1- Imaninmu Game Da Sani Da Kuma Neman Ilimi


Mun yi imanin cewa da yake Allah Ya Yi mana baiwar karfin tunani kuma Ya ba mu hankali to Ya umarce mu ne da mu yi nazari da tuntuntuni a kan alamun ayyukanSa mu yi tunani a kan hikimarSa da kuma kyautata lura a ayoyinSa a kan duniya baki daya da kuma a kan kanmu, Allah Ta'ala Yana cewa:
"Za mu nuna musu ayoyin Mu cikin sama da kuma a kawukansu, har Ya bayyana gare su cewa Shi lalle gaskiya ne..." (Surar Fussilat: 53)

Kuma Ya zargi masu bin iyaye ba tambaya da cewa:

"Suka ce mu dai kawai za mu bi abinda muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba sa hankalta ne kuma ba sa shiryuwa." (Surar Bakara: 170)

Kamar kuma yadda Ya aibata masu bin zato kawai da dikake a cikin duhu da cewa:
"Babu abinda suke bi sai zato kawai." (Surar An'am: 116)

Alal hakika mu abinda muka yi imani da shi shi ne cewa: Lalle hankulanmu su ne suka wajabta mana yin tuntuni kan halittu kamar yadda suka wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da'awar cewa shi Annabi ne da mu'ujizarsa. Kuma a gurin hankali bai dace ba a yi koyi da wani ba a cikin wadannan al'amuran kome matsayinsa da darajarsa kuwa.



( 13 )


Abinda Ya zo a cikin Alkur'ani na kwadaitarwa a kan tuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne kawai don kara tabbatar da wannan `yancin na dabi'ar halitta a hankali da suka dace da ra'ayoyin ma'abuta hankali, Ya kuma zo ne don fuskantarwa zuwa ga abinda dabi'ar hankula ta hakunta.4
Bai dace ba a cikin irin wannan hali mutum ya yi wa kansa saki na dafe a kan al'amarin akida, ko kuma ya kare da dogaro a kan wadanda suka masa tarbiyya, ko kuma wasu mutane daban, lalle ma ya wajaba ne a kansa daidai yadda yake a dabi'a karfafa kan ya yi bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi kididdiga a kan jiga-jigan akidarsa5 wadanda ake kira jiga jigan addini wadanda mafi muhimmancinsu su ne: Tauhidi, wato kadaita Allah, da Annabci da Imamanci da kuma Tashin Kiyama.
Duk wanda Ya yi koyi da iyaye haka siddan ko kuma makamantansu a imani da wadannan jiga-jigan, to lalle ya ketare iyaka ya fandare daga hanya madaidaiciya kuma ba zai taba zama an yafe masa ba har abada. A takaice dai mu muna da'awar abubuwa biyu ne:


____________
4- Wanan kuwa shi ne daga fadar Allah Ta'ala cewa: "Ka ce ku yi dubi zuwa ga sammai da kasa." Surar Yunus:l01 da Kuma Fadar Allah Ta'ala: "Shin ba sa duba rakumi yadda aka halitta shi, da kuma sammai yadda aka kakkafa su. Da kuma kasa yadda aka shimfida ta. To ka yi fadakarwa kai dai mai fadakarwa ne kawai." Surar Gashiya: 17-21.
Da kuma fadar Allah Ta'ala: "Shin su ba sa yin tuntuni ne .:an kawu'kansu" Surar Rum: 8. Da kuwa fadar Allah Ta'ala: "Ka sani cewa babu wani abin bautawa sai Allah". Surar Muhammad: 19.
5- Ba wai dukan abinda aka ambata wannan littafi ba ne yake daga cikin jiga-jigan akida, da yawa daga cikin akidojin da aka ambata kamarsu Hukuncin Allah da kaddara, da Raja'a da sauransu ba wajibi ba ne a kudurce da su ko kuma a yi bincike a kansu, ya halatta a dogara ga wani da aka san ingancin maganarsa game da su kamar Annabawa da Imamai. Da yawa daga cikin al'amura irin wadannan da muka yi Imani da su dogaro ne kawai da abinda aka samo daga Imamanmu na daga ingantattun hadisai tabbatattu. (Marubuci R.A.)


( 14 )


Na Farko: Wajabcin bincike da kuma nema sani a kanjiga jigan akida bai halatta a koyi da wani ba a kansu.
Na Biyu: Wannan wajabcin wajabci ne na hankali kafin ya zamanto na shari'a wato saninsa ba wai ya samo asali daga nassosin addini ba ne koda yake ya inganta su karfafa shi bayan hankali ya tabbatar da shi.
Kuma Ma'anar wajabcin hankali babu abinda take nufi illa fahintar neman sani da hankali ya yi da kuma lizimtar yin tuntuni da kokari a jiga-jigan akida.


( 15 )


2- Imaninmu Game da Koyi da Wani a Rassan
Al'amuran Addini.



Rassan al'amuran addini su ne hukunce hukuncen shari'a wadanda suka shaif ayyuka, su ba wajibi hukunce-hukuncen ba ne a yi bincike da ijtihadi a kansu sai dai ma idan ba su kasance daga cikin muhimman al'amura wadanda suka tabbata da ingantattun hujjoji kamarsu wajabcin salla da zakka da azumi ba to dayan uku ne ya wajaba:
Ko Ya yi ijtihadi Ya yi bincike a kan hukumce-hukumce idan yana daga cikin masu iya yin hakan.6
Ko kuma ya zama mai ihtiyadi, idan yin ihtiyadi zai wadatar da shi.7
Ko kuma ya yi koyi da Mujtahidi wanda ya cika saharruda.8 Wato ya zamanto cewa wanda zai yi koyin da shi, mai hankali ne, Adali


____________
6- Ijtihadi kalma ce ta larabci da aka samo ta daga Juhud a lugga wato yin kokari don yin wani aiki amma a Ka'idar malaman mu na fikihu tana nufin tsamo hukunce-hukuncen shari'a daga nassosinsu tsararru. Akwai Mujtahidi Mudlak, wato cikakken mujtahidi, akwai kuma Mujtaliid Mutajazzi wato Mujtahiddi a wasu sassa, shi ne Mujtahidin da zai iya tsamo hukunce- hukunce a kan wasu al'amura banda wasu. Don karin bayani ana iya duba Littafin Al- Usul Amma lilfikihil Mukarin na Hujjat Muhammad Taki Al- Hakim Shafi na 561 zuwa 565. Da kuma Al- Masa'il Al-Muntakaba na fatawoyin Ayatullahil Uzma Sayyid Sistani shafi na 9 zuwa 10. 7- Ihtiyadi shi ne aikin da mutum zai sami yakinin cewa ya sauke wajibin da ke kansa idan ya aikata shi wannan shi ne ihtiyadi a dunkule, akwai kuma ihtiyadi a kebe da ke nufin bin fatawoyin mujtahidai don tabbatar da cewa an yi aiki da fatawar daya daga cikinsu. Littafin da ya gabata shafi na 10 zuwa 14.
8- Taklidi, koyi, shi ne yin aiki daidai da fatawar Mujtahidi wanda maganarsa hujja ce a aikace a halin yanzu tare da kiyaye cewa a bi ta daidai. Masu koyi sun kasu kashi biyu: (1) Wanda bai san kome ba a hukunce-hukuncen sahri'a. (2) Da kuma wanda ya san wani abu amma ba zai iya tsamo hukunce-hukuncen da kansa ba.


( 16 )

"mai kiyaye kansa, mai kare addininsa, mai saba wa so ransa, mai bin umarnin Ubangijinsa",9 ·
Duk wanda ba Mujtahidi ba ne kuma ba mai yin ihtiyadi ba ne kuma bai yi koyi da mujtahidi wanda ya cika sharuda ba to dukkan ayyukan ibadarsa batattu ne ba za a karba daga gare shi ba, ko da kuwa ya yi salla ya yi azumi ya y ta ibada duk tsawon rayuwarwa, sai dai idan aikin sa Ya dace da ra'ayin wanda zai yi koyi da shi daga baya, ya kuma yi gamon katar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah Ta'ala.10



____________
9- Tafsirul Askari shafi na 300 da Littafin Al- Ihtijaj, 511, H. 337, abinda ya wadatar da karin bayani.
10- Manyan Malamai sun kawo abinda ya wadatar da karin bayani a cikin mukaddamomin Risalolinsu na hukunci da ke kunshe da fatawoyinsu a Babin Takalidi (yadda ya wajaba a kan dukan baligi wanda bai kai ga darajar ijtihadi ba kan cewa ya zamanto a cikin dukkan ayyukan ibadarsa da mu'amalarsa da sauran ayyukansa, ya zamanto mai yin koyi ko mai yin ihtiyadi, sai dai kawai idan yana da tabbacin cewa ba ya bukatarsa a aikinsa ko kuma barinsa ba zai zama saba wa hukunci ba koda da gwargwadon haramcin shari'a, ko kuma hukuncin ya kasance daga larurar addini da mazhaba kamar yadda yake a wasu wajibai da haramtattu da kuma da dama daga mustahabbai da halalai, ko ya kuma zamanto ya sami sani a zuci da kuma natsuwa a zuciya daga madogarai na hankali, kamar yaduwar labari, da fadar kwararren da ya tabbatar da cewa suna daga ciki.) A duba: Minhajis Salihin Juzu'i na daya daga fatawoyin Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Husain Sistani shafi na 9.


( 17 )

3- Imaninmu Game da Ijtihadi



Mun yi Imanin cewa: Ijtihadi (matsayin tsamo hukunce-hukunce) a rassan hukunce-hukuncen shari'a wajibi ne da wajabcin kifa'iyya da ya doru a kan dukkan musulmi a zamanin boyuwar Imam11, wato.


____________
11- Imam Muhammad Mahadi dan Imam Hasan Askari (a.s) wanda shi ne cikamakin Imamai goma sha biyu - Boyuwarsa ta kasance sau biyu ne:
Ta farko: Ana ce da ita karamar boyuwa: Ta fara ne a daga shekarar da mahaifinsa Imam Hasan Askari (a.s) ya rasu shekara ta 260 Hijiriyya kuma ta kare a shekara ta 329 Hijiriyya kuma ya kasance yana da jakadu hudu su ne: Na farko Usman bin Sa'id Al -Umari Al- Asadi, shi ya kasance wakilin Imam Hadi sa'an nan kuma wakili ga Imam Askari sai kuma ga Imam Muhammad Mahadi. Aminci ya tabbata gare su.
Na Biyu: Muhammad bin Usman bin Sa'idul Umari al- Asadi wanda ya dauki nauyin wakilci bayan rasuwar mahaifinsa na tsawo kimanin shekaru arba'in har zuwa mutuwarsa; a shekarar 329 Hijiriyya.
Na uku: Husain bin Ruh wanda ya dauki nauyin al'amarin wakilcin tun daga rasuwar Muhammad bin Usman al- Umarin har zuwa wafatinsa a shekarar 326. Hijiriyya.
Na Hudu: Aliyu bin Muhammad As- Samarri, shi ne na karshe daga cikin wakilai hudu, ya yi wakilcinsa ne na tsawo shekara uku yayin da ya kawo karshe da wafatinsa ranar 15 ga watan Sha'aban shekarar 329. Hijiriyya.
Sananne ne cewa dukkan wadannan wakilai an yi musu kabari ne a birnin Bagadaza bayan rasuwarsu, ya zuwa yanzu kuma Makabartunsu sanannu ne mashahurai.
Ta Biyu: Babbar Boyuwa: Ta fara ne daga ranar 15 ga watan Sha'aban shekarar 329, Hijiriyya daga rasuwar wakili na hudu wanda yayin da aka tambaye shi cewa wa zai gadarwa wannan al'amarin kuma sai ya ce Allah na da wani al'amari kuma shi ne mai isar da shi: A cikin wannan akwai bayani game da abinda Imam al- Muntazar


( 18 )

ma'ana cewa ya wajaba a kan musulmi a kowane zamani. Amma kuma idan har wani da zai iya kuma zai wadatar ya dauki nauyin yi to ya fadi daga kan sauran musulman, sai su wadatu da wanda ya dauki nauyin yin hakan kuma ya kai ga matsayin ijtihadi kuma ya zamanto ya cika sharudan, sai, su yi masa takalidi, su yi koyi da shi, su koma gare shi a kan rassan hukunce-hukuncen addininsu.
Don haka a kowane zamani wajibi ne musulmi su duba kansu su gani, idan sun sami Mujtahidi a tsakaninsu wanda ya sadaukar da kansa ya kai ga matsayin Ijtihadi- wanda babu mai samunsa sai mai babban rabo- kuma ya kasance ya cika sharudan da suka sa ya cancanci a yi masa takalidi, a yi koyi da shi, sai su wadatu da shi su yi masa takalidi, su koma gare shi domin sanin hukunce-hukuncen addininsu.


____________
Allah Ya gaggauta bayyanarsa ya sanar da shi game da fara babbar boyuwa wadda take ci gaba har zuwa yau, yayin wakilcin Imam a zamanin boyuwar babba ya zama an sallama shi ga Mujtahidi wanda ya cika sharudan da aka bayyana a littafan fikihu.
Kamar yadda ya gabata a bayanin ma'anar ijtihadi za mu ga cewa tsamo hukunce-hukunce wanda ke nufin "ayyana matsayin aiki game da shari'a tare da dalilai kuma Muhimmancin ijtihadi yana zuwa ne saboda bayyana cewa mutum a bisa biyayyarsa ga shari'a mai tsarki da kuma wajibcin gudanar da hukunce-hukuncenta -lalle ne gare shi ya ayyana abin da zai aikata game da ita. Tunda yake yawancin hukunce-hukuncen shari'a ba su bayyana karara yadda za ta wadatar daga neman dalilai ba, bai dace da hankali ba a ce za a haramta wa mutane baki daya ayyana matsayin aiki a bisa dalilai, a hana su duba dalilan da suka ayyana matsayinsu game da shari'a. Don haka aikin tsamo hukunce-hukunce ba ma kawai ya halatta ba ne, larura ne ma a yi shi, wannan larura kuma asalinta daga biyayyar mutum ne ga shari'a, musu a kan haka tamkar musu ne a kan abinda yake bayyananne kuma kalmar ijtihadi a tarihi ta sami fassarori dabam-daban yadda har fassarorin suka sanya ma'anoninsa a cikin duhu har ya kai ga sabani saboda damarwa da rikitarwa ba a samu tabbacin ma'anarta ba a yau har sai da ya ketare matakai daban-daban na fassarar ma'anoninsa.
A duba Littafin "Ma'alimuj Jadid Lil Usul: Sayyid Shahid Sadr (r.a) shafi na 23 zuwa sama. Don karin bayani kuma game da Boyawar Imam a duba Littafin Tarikhul Gaibatus Sugra na Sayyid' Muhammad Sadr: 395 fasali na uku (Assufara'ul Arba'ati Hayatuhum wa Nashadatuhum).


( 19 )

Idan kuwa ba su sami wanda yake da wannan matsayin ba to Ya wajaba a kansu kowane daya daga cikinsu Ya kai ga matsayin Ijtihadi, ko kuma su shirya a tsakaninsu wanda zai dukufa domin kaiwa ga wannan mukami domin ba zai yiwu ba dukansu su dukufa domin neman wannan al'amari ko kuma zai yi wahala.
Kuma bai halatta gare su ba su yi koyi da wanda ya rigaya ya mutu daga cikin Mujtahidai.l2 Ijtihadi shi ne nazarin dalilan shari'a domin samun masaniya game da rassan hukunce-hukuncen shari'ar da shugaban Manzanni (S.A.W.A.) Ya zo da ita, kuma ba ta canzawa ba ta sakewa da sakewar zamani da kuma halaye "Halalin Muhammadu halal ne har zuwa ranar Kiyama, haramun dinsa kuma haramun ne har zuwa ranar tashin Kiyama."13
Dalilan shari'a su ne: Alkur'ani mai girma, da sunna, da Ijma'i, da Hankali kamar yadda yake a filla filla a littafin Usulil Fikhi.
Samun matsayin Ijtihadi kuwa yana bukatar tarin ilimi da sani wandanda ba sa samuwa sai ga wanda ya dage ya wahalay ya sallama kansa ya ba da kokarinsa wajen samun sa.14


____________
12- Takalidi, koyi da Mujtahidi kashi biyu ne: (1) Farawa (2) da Dorewa Farawa: Shi ne baligi ya yi wa mujtahidi matacce taklidi ba tare da ya riga fara yi masa taklidi tun yana raye ba. Wannan bai halatta ba koda kuwa mujtahidi matacce ya fi wadanda ke raye ilimi.
Dorewa: Wannan kuma shi ne mukallafi ya fara ya yi wa wani mujtahidi ayyananne taklidi tun yana raye sa'an nan ya ci gaba da binsa bayan rasuwarsa. Wannan ya halatta idan har Mujtahidin da ya rasun ya fi wadanda suke raye ilimi ko kuma idan ba a sani ba ko da a dunkule cewa fatawar wanda ya rasun ta saba wa ta wanda yake raye a al'amuran da ya zama yana fuskantar mushkila game da su. Domin karin bayani a duba littafin Urwatul Wuska Juzu'i na 1 shafi na 17-18, da kuma Masa'ilul Muntakhaba na Sayyid Sistani Matsala ta 13 (12, 13, 14).
13- Al- Kafi Juzu'i na 58/1 H. 19, Al- Mahasin 1/420 H. 963.
14- Abubuwan da Mujtahidi ke bukata na ilimi kashi tara ne, uku daga-cikinsu daga ilimin adabi su ne ilimi,lugga, da ilimin Sarfu, da ilimin nahwu, akwai kuma ilimin aiki da hankali da suka hada da ilimin Usuli, da Ilmul Kalam, da kuma ilimin Mandiki, sai kuma ilimin tafsirin ayoyin hukunce-hukuncen Kur'ani, da ilimin hadisan hukunce-hukunce sai kuma ilimin sanin rauni da kuma inganci da kuma


( 20 )

4- Imaninmu Game da Mujtahidi



Abinda muka yi imani da shi game da Mujtahidi wanda ya cika sharuda: cewa shi Na'ibin Imam (A.S.) na halin boyuwar shi Imam din.15 Kuma shi mai hukunci ne, shugaba cikakke, abinda yake ga Imam (A.S.) yana gare shi a fannin al'amura da shugabanci a tsakanin mutane kuma duk wanda ya ki hukuncinsa tamkar ya ki hukuncin Imam (A.S.) wanda ya ki hukuncin Imam (A.S.) kuwa Ya ki hukuncin Allah ne wannan kuwa a matsayin shirka da Allah yake, kamar yadda Ya zo a hadisi daga Sadikun Ahlul Baiti (A.S.).16
Shi Mujtahidin da ya cika sharruda ba wai madogara ne kawai a wajen ba da fatawa ba, a'a har ma yana da jagoranci na gaba daya,17



____________
inganci masu ruwaya. Don Karin bayani a duba Al-Wafi fi Usul'ul Fikhi na Fadhilul Tuni 25-29 da kuma AlKur'an wal Akida na Sayyid Muslim Hamudil Hilli: 248-252.
15- A duba karin bayanin da ya gabata a kan Abinda muka yi Imami da shi game Ijtihadi.
16- Ihtijaj 2/260 H. 232 Al-Kafi 1/54 H. 10.
17- Willayatul Fakihi, shugabancin Malami, ma'ana ce da ke nufin shugabanci na shari'a da jagorancin dokoki ga Mujtahidi wanda ya cika sharruda wanda shi wannan matsayi yana mazaunin ci gaban sakon Imama ne kuma ba ya da cikin fararrun al'amuran addinin a wannan zamanin sai dai ma asalin wannan batu yana da tushe ne tun daga farkon sako da kuma zamanin Imamai Ma'asumai (A.S.) a halin wannan matsayi yana misalta ci gaban Imamanci ta bangaren ayyuka baki daya ya bambanta da Imamanci ta nassosi na musamman ga kowane fakihi, da kuma ismar da ta kebantu ga Mamzon Allah (S.A.W.A.) da kuma Imami goma sha biyu bayansa tunda yake nassi da isma sun kebantu ne da Ma'asumai (A.S.).
Babu makawa a san hikimar wannan shugabanci na gaba daya a zamanin Boyuwar Imam, wannan matsayi yana nufin kafa hujja ne ga mutane, da kuma ja-



( 21 )

don haka ana komawa gare shi a hukunci da raba gardama da shari'a, wannan duk na daga cikin abubuwan da suka kebantu da shi kuma bai halatta ga wani ba ya dauki nauyinsu sai shi, sai dai da izininsa, kamar kuma yadda bai halatta ba a yi haddi ko labadtarwa sai da umarninsa da hukuncinsa.18
____________
gorancin wannan zamanin domin kare amfanin bayin Allah da kuma tafi da al'amuransu a kan yadda shari'ar musulunci ta tsara. Daga cikin manyan manufofinta kuwa akwai kare hukunce-hukuncen shari'a domin al'amarin tsara shari'a da sanya dokoki na Allah Ta'ala ne mahalicci mai kudura ,amma dangane da hukunce-hukunce al'amuran rayuwa kuwa musamman sababbi da ke aukuwa yanzu, ba za su gaza kasan cewa tabbacin hukunce-hukunce ne da aka gama gabatar da su daga bangaren Manzo (S.A.W.A.) ba yayin rayuwarsa... An ruwaito daga Imam Mahadi, (Allah ya gaggauta bayyanar sa) cewa "Amma hakikanin al'amura masu faruwa to dangane da su ku koma ga masu ruwaita hadisanmu, domin su hujjatu ne a kanku ni kumar hujjar Allah ne a kansu." A duba Littafin Al- Imama Hatta Wilayatul Fakih shafi na 51."
18- Ruwayar Umar Bin Hanzala na ishara da haka yayin da ya ce: 'Na tambayi Aba Abdillah, Alaihis Salam dangane da mutane biyu daga cikin ma'abutanmu (shi'a) wadanda ke da rikici a tsakaninsu a kan bashi ko kuma gado suka kai kara zuwa gurin shugaba ko Alkalai shin haka ya halatta? Ya ce: Wanda ya kai kara gare su a kan gaskiya ko karya to ya kai kara gurin Dagutu da kuma abinda Allah Ya yi umarni a kafirce masa, Allah Ta'ala Ya ce: "Suna so ne su kai kara zuwa ga Dagutu alhali kuwa an umarce su da su kafurce masa" Na ce: To yaya za su yi? Ya ce: Su duba wanda ya ruwaito hadisanmu, ya kuma duba halal dinmu da kuma haram dinmu, kuma ya san hukunce-hukuncenmu su amince da shi a matsayin mai hukunci, domin ni na sanya shi mai hukunci a kanku, idan ya yi hukunci da hukuncinmu bai amince ba to ya wawaitar da hukuncin Allah kuma ya dawo mana da hukuncin ne, wanda ya mayar mana kuwa ya mayar wa Allah, kuma daidai yake da shirka da Allah".
Al-Wasa'il Juzu'i na 27 shafi na 136 Hadisi na 33416, Al Kafi Juzu'i na 1 shafi na 54 Hadisi na 10, Al- Ihtijaj Juzu'i na 2 shafi na 260 Hadisi na 232, Tahzibil Ahkam Juzu'i na 6 shafi na 218 hadisi na 514 da shafi na 301 hadisi na 845 da kuma surar Nisa'i aya ta 60.


( 22 )


Kuma ana komawa gare shi a kan dukiyoyin da suke hakkokin Imam ne da suka kebantu da shi.19


____________
19- Abin nufi da dukiya: Zakka da khumusi. Zakka tana daga wajiban addini. Hadisai da dama suna nuna cewa mai hana Zakka kafiri ne, da kuma cewa wanda baya ba da zakka ba shi da salla. Zakka tana wajaba ne a kan abubuwa tara:
1- Dabbobin Ni'ima guda uku wadanda su ne: Rakumi da shanu da kuma tumaki da Awaki.
2- Zinare da Azurfa.
3- Kayan Abinci hudu:Alkama, Sha'ir, Dabino da kuma zabibi.
A kowace shekara ake karbar zakka a wadannan abubuwan tara a bisa kimanin da aka sani, da sharrudan da aka ambata a gurarensu, zakka ba ta wajaba ba a kan abubuwan da ba wadannan taran ba sai dai kuma mustahabbi ne a fidda zakka a dukiyar kasuwanci da dawaki da kuma abubuwan da kasa ke tsirarwa na daga `ya'yan itaciya da wasunsu. Wadannan dukiyoyin kuma ana kashe su ne a kan kasafi takwas wadanda su ne: 1- Fakiri 2- Miskini 3- Masu Aikinta 4- Wadande aka son jawo hankalinsu ga musulunci 5- Bayi 6- Wadanda ake bi bashi 7- A tafarkin Allah -wawo dukkan wata hanya ta alheri, an kuma ce ya kebanta ne ga abinda ya shafi fa'idar kowa da kowa. 8- Wanda ke kan Tafarki, shi ne matafiyi wanda guzuri ya yanke masa ko kuma kayansa ya bace yadda ba zai iya komawa muhallinsa ba koda kuwa mawadaci ne, babu wani al'amari na zakka a mazhabar Shi'a Imamiyya face ya yi daidai da sauran mazhabobi hudun nan sanannu.
A duba littafin Urwatul Wuska Juzu'i na 2 shafi na 87-134, da masa'ilul Muntakhaba na Sayyid Sistani, da Aslus Shi'a wa Usuliha da rubuto hujjojinsa na Mu'assasar Imam Ali (A.S.) shafi na 243.
Khumusi: A gurin Shi'a Imamiyya hakki ne da Allah Ya wajabta saboda zuriyar gidan Manzon Allah Muhammadu (S.A.W.A.) a madadin sadakar zakka wadda take haramun ce gare su. Asalinsa kuma shi ne fadar Allah Ta'ala: "Ku sani cewa lalle abinda kuka samu ganimarsa da wani abu to lalle khumusinsa na Allah ne da Manzonsa da kuma dangi makusata." Surar Anfal ayata 41.
Khumusi ya wajaba ne a kan abubuwa bakwai:
1- Ganimar da aka kwata daga kafiran yaki yayin yakayya da su tare da izinin Imam.
2- Ma'adanai kamar su zinare da azurfa da.....
3- Taskar tsintuwa a karkashin kasa
4- Jawharai da aka tsamo a teku.
5- Dukiyar Halal da ta gauraya da ta Haram kuma ba'a san mamallakinta ba.



( 23 )


Wannan matsayin ko kuma shugabanci na gaba daya Imam (A.S.) Ya ba da shi ga Mujtahidi wanda ya cika sharruda domin ya kasance na'ibinsa wato wakili ko magajinsa a yayin boyuwarsa, wannan shi ne abinda ya sa ake ce masa "Na'ibin Imam".



____________
6- Fegin da kafirin amana ya saya a gurin musulmi.
7- Abinda ya saura daga kasafin shekara da kasafin iyali na ribar kasuwanci da aiki.
Ana raba khumusi kashi shida:
l- Na Allah
2- Na Annabi.
3- Na Imam. Wanan kasafin gida uku ya kebanta ne ga Imam Mahadi da ake jira. Allah ya gaggauto da bayyanarsa, Amin.
4- Marayu
5- Miskinai da kuma
6- Wadanda ke kan tafarki guzuri ya yanke musu.
Domin karin bayani a duba Urwatul Wuska Juzu'i na 2 shafi na 170-199, da kuma masa'ilul Muntakhaba na Sayyid Sistani matsala ta 251-239, da Aslushi'a wa Usuliha shafi na 245 da ma dukkan Risalolin hukunce-hukunce.



( 24 )


( 25 )

FASALI NA FARKO


Sanin Ubangiji Imaninmu Game da:

  • Allah Ta'ala
  • Tauhidi
  • Siffofinsa Ta'ala
  • Adalci
  • Wajabta Aiki
  • Hukuncin Allah da Kaddara
  • Al-Bada'
  • Hukunce - Hukuncen Addini




    ( 26 )


    ( 27 )

    5- Imaninmu Game da Allah Ta'ala.


    Mun yi imani cewa Allah Madaukaki daya ne Makadaici babu wani abu kamar Shi, Wanzazze bai gushe ba kuma ba Ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai Hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai Ji, Mai gani, ba a siffanta Shi da abinda ake siffanta halittu, Shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jiki ba ne kuma ba rabi ba ne, ba Shi da nauyi ko sakwaikwaya, ba Shi da motsi ko lambo, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi.20 Kamar kuma yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu da, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi, maganai ba sa riskar Sa Shi kuwa yana riskar maganai.

    ____________
    20- An ruwaito daga Amirul Muminin Imam (A.S.) a amsar da ya ba wa Za'alab cewa: "Ni ba bawan Ubangijin da bana gani ba ne" sai kuma ya kara bayani game da siffofin Allah yana cewa: "Kaiton ka ai idanduna ba sa ganin Sa da hallarar maganai sai dai zukata ne ke ganin Sa da hakikanin imani, Kaitonka ya Za'alab, lalle Ubangijina ba a siffanta Shi da nisa, ba a siffanta Shi da motsi ko lambo, ko tsayuwa, tsayuwa ta mikewa kyam, ba kuma a siffanta Shi da zuwa ko kuma tafiya, mai Taushin Tausasawa ba a siffanta Shi da babba ,mafi girman masu girma wanda ba a siffanta Shi da girma mafi daukakar masu daukaka wanda ba a siffanta shi da gallazawa, Mai jin kai da rahama ba a siffantashi da rauni mumini ba wai da ibada ba, mai riska amma ba da jiki ba, mai magana amma ba da lafazi ba, Ya na tare da abubuwa amma bada gauraita ba, Yana kuma rabe da su amma ba wai da sabani ba, Ya na sama da kome ba a ce wani abu na sama da shi, Yana gaban kome ba a ce yana da gaba, Yana cikin kome ba wai kamar yadda wani abu ke wajen wani abu ba."
    Littafin At-Tauhid na Saduk Shafi na 304 Babin Hadisin Za'alab da kuma Amali Saduk Shafi na 280 Al-Majlisul Khamis Wal Khamsun, da Biharul Anwar juzu'i na 4. Shafi na 27.


    ( 28 )


    Duk wanda Ya ce ana kamanta Shi to Ya zamar da Shi halitta ke nan, wato Ya suranta fuska gare Shi da hannu da kuma idaniya, ko kuma cewa Shi yana saukowa zuwa saman duniya, ko kuma cewa zai bayyana ga 'yan aljanna kamar wata, ko kuma makamantan wannan,21 to lalle yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne, wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da Ya tsarkaka daga nakasa, kai duk ma abinda muka bambance Shi da sake-saken zukatanmu a mafi daldalewar ma'anarsa to Shi abin halitta na kamar mu wanda kuma mai komawa ne gare mu, kamar yadda Imam Bakir (A.S.) fassara Shi gare mu da bayyani mai hikima da kuma zurfin ma'ana ta ilimi mai zurfi.
    Har ila yau ana hade duk wanda ya ce yana nuna kanSa ga halittunSa ranar kiyama,ana hade shi a cikin kafirai22, koda kuwa ya

    ____________
    21- Kamar Yadda Karamiyawa ke fada cewa yana sama.
    22- Asha'irawa sun hukunta cewa Allah Zai nuna Kansa ga bayinSa. A duba littafin Al-Ibana fi Usulid Din na Al- Hasanul Ash'ari Juzu'i na 5 da na 6 da Almilal wan Nihal Juzu'i na 1 shafi na 85-94, da kuma Hashiyyar kastali da aka buga a Hamish sharhin Al-Aka'id na Taftazani shafi na 70 da kuma Allawani'u Ilahiya Shafi na 82-981
    Al-Bagadadi ya kara da cewa: "Ahlussunna sun hadu a kan cewa ranar Alkiyama Muminai za su ga Allah kuma suka ce ya halatta a gan Shi ko ta halin kaka ta hanyar hankali, amma wajabcin ganin Sa ga muminai ranar Alkiyama ya zo ne a hadisasi Littafin Al fark bainal Firak shafi na 335-336.
    In banda Jama'ar da ake kira Mujassama daga cikin Ahlussunna, wadanda suka yi imanin cewa dukkan wadanda za su tashi ranar Kiyama za su gan Shi tamkar yadda ake ganin rana da wata ba tare da giragizai a tsakaninsu. Abinda ake da sabani a kai baki daya shi ne ganin Allah Ta'ala, shi zai yiwu ne tare da tsarkake Shi? Ko kuwa sam ba zai yiwu ba ne sam, tare kuma da tsarkake Shi? Su Asha'irawa sunyi imani da na farko (yiwuwar ganinsa) mu kuma Shi'a mun yi imani da na biyu (rashin yiwuwar ganin sa) muna masu bin maganar Imamanmu (A.S.) na Ahlul Bait.
    A duba Littafin: Kitab Haular Ru'uya na Imam Sharafuddin ya warware wannan al'amari yadda ya kamata ta hanya mai karfi.
    Wannan kuma duk kari ne a kan abinda ya zo na cewa Allah Ya halitta Annabi Adam (A.S.) a kan kama irin tasa, kuma cewa yana da gabobi bayyanannu kamar su yatsu da makyangyama, da kasfa da kuma cewa akwai wata alama a makyangyamarSa da za a gane shi da ita, da kuma cewa zai sanya kafarSa a cikin


    ( 29 )

    kore masa kamantawa da jiki, batun baka ne kawai kuma irin wadannan masu da'awa sun sandare ne kawai a kan wasu laffuza na zahiri na Alkur'ani ne ko kuma wasu hadisai kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su a bayansu. Don haka suka gaza yin aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai suka hukunta da kuma ka'idojin lakabi da kuma aron ma'anar kalma ba.



    ____________
    wutar Jahannama ranar Alkiyama har sai ta ce kad-kad,. Da kuma Manzon (S.A.W.A) zai ga Allah sai ya fadi ya yi sujada. Da kuma cewa Allah zai sauko ranar Kiyama zuwa gurin bayinSa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu. Da kuma cewa muminai za su ga Ubangijinsu ranar Alkiyama kuma ba za su matsatsu ba wajen ganinsa. Da dai irinsu irinsu da yawa. A duba Sahih Bukhari Juzu'i na 8 shafi na 62 da Juzu'i na 9 shafi na 156. Da kuma Sahih Muslim Juzu'i na 4 shafi na 2, 83. Da ibn Majah Juzu'i na 1 shafi na 64, da Musnad Ahmad Juzu'i na 2 shafi na 264 da Muwadda Juzu'i na 1 shafi na 214 Hadisi na 30.


    ( 30 )

    6- Imaninmu Game da Tauhidi.


    Mun yi imani ya wajaba a kadaita Allah ta kowace nahiya, kamar yadda ya wajaba a kadaita Shi a zatinSa haka nan kuma muka yi imani da cewa Shi kadai ne a zatinSa da wajabcin samuwarSa, kazalika Ya wajaba kadaita Shi a siffofi. Wannan kuwa saboda imani ne da cewa siffofinSa ainihin zatinSa ne kuma Shi a ilimi da kudura ba Shi da na biyu a halitta da arzutawa kuma ba Shi da abokin tarayya, a cikin dukkan kamala kuma ba Shi da kwatankwaci.
    Kazalika mun yi imani da kadaita Shi a bauta. Bai halatta a bauta wa waninSa ba ko ta wace fuska, kamar kuma yadda bai halatta ba a hada Shi da wani nau'i na nau'o'in ibada, wajiba ce ko kuma wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma a wasu da ba ita ba na daga ibadoji.
    Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to shi Mushiriki ne kamar kuma wanda yake riya a ibadarsa yana neman kusancin wanin Allah Ta'ala, hukuncinsa shi wanda ya yi haka hukuncin wanda ya bauta wa gumaka ne babu bambanci a tsakaninsu.23

    ____________
    23- Shaikh Muzaffar (R.A.) ya ambata ta a laccarsa ta Falsafar Musulunci cewa: "A bayananmu game da Ubangiji muna bin mataki-mataki ne, muna ketare marhaloli:
    1- Marhala ta farko: a tabbatar da asalin wanda samuwarsa wajibi ne.
    2- Marhala ta Biyu: Bayan tabbatar da asalin wanda samuwarsa wajibi ne ya zamonta abin siffantawa da ainihin samuwa.
    3- Marhala ta uku: bayan mun tabbatar da marhalolin biyu sai mu zarce zuwa kadaitakarSa, domin idan har ya tabbata cewa ainihin samuwa ne to lalle ne

    ( 31 )


    Amma abinda ya shafi ziyatar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau'in neman kusaci ga wanin Allah (ibada) kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi'a Imamiyya suke rayawa suna masu jahiltar hakikanin al'amarin su.24 Sai

    ____________
    ya zamanto shi makadaici ne domin ainihin samuwa makadaici ne idan kuwa ba haka ba zai zama ainihin samuwa ba.
    Sa'annan kuma sai ya ambato dalilin malamai magabata wajen tabbatar da samuwar Allah a takaice kamar haka: "Duniya daya ce don haka mahaliccinta ma lalle ne ya zamanto daya. Akwai dangantaka tsakanin kasancewar mahalicci daya abin halittar ma daya wato duniya ta yadda idan da an kaddara cewa an samu duniyoyi biyu ko da iyayen gijinsu ma sun kasance biyu shi ne fadinsa cewa: Makadaici ba ya samarwa illa makadaici.
    Sa'an nan sai ya yi ishara ga hudubar Imam Ali (A.S.) game da tauhidi da ke cewa "cikar tauhidi shi ne tsarkake aiki gare Shi." Gajeruwar fahinta game da tsarkakewa shi ne tsarkakewa gare Shi a ayyukan ibada, sai dai kuma wannan ba zai dace da abin da ya gabace shi da kuma wanda ya biyo baya ba a maganar.
    Tsarkakewa gare Shi na nufin tsarkake Shi daga dukkan nakasa, da kuma dukan abinda zai soke cewa Shi Wajibin samamme ne, wato tsarkakewa ta fi da'irar tsarkake aikin ibada girma. Don haka tawhidi ko kuma kadaita Allah ba ya zamantowa na hakika har sai ya zamanto ka kadaita Shi ta kowace jiha, a zatinSa, da siffofinSa, da ayyukanSa, da kuma bautarsa, tsarkakewa gare Shi na nufin kadaita Shi ta kowace fuska, da kuma tsarkake Shi daga abokin tarayya ta kowane bangare..."
    A duba littafin Falsafatul Islamiyya; laccocin Shaikh Muzaffar (R.A.) da ya yiwa daliban kwalejin Fikihu a garin Najaf mai Alfarma, darasi na goma shafi 91, da kuma darasi na goma sha daya shafi na 93, da darasi na goma sha hudu shafi na 103.
    24- A nan marubucin yana ishara ne ga irin batutuwan rikitarwar da wasu masu husuma da Shi'a suka tayar kan cewa ziyartar kaburbura haramun ne kuma suka yi ta yayatawa. Suka dogara da wani hadisi da Nisa'i ya ruwaito a cikin littafinsa sunan Nisa'i wanda lafazinsa ya zo kamar haka:
    "Allah Ya la'anci masu ziyartar kaburbura da kuma wadanda suka rike masallatai da kuma gurin kunna fitila." Juzu'i na 4 shafi na 95. Littafin Kanzul Ummal ma ya kawo shi da lafazi iri daya, Juzu'i na 16 shafi na 388 hadisi na 45039, Ibn Majah shi ma ya kawo shi da lafazi sabanin wannan da ke cewa: "Manzon Allah (S.A.W.A.) ya la'ani masu ziyartar kaburbura" Juzu'i na 1 shafi na 502 Babu Ma Ja'a fin Nahyi an Ziyaratun Nisa'il Kubura hadisi na 1574 da 1576. A sarari yake cewa a hadisan biyu akwai sabanin lafazi da kuma rikitarwa lafazin masu ziyarta mata ya bambanta daga lafazin masu yawan ziyarta da ke nufin matukar ziyarta ta


    ( 32 )


    ____________
    kali. Kamar kuma yadda akwai rashin karin da yake Nisa'i ya ambata, bugu da kuma Muhammad Nasiruddin Albani ya ambata wannan hadisin a ciki raunanan hadisai "Silsilatul Ahadisid Dha'ifa Juzu'i na 1 shafi na 258 hadisi na 225 da kuma Ibn Uday a littafi Al- Kamil Fid Dhu'afa Juzu'i na 5 shafi na 1698 ba tare da ya ambata karin da ke akwai a cikin sunani Nisa' i ba.
    Wannan dangane da matanin hadisin ke nan, amma abinda ya shafi Isnad wato hanyar ruwaito hadisin. A cikin Isnadin wannan hadisin akwai Abdul Waris bin Abu Salih a ruwayar Nisa'i da kuma ruwayar Ibin Majah na farko da kuma Abdullah bin Usman da kuma Abdurrahman bin Bahman a ruwayar Ibin Majah ta biyu wadanan maruwaita kuwa za a iya fahintar al'amarinsu kamar haka:
    Abdulwaris bin Sa'id Ibin Haban ya ce shi dan Kadariyya ne. Assaji ya ce dan Kadariyya ne da ake zargi saboda bidi'arsa. Ibin Mu'in ma ya ce: Ya yi imani da kadariyya kuma yana bayyana haka. An ambata wannan ne a cikin littafin Tahzibut Tahzib Juzu'i na 6 shafi na 391-392.
    1 - Abu Salih: Shi ana taraddudi a kansa tsakanin kasancewarsa shi ne Mizanin al-Basari ko kuwa shi Bazam Mawla Ummi Hani. Wanda mafi yawancin malaman sanin maruwaita suka fi ba da karfi a kan shi ne cewa shi Baz Bazam kuwa Ibin Hijir ya fada a cikin Tahzibit Tahzib a Juzuz'i na 1 shafi 364 da 365 cewa game da shi Ahmad ya ce: Ibin Mahdi ya bar hadisin Abu Hatim kuma ya ce: Ana rubuta hadisinsa amma ba a kafa hujja da shi. Nisa'i kuma ya ce: Shi ba amintacce ba ne. Ibin Udayyi ya ce: Ban san wani daya daga cikin magabata da ya yarda da shi ba. Zakariyya bin Abi Za'ida kuma ya ce: Sha'abi ya kasance yana wucewa ta gurin Abi Salih ya kama kunnensa ya ja kana ya ce: kaitonka kana fassara Alkur'ani alhali kai ba ka kiyaye Alkur'ani ba,Ibin Madini kuma daga Kaddani daga Sauri ya ce: Kalbi yace Abu Salih ya ce mini duk hadisin da na fada karya ne. An kuma kawo daga Jawzi daga Azdi cewa ya ce: Makaryaci ne. Wannan abinda Tahzibut'Tahzib ya ambata ke nan kawai. Amma a littafin Silsilatul Ahadisud Dha'ifa " Silsilar Raunanan Hadisai" bayan an ambato hadisin an kuma ba da karfin cewa AbuSalih din shi ne Bazam sai ya ce: "Abu Salih din nan shi ne Mawla Ummi Hani Bint Abi Dalib Kuma sunansa Bazan ne ana kuma ce masa Bazam shi rarrauna ne a gurin kowa da kowa, kuma mai yawan suka ne babu wani da ya amince shi sai dai Ajali shi kadai. Hatta Isma'il Bin Abi Khalid Azdi ma cewa ya yi makaryaci ne wasunsu kuma sun siffata shi da gurbatarwa. Hafiz yace a cikin At-Takrib mai rauni ne mai cudanya hadisi. Shi rarrauna ne a gurin Ibin Mulakkan da kuma Abdul Hak Asbili. Silsilatul Ahadisud Dha'ifa juzu'ina 5 shafi na 275-276.


    ( 33 )


    ____________
    2- Abdullahi Bin Usman: Nisa'i ya ce: Amintacce ne: Wani lokaci kuma ya ce: ba kakkarfa ba ne. Ibin Haban kuma ya ce: ya kasance yana yin kuskure. Abdullah bin Dauraki kuma daga Ibin Mu'in ya ce: Hadisansa ba su da karfi. Ibin Khasim kuma ya ce: Ba mai karfi ba ne. Aliya Binul Madini kuma ya ce: Ibin Khasim ya ce: Ana kiya masa hadisi. Ya ambata haka ne a cikin littafin Tahzibit Tahzib, Juzu'i na 5 shafi na 275-276.
    4- Abdurrahman Bin Bahman: Wannan kuwa game da shi ibin Madini cewa ya yi: Ba mu san shi ba, kamar yadda ya zo a Tahzibit Tahzib, Juzu'i na 6 shafi na 135.
    Wannan shi ne al'amarin sanadin, ko tafarkin wannan hadisi da kuma nassinsa, karin kuma a kan wannan shi ne cewa yana da sabani da hadisai da dama da suka fi shi kyawun matani da karfin isnadi. Ya zo a cikin hadisan da ake kwadaitar da ziyartar kabarin Annabi (S.A.W.A.) wadanda da yawa daga cikinsu a Kanzul Ummal suke: Juzu'i na 15 shafi na 651 Hadisi na 42582 da 42584. Kazalika ya zo a Juzu'i na 5 shafi na 135 hadisi na 12368 da 12373 kamar kuma yadda ya zo a Sunanul Kubra na Baihaki Juzu'i na 5 shafi na 249 Babin ziyaratul Kuburil Lati fi Baki'i Farkad, da kuma Babu Ziyaratil Kuburus Shuhada. Kamar kuma yadda ya zo a Sunani ibin Majah Juzu'i na 1 shafi na 500 Babu Ma Ja'a fi Ziyaratil Kubur da dai sauran littafa da dama wadanda wannan gurin ya yi kadan ya kidaye su.
    Idan ma da a ce mun sallama mun yarda da ingancin wancan hadisin da ya gabata, duk da karonsa da kuma sabawarsa da ya yi da dukkan wadannan hadisan ingantattu, ai wadannan hadisan ana iya daukansu a matsayin shafaffu idan muka lura da maganar Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Na kasance na hana ku ziyartar kaburbura, to ku ziyarce su, domin suna tunatar da ku game da lahira" Kanzul Ummal Juzu'i na 15 shafi na 646 Hadisi na 42555...
    Wannan kuma duk da cewa musulmi baki daya sun yi ittifakin cewa ziyartar kabari abu ne da yake halattacce. Mun ma karfafa cewa mustahabi ne tare kuma da kasancewar al'ada a kan haka tun zamanin Annabi (S.A.W.A.).
    Baihaki ya kawo a cikin littafinsa Sunanul Kubra da waninsa cewa duk wani daren da Manzon Allah (S.A.W.A.) ya kasance a Dakin A'isha yakan fita a karshen dare zuwa makabartar Baki'a yana cewa: "Aminci ya tabbata gare ku gidajen mutane muminai, kuma abinda aka muku alkawari ya zo gare ku." Ya ambata wannan a Juzu'i na 5 shafi na 249. Nisa'i ma ya ambata a littafinsa Sunan a kitabul Jana'iz Babu Ziyaratu Kuburil Mushrikin, da kuma Abu Dawud a littafinsa Sunan a sashen Ziyaratul Kubur Hadisi na 3234 da kuma Ibin Majah a littafinsa sunan a Babin Ziyartar kaburburan Mushirikai cewa Annabi (S.A.W.A.) ya ziyarci kabarin Mahaifiyarsa har ya yi kuka sa'an nan wadanda ke kewaye da shi ma suka yi kuka. Tare kuma da kari a kan cewa akwai hadisai da dama da aka ambata wadanda ke nuna


    ( 34 )

    dai ma wani nau'i ne na kusaci ga Allah Ta'ala ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusaci gare Shi ta hanyar gaishe da marar lafiya, da raka gawa zuwa kabari, da ziyartar 'yan'uwa a addini, da kuma taimakon fakiri.
    Don zuwa gaishe da marar lafiya shi a kan kansa, alal misali, kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusaci ga Allah ta hanyarsa, ba neman kusaci ga marar lafiyar ba ne da zai zamar da aikata shi ya zama bauta ga wanin Allah Ta'ala ko kuma shirka a bautarSa. Kazalika sauran misalan kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda a cikinsu har da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da rakiyar gawa zuwa kabari da kuma ziyartar 'yan'uwa.

    ____________
    cewa Annabi (S.A.W.A.) ya kasance yana koya wa A'isha yadda ake addu'a idan an ziyarci kabari.
    Idan ma har muka kyale duk wadannan muka koma ga hadisin da suka dogara da shi muka yi nazarin sa tare da kawar da kai daga dukkan abubuwan da muka ambata to sam ba za mu sami wata ishara a cikinsa manyan malaman hadisi da malaman fikihu sun hukunta makaruhancin ziyartar kaburbura ne ga mata kawai.Ga nassin abinda Baihaki ya kawo a littafinsa Sunanul Kubra Juzu'i na 4 shafi na 78. Ya ce: "Lalle Fatima 'Yar Annabi (S.A.W.A.) ta kasance tana ziyartar kabarin kawunta Hamza kowace Juma'a tana yin salla tana kuma kuka a gurin... Sa'an nan kuma sai ya ce; kuma mun riga mun ruwaito a hadisi tabbatacce daga Anas bin Malik cewa Manzon Allah (S.A.W.A.) ya wuce wata mata tana kuka a gurin wani kabari tana kuka sai ya ce; " Ki ji tsoron Allah ki yi hakuri" kuma a wannan hadisin babu cewa ya hana ta zuwa Makabarta, sai dai kuma a cikin wannan akwai karfi a kan abinda muka ruwaito daga A'isha sai dai kuma mafi ingancin abinda aka ruwaito a kan hakan hadisa bayyanan, shi ne hadisin Ummu Atiyya da kuma hadisan da suka yi daidai da shi, cewa; idan da su tsarkaka daga rakiyar gawawwaki zuwa makabarta da kuma fita zuwa makabarta da ziyartar kaburbura to da haka ya fi musu dacewa". A nan maganarsa ta kare.
    Hadisin Ummu Atiyya kuwa shi ne " Ta ce an hane mu rakiyar gawawwaki zuwa makabarta, Kuma bai wani nauyaya a kanmu ba." Sunanul Kubra Juzu'i na 4 shafi na 77 kuma ya ce Muslim ma ya ruwaito shi a cikin Sahihi Muslim ta fuskoki biyu daga Hisham. Da kuma Sunanu Ibin Majah Juzu'i na 1 shafi na 502 hadisi na 1577.
    Idan ana bukatar Karin bayani sai a duba littafin `Kashful Irtiyab fi Atba'i Muhammad bin Abdulwahab wanda Sayyid Muhsin Al- Amin Al- Amuli ya rubuta.


    ( 35 )


    Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan addini a matsayin kyawawan ayyuka a shari'a al'amari ne da fannin fikihu ke tabbatar da Shi ba nan ne gurin tabbatar da Shi ba.25
    Manufa ita ce cewa aikata irin wadannan ayyukan ba sa daga cikin shirka a ibada kamar yadda wasu suke rayawa kuma ba ma ana nufin bauta wa Imamai da su ba ne, abin nufin da su kawai shi raya al'amarinsu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin addinin Allah da tare da su "wancan duk wanda ya girmama alamomin addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyakun ibadar zukata." Surar Hajj: 32.


    ____________
    25- Alal misali za mu ambata misali daga sunna da kuma tarihin rayuwar Annabi (S.A.W.A.) da kuma na Zuriyarsa dangane da fifita wadannan irin kyawawan ayyuka. Akwai misalin abinda Bukhari ya ruwaito a Sahihul Bukhari a Babin Fadha'ilil Sahaban Nabi juzu'i na 4 shafi na 204 daga Annabi (S.A.W.A.) "Masu kuka su yi kuka ga Mutum kamar Ja'afar." Kazalika Annabi (S.A.W.A.) ya sunnata kuka ga Hamza ya ce: "Masu kuka su yi kuka ga mutum kamar Hamza". A duba littafin Tabakat na Ibin Sa'ad Juzu'i na 2 shafi na 44 da kuma littafin Magazi na Wakidi Juzu'i na 1 shafi na 317, da Musnad Ahmad Juzu'i na 2 shafi na 40. Nisa'i ma ya ambata shi a cikin littafinsa Sunan a kitabul Jana'iz Babu Ziyarati Kuburil Mushrikin, da kuma Abu Dawud a littafinsa sunan a Ziyaratul Kubur hadisi na 3234 da kuma Ibin Majah a littafin Sunan a Babu Maja'a fi Ziyarati Kuburil mushrikin: Cewa Annabi (S.A.W.A.) ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa ya yi kuka ya sa wadanda ke tare da shi suka yi kuka.
    Kazalika kukan Fatimatuz-Zahra (a.s.)ga mahaifinta, kukan Zainab 'yar Amirul Muminin Aliyu bin Abi Talib (a.s.) ga yayunta Hasan da Husaini (a.s.), Imam Sadik (a.s.) ya ce: Imam Husain (a.s.) ya ce: Ni wanda aka kashe ne don in zama darasi, babu muminin da zai tuna ni face ya yi kuka." [ Littafin Kamiluz Ziyarat shafi na 108] har ila yau kuma ya kara da cewa: Nisawar bakin ciki saboda mu tasbihi ne, himmar yinsa saboda mu kuma ibada ne, boye asirinmu kuma jihadi ne a tafarkin Allah" Biharul Anwar juzu'i na 44 shafi na 278 hadisi na 4.
    Imam Ridha (A.S.) kuma ya ce: "Duk wanda ya tuna masifar da ta same mu ya yi kuka kuma ya sa aka yi kuka idonsa ba zai yi kuka ba ranar da idanduna suke kuka, wanda kuma ya zauna a gurin zaman da ake raya al'amarinmu zuciyarsa ba za ta mutu ba ranar da zukata ke mutuwa". Littafin Amali Saduk Majilisi na 17.


    ( 36 )

    7- Imaninmu Game da SiffofinSa Ta'ala


    Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa Ta'ala akwai wajiban siffofi tabbatattu na Hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi da kudura, da wadata, da irada, nufi, da rayuwa wadanda su kansu su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne kari ne dabam a kan zatinSa. Ainihin samuwarSa ba wani abu ba ne a kan zatinSa, kudurarSa kuma dangane da rayuwarSa, rayuwarSa ita ce kudurarSa, Shi mai kudura ne ta yadda Ya ke rayayye, kuma rayayye ta yadda Yake mai kudura, babu tagwaye tsakanin siffofinSa da samuwarSa, haka nan kuma a sauran siffofinSa na kamala.
    Na'am siffofinSa sun sha bamban a ma'anoninsu da manufofinsu amma ba wai a hakikaninsu da samuwarSa ba saboda idan da sun kasance haka to da lalle Ya kasance an sami wajibabbun samammu da dama kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ba wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.26

    ____________
    26- Shaikh Muzaffar na ishara da wannan da fadinsa cewa: "Amma fadin cewa daukar abu a kaddare wanda ke nufin cewa siffofi ba su da ayyananniyar ma'ana ta zahiri a sarari, mu mun dauki wannan batun da cewa ba sahihi ba ne, domin Allah Ta'ala Ya siffanta kanSa da cewa Shi masani ne, Mai Hikima, Mai kudura. Shi ne tsantsan kudura, da ilimi da rayuwa, domin Shi zati ne wanda ke da kudura da ilimi da rayuwa, sai dai wadannan siffofin sun sha bamban da ma'anar da ake fahinta ga hankali, domin laffuza ba ma'ana guda suke da ita ba, sassabawarsu a ba da surar ma'ana ne kawai, ba sa sassabawa a siffofi a samuwa, da kuma kasancewa a samuwa, kuma babu adadi a daukar ma'ana kamar yadda suka ambata sai dai akwai adadin maanoni da ke hakaito wannan hakika, wannan kuwa ita ce hakika baki dayanta: Amirul Muminin Aliyu bin


    ( 37 )


    Tabbatattun siffofi kamarsu halitta da arzurtawa kuwa, da gabatarwa, da kuma musabbabi duk alal hakika suna komawa ne ga siffa guda ta Hakika, ita ce kasancewarSa mai tafiyar da al'amuran bayinSa. Wannan ita ce siffa guda wadda siffofi da dama ke samuwa daga gare ta gwargwadon tasirori dabam-daban da kuma la'akari iri dabam-daban.
    Amma siffofn da ake kira salbiyya wato korarru wadanda har wa yau ake kiran su siffofn Jalala, siffofi girma, su dukansu suna komawa ne ga siffa korarriya guda, wanda ita ce siffar kore kasancewarSa mai yiwuwar samamme ba wajibin samamme ba, ma'anarsa kore jiki gare Shi, da kore sura, da kore motsi, da kore rashin harka, da kore nauyi, da kore rashin nauyi, da dai sauran makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa.
    Sa'an nan kuma tushen kore kasancewarSa ba wajibin samamme ba-Shi ne kasancewarSa wajibin samamme, wajabcin samuwa kuwa na daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru dai a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah Ta'ala kuwa Shi kadai ne Makadaici ta kowace fuska, babu adadin yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawarwa a hakikaninSa makadaici abin nufi da bukata.
    Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra'ayin cewa siffofin tabbatarwa wadanda suke wajibai ga Allah duk suna komawa ne ga siffofin da suke korarru. Saboda haka ne Siffofin da suke korarru. Saboda Ya yi masa wahala ya fahinci cewa siffofinSa su ne ainihin zatinSa, don haka Ya kintata cewa siffofin subutiyya, tabbatattu wajibai ba sa koruwa ga Allah, duk suna komawa ga korarrun siffofi ne domin kawai Ya natsu da fadin kadaitaikar zati da

    ____________
    Abi Talib (A.S.) ya ce: "Duk wanda ya siffanta Shi to ya sanya Shi, adadi..." Ashe ba ya siffanta shi da siffofi da dama ba ne? Abinda yake nufi Shi ne wanda ya siffanta Shi da siffofi kari a kan zatin ta yadda zai zamanto zati adadi-adadi da kuma adadin masu wanzuwa da dama har ya zamanto ya fita daga kasance wajibin samamme." Laccocin marubacin Al- Falsafatul lslamiyya. Shafi na 102.


    ( 38 )

    rashin yawaitarsa sai kawai ya auka a cikin abinda ya fi shi muni, domin zamar da ainihin zati wanda shi ne samuwa, tsantsan samuwa, wanda ba shi da duk wata nakasa, da kore duk wata mafuskanta da ba ta dace da samamme wajibin samuwa ba, Ya sanya shi Ya aininin ma shi ne rashi kuma ainihin korarre,27 Allah Ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma tuntubewar duga-dugai.

    ____________
    27- A maganar marubucin akwai ishara ga ra'ayin da Shaikh Saduk ya tafi a kai na cewa: "Duk yayin da muka siffanta Allah Ta'ala daga siffofin zatinSa to muna nufin kore kishiyoyinsu ne kawai daga gare Shi Ta'ala. Muna cewa: Allah Ta'ala bai gushe ba Ya na Mai ji, Mai gani, Masani, Mai Hikima, Mai kudura, Madaukaki, Rayayye, Tabbatacce, Makadaici, Wanzazze, wadannan kuma siffofin zatinSa ne.
    Mu ba ma cewa: Shi Azza Wa Jalla bai gushe ba yana mai yawan halitta, mai Aikatawa, Mai so, Mai Nufi, Mai Yarda, Mai ki, Mai Arzurtawa, Mai yawan kyauta, Mai magana, domin wadannan siffofin ayyukanSa ne, su kuma fararru ne bai halatta ba a ce: Allah Ta'ala bai gushe ba ana siffanta shi da su". Littafin Al- I'itikadat shafi na 8.
    Ba boyayye ba ne cewa za a iya danganta koruwa da dama ga al'amari guda, domin ma'anar rayuwa ita ce rashin mutuwa, ma'anar ilimi kuwa shi ne rashin jahilci, ma'anar kudura kuwa koruwar gazawa.... haka nan, wadannan korewar dabam-dabam zai yiwu a danganta su ga Zati Makadaici wato ma'ana dai, Allah Ta'ala wanda ya daukaka ga haka, shi tarin korarru dabam-dabam ne, sa'an nan sai kuma Shaikh Muzaffar ya biyar da batun cewa: "Mu muna girmama Shaikh Saduk, a matsayin mai hadisi, mai ruwaitowa, amma idan ya fadi irin wadannan maganganu to ba za mu karbi ra'ayoyinsa ba. Mu muna nufin mu ce ne hakika ba ta yawaita, ta fuskar kasancewa ne ko kuma ta adadi kawai a manufa domin yawa ko adadi ta fuskar kasantuwa ko kuma manufa ba shi da wata ma'ana. Ra'ayin da muka yi imani da shi shi ne abinda Farabi ya ke fadi da cewa:
    "Shi Masani ne ta inda Yake Mai kudura ta yadda yake rayayye, rayayye kuma ta yadda yake masani... Wadannan siffofin babu yawan adadi tare da su a hakika ne ko kuma ta fuskar manufa.
    Domin fuskar sani ba daban take da fuskar rayuwa ba. Don haka kasancewarsu adadi a fahinta ne kawai abin nufi ne kawai. Kuma ba ma nufin cewa fahintar abin nufi tana nufin ma'ana wanda take fassara hakika, wadda yawanta shi ne kadaitakarta. Mu abinda muke fada shi ne cewa: "Shi masani ne ta yadda yake mai kudura, wadannan kuwa manufofi ne na hakika amma ba wai don cewa suna da samuwarsu ta kai tsaye su ya su ba. Sai dai ma'anar cewa samuwa kanta ita ce ilimin, ita ce kudurar ba wai kudurar kanta samammiya ba ce wadda da wannan samuwar


    ( 39 )


    Kamar kuma yadda mamaki ba zai kare ba ga wanda ke da ra'ayin cewa siffofinSa na subutiyya, tabbatattu, kari ne a kan zatinSa, saboda haka wanzazzu suna da dama kenan, ya kuma wajabta abokan tarayya ke nan ga wajibin samamme, ko kuma kenan ya ce Shi mai hauhawa ne sashe bisa sashe.28
    Sayyyidina Ali Amirul Muminin (A.S.) kuwa Ya ce:
    Cikar Ikhlasi gare Shi kuwa shi ne kore siffofi gare Shi saboda shaidar cewa dukkan abin siffantawa to ba shi ne siffar ba, da kuma shaidar cewa dukkan abin siffantawa ba shi ne siffar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi wanda ya tagwaita Shi kuwa ya zamar da Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi."29

    ____________
    ne, wadda manufarta za ta zama daura da waccan manufar. Saboda haka wadannan siffofin koda yake dai tabbatattu ne da gaske amma a halin kasancewarsu masu yawa ne har ila yau kuma su kadaitaka ne kuma adadin manufofinsu yana bayyana ma'ana ta hakika ne amma dai babu yawaitaka ta fuskar ma'ana. Wannan shi ne kolin al'amari a wannan batu kuma shi ne abinda ya shiga duhu ga tunanin masu maganganun da suka gabata. A duba littafin Falsafatul Islamiyya na Shaikh Muzaffar shafi na 101 zuwa shafi na 102. A kuma duba littafin Tashihul I'itikad na Shaikhul Mufid shafi na 41 da kuma littafin Matarihun Nazar fi sharhil Babil Hadi Ashar na Shaikh Safiyuddin Turaihi fasali na 3 Shafi na 131-162.
    28- Marubucin ya yi karin bayani a kan wannan al'amari kamar haka:-
    a- Cewa siffofi kari ne a kan zati, kuma su ma wajiban samammu ne to wannan maganar Ash'ari yawa ce.
    b- Maganar Karramiyawa kuwa ita ce cewa siffofi kari ne a kan zati sai dai kuma ba lazimai ba ne ga zatin saboda kasancewarsu lazimai zai wajabta kasancewarsu wajiban samammu ya zamanto an samu wajibai da dama.
    29- Nahjul Balagha: Huduba ta 1, maganar Amirul Muminin game da fara halittan sama da kasa da kuma Al- Ihtijaj juzu' i na 2 sha i na 473 hadisi na 113.


    ( 39 )

    8- Imaninmu Game da Adalci.


    Mun yi imani da cewa: Lalle daga cikin siffofin, Allah Ta'ala, As-Subutiyya Kamaliyya wato tabbatattun siffofin kamala akwai cewa Shi, Adali ne ba azzalumi ba, ba Ya karkacewa a hukuncinSa ba Ya tabewa a hukuncinSa, Zai yi sakayya ga masu biyayya, kuma yana gare Shi Ya hukunta masu sabo, ba Ya kallafa wa bayinsa abinda ba za su iya ba, ba zai musu ukuba fiye da abinda suka cancanta ba.30

    ____________
    30- Adalci shi ne sakamako a kan aiki gwargwadon abinda aka cancanta a kansa, zalunci kuwa shi ne hana hakkokin Allah Ta'ala kuwa Adali, Karimi, Mai yawan alheri, Mai bayar da alheri don zabinsa, Mai Jin kai, Ya riga Ya ba da tabbacin yin sakamako a kan ayyuka da kuma musanya al'amari ga wanda ya fara alheri ya wahala Ya kuma yi alkawarin ba da kari daga gare shi. Allah Ta'ala Ya ce: "Wadanda suka kyautata suna da kyakkyawa da kuma kari." Surar Yunus aya ta 26. Wato Ya ba da labarin cewa masu kyautata aiki to yana da kwatankwacinsa goma" wato yana da kwatankwacin abinda ya cancanta a kan haka har rubi goma. "Kuma wanda ya zo da mummuna ba za a sakamta masa ba sai dai gwargwadonsa kuma su ba za a zalunce su ba." Surar An'ami aya ta 160. Wato ma'ana ba za a yi masa sakayya sama da abinda ya cancata ba. Sa'an nan kuma Ya ba da tabbacin yafewa kuma Ya yi alkcawarin gafartawa. Allah Ta'ala ya ce: "Kuma lalle Ubangijinka tabbas ma'abucin ga mutane a kan zaluncinsu ne." Surar Ra'ad aya ta 6. gafatawa Kuma yana cewa: "Allah ba ya gafarta cewa a yi shirka da shi amma Yana gafarta abinda ba wannan ba ga wanda Ya so" Surar Nisa'i aya ta 48.
    Kuma Allah Ta'ala Ya yi umarni da a yi adalci kuma Ya hana yin zalunci. Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle Allah Yana umarni da adalci da kuma kyautatawa." Surar Nahl aya ta 90.
    Da kuma Tashihul I'itikad na Shaikh Mufid shafi na 103.


    Kuma mun yi imani cewa Allah Ta'ala ba Ya barin abu mai kyau matukar ba gwamuwa ya yi da abu wanda shi ne mafi kyau ba kuma ba Ya aikata mummuna saboda Shi Allah Ta'ala Mai kudura ne a kan Ya aikata kyakkyawa Ya bar mummuna tare da kaddara saninSa game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan. Babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi balantana Ya bukaci barin sa, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarSa ballantana Ya aikata shi kuma duk da haka Mai hikima ne babu makawa aikinSa Ya kasance ya dace da hikima kuma daidai gwargwadon tsari mafi kamala.31

    ____________
    31- Mazhabar Ja'afariyya wato Shi'a Isna Ashariyya ta dauki adalci a matsayin jigo daga cikin ginshikan addini sai dai kuma alal hakika shi ba ginshiki ne guda shi kadai mai zaman kansa ba sai dai shi yana kunshe ne a cikin siffofin Allah Ta'ala kuma wajabcin samunsa ya lizimta tattara siffofin kyawu da kamala saboda haka shi dai adalci yana daga cikin al'amuran tauhidi ne. Sai dai kuma su Asha'irawa da suka saba wa Adaliyyawa, wato Mu'utazilawa da kuma `yan Ja'afariyya, Shi'a Isna Ashariyya sai suka musa abu mai kyau da kuma mummuna wadanda hankali ya tabbatar da su. Suka ce babu wani abu mai kyau sai wanda shari'a ta ce mai kyau ne, babu mummuna kuma a sai wanda shari'a ta ce mummuna ne kuma cewa idan da Allah zai dawwamar da mai biyayya a gidan wuta mai sabo kuma a gidan aljanna to wannan ba mummuna ba ne saboda yana jujjuya al'amura ne da ke karkashin mulkinSa kuma kamar yadda Alkur'ani ya ce: "Ba a tambayarSa a kan abinda ya aikata su kuwa ana tambayar su" Surar Anbiya'i aya ta 23. Su kuwa Adaliyyawa kuwa cewa suka yi: Mai yanke hukunci a wannan al'amari shi ne hankali shi kadai dinsa, babu abinda zai shigar da shari'a a cikinsa sai dai karin ta'akidi da kuma shiryarwa. Shi kuma hankali ya kebantu da hukunta kyawun wasu ayyuka da hukumta munin wasu kuma yana hukumta cewa danganta mummunan abu ga Allah abu ne da ba shi da kyau kuma ba zai yiwu ba Allah Ya aikata shi domin Shi Mai hikima ne azabtar da mai biyayya kuwa zalunci ne; zalunci kuwa mummunan abu ne kuma ba zai taba faruwa daga Allah Ta'ala ba.
    Da haka ne suka tabbatar da siffar Adalci ga Allah suka kebance ta da ambato banda sauran siffofn don ishara ga sabani da Asha'ira. Su kuwa Adaliyawa ta hanyar ka'idar kyakkyawa da mummuna kamar yadda suke a hankali sun tabbatar da wasu ka'idoji daga ka'idojin ilimin sanin Allah: Kamar su Ka'idar Tausasawa, da kuma Wajabcin godiva ga wanda ya yi alheri da wata ni'ima, da kuma wajabcin bincike da


    ( 42 )


    Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki -Shi Ya daukaka ga aikatawa- to da al'amarin hakan ba zai zamanto ya rabu da daya daga cikin surorin nan hudu:
    1- Ya kasance Ya jahilci al'amarin bai san cewa mummuna ba ne.
    2- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi amma kuma Ya zamanto Ya aikata shi ala tilas Ya gaza barin aikata shi.
    3- Ko kuma Ya kasance Ya na sane da shi ba a kuma tilasta Shi Ya aikata ba bai kuma gaza kin bari ba amma Ya zamanto Yana bukatar aikatawa.
    4- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi, ba mai aikata shi ala tilas ba, ba kuma mai bukata Ya zama Ya takaita ke nan da aikata shi a bisa sha'awa da wasa da bata lokaci.
    Dukan wadannan surori kuwa sun koru ga Allah Ta'ala, Kuma tabbatar da nakasa gare Shi alhali Shi kuwa zallan kamala ne saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa Shi tsarkakakke ne daga zalunci da kuma aikata abinda yake mummuna.
    Sai dai kuma wani bangare daga cikin musulmi sun halatta wa Allah Ta'ala aikata mummuna,32 sunayenSa sun Tsarkaka, suka halatta cewa zai iya hukunta musu biyayya, Ya kuma shigar da masu


    ____________
    nazari a mu'ujiza, kuma a kan wadannan ka'idojin suka gina al'amari tilasta wa da kuma `yancin zabi da ke daga cikin mafi wahalar matsaloli.
    Domin karin bayani a duba: Aslus Shi'a da kuma Matarihun Nazar na Shaikh Turaihi, Fasali na 4 shafi na 164.
    32- Da dai sauran wadannan da Asha'irawa suka tafi a kai na daga maganganunsu na cewa Allah Ta'ala Ya aikata mummuna da maimaitawarSa na nau'o'in zalunci da shirka da dagawa da ketare haddi da kiyayya da yarda da su ya kuma so su -Allah Ta'ala Ya daukako ga haka, Tsarki ya tabbata gare Shi-, domin kara samun filla-fillan wadannan munanan ra'ayoyi'a duba littafi Nahjul Hak na Allama Hilli shafi na 85, da kuma sharhin Aka'ida da kuma Hashiyar na kistal, shafi na 109-113, da Milal wan Nahal Juzu'i 1 shafi na 85, 91 da kuma Al- Faslu na Ibin Hazm Juzu'i na 3 shafi na 66 da 69 da kuma Sharhit Tajrid na Kurshaji shafi na 373.


    ( 43 )

    sabo aljanna kai hatta katirai ma, kuma suka halatta cewa Yana iya kallafa wa bayinSa abinda Ya fi karfinsu da abinda ba za su iya aikatawa ba amma kuma duk da haka Ya azabtar da su idan har suka bari ba su aikata shi ba. Har ila yau kuma sun halatta zalunci na iya faruwa daga gare Shi da tabewa, da karya da yaudara, kuma Ya aikata aiki ba tare da wata hikimaba, ba da manufa ba, ba da amfani ba, ba da fa'ida ba da hujjar cewa "Ba a tambayar sa a kan abinda yake aikatawa su kuwa ana tambayar su." Surar Anbiya: 23.
    Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, mai Ja'irci, mai wauta ne, mai wasa ne, mai karya ne, mai yaudara ne, Yana aikata mummuna, Yana kuma barin kyakkyawa, Allah Ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa, daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa. Kuma Allah Ta'ala Ya ce: "Kuma Allah ba Ya nufin Zalunci ga bayi." Surar Mumin aya ta 23. "Kuma Allah ba Ya son barna." Surar Bakara: 31 "Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abinda ke tsakaninsu muna Masu wasa ba." Surar Dukhan: 205. "Kuma ban halitta Aljannu da Mutane ba face don su bauta Mini." Surar Zariyat: 56.


    ( 44 )

    9- Imaninmu Game da Wajabta Aiki.


    Mun yi imani cewa Allah Ta'ala ba Ya kallafa wa bayinSa aiki sai bayan Ya tabbatar musu hujja a kansu33 kuma ba Ya kallafa musu sai

    ____________
    33- Lalle ne a san cewa abinda ake nufi da kallafa aiki shine cewa va kallafa aiki ya bukaci wanda ya kallafawa din da ya aikata wani abu mai wahala mai tsanani. Wato ke nan abin dubawa da komawa gare shi a nan shi ne bukata saboda yadda ya zo a cikin fassara ko bayyana ma'ana da kuma fassarar kallafa aiki da cewa shi ne bukatar aiki mai tsanani da wahala daga wanda aka kallafawa. Kazalika Sayyid Sharif Murtadha Alamul Huda ya biyar da magana yana mai gyara batun da cewa: Kallafa aiki ba ya inganta sai bayan kamalar hankali da tabbatar da dalilai:
    "Kuma Shi Allah Ta'ala mafi kammala hankula kuma ya kuma cika sauran sharuda don babu makawa Ya ba da taklifi wannan yana ishara da cewa takalifi ba shi ne sanarwa ba." Malamanmu sun yi bayanai masu yawa game da kallafa aiki tare da ambata fuskoki dabam-daban na abinda ake nufi da takalifi da kuma alakarsa da shi mukallafi wanda aka kallafawa aikin da kuma aikin da aka kallafa masa da siffofi shi wanda aka kallafa wa aikin da kuma manufar shi kansa aikin da kuma yadda za a yi a aiwatar da shi da kuma irin ayyukan da za a yi ya zama an aiwatar da wannan takalifin, da wanda ya kallafa masa wannan aikin, da kuma abubuwan da ya kebanta da su domin ya zamanto ya kyautata aiki ko kuma wadanne abubuwa ne wajiban wannan aikin. Sananne ne cewa wannan bangare yana daga cikin bayanan Irada wadanda suka cancanci himmatuwa ta musamman daga bangaren malaman Akida tare kuma da kebe masa sashe na musamman a sakamakon babban sabanin da ke akwai a kansa a tsakanin malamai da shugabannin mazhaba game da nufin Allah da aka ambata a ayoyin Alkur'ani da kuma alakarsa da al'amuran da Allah bai yarda da su ba da kuma tawilinsu da fuskokin da ba za su rasa matsa wa kai ba ,mafi muhimmanci daga cikinsu kamar aya ta 148 daga surar An'am da ke cewa: "Wadanda suka yi shirka za su ce idan da Allah Ya so da ba mu yi shirka ba, kuma da iyayenmu (ma ba su yi ba) kuma da ba muharamta daga wani abu ba, haka nan wadanda suka kasance kafin su suka yi karya har suka dandani azabarmu, ka ce shin kuna da wani abu na daga ilimi da za ku fito mana da shi? Babu abinda kuke bi face

    ( 45 )

    abinda za su iya aikata shi kuma suke da ikon aikata shi kuma suka san shi domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, wanda ba zai iya


    ____________
    zato ku ba kome ba ne illa kuna dirkaniya kawai." Da kuma aya ta 20 daga surar Zukhruf: "Kuma suka ce idan da mai Rahama Ya so da ba mu bauta musu ba, ba su da wanidalili game da wannan ba sa kome sai dai dirkaniya."
    Da dai ayoyi da dama da ake wahimtar cewa su shafi Iradar mahalicci ne game da abinda halittu ke aikatawa mummuna. Allah Ta'ala Ya daukaka ga yin haka, daukaka mai girma. Daga nan na Shaikh Muzaffar (R.A.) ya ware sashe guda shi kadai domin ya rubuta abinda ya dace a cikinsa game da abinda ya kebantu da matsayin Shi'a Imamiya. Domin Mazhabar Ahlul Bait (A.S.) tana da matsayinta bayyananne wanda ke yin ta'akidi a kan tsarkake Ubangiji da kuma raba Shi da duk wani mummunan abu ko kuma mai kama da mummuna tare da matukar kore cewa Allah Ta'ala ne Ya nufi a yi shirka ko zalunci ko alfasha, ballantana ma aikata shi, ko kuma halatta aikata shi ko umarni da shi domin dukkan wannan zai kai ga saba wa hikimarSa da adalcinSa da falalarSa.
    Abinda Shaikh Mufid (R.A.) ya ambata shi ne sakamako ko kuma amfanin wannan magana inda yake cewa: Allah Ta'ala ba Ya nufin a aikata sai kyakkyawa daga ayyuka, kuma ba Ya so sai kyakkyawa daga ayyuka kuma ba Ya son munanan ayyuka, ba Ya nufa a aikata alfasha, Allah Ya daukaka daukaka mai girma daga abinda mabarnata suke fada Allah yana cewa: "Kuma Allah ba Ya nufin Zalunci ga bayi." Surar Mumin: 31
    "Allah Ya na nufin sauki gare ku ba Ya nufin tsanani gare ku." Surar Bakara: 185
    "Allah Yana nufin Ya yi muku bayani kuma Ya shiryar da ku tafarkin wadanda suka gabace ku." Surar Nisa'i: 26.
    "Allah Yana nufin Ya yafe ku wadanda suke bin sha'auce-sha'auce kuwa suna nufin ku fandare fandarewa mai girma." Surar Nisa'i: 27.
    Allah Ta'ala Ya ce: "Allah Yana nufin Ya saukaka muku kuma shi mutum an halitta shi rarrauna ne." Surar Nisa'i 28.
    Allah Ta'ala Ya bayyana cewa ba Ya nufin tsanani ga bayinSa Yana nufin sauki ne gare su, kuma cewa Yana nufin bayani gare su, ba Ya nufin bata gare su, kuma Yana nufin saukakawa gare su ba ya nufin nauyayawa. Kuma idan har da Allah Ya kasance Shi ne mai nufar su da sabo to ai da wannan ya sabawa nufinSa na yin bayani gare su da saukakewa gare su. Littafin Allah shaida ne a kan sabanin abinda batattu masu kaga karya ga Allah suka tafi a kai. Allah Ya daukaka daga abinda azzalumai, suke fada daukaka mai girma.
    A duba littafin Azzakhira na Sayyid Murtadha Mufid Juzu'i na 5 shafi na 48-51.


    ( 46 )

    ba, da kuma jahilin wanda ilimi bai isa zuwa gare shi ba, ba wai ya ki neman ilimin da ganganci ba.
    Amma shi kuwa Jahili wanda ya ki neman sani da gangan alhali yana da damar samun ilimin hukunce-hukunce da ayyukan ibada to shi ne mai amsa tambaya a gurin Allah Ta'ala, kuma shi za a yiwa ukuba a kan sakacinsa domin wajibi ne a kan kowane mutum ya koyi abinda yake bukata na daga hukunce-hukuncen shari'a.34
    Kuma mun yi imani cewa: Shi Allah Ta'ala babu makawa Ya kallafa wa bayinsa ayyuka Ya kuma sanya musu shari'o'i abinda na amfani da kuma alheri gare su a cikinta domin Ya sanya su a kan hanyoyin alheri da rabo ta dindindin, sa'an nan kuma Ya shirye su zuwa ga abinda Yake shi ne maslaha kuma Ya gargade su game da abinda yake akwai fasadi da barna a cikinsa da kuma cutarwa gare su


    ____________
    34- Abinda ke nuna haka shi ne fadin Allah Ta'ala cewa: "To ku tambayi ma'abuta sani idan har kun kasance ba ku sani ba." Surar Nahli: 31.
    Da kuma fadin Allah Ta'ala da ke cewa: "Don me wata jama'a daga cikinku ba za ta fita domin su nemi ilimi don su fahinci addini kuma su yi gargadi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su ko sa yi taka tsatsan ba." Surar Tauba aya ta 122.
    Kazalika maganar Imam Sadik (A.S.) na yin ishara da haka yayin da aka tambaye shi dangane da maganar Allah Ta'ala da cewa "ka ce: To Allah na da cikakkiyar hujja a kanku" Sai Imam (A.S.) ya ce: "Ranar Alkiyama Allah zai ce wa bawa, bawaNa shin ka kasance masani? Idan ya ce "E" sai Ya ce masa: Shin ka yi aiki da abinda ka sani. Idan kuwa ya ce: Nina kasance Jahili sai ya ce masa: Ashe ba ka koya ba har ka yi aiki: Sai yaja da shi: To wannan ita ce cikakkiyar hujja." Haka ya zo a littafi Amali Shaikh Tusi shafi na 9 Juzu'i na 10/10. Kuma mai Biharul Anwar ya kawo daga gare shi Juzu'i na 2 shafi na 29 hadisi na 10. Da kuma hadisin da aka kawo daga Imam Sadik (A.S.) cewa: "Ku lizimci neman ilimi addinin Allah kada ku zamanto jahilan kauye, domin wanda bai nemi ilimi addinin Allah ba, Allah ba zai dube shi ba ranar Alkiyama kuma ba zai tsarkake masa aiki ba." Alkafi Juzu'i na 1 shafi 24 hadisi na 7.
    Kamar kuma yadda ya zo a "Risalolin" hukunce-hukuncen ibada da ake aiki da su cewa: Wajibi ne akan mukallafi wato balagi ya nemi ilimin al'amuran shakku da na mantuwa wadanda zai yiwa su taso masa, domin kada ya auka cikin saba wa abinda aka kallafa masa idan har bai koya ba. A duba Risalar Sayyid Sistani mai suna Minhajis Salihin Babin Ibada shafi na 13 matsala ta 19.


    ( 47 )

    da kuma mummunan karshe gare su. Koda kuwa Ya san cewa su ba za su bi Shi ba, domin wannan tausasawa ne da kuma rahama ga bayinSa don kasancewarsu sun jahilci mafi yawancin amfanin kansu da hanyoyinsu a nan duniya da kuma lahira. Sun jahilci da yawan abubuwan da za su jawo musu cuta da hasara, Shi kuwa Allah Ta'ala Shi ne Mai Rahama mai Jin kai a ainihin zatinSa, Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa kuma har abada bai rabu daga gare shi.
    Wannan tausasawa kuwa ba za ta gushe ba, don bayinsa sun kasance sun bijire sun ki bin sa, sun ki kayyaduwa da umarce-umarcensa kuma sun ki hanuwa da hane-hanenSa.

    ( 48 )

    10- Imaninmu Game da Hukuncin Allah da
    Kuma Kaddara


    Jama'ar Al- Mujabbira35 sun tafi a kan cewa Allah' Ta'ala shi ne mai aikata ayyukan halittu don haka sai Ya zamanto ke nan Ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma Ya yi musu azaba.
    Sa'an nan kuma Ya tilasta su a kan yin da'a duk da haka kuma Ya ba su lada a kai. Domin su suna cewa: Lalle ayyukansu alal hakika ayyukanSa ne ana dai dangata ayyukan gare su ne kawai don sassautawa domin su ne muhallin ayyukan, asalin wannan kuwa shi ne
    ____________
    35- Daga cikinsu akwai Al- Asha'ira wadanda suke inkarin musabbabi inda suka kayyade musabbabin da cewa Allah Ta'ala ne kawai, suka ce, alal misali wuta ba za ta kona kome ba sai dai kawai al'adar Allah Ta'ala ce ta gudana a kan cewa duk yayin da tutafi suka shafe ta za su kone ba wai don wuta ita ce mai wani shiga cikin al'amarin konawar ba. Don hakan ne suka tafi a kan cewa ayyukan mutane Allah ne Ya halitta su ba tare da wani hannun su bayin a kai ba, wato shi bawa bashi da wani tasiri a kan aikata aiki. A duba littafin Bidayatut Ma'ariful Ilahiyya Juzu'i na 1 shafi na 159 da shafukan da ke biye
    Ba boyayye ba ne ga duk wanda ya bibiyi littafan Mazhabar Ja'fariyya, Shia Imamiya, cewa suna soke akidar Jabru da ke cewa duk abinda mutun ya yi Ubangiji ne Ya sa shi sun yi sabani da Asha'ira da suka yarda da hakan kamar kuma yadda har ila yau su 'yan Mazhabar Ja'fariyya ba su yarda da sallama kome gar bawa ba shi ne mai iko a kan kome da kome sabanin Mu'tazilawa. An ruwaito daga Imam Abi Hasan Aliyu Bin Muhammad Al-Hadi (A.S.) cewa an tambaye shi game da ayyukan mutane inda aka ce masa: Shin Allah ne Ya halitta su? Sai Ya ce: "Ai idan da Shi ne ya halitta su to da bai kore su daga gare Shi ba ai Allah Ta'ala Ya ce lalle Allah ba Shi ba mushirikai haka nan ma ManzonSa." Surar Tauba aya ta 3. Babu abinda yake nufi da rabuwar ba wai daga ainihin halittarsu ba na abin nufi shi ne shirkarsu da munanansu."

    ( 49 )

    kasancewarsu sun yi inkarin musabbabai na dabi'a a tsakanin abubuwa domin sun yi tsammani cewa hakan shi ne ma'anar kasancewar Allah Ta'ala mahalicci da ba Shi da abokin tarayya kuma Shi ne mai sabbabawa na ainihi ba waninSa ba.
    Duk wanda yake fadin irin wannan ra'ayi kuwa to lalle ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa Ya daukaka ga haka.
    Wasu jama'a kuma wato- Mufawwidha36 sun yi imanin cewa Allah Ya sallama ayyuka ne ga halittu, Yajanye kudurarSa da hukuncinSa da kuma kaddarawarSa daga gare su, wato ma'ana danganta ayyuka gare shi Ta'ala yana nufin dangata nakasa gare shi, kuma samammun halittu suna da nasu musabbaban na musamman koda yake dai dukansu suna komawa ne ga musabbabi guda daya na farko wanda shi ne Allah Ta'ala.
    Duk wanda yake fadin wadannan irin maganganu to lalle Ya fitar da Allah daga mulkinSa Ya kuma hadar da Shi a shirka da halittunSa.
    Kuma mun yi Imani muna masu biyayya ga abinda Ya zo daga Imamanmu tsarkakakku da ke cewa al'amari ne tsakanin al'amura biyu kuma tafarki matsakaici a tsakanin maganganun biyu, wanda irin wadancan ma'abuta tsaurin kan suka gaza fahimtarsa wasu suka zurfafa wasu kuma suka yi kwauro, babu wani daga cikin masana ilimi da ma'abuta falsafa da ya fahince shi sai bayan karnoni.37

    ____________
    36- Mufawwadha su ne wadanda suka kare tilasta mutum a kan ayyuka, yawancinsu Mu'utazilawa ne, suka ce ayyuka dai an sallama su gare mu ne babu abinda ke sanya Irada da Izinin Allah Ta'ala a cikin ayyuka. Abinda ya jawo wannan mummunan ra'ayi shi ne gudun danganta sabo da kafirci ga Allah Ta'ala. Al-Tafwidh shi ne kore taka tsantsan a ayyuka ga bayin Allah da kuma halitta musu aikata abinda suka so na daga ayyukan. Wannan magana ce irinta Zindikai da ma'abuta halastarwa.
    37- Shaikh Mufid ya fadi a cikin littafin Tashihul I'itikad cewa: "Hanya matsakaiciya a tsakanin wadannan maganganun biyu wato Aljabru - tilasta aiki- da kuma Tafwidh - sallama ayyuka-. Ma'ana cewa Allah Ta'ala Ya kaddara wa bayinSa ayyuka da Ya sa su aikata su Ya kuma sanya musu iyakoki a kan haka, Ya kuma shata musu zane-zanen, kuma Ya hane su aikata munanan ta hanyar gargadi da tsoratarwa da narko da azabtarwa. Kuma bai kasance Yana ma tilasta su ba ta hanyar barinsu da

    ( 50 )


    Ba abin mamaki ba ne ga wanda ba shi da masaniya game da hikimar Imamai (A.S.) dangane da al'amari tsakanin al'amura biyu ba, da kuma hanya matsakaici ba a maganganun biyu Ya ce wannan batu ne daga cikin al'amuran da masana falsafa a Yammacin Turai na baya bayan nan suka gano alhali kuwa Imamai sun riga su tun kafin karni goma da suka wuce.
    Imam Sadik (A.S.) yayin da yake bayanin hanyar nan matsakaiciya yana cewa: "Babu Jabru, (tilastawa), kuma babu sallamawa ayyuka baki daya sai dai al'amari ne tsakanin al'amuran guda biyu.38
    Wannan ma'ana girmanta na da yawa manufarta kuma na da zurfi. Abin nufi a takaice shi ne cewa: Lalle ayyukanmu a bangare guda ayyuka namu alal hakika kuma mu ne musabbabansu na dabi'a kuma suna karkashin ikonmu da iyawarmu. A daya bangaren kuma su ayyukan kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin ikonSa. Domin Shi ne Mai ba da samuwa Mai samar da ita. Bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana Ya zamanto Ya zalunce mu a kan yi mana ukuba idan har muka saba. Saboda muna da iko da kuma zabi a kan abinda muke aikatawa. Kuma bai sallama mana samar da ayyukanmu ba ballantana Ya zamanto Ya fitar da su daga karkashin ikonSa ba, Shi dai Shi ne Mai halittawa Shi ne kuma mai hukuntawa, Shi ne kuma mai umarni, Shi kuma Mai iko ne a kan kome, kuma a kewaye Yake da bayinSa.39


    ____________
    ikon aikatawa, kuma bai sallama musu ayyuka ba saboda hana su aikata mafi yawa daga cikin su da kuma sanya musu iyaka a kansu, Ya umarce su da masu kyau Ya hana su munana, wannan shi ne bambanci tsakanin tilastawa da kuma sallamawa, Musanafat Shaikhul Mufid. Juzu'i 15.
    38- Al-Kafi Juzu'i na 1 shafi na 160 hadisi na 13 da kuma Al-Ihtijaj Juzu'i na 2 shafi 490, da Littafin Al Tauhid Shafi na 362, da Al- Itikadat na Shaikh Saduk: 10 da Tashihul I'itikad Musanafat na Shaikh Mufid Juzu'i na 5 shafi na 46.
    39- An tambayi Abul Hasan Musa bin Ja'afar (A.S.) dangane da ayyukan bayin Allah, daga wa suke? Sai ya ce: "Ayyukan bayin Allah ba sa wuce dayan uku: Ko dai su kasance daga Allah da kebe, ko kuma su kasance daga gare Shi ta fuskar Yana da hannu a ciki ko kuma su zamanto daga bawa zalla. Idan da sun kasance daga Allah ne zalla to da Shi ne Ya fi cancantar yabo a kan Kyawawansu, da zargi kuma a kan

    ( 51 )


    Ko ta halin kaka dai abinda muka yi imani da shi game da hukuncin Allah da kuma kaddara shi ne cewa sirri ne daga asirran Allah Ta'ala duk wanda ya iya ya fahince Shi yadda ya dace ba tare kwauro ko zurfafawa ba to shi kenan, idan kuwa ba haka ba to ba wajibi ba ne ya kallafa wa kansa cewa sai ya fahimce Shi daidai wa daida, domin kada ya je ya bata akidarsa, kuma ta baci saboda wannan yana daga cikin al'amura masu wahala, har ma sun fi binciken al'amuran falsafa zurfi. Babu mai iya gane su sai `yan kalilan daga cikin mutane wannan shine abinda ya sa da yawa daga cikin ma'abuta ilimin akida suka tabe.40
    Don haka kallafa shi ma ga bayi kallafa abu ne da ya fi karfin mutum wanda yake daidai da sauran mutane. Ya wadatar mutum ya zamanto ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga maganar Imamai tsarkaka, amincin Allah ya tabbata gare su, cewa shi wani al'amari ne tsakanin al'amura guda biyn, babu tilastawa babu kuma sallamawa a cikinsa.
    Kuma shi baya daga cikin jigo daga cikin jiga jigan addini ballantana ya zama kudurcewa da shi wajibi ko ta halin kaka filla-flla daram.


    ____________
    munanansu, yabo da zargi ba zai taba zama ya ta'allaka ga kowa ba. Idan kuwa da daga Allah ne da kuma bawa to da yabo da suka ya zamanto nasa tare idan wadannan biyun sun tabbata ba daidai ba to ya tabbata ke nan ayyuka daga halittu ne, idan Allah ya yi musu ukuba a kan laifinsu da suka aikata to hakkkinsa ne ya yi haka. Idan kuwa ya yafe su shi ma'abucin takawa ne da gafara." Tashihul I'itikad Shaikh Mufid Juzu'i na 5 shafi na 44.
    40- A cikin littafin laccocin Falsafa Shaikh Muzaffar na da wannan ra'ayin mai zurfi da ke cewa:
    "Kowane daya daga cikin Mujabbira wato masu ra'ayin tilasta ayyuka ga bayin Allah, da kuma Mufawwidha, masu ra'ayin sallama ayyuka bai daya ga bayi, sun dubi kwuibi daya ne kawai sun mance da dayan sai dai kuma wajibi ne mutum ya zamanto mai ido biyu ba mai ido daya ba, duk wanda ya duba da kwuibi daya to ya zama mai ido daya yana duban bayar da samuwa ta bangare har ya suranta cewa ana tilasta mutane a kan ayyuka, sa'an kuma idan ya duba kwuibi dayan da mutane ke aikata ayyukansu da zabinsu sai ya suranto cewa an sallama musu ne. Amma kuma idan da kulawar Allah za ta katse mini koda na dan lokaci ne to da na gushe kuma da ayyuka na ma sun gushe ni ina linkaya ne a karkashin mulkinSa.

    ( 52 )

    11- Imaninmu Game da Bada'.


    "Bada" ga mutum: shi ne wani sabon ra'ayi ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra'ayin ba, wato ya canja himmarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi, wannan kuma saboda jahilcine game da amfani da kuma nadama a kan abinda ya riga ya gabata daga gare shi.
    "Bada" da wannan ma'anar ta koru ga Allah Ta'ala. Domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa wannan kuwa ya koru ga Allah Ta'ala Shi'a Imamiyya kuma ba su yarda da shi ba.
    Imam Sadik (Alaihis Salam) Ya ce:
    "Wanda Ya yi da'awar cewa Bada ta auku ga Allah Ta'ala game da wani abu. Bada irin na nadama ta a gurinmu wannan Kafirine a game da Allah mai girma.41 Har ila yau kuma Ya ce: "Wanda ya raya cewa wani abu ya yi Bada ga Allah wanda da Ya kasance bai san shi ba jiya to ni ba ni ba shi".42
    Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kamar nuni da ma'anar "Bada" yadda ta gabata. Kamar yadda ya zo daga Imam Sadik (Alaihis Salam) cewa: "Bada bai taba yiwuwa ga Allah ba kamar yadda ya yiwu gare shi ba a kan Isma'ila dana."43 Don haka ne wadansu marubuta daga cikin bangarorin

    ____________
    41- Kamaluddin shafi na 69.
    42- Kamaliddin shafi na 70.
    43- Al- Tauhid shafi na 336 Hadisi na 10, da Kamaluddin shafi na 69 da kuma Tashihul I'itikada na Shaikh Mufid Juzu'i na 5 shafi na 66. Shaikh Mufid ya kara bayanin hadisin da cewa: "Abinda yake nufi, (Alaihis Salam), shi ne abinda ya


    ( 53 )

    musulmi suka dangata Bada' ga Shi'a Imamiyya don yin suka ga mazhaba da tafarkin Ahlul Bait suka sanya shi ya zama abin kyama ga Shi'a.
    Sahihin al'amari a nan shi ne mu fadi kamar yadda ya fada a Alkur'ani "Allah Yana shafe abinda Ya so kana Yana tabbarwa asalin littafi kuma gare Shi Yake." Surar Ra'ad: aya ta 39.
    Abin nufi shi ne cewa Allah Ta'ala na iya bayyana wai abu a bisa harshen Annabinsa ko waliyinSa ko kuma a zahiri wata maslaha ta sa bayyanawar sa'an nan daga baya kuma Ya shafe shi Ya zama ba abinda ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma'il (A.S.) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S.) ya ga yana yanka shi.44
    Wato kenan ma'anar maganar Imam (Alaihis Salam) sai ta zama kenan cewa: Lalle babu wani abu da ya bayyana ga Allah Ta'ala na daga al'amari a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma'ila dansa domin (Allah) Ya dauke shi (Isma'ila) kafin shi (Imam Sadik (A.S.) domin mutane su san, (cewa) shi (Isma'ila) ba Imami ba ne, a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.45

    ____________
    bayyana daga Allah Ta'ala na kore kisa gare shi, masa sai ya tausasa gare shi wajen kore shi daga gare shi.
    Labarin haka ya zo ga Sadik (Alaihis Salam), an ruwaito daga gare shi cewa har sau biyu sai na roki Allah don ya kore masa kuma ya kore". Abu na iya zama rubutacce da sharadi sai halin al'amarin ya canja.
    44- Allah Ta'ala Ya ce: "Kuma yayin da ya isa aiki tare da shi ya ce: Ya karamin dana ni na gani a mafarki lalle in yanka ka. To ka duba me ka gani. Sai ya ce: "Ya Babana ka aikata abinda aka umarce ka, in Allah Ya so za ka same ni daga masu hakuri. To yayin da suka amince kuma ya kayar da shi a gefen goshinsa. Kuma Muka kiraye shi cewa ya Ibrahim.,Hakika ka gaskata mafarki kuma tamkar haka ne Muke sakamtawa masu kyautatawa. Lalle wannan tabbatacce shi ne babban bala'i bayyananne. Kuma sai Muka musanya shi da abin yanka mai girma." Surar Saffat: 102-107.
    45- Akwai wasu jama'a daga cikin Shi'a - duk da abinda Imamus Sadik (Alaihis Salam) da abubuwan da ya fada dangane da rasuwar dansa da kuma shirya jana'izarsa


    ( 54 )


    Abu da yake da "Bada" a ma'ana kuma shi ne shafe hukunce-hukuncen shari'o'in da suka gabata da shari'ar Annabinmu Muhammadu sallallahu Alaihi wa ahlihi hatta ma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen shi Annabin namu sallallahu Alaihi wa ahlihi.46

    ____________
    da kai shi kabari-suna cewa Isma'il shi ne Imami bayan mahaifinsa Imam Sadik (Alaihis Salam). Wadannan su ne ake kira da `Yan Isma'iliyya, su dabam suke da Shi'a Imamiyya da fadinsu cewa "Imamanci bayan Imam Sadik (Alaihis Salam) ya koma ga babban dansa ne Isma'il kuma suna raya cewa Imam Sadik (Alaihis Salam) shi ne ya ba da nassin haka game da shi tun yana da rai. Kuma sun yi sabani game da Isma'ila. Wasu daga cikinsu suka ce ya rasu tun zamanin Mahaifinsa Imam Sadik - wannan shi ne ya tabbata a tarihi kamar yadda marubucin littatin ke ishara da shi a nan. Su wadannan su ne suke cewa Imamanci ya ci gaba a zuriyar shi Isma'ila na farkonsu kuwa shi ne Muhammad bin Isma'ilu, wasu daga cikinsu kuma suke cewa shi Isma'la bai mutu ba mahaifinsa ya bayyana rasuwarsa don takiyya, gudun kada Abbasiyawa su kashe shi har ma ya sa gwamnan Mansur a Madina Muhammad bin Sulaiman ya halacci mutuwarsa da shirya jana'izarsa da kuma kai shi kabari. Wadanda suka tsaya a kan shi Isma'ila daga cikinsu, ba su ketare shi ba, su ake kira "yan wakafiyya" a zahiri suna kidaya Imamansu bakwai ne daga kan Imam Aliyu bin Abi Talib (Alaihis Salam) zuwa kan shi Isma'ila da suke ce Imami ne. Sashensu kuwa da suke ce dan Isma'il Muhammad shi ma Imami ne suna da Imami goma sha hudu, bakwai na zahiri bakwai kuma na boye, na zahirin sun fara daga kan Imam Aliyu bin Abi Talib (Alaihis Salam) zuwa kan shi Isma'il bakwai boyayyu kuwa sun fara ne daga kan Muhammad bin Isma'il sai dansa Ja'afar As-Sadik, sai dansa Muhammadul Habib, sai kuma Abdullahil Mahdi wanda ya bayyana a Arewacin Afirka daga cikin 'ya'yan Fatima har ya kafa hukumar Fatimiyya.
    A duba littafin: Firakus Shi'a shafi na 67, da kuma Al-Fusulul Mukhtara minal Uyuni wal mahasin shafi na 308, da kuma Asshi'atu Bainal A'sha'ira wal Mu'utazila shafi na 78, da Tarikhul Mazahibi Islamiyya shafi na 54, da al-Milal wan Nihal na Shahrastani Juzu'i na 1 shafi na 149, da kuma al-Farku Bainal Firak shafi na 62.
    46- As- Shaikh Muhammadul Husain Kashiful Gita ya yi bayani game da haka yana cewa: "Shi Bada a duniyar halitta tamkar shafe hukunci da maye gurbinsa da wani ne a duniyar tsara shari'a. Kamar yadda shafe hukunci da maye gurbinsa akwai wasu fa'adoji da asirrai wadanda wusunsa sun fito sarari wadansu na boye kazalika a wajen boyewa da kuma bayyanawa a duniyar halitta. A bisa asasin cewa wani bangare na Bada (Bayyanawa) saboda sanar wa zukatan, ke da sadarwa da madaukakin matsayi ne, wasu abubuwa sa'an nan a kange musu sharudansu ko kuma


    ( 55 )

    12- Imaninmu Game da Hukunce-Hukuncen Addini


    Mun yi imani cewa Allah Ta'ala Ya sanya hukunce-hukunce -wajibai da haram-haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ainihin su ayyukan, abinda maslaharsa ta zama babu makawa sai da ita Ya sanya shi wajibi wanda kuma cutarwar da ke tare da shi ta kai matuka to Ya haramta shi wanda kuwa maslaharsa ta zama da kadan ta rinjayi cutarwarsa to Ya sanya mana shi mustahabi.
    Kazalika ma sauran hukunce-hukuncen, wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarSa ga bayinSa.
    Kuma lalle babu makawa Ya zamanto Yana da hukunci a kan kowani al'amari47, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto

    ____________
    shamakinsu. Alal Misali an nuna wa Annabi Isa (A.S.) cewa wani ango zai mutu ranar da zai shiga dakin amarya amma ba a nuna masa cewa da sharadin rashin sadaka ba ne sai aka yi gamon katar mahaifiyarsa ta yi masa sadaka, shi kuma Annabi Isa (A.S.) ya riga ya sanar da cewa zai mutu a daren shiga dakin amarya sai ya zamanto bai mutu ba. Da aka tambaye shi game da haka sai ya ce: "Mai yiwuwa kun yi masa sadaka ne, sadaka kuwa na iya kare bala'i mummuna." Hakaza da makamantan wannan... Idan da ba don Bada' ba to da babu wata ma'ana ga sadaka da addu'a da ceto, da ma kukan Annabawa da Waliyai da tsananin tsoronsu da taka tsantsan dinsu ga Allah alhali ba su taba saba masa ba ko da gwargwadon kiftawar ido, tsoronsu kawai saboda saninsu ne game da shamakin nan taskantacce wanda babu wani da ya gan shi."
    Littafin Aslus Shi'a wa Usuliha shafi na 314.
    47- "Ba mu bar wani abu ba daga littafi" Surar An'am aya ta 38. Kuma ya zo a hadisi "Babu wani da mutane biyu ke da sabani a kansa face yana da asalinsa a cikin littafin Allah." Usulul Kafi Juzu'i na 1 shafi na 78 hadisi na 6. Har ila yau kuma ya


    ( 56 )

    ba shi da hakikanin hukuncin Allah a kansa koda kuwa tafarkin saninsa a toshe yake gare mu.
    Kuma har ila yau muna cewa lalle yana daga mummunan abu Ya zamanto Ya yi umarni da aikata abinda yake akwai cutarwa a cikinsa, ko kuma Ya hana abinda akwai maslaha a cikinsa.
    Sai dai kuma wasu daga cikin bangarorin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne kawai abinda Allah Ta'ala Ya hana, kyakkyawa kuwa shi ne abinda Ya kyautata kuma Ya yi umarnin a aikata, ba wai ainihin maslaha da cutarwar a ayyukan suke ba, kuma babu kyawu ko rashin kyawu a ainihin zatin.48 Wannan kuwa batu ne da ya saba wa abinda hankali ya wajabta.
    Kazalika sun halatta cewa Allah na iya aikata mummuna Ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma Ya hana abinda yake akwai maslaha a cikinsa. Ya riga Ya gabata cewa wannan irin magana akwai rashin girmamawa a cikinta kwarai. Saboda wannan magana na hukunta danganta jahilci da gazawa ga Allah, Allah Ta'ala Ya daukaka, daukaka mai girma ga barin irin wadannan al'amura.
    A takaice dai: Abinda yake sahihi a akida shi ne mu ce: Shi Allah Ta'ala ba Shi da wata maslaha ko fa'ida a kallafa wajibai da kuma haramta haramtattu sai maslahar da fa'idojin duka suna komawa ne gare mu a dukan ayyuka. Kuma babu wata ma'ana wajen a kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni ko aka hana aikatawa, Allah ba Ya umarni don wasa ba Ya hani haka banza shi kuma mawadaci ne ga barin bukatar bayinSa.


    ____________
    zo cewa: "Babu wani abu da ke faruwa face Allah yana da hukunci a kansa." Biharul Anwar Juzu'i na 93 shafi na 91-93.
    48- Asha'ira na cewa: Kyakkyawa da mummuna al'amura biyu ne da suke daga shari'a kuma hankali ba ya hukunta kyawun daya daga cikinsu ko kuma muninsa, sai dai mai hukunta haka ita ce shari'a kawai duk abinda ta ce mai kyau to shi ke nan shi ne mai kyau wanda kuwa ta munana to shi ne mummuna.
    A duba littafin: Nahjul Hak shafi na 83 da Almilal wal Nihal juzu'i na 1 shafi na 89 da Sharhut Tajrid na Kaushaji: 375.


    ( 57 )

    FASALI NA BIYU ANNABCI



  • Annabci
  • Annabci Tausasawa Ne.
  • Mu'ujizar Annabawa.
  • Ismar Annabawa.
  • Siffofin Annabawa
  • Annabawa da Littafansu.
  • Musulunci
  • Mai Shar'anta Musulunci
  • Alkur'ani Mai Girma
  • Tafarkin Tabbatar da Alkur'ani da Shari'un Magabata.


    ( 58 )


    ( 59 )

    13- Imaninmu Game da Annabci



    Mun yi imani cewa Annabci aiki ne na Allah Ta'ala, wakilci ne na Ubangiji, wanda shi Allah Ta'ala Yake daukar wadanda Ya zaba daga cikin bayinSa salihai da waliyanSa kamilai a `yan Adamtakarsu, Ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abinda yake da amfani da maslaha gare su a duniya da kuma lahira. Tare kuma da nufin tsabtace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi'u da munanan al'adu kuma da koya musu hikima da ilimi da bayyana musu hanyoyin Sa'ada da alheri domin `yan Adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita domin ta daukaka ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da na lahira
    Kuma mun yi imani cewai Lalle ka'idar tausasawa -wanda da sannu za mu yi bayanin ma'anarta nan gaba- ta sanya ya zama babu makawa Allah Ya aiko ManzanninSa domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sokan gyara domin su zamanto wakilan Allah kuma halifofinSa.
    Kamar kuma yadda muka yi imani da cewa Allah Ta'ala bai dora wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko kuma kaddamar da shi ko zaben sa. Ba su da wani zabe a kan haka, sai dai al'amarin haka ga Allah yake domin "Shi ne Ya fi sanin inda zai sa sakonSa." Surar An'am ayata 124. Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, kamar kuma


    ( 60 )

    yadda ba su da wani hukunci a kan abinda ya zo da shi na daga hakunce-hukunce da sunnoni da shari'a.49



    ____________
    49- Imam Aliyu Bin Abi Talib (a.s.) yayin da yake bayani ya siffanta fara halitta sama da kasa da halitta Annabi Adam (A.S.) da kuma ambata Annabawa da aiko su ya fada a hudubarsa cewa: "Kuma Subhanu Ya zabi Annabawa daga cikin `ya'yansa (Adam) Ya karbi alkawarinsu a kan wahayi da kuma amanarsu a kan isar da sako. Yayin da yawancin halittunSa suka canja suka jahilci hakkinSa, suka riki ababan bauta tare da Shi shedanu suka fitsare su daga saninSa, suka yanke su daga bautarSa. Sai Ya aiko musu da ManzanninSa, kuma Ya bibiyar musu da AnnabawanSa domin su sake shiryar su ga alkawarin halittarsu, su tunatar da su mantattun ni'imominSa kuma su kafa musu hujja da isar da sako, su farfado da abubuwan da hankali ya mance, su nuna musu ayoyin kudura, na daga rufin da ke dage a samansu, da shinfidar da ke sanye a karkashinsu da abincin rayuwarsu, da ajalin da ke kare su, da gajiya da ke tsofar da su, da faruwar al'amura dake bibiye da su, kuma Allah bai taba barin bayinSa babu Annabi aikakke ko kuma littafi saukakke ba, ko kuma wata hanya bayyananniya ba. Manzanni da karancin mabiya ba ya sa su gaza ko kuma yawan masu karyatawa gare su, duk wanda ya gabata daga cikinsu kan sanar musu wanda zai zo daga bayansa ko kuma wanda ya zo daga baya ya sanar da wanda ya gabance shi. A kan haka karnoni suka yi ta shudewa, zamunna suka yi ta wucewa, iyaye suka yi ta gabata Annabawa suka yi ta biyowa, har Allah subhanahu ya aiko Muhammadu Rasulullahi, sallallahu Alaihi wa alihi, domin aiwatar da alkawarinSa da cika AnnabcinSa da Ya karbi alkawari a gurin AnnabawanSa wanda sunansa mashahuri ne, haihuwarsa kuma mai girma ce. A lokacin mutanen bayan kasa al'ummu ne a rarrabe, masu ra'ayoyin zukata dabam-dabam, da hanyoyi mabambanta, tsakanin masu kamanta Allah da halittunSa, ko kuma wuce iyaka a sunanSa, ko kuma mai nuni zuwa ga waninSa, sai Allah Ya shirye su da shi daga bata, ya tserar da su da kokarinsa daga jahilci." Nahjul Balagha Huduba ta. 1.


    ( 61 )

    14- Annabci Tausasawa


    Lalle shi mutum halitta ne mai haddodi masu ban al'ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa da dabi'arsa da ruhinsa da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kan kowane daya daga cikin jama'arsa nauo'in zaburar fasadi sun tattara a cikinsa kamar kuma yadda masu zaburarwa zuwa ga alheri da gyara suka tattara a cikinsa ta bangare gudan.
    Allah Ta'ala yana cewa: "Da rayi da abinda Ya daidaita da kuma Ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta." (Surar Shamsi: 7-8) "Lalle shi mutum tabbatacce yana c ikin hasara." Surar Asri: 2, da kuma "Lalle ne shi mutum tabbas yana dagawa. Don kawai ganin ya wadata" Surar Alak: 6-7 "Lalle zuciya tabbas mai umarni da mummuna ce". Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da ke bayyanawa a sarari suna nuni ga irin yadda ran mutum ke kunshe da rauni da kuma sha'awa.
    A bangare na biyu kuma, Allah Ta'ala Ya halitta masa hankali mai shiryarwa tare da shi wanda zai kai shi zuwa ga gyara da kuma guraren alheri da kuma zuciya mai gargadi da ke masa fada kada Ya aikata mummuna da zalunci tare da aibata shi a kan aikata abinda yake mummuna abin zargi.
    Abokin husumar rai da ke cikin zuciya da imani yana tsakanin aron raunanawa ne da kuma hankali. Duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan rauninsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a `yan adamtakarsu, kammalallau a ruhinsu wanda kuwa rauninsa ya rinjaye shi to lalle yana daga cikin masu hasarar matsayi,


    ( 62 )

    masu taraddudi a yan Adamtaka, masu faduwa zuwa matsayin dabbobi.
    Mafi tsanani daga cikin wadannan masu husuma biyu itace tausasawar zuciya da rundunarta. Don haka ne kake ganin yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha'awace-sha'awace da amsa kiran raunin zuciya, "kuma mafi yawan mutane ba za su zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka." Surar Yusuf 103.
    Shi mutum saboda gazawarsa da rashin saninsa game da abubuwan da ke kewaye da shi, da kuma rashin sanin asirran abubuwan da ke kewaye da shi da ma wadanda ke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukan abinda zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, ba kuma zai iya sanin abinda zai kai shi ga samun sa'ada ko ya kai shi ga tsiyacewa ba, sawa'un a kan abinda ya kebatu da shi ne shi kadai ko kuwa wanda ya shafi dan Adam baki daya da kuma al'ummar da ke kewaye da shi. Shi bai gushe yana jahili kuma yana kara jahilci ne ko kuma kara fahintar jahilcinsa ne duk yayin da iliminsa game da dabi'a ko kuma ababan halitta ya kara karuwa. Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kaiwa ga darajar sa'ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya shararriya zuwa ga shiriya domin rundunar hankali ta kara karfafa da haka har ya zamanto mutum zai iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da raunin tausasawar zuciya.
    Yawanci bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara na kara tsananta ne yayin da tausasawar zuciya ke yaudarar sa ta hanyar nuna masa abinda yake mummuna cewa mai kyau ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne ta nuna masa kyawun fandarewarsa, ta rikitar masa hanyar gyara da sa'ada da ni'ima a lokacin da shi ba shi da masaniyar da zai bambance dukan abinda yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna marar amfani ga mai gaggawar kutsawa cikin wannan arangamar ne ta yadda ya sani ko kuma ta inda bai sani ba sai dai wadanda Allah Ya kubutar.


    ( 63 )


    Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukan tafarkunan alheri da amfani da kuma sanin dukan abinda zai amfane shi ko ya cutar da shi a duniya da lahira ballantana kuma jahili; sawa'un al'amari ne da ya kebe shi shi kansa ko kuma ya hada da al'umma da yake zaune a cikinta ne. Ba ya taba kaiwa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi ko da kuwa sun hadu sun yi bincike, koda kuwa sunyi tarurruka da zama dabam-dabam da kuma shawarwari.
    Don haka ne ya zama wajibi Allah Ta'ala Ya aiko da Annabawa da manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. "Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima" (Surar Juma'a: 2). Yana musu gargadi game da abinda ke da cutarwa gare su kuma yana musu albishir game da abinda yake da alheri da gyaruwa da sa'ada a gare su. Tausasawar daga Allah wajibi ne domin tausasawa ga bayinSa na daga cikin tsantsan kamalarSa. Shi mai tausasawa ne ga bayinSa, Mai yawan baiwa, Mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar Ya kwarara kyautarSa da tausasawa to babu makawa Ya zuba tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu nakasa da tawaya a kyautarSa da karimcinSa.
    Ma'anar wajibi a nan ba wai tana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba ne har Ya zama tilas a kansa Ya yi wa wanda Ya yi umarni biyayya! Allah Ya daukaka ga haka, ma'anar wajibi a nan tamkar ma'anar fadin da ake yi ne cewa shi Allah wajibin samamme ne wato ba zai taba koruwa ba ba zai taba yiwuwa a raba shi da samuwa ba.


    ( 64 )

    15- Imaninmu Game da Mu'ujizar Annabawa


    Mun yi imani da ccwa lalle Allah Ta'ala tunda Yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa da kuma Manzo to babu makawa Ya sanar da shi gare su, Ya kuma nuna musu ko wane ne shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasasarSa da kuma kammala rahamarSa.
    Allah Ta'ala Yana cewa: "Manzanni masu bushara da kuma gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a gurin Allah bayan Manzanni kuma Allah Mabuwayi ne Mai hikima." Surar Nisa'i: 165.
    Wannan, kafa hujjar kuwa babu makawa ya ramanto irin wanda ba ya samuwa sai daga mahaliccin halittu, mai sarrafa samammu- wato ya zamanto abin ya dara kudurar dan Adam. Ya sanya shi a hannun shi manzon mai shiryarwa, domin ya zamanto an san shi da shi kuma ya zamanto mai shiryarwa zuwa gare shi wannan dalili da hujja shi ake kira mu'ujiza; wato gagara badau saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam, ya yi gasa da shi ko kuma ya kawa makamancinsa.
    Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu'ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja haka nan babu makawa wannan mu'ujizar ya nuna ta kuma yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa; ballantana kuma sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu'ujizar da ikrarin Annabci daga mai mu'ujizar, saboda kasancewarsa yana da sadarwa ruhi da wanda yake jujjuya halittu.
    Idan wannan ya tabbata ga mutum, bayyanar mu'ujiza wadda ta saba wa al'ada, ya kuma yi da'awar Annabci da sako, to a lokacin sai


    ( 65 )

    ya zamanto abin gaskatawar mutane a kiran da yake yi, tare da yin imani da sakon nasa, da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi Ya yi imani da shi wanda zai ki kuma ya kafirce masa.
    Wannan shi ne abinda ya sa muka ga cewa mu'ujizar kowane Annabi ta dace da ilimi da kuma fasahar zamaninsa. Mu'ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda ke hadiye sihiri da abinda suke yin ba duhunsa saboda kasancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri yayin da sandan ya zo sai dukan abinda suke aikatawa ya baci suka san cewa lalle wannan abu ne da ya fi karfinsu kuma ya dara irin fannin fasaharsu, lalle wannan yana daga cikin abubuwan da, dan Adam ya gaza ya kawo shi kuma kwarewa da ilimi sun dushe a gabansa. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandanka sai ga shi yana hadiddiye abubuwan da suke kirkirawa. Kuma gaskiya ta tabbata abinda suke aikatawa kuma ya baci. Sai aka rinjaye a nan ,sa'annan suka koma suna kaskantattu. Kuma aka kifarda masu sihirin suna sujada." Surar A'araf: 117-120.
    Hakanan mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) ita ce warkar da makafi da masu albaras da kuma raya matattu saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci shi ne fannin fasahar kwarewar da ke tsakanin mutane kuma akwai malamai akwai likitoci da suke su ne manyan bokaye gare su sai iliminsu ya gaza jeruwa da abinda Annabi Isa (A.S.) Ya zo da shi. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra'ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abinda yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai albaras kuma ina raya mamata da izinin Allah kuma ina ba ku labarin abinda kuke ci da wanda kuke taskancewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai." Surar Al- Imran: 49.
    Mu'ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Alkur'ani saboda shi ya zo ne a lokacin ma'abuta ilimin balaga su ne kan gaba a tsakanin mutane inda ya kure su da balagarsa da bayaninsa. Duk da fasaharsu da balagarsu sai da Alkur'ani ya kaskantar da su ya rikitar da su ya


    ( 66 )

    fahintar da su cewa su ba za su iya fito na fito da shi ba don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza kasawa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu.
    Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma idan da mutane da Aljannu za su taru a kan su zoda kwatankwacin wannan Alkur'anin to da ba za su zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe." Surar Isra'i: 88.
    Kalubalantar su da ya yi kan cewa su kawo sura goma suka kasa na tabbbatar da cewa lalle ya gagare su. Allah Ta'ala Yana cewa: "Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah in kun kasance masu gaskiya" Surar Hud: 13
    Sa'an nan kuma ya sake kalubalantar su kan su kawo sura guda kamar sa suka gaza. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abinda muka saukar to ku zo da sura guda kamar sa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya". Surar Bakara: 23
    Allah Ta'ala Yana cewa: "Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya ba Allah in kun kasance masu gaskiya". Surar Yunus: 38.
    Ya sanar da mu yadda suka koma fito na fito da hakora ba da harshe ba Ya sanar da mu cewa shi Alkur' ani wani nau'i ne na mu'ujiza kuma Annabi Muhammad bin Abdullah ya zo da shi ne da kira da kuma da'awar sako. Don haka muka san cewa Manzon Allah (S.A.W.A.) ya zo da gaskiya da hakika kuma shi ma ya gaskata da shi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.



    ( 67 )

    16- Imaninmu Game da Ismar Annabawa


    Kuma mun yi imani da cewa Annabawa ma'asumai ne, ba sa aikata sabo dukkaninsu kazalika Imamai kyakkyawar gaisuwa ta tabbata a gare su. Mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma (rashin aikata sabo) ga Annabawa50ballantana ma Imamai.
    Isma: Ita ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu; da kuma tsarkaka daga mantu

    ____________
    50- A duba sharhin al-Makasid Juzu'i na 5 shafi na 50, da kuma al-Ganiyyatu fi Usuluddin shafi na 161.
    Sayyid Murtadha ya ambata a cikin littatin Tanzihil Anbiya da nassi kamar haka: "Asahabul Hadis da Hashwaiyawa sun halatta wa Annabawa aikata manyan zunubai kafin a ba su Annabci. Daga cikinsu ma har akwai wadanda suka halatta wa Annabawa aikata sabo hatta bayan karbar Annabcin in banda karya a kan al'amuran shari'a, akwai ma wadanda suka halatta karyar amma da sharadin a boyewa ba bayyanawa ba, akwai ma wadanda suka halatta a kowane hali, su Mu'utazilawa kuwa sun haramta cewa Annabawa na aikata sabo babba ko karami kafin annabci da kuma bayan ba su annabcin amma sun halatta aukuwar abinda bai kai karamin zunubi ba gare su kafin annabci da kuma bayan annabcin amma sun yi sabani a kan Shugaban Manzanni Muhammadu (S.A.W.A.) wasu sabi daga cikinsu akwai wadanda suka ce zai iya aikata kananan ayyukan sabo haka nan da gangan, daga cikinsu kuma akwai wadanda suka ce ata tau sam annabawa ba sa taba aikata wani abu da suka san cewa sabo ne sai dai kawai fuskar ba shi wata ma'ana ta dabam. An hakaito daga Nizam da Ja'afar Bin Mubasshir da kuma wasu jama'a da suka bi su a kan cewa aikata sabo daga gare su ba ya yiwuwa sai dai a kan mantuwa da rafkanuwa kuma za a kama su da haka koda kuwa an yafewa al'ummunsu saboda karfin saninsu da kuma martabarsu.

    Tanzihul Anbiya: Gabatarwa.



    ( 68 )
    wa51 , koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba. Sai dai kawai wajibi ne ya zamanto ya tsarkaka hatta daga dukkan abinda ke zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane ko kuma kyalkyala dariya da dai dukkan abinda bai dace a aikata shi ba a tsakanin mutane ba.
    Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi kuwa shi ne idan da har ya halatta Annabi ya aikata sabo ko kuma ya yi kuskure, ko kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare su to kuwa lalle da biyayya gare su a aikin da suka aikata da sabo ko kuskure bai wajaba ba, ko kuma da idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, bilhasali ma dai mun wajabta haka52 ne wannan kuwa abu ne tabbatacce a wajiban addini da kuma a gurin hankali.


    ____________
    51- Ma'anar Isma a luga ita ce: Abu da ke kange mutum daga wani abu wato kamar ya kange shi daga aukuwar wani abu da ba ya so. Akan ce wane ya yi isma da dutse idan ya yi kariya da shi, da haka ne ake kiranta Isma wato fakewa a dutse don kariya da shi, ya zo a Lisanil Arab cewa: "Isma ita ce kariya, a kan ce na kare wani sai ya karu, na yi kariya da Allah idan har ya tsaru daga sabo da tausasawarSa.
    Isma daga Allah Ta'ala kuwa ita ce: Muwafaka da ke kubutar da mutum daga abinda da ya so idan har ya zamanto ya aikata aikin biyayya, kamar yadda muke mika igiya ga mutumin da kogi yake kokarin dulmuyarwa ya kama ya tsira da ita, Allah Ta'ala ya bayyana wannan ma'ana a littafinSa da cewa: "Ku yi riko da igiyar Allah baki daya" Surar Ali Imran: 103. A nan abin nufi da igiyar Allah shi ne addininsa.
    Ya zo daga Imam Zainul Abidin (A.S.) cewa yayin da aka tambaye shi ma'anar ya ce: Shi ne mai riko da igiyar Allah, igiyar Allah kuma shi ne Alkur'ani da Imam, ba sa taba rabuwa har zuwa ranar tashin kiyama, Imam yana shiryarwa ne zuwa ga Alkur'ani shi ma Alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga Imam. Wannan shi ne fadin Allah Ta'ala: "Lalle ne shi wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga wadanda suke su ne mafiya daidai " Surar Isra'i: 9.
    Biharul Anwar Juzu'i na 25 shafi na 194 da kuma farko al-Makalat na Shaikh Mufid Juzu'i na 4 shafi na 34. Da kuma Lisanul Arab Juzu'i na 12 shafi na 403 bayani game "Asama".
    52- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur'ani wadda take kwadaitarwa da a yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana a karkashinsu." Surar Nisa'i: 13. da kuma fadin Allah Ta'ala cewa: "Kuma wanda


    ( 69 )


    Idan kuwa biyayya gare shi bata wajaba ba a kan haka to kuwa wannan ya saba wa annabci wanda babu makawa tana tare da wajabcin da'a dimin da'iman. Idan kuwa ya zamanto duk abinda ya auku daga gare shi muna jin cewa imma daidai ne imma kuskure to bai wajaba a yi masa da'a a kan kome ba, sai fa'idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan kawai Annabin kuma sai ya zama kamar sauran mutane, maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da'iman kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba. Ba ma za a sami kwanciyar hankali ba baki daya game da maganganunsa da ayyukansa.53
    Wannan kuma dalili ne da ke tabbatar da cewa Isma na tare da Imami domin kaddara cewa shi zababbe ne daga Allah Ta'ala don shiryar da mutane a matsayin halifan Annabi. Za mu yi karin bayani a fasali game da Imamah.

    ____________
    ya bi Allah da Manzon to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima gare su," Nisa'i: 69 da kuma fadinsa cewa: "Kuma wanda ya bi Manzon Allah to Lalle ya bi Allah ne" surar Nisa'i: 80 da kuma: "Lalle hakika gare ku daga Manzon Allah akwai kyawawan abin koyi ga duk wanda ke kaunar Allah da ranar Lahira kuma ya ambaci da yawa" Surar Ahzab: 22 da kuma fadin Allah Ta'ala: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa to lalle ya rabbonta da rabo mai girma". Surar Abzab: 71.
    53- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur'ani da ke kwadaitar da biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna da koramu ke gudana a karkashinsu." Nisa'i: 13
    "Kuma wadanda suka yi da'a ga Allah da ManzonSa to wadan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima gare su". Surar Nisa'i: 69.


    ( 70 )

    17- Imaninmu Game da Siffofin Annabi


    Mun yi imani da cewa, Annabi kamar yadda ya wajaba ya zamanto ma'asumi haka nan ya wajaba ya zamanto yana da mafi kamalar siffofin dabi'u da hankali wadanda mafifita sune jarumtaka, da iya tafida jama'a, da shugabanci da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba da babu yadda Annabcin ya zamanto shugabaci a kan dukan halittu kamar kuma yadda ba zai yiwu ya zamanto ya tafi da al'amuran duniya baki daya ba.
    Kazalika wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun dabi'u hatta kafin aiko shi saboda zukata su amintu da shi rayuka kuma su juya zuwa gare shi hatta ma don ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.



    ( 71 )

    18- Imaninmu Game da Annabawa da Littafansu


    Mun yi imani a dunkule da cewa dukkan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da kasancewarsu ma'asumai tsarkakakku. Musanta Annabcinsu kuwa, da zaginsu, da yin izgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda Ya ba da labari game da su da kuma game da gaskiyarsu.54
    Wadanda aka sani daga cikinsu kuwa kuma aka san shari'o'insu kamar Annabi Adam (A.S.) da Annabi Nuhu (A.S.) da Annabi Ibrahim (A.S.) da Annabi Dawud (A.S.) da Annabi Sulaiman (A.S.) da Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) da sauran Annabawan da Alkur'ani ya ambace su a sarari ya wajaba a yi imani da su a ayyane55


    ____________
    54- "Ku ce mun yi imani da Allah da abinda aka saukar gare mu da abinda aka saukar zuwa ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba da Jikoki da abinda aka ba wa Musa da Isa da abinda aka ba wa Annabawa daga Ubangijinsu, ba ma rarrabewa a tsakanin kowa daga cikinsu kuma mu masu sallamawa ne a gare shi." Surar Bakara: 136
    "Amma tabbatattu a cikin ilimi daga cikinsu da muminai, suna imani da abin da aka saukar zuwa gare ka da abinda aka saukar kafin kai kuma suna masu tsai da salla suna ba da zakka suna masu imani da Allah da ranar lahira wadannan za mu ba su lada mai girma" Surar Nisa'i: 162.
    55- Ya zo a ruwayoyi da hadisai cewa adadin Annabawa ya kai dubu dari da ashirin da hudu da dari uku da ashirin da uku daga cikinsu ne, ko kuma dari uku da ashirin da biyar a bisa sabanin ruwaya, su kuma wadannan Annabawan sunan mafi yawansu bai zo a Alkur'ani ba. Allah Ta'ala na cewa: "Kuma lalle hakika mun aika wasu Manzannin kafin kai, daga cikinsu akwai wadanda muka ba ka


    ( 72 )


    ____________
    labarinsu daga cikinsu akwai wadanda ba mu ba ka labarinsu ba" Surar Ghafir: 78.
    Adadin wadanda sunansu yazo a Alkur'ani kuwa ashirin da shida ne kamar haka:-
    1- Annabi Adam (A.S.): sunansa ya zo sau 18 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Lalle Allah ya zabi Adama da Nuhu da zuriyar Ibrahim da zuriyar Imran a kan dukkan talikai." Surar Al- Imran 33, Kamar Kuma yadda ya zo da Kiran Bani Adam sau Bakwai,
    2- Annabi Nuhu (A.S.): sunansa ya zo a Alkur'ani sau 43, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa ya zauna a cikinsu har shekaru dubu babu hamsin" Surar Ankabutu: 14.
    3- Annabi Idris (A.S.): sunansa ya zo sau biyu a Alkur'ani, Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ka ambata Idris a cikin littafi Lalle shi ya kasance mai yawan gaskiya Annabi" Surar Maryam: 56.
    4- Annabi Hudu (A.S.): Sunansa ya zo sau goma a cikin Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala na cewa: "Kuma zuwa ga Adawa dan'uwansu Hudu, ya ce ya mutanena ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa baicin Shi." Surar A'araf: 69 da Surar Hudu: 50.
    5- Annabi Salihu(A.S.): Sunansa ya zo sau tara a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Mun aika wa Samudawa dan'uwansu Salihu ku bauta wa Allah sai suka zamanto bangarori biyu suna husuma." Surar Namli: 45.
    6- Annabi Ibrahim(A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau 69 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Mun aika Ibrahima kuma Muka sanya Annabci da littafi a zuriyarsu..." Surar Hadid: 26.
    7- Annabi Ludu(A.S.): sunansa ya zo a gurare 26 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Ludu tabbas yana daga Manzanni". Surar Saffat: 133.
    8- Annabi Isma'il(A.S.): Ambaton sunansa ya zo a gurare goma sha daya a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba..." Surar Nisa'i: 163.
    9- Alyasa'u(A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau biyu a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Isma'ila da Alyasa'u da Yunusa da Ludu kuma kowanne Mun fifita shi a kan talikai."
    10- Zulkifli(A.S.): An ambace shi sau biyu a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ka ambaci Isma'ila da Alyasa'u da Zulkifli kuma duka suna daga zababbu." Surar Sad: 48.


    ( 73 )


    ____________
    11- Annabi Ilyasu (A.S.): An ambace shi sau biyu a Alkur'ani, Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Ilyasu tabbas na daga cikin manzanni." Surar Saffat: 123.
    12- Annabi Yunus (A.S.): Ambatonsa ya zo sau hudu a Alkur'ani. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Yunusa Tabbas yana daga cikin Manzanni." Surar Saffat: 139.
    12- Ishak (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma mun yi Masa albishir da Ishaka Annabi daga cikin Salihai." Surar Saffat: 112.
    14- Annabi Yakub (A.S.): An ambaci sunansa sau goma sha shida a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "...Kuma Muka yi wahayi ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba da Asbata da Isa..." Surar Nisa'i: 163
    15- Annabi Yusuf (A.S.): Ambatonsa ya zo sau ashirin da bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma daga cikin zuriyarsa akwai Dawuda da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufa da Musa da Haruna kuma haka nan Muke sakamtawa masu kyautatawa." Surar An'am: 84.
    16- Annabi Shu'aib (A.S.): Sunansa ya zo sau goma sha daya a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa:"Kuma ga Madyana dan'uwansu Shuaibu." Surar A'araf: 85, Hud: 84, Ankabut: 36.
    17- Annabi Musa (A.S.): Ambatonsa ya zo sau dari da talatin da shida a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle tabbatacce Mun aiki Musa da ayoyinMu kan cewa ka fitar da al'ummarka daga duffai zuwa ga haske kuma ka tunatar da su game da ranakun Allah lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga dukkan mai hakuri mai yawan godiya." Surar Ibrahim: 5.
    18- Annabi Haruna (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau ashirin a Alkur'ani. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma Muka ba shi Dan'uwansa Haruna Annabi daga rahamarMu." Surar Maryam: 53.
    19- Annabi Dawud (A.S.) Ambatonsa ya zo sau goma sha shida a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimana kuma Mun ba wa Dawuda Zabura." Surar Nisai: 163.
    20- Annabi Sulaiman(A.S.): Ambatonsa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun ba wa Dawuda da Sulaimanu ilimi" Surar Namli: 15.
    21 - Annabi Ayyuba (A.S.): An ambace shi sau hudu a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Ibrahima da Isam'ila da Ishaka da Ya'akuba da Asbata da Isa da Ayyuba." Surar Nisa'i: 163.


    ( 74 )


    ____________
    22- Annabi Zakariyya (A.S.): Ambatonsa ya zo sau bakwai a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Zakariyya da Yahya da Isa da Ilyasu kowane yana daga Salihai" Surar An'am: 85.
    23- Annabi Yahya (A.S.): Sunansa ya zo sau biyar a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Ya Yahya ka riki littafi da karfi kuma Mun ba shi hukunci yana yaro." Surar Maryam: 12.
    24- Annabi Isma'ila Sadikul Wa'ad (A.S.): shi wani Isma'ilan ne dabam banda dan Annabi Ibrahim (A.S.). Game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma ka ambaci Isma'ila a cikin littafi lalle shi ya kasance mai gaskiyar alkawari kuma ya kasance Manzo Annabi." Surar Maryam: 54.
    25- Annabi Isa (A.S.): Sunansa ya zo sau ashirin da shida a Alkur'ani. Game da shi ne Allah Ta'ala Yake cewa: "Lalle abin sani kawai shi ne cewa Al-Masihu Isa dan Maryama Manzon Allah ne kuma KalmarSa. Ya jefa ta zuwa ga Maryama..." Surar Nisa'i: 171.
    26- Annabi Muhammadu (S.A.W.A.): Ambatonsa da sunan Muhammad ya zo sau hudu a Alkur'ani, da Ahmad kuma ya zo sau daya. "Kuma Muhammadu bai kasance ba face Manzo kuma Manzanni sun gabata kafin shi." Surar Al-Imran: I 44.
    Daga cikin Annabawa akwai wadanda aka kawo siffofinsu ba sunayensu ba a Alkur'ani. Allah Ta'ala na cewa: "Shin ba kaga wasu mashawarta ba daga Bani Isra'ila bayan Musa, yayin da suka ce ga wani Annabinsu, nada mana wani sarki mu yi yaki a tafarkin Allah". Surar Bakara: 246.
    Su Manzannin an rarraba su ne an aika su zuwa ga al'ummu dabam daban a zamunna dabam-daban. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun aika Manzo ga kowace al'umma". Surar Nahl: 36.
    Wasu Annabawa da Manzannin kuma an fifita su a kan wasu: Allah Ta'ala Yana cewa: "Wadancan Manzannin Mun fifita wasunsu a kan wasu daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya daukaka sashensu a daraja." Surar Bakara: 253
    "Kuma lalle hakika Mun fitita wasun Annabawa a kan wasu kuma Mun ba wa Dawuda Zabura." Surar Isra'i: 55.
    Mafifita daga cikin Annabawa da Manzanni su ne Ulul Azami su biyar wadanda game da su Allah Ta'ala ke cewa: "Kuma yayin da Muka karba daga Annabawa alkawarinsu da kuma daga gare ka da kuma daga Nuhu da Ibrahima da Musa da Isa Dan Maryama kuma Mun karba daga gare su alkawari mai tsanani." Surar Ahzab: 7.


    ( 75 )

    duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya kuma ya karyata Annabinmu a kebance.
    Kazalika ya wajaba a yi Imani da littafansu da abinda aka saukar musu.
    Attaura da Linjila ko kuma Bebul Tsoho da Sabon Alkawarin da ke hannun mutane a wannan zamanin ya tabbata cewa gurbatattu ne daga ainihin wadanda aka saukar saboda abinda ya auku gare su na daga canje-canje da musanyawa, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S.) saboda wasan da ma'abuta son rai da kwadayi suka yi da su. Bilhasali ma dai yawanci ko kuma ma dukkaninsu mabiya ne suka kaga su; bayan su Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) ba sa nan.

    ____________
    "Don haka ka yi hakuri kamar yadda ma'abuta karfin himma daga Manzanni suka yi hakuri." Surar Ahkaf: 35.
    Kuma sananne ne cewa himmar Annabawa ta sha bamban, ba daya take ba a gurin dukkaninsu kamar yadda Allah Ta'ala ke bayyana haka da cewa: "Kuma lalle hakika mun yi alkawari ga Adam kafin wannan sai ya manta kuma ba Mu sami karfin himma gare shi ba." Surar D.H.: 115.
    Mafificin Annabawa da Manzanni baki daya shi ne cikamakinsu, Annabi Amintacce Muhammad Dan Abdullahi (Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi da zuriyarsa tsarkakku). A duba Biharul Anwar Juzu'i na ll shafi na 77 da kuma Alkhisal. Al- Amali Shaikh Mufid, da Kanzul Ummal, 32276, 32277, 32282, da sauransu, da Tafsirin Al- Mizan Juzu'i na 2, da Mizanil Hikma Juzu'i na 7 da dai sauransu.


    ( 76 )

    19- Imaninmu Game da Musulunci


    Mun yi imani cewa lalle addini a gurin Allah kawai shi ne Musulunci56, kuma shi ne Shari'ar Ubangiji ta gaskiya wadda ita ce Shari'ar karshe kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga alherin Bil Adama, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al'amuran duniya da Lahira, ita ce mafi dacewa duk tsawon zamani, ba ta canjawa ba ta sakewa, kuma matattara ce ga duKkan abinda Dan Adam ke bukata na daga tsarin rayuwar daidaiku da halin zaman jama'a da na siyasa.
    Da yake Shari'ar Musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari'a da za ta zo ta yi gyara ga Dan Adam da ya rigaya ya dulmuye a cikin zalunci da fasadi, don haka babu makawa wata rana ta zo addinin Musulunci ya yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.57
    Idan da an gudanar da Shari'ar Musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da addinin Musulunci ya game tsakanin Bil Adam kuma da alheri ya game su, kuma da sun kai kololuwar abinda Dan Adam ke mafarkinsa na daga jin dadi da daukaka da sa'ada da ginuwa da halin kwarai, kuma da zalunci ya kare a duniya, soyayya da 'yan'uwantaka, kuma da talauci da fatara da miyata sun kare baki daya.

    ____________
    56- Ishara ga Fadin Allah Ta'ala "Lalle addini a gurin Allah shi ne musulunci" Al- Imran: 19. "Kuma duk wanda ya bi wani addini ba musulunci ba za a taba karba masa ba kuma ranar lahira yana daga cikin masu hasara."
    57- "Kuma lalle Mun rubuta a littafi bayan ambato cewa kasa bayiNa Salihai ne masu gadonta." Anbiya'i: 105.


    ( 77 )


    Koda a yau muna ganin halin ban kunya da ketare hakki daga gurin wadanda ke kiran kansu musulmi dalili shi ne kawai cewa ba a aiwatar da musulunci a aikace ba a hakikaninsa tun daga karni na farko - kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummuna hali zuwa wanda ya fi shi muni har zuwa yau din nan da muke ciki. Sai dai kuma ba wai riko da Musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa Musulmi wannan jinkiri ba sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar Musulunci da tozarta dokokinsa da yaduwar zalunci da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki dayansu, Shi'ansu da Ahlussunnansu. Wannan shi ne abinda ya lagarta yunkurin ci gaba, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala'i da halaka har Allah Ta'ala Ya halaka su saboda zunubinsu. Allah Ta'ala Yana cewa:
    "Wannan kuwa domin lalle Allah bai kasance Yana canja wata ni'ima da Ya ni'imtar da ita a kan wasu face sun sauya abinda ke zukatansu ne kuma lalle Allah mai Ji ne masani." Surar Anfal: 53.
    Wannan ita ce sunnar Allah a halittunSa "Cewa lalle tabbas masu laifi ba sa cin nasara." Surar Yunus: 17.
    "Kuma Ubangijinka bai kasance yana halaka Alkaryu saboda wani zalunci ba alhali mutanensu suna masu gyara." Surar Hudu: 117.
    "Kuma haka nan kamun Ubangijin ka yake idan Ya kama Alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai zafi ne mai tsanani." Surar Hudu: 102.
    Ta yaya za a tsammaci addinin musulunci ya daga al'umma daga gadon barcinta alhali kuwa tana da alkalami da tawada ba ta amfani da mafi karanci daga koyarwarsa. Lalle imani da amana, da gaskiya da ikhlasi, tsarkin niyya, da kyautata mu'amala, sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa dan'uwansa musulmi abinda yake sowa kansa da makamantansa duk suna daga asasan addinin Musulunci na sahun farko-farko kuma musulmi sun yi ban kwana da su har muka kare ga halin da muke ciki a yau. Duk lokacin da zamani ya kara nisa sai mu kara jama'a-jama'a dabam-daban da kungiyoyi suna kifuwa a kan



    ( 78 )

    duniya suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra' ayoyi gagara fahimta ko kuma a kan wasu al'amura da ba su dame su ba, suka mance da ainihin addini, suka bar maslaharsu da maslahar jama'a suka shagala da jayayya a kan al'amura kamar su halitta Alkur'ani ko rashin kasancewarsa halittacce, da batun alkawari game da azaba da raja'a, da kuma cewa Aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halitta su ne nan gaba. Makamantan wadannan gardandamin wadanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta wasunsu da ita, babu abinda suke tabbatarwa illa kawai kaucewar musulmi da madaidaicin tafarkin da aka riga aka gyara zuwa ga halaka da karewa.
    Fandarewar ta karu kuma tare da shudewar zamani har ta hada da jahilci da bata, suka dukufa a kan aibobi da bawawwaki a kan al'amura da surkulle da wahamce-wahamce tare kuma da yake - yake, da jayayyar rikitarwa. Wannnan shi ne abinda ya sa suka auka a cikin halakar da ba ta da iyaka. A yau Yammacin Turai babban sanannen makiyin Musulunci har sun iya sun yi mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanuwa yadda har Yammacin Turai din na iya jefa mummunna halin da Allah ne kadai Ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ubangijin ka bai kasance yana halaka Alkaryu saboda wani zalunci ba alhali mutanensu suna masu gyara." Surar Hudu: 117.
    A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita illa su koma ga kawukansu su yi wa kansu hukumci a kan sakacin da suka yi. Su yi yunkurin gyara kansu da zuriyoyi masu zuwa ta hanyar ba su koyarwar addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja'irci a tsakaninsu. Da haka ne kawai za su tsira daga wannan halaka mai girma kuma babu makawa daga bisani a cika kasa da adalci da daidaitawa bayan an cika ta da zalunci munanawa kamar yadda Allah Ta'ala Ya yi alkawari.
    "Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa kasa bayiNa salihai ne masu gadon ta. Lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada." Surar Anbiya'i: 105-106.


    ( 79 )


    Hadisai kuma sun zo da silsila dabam-daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.A.) da kuma Imamai (A.S) cewa Mahadi (A.S) daga 'ya'yan Fatima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da daidaitwa da adalci bayan an cika ta da zalunci da rashin daidai. Karin bayani zai zo filla-filla a sahen "Abinda Muka yi Imani da shi game da Mahadi (A.S.)".
    Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa Musulunci abinda aka lillika masa na daga bidi'a da bata kuma ya tserar da Bil Adama ,ya kubutar da su daga abinda suka kutsa ciki na daga fasadi gama gari da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da koyar var kyawawan dabi'u da ruhin dan Adamtaka. Allah Ta'ala Ya gagagauta bayyanarsa Ya saukake hanyar bayyanarsa.



    ( 80 )

    20- Imaninmu Game da Mai Shara'anta Musulunci.

    Mun yi imani da cewa ma'abucin sakon addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi, kuma shi ne cikamakin Annabawa shugaban Manzanni, kuma mafificinsu baki daya, kamar kuma yadda shi ne shugaban Bil Adama baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci, babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali babu wani kamar shi kuma a kyawawan dabi'u kuma shi yana kan manyan kyawawan dabi'u. Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle shi kana kan manyan halayen kwarai, masu girma." Surar Al- kalam: 4.
    Wannan kuwa tun daga farkon tasowarsa ne har zuwa ranar tashin alkiyama.
    Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ys siffantashi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa:
    "Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mafi tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai, da kuma mabubbugar hikima."
    Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminina (A.S.) yana cewa: "Likita mai zazzagawa da maganinsa, ya shirya kayan aikinsa. Yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa. Ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastun makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo da duwatsu masu tsauri."

    Nahjul Balagha Huduba ta 108.



    ( 82 )

    21- Imaninmu Game da Alkur'ani Mai Girma.



    Mun yi imani cewa Alkur'ani wahayin Ubangiji ne da ya sauko daga Allah a harshen AnnabinSa, akwai bayanin kome da kome a cikinsa; shi ne Mu'ujiza madawwamiya wadda ta gagari bil Adama wajen karawa da ita a fasaha da azanci, abinda ya kunsa na daga hakika da sannai madaukaka. Jirkita ko canji ko karkacewa ba sa shafar sa. Allah Ta' ala Yana cewa:
    "Mu Mu ne Muka saukar da ambato kuma Mu gare shi lalle masu kariya ne". Surar Hijri: 9.
    Alkur'anin da ke hannunmu wanda ake karanta shi a yau shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W.A.), duk kuma wanda ya yi da'awar sabanin wannan to shi mai kage ne, ko mai rikitarwa ko mai kuskure ne dukaninsu kuma ba a kan shiriya suke ba; domin shi Alkur'ani zancen Allah ne wanda: "Karya ba ta zuwa masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa." Surar Fusilat: 42.
    Daga cikin dalilan da ke tabbatar da mu'ujizarsa akwai cewa duk yayin da zamani ya dada tsawo ilimi da fasaha kuma suka dada ci gaba shi yana nan daram a kan abubuwan da yake kaddamarwa da daukarkar manufa da abubuwan da ya kunsa na ra'ayoyi babu wani kuskure da ke bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi kamar kuma yadda ba ya taba kunsar tawaya game da falsafa ta hakika da yakini, sabanin littafan da malamai da manyan masanan falsafa kome matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani. Domin duk yayin da bincike ya ci gaba to yakan bayyana a sarari cewa rarrauna ne ko sabo ne ko kuma kuskure, hatta a gurin manyan masana falsafar kasar Girka kamarsu Sakarot da

    ( 83 )

    Aplato a Arostatle wadanda kowa da kowa daga cikin wadanda suka zo daga bayansu suka musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa.
    Kazalika mun yi imani da mutunta Alkur'ani mai girma da daukaka shi a magana da kuma a aiki. Bai halatta a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda aka dauka cewa yanki ne daga cikinsa da kuma nufin cewa daga cikinsa take.
    Kamar kuma yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ya shafa kalmominsa ko harrufansa. "Babu mai shafa shi sai wadanda suke tsarkakakku". Surar Waki'a: 79.
    Sawa'un sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba ko haila ko jinin biki da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne kUwa sai dai bayan yin alwala ko kuma yin wanka a bisa asasin filla-fillan bayanan da ke cikin littafan fikihu.
    Kazalika bai halatta a kona su ba, bai halatta a wulakanta shi ba, koda ta wace fuska ne kuwa da yake sananne a tsakanin mutane kamar jefarwa, ko sanya masa kazanta, ko shurin sa da kafa , ko sanya shi a guri wulakantacce. Idan da wani zai wulakanta shi da gangan ko tozarta shi da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu to shi ya shiga cikin masu karyata addinin Musulunci da abubuwan tsarkakewarsa, kuma abin hukuntawa ne da ficewa daga addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.


    ( 84 )

    22- Hanyar Tabbatar Da Gaskiyar Addinin
    Musulunci Da Sauran Shari'u Magabata.


    Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin addinin Musulunci za mu iya ja da shi mu tabbatar masa da mu'ujizarsa madawwamiya wato Alkur'ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagarabadau. Kazalika Alkur'ani shi ne hanyar sanya mana yakini mu da kanmu yayin da kokwanto ya fara shigar mu saboda irin tambayoyin da kan tasowa mutum a zuciya kamar yadda babu makawa kowane mutum mai yanci ya fada cikin irin wadannan tambayoyin yayin karfafa akidarsa da tabbatar da ita.
    Dangane da shari'o'in da suka gabata kuwa kamarsu Yahudanci da Kiristanci ba mu da wata hujja kafin amincewarmu da Alkur'ani ko kuma idan muka raba kammu da addinin Musulunci, babu hanyar da za mu bi mu gamsar da kammu ko kuma mu gamsar da mai tambaya, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu'ujiza tasu da ta saura kamar yadda Alkur'ani yake. Abinda mabiyan wadannan addinan ke dauke da shi kuma ana zarginsu a kan daukar da suke yi ko kuma sun sanya hannu a cikinsa. Babu wani abu da ke cikin littafan addinan da suka gabata da ke hannun mutane a wannan zamanin wanda ya dace ya zama mu'ujiza madawwamiya mai karfi da za ta iya yanke hanzari, ko dalili mai gamsarwa kafin a yi imani da Musulunci.
    Sai dai kawai mu musulmi ya inganta ne a gare mu da mu gaskata Annabcin ma'abuta shari'unda suka gabata domin bayan gaskatawarmu da addinin musulunci to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abinda ya zo da shi, kuma a cikin abinda ya zo da shi akwai gaskata Annabcin Annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a

    ( 85 )

    sashen bayani game da abinda muka yi imani da shi game da Annabawa da littafansu.
    Saboda haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari'un da suka gabata, kiristanci da kuma abinda ya gabace shi bayan ya yi imani da Musulunci domin yin imani da shi imani da su ne, imani da shi imani ne da sakonnin da suka gabata da kuma Annabawan da suka shude. Bai wajaba a kan musulmi ya yi bincike game da gaskiyar mu'ujizar Annabawansu, domin abin kaddarawa shi ne cewa shi musulmi ne kuma ya yi imani da su saboda imaninsa da Musulunci kuma ya wadatar.
    Na'am, idan da mutum, zai yi bincike game da addinin Musulunci ya ji cewa bai gamsu ba to lalle ne a kan kamar yadda hankali da kuma wajabcin neman ilimi suka wajabta Ya yi bincike game da addimin kirista domin shi ne addinin karshe kafin musulunci. Kazalika idan ya bincika addinin kirista bai gamsu ba ta sai kuma ya dukufa a kan addinin da ya gabace shi wato Yahudanci... Haka nan dai zai yi ta bincike har sai ya kai ga yakini yana binciken addinan da suka gabata har ya tabbatar da ingancinsa ya yi imani da shi ko kuma rashin ingancinsa ya yi watsi da su baki daya.
    Wato sabanin wanda ya tashi a addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da addininsa ba zai wadatar da shi ba ya bar binciken addinin Nasaranci da kuma addinin Musulunci bilhasali ma aiki da hankali da neman sa wajibi ne a kansa - kamar yadda hankali ya hukunta, haka nan shi ma addinin Kiristanci ba isar masa ba ya zama ya yi imani da Almasihu (A.S.) wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa. Domin Yahudanci da addinin kirista ba su kore shari'ar da za to daga bisani ba; wadda za ta shafe ta, kazalika Annabi (A.S.) bai ce babu Annabi bayan shi ba sabanin haka ma Annabi Isa (A.S.) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma yayin da Isa dan Maryama ya ce Ya Bani Isra'la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abinda ke gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da ke zuwa bayana, sunansa

    ( 86 )

    Ahmad. Sai dai a lokacin da Ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne." Surar Saff: 6.
    Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da addininsu kafin su yi bincike game da shari'ar da ta biyo bayansa wato kamar shari'ar addinin Kirista, da kuma addinin Yahudanci dangane da Musulunci. Wajibi ne kamar yadda yake a bisa dabi'ar hankali su yi bincike game da shari'ar da ta zo daga baya. Idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta a addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankali su ci gaba da bin addininsu na da tare da riko da shi.
    Shi kuwa musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da Musulunci to ba bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci addininsa da kuma wadanda ake da'awa bayansa. Wadanda suka gabata dai a kaddare an san cewa ya yi imani da su don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da ita? Abin kawai da ya hukunta masa game da su shi ne cewa Shari'ar Musulunci ta shafe su don haka bai wajaba a yi aiki da hukunce-hukmcensu ko littafansu ba.
    Wadanda ake da'awarsu daga baya kuwa shi ne saboda cewa Annabin Musulunci Muhammadu (S.A.W.A.) Ya ce: "Babu wani Annabi bayana."58 Kuma shi mai gaskiya ne kuma Amini. "Kuma shi ba ya magana a kan son rai ba wani abu ba ne face wahayi da ake yiwo wahayinsa" Surar Najmi: 3-4.
    Don haka saboda mene ne ba za'a bukaci hujjar da'awar Annabcin da aka yi daga baya ba idan har mai da'awar ya yi da'awa?
    Na'am yana kan musulmi ya yi bincike bayan tsawon lokaci tsakaninsa da wanda ya kawo sakon, a kuma sami Mazhabobi da tafarkuna dabam-daban ya yi bincike ya bi hanyar da ta fi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar wa

    ____________
    58- Sahih Muslim Juzu'i na 3 shafi na 1471 hadisi na 1842 da Musnad Ahmad Juzu'i na 3 shafi na 32, da Mu'ujamul Kabir Juzu'i na 8 shafi na 161 hadisi na 7617 da sunanu Baihaki Juzu'i na 8 shafi na 144 da Amali Shaikh Mufid: 33.


    ( 87 )

    wanda ya kawo sakon Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukkan hukunce hukuncen da shari'a ta zo da su kamar yadda aka saukar.
    Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari'ar da aka saukar kamar yadda take alhali musulmi sun sassaba jama'a-jama'a, sun rarraba, babu salla guda, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai ba hatta a bangaren mu'amala... don haka yaya zai yi? Da wace irin hanya zai yi salla? Da wace irin fuska na daga ra'ayoyi zai yi aikin ibada da mu'amalarsa kamar aure, da saki, da gado da saye da sayarwa da zartar da haddi, da sauransu?
    Kuma sam bai halatta gare shi ya bi ra'ayin iyaye ba ko ya koma ga abinda zuriyarsa da mutanensa ke kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah Ta'ala domin babu wata zazzagawa a nan ba rufa-rufa, babu raragefe babu zurfafawa.
    Na'am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da ke kansa tsakaninsa da Allah. Ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai aibata shi a kan bin ta da aiki da ita ba. Bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah "Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai." Surar Alkiyama: 36.
    "Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne." Surar Kiya 14.
    "Lalle wannan fadakarwa ce don haka wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa." Surar Muzammil: 19.
    Tambaya ta farko da za ta fara taso masa ita ce, shin ya kama tafarkin zuriyar gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Bait, zuriyar gidan Manzo (S.A.W.A.) shin tafarkin Imamiyya "Isna Ashara', masu bin Imamai sha biyu, shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori dabam-daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi daga cikin Mazhabobi hudun nan ne ko kuwa daga wasu

    ( 88 )

    mazhabobi daban daga cikin wannan bangaren? Haka nan dai tambayoyi za su yi ta tasowa ga duk wanda ba ya tunani 'yanci da zabi har ya kai ga gaskiya abar dogaro.
    Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bayani a kan abinda ke biye da ita game da akidar Imamiyya Isna Ashariyya, Masu bin Imamai goma sha biyu.



    ( 89 )

    FASALI NA UKU



    Imaninmu Game Da Imamanci:

  • Ismar Imami
  • Siffofin Imami da Iliminsa
  • Biyayya ga Imamai
  • Son Ahlul Bait, Zuriyar Gidan Manzo
  • Imamai
  • Imamanci Da Nassinsa Yake
  • Adadin Imamai
  • Al- Mahdi
  • Raja'a
  • Takiyya


    ( 90 )


    ( 91 )

    23- Imaminmu Game Da Imamanci


    Mun yi Imani cewa asalin Imamanci na daga cikin jiga-jigan addini59 kuma imani ba ya cika sai da imani da shi kuma bai halatta a

    ____________
    59- Imamanci shi ne jigo na hudu a cikin jiga-jigan musulunci a gurin Mazhabar Ahlul Bait Masu bin Imamai goma sha biyu, wato Shi'a Imamiyya, Imamanci kuma yana bayan Annabci a muhimmanci kuma za'a iya cewa ita ce ka'idar da ke bambance Mazhabar Imamiyya daga sauran Mazhobabi na Musulunci; kuma Imamanci asasi ne na tunani da Mazhabar mabiya Ahlul Baiti suka gina Mazhabarsu a kai.
    Imamanci: a lugga yana nufin shigewar gaban wani mutum domin sauran mutane su bi shi su yi koyi da shi, don haka Imami shi ne wanda mutane suke koyi da shi, mutanen da ke bin sa kuma su ne mamu. Jam'insa kuma shi ne Imamai. Kalmar Imami ta zo a Alkur'ani har sau goma sha biyu gurare dabam-daban. Akwai guraren da ta zo da sigar mufradi ba jam'i ba har sau bakwai a: Surar Bakara aya ta 124 da Surar Hudu: 17 da Surar Hijri aya ta: 79 da Surar Isra'i aya ta: 71 da Surar Furkan aya ta 74 da Surar Yasin aya ta 12, da Surar Ahkaf aya ta 12.
    Sa'an nan kuma akwai guraren da ta zo da sigar jam'i sau biyar wadanda su ne kamar haka: "Surar Taubati:12, Surar Anbiyai aya ta 73, Surar Kasas aya ta 5 da kuma ta 41 da Surar Sajdati aya ta 24".
    Ma'anarsa ta Ka'ida kuwa Imamanci yana nufin: Mukami ne da Ubangiji Allah kan zabi bayinSa ya ba su kamar yadda yake zaben Annabawa, kuma yakan umarci Annabi ya sanar wa al'umma wannan Imamin ya kuma umarci mutane da su yi masa biyayya. Mutane ba su da wani ikon su zaba wa kansu Imami: Allah Ta'ala yana cewa:
    "Kuma Ubangijinka yakan yi halitta kuma Yana zabe su ba su da wani zabi." Surar Kasas: 68.
    Shi Imami ya bambanta da Annabi ne da cewa Annabi ana yi masa wahayi shi kuwa Imami ba a yi masa wahayi, shi Imami yana karbar hukunce-hukunce ne daga Annabi da shiryarwar Ubangiji. Don haka shi Annabi mai isar da sako ne daga Allah


    ( 92 )

    kwaikwayi iyaye a kan haka ba, ko kuma zuriya ko masu tarbiyya kome girmansu da darajarsu kuwa, sai dai ma ya wajaba ne a nemi sani a yi bincike a game da shi kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.
    Alal akalla imani da sauke nauyin da ke kan mukallafi yana daga cikin wajiban shari'a wadanda aka wajabta masa kuma sun dogara ne a kan Imani da su tabbatarwa ko korewa koda kuwa ba jigo ne daga cikin jiga-jigai da a kwaikwayi wani a kansu ba saboda shi kansa ta wannan kwibin wajibi ne a yi imani da shi. Wato ma'ana ta bangaren wajabcin sauke nauyin da ya wajaba a kansa tabbatacce daga Allah Ta'ala da kuma a hankalce; kuma ba dukkansu ne aka san su ta fuskar matabbacin dalili ba don haka babu makawa a koma ga wanda muka san cewa tabbas bin sa zai kai mu ga sauke nauyin da ya wajaba a kanmu, wato mu koma ga Imam ga wanda ya yi Imani da Imam ko kuma wani da ba Imam ba ga wadanda suka yi imani da wanin Imam.
    Kazalika mun yi imani cewa Imamanci tausasawa ne daga Allah kamar Annabci. Don haka babu makawa a kowane zamani ya zamanto , akwai Imami mai wakiltar Annabi a aikinsa na shiryar da bil Adama60 , da dora su a kan abinda yake maslaha a Sa'adar duniya da Lahira kuma biyayyar da Annabi ya cancata daga mutane baki daya shi ma ya

    ____________
    shi kuma Imami mai isarwa ne daga Annabi. Wannan shi ne abinda Mazhabar Ahlul Bait ke nufi da Imamanci.
    Amma a gurin sauran Mazhabobi kuwa Imamanci na nufin shugabanci ne na gaba daya a kan al'amuran addini da al'amuran duniya don Halifantar Annabi (S.A.W.A.) da hukunce hukuncensa a rassan al'amuran ibada. Domin karin bayani a duba littafan luga, da Aslus Shi'a wa Usuliha da Al'aka'iduj Ja'afariyya da Milal Wan Nihal na Shahristani da Sharhil Makasid.
    60- Allah Ta'ala Yana cewa: "Mu Mune Muka aika Manzo mai albishir kuma mai gargadi kuma babu wata al'umma face mai gargadi ya je mata". Surar Fatir: 24.
    Hadisai da dama da ke nuna cewa kasa ba ta taba zama babu Hujja. A duba Usul Kafi Juzu' i na 1 shafi na 136 Babun Annal Aradha la Takhlu minal Hujja, da kuma na 137 Babun Annahu Law Lam yabka fil Ardhi Illa Isnani La kana Ahaduhuma Hujja.


    ( 93 )

    cancata domin tafi da al'amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da kiyayya daga tsakaninsu.
    A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin kuma da ke wajabta aiko da Annabawa da Manzanni ne ainihin wanda ke wajaba ayyana Imami bayan Manzon Allah.
    Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa muke cewa: Lalle Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah Ta'ala a bisa harshen Annabi ko kuma a bisa harshen Imamin da ya gabata; kuma Imamanci ba nadin ko zabin kowa ba ne a tsakanin mutane61, ba wai al'amarinsu

    ____________
    61- Ya riga ya shahara a tsakanin malaman addinin Musulunci game da sanya Imami akwai maganganu biyu da ba su da na uku. Akwai masu cewa Imamanci ra'ayi ne kuma zabin mutane ne ke ayyana shi. Akwai kuma wadanda ke cewa ayyanawa ne daga Allah. Kuskuren ra'ayi na farko abu ne da shi'a Imamiyya suka yi ittifaki a kai domin wajibi ne Imami ya zama Allah ne Ya ayyana shi kuma shi kuma Annabi ya nuna shi ya kuma yi wasici da yi masa biyayya bayansa - wato kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi a Ghadir Khum - sa'annan shi kuma Imamin sai ya yi wasici da biyayya ga mai zuwa bayansa kuma ya sanar da shi, haka nan za a yi ta yi bi da bi. Ko kuma a ga wata Mu'ujiza ta bayyana a hannunsa domin "Isma" Sharadin Imamanci ce kuma tana daga boyayyun al'amura wadda babu wanda ya san ta sai Allah Ta'ala.
    Su kuwa sauran Mazhabobi da ba Imamiyya ba cewa suka yi:
    Imamanci ba a shardanta nadawar Annabi ko alkawartawarsa game da shi ba, yana iya zama ta hanyar yin Mubaya'a, wato shi ne malamai masana halal da haram su yi wa wani mutum guda mubaya'a su sanya shi Imami - wannan kuwa yana ginuwa ne a kan sharadin rashin "Isma" ga shi Imamin kuma ba sharadi ba ne ya zamanto duka kowa da kowa ya yi masa mubaya'a hatta mubaya'ar mutum guda ma tana iya wadatarwa. Idan kuwa har Mubaya'ar ba ta yiwu ba to akwai wata hanyar nada Imamin: Tilastawa da kankanewa, idan Imami ya mutu wani wanda ya cika sharuda ya maye gurbinsa ba tare da an sanya shi ko an yi masa mubaya'a ba ya kuma tilastawa mutane kansa to halifancinsa ya tabbata koda kuwa fasiki ne Jahili, Ja'iri, Azzalumi kuma suka ce bai halatta ba a tsige Imami koda kuwa fasiki ne amma idan da wani da ya fi shi karfi zai zo ya kifar da shugabancinsa ya kuma tilasta kansa a kan mutane to da shi ma ya zama Imami.
    Tambaya a nan ita ce shin hankali yana yarje wa mutum ya bi mazhabar da ke wajabta biyayya ga Imami fasiki, ja'iri, jahili ba don kome ba sai dan kawai shi ne ya fi karfi da kudurar tilasta kansa a kan wasu koda ta hanyar fasikanci da ja'irci?


    ( 94 )

    ba ne da idan suka so za su dasa wanda suke son dasawa ko kuma su ayyana wanda suka son ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan sakaka ba su da Imami bil hasali ma "Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu ne mutuwa irin ta jahiliyya"62 kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W.A.) a hadisi.
    A bisa wannan asasin ba zamani daga zamuna da zai zamanto babu Imami wanda aka wajabta yi masa biyayya ba a cikinsa, wanda kuma Allah ne Ya nada shi, sawa'un mutane sun ki ko ba su ki ba, sawa'un sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sawa'un sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, sawa'un yana hallare ne ko kuwa yana suturce ne daga idandunan mutane - domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W.A.) ya suturtu daga ganin mutane, kamar yadda ya suturtu a cikin kogo wanda game da shi Allah Ta'ala ke cewa: "Idan ma ba ku taimake shi ba to ai Allah Ya riga Ya taimake shi yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa

    ____________
    Kuma bai halatta a cire shi ba sai dai da wanda ya fi shi karfi ya tilasta shi sa'an shi ya zamanto shi ne Imamin? Shin wannan shi ne Imamin da idan mutum ya mutu bai san shi ba ya mutu mutuwar jahiliyya? To wannan Mazhabar ina matsayinta game da maganar Allah Ta'ala cewa: "Shin wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya shi ne ya fi cancantar a bi shi ko kuwa wanda ba ya shiryarwa sai an shiryar da shi, me ya same ku kuke hukunta haka?" Surar Yunus: 35.
    A duba Littafin "Nahjul Hakk wa kashussidki shafi na 168. Da sharhul Makasid na Taftazani Juzu'i na 5 shafi na 233, da At- Tamhid na Bakilani: 168 da Aslus shi'a wa Usuliha 22'da Aka'idi Ja'afariyya: 29.
    62- Al- Kafi Juzu'i na 1 shafi na 377 hadisi na 3 da Al- Mahasin Juzu'i na 1 shafi na 176 hadisi na 273, da Uyuni Akhbarir Ridha (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 58 hadisi na 214 da Kamaluddin shafi na 413 Hadisi na 15, da Al-Gaybatu na Nu'umani shafi na 130 hadisi na 6, da Rijal Al- Kasshi Juzu'i na 2 shafi na 723 hadisi na 799, da Musnad Al- Tayalasi shafi na 259 hadisi na 1913, da Hilliyatul Awliya'u Juzu'i na 3 shafi na 224 da Al- Mu'ujamul Kabir na Tabarini Juzu'i na 10 shafi na 350 hadisi na 10687, da Mustadrakul Hakim Juzu'i na 1/77 da Sharhun Nahjul Balaga na Ibin Abil Hadid Juzu'i na 9 shafi na 155 da Yanabi'ul Muwadda Juzu'i na 3 shafi na 155 da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 5 shafi na 224 da Musnad Ahmad Juzu'i na 4 shafi na 96.


    ( 95 )

    ma'abucinsa kada ka damu lalle Allah na tare da mu, sai Allah Ya saukar da natsuwarSa gare shi Ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah kuma ita ce Madaukakiya kuma lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima" Surar Tauba: 40.
    Ko kuma kamar yadda ya suturtu a wadi63, to haka nan ya inganta Imami ya suturtu kuma babu bambanci tsakanin fakewa mai tsawo da gajera a hankalce.
    Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ga kowace a'luma akwai mai shiryarwa." Surar Ra'ad: 7.
    "Kuma babu wata al'umma face mai gargadi ya zamanto cikinta." Surar Fatir: 24.

    ____________
    63- Wadi shi ne fili tsakanin duwatsu biyu. Wadin da ake nufi a nan shi ne wadin da ake kira "Wadin Abi Talib (A.S.) wanda Bani Hashim da Banu Abdul Mutallibi bin Abdu Manaf, in banda Abu Lahab, suka shiga cikinsa har na tsawo shekaru biyu ko kuma uku yayin da Kuraishawa suka sanya masu fago don kada wani ma ya kai musu abinci. A duk tsawan wannan lokacin sun kasance suna amfani da dukiyan Nana Khadija ne da ta Abu Talib har suka kare. A lokacin ba su kasance suna fita daga wannan wadi ba sai dai lokacin Umura a watan Rajab da kuma lokacin aikin Hajji. A wannan lokacin Aliyu bin Abi Talib (A.S.) shi ne ya kasance yana fita a boye zuwa Makka yana samo musu abinci.
    A duba As- Sahih Fi Siratin Nabi Juzu'i na 2 shafi 108, da Lisanil Arab Juzu'i na 1 shafi na 499.


    ( 96 )

    24- Imaninmu Game da Ismar Imami.


    Mun yi Imani da cewa Imami ma tamkar Annabi wajibi ne ya zama katangagge daga dukka munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da mantuwa ko da ganganci.
    Kazalika wajibi ne ya zama katangagge daga kuskure da mantuwa, da rafkanuwa domin Imamai masu kare shari'a, masu tsayiwa a kanta halinsu tamkar halin Annabi ne. Dalilin kuwa da ya hukunta mana imani da ismar Annabawa haka nan shi ne dalilin da ya hukunta mama imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci64 ba.
    Kuma ba gagararre ba ne ga Allah Ya tare talikai duk cikin abu dai duk jimillah65

    ____________
    64- Idan da ba don sun kasance ma'asumai ba to da ba su cancanci su zamo Halifofin Annabi (S.A.W.A.) domin rashin Ismarsu zai kare a dori a kan dori ne marar iyaka. Domin dalilin bukatar Imami bayan Annabi (S.A.W.A.) shi ne rashin Ismar mutane don haka suke bukatar wanda zai sa su a tafarki madaidaici, idan kuwa mai shiryarwar bai zama Ma'asumi ba to lalle da akwai bukatar wani ba shi ba wanda wannan zai sa a yi ta bi ni in bi ka har abada. Awa'ilul Makalat Shaikh Mufid 37 Tajridul I'itikad: 222.
    65- Dala'ilul J'ijaz 196(2l8), 424 (499) da 428 (502) Diwani Abi Nuwas.


    ( 97 )

    25 - Imaninmu Game da Siffofin Imami


    Mun yi Imani cewa Imami tamkar Annabi shi ma ya wajaba ya zamanto mafificin mutane a siffofin kamala, kamar su jaruntaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al'amura, da hkima da kuma kyawun hali.
    Dalilinmu kuma game da Annabi shi ne ainihin dalilanmu ma game da Imami a game da haka...
    Dangane da Iliminsa kuwa, shi yana samun saninsa da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukkan masaniyarsa ne ta gurin Annabi ko kuma Imamin da ya gabace shi.
    Idan kuwa aka sami wani sabon abu to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhami daga karfin kwanyar da Allah Ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al'amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure kuma ba ya rikirkicewa kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka kuma ba ya bukatar fahintarwar Malamai66; koda yake ilimin nasa na iya karuwa ya kara inganta, wannan shi ne abinda ya sa Annabi (S.A.W.A.) a addu'arsa yake cewa: "Ubangiji ka kara mini ilimi." Yana kunsa fadar Allah "Ka ce Ya Ubangiji Ka kara mini ilimi." Surar Taha.: 114.
    Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayya cewa kowa yana da wata sa'a ayyananniya ko ma awowi da yakan san wani abu shi da kansa ta

    ____________
    66- Domin a bisa dabi'a idan da yana bukatar malami to da malamin nasa ya fishi ilimi a kan abinda ya koya masa don haka sai ya zama tilas ya bi shi a umarnin da ya masa kuma shi kansa malamin yana bukatar malami sai al'amari ya zamanto bi ni in bi marar iyaka. Don haka ne ya zama wajibi Imami ya zaman mafi ilimin zamaninsa.

    ( 98 )

    hanyar kaifin fahimta wanda shi a kan kansa reshe ne na ilhami, saboda abinda Allah Ya sanya masa na karfin yin haka, wannan kudurar ta sha bamban wajen tsanani da raunana, da karuwa da kuma raguwa a bil Adama gwargwadon sabanin daidaikunsu, sai tunanin mutum ya kai ga sani a wancan lokacin ba tare da bukatar ya tsaya ya yi tunani ko kuma tsara mukaddama da hujjoji ba ko kuma koyawar malamai ba, kuma sau da yawa mutum kan sami irin haka sau da yawa a kan kansa a rayuwa.
    Idan kuwa al'amarin haka yake to ya halatta ga mutum ya kai ga madaukakan darajojin kamala a karfin tunaninsa na samun ilhami. Wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da da na yanzu.
    Don haka muke cewa: shi a kan kansa: to lalle karfin ilhami a gurin Imami da ake kira "kuwwal kadsiyya" ya kai ga mafi kololuwar darajar kamala, don haka yana da tsarkakar ruhi da ke daidai da karbar sannai a kowane kokaci ta kowane hali, don haka duk lokacin da ya mai da hankali ga wani abu daga abubuwa yana bukatar ya san shi sai ya san shi da wannan kudurar ta "Kuwwa Kudsiya" ta Ilhami ba tare da jinkirtawa ba ko shirya wasu mukaddimomi ko kuma koyo daga bakin malami, haka abinda yake son sanin zai bayyana gare shi kamar yadda abubuwa ke bayyana a tsaftatacce madubi, babu wani dindimi ko rikitarwa game abinda ya so sanin.
    Wannan kuwa abu ne da yake bayyananne game da tarihim Imamai (A.S.) tamkar Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) ba su yi tarbiyya a hannnu kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwansu shekarun balaga, koda rubutu ba su koya a gurin wani ba, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu ya shiga gurin koyon rubutu ko ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu duk kuwa da cewa kuwa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa67. Kuma ba a taba tambayar wani abu ba face sun ba da

    ____________
    67- Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya ce: "Manzon Allah (S.A. W.A.) ya sanar da ni Babi dubu, kowane Babi daga cikinsu kuma yana bude Babi dubu wato Babi dubu-dubu kenan har sai da na san abinda ya kasance da wanda zai kasance har zuwa ranar tashin Kiyama, kuma na san ilimin bala'o'i da

    ( 99 )

    amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a tabajin kalmar (ban sani ba)68 daga bakinsu ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu.69
    Alhali kuwa ba za ka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba face wadanda ya yi tarbiyya a hannunsu da kuma guraren da ya ciro ruwayoyinsa ko kuma inda ya sami iliminsa daga mashahurai, da kuma cewa ya dakata a kan wasu matsaloli, ko kuma ya yi shakka a kan al'amura da dama kamar dai yadda al'adar mutum take a kowane guri a kowane zamani.

    ____________
    Mutuwa da kuma fasahar magana" Al- Kafi Juzu'i na 1 shafi na 239, Yanabi'ul Muwadda Juzu'i na 1 shafi na 75.
    Kazalika ya kara cewa: "Wallahi idan da na so da na ba wa kowa daga cikinku labarin in da ya fto da inda zai je da dukkan al'amuransa da na yi haka, amma ina jin tsoro ne kada ku kafircewa Manzon Allah (S.A.W.A.) a kaina. Ku sani cewa ni zan sanar da shi ga wani daga cikin kebabbun da aka amince da shi game da haka. Na rantse da wanda ya aiko shi da gaskiya ya kuma zabe shi a kan ba na magana face gaskiya. Kuma tabbas ya sanar mini da wannan duka da kuma mutuwar duk wanda zai mutu da tsiran wanda zai tsira da kuma makomar wannan al'amarin. Bai bar wani abu da ke shiga kaina ba face ya saka mini shi a kunnena ya bayyana mini shi." Nahjul Balaga Huduba ta 175.
    68- Ya zo a hadisi daga Hisham Bin Hakam cewa Imam Sadik (A.S.) ya ce "Lalle Allah Ta'ala ba Ya sanya hujjarsa a bayan kasa a tambaye shi ya ce ban sani ba." Al-Kafi Juzu'i na 1 shafi na 177 karshen hadisi na 1 Tanbihi na 32.
    69- Abu ne da ya shahara daga Amirul Mumini Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) cewa: "Ya ku mutane ku tambaye ni kafn ku rasa ni, na fi sanin hanyoyin sammai fiye da na kasa" Nahjul Balaga Huduba ta 184.


    ( 100 )

    26- Imaninmu Game da Biyayya Ga Imamai.


    Mun yi imani da cewa Imamai su ne "Ulul-Amri" Shugabannin da Allah Ta'ala Ya yi umarni a yi musu biyayya70, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane,7l kuma su ne kofofin Allah kuma tafarkin isa gare Shi, kuma masu shiryarwa zuwa gare Shi.72 Kuma su ne taskar iliminSa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma'ajiyar saninSa,73 don haka su ne aminai ga mazauna bayan kasa kamar kuma

    ____________
    70 - Ishara ga fadar Allah Ta'ala: "Ya ku wadanda suka yi Imani ku bi Allah ku bi Manzo da shugabanni daga cikinku kuma idan kuka yi jayayya a kan wani abu ku mayar da shi ga Allah da Manzo idan kun kasance masu imani da Allah da Ranar Lahira wannan shi ne aiheri kuma mafi kyau." Surar Nisa'i: 59.
    71- Ya zo daga Imam Bakir (A.S.) da kuma Imam Abi Abdullah Sadik (A.S.) cewa sun ce: "Mu mu ne al'umma tsakatsaki, mu mu ne shaidun Allah a kan halittunSa". Al-Kafi Juzu'i na 1 shafi na 146 Hadisi na 2 da na 4 inda ayar nan ta zo "Haka nan muka sanya ku al'umma matsakaiciya domin ku kasance shaidu a kan mutane Manzo kuma ya zama shaida a kanku". Surar Bakara: 143.
    72- Saboda su su ne Imamai na gaskiya, ya zo daga Manzon Allah (S.A.W.A.) ta fuska maruwaita da dama cewa: "Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwar jahiliyya" A duba Abinda Muka Yi imani da shi game da Imamai.
    Ya zo daga Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) cewa: "Lalle idan da Allah Ya so hakika da Ya sanar da bayinSa kansa amma Ya sanya mu kofofinSa, da tafarkinSa, da hanyarSa, da kuma mafuskantarSa da ta nan ne ake zo maSa, duk wadanda suka fandare da shugabancinmu ko kuma suka fifita wani a kanmu to lalle su sun tabe daga kan tafarki." Al Kafi: 192.
    73- Kazalika ya zo daga Imam (A.S.) cewa "Mu mu ne taskokin ilimin Allah, kumu mu ne masu fassarar wahayin Allah, kuma mu mu ne hujjar Allah cikakkiya a kan


    ( 101 )

    yadda suke su ne taurarin amincin mazauna sama. Kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.A.) ya fassara.74
    Kazalika kamar yadda ya fada (S.A.W.A.) : "Lalle misalansu a wannan al'umma kamar jirgin Nuhu ne , wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka."75
    Kamar kuma yadda ya zo a Alkur'ani mai girma , "Sai dai su bayi ne ababan girmamawa. Ba sa zarce shi da magana kuma su da umarninSa masu aiki ne." Surar Anbiya'i :26 - 27.
    Kuma su su ne wadanda Allah Ya tafiyar mmsu da datti Ya tsarkake su Sosai76: Bil hasali ma mun yi Imani da cewa umarninsu umarnin

    ____________
    wadanda ke koma bayan sama, da wanda ke doron kasa." Al-Kafi: Juzu'i na 1 shafi na 192.
    Kazalika ya zo daga Imam Sadik (A.S.) cewa: "Mu mu ne Shugabanni a kan al'amuran Allah, kuma taskar ilimin Allah kuma ma'ajiyar wahayin Allah" Al- Kafi Juzu'i 1 shafi na 192.
    74- A duba Sahifatul Imam- Ridha (A.S.) shafi na 47 hadisi na 67, da kuma Uyuni Akhbarir Ridha (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 27 hadisi na 14, da Ilalis Sharai'i Shafi na 123 Hadisi na 1 da Kamaluddin Juzu'i na 1 shafi na 205 hadisi na 19 da Fadha'ilu Ahmad: Shafi na 189 Hadisi na 267 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 7 shafi na 25 Hadisi na 6260 , Matalibul Aliya Juzu'i na 4 shafi na 74 Hadisi na 4002, da Ihya'ul Mayyit Bi Fadha'ili Ahlul Bait na Suyuti, Shafi na 42 hadisi na 21, da Zakha'irul Ukba shafi na 17, Fara'idus Sumtain Juzu' i na 2 shafi na 241 hadisi na 515, da Kanzul Ummal Juzu'i na 12 shafi na 101 Hadisi na 34188, da Mustadrak na Hakim Juzu'i na 3 shafi na 149, da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 9 hadisi na 174, da Sawa'ikul Muhrika shafi na 234.
    75- Malaman tafsiri sun yi ittifaki kuma an ruwaito daga Imaman Ahlul Bait (A.S.) da kuma sahabbai da dama cewa fadar Allah Ta'ala: "Abin sani kawai shi ne cewa Allah Yana nufin kawai Ya tafiyar muku da datti ne Ya ku Mutanen gida kuma Ya tsarkake ku sosai " Surar Ahzab: 33.
    76- Cewa wannan ayar ta sauka ne game da Manzon Allah (S.A.W.A.) da Aliyu (A.S.) da Fatima (A.S.) da Hasan (A.S.) da Husain (A.S.) kuma wannan shi ne abinda marubucin littafin ya yi ishara da shi.
    Domin karin bayani a duba: Nahjul Hakk shafi na 173, da Shawahidut Tanzil na Haskani Juzu'i na 2 shafi na 10 Hadisi na 192, da Durrul Mansur Juzu'i na 5 shafi na 198, da Mushki Lil Asar Juzu'i na 1 shafi na 332, da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 9


    ( 102 )

    Allah Ta'ala ne, biyayya gare su biyayya ce gare Shi, saba musu kuma saba Masa ne, kuma soyayya gare su soyayya ce gare Shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi.77
    Bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne.78
    Don haka Ya wajaba mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu da riko da maganganunsu.
    Saboda haka: Mu mun yi imani cewa hukunce-hukuncen Shari'ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai dai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta sai dai daga gurinsu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun kwanciyar hankalin cewa ya ba da wajibin da aka dora masa face ta hanyarsu.79

    ____________
    shafi na 121; da Musnad Ahmad Bin Hanbal Juzu'i na 1 shafi na 330 da Juzu'i na 4 shafi na 107 da Juzu'i na 6 shafi na 292, da Sawa'ikul Muhrika shafi 85, da Tafsirut Tabari Juzu'i na 22 shafi na 5 da Usudul Ghabati Juzu'i na 4 shafi na 29, da Khasa'isun Nisa' i Shafi na 4, da Al-Gadir Juzu'i na 1 shafi na 49 da Juzu'i na 3 shafi na 195 da Juzu'i na 5 shafi na 416 da Ihkakul Hakk Juzu'i na 2 Shafi na 501-553 da kuma Juzu'i na 5 shafi na 54, 55, 58 da kuma Juzu'i na 9/69-1 da Juzu'i na 18 shaf na 359-383, da Dala'ius Sidki Juzu'i na 2 sahfi na 103, da Sahih Muslim Juzu'i na 4 shafi na 1883, Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 351, da Tafsirin Ibin Kathir Juzu'i na 3 shafi na 493.
    77- Tunda yake Manzon Allah (S.A.W.A.) game da Aliyu bin Abi Talib (A.S.) a hadisin Gadir "Ya Allah so wanda ya ka so shi, Ka ki wanda ya yi kiyayya da shi Ka tozartu wanda ya tozarta shi Ka sanya gaskiya ta juya tare da shi duk inda ya juya." Bayani game da haka zai zo a sashen bayanin Abinda muka yi imani da shi cewa Imamanci da nassi ne.
    78- Saboda cewa Imami sanarwa ce daga Manzon Allah (S.A.W.A.) kuma da yake Manzon Allah (S.A.W.A.) ya fada da nassi cewa: "Duk wanda na kasance ni shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa ne." Wannan yana nufin cewa da'a ga Imam da'a ce ga Manzo (S.A.W.A.) kuma yin watsi da hukuncinsa tamkar watsi da hukuncin Manzo ne, Allah Ta'ala Ya ce: "Duk wanda ya bi Manzon Allah to ya bi Allah ne." Surar Nisa'i: 80.
    79- Ya zo daga Abi Hamza cewa daga Imam Sajjad (A.S.) cewa: "Aliyu Binul Husain (A.S.) ya ce mana: Wane guri ne mafifici? Sai muka ce Allah da ManzonSa


    ( 103 )

    Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S.) suke duk wanda ya hau to ya tsira wanda kuwa ya jinkirta ya bar su to ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da ke makare da igiyoyin ruwan rikitarwa da bata da da'awowi da rikice- rikice.
    A wannan zamanin bayanin tabbatar da Imamai (A.S.) a matsayin cewa su ne halifofin gaskiya a shar'ance kuma shugabanni zabin Ubanjiji domin wannan al'amari ne da ya riga ya shude a tarihi , kuma tabbatar da hakan ba zai sake dawo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari'a ba, da kuma samar da abinda Manzon Allah (S.A.W.A.) kamar yadda ya zo da shi din ba.
    Sai dai kuma karban hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu to nesanta ne daga tafarkin sawaba a addini, kuma baligi ba ya taba samun kwanciyar hankalin cewa ya saukar da abinda aka kallafa masa daga

    ____________
    da dan ManzonSa su ne suka fi sani, sai ya ce mana guri mafifici shi ne tsakanin Makama Ibrahim (A.S.) da Rukun, kuma koda mutum zai yi tsawon rai irin na Annabi Nuhu (A.S.) wato shekaru dubu ba hamsin - yana azumtar yininsu yana kuma tsayuwar kiyamullailin dararensu a wannan gurin sa'an nan yaje ga Allah ba ya da biyayya ga shugabancinmu to wannan ba zai amfana masa kome ba."
    Man La Yahdhuruhu Fakih Juzu'i na 2 shafi na 159 hadisi na 17, da Ikabul A'amal shafi na 243 hadisi na 2, da Amali na Tusi shafi na 132 Hadisi na 209 Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na 1 shafi na 122 hadisi 308 da baki dayan hadisan Babi na 29 da Babobin mukaddamar Al-Ibadat a Wasa'il Juzu'i na 1.
    Al- Hakimul Haskani ya kawo hadisin da ke biye a littafin Shawahidut Tanzil Juzu'i na 2 shafi na 141 daga Abi Amamal Bahili cewa: "Manzon Allah (S.A.W.A.) ya ce: Allah Ya halitta Annabawa daga bishiyoyi dabam-daban, ni da Aliyu kuma an halitta mu daga bishiya guda, ni ni ne tushenta Aliyu kuma reshenta Hasan da Husain kuwa 'ya'yanta, Shi'awanmu kuma ganyayenta duk wanda ya makale wa wani reshe daga rassanta ya tsira wanda kuwa ya kauce to ya halaka, kuma idan da Bawan Allah zai yi bauta a tsakanin Safa da Marwa shekaru dubu har ya zamanto kamar tsohon kirgi da fatarsa ta tattara amma bai samu soyayyarmu ba Allah zai kifa shi a kan fuskarsa ranar Alkiyama, Sa'an nan sai Manzo (S.A.W.A.) ya karanta wannan aya "ka ce ni ba na rokon ku wani lada kansa sai dai soyayyar dangi makusata". Surar Shura: 23.


    ( 104 )

    Allah Ta'ala, domin tare da kaddara cewa akwai sabanin ra'ayoyi a tsakanin jama'ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari'a sabani irin wanda babu mai sa ran yin daidai a kansa to kuwa babu wani abu da ya saura ga mukallafi face ya juya ga mazhabar da ya so da kuma ra'ayin da ya zaba, kai babu makawa gare shi face ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah Ta'ala wajen ayyana mazhaba kebantacciya wadda ya hakikance cewa da ita ce zai isa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ce zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abinda ake da yakinin wajibcinsa babu makawa yana bukatar a samu yakinin saukar da shi.
    Dalili tabbatacce da ke nuna wajabcin komawa ga Ahlul Bait, da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W.A.) akalla shi ne maganar Manzon Allah (S.A.W.A.) "Ni lalle na bar muku abinda idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, su abubuwa biyu masu nauyi, dayansu ya fi daya girma, wato littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa da kuma zuriyata mutanen gidana, kuji ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su iske ni a tabki.80

    ____________
    80- Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 663 Hadisi na 3788 da Musnad Ahmad Juzu'i 3 shafi na 14 da 17 da 26, Juzu'i na 5 shafi na 182 da shafi na 189, da Sunanud Darimi Juzu'i na 2 shafi na 431 da Al- Musannif na Ibin Abi Shaiba Juzu'i na 11 shafi na 452 hadisi na 11725, da Sunan Ibin Abil Asim Juzu'i na 2 shafi na 336 hadisi na 754, da 628,m 630, 1548, 1549, 1553, 1555, da Tabakat na Ibin Sa'ad Juzu'i na 2 shafi na 194 da Mushkilul Asar Juzu'i na 4 shafi na 368, da Mustadrikul Hakim Juzu'i na 3 shafi na 109 da 148 da Hillayatul Awliya'i Juzu'i na 1 shafi na 355 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 5 shafi na 153-154 hadisi na 4921-4923 da hadisi na 169-170, 4980-4982, Mu'ujamul Sagir Juzu'i na 1 shafi 131, da Al-Munakib na Ibin Magazili 234-235 hadisi 281-283, da Masabihus Sunna Juzu'i na 4 shafi na 190 hadisi na 4816 da Jami'ul Usul-Juzu'i na 1 shafi na 278 da Usudul Gaba Juzu'i na 2 shafi na 12 da Zakha'irul shafi na 16 da Ihya'il Mayyit bi Fadha'ili Ahlit Baiti (A.S.) na Suyuti shafi na 30-32 hadisi na 6-8 da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 1 shafi na 170 da kuma Juzu'i na 9 shafi 162, da Kanzul Ummal Juzu'i na 1 shafi na 172-173 hadisi na 870-873 da 875, 876, da 185-186 hadisi na 952-9S3 da Sahih Muslim Juzu'i na 4 shafi na 1873 hadisi na 36 da 37, Tafsirur Razi Juzu'i na 8 shafi na l63 da Tafsirin Ibin Kasir Juzu'i na 4 shafi na 122.


    ( 105 )

    Wannan hadisin masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi'a sun yi ittafaki a kansa. Don haka ka kyautata nazarin wannan hadisin da kyau za ka iske abinda zai gamsar da kai ya kuma ba ka mamaki a ma'anarsa da abinda ya kunsa, manufar maganar Manzo "Matukar kun yi riko da shi ba kwa taba bacewa bayana har abada", tana da zurfi, kuma abinda ya bari a tsakaninmu masu nauyi guda biyu ne a hade tare, domin ya sanya su ne kamar abu guda daya bai wadatu da a yi riko da guda daya ba kawai daga cikinsu, saboda haka ta riko da su tare ne kawai ba za mu taba bacewa ba har abada.
    Kuma ma'anar fadinsa (S.A.W.A.) cewa "Ba za su taba rabuwa ba har su iso gare ni a tabki" a sarari take sosai, wato wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su tare ba to ba ya taba samun shiriya har abada, wannan kuma shi ne abinda ya sa suka zamanto "Jirgin Ruwan Tsira" da "Amincin Allah a bayan kasa". Kuma duk wanda ya jinkirta ya dakata ya bar su to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba.
    Fassarar wannan kuwa da soyayya gare su ne kawai ba tare da riko da maganganunsu da bin hanyarsu ba guje wa gaskiya ne, babu abinda ke kaiwa ga hakki illa ra'ayin rikau da gafala daga ingantacciyar hanya a bisa fassarar bayyanannen zancen Larabci.



    ( 106 )

    27 - Imaninmu Game da Son Ahlul Bait (A.S.)


    Allah Ta'ala Yana cewa:

    "Ka ce ni bana rokon ku wani Lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai."81 Surar Shura: 23.
    Mun yi imani cewa baicin wajabcin riko ga Ahlul Bait wajibi ne a kan kowane musulmi ya yi addini da soyayya gare su da kaunarsu domin a wannan ayar Allah Ta'ala Ya kayyade abinda ake rokon mutane da su yi shi shi ne soyayya ga dangi makusata.
    Ya zo jejjere ta hanyoyi daban-daban da dama daga Ananbi (S.A.W.A.) cewa soyayya gare su alamar imani ne kuma kiyayya gare su alamar munafunci82 ne da kuma cewa wanda ya so su ya so Allah da ManzonSa wanda kuma ya ki so to ya ki Allah da Manzonsa.83

    ____________
    81- Ya zo daga Ibn Abbas cewa ya ce: Yayin da wannan aya ta "Ka ce ni ba na rokon ku kome na lada a kansa sai dai soyayya ga dangi na kusa kawai" ta sauka, sun ce: Ya Manzon Allah su wane ne danginka na kusa wadanda soyayyarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fatima da Hasan da Husaini."
    Domin karin bayani a duba Durrul Mansur Juzu'i na 6 shafi na 7, da Tafsirin Tabari Juzu'i na 25 shafi na 14 da Mustadrakul Hakim Juzu'i na 2 shafi na 444 da Musnad Ahmad: 199 da Yanabi'ul Muwadda: 15, da Sawa'ikul Muhrika shafi na 11 da na 102, da Zakha'irul Akbar: 25 da sauransu.
    82- Fadha'ilu Ahmad shafi na 176 hadisi na 248, da Zakha'irul Akbar shafi na 18 da Kunuzul Haka'ik na Mannawi shafi na 135 da Ihya'ul Mayyit bi Fadhli Ahlil Bait (Alaihimus Salam), shafi na 35 hadisi na 13 da Musnad Ahmad Juzu'i na 1 shafi na 84, 95, 128 da Sahih Muslim Juzu'i na 1 shafi na 86 hadisi na 131, da Tajuj Jami'u Lil Usul Juzu'i na 3 shafi na 335, da Sunan Tirmizi Juzu'i na 2 shafi na 301, da


    ( 107 )

    Bilhasali ma soyayya gare su farilla ce da wajiban addinin Musulunci wadda ba zai yiwu a yi jayayya ko shakka a kai ba. Dukkan musulmai sun yi ittafaki a kai duk da sabanin da suke da shi kuwa a tsakaninsu a tafarkuna da ra'ayoyi in banda wata jama'a kalilan ba da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah ba wadanda aka yi watsi da su da suna "Nawasib" wato wadanda suka kulla gaba da zuriyar gidan Muhammadu(S.A.W.A.). Don haka ne ma ake kidaya su a cikin masu karyata wajiban addinin musulunci tabatattu, mai karyata wajiban addinin musulunci- kamar salla da zakka - to ana kidaya shi ne a cikin hukuncin wanda ya karyata ainihin addinin musulunci, kai tabbatacce ne ma cewa shi ya karyata Sakon koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada.
    Wannan shi ne abinda ya sa kiyayya ga zuriyar Muhammadu (S.A.W.A.) ta zama daga cikin alamun munafunci, soyayya gare su kuma daga alamun imani, saboda haka ne kuma har wa yau kiyayya gare su ta zama kiyayya ga Allah da ManzonSa. Kuma babu shakka Allah Ta'ala bai farlanta soyayya gare su ba sai don sun cancanci soyayya da biyayya, ta bangaren kusancinsu gare shi Ta'ala, da matsayinsu a gurinSa, da tsarkakarsu daga shirka da sabo, da kuma daga dukkan abinda zai nesantar daga gidan karamarSa da farfadiyar yardarSa.
    Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa Allah Ta'ala Ya wajabta son wanda ke aikata sabo, ko kuma wanda ba ya bin sa yadda ya kamata, domin shi ba shi da wata kusantaka ko abota tare da kowa, mutane a gurinsa ba kome ba ne illa bayi halittattu a matsayi guda, sai dai kawai maffici a cikinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoron Allah daga

    ____________
    Sunan Nisa'i Juzu'i na 8 shafi na 117, da Sawaikul Muhrika shafi na 263 da Al-Mahasin Juzu'i na 1 shafi na 176 hadisi na 274, da Amali Saduk shafi na 384.
    83- Amali Saduk shafi na 384 hadisi na 16 da Kanzul Ummal Juzu'i na 12 shafi na 98 hadisi na 34168 da shafi na 12: 103 hadisi 34194, da 12 shafi 116 hadisi na 34286, da Maktalul Husain na Khuwarzami na 1/109 da Zakha'irul Akbar shafi na 18 da Sawa'ikul Muhrika shafi na 263.


    ( 108 )


    ( 109 )

    28- Imaninmu Game da Imamai (A.S.)


    Ba mu yi imani game da Imamai (A.S.) irin yadda 'Yan Gullatu85, masu wuce iyaka suka yi ba haka nan ba mu yi irin yadda 'Yan

    ____________
    85- 'Yan Gullatu, masu wuce iyaka, sune wadanda suke imani da abinda ba daidai ba kana ba gaskiya ba game da Imamai (A.S.) suna cewa su Imamai Iyayengiji ne kuma su ba halittattu ba ne da dai sauransu na daga batattun akidu. Su 'Yan Gullatu sun kasu kashi daban-daban kamar haka:
  • Garabiyawa: Su ne wadanda suke cewa Allah Ta'ala Ya aiko Jibrilu da sako zuwa ga Aliyu bin Abi Talib (A.S.) sai ya kuskure ya ba wa Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) saboda tsananin kama da juna da suka yi.
  • Ulya'iyawa: Su ne mabiya Ulya'i bin Dira'id Dausi ko kuma Asadi, su ne wadanda suke da imanin cewa Aliyu bin Abi Talib (A.S.) Ubangiji ne da kuma cewa Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) bawan Aliyu bin Abi Talib (A.S.) ne -wal iyaza billahi!
  • Khamsiyyawa: Su ne wadanda suke da imanin cewa Aliyu bin Abi Talib (A.S.) Ubangiji ne kuma Salmanu Farisa da Abu Zar da Mikdada bin Aswad da Ammar Yasir, da Amru Bin Umayyatad Dhamiri su Annabawa ne da ubangiji Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya wakilta su su gyara duniya baki daya.
  • Bazi'iyawa: Su ne mabiya Bazi'i Bin Musa Al- Ha'ik wadanda suke cewa shi Annabi Ma'aiki ne kuma Imam Sadik (A.S.) shi ne ya aiko shi. Imam Sadik (A.S.) yaji Labarin sa kuma ya la'ance shi a sarari.
  • Saba'iyawa: Su ne mabiya Abdullahi Bin Saba wanda malaman tarihi ke da sabani game da shi kan cewa shi hakika mutum ne da aka yi shi ya rayu da gaske a tarihi ko kuma dai wani tatsuniya ne kawai da makiyan Shi'a suka kago shi, mabiyansa su ma sun yi Imani ne da cewa Aliyu Bin Ali Talib (A.S.) Ubangiji ne abin bautawa.


    ( 110 )

    Halluyuna86 suka yi ba, "Kalmar da ke fita daga bakunansu ta girmama." (Surar Kahf: 5).
    Mu Imaninmu a kebe shi ne cewa su mutane ne kamar mu, suna da abinda muke da shi, kuma abinda yake kanmu yana kansu, sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa Allah Ya kebance su da


    ____________
  • Mugiriyyawa: Su ne mabiya Mugira Bin Sa'idil Ajali wanda ya yi da'awar annabci, kuma ya halalta haram da yawa kuma ya cusa barnace-barnacensa a littafin Shi'a hatta ya zo a hadisi cewa Imam Sadik (A.S.) ya la'ance shi.
  • Mansuriyyawa: Su ne mabiya Abi Mansur Ajali wanda Imam Bakir (A.S.) ya yi masa ba ni ba kai kuma shi ne wanda ya yi wa kansa da'awar Imamanci kuma ya ce Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) shi ne ballin tarsashin da ke fadowa daga sama kuma sakon manzanci da ba ya karewa har abada.
  • Khaddabiyawa: Su ne mabiya Abil Khaddab Muhammadu bin Abi Zainab Al-Ajda'il Asadi wanda ya yi da'awar cewa shi Annabi ne Manzo, kuma shi yana daga cikin Mala'iku da dai ire-irensu na daga bace-bace.
    Duk wadannan kungiyoyin bata da makamantansu fandararru, Imamai (A.S.) sun nesanta kansu daga wata alaka da su kamar yadda ya zo a hadisai da dama, kana kuma sun gargadi Shi'awansu game da su. Alal Misali ya zo daga Imam Sadik (A.S.) yayin da Sadir ya tambaye cewa: "Lalle wasu jama'a suna da'awar cewa ku iyayengiji ne kuma suna karanta mana ayar Alkur'ani game da haka wadda take cewa "kuma Shi ne wannan da yake Ubangiji a sama kuma Ubangiji a kasa" Sai ya ce: "Ya Sadir Jina da ganina da fatata da namana da jinina da gashina duk ba su ba wadannan, Allah Ya barranta daga gare su, wadannan ba a kan addinina suke ba kuma ba sa kan addinin iyayena, Wallahi Allah ba zai hada ni da su ba ranar Alkiyama face Yana fushi da su." Al- Kafi Juzu'i na 1 shafi na 269. Milal Wan Nihal Juzu'i na 1 shafi na 154 Al- Farku Bainal Firak shafi na 238, Firakus Shi'a shafi na 42, Muruji'z Zahab Juzu'i na 3 shafi na 220.
    Mikbasul Hidaya Juzu'i na 2 shafi na 361 Aslus shi'a wa Usuliha shafi na 172, Wasu hadisai da dama kuma sun yi gargadi game da 'Yan gullatu, masu ketare iyaka, daga cikinsu akwai wadanda ke Biharul Anwar Juzu'i na 25 shafi na 265 da dai sauransu.
    86- 'Yan Halluyuna: Su ne wadanda suke cewa "Ruhin Ubangiji" Ya sauka a jikin Imami kuma su kansu dukansu asalinsu 'Yan Gullatu ne, bayani game da su kuma tamkar bayani ne game da'Yan gullatu.


    ( 111 )

    karamarSa kuma Ya so su da soyayyarsa, domin sun kasance a kan daraja mafi kamala mafi dacewa ga mutum na daga ilimi, da takawa, da jarumta da karimci, da kamewa, da dai dukkan kyawawan dabi'u mafifita na daga kyawawan siffofi, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abinda aka kebance su da shi.
    Da wannan ne kuma suka cancaci su zamo Imaman shiriya, da kuma duk abinda yake ya shafi bayanin shari'a da kuma abinda ya kebanci shari'a da kuma abinda ya kebanta da Akur'ani na daga tafsiri da bayani.
    Imam Sadik (A.S.) Ya ce:
    "Duk abinda ya zo muku daga gare mu wanda ya halatta ya zamanto daga halittu ba kuma ba ku san shi ba ba ku fahince shi ba to kada ku musa shi ku mayar da shi gare mu, kuma abinda ya zo muku daga abinda bai halatta ya kasance daga halittu ba ku musa shi kuma kada ku mayar da shi gare mu."87



    ____________
    87- Mukhtasarul Basar'irud Darajat: 92


    ( 112 )

    29- Imaninmu Game da Cewa Imamanci
    Sai da Nassi


    Mun yi imani cewa Imamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah Ta'ala a harshen ManzonSa, ko kuma a bisa harshen Imamin da ya kasance da nassi idan har ya so ya ba da nassi game da Imamin bayansa. Hukuncin Imamanci a kan haka tamkar hukuncin Annabci ne ba tare da wani banbanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah Ya ayyana shi mai shiryarwa ga bil Adama baki daya, kamar kuma yadda ba su da hakkin ayyana shi, ko kuma kaddamar da shi, ko zabensa, domin wanda yake da tsarki da kwazon daukar alkyabbar Imamanci baki daya da kuma shiryawa da illahirin bil Adama gaba daya bai dace ya san wani abu ba face da sanarwar Allah kuma bai kamata a ayyana shi ba face da ayyanawar Allah.88
    Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W.A.) ya ba da nassi game da halifansa kuma Imamin talikai Aliyu Bin Abi Talib Amirul muminina (A.S.), amini a kan wahayi Imamin halittu, ya ayyana shi a gurare da dama kuma ya nada shi ya kuma karba masa bai'a a kan shugabancin Muminai ranar Gadir Ya ce: "Aji a fadaka duk wanda na kasance ni shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa ne, Ya Allah Ka so wanda ya so shi Ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake


    ____________
    88- ya riga ya gabata cewa Imami tamkar Annabi ne sai dai cewa Annabi ana yi masa wahayi Imami kuwa ba a yi masa wahayi.


    ( 113 )

    shi Ka tozorta wanda ya tozarta shi kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya."89
    Daga cikin guraren farko dangane da nassi a kan imamancinsa maganarsa (Manzo) yayin da ya kirayi danginsa makusata da 'yan'uwansa na kusa kuma ya ce. "Wannan shi ne dan'uwana kuma wasiyyina kuma halifana, ku bi shi"90, a yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba.


    ____________
    89- Al- Musannaf na Ibin Abi Shaiba Juzu'i na 12 shafi na 67 hadisi na 1214 da 68 hadisi na 12141, da Sunan Ibin Majah Juzu'i na 1 shafi na 43 hadisi na 116, Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 633 hadisi 3713, da As- Sunna na Ibin Abi Asim shafi na 59l hadisi na 1361, Musnad Ahmad Juzu'i na 118- 119 da kuma Juzu'i na 4 shafi 281 da 368 da 370 da 372, da Khasa'is na Nisa'i shafi na 102 hadisi na 88, Ansabul Ashraf na Balaziri Juzu'i na 2 shafi na 156 hadisi na 169, da Kashful Astar na Bazari Juzu'i na 3 shafi na 190-191, da Al- Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 3 shafi na 21 hadisi na 3052 da kuma Juzu'i na 4 shafi na 173 hadisi na 4053, da Mu'ujamus Sagir Juzu'i na 1 shafi na 1 da shafi na 65 da Mustadrakul Hakim Juzu'i 3 shafi na 109 da Akhbaru Isfahan Juzu'i na 1 shafi na 107 da Juzu'i na 2 shafi na 228 da Tarikhu Bagdad Juzu'i na 7 shafi na 377 da Juzu'i na 14 shafi 236, da Al-Manakib na lbin Magazili shafi na 16-27 hadisi na 23, 26, 27, 29, 33, 37, 38, da Shawahidut Tanzil na Haskani Juzu'i na 1 shafi na 157 hadisi na 211, da Tarikhu Dimashk na Ibin Asakir - Tarjamatul Imam Ali (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 38-84 Tazkiratul Khawas shafi na 36, da Usdul Ghaba Juzu'i na 1 : 367 da Juzu'i na 4 shafi na 28 da Zakha'irul Akba shafi na 67, da AI- Isaba Juzu'i na I shafi na 304, don karin bayani kuma ana iya duba Littafan- Al- Gadir na Shaikh Amini da littafin Ihkakul Hak, da Abkatul Anwar da Dala'ilus Sidki da sauransu da dama.
    90-Amali Saduk shafi na 523, A'alamul Wara shafi na 167, da Ihakak Hak Juzu'i na 4 shafi na 297, Musnad Ahmad Juzu'i na 111 da shafi na 159 , Khasais na Nisa'i shafi na 83 hadisi na 66, da Tarikhut Tabari Juzu'i 19 shafi na 74, da Shawahidut Tanzil Juzu'i na 1 shafi na 420 da Sharhin Nahjul Balaga na Ibin Abil Hadid Juzu'i na 3 shafi 267, da Yanabi'ul Muwadda Juzu'i na 1 shafi na 104, Al- Kamil Juzu'i na 2 shafi na 62 da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 8 shafi 302 da sauransu, da ba za su kidayu ba.


    ( 114 )


    Kuma ya maimaita maganarsa sau da dama cewa: "Kai a gare ni matsayin Haruna ga Musa kake sai dai kawai babu Annabi ne bayana."91
    Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar da ke cewa: "Tabbatacce kawai shi ne cewa Allah ne Majibincinku da ManzonSa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka su suna masu ruku'i." Surar Ma'ida: 55.
    Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya ba da sadakar zobensa yana cikin ruku'u.92


    ____________
    91- Al- Musannif na Ibin Abi Shaiba Juzu'i na 12 shafi na 60 hadisi na 12125 da shafi na 61 hadisi na 12126, da Tarikhul Kabir na Bukhari Juzu'i na 1 shafi na 115 hadisi na 333 da Juzu'i na 7 shafi na 301 hadisi na 1284, da Sahih Muslim Juzu'i na 4 shafi na 1870 hadisi na 2404, da Sunanut Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 640 hadisi na 3730, Sunan na Ibin Abi Asim: Ya ambata shi da isnadai dabam-daban daga hadisi na 1333-1348, Musnad Ahmad Juzu'i na 1 shafi na 179 da Juzu'i na 3 shafi na 32, da Juzu'i na 6 shafi na 438, Khasa'is na Nisa'i shafi na 68-79 hadisi na 45, 48, 50, 51, 62, 63, 64 da Hilliyatul Awli'ya'u Juzu'i na 4 shafi na 345 da Juzu'i na 7 shafi na 195 da 196 da Tarikhu Isfahan Juzu'i na biyu shafi na 281, 328 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 1 shafi na 146 hadisi na 328 da 148, 333, 334, da Juzu'i na 2 shafi na 247 hadisi na 2035, da Juzu'i na 4 shafi na 17 hadisi na 3515 da Juzu'i na 11 shafi na 74 hadisi na 11087 da Juzu'i na 24 shafi na 146 hadisi na 384-389, da Mu'ujamus Sagir Juzu'i na 2 shafi na 53,54, Tarikhu Bagdad Juzu'i na 1 shafi na 325 da Juzu'i na 3 shafi na 406, Juzu'i na 8 shafi na 53 da Juzu'i na 9 shafi na 365 da na 10 shafi 43, da'Juzu'i na 12 shafi na 323, da Isti'ab Juzu'i na 3 shafi na 34, da Al-Manakib na Ibin Magazili shafi na 27-36 hadisi na 40-56, Tarikhu Dimashk Tarjamatu Imam Ali (A.S.) Juzu'i na 1 shafi na 306-390, Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 9 shafi na 109 da sauransu.
    92- Tafsiru Furatul Kufi shafi na 40-41, da Amalis Saduk shafi na 107 hadisi na 4, da Tafsirut Tibyan na Tusi Juzu'i na 3 shafi na 559, da Ihtijaj na Tabrisi Juzu'i na 2 sha 489, da Tafsiriut Tabari Juzu'i na 6 shafi na 186, da Asbabun Nuzul na Wahidi shafi na 113 da Al- Munakib na Ibin Magazili shafi na 3 12 hadisi na 356 da shafi na 313 hadisi na 357, Al-Manakib na Khawarzimi shafi 264, Tazkiratul Khawas shafi na 24, Tafsiri


    ( 115 )


    Bin diddigin duKkan abinda ya zo na daga ruwayoyi da ayoyin Alkur'ani ba ya goyon bayan cewa wannan sakon kagagge ne kazalika bayani manufofinsu da suke nuni da su.93
    Sa'an nan shi kuma kansa (A.S.) ya ba da nassi game da Imamancin Hasan da Husain (A.S.), shi kuma Husain94 ya ba da nassin Imamancin dansa Aliyu Zainul Abidin (A.S.) haka nan dai Imami ke ba da nassin Imami bayan Imami, wanda ya gabata ya ba da na mai zuwa har zuwa kan na karshensu kuma shi ne zababbensu kamar yadda zai zo.



    ____________
    93- Littafin As- Sakifa na marubucin wannan Littafin sashen Aliyu bin Abi Talib (A.S.)" shafi na 59-73 Akwai sharhin wasu ayoyin.
    94- Kari a kan abinda ya zo daga Manzo (S.A.W.A.) game da su biyu domin hadisi ya zo a jejjere da hanyoyi da dama kan cewa ya ce: "Wadannan 'Ya'yan nawa guda biyu Imamai, sun tashi ko sun zauna" Annaukat shafi na 48, Ilalus Shara'i-i Juzu'i na 1 shafi na 21 1, Al- Irshad shafi na 220, Kifayatul Asar: 117, da At Tuhaf na Majduddin shafi na 22, da Yanabi'un Nasiha shafi na 237, da ya ce "Babu wata rikitarwa game da kasancewar wannan hadisin daga wanda al'umma ta karbe shi domin Ya kai darajar hadisi mutawatiri, mai hanyoyin zuwa da yawa, don haka ya inganta a kafa dalili da shi." Game da shi ne ma Ibin Shahar Ashubi ya ce a manakib: "Ma'abuta Alkibla sun yi ittifaki a kansa".


    ( 116 )

    30-Imaninmu Game da Adadin Imamai.


    Mun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar imamanci na gaskiya, sune wadanda muke komawa gare su a hukumce - hukumcen shari'a wadanda aka bada nassi game da Imamancinsu su goma sha biyu ne ,Annnabi(S.A.W.A.) ya bada nassi a kansu dukkanninsu da sunayensu95 sa'an nan kuma duk wanda ya gabata daga cikinsu to ya ba da nassi akan wanda ke biye da shi kamar haka:-


    ____________
    95- Kamaluddin shafi na 250-256 hadisi na 1-4 da Uyunu Akhbarur Ridha (a.s.) Juzu'i na 1 shafi na 41-51 hadisi na 2-16, da Amalit Tusi juzu'i na 1 shafi na 291 hadisi na 556/13 da Fara'idus Simtain juzu'i na 2 shafi na 132 hadisi na 431 da na 136 da na 435 da 313 da 564.
    Ya zo a ruwayoyi da dama wadanda maruwaitan Ahlus Sunna da dama suka kawo wadanda a cikinsu Annabi (S.A.W.A) yake cewa: lalle halifofi bayansa goma sha biyu ne da kuma cewa lalle dukkaninsu daga Kuraishawa suke. Daga cikinsu akwai wanda Jabir bin Samrata ya kawo yayin da ya ce:" Na kasance tare da mahaifina a gurin Annabi (S.A.W.A) sai na ji yana cewa: Bayana akwai halifofi goma sha biyu sa'an nan sai ya yi kasa-kasa da muryarsa a kai, ya ce cewa yayi dukkanninsu daga Bani Hashim suke". Da dai wasun wannan ruwayar da dama.
    A duba Musnad Ahmad Juzu'i na 5 shafi na 89 da 90 da 92, da kuma Musradrakul Hakim Juzu'i na 4 shafi na 501 da Majma'ul Zawa'id Juzu'i na 5 shafi na 190 Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 201 da 206 da kuma Sahih Bukhari Juzu'i na 9 shafi na 101 da Sahih Muslim juzu'i na 2 shafi na 192 da Tarikhul Khulafa'i shafi na 10 da Sunan Tirmizi Juzu'i na 2 shafi na 35 da Yanabi'ul Muwadda shafi na 444 da sauransu da dama.


    ( 117 )

    Adadi
    Al-Kunya
    Suna
    Lakabi
    Haihuwa
    Rasuwa
    1
    Abul Hasan
    Aliyu bn Abi Talib
    Al-Murtadha
    Shekara ta 23 Hijiriyya
    Shekara ta 40 Hijiriyya
    2
    Abu Muhammad
    Al-Hasan bn Ali
    Az-Zakiy
    Shekara ta 2 Hijiriyya
    Shekara ta 50 Hijiriyya
    3
    Abu Abdullah
    Husain bn Ali
    Sayyidush-Shuhada'u
    Shekara ta 3 Hijiriyya
    Shekara ta 61 Hijiriyya
    4
    Abu Muhammad
    Ali bn Husain
    Zainul Abidin
    Shekara ta 38 Hijiriyya
    Shekara ta 95 Hijiriyya
    5
    Abu Ja'afar
    Muhammad bn Ali
    Al-Bakir
    Shekara ta 57 Hijiriyya
    Shekara ta 114 Hijiriyya
    6
    Abu Abdullah
    Ja'afar bn Muhammad
    Al-Sadik
    Shekara ta 83 Hijiriyya
    Shekara ta 148 Hijiriyya
    7
    Abu Ibrahim
    Musa bn Ja'afar
    Al-Kazim
    Shekara ta 128 Hijiriyya
    Shekara ta 183 Hijiriyya
    8
    Abul Hasan
    Aliyu bn Musa
    Ar-Ridha
    Shekara ta 148 Hijiriyya
    Shekara ta 203 Hijiriyya
    9
    Abu Ja'afar
    Muhammad bn Ali
    Al-Jawad
    Shekara ta 195 Hijiriyya
    Shekara ta 220 Hijiriyya
    10
    Abul Hasan
    Aliyu bn Muhammad
    Al-Hadi
    Shekara ta 212 Hijiriyya
    Shekara ta 254 Hijiriyya
    11
    Abu Muhammad
    Al-Hasan bn Ali
    Al-Askari
    Shekara ta 232 Hijiriyya
    Shekara ta 269 Hijiriyya
    12
    Abul Kasim
    Muhammad bn Hasan
    Al-Mahdi
    Shekara ta 256 Hijiriyya
    .........


    Shi ne Hujjar wannan zamanin namu, shi ne boyayyen da ake jira, Allah Ya gaggauta bayyanarsa Ya saukaka mafitarsa, domin Ya zo Ya cika kasa da adalci da daidaito bayan an cike ta da zalunci da ja'irci.


    ( 118 )

    31-Abinda Muka Yi Imani da shi Game
    da Mahadi (A.S.)


    Lalle yin albishir game da bayyanar Mahadi (A.S.) daga 'ya'yan Fatima (A.S.) a karshen Zamani -domin ya cika kasa da daidaitawa da adalci bayan an cika ta da zalunci da jairci- tabbatacce ne daga Annabi (S.A.W.A) daga hanyoyin ruwayoyi daban-daban masu yawa, kuma dukkan musulmi sun ruwaito hadisi game da haka a bisa mabanbantan hanyoyinsu na karbar ilimi.96
    Kuma wannan ba wani sabon ra'ayi ba ne da Shia suka kago shi saboda iza su da yaduwar zalunci da ja'irci ya yi zuwa gare shi, har suka yi mafarki game da bayyanar wani da zai tsarkake kasa daga kazantar zalunci kamar yadda wasu 'Yan rikikitarwa marasa insafi ko adalci suke kintatawa.97


    ____________
    96- Al- Gaibatu na Tusi shafi na 148 da 187, da Umdatu na Ibinil Batrik shafi aa 433 hadisi na 909 da shafi na 436, hadisi na 920, da Isbatul Hudat Juzu'i na 3 shafi na 504 hadisi na 303-304 da Sunan Abi Dawud Juzu'i na 4 shafi na 107 hadisi na 4284, da Sunan Ibin Majah Juzu'i na 2 shafi na 1368 hadisi na 4086 da dukkan hadisan Al- Babul 34 Kitabul Fitan, da Mustadrakul Hakim Juzu'i na 4 shafi na 557 Al- Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 23 shafi 267 hadisi na 566, da Kifayatut Talib shafi na 486, da Kanzul Ummal Juzu'i na 14 shafi na 264 hadisi na 38662, Sunan Tirmizi Juzu'i na 4 shafi na 505, Al-Bayan fi Akhbari Sahibuz Zaman shafi na 479, Al- Hawi na Fatawi Juzu'i na 2 shafi, Al- Burhan Fi Alamatul Mahdi (A.S.) shafi na 94.
    97- La'alla daga cikin masu rikitarwar Dokta Rundasan wanda yake cewa: "Lalle mai yiwuwa ne kwarai cewa rashin cin nasarar hukumar Ummayyawa na zahiri wajen kasa kafa rukunan adalci da daidaito a zamaninsu shekara ta 41-132 na daga


    ( 119 )


    Idan da ba don tabbatar akidar Mahadi (A.S.) daga Annabi (S.A.W.A) ta yadda dukkan musulmi suka sani ba ya kuma kafu a zukatansu suka yi imani da shi ba to da masu da'awar imani da Mahadi (A.S.) a karnonin farko kamarsu Kisaniyawa98 da Abbasawa


    ____________
    cikin abubuwan da suka sabbaba akidar Mahadi a karshen zamani." Littafin Akidar Shi'a shafi na 231.
    98- Kisaniyawa: Jama'a ce da suka yi ittifaki a kan Imamancin Muhammad Bin Hanafiyya. Wasunsu sun ce lalle Muhammad Bin Hanafiyya shi ne Imami bayan Mahaifinsa Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) domin Imam Ali (A.S.) ya ba shi tuta ranar Yakin Jamal inda ya ce da shi: Soke su suka irin na Mahaifinka a yabe ka, babu alheri a yaki matukar ba ka gwabza ba.
    Wasunsu kuma sun ce: Lalle Imami bayan Imam Ali (A.S.) shi ne Imam Hasan (A.S.) sai Husain (A.S.) sa'an nan kuma sai shi ya zamanto Imami bayan Imam Husain (A.S.) ya fita daga Madina zuwa Makka kafin aukuwar al'amarin Karbala. Wasunsu suna da ra'ayin cewa shi Muhammad Bin Hanafiyya yana raye bai mutu ba kuma wai shi ne Mahadi da ake saurare, wannan su ne wadanda marubucin wannan littafin ya yi ishara game da su a nan.
    Wasunsu kuma sun tafi a kan cewa ya rasu kuma Imami bayansa shi ne Imam Aliyu Binul Husain Zainul Abidin (A.S.).
    Daga cikinsu kuma akwai masu cewa: Imamanci bayansa ya koma ga Abi Hashim Bin Muhammad Ibin Hanafiyya, sa'an nan kuma su kansu sun saba a kan Imamanci bayansa. Wasunsu suka ce ya koma ga Muhammad Bin Ali Bin Abdullah, wasunsu na cewa bayansa Imamanci ya koma ga Bayan Bin Sam'an suna kuma raya cewa ruhin Allah Ya kasance a jikin Hashim sa'an nan Ya fita Ya koma jikin shi Bayan.
    Watakila an sa musu suna Kisiniyawa ne saboda Mukhtar Bin Abi Ubaidus Sakafi ya kasance shugabansu kuma an kasance ana yi masa Lakabi da "Kisana" domin shugaban dogaransa shi ne (Abu Umrata) kuma sunansa kisana ne kuma ya zurfafa wajen shi Mukhtar din.
    Wannan kuwa a bisa asasin cewa akidar Shi'a Imamiyya ita ce mafi daidai a gurinsu kan cewa shi Mukhtar mutum ne Salihi mai akida sahihiya, kuma ya kasance yana kira ga Imamancin Imam Sajjad (A.S.) yabo gare shi kuwa ya zo a harshen Imam Sajjad (A.S.), da Imam Bakir (A.S.) da Imam Sadik (A.S.) kamar kuma yadda yabo gare shi da kuma rashin zargi a kansa ya zo daga Malaman Shi'a kuma babu wanda ya zarge masa illa kalilan daga cikinsu. Abin kuma da ake jifan sa da shi duk kazafi ne da makiya domin su bata shi domin shi ne ya yunkura don ramuwar gayya


    ( 120 )

    da wasu daga cikin Alawiyawa da sauransu ba su iya sun yaudari mutane sun yi amfani da wannan akida wajen neman mulki da shugabaci ba, domin sun sanya da'awarsu ta karya game da Mahadi (A.S.) hanyar tasiri a kan jama'a gama gari da kuma yada karbuwarsu a kansu (jama'ar).
    Mu kuwa duk da Imaninmu da ingancin addinin Musulunci, da kuma cewa shi ne cikamakin addinan Ubangiji, kuma ba ma sauraron wani addini da zai zo ya gyara bil Adama, tare da dukkan abinda muke gani na yaduwar zalunci da yawaitar fasadi a duniya ta yadda ba za ka iya samun masakar tsinke ba ga adalci da gyara a kasashe mallakakku, tare kuma da abinda muka gani kuru-kuru na nesantarsu da addininsu su da kansu, da kuma jingine hukunce-hukuncen musulunci da dokokinsa a dukkan kasashen musulunci da kuma rashin lizimtuwarsa ga dubban hukunce-hukuncen musulunci amma duk da haka babu makawa lalle ne mu saurari budi yayin da addinin musulunci zai dawo da karfinsa da iyawarsa da gyaran wannan duniyar da ta dulmuye a cikin rashin gaskiyar zalunci da fasadi.
    Sa'an nan kuma ba zai yiwu ba ga musulunci ya dawo da karfinsa da shugabancinsa a kan bil Adama baki daya yana cikin halin da yake ciki a yau da ma kafin yau din na daga sabanin mabiyansa a dokoki da hukunce-hukunce da ma ra'ayoyinsu game da shi tare kuma da kasancewarsu a halin da suke ciki a yau na daga bidi'a da fandarawa a dokokinsa da ma bata a da'awarsu.
    Na'am ba zai yiwu ba addini ya koma ga karfinsa sai dai idan har wani mai gyara babba ya bayyana ya shige masa gaba, yana hade kalma guri guda kuma yana soke abinda aka lika masa na daga bidi'a da bata tare da taimakon Ubangiji domin Ya sanya shi ya zamanto shiryayye mai shiryarwa, mai girma da Shugabanci na gaba daya da


    ____________
    da daukar fansa ga Imam Husain (A.S.) ya kuma kashe wadanda suka kashe shi da zuriyar gidansa a Karbala. Malamar Shi'a Imamiyya da dama sun yi rubuce-rubuce game da rayuwar shi Mukhtar da ayyukansa. A duba Al-Milal wan Nihal Juzu'i na daya shafi na 131, Al- Farku bainal Firak shafi na 38 da Firakus Shi'a shafi na 23.


    ( 121 )

    kuma iko wanda ya saba wa al'ada domin ya cika ta da daidaituwa da adalci bayan an cika ta da zalunci da jairci.
    A takaice dai dabi'ar mummunan halin da dan Adam ke ciki wanda ya kai kololuwa a fasadi da zalunci kuma da imani da cewa wannan shi ne cikaton addinai tare kuma da imani da ingancinsa na tabbatar da jiran wannan Mahadi (A.S.) mai kawo gyara domin ya kubutar da duniya daga halin da take ciki.
    Saboda haka ne dukkan bangarorin Musulmi suka yi imani da wannan jiran, kai hatta ma al'ummun da ba musulmi ba, sai dai kawai bambancin da ke akwai tsakanin mazhabar Imamiyya shi ne cewa Mazhabar Ja'afariyya Imamiyya ta yi imani da cewa wannan mai gyaran wato Mahadi (A.S.) mutum ne ayyananne wanda aka haife shi a shekara ta 256 Hijiriyya kuma bai gushe ba yana nan da rai, shi ne dan Imam Hasan Askari (A.S.) kuma sunansa "Muhammad". Wannan kuwa saboda abinda ya tabbata daga Annabi (S.A.W.A) da kuma Ahlul Bait (A.S.) game da alkawari99 game da shi, da kuma hadisan da suka tabbata a gare mu ta hanyoyin ruwaya daban-daban masu yawa game da haihuwarsa da kuma bayyanarsa.


    ____________
    99- Domin tabbatar maganar Allah Ta'ala da ke cewa: "Shi ne wanda ya aiko Mazonsa da shiriya da addinin gaskiya don Ya tabbatar da shi a kan dukkan adddinai baki daya." Surar Tauba: 33, Fathi: 28, saf: 9.
    Domin ya zo a ruwayoyi da hadisai da dama daga Annabi (S.A.W.A) da kuma daga Imamai (A.S.) game da bayyanar Mahadi (A.S.) daga 'ya'yan Fatima (A.S.), kuma cewa zai cika kasa da daidaito da adalci bayan an cika ta da zalunci da rashin daidai kamar yadda ya riga ya gabata.
    Sidi Shahid Sadr ya ambata nassi kamar haka: "Akidar Mahadi a matsayinsa na shugaba da ake jira domin canja duniya zuwa ga mafi dacewa, hadisai da dama daga Annabi (S.A.W.A) baki daya da kuma daga Imamai (A.S.) a kebe, kuma sun yi ta'akidi a nassosi masu yawa ta yadda ba zai yiwu a yi shakku a kansu ba, an kidaya hadisai dari hudu daga Annabi (S.A.W.A) daga bangaren 'Yan'uwanmu Ahlus Sunna, kamar kuma yadda aka kididdige hadisai dangane da Imam Mahadi (A.S.) daga bangaren Shi'a da Sunna inda adadinsu ya kai sama da dubu shida. Wannan adadi ne mai yawan gaske wanda babu kamarsa a cikin sauran al'amuran musulunci bayyanannu, wadanda a bisa dabi'a musulmi ba ya shakka a kansu." Al- Bahas haulal Mahadi shafi na 63.


    ( 122 )


    Ba ya halatta Imamanci ya yanke, ko ya katse a wani zamani daga zamuna100 koda kuwa Imamin a boye yake, domin ya bayyana a ranar da Allah Ya yi alkawari wanda kuma wannan daga cikin asirran Ubangiji babu wanda ya san su sai Allah.
    Ba zai gagara ba cewa wannan rayuwa tasa mai tsawo da dogon zamaninsa su zama Mu'ujiza da Allah Ta'ala Ya ba shi, kuma wannan ba ta fi Mu'ujizar kasancewarsa Imami yana dan shekara biyar kawai ba, yayin da mahaifinsa ya koma ga Ubangiji101 Madaukaki, kuma ba ta fi Mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) girma ba yayin da ya yi magana da mutane yana cikin shimfidar jaririnsa yana yaro, kuma aka aike shi Annabi ga mutane.
    Tsawon rayuwa fiye da dabi'a kuwa, ko kuma ga wanda ya dauka cewa ta dabi'a ce - fannin Likitanci ba zai hana ta ba kuma ba zai shamakance ta ba, sai dai kawai cewa ilimin likita bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba, idan kuwa har ya gaza ai Allah Ta'ala mai iko ne a kan kome, kuma haka ya auku tabbatacce a


    ____________
    100- Saboda abinda ya gabata cewa kasa ba ta zama ta tsiraita daga hujja ba.
    101- Ya zo a ruwayoyi cewa Imam Askari (A.S.) ya yi wafati a shekarar 260 a lokacin kuma shekarar Imam Mahadi (A.S.) shekara biyar kuma ya dauki nauyin Imamanci.
    Ruwayar Abil Adyan wanda ya kasance yana yi wa Imam Askari (A.s) hidima yayin da Imam din (A.S.) ya aike shi ya kai wasu littafa zuwa wasu birane lokacin da yake rashin lafiya, ya ce masa, lalle za ka boyu kwana goma sha biyar kuma ranar kwana na goma sha biyar din za ka shiga garin Samurra kaji ka kiyaye. Sai Abul Adyan ya tambaye shi game da Imamin bayansa sai ya ce masa shi ne wanda zai neme ka da amsoshina kuma ya yi mini salla kuma zai ba ka labarin abinda ke cikin buhun da ke tare da kai. Wannan kuwa duk abinda Imam ya fade haka ya auku. Abul Adyan ya dawo wanda ya nemi amsoshin shi ne Imam Mahadi (A.S.) kuma shi ne ya yi wa mahaifinsa salla bayan ya sallami baffansa sa'an nan kuma ya ba wa Abul Adyan labarin abinda ke cikin buhun da ke tare da shi, kamar kuma yadda ya bawa mutane da dama labarin wasu al'amura da babu wanda ya san da su sai su kansu, a wannan lokacin shekararsa biyar. A duba Kamaluddin wa Tamamun Ni'ima Juzu'i na 2 shafi na 476, da Biharul Anwar Juzu'i na 50 shafi na 332 hadisi na 4 da Tarikhu Ghaibatus Sugra shafi na 282 da abinda ya biyo baya.


    ( 123 )

    tsawaita rayuwar Annabi Nuhu102 (A.S.) da wanzar da Annabi Isa103 (A.S.) kamar yadda Alkur'ani ya bayyana. Idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abinda Alkur'ani ya ba da labari game da shi to musulunci kam sai wata rana.
    Abin mamaki ne har Musulmi ya tsaya yana tambaye-tambaye game da yiwuwar haka alhali kuwa yana da'awar imani da Littafi Mabuwayi.
    Daga cikin abinda lalle ne mu ambata shi a nan shi ne cewa zamanin jiran ba wai yana nufin cewa musulmi su nade hannuwansu ba ne game da al'amuran da suke na gaskiya dangane da addininsu da abinda ya wajaba na taimaka masa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.
    Bilhasali ma musulmi dimin da'iman an kallafa masa ya yi aiki da abinda Allah Ya saukar na daga hukunce-hukuncen Shari'a kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon abinda ya iya kuma ikon yin haka ya samu gare shi:


    ____________
    102- Domin Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun aiki Nuhu ga mutanenSa ya kasance a cikinsu shekara dubu ba hamsin sai ambaliyar ruwa ta kama su alhali su suna azzalumai." Surar Ankabutu: 14. Kuma tabbatacce ne cewa wannan gwargwadon shekarun lokacin zamansa a cikin mutanensa ne kawai amma shekarunsa duka-duka an ce akalla dubu da dari shida ne an ce ma sun fi haka. Tafsirul Kasshaf Juzu'i na 3 shafi na 200 Tafsirul Ibin Kasir Juzu'i na 3 shafi na 418, da Zadul Masir na Ibinul Jauzi Juzu'i na 6 shafi na 261.
    103- "Da fadarsu; Lalle ne mun kashe Al-Masihu Isa dan Maryama Mazon Allah", alhali kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su tsire shi ba sai dai an kamanta shi gare su ne. Lalle ne wadanda suka saba wa juna a kan sha'aninsa suna shakka game da shi, ba su da wani ilimi face bin zato, kuma basu kashe shi ba a hakika. Sai dai Allah ya dauke shi ne zuwa gare Shi. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi, Mai hikima" Surar Nisa'i: 157-158.


    ( 124 )


    "Dukkanku makiyaya ne kuma dukkanku ababan tambaya ne game da abin kiwonsa."104
    Don haka bai halatta gare shi ba ya jinkirta wajibansa don kawai yana jiran Mahadi (A.S.) mai kawo gyara, mai shiryarwa, wanda aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya sauke aikin da aka kallafa, kuma ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama sun bar aiki.



    ____________
    104- Jami'ul Ahadis na Kummi shafi na 21 da Jami'ul Akhbar Shafi na 337 hadisi na 919, Sahih Bukhari Juzu'i na 2 shafi na 6 da Juzu'i na 3 shafi na 196, Musnad Ahmad Juzu'i na 2 shafi na 5 Sunan Baihaki Juzu'i na 6 shafi na 287.


    ( 125 )

    32- Imaninmu Game da Raja'a (Komowa).


    Abinda Mazhabar Ja'afariyya -Imamiyya take kai- tare da riko da abinda ya zo daga Ahlul Bait (A.S.) Shi ne cewa Allah Ta'ala zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, Zai daukaka wasu kana kuma Zai kaskantar da wasu, kana Zai rarrabe masu gaskiya daga cikinsu daga marasa gaskiya, da wadanda aka zalunta daga azzalumai, wannan zai auku ne bayan bayyanar Mahadi daga zuriyar gidan Manzon Allah mafifita (tsira da aminci su tabbata a gare su).
    Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani ta daukaka, ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna. Bayan nan kuma sai a mutu daga nan kuma sai zuwa tashin Alkiyama zuwa ga abinda suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuwa ukuba, kamar yadda Allah Ta'ala Ya kawo a cikin Alkur'ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din ke yi, wato wadanda ba su gyaru ba da komowarsu, don haka suka sami ukubar Allah kan cewa a dawo da su zuwa na uku ko sa gyaru;
    "Suka ce Ya Ubangijinmu Ka matar da mu sau biyu kuma Ka rayar da mu sau biyu to mun yi ikrari da zunubanmu shin akwai wata hanyar fita." Surar Mumin: 11.
    Na'am Alkur'ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya, hadisai da dama kuma daga Ahlul Bait (A.S.) suka zo a kan haka, mabiya Mazhabar Ja'afariyya ko kuma Imamiyya sun yi ittifaki a kan haka sai dai 'yan kalilan daga cikinsu da suka yi tawilin abinda ya zo game da raja'a da cewa ma'anarta ita ce komowar hukuma da Umarni da hani


    ( 126 )

    ga Ahlul Bait da bayyanar Imamin da ake jira (A.S.) ba tare da komowar wasu ayyanannu ko raya matattu ba.
    Batun raja'a kuwa a gurin Ahlus Sunna yana daga cikin abin ki wanda imani da shi ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja'a a matsayin suka ga mai ruwaya da kuma abin kiyayya gare shi wadda ke wajabta kore ruwayarsa da watsi da ita, kuma ya bayyana cewa suna kirga ta a matsayin karfirci da shirka, har ma ta fi muni, don haka, wannan na daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi'a Imamiyya da shi da kiyayya da su a kansa.
    Babu shakka wannan duk wata mafaka ce kawai da bangarorin kungiyoyin musulunci da can suka kasance suna riko da ita don sassansu su soki sashe da shi, kuma alal hakika mu ba muga wani abu da zai halatta wannan mafakar ba domin imani da raja'a ba ya soke imani da tauhidi kuma ba ya soke imani da Annabci bilhasali ma kara inganta akidu biyun yake yi. Domin Raja'a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya tamkar dai tashin Kiyama da tayar da mamata, kuma tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al'ada wadanda ya inganta ta zama Mu'ujiza ga Annabinmu Muhammadu (S.A.W.A) da zuriyar gidansa. Kuma ita raja'a tamkar mu'ujizar raya matattu ce wadda ta kasance ga Annabi Isa (A.S.) ne sai dai ma ta fi ta cika a nan domin wannan za ta zo ne bayan mamata sun zama rididdigaggu.
    "Ya ce wane ne zai raya kasusuwa alhali sun zama rididdigaggu. Ka ce Zai raya su Wannan da Ya fare su karon farko kuma Shi game da dukkan halitta Masani ne." Surar Yasin: 79-87.
    Amma wanda ya soki raja'a kuwa da dalilin cewa tana daga shafewa batacciya to lalle bai fahimci bambanci tsakanin "tanasuhi" da kuma ainihin tayar da mamata da ainihin jikinsu ba, ita raja'a wani nau'i ne na tayar da mamata da ainihin jikinsu. Domin ma'anar tanasuhi ita ce kauratar da rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba, ma'anar tayar da matattu da ainihinjikkunansu kuwa ba haka take nufi ba, ma'anarsa ita ce komo da ainihin jikin da ainihin abubuwan ransa da suka kebantu da shi, haka nan ma Raja'a take.


    ( 127 )


    Idan kuwa har aka ce "Raja'a" "Tanasuhi' ce to raya mamata da Annabi Isa (A.S.) ma ya kasance yana yi "tanasuhi" ce to tayar da mamata da komo da ainihin jikkunan mamata ma "tanasuhi" ne ke nan.
    Saboda haka babu abin da ya saura illa muhawara ta fuska biyu game da "Raja'a".
    Na farko: Korarriya ce sam ba za ta auku ba.
    Ta Biyu: Karyata hadisan da suka zo game da ita.
    A bisa asasin Kaddara cewa muhawarorin biyu daidai suke, sam yin imani da ita ba a daukar sa a matsayin kyamar da masu adawa da Shi'a suka juya ta.
    Kuma nawa ne daga cikin abubuwan da suke daga cikin korarru wadanda sauran bangororin musulmi suka yi imani da su ko kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su, amma ba su wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba. Akwai Misalin su da dama, a cikinsu akwai:
    Yarda da yiyuwar rafkanuwa ga Annabi (S.A.W.A) ko kuma aikata sabo105 da kuma imani da Wanzuwar Alkur'anit106 da kuma batun "Wa'idu"107 da kuma imani da cewa Annabi bai ba da nassi kan halifan bayansa ba.
    To dangane da Muhawarori biyun da muka kawo a dauka cewa ba su da wani asasin ingancin tabbatar da Raja'a amma ai mun riga mun


    ____________
    105- Sahihul Bukhari Juzu'i 2 shafi 68, Sahih Muslim Juzu'i 1 shafi na 399 hadisi na 85, 86, 87, 89, Tirmizi Juzu'i na 2 shafi 235 hadisi 391-395, Sunan Abi Dawud Juzu'i 1 shafi na 264 hadisi na 1008-1023.
    106- Sharhul Makasid Juzu'i na 4 shafi na 143-146 A cikinsa akwai ishara ga maganar 'Yan Hambaliyya da Hashawiyawa game da wanzuwar Alkur'ani har ma da magarnar wasunsu kan cewa bangonsa da jakarsa ma azali suke, akwai kuma ishara ga muhawarar Abu Hanifa da Abu Yusuf da ta dauki tsawan wata shida inda ta kare da cimma ittifaki a tsakaninsu kan cewa Alkur'ani wanzazze ne duk wani batu sabanin haka kuwa kafirci ne.
    107- Sharhul Makasid Juzu'i 5 shafi na 125 da Mazahibul Islamiyyin: 62.


    ( 128 )

    bayyana cewa ita Raja'a wani nau'i ne na tayar da mamaci ko kuma komo da ainihin jiki, sai dai kawai cewa ita tana aukuwa ne a wannan duniyar. Dalilin kuma da ke tabbatar da yiwuwar tashin kiyama shi ne dalilin da ke tabbatar da ita babu wani abu kuma da zai sa a yi al'ajabi game da ita sai dai kawai don zukatanmu ba su saba da ita ba ne a rayuwanmu ta duniya, kuma ba mu da sabubbanta da abubuwan da ke hana ta da za su sa mu yi ikrari da ita ko mu kore ta, da kuma fahimtar cewa abu ne marar sauki ga mutum ya yarda ya gaskata abinda bai saba da shi ba, wannan kuwa kamar wanda ya ga cewa tayar da mamata abu ne bako ya ce: "Wanene zai tayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu". Aka ce Masa:
    "Wanda Ya fare su a karon farko Shine zai raya su kuma Shi a kan komai Masani ne". (Yasin: 78-79)
    Na'am a kan makamancin wannan da ba mu da dalili na hankali akai na tabbatar da ita ko kore shi, ko kuma muka raya rashin dalili to wannan kuwa zai kallafa mana komawa ga nassosin addini wadanda suke daga tushen wahayin Ubangiji. Kuma abinda zai tabbatar da yiwuwar Raja'a ga wasu matattu a duniya ya zo a Alkur'ani kamar dai Mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) a raya matacce: "Kuma ina warkar da wanda aka haifa makaho da kuturu kuma ina rayar da matattu da izinin Allah." Surar Ali Imran: 49.
    Da kuma fadin Allah Ta'ala: "Ta yaya Allah Zai raya wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah Ya matar da shi shekara dari sa'an nan kuma Ya raya shi." Surar Bakara: 259.

    Da kuma ayar da ta gabata da ke cewa: "Suka ce Ya Ubangijinmu Ka matar da mu sau biyu." Surar Mumin: 11.
    Ma'anar wannan ayar ba za ta fito daidai ba ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba koda yake wasu masu tafsiri sun wahalar da kansu wajen yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba kuma ba zai tabbatar da ma'anar ayar ba.
    Muhawara ta biyu kuwa wadda ke cewa hadisai game da ita Raja'a kagaggu ne kawai wannan da'awar ba ta da wani asasi, domin Raja'a


    ( 129 )

    na daga cikin al'amuran da suke ba makawa sun zo daga Ahlul Bait (A.S.) daga hadisai masu tafarkunan ruwaya da dama.
    Bayan duk wannan ashe ba a yi mamaki ba game da mashahurin marubuci mai da'awar sani kamar Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam, saboda yana cewa; "Ai Yahudanci ya bayyana a cikin Shi'anci ta hanyar batu game da raja'a108." Don haka ni nake cewa gare shi:
    "To ai Yahudanci ma ya bayyana a Alkur'ani game da batun Raja'a" kamar yadda ya gabata game da ayoyin Alkur'ani da suka ambaci raja'a.
    Za kuma mu kara masa da cewa:
    Alal hakika babu makawa Yahudanci da Nasaranci su bayyana a cikin da dama daga abubuwan da aka yi imani da su da kuma hukunce-hukuncen musulunci, domin Annabi Mai girma (S.A.W.A) ya zo yana mai gaskata Shari'o'i da suka gabata109 kuma koda yake an shafe wasu daga hukunce-hukuncensu. To bayyanar Yahudanci da Nasaranci a wasu abubuwan da Musulunci ya yi imani da su ba aibu ba ne cikin Musulunci idan ma har aka dauka cewa lalle Raja'a daga akidojin Yahudanci take kamar yadda wannan marubucin yake da' awa.
    Ko ta halin kaka dai Raja'a ba wai tana daga cikin jiga-jigan addinin (Musulunci) da ya wajaba a dauke ta a akida ba ne da kuma yin bincike a kanta sai dai kawai imani da muka yi da ita biyayya ne ga hadisai ingantattu daga Ahlul Bait (A.S.) wadanda muka yi imani da


    ____________
    108- Fajrul Islam shafi na 33 kan cewa Ahmad Amin bai takaita ba a wannan a kan wannan magana ta sa, sai dai ya yi karin gishiri mai yawa da maganganu marasa madogara ba su kuma da asasi, A duba Littafin Aslus Shi'a wa Usuliha shafi na 140 don karin bayani. A ciki an kawo wannan maganar da kuma takaitaccen martani game da ita.
    109- Ishara ga maganar Allah Ta'ala Yana mai Shaidawa Manzonsa Muhammadu (S.A.W.A) cewa "Ya saukar da littafi a gare ka da gaskiya Yana mai gaskata abinda ya gabace shi kuma Ya saukar da Attaura da Linjila" Ali Imran: 3.
    Da kuma da dama makamantanta da ke nuna cewa Manzon Allah (S.A.W.A) da Alkur'ani sun zo suna masu gaskata Annabawa da shari'o'i da suka gabata.


    ( 130 )

    kubutarsu daga karya, kana kuma tana daga cikin al'amuran gaibi da suka ba da labari game da ita kuma aukuwarta ba gagara badau ba ne.




    ( 131 )

    33- Game da Takiyya.


    An ruwaito daga Imam Sadik -Sadiku AhlulBait- (A.S.) a sahihin hadisi cewa: "Takiyya addinina ce110 kuma addinin iyayena ce." Da kuma "Duk wanda babu takiyya gare shi babu addini gare Shi."111
    Kazalika haka nan ta kasance taken Ahlul Bait (A.S.) wajen kore cutar da su kansu da kuma ga mabiyansu don kare jininsu sa'an nan da kawo gyara ga halin da musulmi ke ciki da kuma hade kalmarsu da taro tsakaninsu.112
    ____________
    110- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 174 hadisi na 12, Mukhtasarul Basa'irud Darajat shafi na 101 da al-Mahasin Juzu'i na 1 shafi na 397 hadisi na 890.
    111- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 172 hadisi na 2, da kuma Al Fikhul Mansub ilal Imam Ridha (A.S.) shafi na 338.
    112- Takiyya ita ce boye gaskiya da suturce imani da ita, da boye wa wadanda ake da sabani da su, da rashin fitowa sarari gare su da abinda zai jawo cutarwa a addini ko a (abin) duniya. Kuma tana daga cikin abubuwan da wasu ke kin Shi'a saboda ita, domin jahiltar ma'anarta da suka yi da kuma guraren da ta dace da su da hakikaninta, idan da sun tsaya daidai sun dakanta sun yi hakuri sun hakarkur-kurtar da sun san cewa takiyya ba wai ta takaita kawai ga Shi'a ba ne kuma ba su kebantu da ita su kadai ba, sai dai ita aba ce La budda sai da ita a bisa hukuncin hankali kuma a kanta dabi'un dan Adam suka tattara, hankali kuma shi mai mata jagora ne ilimi kuma shi ne mai kula da ita kuma ba'a taba rabuwa da su biyun koda gwargwadon kiftawar ido, domin kowane mutum dabi'arsa ne ya kare kansa ya kiyaye rayuwarsa.
    Sahihul I'itikad daga Musannafatu Shaikh Mufid Juzu'i na 5 shafi na 137, Aslus Shi'a wa Usuliha shafi na 315, Waki'ut Takiyya indal Mazahib wal Firakil Islamiyya wadanda ba Shi'a Imamiyya ba, na Sayyid Samir Amidi, a ciki akwai bayani game da takiyya da kuma cewa batu game da ita bai kebanta ga Shi'a Imamiyya ba kawai.


    ( 132 )


    Kuma Mazhabar Shi'a Imamiyya ba ta gushe ba ana saninta da takiyya ba kamar sauran jama'o'i da al'ummu ba, dukkan mutum kuma idan ya ga alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yada abinda ya yi imani da shi ko kuma fito da shi sarari babu makawa ya boye ya kare a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi'ar hankali ke hukunci da shi.
    Abu ne sananne cewa Mazhabar Shi'a Imamiyya da Imamansu sun sha nau'o'in jarrabawa da matsa lamba da babu wata jama'a113 da ta sha irinta. Saboda haka ne ya zamanto tilas gare su a yawancin lokuta su yi takiyya suna masu boye wa masu sabani da su, da kuma barin bayyana hakikanin abinda bayyanarwar ke jawowa a addini da kuma duniya. Saboda wannan ne suka bambantu daga wadanda ba su takiyya kuma aka san su da ita banda wasunsu.
    Takiyya tana da hukunce-hukunce dangane da wajabcinta da rashin wajabcinta gwargwado sassabawan guraren tsoron cutarwar kamar yadda aka ambata a littafan malaman fikihu.
    Takiyya ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya halatta kuma saba mata kan wajaba a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiya da fitowa da ita sarari ya zama taimako ne ga addinin musulunci da jihadi a tafarkinsa, to a wannan lokacin sai a yi banza da dukiya kuma ba za a fifita rai ba.
    Takiyya na iya zama haram114 a ayyukan da ka iya wajabta115 kashe rayuka masu alfarma ko kuma yada karya, ko barna a addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su ko kuma yada zalunci da ja'irci a tsakaninsu.


    ____________
    113- As- Shi'atu wal Hakimun, Shaikh Muhammad Jawad Mugniya.
    114- Domin ya zo daga Imam Bakir (A.S.): "An sanya takiyya ne domin a kare jini da ita idan kuwa har ta kai ga jini to ba takiyya ba ce." Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na ll shafi na483 hadisi na 1.
    115- Domin hadisi ya zo daga Imam Ridha (A.S.) "Don an sanya takiyya don kare jini ne kawai idan har ta kai ga jini to ba takiyya ba ce."


    ( 133 )


    Ko ta halin kaka dai takiyya a gurin Shi'a Imamiyya ba wai tana nufi zamar da su `yan wata kungiyar asiri ba ne domin aiwatar da rushe-rushe da ruguje-ruguje kamar yadda wasu daga cikin makiyan Shi'a marasa fahimtar al'amura ke surantawa kuma ba sa dora wa kansu nauyin su zo su san ingantaccen ra'ayin daga garemu.1l6
    Kamar kuma yadda ma'anarta ba ita ce a sanya addini ya zama wani sirri daga asirran da bai halatta a bayyana shi ba ga wanda bai dauke shi a matsayin addini ba, ta yaya zai zamanto haka alhali littafan mazhabar Imamiyya da rubuce-rubucensu dangane da fikihu da hukunce-hukunce bayanai game da akida sun game duniya, sun ma wuce yadda ake tsammani daga kowace al'umma da ke bin addininta?
    E, gaskiya ce makiyanmu da ke nufin kiyayya da Shi'a sun munana amfani da takiyya sun sanya ta daya daga cikin abubuwan soke-soke ga Shi'a, tamkar ka ce ba sa wadatuwa har sai dai in an sassare wuyansu domin a ga bayansu baki daya a wancan zamanin da cewa mutum Shi'a ne kawai ya isa ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Bait daga Umayyawa da Abbasawa hatta zuwa Zamanin daular Usmaniyya.
    Idan sukan mai suka ya dogara ne da abinda yake zaton cewa suka ba halas bane a addini to sai mu ce masa:
    Na Farko: Mu dai masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S.) mu muna bin shiriyarsu ne su ne suka umarce mu da ita, kuma su ne suka farlanta ta a kanmu a lokacin bukata, kuma ita tana daga addini a gurinsu kuma lalle ka ji hadisin Imam Sadik (A.S.) da yake cewa: "Duk wanda babu takiyya gare shi babu addini gare Shi."
    Na Biyu: Shar'anta ta kuma ya zo a Alkur'nai mai girma, wato fadar Allah Ta'ala cewa: "Sai dai wanda aka tilasta shi zuciyarsa kuwa tana natse da imani." Surar Nahli: 106.
    Wannan aya ta sauka ne game da Ammar bin Yasir wanda ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan musulunci.


    ____________
    116- Ta'alikin kausari a littafin Isfirayini, Attabsira fida din shafi na 185 da kuma Nash'atul Ash'ariyya wa Tatawwuriha shafi na 87-88.


    ( 134 )


    Da kuna fadin Allah Ta'ala: "Sai dai in kuka ji tsoron su don kariya." Surar Ali Imran: 28.
    Da kuma: "Kuma wani mutum daga mutanen fir'auna yana mai boye Imaninsa Ya ce." Surar Gafir: 28.





    Koma Ga Fehrisan Littafin



    Koma ga Shafin Littattafai