GABATARWA


Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai


Yabo da godiya su tabbata ga Allah, Tsira da aminci su tabbata ga Muhammadu Mafificin `yan Adam da zuriyarsa shiryayyu.
Na yi shiftar wannan littafi ne kuma babu wata manufa tare da shi illa rubuce takaitaccen abinda na kai gare shi na fahintar akidojin musulunci a bisa tafarkin Ahlul Baiti (Zuriyar Gidan Manzo (S.A.W.A.) aminci Ya tabbata gare su.
An dai rubuce wannan takaitaccen littafin ne ba tare da kawo nassosin da yawanci suka iso daga Ahlul-Baiti game da su ba, domin sabon kamu da kuma mai koyo da kuma malami su amfana da shi, na sanya masa suna "Akidojin Shi'a"1 abinda nake nufi kuwa shi ne "Shi'a Imamiya Ithna Ashariya" a kebe.
Shiftar wannan littafi an yi ta ne a shekarar 1363 Hijiriya, kuma an yi ta ne da nufin ba da ita a matsayin laccar da ake yi a ayyanannen lokacin


____________
1- Wannan shi ne sunan da marabucin Littafin ya sanya wa Littafin a bugu na farko.


( 10 )

koyarwa da kwalejin "Muntadan Nashrid Diniya"2 don amfani da ita wajen share fagen dogon bincike game da akida daga bisani.
A wancan lokacin na ci nasarar gabatar da dama daga cikinta a laccoci kuma sam ban kasance na shirya su domin a wallafa a yada a kuma karanta ba, don haka na zamanto na jinkirtar da dama daga cikin takardun laccoci masu muhimmanci da kuma darrusan da na ba da shiftarsu a cikin wancan halin, musamman ma dangane da abinda Ya shafi Akida da ilimin tabbatar da samuwar Allah.
Sai dai kuma a wannan shekarar - bayan wucewar shekaru takwas- babban malami mai alfarma Malam Muhammadu Kazim Al-Kutbi3 Allah Ya kiyaye shi, ya kwadaitar da ni wajen sake tunani a kansu, da kuma taro su a maida su rubutaccen littafi takaitacce mai isar da dukan bangarori da nufin yada su domin amfana baki daya, domin kuma a kore da dama daga cikin soke - soke da aka lika wa Shi'a Imamiyya, musamman ma da yake wasu marubutan wannan zamani a kasar Masar da sauransu ba su gushe ba suna ta dira a kan Shi'a da alkalumansu suna soke - soken rashin adalci a kan mazhabar Shi'a da akidojinta domin jahilci ko kuma kin sani da gangan game da tafarkin Zuriyar Gidan Manzon Allah (S.AW.A.) a tafarkunansu na addini kuma da haka ne duk suka hadu a kan zaluntar gaskiya da yada jahilci a tsakanin masu karanta littafansu suna masu kira zuwa rarraba kalmar musulmi, da haifar da husuma da kufe a zukatanru, kai har ma da cuna wasunsu a kan wasunsu... Kuma babu masani da a yau zai jahilci gwargwadon bukatar kusato da jama'ar musulmi ga junansu da binne kullace - kullacensu idan har ba mu iya mun zamar da su sahu daya baki daya a karkashin tuta guda ba.
Ina fadan haka alhali kuma ina mai jin cewa - abin ban takaici - ba za mu iya yin kome game da irin wadannan miyagun soke-soken tare da wadanda muka jarraba daga cikin irin wadannan marubutan ba


____________
2- Wannan kwalejin makarantar marubucin ce shi kansa kuma daga bisani an canja mata suna zuwa "Kwalejin Fikihu". 3- Shi ne mai Dakin karatu da ake kira Haidariyya - Najaf shi ne farkon wanda ya biya kudinsa aka fara yada wannan littafin.


( 11 )

kamarsu Dokta Ahmad Amin marubucin littafin Fajrul Islam da makamancinsa masu kira zuwa ga rarraba, su bayanin akidojin Shi'a Imamiya bai kara musu kome ba illa tsaurin kai, kuma fadakar da su kura-kurensu bai kare da kome ba sai jayayya.
Kuma bai dame su ba kan cewa su wadannan da ma wadanda ba su ba don sun ci gaba da tsaurin kan su sun dage a kai ba don gudun kada wadanda ba su sani ba su yarda da su wannan dibilbilewar ta baibaye su kuma soke-soke su kwashe su su tsiro musu da kufe da kunci.
Kuma koda ma mene ne wannan al'amarin , ni dai ina mai kaddamar da wannan littafin ne da fatan cewa a cikinsa za a sami abinda zai amfani mai neman gaskiya, don in zamanto ni ma na ba da gudummawa mai amfani ga musulunci, kai hidima ma ga `yan Adamtaka baki daya, na tsara shi a kan gabatarwa da kuma Fasali-Fasali; kuma daga Madaukaki Shi Kadai nake neman gamon katar.

Muhammad Ridha Al Muzaffar
Najaf - Iraki
27 watan Jumada Akhir 1370
Miladiyya 1950



Matsa Wannan Don Komawa Ga Feherisan Littafin