaskata wannan lamari da ya tabbata na gaskiya wanda ya faro daga kan Amirul Mumineen All (A.S.) ya kuma kare kan Imam 135- Yanabi'uI Mawadda na 3 shafi na 105 babi na 77 a cikin binciken hadisin: Bayana khalifofi Goma sha biyu ne. Mahdi (A.S.), kuma wannan shine fassara guda kacal wadda tayi daidai da hadisin kuma ya dace da hankali.'36 To saboda haka abinda ya zama ya inaganta shine a dau wannan hadisi ya zama daya daga cikin dalilai akan Annabcin Manzo (S.A.W.A.) wajen gaskata shi a cikin labaran da ya bayar na boye (Gaibi).? Amma nenian fassara wannan hadisin da wadanda aka san su da munafunci da laifuffuka da zubar da jini daga mutanen Bani Abbas da Bani Umayya da wasunsu, to wannan fassara ce wadda ta saba ma wannan hadisin ciki da waje, gaba da baya, sannan wannan fassara cc wadda ta zubar wa Annabi da mutunci ta kuma rage darajarsa domin wato kenan ya bada labarin cewa addini zai saura zuwa zamanin Umar bin Abdul Aziz misali amma ba zuwa tashin kiyama ba!! 136- Bahsun haulal Mahdi na shahid Mohd Bakir sadr shafi na 54-55. AMBATON IMAMAI GOMA SHA BIYU KARARA DA SUNAYENSU YANA BAYYANA ABINDA AKE NUFI DA KHALIFOFI GOMA SHA BIYU: Domin dada bin diddigin sauran dalilai wanda ke bayyana abinda ake nufi da hadisin: "khalifofi Goma sha biyu ne", kuma suke ayyana shi Imam Mahdi da sunansa da nasabarsa da kuma darajarsa, to anan babu makawa mu yi tunatarwa dangane da wani lamari mai muhimmanci kafin mu zo ga waccan, wannan Iarnari kuwa idan mutum mai adalci yayi tunani akai ya kuma mai da hankali to da wani dan kankanin duhu bai saura ba tare da shi, kuma da ya wadatu da ma'aunin da ya gabata wanda Manzo (S.A~W.A.) ya bar mana shi domin sanin lmamin zamani a cikin kowane lokaci kuma cikin ko wadanne rnutane, kuma da bai nemi wani dalili ba bayan haka. ******************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************* Goma sha biyu su yi wuyan samu a cikin littattafan da aka rubuta su da umarnin shugabannin kuma akarkashin hukumominsu, hukumomin da suka kai hare-hare ma zuriyar Manzo (S.A.W.A.) suka kusa su halakar da 'ya'yan Nana fatsuma (S.A.) dukkaninsu a yayin da Hamadar karbala ta rufe dajinin Mutumi na biyar daga Ashabul kisa (A.S.) wato ma'abuta gwado (wato yayin da aka zubar dajinin Imam 1-Iusain (A.S.) a karbala yayi shahada acan). To lallai kuwa ba abu ne da hankali zai karba ha ace shi wannan azzalumi ya zargi kansa har ya ban a rubuta ruwayar dake nuna cewa Mahdi shine da na tara daga 'ya'yan Husain (A.S.), ko kuma ace abinda ake nufi da khalifofi Goma sha biyu'su ne Imaman shi'ah lmamiyya, to saidai dai ruwayoyin da suka kubce masa aka kuma ruwaito su ha tare da ya ji ba, to duk kuwa da inn wannan takunkumi, sai gashi abinda ya bulla daga wadannan ruwayoyi ya watsu tankar hasken rana. "kuma babu abinda zai inganta a zance ldan rana ita ma ta bukaci dalili" kuma wannan wani abu ne da bai kamata a mance da shi ha, to yanzu za mu kawo tare da takaita Wa, wasu hadisai dake bayyana ma' anar (khalifofi Goma sha biyu ne). 1- A cikin littafin YANABI'UL MAWADDA na marubucin nan kanduzi Bahanafe, shima ya ciro ne daga kitabul Manakib na khawarizmi Bahanafe tare da tafarkin ruwayar daga Imam Rida (A.S.) daga lyayensa (A.S.) daga Annabi (S.A.W.A) a cikin wani hadisi wanda sunayen lmamai Gorna sha biyu dinnan sun zo ciki karara a flu an ambace su daya bayan daya tun daga kan Amirul Mumineen Au bin Abi Talib har aka zo karshensu wato zuwa Imam Mahdi, Mohammad bin Hasan AL-Askari (A.S.). Sai kanduzi yace bayan ya ruwaito wannan hadisin: "kunia Hamwini ya fito da shi"'37 wato rna'abucin littafin fara'idus simtain, AL Juwaini AL Harnwin Bashafi'e. 2- Ya zo kuma a cikin YANABI bar wa yau a karkashin fasalin: "Bayanul A'immah AL Ithna Ashara hi asma 'ihim" wato Babin bayanin imamai Goma sha biyu da sunayen su, ya kawo daga fara'idus simtain a tafarkin lbnu Abbas ruwayoyi guda biyu daga Annabi (S.A.W.A.) a cikiakwai ambaton lmamai da sunayensu kuma na farkonsu shine Au na karshensu kuwa shine Mahdi (A.S.).'38 kuma daidai haka ne za ka samu a babin "zikr khalifatin Nabiy (S.A.W.A.) Ma'a Ausiya' ihi (A.S.)"'39 wato wajen anibaton khalifan Manzo tare da wadanda aka yi wasicci da su. 3- A cikinsa bar wa yau daga Jabir bin Abduilah AL-Ansari daga Annabi (S.A.W.A.): "ya kai Jabir hakika wadanda na yi wasicci da su wadanda kuma su ne lmaman musulmai a baya na nafarkonsu shine Au sannan Hasan, sannan Husain..." Sa'annan sai ya ambaci sauran lmamai Guda tara daga 'ya'yan Husain da sunayensu, ya fara da arnbaton Au bin Husain har zuwa kan na karshe wato Imam Mahdi bin Hasan AL-Askari (A.S.)'40 4-A cikin kamaiud-deen: "Hasan bin Ahmad bin ldris (R.A.) ya bamu labari, ya Ce: Mahaifina ya bainu labari daga Ahmad bin Mohd bin isa da ibrahim bin Hashim dukkansu daga Flasan bin Mahbub daga Abil Jarud daga Abu Ja'afar A.S., daga Jabir bin Abduliah AL-Ansari, 137- Yanabi'ul Mawadda na 3 shall na 161 Babi na 93. 138- Yanabi'ul Mawadda na 3 shall na 99. 139- Yanabi'uI Mawadda tia 3 shall na 212 babi na 93. 140-Yanabi'ul Mawadda na 3 shall na 170 babi na 94. yace: Na shiga wajen fatima (A.S.) kuma a gaba gareta akwai allo akan allon akwai sunayen wadanda aka yi wasicci da su, sal na kirga na tarar sunaye Goma sha biyu ne na karshensu shine AL-ka'im, uku daga cikin su Muhammad ne, hudu daga cikin su AU ne (wato masu suna Au,) A.S."14' Ya kuma ruwaito shi daga wani tafarkin daga Ahmad bin Mohd bin yahya AL-Attar daga Babansa daga Mohd bin Hasan bin Abil khattab daga Hasan bi~ Mahbub har zuwa karshen tafarkin da ya gabata. Za'a iva cewa wannan tafarkin ruwayar ba hujja ba ne daga fuska biyu: Na farko: Hakika Husain bin Ahmad bin ldris a tafarki na farko da kuma Ahmad bin Mohd bin yahya Al-Attar a tafarki na biyu su wadannan ba'a fadi amincinsu a Iittattafan masu ruwaya ba. Amsa: su wadannan mutum biyu suna daga cikin shaihunnan Ijaza wato masu bada izinin ruwaya. kuma saduk bai ambaci daya daga cikin su ba a dukkan littafansa face yace yardan Allah ..ya tabbata a gareshi, kuma a flu yake cewa ba'a ce wa fasiki (yardan Allah ya tabbata a gareshi) a'a ana fadin wannan ne ga mutum mai daukaka, idan kuma muka ce wannan lafazi bata nuni ga cewa mutum amintacce ne, to hakika abu ne mai nisa matuka, kowane dayansu yayi ittifaki akan kaga karya wa mahaiflnsa domin kuwa sun ruwaito wannan hadisi ne daga mahaifansu. Kuma wani abinda ke nuna gaskiyarsu shine cewa kulaini ya fitar da hadisin da tafarki ingantacce daga Abu Jarud kuma ya fara tafarkin da mahaifin sheikh saduk 141- Kamalud-Deen na 1 shafl na 313/4 Babi na28. 115

Koma Ga Fehrisan Littafin



Koma ga Shafin Littattafai