( 135 )
FASALI NA HUDU.
ABUBUWAN DA AHLUL BAIT SUKA
LADABTAR DA MABIYANSU DA SU.
Imaninmu Game da Addu'a:
Addu'o'in Sahifatus Sajjadiyya.
Ziyartar Kaburbura.
Ma'anar Shi'anci A Gurin Ahlul Bait (A.S.).
Ja'irci da Zalunci.
Taimakekeniya da Azzalumai.
Aiki a Hukuma Azzalumai.
Kira Zuwa Ga Hadin Kai.
Hakkin Musulmi a kan Musulmi
( 136 )
( 137 )
Shimfida:

Lalle Imamai daga Ahlul Bait (A.S.) sun sani sarai tuntuni cewa hukumarsu ba za ta taba dawowa hannunsu ba a rayuwarsu da kuma cewa mabiyansu za su ci gaba da zama a karkashin shugabanni ba su ba, wadanda suke ganin babu makawa a kashe su da dukkan wata hanyar gwada karfi da tsanantawa.

Don haka a bisa dabia- a bangare guda- su yi sirrance, "Takiyya" a addini da al'ada ga su kansu da kuma mabiyansu matukar dai takiyyar tana kare masu
jininsu kuma ba ta munanawa ga wasu da kuma addini, saboda su iya ci gaba da wanzuwa a cikin wannan husuma mai ruruwa da fitina, da neman ramuwar gayya ta kiyayya a kan Ahlul Bait (A.S.).

Saboda haka a bisa hukunci na kasancewarsu Imamai babu makawa su-a daya bangaren- su koma ga cusa wa mabiyansu hukunce-hukuncen Shari'ar Musulunci, da kuma fuskantar da su fuskantarwa ta addini sahihi, da kuma shiga da su tafarkin zaman jama'a mai amfani tare da kusantar da su ga Allah, da tsarkake zukatansu daga sabo da kaskanci don zamar da su adalai masu gaskiya.

Magana game da "takiyya" ta riga ta gabata kuma tana daga cikin wadannan ladubba masu amfani a halin zaman jama'a. A nan za mu ambata wasu daga cikin wadannan ladubban da suka shafe mu.
( 138 )
34- Imaninmu Game da Addu'a

Manzon Allah (S.A.W.A) Ya ce:

"Addu'a makamin Mumini ce, kuma jigo addini sa'an kuma hasken sammai da kasa ce."
117

Kazalika ta zamanto daga abubuwan da shi'a suka kebantu da su na musamman kuma sun rurrubuta littafa a kan falalarta da ladubbanta kuma a addu'o'in da aka ruwaito su daga Ahlul Bait sun kai littattafa da dama, mayalwatansu da takaitattunsu. A cikin wadannan littafan akwai abubuwan da aka kawo da ke nuna cewa Annabi (S.A.W.A.) da Ahlul Bait (A.S.) suna zaburar da musulmi da kwadaitar da su ga addu'a hatta ya zo daga gare su cewa: "Ibada mafifciya ita ce addu'a.
118 Da kuma cewa:"Aikin da yake mafi soyuwa a gurin Allah shi ne addu'a."
119

Hakaza ya zo cewa: "Lalle addu'a tana kore kaddara da bala'i."
120 Da kuma cewa "Addu'a ita ce maganin dukkan cuta. "
121

Har ila yau ya zo cewa Amirul Muminin Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya kasance Mutum ne ma'abucin addu'a Wato mai yawan addu'a hakan nan kuwa ya kamata ya kasance saboda kasancewarsa shi ne shugaban masu tauhidi kuma shugaban mabiya ubangiji. Addu'o'insa
____________
117- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 339 hadisi na 1 .
118- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 338 cikin hadisi na 1.
119- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 339 hadisi na 8.
120- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 341 hadisi na 1-8.
121- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi ha 341 hadisi na 1.
( 139 )
sun zama tamkar hudubobinsa a matsayin ayoyi daga fasahar Larabci ne kamar shahararriyar addu'ar Kumail Bin Ziyad
122 wadda ta kunshi ilimin sanin ubangiji fuskantarwar addini da kuma abinda ya dace ya zamanto madaukakin tafarki ga sahihin musulmi.

Alal hakika lalle addu'o'in da aka kawo daga Annabi (S.A.W.A) da Ahlul Bait (A.S.) su ne mafificin tsarin rayuwa ga musulmi idan ya yi tuntuntuni a kansu, sukan cusa masa karfin imani da karfin akida da ruhin sadaukar da kai a kan gaskiya, kuma tana sanar da shi sirrin ibada da dadin Zance da Allah Ta'ala da yankewa daga kome zuwa gare shi, da kuma cusa masa abinda ya wajaba a kan mutum ya aikata ga Allah Ta'ala sosai; ya kuma nesanta shi daga barna da son rai da bidi'a da bata.

A takaice dai wadannan addu'o'in takaitacciyar sani ne na addini ta fuskar kyawawan dabi'u da gyara zukata da kuma nahiyar akidar Musulunci bil hasali ma dai ita tana daga cikin muhimman madogarar ra'ayoyin falsafa, da binciken ilimi dangane da sanin ubangiji da kyawawan dabi'u.

Idan da mutane sun iya - kuma ba dukansu ne masu iyawa ba,- da sun shiriya da shiryarwar da wadannan addu'o'in ke tasowa da ita a cikin madaukakin abinda ta kunsa to da ba za ka sami irin wannan fasadin da kasa ke cike da ita ba. Kuma da wadannan rayukan da sharri ya daure su, da sun yi shawagi a sammai na Allah Ta'ala cikin `yanci da walwala.

Saidai ina ma dan Adam zai samu ya saurari kalmar salihai da masu kira zuwa ga gaskiya. Hakika fadar Allah a wannan aya ta bayyana hakikanin mutane inda Allah ke cewa:
____________
122- Addu'a ce wadda Amirul Mumini Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya koya wa Kumail Bin Ziyad Annakha'iy (R.A.) kuma ita ce addu'ar da ake kira addu'ar Khizru (A.S.) Kuma an sanya mata suna Addu'ar Kumail Ibin Ziyad- wanda daya ne daga cikin kebabbun Imam Ali (A.S.) da Imam Hasan (A.S.) ne wanda kuma ya ce ya karanta ta yana cikin sujada da daren rabin watan Sha'aban da daren kowace Juma'a, ko kuma sau daya a wata ko sau daya a shekara ko sau daya a rayuwa. A duba Misbahul Mutahajjid shafi na 844 da Al-Misbah na Kafami Juzu'i na 2 shafi na 282.
( 140 )
"Lallai zuciya tabbas mai umarni da mummuna ce." Surar Yusuf: 53.
"Kuma yawancin mutane ba masu shiryuwa ba ne ko da kayi kwadayi". Surar Yusufi: 103.

Na'am lalle kankamar mummunan aiki a zuciyar mutum shi ne rudin kansa da kansa da jahiltar mumumunan aikinsa da gangan da yaudarar kansa cewa shi yana aikata kyakkyawan aiki ne, don haka yake zalunci yana ketare iyaka, ya yi karya, ya yi kage, ya bi sha'awarsa yadda ransa yake so, amma tare da haka yana yaudarar kansa da cewa shi bai yi kome ba face abinda ya dace ya aikata, ko kuma ya runtse da gangan a kan mummunan da ya aikata yana kuma kaskantar da kuskurensa da kansa.

Su wadannan addu'o'in daga hadisai da ke samun karfafa daga tushen wahayi suna kokari ne su sa mutum ya koyi zargin kansa, ya juya ga Allah Ta'ala, domin su cusa masa ikrari da kuskurensa da kuma cewa shi mai aikata zunubi ne wanda ya wajaba a kansa ya katse kome ya juya ga Allah Ta'la domin neman tuba da gafara; kuma domin ya shafe guraren rudi da na laifi a zuciyarsa, wato kamar misali ya ce yana mai addu'a daga cikin Addu'ar Kumail:

"Ya Ubangijina, Ya Majibincina, ashe Za ka gudanar da hukunci a kaina a kan abinda na bi son raina a cikinsa, kuma ban kiyaye kawatawar abokin gabata ba a cikinsa, don haka ya rude ni da abinda ya so, kuma hukuncinKa ya taimake shi a kan haka, har na ketare wasu daga cikin dokokinKa da abinda ya gudana gare ni na daga haka, kuma na saba wa wasun umarce-umarcenKa."
123

Babu shakka cewa misalin irin wannan ikrarin a cikin kadaici ya fi sauki ga mutum a kan ikarari a cikin jama'a koda kuwa yana daga cikin mafi tsanani halaye a kan zuciya kawai, idan kuwa tsakaninsa da kansa daga shi sai shi a kadaice, kuma idan hakan ya tabbata ga mutum to lalle yana da al'amari mai girma wajen rangwamta
____________
123- Da ga Littafin Mishabul Mujtahid shafi na 844 Du'a'ul Kumail.
( 141 )
zurfafawar zuciyarsa masharraciya da kuma horar da ita a kan neman alheri.

Duk wanda yake son tarbiyyar zuciyarsa to babu makawa ya koyar da ita kadaitaka da `yantaccen tunanin domin yi mata hisabi, kuma mafificiyar hanyar wannan kadaitakar da yi wa kai hisabin shi ne mutum ya dukufa a kan karanta wadannan addu'o'in da aka samo daga ruwayoyi wadanda ke ratsa zuciya da abinda ta kunsa, alal misali kamar ya karanta addu'ar Abi Hamza Simali (R.A.)
124.

"Ya Ubangiji Ka rufe ni da suturcewarKa, Ka yafe mini zargina da girman fuskarKa."

Yi tunani a kan wannan kalma, "Ka rufe ni" a cikinta akwai abinda ke tayar wa zuciya kwadayin suturce abinda ta tattara a kai na daga mummunan aiki, domin mutum ya fadaka, a kan wannan sashen na kunshe wanda kuma zai san haka idan ya karanta wannan addu'ar da ke biye daga bisani.
"Idan da yau wani baicin Kai ya san da zunubina to da ban aikata ba kuma da na tsoraci gaggauta ukuba da na nesanci zunubin".

Wannan irin ikrari daga cikin zuciya da kuma fadaka zuwa ga kwadayin suturce abinda yake da shi na daga munana yana tayar da kwadayin neman gafara da yafewa daga Allah Ta'ala don gudun kada ya tozarta shi a gurin mutane idan da Allah Ya so Ya yi masa ukuba a nan duniya ko kuma a lahira a kan ayyukansa, to mutum sai ya dandani dadin addu'ar asiri da zance da Allah a asirce, ya yanke ya koma ga Allah Ta'ala, ya yi godiya gare Shi, da Ya yi masa afuwa baicin Yana da kudura amma Bai fallasa shi ba yayin da yake cewa a addu'a bayan abinda ya gabata:
____________
124- Ita ce addu'ar da Abu Hamza Sumali ya ruwaito daga Imam Zainul Abidin (A.S.) ya ce ya kasance yana yana salla tsawon daren watan Azumi lokacin suhur sai ya karanta ta.
( 142 )
"To godiya ta tabbata gare Ka akan hakurinKa bayan saninKa da yafewarKa bayan kudurarKa."125

Sa'an nan kuma addu'ar ta sake biyar da ainihin wannan tafarkin na neman uzuri ga zuciya a kan abinda ta yi sakaci dangane da shi saboda wannan afuwa da hakuri daga gare Shi Allah Ta'ala, domin sadarwa tsakanin bawa da Ubangijinsa har ila yau kuma domin koya wa bawa cewa sabonsa ba wai don kafirce wa Allah ba ne ko kuma wulakanta Umarninsa yayin da yake cewa:

"Kuma hakurinKa gare ni yana dauka ta yana ja na zuwa ga saba maKa kuma suturcewarKa na kira na zuwa ga karancin jin kunya, kuma sanina game da yalwar rahamarKa da girman afuwarKa yana gaggautar da ni zuwa ga kifuwa a kan abubuwan da ka haramta."

Wannan shi ne tsarin salon addu'ar asirce ta tarbiyyantar da zukata, da sabar musu da da'a da barin aikata sabo.

Wannan littafi ba zai wadatar ba in kawo irin wadannan misalai fiye da haka kuma suna da yawan gaske amma kuma yana kayatar da ni in kawo wasu misalan addu'o'in salon kafa hujja gaba ga Allah Ta'ala domin neman afuwa da gafara kamar dai yadda kuke karantawa a addu'ar Kumail Bin Ziyad:

"Kuma kaitan sanina, Ya shugabana, Ya majibincina, ashe Ka sanya wuta a kan fuskokin da suka kifu ga girmanKa suna masu sujada, da kuma a kan harsunan da suka yi furuci da kadaitakarKa suna masu gaskiya, sannan kuma da godiyarKa suna masu yabo, da kuma a kan zukata da suka kewaye ilimi game da kai har suka zamanto masu tsoro, da kuma a kan gabobi da suka yi kokari zuwa guraren ibadarKa da son ransu, suka kuma yi ishara ga afuwarKa suna masu mika wuya? Ba haka zato yake game da Kai ba, ba kuma mune muka fi sanin falalarka ba."
____________
125- Haka ya zo a Misbahul Mutahajjid Shafi na 582 da Al- Misbahu na Kafami Juzu'i na 2 shafi na 345.
( 143 )

Ka maimaita karanta wannan bangaren sa'annan ka yi tunani game da taushin wannan irin kafa hujjar da kololuwar fasaharsa da azancin bayaninsa. A halin tana sanya wa zuciya ikrari da kwauronta a ibada har ila yau kuma tana cusa mata rashin debe tsammani daga rahamar Allah da baiwarSa, sa'annan kuma tana yi wa zuciya magana da zance irin na tausasawa wani bangare a boye domin ya cusa mata madaukakan wajibanta, domin tana kaddara cewa ita dama ta riga ta ba da wadannan wajibai baki daya. Sa'an nan kuma tana koya wa mutum cewa da wadannan ayyukan ya cancanci fifitawa daga Allah ta hanyar gafartawa, wannan kuwa wani abu ne da kan zaburar da mutum ya koma ga zuciyarsa don ya aikata abinda ya wajaba a kansa ya aikata idan har bai aikata shi ba.

Karanta wani salon addu'ar da a ke neman uzuri a ci gaba da wannan addu'ar har wa yau: "To Ka sani ina iya hakuri Ya ubangijina Ya shugabana majibincina a kan azabarKa amma ta yaya zan yi hakuri a kan rabuwa da Kai, kuma ko da na iya hakuri a kan zafin wutarKa amma yaya zani yi hakuri a kan rashin dubi zuwa ga girmanKa."

Wannan wani irin cusa wa zuciya jin dadin samun kusanci ga Allah Ta'ala da halartar karamcinsa, da kudurarsa ne don soyayya gare shi da kuma cewa wannan irinn jin dadin ya kamata ne ya kai ga darajar da tasirinta da ta bari a kan zuciya ya fi azaba da zafin wuta girma. Idan muka kaddara cewa mutum na iya jure zafin wuta to da ba zai iya hakuri a kari waccan rabuwar ba kamar kuma yadda daga wannan bangaren addu'ar za a fahimci cewa wannan soyayyar da jin dadin na kusaci da abin kauna, abin bauta shi ne mafificin mai ceto ga mai zunubi a gurin Allah yadda Zai yafe Ya shafe masa.

Wannan dadin salo ba zai buya ba daga jin mamaki da kankan da kai ga Mai girma, Mai Hakuri, Mai karbar tuba, Mai gafarta zunubi.

Babu Laifi mu rufe wannan bayani da kawo takaitacciyar addu'a da ta kunshi kyawawan dabi'u da kuma abinda ya kamata kowane yanki na mutum da kuma nau'insa ya kamata ya siffantu da su na daga siffofi ababan yabo:
( 144 )

"Ya Allah Ka arzuta mu da muwafakar da'a da nesantar sabo, da gaskiyar niyya, da sanin abubuwa masu alfarma kuma Ka girmama mu da shiriya da tsayuwa daidai da daidaita harsunanmu da daidaito da hikima Ka cika zukatanmu da ilimi da sani, Ka tsarkake cikkunanmu daga haramiya, da kuma gauraye-gauraye, Ka kame hannauwanmu daga zalunci da sata, Ka runtsar da idandunanmu daga fajirci da ha'inci, Ka toshe kunnuwanmu daga jin hululu da giba, kuma Ka yi falala ga malamanmu da zuhudu da nasiha, ga masu neman ilimi kuma da kokari da shauki, ga masu sauraro kuma da biyayya da wa'aztuwa. Ga marasa lafiyar musulmi kuma da waraka da hutawa, ga matasansu kuma da rangwame da rahama.

Ga tsofaffinmu kuma da natsuwa da kwanciyar hankali, ga matasanmu kuma da komowa da yawan tuba ga matanmu kuma da jin kunya da kamewa, ga mawadatanmu kuma da kankan da kai da yalwatawa, ga matalauta kuma da hakuri da wadar zuci.

Ga mayaka kuma da cin nasara da galaba, ga kamanmun yaki kuma da kubuta da hutawa, ga shugabanni kuma da adalci da tausayawa, ga makiyaya kuma da yin daidai da kyawun hali.

Ka sanya albarka ga mahajjata da masu ziyara a guzuri da ciyarwa. kuma Ka hukunta abinda Ka wajabta masu na daga Hajji da Umara. Don falalarKa da rahamarKa, Ya mafi rahamar masu rahama."
126

Kuma ni ina mai wasiyya ga 'Yan'uwana masu karatu da cewa kada damar karanta wannan addu'a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tuntuntuni a kan ma'anoninta da abubuwan da take nufi tare da halarto da zuciya da fuskantowa da juyowa ga Allah da tsoro da kankan da kai da kuma karanta ta tamkar daga shiftarsa take domin bayyana kansa da ita, tare kuma da bin ladubban da aka ambata mata daga Ahlul Bait (A.S.). Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to zakin baki ne kawai kuma ba ya kara wa mutum sani, ba ya sama masa kusaci, kuma ba a yaye masa tsanani ba a amsa masa addu'a da shi.
____________
126- Al- Baladul Amin shafi na 349.

"Lalle Allah Mai girma da buwaya ba Ya amsa addu'a daga zuciya dulmiyayyiya, don haka idan kuka yi addu'a ku yi da fuskantowar zuciya sa'an nan ku jicewa lalle Za a amsa."
( 146 )
35- Addu'o'in Sahifatus Sajjadiyya

Bayan aukuwar al'amarin Karbala mai ban takaici
121 da kuma kame ragamar shugabancin al'ummar musulmi da Banu Umayya suka yi kuma suka dulmuya a cikin danniya, suka yi dumu-dumu da jinin mutane, sa'an nan suka yi watsi da koyarwar addini sai Imam Zainul Abidin (A.S.) wato Sayyiddus Sajidin Ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici. Yana gida babu wani mai kusatarsa kamar yadda ba zai iya yada wa mutane abinda ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba na addini.

Don haka ala tilas ya zama babu makawa gare shi ya dauki salon addu'a wanda muka ambata da cewa yana daga cikin hanyoyin koyarwa da ladabtar da zukata ya rike shi a matsayin hanyar yada koyarwar Alkur'ani da ladubban musulunci da kuma sanar da tafarkin Ahlul Bait (A.S.) da kuma hanyar cusa wa mutane ruhin addini da zuhudu da kuma abinda ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi'u.

Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar wa mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da ke matsa masa ba, ba kuma za su iya kafa masa wata hujja ba. Don haka ne yawancin
____________
127- Wato al'amarin da ya kai ga shahadar Imam Abu Abdullahi Husain Bin Ali (A.S.) ranar goma da watan Al-Muharram a shekara ta 61 bayan hijira tare da zababbun sahabbansa a Karbala a Iraki, babu wani da ya saura daga cikinsu sai Imam Sajjad wato Aliyu Bin Husain (A.S.)... Wannan Shi ne mafi tashin hankalin al'amarin da ya auku a farkon tarihin musulunci. Marubuta tarihi da Malaman hadisai sun kawo shi a ko'ina da kuma malaman hadisi da kuma a wake-wake daban-daban. An nuna mafi kolin matsayin kariya ga akida.
( 147 )
Wadannan addu'o'i masu zurfi an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya wanda ake yi wa lakabi da "Zaburar Zuriyar Muhammadu (S.A.W.A)" salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, da mafi ingancin asirran tauhidi da Annabci da kuma mafi ingancin hanyar koyar wa da kyawawan dabi'u ababan yabo da kuma ladubban musulunci.

Wadannan addu'o'in sun shafi al'amura dabam-daban ne na tarbiyya ta addini ta shafi koyarwar addini da kyawawan dabi'u ta hanyar addu'a, ko kuma addu'a ce amma da salon koyar da addini da kuma kyawawan dabi'u. Alal hakika bayan Alkur'ani da Littafin Nahjul Balagha wannan Littafin addu'o'in shi ne salon bayanin Larabci mafifici kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi'u. Daga cikinsu akwai wanda ke sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake Shi, kana kuma ka yi hamdala ka yi wa Allah godiya, daga bisani ka tuba gareShi.

Daga ciki akwai wadda ke sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah, kuma ka kadaita da kai ga Ubangijinka kana mai bayyana Masa asirinka sannan ka zabura zuwa gare Shi.

Daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma'anar Salati ga Annabi (S.A.W.A) da Manzannin Allah da zababbunSa daga cikin halittunSa da yadda za ka yi da Shi.

Daga cikinsu akwai wadanda za su fahimtar da kai abinda ya dace ka bi iyayenka da shi.

Kazalika akwai wadanda ke maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa, ko kuma hakkokin makwantai, ko wadanda kuke ciki daya, ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka.
l28

Daga cikin addu'o'in akwai wanda zai fadakar da kai kan abinda ya wajaba na basussukan mutane akan ka, da kuma abinda ya kamata ka aikata akan lamurran kafi da tattalinsu, haka na da abinda ya kamata
____________
I28- Addu'a ta 24 da 25 da 26. Addu'arsa ga Mahaifansa da addu'arsa ga dansa da kuma addu'arsa ga makwabtansa.
( 148 )
kayi mu'amala da shi tsakaninka da masu hulda da sauran abokanka da kuma mutane baki daya, har yanzu akwai wanda zai gwada maka irin mutanen da za ka iya hulda da su domin amfanin kan ka.

Daga cikinsu akwai wadanda suke hado maka dukkan manyan halayen kwarai da za sa su iya zama cikakken tsari na ilimin kyautata dabi'u.

Daga cikinsu akwai wadanda za su koya maka yadda za ka yi hakuri a kan munanan abubuwa da ke aukuwa da kuma yadda za ka yi yayin da kake ciwo da kuma yayin da kake kalau.
l29

Daga cikinsu akwai wadanda ke maka sharhin wajiban sojojin musulunci da wajiban mutane dangane da su
130... da dai sauran wadannan da kyawawan dabi'u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu'a kawai.

Bayyanannun al'amuran da ke fitowa fili a addu'o'in Imam sun kasu kamar haka:- Na farko:

Sanin Allah Ta'ala da girman kudurarSa da bayanin kadaita Shi, da tsarkake Shi, da mafi dacewar ma'anoni na ilimi, wannan kuwa yana maimaituwa ne a kowace addu'a ta salo dabam-daban kamar yadda kake karantawa a addu'a ta farko:

"Godiya ta tabbata ga Allah na farko wanda babu wani na farko da Ya kasance kafin Shi, Na karshen da babu wani na karshe da zai kasance baicin Shi Wanda idandunan masu gani suka gaza ganinSa, wahamce - wahamcen masu sifance - sifance kuma suka gajiya wajen siffanta Shi. Ya fari halittu da kudurarSa a farkon farawa Ya kuma kago su kamar yadda Ya so kagowa."
131

Karanta ma'ana ta farko da kyau kuma ka yi tunani a kanta za ka tsarkake Allah Ta'ala daga kasancewarSa wani ya zamanto ya gewaye
____________
129 - Addu'a ta 15 addu'arsa yayin rashin lafiya.
130-
131- Addu'a ta 15 Addu'arsa yayin rashin lafiya.
( 149 )
da gani ko da wahami, da kuma ginin ingancin ma'anar halitta da kuma halittar duniya baki daya.

Daga nan kuma ka karanta wani salon wajen bayyana kudurar Allah Ta'ala da yin tuntuni a addu'a ta 6:

"Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta dare da rana da karfinSa, Ya rarrabe tsakaninsu da kudurarSa, Ya sanya ga kowane daga cikinsu su biyun iyaka ayyananniya, Yana shigar da kowane daya daga cikinsu a cikin dan'uwansa a cikinsa da kaddarawarsa ga bayi a cikin abinda yake ciyar da su kuma Yake sanya su su girma. Don haka Ya halitta musu dare ne domin su huta wahalar kaiwa da komowa da dawainiya kuma Ya sanya shi sutura da za su suturtu da kwanciyarsu da natsuwarsa domin hakan ya zama musu wartsakewa da kara samun karfi kuma domin su kara samun jin dadi da sha'awa."
132 Har zuwa karshen abubuwan da ya ambata na fa'idar halittar rana da dare da kuma abinda ya kamata mutum ya yi godiyarsa daga wannan ni'imar.

A wani salon kuma na bayanin dukkan al'amura ga Allah Ta'ala suke za ka karanta a addu'a ta 7 cewa:

"Ya wanda da Shi ne kulle-kullen munanan abubuwa ke suncewa, Ya wanda da shi ne kaifin tsanani ke duskurewa, Ya wanda daga gare Shi ake rokon mafita zuwa tsantsan sauki mawuyatan al'amura na rusunawa ga kudurarKa, sabubba kuma sun samu ne da tausasawarKa, kaddarawarKa kuma ta gudana ne a bisa iradarKa, su da iradarKa suke bin umarninKa, kuma masu umartuwa da maganarKa ne kuma da iradarKa ne suke tsawatuwa da haninKa."
133

Na Biyu:
Bayani game da falalar Allah ga bawanSa, da kuma gazawar bawa wajen bayar da hakkin Allah Ta'ala kome abinda ya yi na da'a da ibada kuwa da kuma yankuwa don juyawa ga Allah kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 37:
____________
132- Addu'a ta 6, addu'arsa da Asuba.
133- Addu'a ta 7, a ddu'arsa yayin da wasu muhimman al'amurra suka auku ko yayin tsanani.
( 150 )
Ya Allah lalle babu wani da zai kai ga matukar godiya gare Ka face wata kyautatawarKa ta same shi wadda za ta sake lizimta masa wata godiyar. Kuma ba ya kaiwa ga matukar da'arKa koda kuwa ya dage face ya gaza yin yadda Ka cancanta a kan falalarKa, Mafificin mai godiya gare Ka a bayinka ya gaza a kan godiyarKa, kuma mafi bautarsu mai kwauro ne a bautarKa."

Saboda girman ni'imomin Allah Ta'ala a kan bawanSa bawan ya yi kadan ya ba da hakkinSa komai kokarin da ya yi kuwa.

To yaya kuma idan har ya sabe Shi yana mai tsaurin kai, yayin nan kuma ba zai taba iya kankare sabo koda guda daya ba, kuma wannan shi ne abinda yankin addu'ar da ke biye a addu'a ta 16 ke nunawa:

"Ya Ubangijina idan da zan yi kuka har fatar idona ta zagwanye, kuma na yi kururuwa har muryata ta dushe, kuma na tsaya gare Ka har kafafuwana su tsattsage kuma na yi maka sujada har kwayar idandunana su faffado, kuma na ci turbayar kasa duk tsawon rayuwata kuma na sha ruwan toka har zuwa karshen zamanina sa'an nan na yi ta ambaton ka duk tsawon wannan lokacin har sai harshena ya gaza, sa'an nan kuma na zama ban taba daga ganina na dubi sama ba don jin kunyar ka, duk wannan ba zai wajabta shafe mini mummunan aiki daya daga miyagun ayyukana ba."
134

Na uku:

Sanar da lada da ukuba da aljanna da wuta da kuma cewa ladan Allah dukkaninsa kyauta ce kawai kuma bawa ya cancanci azaba ne da zarar aikata sabo guda daya kawai da ya yi tsaurin idon aikatawa, Kuma Allah na da hujja a kansa game da haka.

Kuma dukkan addu'o'in Sahifatus Sajjaddiya na ambata wannan ukubar mai tasiri domin samar wa zuciya tsoron ukubar Allah Ta'ala da sanya mata sa tsammani da ladan Allah Ta'ala. Dukkanta shaida ce a kan haka ta salo mafifici da ke sa wa zuciya mai tuntuni tsoro da firgita kan kama hanyar sabo, wato kamar abinda za ka karanta a addu'a ta 46:
____________
134- Addu'a ta goma sha shida.
( 151 )

Hujjarka tabatacciya ce ba za ta shafu ba, Shugabancinka tsayayye ne ba ya ciruwa, don haka tsananin azaba madawwami ya tabbata ga wanda ya nesance Ka, tabewar tozartuwa ta tabbata ga wanda ya karkace daga gare Ka, tsiyacewar tsiyata ta tabbata ga wanda ya rudu ya bar Ka, jujjuyawarsa a azabarKa ta yawaita, taraddudinsa a cikin ukubarKa ya yawaita, bukatarsa ga samun budi ta kai matuka, debe tsammaninsa ga samun mafita mai sauki ya tsawaita, Adalci ne daga hukuncinKa ba Ka zalunci a cikinsa, da kuma yin daidai a hukuncinKa ba ya kaucewa, lalle Ka bayyanar da hujjoji kuma Ka jarraba uzurori."
135

Da kuma kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 31.

"Ya Allah Kaji kan kadaitakata a gaban Ka, da kidimewar zuciyata daga tsoronKa da firgicewar gabobina don haibarKa, kuma lalle Ya Ubangijina zunubina ya sanya ni a matsayin kaskanci a gurinKa. Idan har na yi shiru babu wani da zai yi magana a madadina, idan kuma na nemi a cece ni to ni ban cancanci ceto ba."
136

Da kuma wadda kake karantawa a addu'a ta 39:

"Domin Kai idan har Ka saka mini daidai wadaida to za Ka halakar da ni. Idan kuma ba Ka lullube ni da rahamarKa ba to za Ka halakar da ni. Kuma ina rokon Ka Ka dauke daga zunubina wanda nauyinsa ya dankare ni. Kuma ina neman taimako da kai a kan abinda nauyinsa ya riga ya makure ni. Don haka Ka yi dadin tsira ga Muhammadu da zuriyarsa. Kuma Ka ba wa raina kansa saboda zaluncinsa ga ni kaina, kuma Ka wakilta rahamarKa wajen daukar nauyina."
137

Na Hudu:

Jan mai addu'a zuwa ga madaukakan matsayin ayyuka da kebantattun siffofi domin kyautata ruhinsa da tsarkake zuciyarsa ta
____________
135- Addu'a ta 46.
136- Addu'a ta 31.
137- Addu'a ta 39.
( 152 )
hanyar karanta wannan addu'ar kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 20:

"Ya Allah Ka kammala min niyyata da tausasaawarKa, kuma Ka inganta mini niyyata da abinda ke gare Ka, kuma Ka gyara mini abinda ya baci daga gare ni da kudurarKa, ...Ya Allah Ka yi dadin tsira ga Muhammadu da zuriyar Muhammadu Ka jiyar mini dadi daga shiriya ingantacciya wadda ba zan taba neman musayenta ba, da kuma hanya ta gaskiya wadda ba zan taba karkacewa daga kanta ba, da kuma niyyar shiriya daba zan taba kokwanto a kanta ba.

... Ya Allah Kada Ka bar wani hali da yake aibi gare ni face Ka gyare shi, ko kuma wani laifi da za a zarge ni da shi illa Ka kyautata shi. Ko kuma wani halin karimci da yake tauyayye gare ni har sai Ka cika Shi."

Na Biyar:

Sanya wa mai karanta addu'ar mutumta mutane da rashin kaskantar da su, da kuma cewa kada ya sanya bukatarsa a gurin wani ba Allah ba da kuma cewa kwadayin abinda ke hannun mutane na daga cikin mafi kaskancin abinda mutum zai siffantu da shi kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 20:

"Kuma kada Ka fitine ni da neman taimakon wani ba Kai ba idan na matsu da kuma kankan da kai don tambayar wani ba Kai ba idan na bukata, da kuma mika wuya gaba ga wanda ba Kai ba idan na tsorata, kada na zamanto na tozarta da hanawa da kau da kai ta yin haka."

Da kuma misalin addu'a ta 28:

"Ya Allah ni na tsarkake niyyata gare Ka duka, kuma na juyo zuwa gare Ka baki daya, kuma na juyar da fuskata daga dukkan ma'abucin taimakonKa, Na juyo da al'amarina daga dukkan wanda ba zai taba wadatuwa ya bar falalarKa ba, kuma na gane cewa bukatar mabukaci zuwa ga wani mabukacin wautar ra'ayinsa ne kuma bacewar hankalinsa ne."
( 153 )

Kazalika addu'a ta 13:

" Duk wanda ya yi kokarin magance rashinsa ta gurinKa kuma ya yi kokarin raba kansa da talauci da taimakonKa to lalle ya nemi abin bukatarsa a gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ya dace. Kuma duk wanda ya juya da bukatarsa zuwa ga daya daga cikin halittunKa, ko kuma ya sanya shi sababin cim mata ba kai ba , to lalle ya jawo wa kansa hani kuma ya cancanci kubucewar kyautatuwa daga gare Ka."

Na Shida:

Koya wa mutane wajabcin kiyaye hakkokin wasu, da taimaka musu da tausasawa gare su, da rangwame ga junansu, da sadaukarwa da tabbatar da ma'anar
'yan'uwantakar musulunci, kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 38:

" Ya Allah ni ina mai neman uzuri daga gare Ka a kan dukkan wani da aka zalunta a gabana amma ban taimake shi ba, da kuma wani kyakkawan abu da aka kwararo mini shi amma ban yi godiyarsa ba da kuma duk wani mabukaci da ya roke ni amma ban ba shi ba, da kuma daga hakkin duk wani ma'abucin hakki da ya hau kaina daga muminai amma ban cika mashi ba, da kuma daga dukkan wani aibi na mumini da ya bayyana gare ni amma ban suturce shi ba. "

Lalle wannan irin neman uzuri yana daga cikin mafi bayyanar abinda zai fadakar da zuciya zuwa ga abinda aikata shi ya kamata na wadannan kyawawan dabi'u madaukaka da Ubangiji Ya yarda da su.

A addu'a ta 39 akwai abinda ke bada karin haske a kan haka tare da lizimtar da kai yadda za ka yafe wa wanda ya munana maka yana kuma gargadinka game da yin ramuwar gayya yana kuma daukaka zuciyarka zuwa matsayin tsarkakuwa:

"Ya Allah duk wani bawa da ya cutar da ni da wani abu da ka haramta, kuma ya keta mini abinda Ka riga Ka hane shi a kai, kuma ya mace da zaluntata ko kuma ya auku a kaina daga gare shi yana rayayye, to Ka gafarta masa abinda yayi mini,
( 154 )
Ka yafe masa abinda ya riga ya aukar ya wuce daga gare ni, kada ka dakatar da shi da tambaya a kan abinda ya aikata a kaina, kuma kada ka tona asirinsa a kan abinda ya aikata a kaina, kuma ka sanya rangwamen da na yi masa na afuwa gare su da kuma sallamawar da na yi musu na daga sadaka gare su ya zama sadakar masu sadaka, kuma mafi kololuwar sadarwar ma'abuta kusanci gare Ka. Kuma Ka musanya mini afuwata gare su da afuwarKa, da kuma addu'ata gare su rahamarKa, har ya zamanto kowane daya daga cikinmu ya rabonta da falalarKa ya kuma samu tsira saboda baiwarKa."

Al'ajabin wannan yankin addu'ar da yawa yake, kyawun tasiri da shigarta zuciyar zababbu ya yawaita, don fadakar da su a kan lizimtar kyakkyawar niyya da dukkan mutane, da neman rabbonta ga kowa da kowa hatta ma wanda ya zalunce shi ya ketare masa haddi.
( 155 )
36 - Imanimu Game Da Ziyartar Kaburbura

Ziyartar kaburbura - kaburburan Annabi da na Imamai da katange su da kuma yin gine - gine a kansu na daga cikin manyan al'amura da mazhabar Shi'a Imamiyya (Masu bin Imamai 12) ta kebantu da su kuma suna bayar da dukkan abu mai tsada da mai sauki cikin imani da dadin zuciya.

Asalin duk wannan kuma shi ne wasiyyar Imamai da kuma zaburar da mabiyansu da kuma kwadaitar da su a kan irin ladan da take da shi mai yawa a gurin Allah Ta'ala,
138 saboda kasancewarta mafifiyar ayyukan biyayya da ibadu bayan ayyukan ibadu wajibai da kuma cewa wadannan kaburburan na daga cikin mafifitan guraren amsa addu'a da juyawa ga Allah Ta'ala.

Kuma suka sanya ta daga cikin ainihin cika alkawura ga Imamai, domin, "ga kowane Imami akwai alkawarinsa a kan majibintansa da mabiyansa, da kuwa cewa daga mafificin cika alkawari, ziyartar kaburburansu na daga mafi kyawun cikawa, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da kuma gaskata abinda suka kwadaitar a kai, to su Imaman nasu za su kasance masu ceto gare su ranar Alkiyama."
139
____________
138- Littafin Kamiluz Ziyarat hadisan da suka siffanta Ladan Ziyartar Kabarin Manzo (S.A.W.A) da na Imamai (A.S.).
139- Maganar Imam Ridha (A.S.), Kamiluz-Ziyarat Ibin Kaulawaihi shafi na 122 babi na 44, Ladan wanda ya ziyarci Imam Husain (A.S.); Kafi Juzu'i na 4 shafi na 467 hadisi na 2; Man La Yahduruhul Fakih Juzu'i na 2 shafi na 577 hadisi na 316; Tahzih 6. 78 h.3.
( 156 )

A cikin ziyarar kaburbura akwai fa'idoji na addini da zamantakewa da suka sa Imamanmu himmatuwa da ita, domin a halin cewa a lokacin da take kara kulla walaya da soyayya tsakanin Imaman da mabiyansu tana kuma sabunta tuna hadisansu da dabi'unsu da jihadinsu saboda gaskiya kuma tana hado kan musulmi wadanda suke a warwatse ta taro su guri guda, domin su san juna kana kuma ta dasa ruhin jawuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu da yankewa zuwa gare shi, da bin umarce-umarcenSa tana kuma cusa musu hakikanin tauhidi a cikin ma'anonin addu'o'in ziyarorin da ke cike da fasaha wadda aka samo daga Ahlul Bait (A.S.) tare da koya musu tsarkin musulunci da sakon Muhammadu (S.A.W.A) da abinda ya wajaba a kan musulmi na daga matabbatan halayen kwarai, da kankan da kai ga Mai tafi da halittu, da gode wa ni'imominSa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu'o'in da aka ruwaito wadanda bayaninsu ya riga ya gabata.

Hatta wadansunsu ma sun tattara ne a kan mafi zurfin addu'o'i da madaukakansu kamar ziyarar "Aminullah" wato "Amintaccen Allah" wadda aka ruwaito daga Imam Zainul Abidina (A.S.) yayin da ya ziyarci kabarin kakansa Amirul Muminin
140 (A.S.).

Kamar yadda wadannan ziyarorin da aka ruwaito suke fahimtar da matsayin Imamai (A.S.) da irin sadaukarwarsu a tafarkin taimakon gaskiya da daukaka kalmar addini da dagewarsu a ibadar Allah Ta'ala gashi kuma sun zo da salon larabci zalla, da fasaha madaukakiya, da ma'anoni masu sauki wadanda kowa da kowa yake fahimta, kuma suna kunshe da mafifitan ma'anonin tauhidi kuma mafi zurfi tare kuma da addu'a da yankewa zuwa gare shi Ta'ala.

Alal hakika ita tana daga cikin mafi ingancin laduban addini bayan Alkur'ani mai girma da Nahjul Balagha da kuma addu'o'in da aka ruwaito daga garesu (A.S.) domin a cikinta an kunsa dukkan sanin Imamai (A.S.) a takaice dangane da abinda ya shafi wannan sha'ani na addini da gyaran zuciya.
____________
140- Kamiluz Ziyarat shafi na 39 Babi na 11, ziyarar Kabarin Amirul Muminin.
( 157 )

Sa'an nan kuma a cikin ladubban ziyarar akwai koyarwa da shiryarwar da ke karfafa tabbatar da wadannan ma'anonin addini madaukaka wato irinsu daukaka tsarkin ruhin musulmi, da koya wa ruhinsa tausasawa ga fakiri, da sanya shi tausasawa ga fakiri, da iya zama da jama'a da kyawun hali, da son cudanya da jama'a, domin daga ladubanta akwai abinda ya kamata a aikata kafin a fara shiga cikin gurin makabartar domin ziyartarsa.

Daga nan kuma akwai abinda ya kamata a yi a tsakiyar ziyarar da kuma bayan ziyarar. A nan za mu kawo wasu daga cikin wadannan laduban domin fadakarwa a kan abubuwan da take nufi kamar yadda muka fada:

Daga Ladubbanta akwai:

1- Mai ziyarar ya yi wanka yayin fara ziyararsa ya tsarkaka,
141 fa'idar wannan kuwa kamar yadda muke fahimta a sarari yake, ita ce mutum ya tsarkake jikinsa daga kazanta domin ya kubutar da shi daga cututtuka da kuma domin kada mutane
l42 su gundara da warinsa kazalika kuma ya tsarkake kansa daga kazanta.

Ya zo a hadisai cewa mai ziyara ya karanta wannan addu'a idan ya gama wanka domin ya fadakar da shi a kan wadannan manufofi madaukaka ya ce:
"Ya Allah Ka sanya mani haske da tsarki gare, da kuma tsari wadatacce daga dukkan cuta da ciwo da kuma dukkan bala'i da musiba kuma Ka tsarkake zuciyata da gabobina da kashina da namana da jinina, da gashina da fatata, da bargona da kashina da kuma abinda kasa ta rage shi daga gare ni, kuma Ka sanya mai shaida gare ni ranar bukatata da fakircina da talaucina."
____________
141- Kamiluz Ziyarat shafi na 184 Babi na 75 daga cewa wanda ya yi wanka da ruwan Furat ya ziyarci Imam Husain (A.S.) 198 Babi na 79 ziyarar Imam Husain Bin Ali (A.S.).
142- Amirul Muminin (A.S.) ya ce "ku tsarkaku da ruwa daga mummunan wari kuma ku sabar wa kanku domin Allah yana fushi da bayinsa kazamai wadanda ke gundurar wadanda suka zauna tare da su." Tuhaful Ukul shafi na 24.
( 158 )

2- Ya sanya mafi kyawun da mafi tsaftar tufafin da yake da su, domin sanya kyawawa da tsaftatattun tufafi abu ne da mutane ke so wa junansu lokacin bukukuwa, kuma hakan na kusantar da su ga junansu tare da sanya soyayya a tsakaninsu, yana kara sa musu daukaka da jin daukaka a zuciyarsu da jin muhimmancin bukin da suke halarta.

Abu da ya kamata mu jawo hankali gare shi a wannan koyarwa shi ne ba a wajabta cewa dole ne mutum mai ziyara ya sanya mafi kyawun tufafi baki daya ba dungum, a'a sai dai ya sanya mafi kyawun abinda yake da iko a kai domin ba kowa ba ne zai iya yin haka, kuma akwai kuntatawa ga raunana wadda tausayawa ba ta bukatar a yi haka, wannan ladabin dai hakika ya gwama tsakanin abinda ya kamata na ado da kuma mafi kyawun tufafin, da kuma kiyaye yanayin fakiri da kuma mai rauni.

3- Ya sanya abinda ya saukaka gare shi na turare, kuma fa'idarsa tamkar ta sanya sabin kaya ce.

4- Ya yi sadaka da abinda ya saukaka gare shi, kuma fa'idar sadaka a irin wannan al'amari sananniya ce, domin a cikin hakan akwai taimakawa ga gajiyayyu da kuma sanya ruhin tausasawa gare su.

5- Ya tafi yana cikin natsuwa da kwanciyar hankali yana mai takaita ganin idonsa. Abinda ke cikin wannan irin natsuwar da girmama alfarmar wannan gurin da kuma wanda ake ziyarta din da kuma mai da hankali ga Allah Ta'ala da yankewa zuwa gare shi, da kuma abinda ke tare da haka din na nesantar damun mutane da matsa musu a yayin wucewa, da kuma rashin munanawa shashensu daga sashe a bayyane yake a sarari.

6- Ya yi kabbara yana cewa "Allahu Akbar" ya yi ta maimaitawa yadda ya so, kuma mai yiwuwa ne a wasu ziyarorin a kayyade kabbarar zuwa dari. Akwai fa'ida a cikin yin haka wadda ke sanya wa ruhi jin girman Allah Ta'ala, da kuma cewa babu wani abu da ya fi Shi girma, da kuma cewa ziyara ba wata aba ba ce illa ibadar Allah da girmama Shi da daukaka Shi ta hanyar raya alamun Allah da karfafa agginin Shi.
( 159 )

7- Bayan kammala ziyarar kuma ga Annabi ko kuma ga Imamai to sai ya yi salla akalla raka'a biyu nafila kuma domin ibada ga Allah kawai, saboda ya yi godiya a kan muwafakar da Ya yi masa ya kuma bayar da ladanta ga wanda ya kai wa ziyarar.

A cikin addu'ar da aka ruwaito wadda mai ziyarar zai karanta bayan wannan salla akwai abinda zai fahimtar wa mai ziyarar cewa wannan salla dai da duk abinda da ya aikata na Allah ne Shi kadai da kuma cewa shi ba ya bauta wa wani baicin Shi kuma ziyarar ba wata abu ba ce face wani nau'in neman kusanci gare Shi Ta'ala.

"Ya Allah gare Ka na yi Salla, gare Ka na yi ruku'u, gare Ka na yi sujada, Kai kadai ba Ka da abokin tarayya, domin babu salla da ruku'u da sujada sai dai gare Ka, domin Kai hakika ne Allah babu abin bautawa sai Kai. Ya Allah Ka yi dadin tsira ga Muhammaddu da zuriyar Muhammadu, kuma Ka karba mini ziyarata, kuma Ka ba ni abinda na roka, domin Muhammadu da zuriyarsa masu tsarki."

A cikin irin wannan addu'ar akwai wani nau'in ladabi da ke bayyana manufofin Imamai da mabiyansu masu koyi da su a ziyartar kabari ga duk wanda ke son ya san hakika, da kuma irin abinda masu jahilta ke kagawa yayin da suke raya cewa wai ziyartar kaburbura ibada ce gare su da neman kusanci gare su da kuma cewa shirka ce da Allah a ibada.

8- Daga ladubban ziyara akwai cewa:

Mai ziyarar ya lizimci kyanutata abota da duk wanda ya zama tare da shi, da kuma karanta magana, sai dai abinda yake alheri, da yawaita zikirin
l43 Allah, da kankan da kai, da yawaita salla, da salati ga Annabi Muahmmadu da Zuriyar Muhammadu kuma ya runtse idandunansa, kuma ya gaggauta zuwa gurin mabukata daga cikin yan'uwansa idan
____________
143- Abin nufi da zikirin Allah ba wai shi ne ka yi ta maimaita kabbara da tasbihi da makamantansu ba kawai sai dai adinda ake nufi shi ne kamar yadda Imam Sadik (A.S.) ya bayyana a tafsirin ayar zikirin Allah inda Ya ce: "Ni ba na cewa subhanallah walhamdulillah wa La ilaha illallah wallahu Akbar koda yake shi ma yana daga cikinsa amma Zikirin Allah shi ne a cikin kowane hali idan ka himmatu da da'a ko sabo."
( 160 )
ya ga abubuwa gare su sun yanke, kuma ya taimaka musu, ya kuma nesanci abinda aka hana, da kuma husuma, da yawaita rantsuwa da jayayyar da ta hada da rantse-rantse.
l44

Sa'an nan kuma alal hakika ziyara ba wata aba ba ce face salati ga Annabi ko kuma ga Imami saboda imani da cewa su "suna raye a gurin ubangijinsu ana arzuta su."
145 Don haka su suna jin magana kuma suna amsawa, kuma ya wadatar ka ce alal misali: "Assalamu Alaika Ya Rasulallah." ("Amince Ya tabbata gare ka Ya Manzon Allah".)

Sai dai kuma abinda ya fi shi ne ka karanta abinda aka ruwaito game da addu'o'in ziyara daga Ahlul Bait, Saboda abinda ke cikinta kamar yadda muka ambata na daga madaukakan manufofi, da kuma fa'idojin addini, da zurfin ma'anarsu da fasaharta da kuma abinda ke cikinta na daga addu'o'i masu zurfi da mutum yake juyawa ga Allah Ta'ala da su.
____________
144- Kamilluz Ziyarat shafi na 131 hadisi na 1.
145- Ishara ga aya ta 169 surar Ali Imran.
( 161 )
Imaninmu Game da Ma'anar Shi'anci a
Gurin Ahlul Bait (A.S.)

Imaman Ahlul Bait (A.S.) babu wata himma da suka kasance da ita bayan sun kawar da kansu daga sa ran dawowar al'amarin al'umma gare su face himmar gyara musulmi da tarbiyyantar da su tarbiyyar da ta dace kamar yadda Allah Ta'ala yake so daga gare su. Don haka su kasance tare da duk wani da yake bin su kuma suka hakikance da rashin tona asirinsu suna matukar kokarinsu wajen koya masa hukunce-hukuncen Shari'a, suna cusa masa ilimin Muhammadiyya, suna sanar da shi abinda yake nasa da kuma wanda yake kansa.

Ba sa daukar mutum cewa mabiyansu ne, daga Shi'awansu ne sai dai idan ya kasance mai bin Allah, mai nesantar son zuciyarsa mai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu.

Ba su daukar cewa soyayya gare su kawai ta wadatar wajen tsira, kamar yadda wasu ke gamsar da kansu daga cikin masu kage da bin sha'awace - sha'awace, kuma wadanda ke neman uzurin kangarewa biyayya ga Allah su Imamai, ba sa daukar soyayya gare su da biyayya ga shugabancinsu tsira ne sai dai idan an hada da kyawawan ayyuka, an kuma yi halin biyayya gare su da gaskiya da rikon amana, da tsoron Allah da takawa.

"Ya Khaisama ka isar ga mabiyanmu
146cewa ba za mu dauke masu komai ba daga Allah face da aiki, kuma su ba za su samu soyayyarmu ba sai da tsoron Allah, kuma lalle mafi hasarar mutane ranar Alkiyama
____________
146- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 64 hadisi na 12.
( 162 )
shi ne wanda ya siffanta adalci sannan kuma ya saba masa zuwa wani abu da ba shi ba."
147

Sai dai su suna son mabiyansu ne su zamanto masu kira zuwa ga gaskiya, masu shiryarwa zuwa ga alheri da rabonta kuma suna ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa "Ku kasance masu kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da tsoron Allah daga gare
l48 ku.

A halin yanzu za mu kawo maka wata muhawara da ta gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san tsananin himmatuwarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi'un mutane:

1- Muhawarar Abu Ja'afar Bakir (A.S.) da Jabir Ja'afi:

"Ya Jabir ashe wanda yake sanya wa kansa cewa shi Shi'a ne zai wadantu kawai da soyayya gare mu mu Ahlul Bait? To wallahi babu wani Shi'a mai bin mu sai dai wanda yaji tsoron Allah ya bi Shi."

Su ba a kasance an san su ba sai da kankan da kai da tsoron Allah, da amana da yawan zikirin Allah, da azumi, da salla, da bin iyaye, da alkawari ga makwabta fakirai da matalauta da mabarsa da marayu tare kuma da gaskiyar magana da karatun Alkur'ani da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma sun kasance aminan jama'arsu a kan al'amura.

Saboda haka ku ji tsoron Allah kuma ku yi aiki saboda abinda yake ga Allah, babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, mafi samun soyayya a gurin Allah a cikin bayi shi ne mafificinsu a tsoron Allah da kuma mafificinsu a aiki da biyayyarsa."

Ya Jabir Wallahi ba mu kusanta ga Allah sai dai da da'a, kuma babu kubutarwa daga wuta a gare mu, kuma babu wata hujjar wani a kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi
____________
147-
148- Al Kafi Juzu'i na 2 shafi 40 hadisi na 2.
( 163 )
ne gare mu, kuma ba a samun jagorancin mu sai da aiki da tsoron
149 Allah."

2- Muhawarar Abu Ja'afar (A.S.) da Sa'id Bin Hasan:

Abu Ja'afar (A.S.): " Ashe dayanku zai zo ga dan'uwansa ya iya hannunsa a jakarsa ya dauki abinda yake so bai cire shi ba".

Sa'id: Ban san wani da haka ba a cikinmu.

Abu Ja'afar (A.S.): " To babu kome ke nan."

Sa'id: " To halaka ke nan."

Abu Ja'afar (A.S.): " Mutane ba a ba su mafarkinsu ba ke nan tukunna."
150

3- Mahawarar Abu Abdullah Sadik (A.S.) da Abi Sabahi Kanani:

Kanani ya ce ga Abi Abdullahi "Abinda muke gamuwa da shi daga mutane game da ku."

"Menene abinda kuke gamuwa da shi daga mutane?"

Kanani: Bai gushe ba magana na gudana tsakaninmu da mutane ya ce dan Ja'afariyya ne mugu.

Abu Abdillahi: "Mutane na aibata ku a kaina ?"

Kinani: E!

Abu Abdillah: Karanci mai bin Ja'afar a cikinku ya yawaita! Sahabbaina kawai su ne wanda tsoron Allah gare Shi ya yawaita, kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa kuma ya tsammaci ladansa. Wadannan su ne sahabbaina."
151

4- Abi Abdillah (A.S.) yana da wasu maganganu game da wannan al'amari, daga ciki za mu kawo abinda ke biye:
____________
149- Da wannan ma'anar ne Amirul Muminin Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) yake cewa "Lalle hukuncinsa a kan mazauna sama da mazauna kasa duk tabbas daya ne, kuma babu wani tsakanin Allah da wani daga zikin bayinsa kan halatta gewayen haramiyyarsa ga halittu." Nahjul Balagha Khutuba ta 192.
150- Al-kafi Juzu'i na 2 shafi na 139 hadisi na 13.
151- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 62 hadisi na 6.
( 164 )

a- "Baya daga cikinmu -babu karama kuma- wanda ya kasance a cikin wani birni da adadin dubu dari ko fiya da haka, kuma wani a cikin wannan birni ya zamanto ya fi shi tsoron Allah."
152

b- "Mu ba ma kidaya mutum mumini har sai ya zamanto mai biyayya ga dukkan umarninmu da kuma nufi, ku ji ku sani daga cikin bin umarninmu da kuma nufinsa ne tsoron Allah, don haka ku zamanto kun kawata da Shi, Allah Ya rahamshe
153 ku."

c- "Wanda mata masu tsari basu magana game da tsanteninsa ba ya daga cikin Shi'awanmu, haka kuma wanda ya kasance a cikin karamin gari mai adadin mutane dubu goma, daga halittun Allah daya a cikinsa ya fi shi tsoron Allah."
154

d- "Shi'awan Ja'afar, mabiyansa, kawai su ne: wanda ya kame cikinsa da farjinsa kokarinsa ya tsananta, kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa ya sa rai da sakamakonSa kuma ya ji tsoron ukubarSa. To idan ka ga wadannan to wadannan su ne Shi'awan Ja'afar."
155
____________
152- Al-Kafi Juzu'i na 2 shafi na 63 hadisi na 10.
153- Al-Kafi Juzu'i na 2 shafi na 63 hadisi na l3.
154- Al-Kafi Juzu'i na 2 shafi na 64 hadisi na 15.
155- Al-Kafi Juzu'i na 2 shafi na 183 hadisi na 9.
( 165 )
Imaninmu Game da Ja'irci da Zalunci.

Ketare haddi ga wani da zaluntar mutane na daga cikin mafi girman abubuwan da Imamai (A.S.) ke girmama yawan zunubinsa, kuma yin haka na tafiya ne daidai da yadda ya zo a Alkur'ani na daga tsorotarwa game da zalunci da kuma kushe shi kamar yadda ya zo a fadar Allah Ta' ala:
"Kada ka tsammaci Allah Mai mancewa ne game da abinda azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai Yana jinkirta su ne saboda ranar da idanduna za su fiffito." (Surar Ibrahim: 42)

Abinda ke kai kololuwar bayyana munin zalunci da kore shi ya zo a maganganun Amirul Muminin Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) kamar maganar sa shi mai gaskiya abin gaskatawa, daga maganarsa a khutuba ta 219 a Nahjul Balagha.

"Wallahi idan da za a ba ni sammai bakwai da kuma abinda ke karkashin falaki-falakinta a kan in saba wa Allah game da tururuwa in kwace mata sha'irin da ta jawo ba zan aikata ba."
156

Wannan shi ne matukar abinda zai iya surantawa a kan kame kai daga zalunci da kuma nesantar ja'irci da kushe shi.

Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan konon sha'iri koda kuwa an ba shi sammai bakwai to yaya halin wanda ke yin dumu-dumu da jinin musulmi, yana handame dukiyoyin jama'a, yana tozarta mutuncinsu da karimcinsu ? Yaya za a auna tsakaninsa da cikin Amirul Muminin ? Kuma yaya matsayin zai kasance a fikihunsa (A.S.)?
____________
156- Nahjul Balagha, maganarsa game da nesantar mutum zalunci.
( 166 )

Wannan shi ne irin ladabin da Ubangiji ya yarda da shi wanda addini ke bukatarsa daga kowane mutum.

E, lalle zalunci na daga mafi girman abubuwan da Allah Ya haramta, don haka ne yake da matsayi na farko a hadisai da addu'o'in Ahlul Raiti (A.S.) wajen zarginsa da kuma kore mabiyansu daga gare shi.

Wannan ita ce siyasarsu (A.S.) kuma a kanta salon rayuwarsu yake har ma dangane da wanda ke ketare haddinsu, yake wa matsayinsu hawan kawara.

Kissar Imam Hasan (A.S.) game da hakurinsa ga mutumin Sham wanda ya yi masa tsaurin ido ya zage shi, shi kuwa ya kyautata masa ya tausasa masa har sai da shi ya ji laifin abinda ya aikata.
157

Ka dai rigaya ka karanta abinda ya gabata a addu'ar Shugaban masu Sujada na daga madaukakan ladubba game da yafewa ga wadanda suka ketare haddi da nema musu gafara, wanda kuma shi ne matukar daukakar zuciya, da cikakkiyar 'Yan Adamtaka, koda yake ketare
____________
157- Ka duba Manakib na Ibin Shahri Ashub Juzu'i na 4 shafi na 19 ya kawo wannan kissa ne daga Mubarrad Ibin A'isha, Ya ce: "Wani Mutumin Sham ya gan shi a kan abin hawa sai ya kama la'anar sa amma Shi Imam Hasan (A.S.) bai rama ba. Yayin da ya gama sai Imam Hasan (A.S.) ya fuskance shi ya yi dariya ya ce: "Ya dattijo ina tsammani kai bako ne, kuma la'alla an ruda ka ne, idan da ka nemi bain mu da mun biyar da kai idan da ka roke mu da mun ba ka, idan da ka nemi mu shiryar da kai da mun sa ka a hanya, da ka nemi mu dora ka a kan abin hawa da mun hawar da kai, idan da ka kasance kana jin yunwa ne da mun kosar da kai, idan ka kasance tsirara ne da muntufatar da kai idan da ka kasance mabukaci da mun wadatar da kai idan kuma kai korarre ne da mun sauke ka, idan da ka koro abin hawanka zuwa gurinmu da kai bakonmu ne har zuwa lokacin da ka tafi kuma kana iya dawowa, domin muna da guri wadatacce da fuska sakakkiya da dukiya mai yawa." Yayin da mutumin yaji maganarsa sai ya fashe da kuka, sa'an nan ya ce ni na shaida cewa kai Halifan Allah ne a bayan kasarSa, Allah shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonSa, kuma kai ka kasance kai da mahaifinka wadanda na fi ki a cikin halittun Allah, amma yanzu kai kai ne wanda na fi so a cikin halittun Allah. Daga nan sai ya kora abin hawansa zuwa cikin karafkarsa ya zama bakonsa har zuwa lokacin da ya tafi kuma ya zamanto ya yi imani da soyayyarsu.
( 167 )
haddi ga azzalumi gwargwadon irin yadda ya ketare din ya halatta
158 a shari'a, kamar kuma yadda yin addu'a a kansa ya halatta mustahabi ne, amma halattar abu daban kai hatta a gurin Imamai ma (a.s.) yawaita addu'a a kan azzalumai na iya zama keta haddi da zalunci, Imam Sadik (a.s.) na cewa: " Bawa na iya zama wanda aka zalunta sai ya yi ta yin addu'a har sai ya zamanto azzalumin."
159

Wato har ya zamanto azzalumi a kan addu'arsa game da azzalumin, saboda ya waitata da yawa.

Subhanallah! Ashe yin addu'a ga azzalumi zai zama zalunci idan ya ketare iyaka? To menene halin wanda ya fara da zalunci da ketare iyaka, yana ketare haddin mutane, yana keta mutumcinsu, yana kwashe dukiyarsu, ko kuma ya yaudare su ya aukar da su a cikin halaka, ko ya kuntata musu ya cutar da su ko kuma ya yi leken asiri a kansu? Menene halin makamantan wadannan a fikihun Ahlulbait (a.s.).

Lalle makamantan wadannan su ne mutane wadanda suka fi kowa nesa da Allah Ta'ala, suka kuma fi tsananin sabo da ukuba, da mafi munin ayyuka da dabi'u.
____________
158- Surar Bakara: 194.
159- Al-Kafi Juzu'i na 2 shafi na 250 hadisi na 17, ikabul A'amal: shafi na 274.
( 168 )
39- Imaninmu Game da Taimakekeniya
da Azzalumai.

Saboda girman hatsarin da ke tattare da zalunci da muninsa har Allah Ta'ala Ya hana taimakekeniya da Azzalumai da kuma karkata zuwa gare su.
"Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai har wuta ta shafe ku kuma ba ku da wasu majibinta baicin Allah sa'an nan ba za a taimake ku ba."

Wannan ita ce ladabtarwar Alkur'ani kuma ladabtarwar Ahlul-Bait (A.S.), ruwayoyi da dama da suka zo daga gare su game da hana karkata zuwa ga azzulumai, da sadarwa da su, da yin haraka tare da su a cikin kowane irin aiki da taimakekeniya da su ko da kuwa daidai da kwatankwacin tsagin dibino.
Babu shakka mafi girman abinda aka yi hani a kansa a musulunci da kuma ga musulmi shi ne sassauci ga azzalumai da rufe ido game da miyagun ayyukansu, da mu'amala da su, ballantana ma cudanya da su da taimaka musu da taimaka musu a kan zaluncinsa.

Babu abinda ya jawo wa al'ummar musulmi bala'o'i illa wancan karkacewa daga kan tafarki madaidaci da gaskiya, har addini ya yi rauni tare da shudewar kwanaki, karfinsu ya zagwanye suka kai cikin halin da suke a yau. Addini ya zama bako musulmi kuma ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani Majibinci baicin Allah kuma ba su da wani mataimaki gare su hatta a kan mafi rauni daga makiyansu da mafi kaskanci masu yi musu hawan kawara, kamar Yahudawa wulakantattu, ballantana kuma a kan kiristoci mafiya karfi.
( 169 )

Lalle Imamai (A.S.) sun yi jihadi wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, sun kuma tsanantawa mabiyansu game da tafiya tare da ma'abuta zalunci da ja'irci da cudanya da su. Abinda aka ruwaito daga gare su game da haka a wannan babin ba zai kididdigu ba, daga ciki akwai abinda Imam Zainul Abidin (A.S.) Ya rubuta zuwa ga Muhammad Bin Muslim Az-Zuhri bayan ya gargade shi game da taimakon Azzalumai a kan zaluncinsu?

"Ashe kiransu gare ka yayin da suka kira ba su sanya ka dan dutsin nika suna juya zaluncinsu da kai ba, da kuma bango da suke ketarawa ta kanka zuwa bala'insu, da tsani na bi ta kai zuwa batansu, mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malami, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su, waziransu da mafiya karin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen nuna ingancin barnarsu, da shigi da ficin kebatattu da gama gari zuwa gare su, abinda suka ba ka ya karanta matuka a kan wanda suka karba daga gare ka, abinda suka rayar gare ka ya karanta kwarai akan wanda suka rusa maka ka duba zuciyarka, domin babu wani mai duba ta baicin kai, ka yi mata hukunci, hukunci irin na mutum abin tambaya
160..."

Girman kalmar "Ka yi mata hukunci, hukunci irin na mutum abin tambaya", ya yawaita mutum yayin da son ransa ya gallabe shi sai ya mance darajarsa da ke tare da shi da sirrin karamarsa, wato ma'ana ya ji cewa shi abin tambaya game da ayyukansa, kuma ya kaskanta abinda zai gudana daga ayyukansa sa'an nan kuma ya raya cewa shi ba shi ne wanda za a yi masa hisabi ba a kan ayyukansa, wannan na daga cikin asirran zuciyar mutum mai umarni da mummuna, don haka Imam ya so ya fadakar da Zuhri game da wannan sirrin na zuciya wanda ke kunshe a cikinsa domin kada wahami ya yi galaba a kansa har ya yi sakaci game da abinda ya ke kansa game da kansa.

Mafi zurfi game da haka kuma game da suranta haramcin taimakekeniya game da azzalumai shi ne maganar Safwan Jammal
____________
160- Tuhful Ukul shafi na 275.
( 170 )
tare da Imam Musa Kazim (A.S.) wanda shi ya kasance daga cikin mabiyan Imam din ne, masu ruwaito hadisi daga gare shi wadanda aka amince da su ya ce kamar yadda Kasshi ya ruwaito a littafinsa na Ilimin sanin masu ruwaya kamar yadda yake bayanin rayuwar Safwan:

Na shiga gare shi sai ya ce mini: "Ya Safwan duk wani abu daga gare ka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu guda daya."

Na ce: A sanya ni fansa gare ka, wane abu?

Ya ce: "Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Haruna Rashid.

Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai alfahari ko dagawa ko don farauta, ko wasa, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin wato don hanyar Makka- kuma ba na daukar sa ni da kaina sai dai ina tura shi da barorina."

Ya ce: "Ya Safwan kudin hayarka na kansu? "

Na ce: E, a sanya ni fansa gare ka.

Ya ce: "Shin kana so su wanzu har su dawo su biya ka kudin hayarka?"

Na ce: "E".

Ya ce: "To duk wanda ya so wanzuwarsu to yana tare da su, duk wanda ya kasance tare da su to ya kasance mai shiga wuta."

Safwan ya ce: "Sai na tafi na sayar da dukkan rakuma na baki daya."
16l

Idan har son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu a kan wannan matsayin yake, to yaya kuma ga wanda yake hada kai da su a kan zalunci, ko kuma yake taimaka musu a kan ja'irci, kuma yaya halin wanda yake shiga cikin jama'arsu ko kuma yake aikinsu ko kuma yake shiga tawagarsu, ko kuma yake bin umarninsu?
____________
161- Rijalul Kasshi shafi na 440 hadisi na 828.
( 171 )
40- Imaninmu Game da Aiki a Hukuma
Azzaluma

Idan har taimakekeniya da azzalumai daidai da rabin dibino, kai hatta ma son wanzuwarsu na daga cikin abubuwa masu tsanani da Imamai (A.S.) suka yi gargadi game da su to mene ne kuma halin tarayya da su a cikin hukunci da kuma shiga cikin aikinsu tare da su da amintuwa da jagorancinsu?

Yaya halin wanda ya kasance daga cikin wadanda suka assasa musu hukumarsu, ko kuma wanda ya kasance daga cikin wadanda su rukunan shugabacinsu ne wadanda suka dulmuye cikin karfafa hukuncinsu, "kuma wannan saboda karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta kuma raya karya ne dukkaninta kuma bayyana zalunci ne da ja'irci da fasadi.
162 Kamar yadda ya zo a hadisi a "Tuhful Ukul" daga Imam Sadik (A.S.)

Sai dai kuma ya zo daga gare su (A.S.) halaccin yarda da Shugabancin Ja'irai idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da mai kyau da hana ayyuka munana, "A kofofin azzalumai Allah na da wadanda Allah Ya haskaka su da hujjoji, Ya ba su iko a kasashe, kuma Yana kare waliyanSa da su, kuma Yana gyara al'amuran musulmi da su... Su wadannan muminai ne na hakika su wadannan manarorin Allah ne a bayan kasa wadannan hasken Allah ne a cikin ababan kiwonsa..." kamar yadda ya zo a hadisi daga Imam Musa Bin Ja'afar
l63 (A.S.)
____________
162- Tuhful Ukul hadisi na 332.
163-Biharul Anwar Juzu'i na 75 shafi na 38 Hadisi na 46 daga Munyatul Murid, a cikinsa akwai hadisi daga Imam Ridha (a.s.).
( 172 )

A wannan Babin akwai hadisai da dama, wadanda ke bayyana tafarkin da ya kamata shugabanni da masu aiki ya kamata su tafi a kai, kamar abinda ya zo a wasikar Imam Sadik (A.S.) ga Najjasi Shugaban Ahwaz (A duba Al- Wasa'il Kitabul Bay'i Babi na 78.
164
____________
164- A duba Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na 17 shafi na 196 hadisi na 22338 da sauran hadisan Babi na 36 daga babobin "Maktusiba bi kashfar Rayba." 86.
( 173 )
41- Imaninmu Game da Kira Zuwa Ga Hadin Kai
A Musulunci

An san Ahlul Bait (A.S.) da kwadayinsu a kan wanzuwa da dorewar zahirin addinin Musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hade kalmar mabiyansa, da kiyaye 'Yan'uwantaka a tsakaninsu da cire kufe daga zukata da kullaci daga rayuka.

Ba za a mance da matsayin Amirul Muminin Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) dangane da halifofin da suka gabace shi ba, duk da hujjar da yake da ita a kansu, da imaninsa cewa sun yi kwacen hakkinsa daga gare shi, amma ya zama tare da su ya zauna lafiya da su, kai hatta ma danne ra'ayinsa ya yi na kan cewa shi ne wanda aka nada da nassi a kan halifanci, har ma shi bai bayyana wani nassi ba a bainar jama'a ba har sai da al'amarin ya shigo hannunsa sa'an nan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al'amarin nassin Al-Ghadir sananniyar ranar nan ta Rahba.
165

Ya kasance ba ya jinkirin yin ishara gare su game da abinda ya shafi musulmi da Musulunci wajen amfani da kuma fa'ida, kuma sauda yawa yana magana game da wannan alkawari:
____________
165- Musnad Ahmad Juzu'i na 1: 83, Fadha'ilu Ahmad shafi na 77 hadisi na
115, Sunan Ibin Ali Asim: shafi na 593 hadisi na 1372 da 1373 da 1374, Mushkilul Asar Juzu'i na 2 shafi na 307, da Khasa'is Na Nisa'i shafi na 100 da 101 hadisi na 85-86 da Al- Mu'ujamus Sagir na Tabarani Juzu'i na 1 shafi na 65, da Al-Mu'ujamul Wasit Juzu'i na 2 shafi na 68 da Hulliyatul Awliya' Juzu'i na 5 shafi na 26, da Al-Manakib na Ibin Magazilli shafi na 20 hadisi na 28, Kanzul Ummal Juzu'i na 13 shafi na 157 hadisi na 36485, 36486, shafi na 170 hadisi na 36514, Usudul Gaba Juzu'i na 3/321, 4/28.
( 174 )

"Sai naji tsoron idan ban taimaki musulunci ba da ma'abutansa zan ga gibi a cikinsa ko rushewa."
166

Kamar yadda babu wani abu da ya taba bullowa daga gare shi wanda zai yi tasiri a kan karfin mulkinsu, ko kuma ya raunana shugabancinsu ko kuma ya rage kwarjininsu sai ya kuntatawa kansa ya zauna a gida duk da abinda yake gani daga gare su.

Duk wannan saboda kiyaye maslahar addinin musulunci baki daya, da kariya kada a ga wani gibi a musulunci ko rusawa, har sai da aka san haka daga gare shi, kuma halifa Umar Bin Khattab ya kasance yana cewa:

"Kada na kasance gurin zaman da babu Baban Hasan a cikinsa Ko kuma, "Idan da ba don Ali ba to lalle da Umar ya halaka."
168

Ba za a mance matsayin Imam Hasan bin Ali (A.S.) ba dangane da yin Sulhu da Mu'awiya ba,
169 bayan ya ga cewa yaki zai cutar da nauyi
____________
166- Nahjul Balagah: al-Kitab 62 (min kitabin lahu alaihis salam ila Ahlul Basra).
167- Tabakat na Ibin Sa'ad, Juzu'i na 2 shafi na 339 Fada'ilu Ahmad, shafi na 1 55 hadisi na 222, da Insabul Asharaf na Balaziri Juzu'i na 2 shafi na 99 hadisi na 29 Sharhin Nahjul Balagha Ibin Abil Hadid Juzu'i na 1 shafi na 18, Al- Manakib na Khawarzimi shafi na 96-97 karshen hadisi na 97 da 98, da Usudul Ghaba Juzu'i na 4 Shafi na 22, Kifatut Talib shafi na 217, Al- Isaba Juzu'i na 2 shafi na 509, Zakha'irul Akaba shafi na 82, Tahzibut Tahzib Juzu'i na 7 shafi na 296, Tazkiratul Khawas shafi na 134 da 137 da Riyadun Nadrah Juzu'i na 3 shafi na 161 da Fara'idus Samtin Juzu'i na 1 shafi na 344 hadisi na 267.
168- Al- Manakib na Khawarzimi shafi na 80 hadisi na 65, Tazkiratul Khawas
shafi na 137, Sharhin Nahjul Balagha Ibin Abil Hadid shafi na 18 da 141, da 12, 179, da 223 Kifayatut Talib 219 Zakai'rul Akaba shafi na 82, da Riyadun Nadrah Juzu'i na 3, shafi na 161.
169- Za a iya duba sulhun da ya auku tsakanin Imam Hasan (A.S.) da Mu'awuya ta kusurwoyi daban-daban, daga ciki akwai:
Na farko: Karya shamakin ruhin da Mu'awuya ya yi kokarin ya nuna wa musulmi baki daya dangane da nacewasa a kan sulhu domin ya yaudari mutane, Imam Hasan (A.S.) Ya bayyana uzurinsa tun farko cewa Mu'awuya ba zai yi aiki da sharudansa ba kuma ba amintacce ba ne a kan addini da kuma al'umma.
( 175 )
____________
Na Biyu: Idan da Imam Hasan (A.S.) Ya dage da ci gaba da yaki da Mu'awuya to da yakin ya kazanta kwarai kuma da ya kai ga halaka Imam din da dukkan Bani Hashim kuma da an cire shi da bangaren masu cirewa kuma da an yi ta ka ce na ce a kansa.
Na Uku: Daga baya al'amarin ya bayyanar da kunyata Mu'awuya wanda bai yi aiki da ka'idojin sulhun ba ko kadan sa'an nan kuma an gano babbar gudummawar da Imam Husain (A.S.) ya kaddamar da sadaukar da kan da ya yi cewa cikato ne na gudummawar Imam Hasan wajen fuskantar azzalumai da fuskantan fandarewa.
Na Hudu: Imam Hasan (A.S.) ya yi aiki da abinda ya zo na daga sunna da salon rayuwar Annabi (S.A.W.A) yana mai koyi da shi, domin ya yi kokarin shiryarwa zuwa ga sakon, sai aka fuskance shi da wannan matsayin, kuma ya rike a matakinsa da kuma kafa hujja da shi daga matsayin Sulhun Hudaibiya.
Na Biyar: Sulhun shi ne kawai abin koyi guda daya wanda Imaman Ahlul Bait (A.S.) suka tsara Siyasarsu ta hikima da shi domin Imam Hasan (A.S.) ya aza nakiya ce a hanyar Mu'awuya da shi wanda zai tarwatsa shi ta yadda bai sani ba, kuma ya sanya sunnar ruguza fadar Umayyawa ta hannun su Umayyawan da kansu.
Tarihi ya kawo cewa Mu'awuya ya karya alkawarin Sulhun da ya yi bayan sojojin Kufa sun koma gare shi yayin da ya tashi yana magana yana cewa:
"Ya ku mutanen Irak -ni- wallahi ban yake ku domin ku yi salla, kuma ba don ku yi azumi ba, kuma ba don ku yi zakka ba, ba don ku yi hajji ba, ni dai na yake ku ne kawai domin zama shugaba a kanku, kuma Allah Ya ba ni wannan alhali ku ba kwason haka ku ji ku sani duk abinda na bayar da shi ga Hasan Bin Ali to na take shi a karkashin kafofina biyu wadannan." Kamar yadda Ibin Asakir ya kawao a Littafin Mukhtasaru Tarikh Dimashk- Yayin da aka game mubaya'a ga Mu'awuya ya tashi ya yi jawabi ya zagi Aliyu ya zagi Hasan- har zuwa karshe karshen abinda ya auko daga manyan al'amuran da suka auku.
Sidi Abdul Husain Sharafuddin (R.A.) ya ambata cewa Imam Hasan da Imam Husain (A.S.) sun kasance kusurwoyi biyu ne na sako guda kowace kusurwa daga cikinsu tana gurinta da ya dace, a lokaci daga marhalolinsa daya na taimakon guda a kan yunkurinsa da kariyarsa yana taya shi da sadaukar da kansa a tafarkinsa...
Ranar Sabit (sulhun Hasan) ita ce mafi sananniyar ma'anar sadaukar da kai fiye da ranar Tif (Ranar Karbala) ga ma'abuta hankali ga wanda ya zarfata, Shahadar Karbala ta Hasan ce a karo na farko sa'an nan ta Husaini a karo na biyu domin Hasan shi ne ya tandi sakamakonta ya shirya musabbabanta.
Mutane sun tsaya bayan aukuwa al'amari Sibat da na Karbala suna nazarin al'amura suna ganin cewa Umayyawa wata jama'a ce ta Jahiliyya.
A duba Littafan Sulhun Hasan na Shaikh Radhi Ala Yasin, da kuma Majalisul Fakhira Fi Ma'tami Itrati Tahira, da Sharhin Nahjul Balagha Juzu'i na 4, da Imamul
( 176 )
mafi girma da kuma hukumar adalci kai hatta sunan Musulunci har zuwa karshen zamani a shafe shari'ar Ubangiji a kuma gama da wadanda suka saura da sauran zuriyar Manzo daga Ahlul Bait, sai ya fifita kiyaye zahirin Musulunci da kuma sunan addinin Musulunci inda ya yi sulhu da Mu'awiya babban makiyin addini da ma'abutansa, kuma abokin husumarsa, mai tsananin kiyayya gare shi da mabiyansa tare da abinda yake sa ran aukuwarsu na daga zalunci da wulakanci gare shi da mabiyansa. Sa'an nan kuma takubba Bani Hashim da takubban mabiyansu sun kasance a zazzare ba sa son komawa, ba tare da kwato hakkinsa da kariya tare da kuma maida martani ba, amma maslahar Musulunci madaukakiya ita ce ta fi kome daga cikin wadannan al'amuran a gurinsu.

Amma Husain Shahidi (A.S.) kuwa ya yunkura ne ba don kome ba sai don cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki ba a sha gabansu an sami wanda ya fallasa mummunar niyyarsu ba to da sannu za su shafe sunan musulunci, za su goge girmansa don haka ya so ya tabbatar wa tarihi ja'ircinsu da ketare iyakarsu, ya fallasa abinda suka kasance suna kukkula shi ga shari'ar Manzon Allah (S.A.W.A) abinda ya so kuma haka ya wakana. Idan da ba don Yunkurinsa ba to da musulunci ya zama sai sunansa a tarihi, a yi ta ambatonsa a tarihi tamkar wani addinin karya.

Kwadayin Shi'a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban-daban kuwa saboda kammala Yunkurinsa ne na fafatawa da zalunci da jairci kuma domin raya al'amarinsa da al'amuran Imaman bayansa ne.

Kwadayin Ahlul Bati (A.S.) wajen ci gaba da daukakar addinin musulunci -koda kuwa masu shugabincin al'umma matsananta makiya ne gare su kuwa.

Matsayin Imam Zainul Abidin (A.S.) game da sarakunan Banu Umayya alhali yana cikin rashin kwanciyar hankali game da su, kuma a zamaninsu ne aka keta martabarsa da mutuncinsa, kuma da'iman
____________
Hasan da Husain na Malam Abdul Ala yili, Mukhtasaul Tarikh Dimashk Juzu'i na 25 shafi na 162, da Al- Kamil Fit Tarikhul Islam na Zahabi Juzu' i na 4 shafi na 5 da Tarikhul Khulafa' (Al- Imama Was Siyasa) na Ibn Kutaiba Juzu'i na 1 shafi na 164.
( 177 )
yana cikin kunci da damuwar abinda suka yi wa mahaifinsa a abinda ya auku a Karbala, amma duk da haka Shi a koyaushe yana addu'a ga sojojin musulmi a asirce don su sami cin nasara; musulunci kuma ya daukaka, musulmi kuma su sami karfafa da aminci, ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi shi ne addu'a. Ya koya wa Shi'a yadda za su yi addu'a ga sojojin musulunci da musulmi wato kamar addu'arsa sananniya mai suna, "Addu'a ga ma'abuta dakon iyaka" wadda yake cewa:

"Ya Allah ka yi dadin tsira ga Muhammadau da zuriyar Muhammadu, kuma Ka yawaita adadinsu, Ka kaifafa makamansu, Ka kare martabarsu, Ka kange iyakarsu, Ka hado taronsu, Ka shirya al'amarinsu, Ka bibiyar da tsakanin abin masarfinsu, Ka kadaita da wadatar da bukatunsu, Ka karfafa su da cin nasara, Ka taimake su da hakuri, Ka tausasa musu wajen shiri,"

Har zuwa inda yake cewa: "Ya Allah Ka karfafa guraren musulunci da haka, Ka kiyaye gidajensu da shi, Ka yada dukiyarsu da shi, Ka raba su da yakayya su dukufa ga ibadarKa, da kuma hana ja da su har kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a doron kasa sai Kai, kuma babu wani mai gafarta wa wani daga cikinsu sai Kai."

Haka nan yake ci gaba da addu'arsa mai zurfi -kuma tana cikin addu'o'insa mafiya tsawo- wajen fuskantar da sojojin musulunci zuwa ga abinda ya kamace su na daga manyan kyawawan dabi'u da kuma shirya kansu a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki a jihadin musulunci da bayanin manufarsa da fa'idarsa kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin shirin da ya kamata su zauna da shi dangane da makiyansu da ya wajaba su yi wajen mu'amala da fuskantarsu da kuma abinda ya wajaba a kansu game da yankewa daga kome da juyawa ga Allah baki daya da nesantar abubuwan da ya haramta da yin abu saboda Shi kawai.

Kamar kuma sauran Imaman (A.S.) game da matsayinsu dangane da sarakunan zamaninsu, duk kuwa da cewa sun fuskanci matsa lamba da azabtarwa mai tsanani daga gare su, saboda ya yin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo gare su ba sai suka dukufa da koya wa
( 178 )
mutane al'amuran addinin suna faskantar da mabiyansu fuskantawa ta addini madaukaki.

Dukkan wani juyi da ya auku a zamaninsu daga bangaren Alawiyawa da wasunsu bai kasance da ishararsu da koyarwarsu ba bil hasali duk sabanin umarninsu ne a bayyane da tsanantawarsu, duk da cewa su sun kasance sun fi kowa kwadayin kafa hukuma hatta halifofin Bani Abbas.

Karanta wasiyyar Imam Musa Bin Ja'afar (A.S.) ga Shi'a mabiyansa: "Kada ku dukar da wuyanku da barin biyayyar shugabanku domin idan ya kasance mai adalci to ku roki Allah ci gabansa, idan kuwa ya kasance ja'iri to ku roki Allah gyaransa, domin gyaruwarku na cikin gyaruwar shugabanku, kuma lalle shugaba tamkar uba mai rahama yake, ku so masa abinda kuke so wa kanku kuma ku ki masa abinda kuke ki wa kanku."
170

Wannan shi ne matukar abinda ake so na kiyayewar ababa kulawa da su, talakawa, game da lafiyar Shugaba wato su so masa abinda suke so wa kansu su ki masa abinda suke ki wa kansu.

Kuma bayan duk wannan laifin wasu marubutan wannan zamani ya girmama wadanda suke cewa wai Shi'a wata jam'iyyar Asiri ce mai tabargaza ko kuma wata kungiyar 'Yan juyin juya hali masu ramuwar gayya.

Gaskiya ne cewa dabi'ar musulmi mai bin kayarwar Ahlul Bait (A.S.) ita ce kiyayya da zalunci da azzalumai da kuma nesantar ma'abuta ja'irci da fasikanci tare da duban mataimakansu da mabiyansu da duban kyama da kiyayya da rashin yarda da wulakanci. Wannan hali bai gushe ba yana tare da su suna gadonsa zuriya bayan zuriya amma duk da haka ba dabi'arsu ba ne kisan gilla ko kisan
____________
Amali na Saduk na 277, da Wasa'ilus Shia Juzu'i na 16 shafi 220 hadisi na 21406.
171- An riga an yi ishara a gurin "Imaninmu Game da Takiyya" zuwa maganar Kausari a inda ya kara bayani a littafin Tabsira Fid Din na Istafra' ini a wajen da yake siffanta Shi'a yana cewa wata Jam'iyya ce ta boye.
( 179 )
yaudara ba, kuma ba ta hanyarsu juyin juya hali da yunkurawa a kan wata hukuma mai jagoranci da sunan addini, ba sa yi a asirce ba sa yi a bayyane, kuma ba sa halattawa kansu kisan gilla ko kwanton bauna ga musulmi koda wace irin mazhaba ko darika yake bi kuwa, suna masu riko da koyawar Imamansu (A.S.).

Bilhasali duk wani musulmi da ke shaidawa da kalmar Shahada biyu to dukiyarsa ta tsira jininsa ya kubuta kuma mutuncinsa katangagge ne. "Dukiyar mutum musulmi ba ta halatta sai dai da son ransa."
172

Bil hasali ma musulmi dan'uwan musulmi ne kuma hakkokin 'Yan'uwantaka na kansa wadannan bayanin da ke biye zai fayyace su.
____________
172- Al- Fakih Juzu'i na 4 shafi na 66 hadisi na 195, Awaliyu Aliy Juzu'i na 3 shafi na 473 hadisi na 3 da Tuhful Ukul Shaf na 34, da Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na 5 shafi na 120 hadisi na 6089 Sunanud Daru Kutni Juzu'i na 3 shafi na 26 hadisi na 91 da 92, Kanzul Ummal Juzu'i na 1 Shafi na 92 hadisi na 397.
( 180 )
42- Imaninmu Game Da Hakkin Musulmi akan
Musulmi.

Daga cikin abubuwa mafiya kyawu kuma mafiya girma da addinin musulunci ya yi kira gare su shi ne 'Yan'uwantaka tsakanin musulmi duk da sabanin martabobi da matsayai da mukamansu kuwa, kamar kuma yadda abu mafi bacin rai da ban takaicin abinda musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne rikon sakainar kashin da suka yi wa koyarwar wannan 'Yan'uwantaka ta musulunci. Domin mafi karancin koyarwar wannan 'yan'uwatakar shi ne "Ya so wa
dan'uwansa abinda yake so wa kansa kuma ya ki masa abinda yake ki wa kansa kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S.).

Ka duba ka kara tunani a kan wannan hali mai sauki a ganin Ahlul Bait (A.S.) za ka iske cewa yana daga cikin abubuwa da ya kamata a yi matukar samar da su a wannan zamanin a tsakanin musulmi, duk da cewa suna da wannan kyakkyawar dabi'a tare da su amma sun yi nesa da ruhin addinin musulunci, yi tunani a kan wannan halayya idan da za a kaddara cewa musulmi za su siffantu da ita su kuma san addininsu sosai, kuma su yi riko da ita kawai cewa dayansu ya so wa dan'uwansa abinda yake so wa kansa, to da ba a ga zalunci daga kowa ba, ko ketare iyaka, ko sata ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ka kuma zargi da mummuna, ka suka da karya, ko wulakanci ko tursasawa.

Hakkan, lalle idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma'anar halin 'yan'uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da shi to lalle da zalunci da ketare haddi sun gushe daga bayan kasa, kuma da ka ga mutane 'Yan'uwa suna masu farin ciki da juna kuma da sa'adar zamantakewa ta kammala ta cika a gurinsu, kuma da mafarkin
( 181 )
ma'abuta falsafa magabata ya tabbata a birnin Falala, kuma da idan suka kasance masu musayen soyayya da kauna to da ba sa butakar hukumomi da mai hukunci, da kuma dan sanda da gidan kurkuku, da kuma dokokin ukuba, da kotunan haddi da kisasi, kuma da ba su rusuna ga 'Yan mulkin mallaka ba, kuma da ba su dukawa azzalumi ba, kuma da dagutai ba su bautar da su ba, kuma lalle da kasa ta canja ta zama aljanna mai ni'ima kuma gidan sa'ada.

Bugu da kari kuma idan da dokokin soyayya sun gudana tsakanin 'Yan Adam-kamar yadda addini yake nufi da koyarwar 'Yan'uwantaka -to da kalmar adalci ta bace daga kamus- kamus din harsunan da muke da su, wato ma'ana ba za mu zamanto muna bukatar adalci da dokoki ba har mu zamanto muna bukatar adalci da dokoki ba har mu zamanto muna bukatar yin amfani da ita kalmar tasa ba, sai dai kawai dokokin soyayya sun wadatar mana wajen yada alheri da aminci da sa'ada da son barka, domin shi mutum ba zai zamanto yana bukatar amfani da adalci ba, kuma dokoki ba za su bukace shi daga gare shi ba sai dai idan an rasa soyayya daga wanda ya wajaba a yi adalci tare da shi, amma a gurin wanda ake musayen soyayya da shi kamar da da dan'uwa -sai dai su ana kyautatawa ne gare su kawai, kuma akan sallamar musu abubuwa da dama daga abubuwan da suke so don kauna da dadin zuciya ba wai don adalci da amfani ba.

Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa kawai da kuma abinda ya dace da kansa, kuma abu ne da ba zai yiwu ba ya so wani abu ko mutum da yake wajen kurwarsa ba sai dai idan yana da alaka da shi ya kuma shiga zuciyarsa da wata sura da ta dace da abinda yake so.

Kamar kuma yadda abu ne korarre ya sadaukar da kansa da zabin kansa kawai a kan kaunarsa da sonsa saboda wani da ba ya son sa ba ya kaunarsa sai dai idan wata akida ta ginu a zuciyarsa wadda ta fi soyayyarsa karfi, wato kamar akidar kyawun adalci da kyautata, yayin nan ne zai sadaukar da daya abubuwan da yake so ya yi fansa saboda daya abin son da ya fi karfi wato kamar akidarsa game da adalci, idan har ta zamanto wani yanki na abinda yake so ko ma yankin zuciyarsa.
( 182 )

Saboda wannan akida abar koyi ta zamanto ta zauna daram a cikin zuciyar mutum har ta bukace shi ya daukaka da ruhinsa a kan dukkan wasu manufofin abin duniya domin ya kai ga fahimtar mafificin abin koyi a adalci da kyautatawa ga wasu, wannan kuwa bayan ya gaza samarwa kansa jin 'yan'uwantaka ta gaskiya da tausasawa tsakaninsa da mutane 'yan'uwansa.

Don haka daraja ta farko da ya kamata musulmi ya samu ita ce jin
'yan'uwantaka da wasu, idan kuma ya gaza game da ita -to ya gaza ke nan a kan mafi yawan, saboda galabar yawan kwadaice- kwadaicensa da son ransa- saboda haka lalle ne a kansa ya cusa wa zuciyarsa akidar adalci da kyautatawa yana mai biyayya ga shiryarwar addinin musulunci, idan kuma ya gaza game da wannan to bai ma cancanci ya zama musulmi ba sai dai na suna kawai. Kuma ya fita daga karkashin jibintar Allah kuma ba shi da kome a gurin Allah a bisa ma'anar abinda ke biye daga Imam.

Shi mutum yawanci sha'awarsa kan yi galaba a kansa har ya zamanto daga cikin abubuwa masu wahala gare shi ya yi imani da akidar adalci ballantana ma ya samar mata cikakkiyar akida wadda ta dara sha'awace-sha'awacensa da karfinta.

Saboda haka kiyaye hakkokin 'yan'uwa na daga koyawar addini masu matukar wahala idan mutum bai kasance yana da wannan jin 'yan'uwantakar na gaskiya ba, saboda haka ne Imam Abu Abdillah (A.S.) ya yi rangwame ga mai tambayar sa daya daga cikin Sahabbansa (Al- Mu'ula Ibin Khunis) da ya yi tambaya dangane da hakkokin 'Yan'uwa bai bayyana masa fiye da ya kamata ba don tsoron kada ya koyi abinda ba zai iya aiki da shi ba.

Mu'ula Ya ce: Na ce masa, mene ne hakkin musulmi a kan musulmi?

Abu Abdillah Ya ce: "Yana da hakkoki bakwai wajibai, kuma babu wani daga cikinsu face shi ma yana da wajibi a kansa, idan ya tozarta daya daga cikinsu to ya fita daga jibintar Allah da da'arSa, kuma ba shi da wani rabo a gurin Allah "

Na ce: A sanya ni fansa gareka wadanne ne su?
( 183 )

Ya ce: `Ya Mu'ula ni lalle ina mai tausasawa gare ka, ina tsoron ka tozarta ba za ka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba za ka aikata ba.

Na ce: Babu karfi sai daga Allah.

Daga nan sai Imam (A.S.) ya ambata hakkokin guda bakwai bayan ya fadi na farko daga ciki akwai: "Mafi sauki daga cikinsu shi ne ka so wa dan'uwanka kamar yadda kake so wa kanka, kuma ka ki masa abinda kake ki wa kanka."

Subhanallahi, wannan shi ne hakki mafi kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a gare mu yau mu musulmi? Fuskar da ke da'awar musulunci amma ba ta aiki da mafi kankantar abinda yake wajaba na daga hakkoki.

Abu mafi ban al'ajabi kuma shi ne a dangata wannan rashin ci gaban na Musulmi ga Musulunci, babu wani laifi kuwa sai laifin wadanda ke sanya wa kansu suna da cewa su musulmi ne amma ba sa aiki da mafi karancin abinda ya wajaba su yi aiki da shi daga addininsu.

Saboda tarihi kawai kuma saboda mu san kanmu da sakacinmu, zan ambata wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S.) ya bayyana:

1- Ka so wa dan'uwanka abinda kake so wa kanka, kuma ka ki masa abinda kake ki wa kanka.

2- Ka nesanci fushinsa ka bi yardarsa kuma ka bi umarninsa.

3-Ka taimake shi da kanka da dukiyarka da harshenka da hannunka da kafarka.

4- Ka zamanto idonsa, manuninsa da madubinsa.

5- Kada ka koshi shi kuma ya zama a yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma ya zauna da kishirwa, kada ka zama a suturce shi ya zama tsirara.

6- In ya zamanto kana da mai hidima shi kuma dan'uwanka ba shi da mai hidima to wajibi ne ka tura mai hidimarka ya yi masa wankin kaya, ya yi masa abinci, ya gyara masa shimfida.
( 184 )
7- Ka sa ya cika rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana'izarsa. Idan kuma ka san cewa yana da wata bukata to ka yi gaggawar biya masa ita, kuma kada ka sa har sai ya tambaye ka kanta, sai dai ka yi gaggawa gare shi.

Sa'an nan ya rufe maganarsa da cewa. "Idan ka aikata haka to ka sadar da jibintarka da jibintarsa da mabiyansa da mabiyanka."

Da irin abinda wannan hadisin ya kunsa akwai ruwayoyi da dama daga Imamanmu da dama, da yawansu a littafin Wasa'il a babobi daban-daban.

Wasu na iya wahamin cewa abin nufi da 'yan'uwantaka a hadisin AhlulBait (A.S.) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu (Shi'a wansu) a kebance amma komawa ga ruwayoyin dukkaninsu na gusar da wannan wahamin -koda yake sun kasance a ta bangare guda tsanantawa a kan kin wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya bin shiriyarsu -ya wadatar mu karanta hadisin Mu'awiya bin Wahab: Ya ce masa- wato Sadik (A.S.) Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu da kuma wadanda muke cudanya da su daga cikin mutane wadanda ba sa kan al'amarinmu?

'
Sai Ya ce: "Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su, ku yi yadda suke yi, don wallahi su suna gaishe da marar lafiyarsu, suna halattar jana'zarsu suna ba da shaida gare su da kuma da kansu, kuma suna ba da amana gare su "
173

Amma 'Yan'uwantakar da Imamai suke nufi game da mabiyansu to ta dara wannan 'yan'uwantakar ta musulunci, ka riga dai ka ji wasu hadisai a Fasalin Sanar da ma'anar Shi'a kuma ya wadatar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana bin Taglib da Sadik (A.S.) daga hadisin da Abanan ya ruwaito da kansa.

Abana Ya ce: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdillah (A.S.) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bullo mini wanda ya riga ya
____________
173- Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 464 hadisi 4, Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na 12 shafi na 6 hadisi na 15497.
( 185 )
tambaye ni in raka shi wani gurin biyan bukatarsa, sai ya yi ishara gare ni sai Abu Abdillahi (A.S.) Ya gan mu.

Sai Ya ce: "Ya Abana wannan kai yake nema ne?"

Na ce: "E."

Ya ce: "Shi yana kan abinda kake kai ne?"

Na ce: "E."

Ya ce: "Maza tafi zuwa gare shi ka katse dawafin"

Na ce: "Koda dawafin wajibi?"

Ya ce: "E "

Abana ya ce: Sai na tafi, na shiga gare shi daga baya na tambaye shi game da hakkin mumini, sai Ya ce: "Kyale shi kada ka kawo shi."

Ban gushe ba ina kawo shi har sai da yace. "Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka" Sa'an nan sai ya dube ni, ya ga abinda ya shige ni sa'an nan yace: "Ya Abana ashe ba ka san Allah Ya riga ya ambaci masu zabi a kan kansu ba.

Na ce: Haka ne.

Ya ce: "Idan ka raba dukiyarka tare da shi ba ka zabe shi ba, kana zabensa ne kawai idan ka ba shi daya rabin.
174

Ina cewa: Lalle hakikanimnu yadda muke mai ban kunya ba zai ba mu tabbacin mu kira kamnu muminai na hakika ba, domin mu muna wani yanki ne koyarwar Imamanmu (A.S.) na wani yankin dabam, kuma abinda ya shiga zuciyar Abana zai shiga zuciyar duk mai karanta wannan hadisin sai dai ya juya fuskarsa yana mai mancewa da shi kamar wanda ake magana da shi wani ne ba shi ba, ba ya yi wa kansa hukuncin mutum abin tambaya.
____________
174- Musadakatil Ikhwan shafi na 38 hadisi 2 da Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na 12 shafi na 209 hadisi na 16106.
( 186 )
( 187 )
FASALI NA BIYAR.
Imaninmu Game da:
Tashin Kabari da Tashin Kiyama.
Tashi da Jikkuna.
( 188 )
( 189 )
43- Imaninmu Game da Tashin Kabari da Tashin
Kiyama
Mun yi imani da cewa Allah zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar da aka yi wa bayi alkawari game da shi. Kuma zai saka wa masu biyayya ya azabtar da masu sabo.
Wannan al'amari ne da baki dayansa da abinda ya tattara akai dangane da abinda wanda saukakkun shari'o'i da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai. Babu wata gujewa ga musulmi ya yi ikrari da akidar Alkur'ani wadda Annabinmu mai girma ya zo da ita (S.A.W.A), domin wanda ya yi imani da Allah, imani tabbatacce to kuwa ya yi imani da Muhammadu (S.A.W.A) a matsayin manzo daga gare shi wanda ya aiko shi da shiriya da addini na gaskiya haka kuma babu makawa ya yi imani da abinda Alkur'ani ya ba da labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da aljanna da ni'ima, da wuta da kuma Alkur'ani ya bayyana haka a sarari kuma yayi ishara da shi a cikin abinda ya kai kimanin aya dubu.
Idan har shakku ya shigi wani game da haka babu wani abu sai dai saboda shakkun da yake da shi game da ma'abucin sakon, ko kuma ma game da samuwar Mahaliccin halittu da kudurarSa, bil hasali ma sai dai da shakkun da yake bullo masa game da asalin addinai baki dayansu, da kuma ingancin shari'o'i dungurungum.
( 190 )
44- Imaninmu Game da Tayar da Jikkuna
Bayan wannan, tayar da jikkuna a kebe wani al'amari ne da yake babu makawa daga cikin al'amuran addinin musulunci, Alkur'ani mai girma ya yi ishara gare ta:
"Shin mutum yana tsammanin ba za mu tattara kasusuwansa ba ne. E Lalle mu masu kudurar madaidaita yatsunsa ne.177
"Idan kayi al'ajabi to abin al'ajabi ce maganarsu eewa ashe idan muka zama turbaya za a dawo da mu halitta sabuwa."176
"Shin mun gajiya ne da halitta na farko a'a su dai suna cikin rudewa ne game da sabuwar halitta."177
Tayar da jikkuna da ba wani abu ba ne illa sake dawo da mutum ranar tashin kiyama, ranar fitowar shi da jikinsa bayan rididdigewa da sake komar da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge.
Ba wajibi ba ne a yi imani da filla-fillan tayar da jikkuna fiye da wannan abinda a kan saukinta da Alkur'ani ya yi kira game da ita a Alkur'ani, kuma mafi yawan abinda yake biye da ita na hisabi da siradi, da auna aiki da Aljana da wuta, da sakamako da azaba duk gwargwadaon abinda bayaninsa ya zo a Alkur'ani ne:
Bai wajaba ba sanin hakikancewar da babu mai kaiwa gare ta sai ma'abucin zurfin nazari mai kaifi, kamar ilimin cewa shin jikkuna za
____________
175- Surar Alkiyama: 3-4.
176- Surar Ra'ad: 5.
177- Surar (Kaf) K: 15.
( 191 )
su dawo ne da kan kansu ko kuma wasu makamantansu ne a sura? Kuma rayuka shin za su gushe ne kamar jikkuna ne ko kuwa za su ci gaba da kasancewa har sai sun sadu da jikkuna yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanta ga mutum ne ko kuwa za a hada har da dukkan dabbobi ne? kuma shin komawa da su da hukuncin Allah tashi daya ne ko kuma sannu sannu ne?
Kuma idan yin imani da Aljanna da wuta wajibi ne to ba ya zama lalle a san da samuwarsu a halin yanzu da kuma sanin cewa suna sama ne ko suna kasa ko kuma sun saba.178
Kazalika idan sanin ma'auni ya zama wajibi to ba wajibi ba ne a san cewa ma'aunin na a surance ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu.
Kuma ba lazimi ba ne a san cewa siradi jiki ne siriri ko kuwa tsayuwar daka ce surantawa. Kuma manufar dai ita ce cewa ba sharadi ba ne a yi binciken hakikancewa don sanin cewa da jikkuna ne ko a'a..."
Na'am wannan akidar tashin kiyamar da saukin da take tare da shi ita ce wadda musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya ketere shi zuwa filla-filla sosai fiye da yadda ya zo a Alkur'ani domin ya gamsar da kansa don kore shakkun da masu bincike ke tayarwa ta hanyar dalilan hankali ko kuma gwajin bincike- to lalle yana wahalar da kansa ne kawai, kuma zai fada a cikin mushkiloli da rikice-rikice da jayayya marar iyaka.
A addini babu adinda ke kira zuwa ga wannan zurfin binciken da littafan masu bincike game da Akida da malaman falsafa, kuma babu wata larurar addini ko ta zamantakewa ko siyasa da ke kira zuwa ga irin wadannan rubuce-rubuce da makalolin da ke cike da littafan haka nan a wasa, da kuma wadanda suka kare karfin da kokarin masu jayayya da karfinsu da lokutansu da tunaninsu ba tare da fa'ida ba.
Mushkiloli da shakkun da ake tasowa da su game da filla-fillansu ya wadatar wajen raddinta mu yi imani da gazawar mutum game da
____________
178- Yanki daga Littafin Kashful Gita, na Shaikh Kabir Kashiful Gita.
( 192 )
fahintar wadannan al'amura boyayyu daga gare mu, da kuma wadanda suke sama da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu na kasa, tare da sanin cewa Allah Ta'ala Mai iko ne a kan Ya ba mu labarin hakikanin aukuwar tashin kiyama da tashin kabari.
Sanin dan'Adam da gwaje-gwajensa da bincike-bincikensa ba zai yiwu su tabo wani abu da ba'a san shi ba su sanya shi a karkashin gwajinsu da kwarewarsu ba sai dai bayan mutuwarsa da ficewarsa daga wannan duniya ta majiyan jiki da gwaje-gwaje da bincike, to yaya za'a sa rai ya yi hukunci da 'yancin tunaninsa, da kwarewarsa wajen kore wannan abu ko tabbatar da shi? Ballantana ma game da filla-fillansa da kebantattun al'amuransa sai dai idan ya dogara a kan bokanci da dikake da al'ajabi da ban mamaki kawai kamar yadda yake a dabi'ar sake-saken zuciyar mutum ya yi mamakin duk abinda bai saba da shi ba bai sami iliminsa da fahintarsa, kamar wanda ya kore yiwuwar tashin Alkiyama da jahilcinsa yana mamaki da al'ajabin tashin kiyama da fitowa daga kabari yana cewa: "Wane ne zai tayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu."
Babu wata madogara ga wannan mamaki sai dai kawai shi bai ganin matacce rididdigagge ba wanda aka koma da shi rayuwa sabuwa. Sai dai kuma ya manta yadda aka halitta shi a karo na farko ne, da ya kasance babu shi, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu daga yankunan kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma a cikin iska a warwatse nan da can aka harhado shi har ya zama mutum daidai mai hankali; "Shin shi mutum ba ya gani ne Mu Mun halitta shi daga digon maniyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya ba Mu misali ya mance halittarsa."
Mai irin wannan maganar sai a ce masa: "Zai raya shi, wannan da Ya fare shi a karo na farko kuma shi masani ne game da dukkan halitta." 179
Kuma a ce masu: Kai lalle bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa kuma ka san Manzo da abinda ya ba da labari game da shi,
____________
179- Surar Y.S: 78, Y.S: 77-78, Y.S: 79.
( 193 )
tare da karancin saninka hatta ma fahimtar sirrin halittarka da sirrin samar da kai, da kuma yadda ka girma da kuma yadda ka fita daga marhalar digon maniyi da ba ya jin kome ba ya da hankali zuwa marhalolin da ke biye da ake tattaro daga kwayoyi manesanta, domin ka zamanto mutum daidaitacce mai hankali mai tuntuni mai ji na jiki da maganai.180
Bayan wannan kuma sai a ce masa ta yaya kake mamakin komo da rayuwa sabuwa bayan zamantowa rididdigagge, kana kokari da haka ka kai ga abinda kwarewar ka da iliminka suka yi kadan wajen gano shi?
Sa'an nan a ce masa ba ka da wata mafita illa ka mika wuya kana mai ikrari game da wannan hakika wadda Mai tafi da halittu Masani Mai kudura game da ita, kuma Mahaliccinka daga babu kome da kuma abubuwa rididdigaggu Ya bada labari kan aukuwarsa.
Duk wani kokari na binciko abinda ba za ka iya gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne kawai na banza da buga-buga a cikin rudu, da bude ido a cikin duhu mai halakarwa kawai.
Shi mutum duk da irin abinda ya kai gare shi na ilimi da shekarun nan na karshe, Ya kago lantarki, da "rada", wato na'urar hangen nesa, da masaniyar amfani da makamin kare dangi da dai sauran irin wadannan kage-kagen da suka auku a shekarun baya-bayan nan wadanda idan da an ba da labarinsu a da can to da an kidaya su a cikin abubuwan da ba za su yiwu ba ya yi watsi da su ya wawaitar da su to har yanzu mutum bai san hakikanin wutar lantarki ba da sirrin kwayar zarra, kai hatta ma hakikanin daya daga cikin abubuwan da suka kebanta da su da siffofinsu, to yaya zai ji tabbacin gano sirrin halitta da samuwa, sa'an
____________
180- Allah Ta'ala Ya ce: "Kuma lalle ne hakika, Mun halitta mutum daga wani tsantsan laka. Sa'an nan kuma muka sanya shi digon maniyi a cikin matabbata natsattsiya sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsoka, sa'an nan Muka halitta tsokar ta zama kasusuwa, sa'an nan Muka tufatar da kasusuwan da wani nama, sa'an nan Muka kaga shi wata halitta dabam. Saboda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne mafi kyawun masu halittawa." Surar Mumin aya ta 12-14.
( 194 )
nan ya kara gaba yana so ya san sirrin tashin kiyama da tashi daga kabari.
E, haka ne, ya kamata ga musulmi bayan ya yi imani da Musulunci ya nesanci bin son zuciya kuma ya shagaltu a kan abinda zai gyara al'amarinsa na duniya da lahira da kuma abinda zai daukaka masa matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abinda zai taimake shi a kan son ransa da kuma abinda zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da hisabi bayan hallara a gaban mai Mulki Masani, kuma yaji tsoron "wata rana da wani rai ba ya wadatarwa wani rai kome kuma ba a yarda da ceto gare shi, kuma ba a karbar fansa gare shi kuma ba a taimakon su."181
____________
181- Surar Bakara: 48.
Koma Ga Fehrisan Littafin


Koma ga Shafin Littattafai