GABATARWAR MAWALLAFI

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI.

Shekaru goma ke nan suka gushe da buga wannan littafi, a duk cikin wadannan shekaru ban sami wani abu da ke iza ni in canja ra'ayina a kansa ba game da cewa ya dace da bukatun musulmi baki daya game bayyanar da akidojin Shi'a Imamiya ( masu bin Imamai sha biyu daga Zuriyar Manzo (S.A.W.A.) ).

Sai dai ma na sake samun karfin gwuiwa a kan sake jaddada yada shi, tare da fatan ya zamanto ya cimma manufa kuma ya biya bukatar kokarin gusar da lullubin giragizan da suka shamakance tsakanin manyan bangarorin musulmi guda biyu masu girma na tsawon lokaci; wato Ahlus Sunna da Shi'a, da kuma kokarin karkade kurar da tsohon tarihi dadadde ya bari a kan akidojin musulunci ingantattu.

Ni ina da tabbacin cewa ra'ayin "kusato da mazhabobi" a yau Ya zama wata bukata matsananciya, kuma manufa mai daukaka ga dukan wani musulmi mai kishin musulunci, koda mene ne kuwa sabanin mazhabarsa da ra'ayinsa a bambance-bambancen akida kuma babu abinda ya fi a wannan ra'ayin kusatowar fiye da cewa kowane mai akida ya dauki nauyin tono bisonta da hakikaninta.

Wannan hanya - a ganina - ita ce mafi aminci wajen ba da ingantaccen tunani game da mazhabar, kuma har wa yau ita ce hanya mafi kusaci ga fahintar daidai daga ra'ayin da jama'arta suke rike da shi.

Saboda in amsa bukatar "Sanyin idona" mai aiki a tafarkin Allah mai daraja Sidi Murtadha Kashmir, na sake duba wannan littafi, na kuma kara shigar da wasu gyare-gyare da kare-karen da kurarren lokaci ya ba da damar yi, tare kuma da gyara kurakuren da suka auku wajen bugawa da ma wadanda ba na bugawa ba, domin in sake gabatar da shi ga Madaba'a, ina mai fatan Allah Ya tabbatar da cimma manufar da ake so, sa'an nan kuma Ya ba mu dacewar rungumar tafarki madaidaici da bin gaskiya, lalle Shi Shi ne mafi alherin wadanda ake roko.
Mawallafi
21 Shawwal 1380 Hijiriyya
1960 Miladiyya
Matsa Wannan Don Komawa Ga Feherisan Littafin