"Ni mai bari muku nauyaya biyu ne tare da ku, littafin Allah da dangina, mutanen gidana (ahlulbaiti) wadanda in kun yi riko da su ba za ku taba bata ba a bayana har abada, kuma lalle ne su biyun ba za su rabu da juna ba har su riske ni a bakin tafki".
Ahlulbaiti (a.s) makaranta ce mai haske kuma taurari ne a sararin samaniyar addinin Musulunci madaukaki. Su ne ja-goranci cikakke mai koyi da Manzon Allah (s.a.w.a.), sun sha daga ilminsa a gidansa suka tashi, sannan suka rayu bisa tafarkinsa. Suna masu kira zuwa ga Littafin Allah da kuma riko da sunnar AnnabinSa (s.a.w.a). Suna nuna misalai madaukaka ta hanyar halayensu, suna kira zuwa ga gaskiya, ba sa karkace mata ko da kamar dan yatsa. Kamar yadda hadisin Manzon tsira ya bayyana mana su (Ahlulbaiti) tagwaye ne na Alkur'ani mai girma, ba sa rabuwa domin su ne hakikanin tamka na Alkur'ani da duk abin da yake tattare da shi na ilminsa da tarbiyyarsa. Domin haka Alkur'ani ya ambace su a sarari:
( ÅäøóãÇ íõÑíÏõ Çááå áöíõÐúåöÈó Úäúßõãõ ÇáÑøöÌúÓó Ãåúáó ÇáÈóíúÊö æíõØåøöÑóßõãú ÊóØúåíÑÇð )
"....Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen Babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33)
Duk wanda ya kyautata karatun tarihin Ahlulbaiti (a.s) da aikin da suka yi na ilmi, zai san rawar da suka taka, wacce ita ce ta kan gaba, zai kuma san aiki mai girma da suka yi. Lallai sun yi matukar dagewa wajen kiyaye tsarkakar shari'a da kuma tsare asalin akidar Musulunci har ma suka sadaukar da kansu da yin jihadi domin tabbatar da ka'idojin nan madaukaka a aikace da ja-gorancin al'umma bisa shiriyar wadannan ka'idojin. A kullum tarihin Ahlulbaiti (a.s) madaukaka yana bayyana a matsayin rayayyiyar baiwa wadda take da tasiri ga tunanin al'umma da kiyayewarta, tana wadatar da rayuwarta tana kuma daukaka wayewarta. Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) su ne kudubin al'umma, su ne rumfa matattara mai hada kan al'umma don gyara.
A cikin wannan matakaicin littafin, mun yi kokarin bayyana sashin abubuwan da rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ya kunsa da kuma abin da ya ta'allaka da martabarsu da rawar da suka taka a tarihi. Game da gabatar da wannan littafin, muna kwadaitar da 'yan'uwa musulmi da su samu fa'idantuwa da shiryarwa ta Ahlulbaiti (a.s) da aiki da ita da komawa wajen wannan ja-gaban da kuma koyi da shi da tsayawa sahu guda don fuskantar 'yan rahoton nan masu kokarin raba kan musulmi da wargaza hadin kansu, a dai-dai lokacin da al'ummarmu ta Musulunci take shiga gumurzu mai tsanani tsakaninta da 'yan mulkin mallaka da 'yan gurguzu da yahudawan
Muna kuma kira ga al'ummar musulmi da su fuskantar da dukkan karfinsu wajen kira zuwa ga Musulunci da kare tsarkakan abubuwansa da tauye damar wadanda suka saba shuka sabani da watsa gubar banga-ranci tsakanin al'ummar musulmi.
Ya ku al'ummar Annabi Muhammadu mai girma! Ya masoya Ahlulbaiti! Ya zama wajibi a gare ku da ku hada kai da kuma karfinku waje guda, domin kuwa wannan al'umma, al'umma ce guda, kuma daukakarku da kara-marku ba sa tabbata sai da riko da sakon Musulunci da kuma aiki da Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (s.a.w.a).
"Kuma ka ce: ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9:105)
Mu'assasar Al-Balagh
Ahlulbaiti (a.s.) suna ne mai haskakawa, kuma daukaka ce madawwamiya, sannan suna ne da yake abin kauna ne ga duk rai mai kaunar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma ya yi imani da shi, kuma yake rayuwa bisa shiriyarsa (s.a.w.a). Hakika musulmi sun san wannan madaukakin suna cikin tarihi da kuma cikin martabar nan da take rataye da Alkur'ani mai girma, tun lokacin da Alkur'anin ya yi furuci da wannan sunan mai albarka, kuma ya sanyawa wannan tauraruwan (Ahlulbaiti) lakabin da babu irinsa a duniyar dan Adam:
( ÅäøóãÇ íõÑíÏõ Çááå áöíõÐúåöÈó Úäúßõãõ ÇáÑøöÌúÓó Ãåúáó ÇáÈóíúÊö æíõØåøöÑóßõãú ÊóØúåíÑÇð )
"....Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33)
Da saukar wannan aya mai albarka wani tafarki ya ayyana a matsayin wani abin dogaro da mafuskanta a rayuwar Musulunci. Alkur'ani ya juya fuskoki zuwa ga wannan tafarki tare da tabbatar da dukkan haske a bisa wannan a kan gaba wajen ja-goranci. Har ila yau ya bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) za su taka a rayuwar al'ummar musulmi, ya kuma kebance su da nufin tsarkakewa, abin karfafawa daga Gwani, Masani.
Hakika wadannan ayoyin sun ayyana wata cibiyar harkar tarihi bayan Manzon Allah (s.a.w.a.), harkar da ta dace da al'ada da tsarin hujjar da Musulunci ke dogara da shi. Wannan ya biyo bayan baiwar da Allah Ya yi wa tatattun nan masu albarka (Ahlulbaiti), baiwa ta tsarka-kewa daga zunubai da sabo da kuma laifi. Hakika Alkur'ani mai girma ya tabbatar musu da mafificiyar darajar falala da kuma mafi girman martabobin cancanta, da'a da shugabanci a rayuwa ta Musulunci wacce falsafarta a rayuwa ita ce:
"Lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa". (Surar Hujurat, 349:13)
Babu shakka duk wanda ya bibiyi Alkur'ani mai girma da sunnar Annabi (s.a.w.a) tsarkakkiya zai samu cewa mutanen gidan Annabi mai daraja (s.a.w.a) suna da matsayi kebantacce da muhalli mabayyani. Za a ga cewa shugabannin wannan al'umma da malamanta da masu fassara da masu ruwaya da ma'abuta tarihi da malaman fikihu da masu yawan ibada duk suna ba da labarin wannan matsayi na Ahlulbaiti (a.s) ta dukkan fuskoki da hanyoyi. Lallai littattafan hadisi, tarihi, tafsiri da na adabi da wake da darajoji wadanda musulmi daga mazhabobi da hanyoyin ilmi daban-daban suka wallafa, sun bayyana kebantaccen matsayin da muhalli muhimmi na Ahlulbaiti (a.s). Wadannan littattafai suna magana a kan daukakar wannan itaciya mai albarka. Ana auna imanin mumini ne
Lallai mutanen wannan gida tamkar tauraruwa ce wacce babu kamarta, domin ilmin da suke dauke da shi da kuma takawa da halayen kwarai da darajoji madau-kaka da kare Musulunci da ilminsu da kuma daukar takobi da yaki da zalunci da keta haddi. Domin haka ne musulmi suka dace a kan cewa babu wani daga cikin wannan al'ummar da ya mallaki mukami da daukaka da daraja irin wanda Allah Ya kebance Ahlulbaiti da su…su kadai Allah Ya kebance da tsarkakewa daga dauda da zunubi:
"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa"
Kuma su kadai ne Allah Ya kebance da wajabta kaunarsu a kan wannan al'ummar Ya kuma sanya kaunar ta su wani hakki na Annabi (s.a.w.a) a kan al'umma:
"...Ka ce: "Ban tambayar ku wata lada a kansa, face dai soyayya ga makusanta....". (Surar Shura, 42:23)
Kuma su kadai ne Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta yi musu salati a cikin salloli biyar, Yana gwama ambatonsu da ambaton ManzonSa (s.a.w.a):
"Lalle Allah da Mala'ikunSa suna yin salati wa Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya riga ya koyawa al'um-marsa yadda za ta yi salati a gare shi da alayensa yayin da suka tambaye shi: Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Rasulallah? Sai ya ce da su:
"Ku ce: Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma"
To babu wanda yake da wadannan darajoji da siffofi cikin wanna al'umma face su. Wannan shi ya sanar da mu daukakar Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da wajibcin kaunarsu da koyi da su da kuma tafiya bisa turbarsu. Ba don kome ne Alkur'ani ya jaddada a kan mutanen wannan gida, ya kuma bayyana matsayi da mukaminsu ba, sai domin a yi koyi da su bayan Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma riko da sonsu da karbar (dukkan ilmi da shiriya) daga gare su.
Babu abin da yasa Alkur'ani ya sanar mana da Ahlulbaiti (a.s) ta hanyar da ya nuna mana su face domin wasu dalilai na akida da abin da ya danganci sakon Musulunci kaco-kam, dalilan da suke sa dukkan wani musulmi ya dora tunani mai zurfi da lura da kuma kokarin riskar da kwakwalwarsa hakikanin wannan jama'a (Ahlulbaiti) da take a kan gaba wajen karbar sako. Wannan jama'a kuwa ita ce Allah Ya yi wa baiwar matsayi na shugabanci a cikin al'umma, bayan Alkur'ani da Manzo (s.a.w.a) sun yi masu wannan gabatarwa. A nan gaba za mu bijiro da gabatarwar da Alkur'ani ma
Alkur'ani mai girma shi ne tushen dukkan tunani, shi ne mabubbugar shari'a da ka'idoji. Duk abin da Alkur'-ani ya zo da shi wahayi ne abin saukarwa, kuma magana ce tsarkakkiya daga Allah, yana furuci da tsarin rayuwa yana kuma ayyana dokokin rayuwar. Duk wani musulmi ya san cewa abin da Alkur'ani ya zo da shi shi ne shari'a da sakon da zai bi a rayuwarsa, sannan kuma an wajabta masa aiki da shi da yin tafiya bisa shiriyarsa. Abin lura kuma shi ne Alkur'anin nan ya yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s) da yanayi da tsari kamar haka:
Bari mu bijiro da sashen wadannan ayoyi - suna kuwa da yawa - wadanda suka yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s), domin bayani a kan falalarsu da matsayinsu, gami da kuma sharhi:
"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa". (Surar Ahzabi, 33:33)
Hakika tafsirai da ruwayoyi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da Ahlulbaiti shi ne mutanen gidan Annabi (s.a.w.a) wadanda kuma su ne, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Bayani ya zo cikin littafin Durrul Mansur na Imam As-Suyudi cewa: (Al-Dabarani ya fitar da hadisi daga Ummu Salma cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da Nana Fadimatu cewa: "Taho min da mijinki da 'ya'yansa biyu", sai ta taho da su sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya lullube su da wani mayafi, sa'an nan ya sanya hannunsa bisansu ya ce:
"Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaitin Muhammadu (a wani lafazin zuriyar Muhammadu) to Ka sanya tsirarKa da albarkarKa wa zuriyar Muhammadu kamar yadda Ka sanya wa zuriyar Ibrahima, lalle Kai ne Abin godiya, Mai girma".
Sai Ummu Salma ta ce: "Sai na daga mayafin domin in shiga in kasance tare da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya janye shi daga hannuna ya ce: "Lallai ke kina tare da
An ruwaito hadisi daga Ummu Salma, matar Annabi (s.a.w.a) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance a dakinta bisa wurin kwanciyarsa yana rufe da wani mayafi sakar Khaibara, sai Fadima ta zo da wata tukunya da abinci a cikinta. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ki kira mijinki da 'ya'yansa Hasan da Husaini". Sai ta kira su. Yayin da suke cin abincin sai aya ta sauko wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:
"…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkake-ku tsarkakewa"
Sai Annabi (s.a.w.a) ya kama gefen ragowar sashen mayafinsa ya rufe su da shi, sannan ya fitar da hannunsa daga mayafin ya nuna sama ya ce:
"Ya Allah! Wadannan su ne mutanen gidana, make-bantana, to Ka tafiyar da kazamta daga gare su kuma Ka tsarkake su, tsarkakewa".
Ya fadi hakan har sau uku. Ummu Salma ta ce: "sai na shigar da kaina cikin mayafin na ce: "Ina tare da ku Ya Manzon Allah? Sai ya ce: "ke kina tare da wani alheri", ya fadi hakan har sau biyu (2).
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ci gaba da bayyana wa al'ummarsa ma'anar wannan aya mai girma, yana tsarkake fahimtarta ga wannan aya domin al'umma ta haskaka da ita ta kuma rayu a kan shiryuwarta. An ruwaito shi yana cewa:
"Wannan aya ta sauka ne a kan mutane biyar: Ni kaina, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini…."…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa (3)"
Kamar yadda kuma aka ruwaito daga Ummul
____________
1- Tirmidhi juzu'i na 2 cikin "Manakib Ahlulbaiti" shafi na 308 daga Umar ibn Abi Salama, wanda ya ce: an saukar da ayar "…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" a gidan Ummu Salma. Daga nan sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kira Fadima, Hasan, Husaini da Ali ya rufe su da mayafi, ya ce: "Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaiti, don haka Ka tafiyar da kazamta daga gare su Ka tsarkake su tsarkakewa". Sai Ummu Salma ta ce: "Ya Manzon Allah shin ni ma ina daga cikinsu ne?, sai ya ce mata: "Ke dai kina a matsayinki, ke kina a kan alheri".
2- An ruwaito wannan hadisi cikin littafin Ghayat al-Maram daga Abdullah ibn Ahmad ibn Hambal ta hanyoyi uku daga Ummu Salama, haka nan ma cikin Tafsirin Tha'alabi…haka nan ma Ibn Mardawihi da Khadib daga Abi Sa'id Khudri da wannan ma'ana sai dai kawai 'yan canje-canje na lafazi. Haka nan kuma an ruwaito shi cikin Ghayat al-Maram daga Abdullahi bn Ahmad bn Hambal daga babansa da isinadinsa zuwa ga Ummu Salama, dubi Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an na Allama Tabataba'i kan Ayar Tsarkakewa. Wanda kuma ya ke son karin bayani kan wasu masdarori na musamman kan tafsirin wannan aya da kuma gabatarwa kan Ahlulbaiti guda biyar (a.s.) to sai ya karin bayani da ke karshen wannan littafi.
3- Ibn Jarir da Ibn Abi Hatam da Dabarani sun ruwaito wannan hadisi daga Abi Sa'id Khudri, kamar yadda kuma aka ruwaito shi cikin Ghayat al-Maram da Tha'alabi cikin tafsirinsa, a cikinsa Tirmidhi ya ruwaito shi kuma ya ingantar da shi, da kuma Ibn Jarir da Ibn Munzir da Hakim, kuma duk sun ingantar da shi. Haka nan ma Ibn Mardawihi da Baihaki cikin Sunan dinsa ta hanyar Ummu Salma. Dubi Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an na Allama Tabataba'i.
"…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa(1) ".
A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana wucewa ta kofar Fadima (a.s.) yayin da ya fito sallar asuba yana cewa:
"Salla! Ya mutanen babban gida (Ahlulbaiti), salla! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa "(2).
Hakan nan Alkur'ani yake magana a kan Ahlulbaiti (a.s) yana iyakance mutanen da suke ciki, tsarkaka manisanta daga dukkan dauda da sabo da zunubi da kuma son zuciya. Saboda haka halayen su abin koyi ne haka nan su kansu. Alkur'ani bai sanar mana da su irin wannan sanarwa ba, sai domin ya jaddada matsayi da mukaminsu ga al'umma, ya kuma ja hankulanmu zuwa ga koyi da su da komawa gare su domin fahimtar shari'a da karbar hukumce-hukumcenta daga wurinsu. Ta wannan hanyar, Alkur'ani ya ayyana mana mizani na aikace (wato ayyukan Ahlulbaiti) da ma'aunin da za mu koma gare shi yayin da ra'ayoyi suka sassaba, aka kuma sami bambancin fahimta da I'itikadi (wato abin da mutum ya yarda da shi).
____________
1- Buhari da Muslim duk sun ruwaito ta hanyar A'isha/ Ghayat al-Maram, haka nan kuma Zamakhshari ya ambato shi cikin tafsirin al-Kashshaf ya yin da yake tafsirin Ayar Mubahala.
2- Ibn Mardawihi daga ibn Abi Shaibah da Ahmad da kuma Tirmidhi sun ruwaito kuma sun inganta shi, sannan kuma Ibn Jarir da Ibn Munzir da Dabarani da Hakim, kuma sun inganta shi, da kuma ibn Mardawihi daga Anas. Mai son karin bayani sai ya duba Al- Mizan na Tabataba'i yayin da yake magana a kan Ayar Tsarkakewa.
Dogewar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi, wata da watanni bisa tsayuwa a bakin kofar Aliyu da Fadima (a.s.) yana kiransu da asuba zuwa salla, yana kiransu da Ahlulbaiti ba kome ba ne face sanar da al'umma mutanen da ake nufi da Ahlulbaiti, kana kuma yana fassara wa musulmi ayar tsarkakewa, yana sanar da su matsayin Ahlulbaiti (a.s) tare da jan hankulansu zuwa gare su da kuma wajabta musu kaunarsu da yi musu biyayya da jibinta al'amari gare su.
Dabarani ya ruwaito daga Abu Hamra' cewa:
"Na ga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa kofar Aliyu da Fadima tsawon wata shida yana cewa: "Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa(1) ".
Fakhru al-Razi ya ambata a cikin tafsirinsa, Tafsir al Kabir, cewa bayan saukar ayar: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta", (Surar Daha, 20: 132), Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kan je (kofar) Aliyu da Fadima kowace safiya yana mai cewa: (lokacin) salla (ya yi), ya aikata hakan har na tsawon watanni.
Sannan kuma ya kawo hadisin Hammad bn Salma, daga Aliyu bn Zaid daga Anas cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana wucewa ta dakin Fadima koyaushe ya fito zuwa ga salla har na tsawon wata shida, yana mai cewa: "Salla! Ahlulbaiti! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa(2) ".
____________
1- Jami al Usul, juzu'i na 9, shafi na 156 ya nakalto daga Sahih Tirmidhi, haka nan ma Hakim ya ruwaito shi cikin Mustadrak juzu'i na 3 shafi na 158, kuma ya inganta shi.
2- Fadhl Aalulbaiti na Takiyuddin Ahmad bn Aliyu al Makrizi (wanda ya rasu a shekara ta 845 bayan hijira), shafi na 21.
Sannan a sarari yake cewa daga abin da ayar: "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa", take nuni da shi da kuma amfani da lafazin maza ba lafazin mata ba da aka yi, wato (Úäßã) da kuma (íØåøöÑßã), akwai nuni zuwa ga wadanda ake nufi, su ne wadannan mutane biyar din. Bayani ya zo a cikin Tafsirai cewa da Allah Yana nufin matan Annabi (s.a.w.) ne da Yayi amfani da kalmar (Úäßäø) da ta (íØåøöÑßäø) da magana irin wacce ake yi wa mata.
A baya mun riga da mun ga Hadisin Mayafi lokacin da aka saukar da wannan aya ta tsarkakewa yayin da Ummu Salama taso shiga cikin wannan mayafi amma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce mata ke dai kina a matsayinka, kuma kina a kan alheri.
Hakan yana nuna mana rashin shigar matayen Annabi (s.a.w.a) cikin wannan aya ta tsarkakewa, kana kuma babu daya daga cikinsu da ta yi ikirarin saukar wannan aya a kansu, duk kuwa da cewa ayar ta falaloli da kuma matsayi mai girma ce.
Wannan ayar ta fitar da wata hanya wacce abin da take nuni da shi da abin da ta tattara suna da yalwar gaske. Tana jan hankulanmu zuwa ga batutuwa na asasi a
"Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu kara masa kyau a cikinsa, lallae Allah Mai gafara ne, Mai godiya". (Surar Shura, 42:23)
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana ko wane ne ake nufi da wannan aya mai albarka, kuma ko su waye kaunarsu da biyayya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu ya wajabta ga musulmi. Malaman tafsiri da hadisi da tarihi sun ruwaito cewa "Makusantar Annabi" wadanda ake nufi a wannan ayar su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.).
Zamakhshari ya fada a cikin tafsirinsa al-Kashshaf cewa: "An ruwaito cewa mushrikai sun taru a wurin taronsu sai sashinsu ya ce wa sashi: "shin kuna ganin Muhammadu zai nemi wani lada a kan abin da yake kira gare shi? Sai aya ta sauka cewa: "Ka ce: "Ba ni tambaya
Sai Zamakhshari ya ce: "Kuma an ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka sahabbai sun tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda sonsu ya wajabta a kanmu". Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu".
A cikin Musnad na Imam Ahmad bin Hambal - da isnadinsa ambatacce -, daga Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da zance Allah Ta'ala cewa: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ya sauka, sai mutane suka tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Rasulallah! Su waye danginka wadanda sonsu ya wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'yayansu biyu(2) ".
Fakhrurrazi ya tabbatar da wannan zancen cikin Tafsirul Kabir bayan ya ambaci maganar Zamakhshari dangane da Alu Muhammad (dangin Muhammadu). Ga abin da yake cewa:
"Ni ina cewa dangin Muhammadu su ne wadanda al'amuransu suke tare da na shi (Annabi), to kuma duk wadanda kusancinsu yafi kusa da shi da kuma cika, to su ne aalu (dangin Annabi). Babu shakka cewa Fadima da Ali da Hasan da Husaini suna da mafi tsananin alaka da Manzon Allah (s.a.w.a.), wannan kuwa an nakalto ta hanyoyi daban. A saboda haka ya wajaba su kasance su ne Aalu".
Har ila yau an sassaba a kan ma'anar aalu, wasu sun ce su ne danginsa, wasu kuma sun ce su ne al'ummarsa. To idan mun dauke shi da ma'anar dangi, to su din dai su ne aalu din, idan kuma muka dauke shi da ma'anar al'umma(3)wadanda suka karbi kiransa to nan ma dai su ne aalu din. Don haka a bisa dukkan yanayi dai su aalu din ne dai.
____________
1- Fakhrurrazi cikin Tafsirul Kabir yayin tafsirin Surar Shura aya ta 23.
2- Ghayat Maram yayin tafsirin ayar.
3- Sanannen al'amari ga mai karatu cewa wannan fassara ta yi nisa ga hakikanin ma'anar kalmar, don kuwa ma'anar kalmar aal a cikin harshen Larabci a fili yake, babu yadda za a fassara kalmar aal da al'umma.
"Fadima yanki ne daga gare ni, abin da yake cutar da ita yana cutar da ni ".
Kamar yadda ingantaccen hadisi ya tabbatar cewa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Aliyu, Hasan da Husaini (a.s.). To idan wannan ya tabbata, lallai kaunarsu ta zama wajibi a kan dukkan al'umma domin fadin Allah (S.W.T.) cewa:
"Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku...". (Surar Ali Imrana, 3:31)
"...ku bi shi, don ku shiryu". (Surar A'arafi, 7: 158)
Da kuma fadinSa cewa:
"...to, wadanda suke sabawa umurninSa, su kiyayi abkuwar wata fitina....". (Surar Nur, 24: 63)
"Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga
Ba a samun wannan girmamawa ga wani wanda ba su dangin ba. To duk wannan yana nuni da cewa kaunar alayen Muhammadu wajiba ce.
Imam Shafi'i yana cewa:
Ibn Munzir da ibn Abi Hatam da ibn Mardawihi da Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir daga Ibn Abbas sun ce: "Yayin da ayar: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka sai mutane suka ce: "Ya Manzon Allah su wane ne makusantanka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu (3)".
A cikin Mu'ujam din dai ya inganta daga Imam Hasan dan Ali (a.s.) cewa wata rana yayin da yake
____________
1- Rafdhu a wajen malaman Ahlussunna shi ne yarda da cewa Imam Ali bn Abi Talib (a.s.) shi ne halifan Manzon Allah (s.a.w.a.) na farko bayan rasuwarsa. Kuma Rafidhi shi ne wanda ya yarda da hakan.
2- Fakhrurrazi cikin Tafsirul Kabir, yayin tafsirin Surar Shura aya ta 23.
3-Ihya'ul Mait bi fadha'il Ahlilbaiti na Suyudi shafi na 8, kuma Suyudin ya ruwaito shi cikin Durrul Mansur , juzu'i na 6 shafi na 7 ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, sannan kuma Dabarani ma ya fitar da shi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 125. Haka ma Tabari ya ruwaito shi cikin Zakha'ir shafi na 25, yana cewa: "Ahmad ya fitar da shi cikin Munakib. Kamar yadda kuma Ibn Sabbag al-Maliki ya ruwaito shi daga Nabawiy daga Ibn Abbas, shafi na 29. Hakan nan kuma Kurdabi ya fitar da shi cikinsa Jami' al-Ahkam al-Kur'an da ruwayar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, juzu'i na 16, shafi na 21-22.
"Ni ina daga cikin Ahlulbaitin da Allah Ya farlanta kaunarsu a kan kowane musulmi, inda Ya ce: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta".
(Ibn Abi Hatam ya fitar daga Ibn Abbas cewa: (lokacin da aka karanta wannan aya): (….æãä íÞÊÑÝú ÍÓäÉ) "…kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau…) (Surar Shura, 42: 23), sai ya ce: "(hakan) shi ne kaunar Ahlulbaiti(1) ".
Alkur'ani mai girma ya tabbatar da tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da ayar tsarkakewa kuma ya fahimtar da al'umma matsayinsu da rawar da suka taka dangane da daukaka sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma. Da wannan ne kuma suka cancanci soyayya da riko zuciya daya wanda Alkur'ani ya yi umurni da shi a wannan ayar.
Abin da Alkur'ani yake nufi da wannan soyayya ba wai bege da doki da soyayya ta zuci kawai ba ne, domin babu wata fa'ida ga soyayya da kaunar da take cikin rai da zuciya, amma ba ta da wata bayyana a waje (a fili). Lallai tabbatar kauna da soyayya ga makusantan Manzon Allah (s.a.w.a.) yana samuwa wajen koyi da su da kuma rayuwa bisa turbarsu da lizimtar mazhabarsu da abin da ya fito daga gare su, da kuma daukar matsayinsu a al'umma matsayin shugaba kuma ja-gora.
Yayin da Alkur'ani yake sanya wannan ayar a bisa harshen Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma Yake umurtansa da cewa ya sanar da al'ummarsa da mutane bai daya cewa ba ya nufin samun wani lada ko sakayya daga gare su domin isar da sako da jure wahalhalun kira zuwa ga Allah da kuma shiryar da su, face soyayya ga makusantansa (s.a.w.a) da tsarkake zuciya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu, abin da kurum Alkur'ani yake
____________
1- Tabataba'i daga Sheik Tusi.
Ba don lamuncewar da ake samu daga Ahlulbaiti (a.s) ba, da kuma ikon ja-gorancin al'umma a kan hanyar shiriya da lamunce hakan ba, da Alkur'ani bai saukar da soyayyar ba, kuma da ba a umurci Manzon Allah (s.a.w.a.) da ya sanya hakkinsa (ladansa) a kan al'umma shi ne kaunar Ahlulbaiti (a.s) ba.
Wannan tarin bayanai da muka kawo na maganganun malaman tafsiri da hadisi sun nakalto mana fassarar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wa wannan aya mai albarka, da sanya kaunar Ahlulbaiti (a.s) cikin zukata kuma ya sanya kaunar ta hakika ce mai tabbata cikin zuciyar ko wane musulmi, tana bayyana a cikin halayensa, tunaninsa da kuma begensa. Soyayyar nan tana kuma ayyana matsayarsa a kan Ahlulbaiti (a.s) da makiyansu da masoyansu da kuma bin tafarki da kuma abin da ya tabbata daga gare su na hadisi, fikihu, tafsiri, tunani, akida, shari'a da kuma tsarin aiki na jagoranci da siyasa.
Wannan lambar girma da daukaka tana da manufa da abin da take nuni da shi a kebance, wanda ya kamata musulmi su kiyaye shi kuma su riski zurfinsa.
"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa'an nan kuma mu kankantar da kai,
Wani abu mai madauwamin tarihi wanda malaman tarihi da tafsiri sun ruwaito shi ya auku, wanda kuma yake nunawa al'umma irin girma da daukakan Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a.), su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) a wajen Allah (S.W.T.) da kuma matsayinsu a cikin wannan al'umma.
Wannan abin kuwa kamar yadda su malaman tafsiri da tarihin suka kawo shi ne cewa wata tawaga(1) ta kiristocin Najran ta zo domin ta yi jayayya da Manzon Allah (s.a.w.a.) don a gane waye yake kan gaskiya. Nan take sai Allah Ya umurce shi cikin wannan aya mai albarka da ya kira Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) ya fita da su zuwa wani kwazazzabo, ya kuma kira Kiristocin da 'ya'yansu da matansu su fito sannan a yi addu'ar Allah Ya saukar da azaba kan makaryata.
Zamakhshari a cikin Al-Kashshaf yana cewa:
"Yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kiraye su zuwa ga Mubahala(2) , sai suka ce: sai mun koma mun yi nazari. Da suka kebanta sai suka ce wa shugabansu; "Ya Abdul Masih! Me ka ke gani? Sai ya ce: "Wallahi, Ya ku jama'ar Nasara, kun sani cewa Muhammadu Annabi ne wanda aka aiko shi kuma hakika ya zo muku da bayani mai rarrabewa game da al'amarin sahibinku. Wallahi babu wata al'umma da ta taba yin mubahala da wani Annabi face babbansu ya halaka, karaminsu kuma ya gagara girma, to idan ko kun aikata hakan to lallai za mu halaka. Idan kun zabi riko da adddininku da zama bisa abin da kuke kansa to ku yi bankwana da mutumin na
____________
1- Wannan tawaga ta kumshi manya-manyan shuwagabannin kiristocin Larabawa kamar haka: Abdul Masih, wanda ya kasance shugabansu, da kuma al-Ayhma, wanda ya kasance mai kula da al'amurran gudanarwa da ayyukan ibada, da kuma Abu Hatam ibn Alkama, wanda ya kasance bishof ne kana kuma kula da makarantunsu. Dubi Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki a sashin gabatarwar marubuci.
2- Yin 'yar kure tsakanin vangare biyu kan Allah Ya saukar da azaba a kan vangaren da ba ya kan gaskiya. A takaice dai yin la'ananneniya tsakanin vangarori biyu don gano wani vangare ne ya ke kan gaskiya.
Ko da gari ya waye sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fito yana mai sammako, yana rungume da Husaini (a.s.) yana rike da hannun Imam Hasan (a.s.), Fadima (a.s.) kuwa tana biye da shi sannan shi kuma Aliyu (a.s.) yana bayanta, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu: "Idan na yi addu'a ku ce amin".
Ko da Kiristocin nan suka hango Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa da tasa tawagar, sai wannan Fadan da ke cikinsu ya ce musu: "Ya jama'ar Nasara! Wallahi ni ina ganin wasu fuskokin da idan Allah Ya so gusar da wani tsauni daga muhallinsa domin alhurmansu sai Ya yi. Don haka (ina shawartarku) da kada ku yi Mubahala da su don za ku halaka ya zamo babu wani kiristan da zai wanzu a bayan kasa har tashin kiyama".
To daga nan sai suka ce wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Abal Kasim! Mun yi shawara ba za mu yi mubahala da kai ba, mu bar ka a kan addininka, mu kuma mu tabbata a bisa addininmu".
Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu:
"Idan kun ki yarda da mubahala, to ku musulunta duk hakkin da musulmai ke da shi kuma kuna da shi, duk kuwa abin da yake kansu yana kanku". Amma sai suka ki, don haka sai ya ce musu: "To ni zan yake ku".
Sai suka ce : "Ba mu da karfin yaki da Larabawa, amma za mu yi sulhu da kai cewa ba za ka kai mana hari ba, ba za ka tsoratamu ba, ba za ka fitar da mu daga addininmu ba. Mu kuma za mu kawo riguna dubu biyu duk shekara, dubu daya cikin watan Safar dubu dayan kuwa cikin watan Rajab, da kuma sulken karfe guda talatin". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi sulhu da su akan hakan, sa'an nan ya ce:
"Na rantse da Wanda raina yake HannunSa, hakika
Sannan Zamakhshari ya ci gaba da bayani kan tafsirin Ayar Mubahala da matsayin Ahlulbaiti (a.s) bayan da ya ba da shaidar matsayinsu mai girma da hadisin Ummul Muminina A'isha, ya ce:
"(Annabi) Ya gabatar da su (Ahlulbaiti) a kan kansa ne wajen ambato domin ya yi mana tambihi a kan taushin matsayinsu da kusancinsu (ga Allah), don ya nuna cewa su abin gabatarwa ne a kan kai kuma abin fansa da su. Wannan kuwa shi ne mafi karfin dalili a kan falalar Ashabul Kisa'i(1).
Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi(2).
Wannan yanayi (na fitowa domin Mubahala) yana nuna mana fitowar rundunar imani ne tana fuskantar rundunar shirka, sannan kuma wadanda suka fito (a sashin imani) su ne 'yan kan gaba wajen karbar shiriya, su ne magabatan al'umma kuma mafi tsarkin cikinsu, rayuka ne wadanda Allah Ya tafiyar da dauda ga barinsu kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa. Ba a mayar masu da addu'a, ba a kuma karyata wata maganarsu. Daga nan za mu fahimci cewa dukkan abin da ya zo mana daga Ahlulbaiti (a.s) yana gudana ne bisa wannan matsaya (ta tsarki da fifiko) sawa'un wani tunani ne ko shari'a ko ruwaya ko tafsiri ko shiryarwa da fuskantarwa. Domin su ne magaskanta cikin maganarsu da harkar
____________
1- Ashabul Kisa' (ma'abuta mayafi), suna ne da ake kiran mutanen da suka kasance tare da Manzon Allah (s.a.w.a.) cikin mayafinsa inda daga baya aka saukar da Ayar Tsarkakewa a gare su. Su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda aka ambata a baya.
2- Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi.
Da Ahlulbaiti (a.s) ne Alkur'ani ya kalubalanci abokan gaba Musulunci, ya sanya masu jayayya da su su ne makaryata abubuwan bijirowar tsinuwa da azaba; "…sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata".
Shakka babu da ba don an lamunce mana tabbatuwa da kuma gaskiya cikin abin da yake fitowa daga gare su ba, da Allah bai ba su wannan daukaka ba kuma da Alkur'ani bai yi furuci da wannan ba.
Fakhrurrazi ya kawo cikin tafsirinsa Alkabir kwaton-kwacin abin da Zamakhshari ya ruwaito, inda tafsirinsu suka dace da juna a wannan matsayin. Sannan ya yi karin bayani a kan zancen Zamakhshari da cewa:
"Ka sani cewa wannan ruwaya daidai take da abin da aka daidaita a kan ingancinsa tsakanin ma'abuta tafsiri da hadisi(1)".
Allama Tabataba'i ya ce wadanda ake nufi a wannan aya kuma wadanda Allah Ya yi nufin (amfani da su wajen) tsinewa abokan gabarsu, su ne Manzon Allah (s.a.w.a.), Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Ga abin da Allama Tabataba'in ya ce:
"Malaman hadisi sun hadu a kan ruwaito wannan ruwaya da samun karbuwarta, kuma ma'abuta manyan littattafai kamar su Muslim a cikin Sahihinsa da Tirmidhi a nasa Sahihin, sun tabbatar da wannan ruwaya, sannan malaman tarihi sun karfafa ta. Kana kuma malaman tafsiri sun hadu a kan kawo wannan ruwaya cikin tafsiransu ba tare da wata suka ba, ba kuma kokwanto. Haka nan kuma akwai malaman hadisi da tarihi kamar su Dabari da Abul Fida da Ibn Kathir da Suyudi da sauransu".
A cikin wannan aya mai albarka, Allah da ManzonSa
____________
1- Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a kan Ayar Mubahala.
A cikin ayar akwai ma'anoni masu zurfi na harshen da aka yi amfani da shi cikin maganar wadanda lallai ne a yi la'akari da su, hakan kuwa shi ne danganta wadannan Taurari (Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini) da Annabi (s.a.w.a.), wato cewan da aka yi "'ya'yanmu" da "matanmu" da "kanmu".
Ba don faruwar wannan lamari da fitar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi da wadannan Taurari tare da shi ba, da mai yiyuwa zukata su koma ga matan Annabi (s.a.w.a) wajen kalmar "matanmu", wajen kalmar "'ya'yanmu" kuwa zuwa ga Fadima da sauran 'ya'yan Ma'aiki (s.a.w.a.), sannan wajen kalmar "kanmu" kuwa zuwa ga zatin Annabi (s.a.w.a) mai tsarki shi kadai.
Amma fita da wadannan mutanen hudu da Annabi ya yi tare da shi koma bayan wasunsu, ya fassara mana cewa mafificiyar macen wannan al'umma kuma abin koyi gare ta ita ce Nana Fadima (a.s.), zababbun 'ya'yan musulmi kuwa su ne Hasan da Husaini (a.s.), don kuwa Alkur'ani ya dangantasu ga Annabi (s.a.w.a.) sai suka zama 'ya'yansa, kamar yadda aya ta nuna. Kana kuma Alkur'ani ya dauki Aliyu (a.s.) tamkar ran Manzo (s.a.w.a).
"Lalle, Allah da Mala'ikunSa suna salati ga Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56)
A cikin ayoyin da suka gabata, Alkur'ani mai girma ya yi magana a kan tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu da kuma cewa su ne mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a.). Masu fassara kuma sun iyakance wadannan mutane da sunayensu cewa su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.).
To wannan ayar kuwa ta kawo umurni ne na wajibcin yin salati ga Annabi (s.a.w.a) da alayensa madaukaka da kuma kebancesu, koma bayan wasunsu da kuma girmama mukaminsu da karamarsu domin al'umma ta san matsayinsu wajen sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma.
Fakhrurrazi ya kawo cikin Tafsirinsa abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.) kan tafsirin wannan aya mai albarka, inda ya ce:
"An tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Manzon Allah? Sai ya ce:
"Ku ce: Ya Allah Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi tsira ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, Ka yi albarka ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai Abin godiya ne, Mai girma".
Kafin ya kawo wannan nassin, sai da ya bijiro da
"Wannan dalili ne kan mazhabar Shafi'i domin umurnin na wajibci ne(1) saboda haka salati ga Annabi yana wajabta. Kuma salatin ba ya wajaba in ba a tahiya ba, saboda haka yana wajaba ne a cikin tahiya(2) ".
Fakhrurrazi ya karkare da cewa: "Idan Allah da Mala'ikunSa sun yi wa Manzon Allah (s.a.w.a.) salati, to wata bukata kuma yake da shi ga salatinmu?
To muna iya cewa yi masa salati ba wai don yana bukatuwa ga salatin ba ne, don kuwa idan ba haka ba ne, to ai babu bukatar salatin Mala'iku bayan salatin Allah a gare shi. Amma ba kome ba ne yasa muke masa salati face bayyana girmamawarmu gare shi, da tausayawarSa gare mu domin Ya saka mana domin salatin. Don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya yi mini salati sau guda, Allah Zai masa goma").
A ciki Durrul Mansur na Imam Suyudi, Abdurrazak da Ibn Abi Shaiba da Ahmad da Abd bn Humaid da Bukhari da Muslim da Abu Dauda da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ibn Mardawihi, daga Ka'ab bn Ujrah, ya ce wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, mun san yadda ake maka sallama, to ya ya ake maka salati? Sai ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka yi tsira a kan Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi tsira kan Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma".
Malamin ya kawo hadisai goma sha takwas ban da wannan hadisin dukkan su suna nuni ga tarayyar Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.) da shi cikin salati. Ma'abuta littattafan hadisi sun ruwaito su daga sahabbai daban-daban. Ga wasu daga cikinsu: Ibn Abbas da Dalha da Abu Sa'id al-Khudri da Abu Huraira da Abu Mas'ud al-Ansari da Buraida da Ibn Mas'ud da Ka'ab bn Umrah da
____________
1- Jumlar "....ku yi salati a gare shi.." wacce ta zo cikin ayar tana nuni da wajibci ne, don malaman Usul al-Fikh sun bayyana fi'ilin umurni a matsayin yana nuni ga wajibci ne, wasu ma suna ganin cewa a duk lokacin da fi'ilin umurni ya zo cikin Alkur'ani ko hadisi yana nuni ga wajibci ne sai dai idan akwai wani abin da yake nuni da cewa wajibcin ya koma zuwa ga mustahabi.
2- Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a tafsirin Surar Ahzab aya ta 56.
Sannan kuma a cikinsa Imam Ahmad da Tirmizi sun fitar da hadisi daga Hasan bn Ali (a.s.) cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a gurinsa bai mini salati ba (1)".
Kamar haka ne malaman fikihu suka ruwaito wajibcin salati ga Annabi Muhammadu da Alayensa (a.s.) cikin tahiyar salla(2) da wajibcin kawo ambaton Alayen Muhammadu cikin salla.
Duk wanda ya sa ido a kan wannan aya zai fahimci cewa manufar shar'anta salatin da lizimtar da shi shi ne girmama Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.), wadanda Allah Ya tafiyar da dauda daga gare su kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa, domin al'umma ta yi koyi da su, ta bi tafarkinsu, kuma ta fake a gare su lokacin fitinu da sassabawa.
To wadannan da salla ba ta inganta sai gami da an masu salati, su ne Shuwagabannin al'umma, su ne a ka yi nuni da su kuma aka lamunce a yi koyi da su. Ba don tabbata da lamuncewar tsayuwarsu da kubutar abin da ya fito daga gare su ba, da Allah bai umurci musulmi a dukkan zamunna da su rataya da su da yi musu salati cikin kowace salla ba.
Hakika cikin wannan maimaitawa - maimaita salati ga Annabi da Alayensa, da kuma farlanta hakan a kowace salla - akwai jaddadawa da jan hankulan musulmi cikin kowace salla saboda muhimmanci Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da kuma koyi da su da rayuwa bisa tafarki da hanyarsu.
"Hakika mutane na gari suna sha daga wani kofin (giya) da mahadinta ya kasance mai kamshin kafur ne.
____________
1- Almizan fi Tafsiril Kur'an na Allamah Tabataba'i, juzu'i na 16, shafi na 344.
2- Allamah Hilli wanda ya kasance daga cikin manyan malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s), kuma yana daga cikin sanannun karni na bakwai bayan hijira, yayin da yake ambaton wajiban salla yana cewa: (Na bakwai) tahiya, wajaba ce a dukkan salla mai raka'o'i biyu sau guda, sannan kuma sau biyu a salloli masu raka'o'i uku da hudu, da mutum zai bar ta da gangan, to salla ta vaci. Akwai abubuwa guda biyar a cikin ko wane daya daga cikinsu da suka kasance wajibai, su ne kuwa: zama gwargwadon tahiya, yin shahadojin nan guda biyu da salati ga Annabi da Alayensa (a.s.). Dubi Shara'ii Islam, juzu'i na 1, babin salla.
A cikin wadannan ayoyi masu albarka, Alkur'ani ya
Abin da ya faru har ya sa aka saukar da wadannan ayoyi dominsa yana nuni ne da matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kaiwarsu matuka wajen aikatawa da lizimtar shari'a da kuma fuskantar Allah cikakkiya. Kuma su ne mutanen kirkin da aka yi musu albishir da aljanna, to duk wanda ya yi koyi da su, ya yi tafiya a kan tafarkinsu, to za a tashe shi tare da su. Zamakhshari ya kawo bayani kan wannan aya cikin tafsirinsa. Ga abin da ya ce:
(Daga Ibn Abbas (r.a.): Wata rana Hasan da Husaini (a.s.) sun yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da wasu mutane suka ziyarce su don gai da su, sai ya ce wa Imam Ali (a.s.): Ya Abal Hasan, da dai ka yi bakance kan rashin lafiyar 'ya'yanka. Sai Aliyu da Fadima da baiwarsu Fiddha suka ce idan suka sami sauki daga wannan ciwo nasu, za su yi azumin kwanaki uku. Sai kuwa suka warke, alhalin kuwa a wannan gida mai albarka babu wani abu na daga abinci. Sai Aliyu (a.s.) ya yi bashin sa'i uku na Sha'ir daga wani Bayahude mai suna Sham'un Alkhaibari, daga nan sai Fadima ta nika sa'i guda ta yi gurasa biyar, adadin mutanen gidan. Sai ta sanya gurasar a gabansu domin su yi buda baki, bayan lokacin shan ruwa ya yi. Sun shirya za su ci kenan sai ga wani almajiri ya tsaya a kofa ya ce: Assalamu Alaikum, mutanen gidan Muhammadu (s.a.w.a), ni miskini ne daga miskinan musulmi, ku ciyar da ni, Allah Ya ciyar da ku daga abincin aljanna. Sai suka fifita shi (wajen cin abincin) wato suka dauka suka ba shi, su kuwa suka kwana ba su dandani kome ba, sai ruwa, sannan kuma
Da suka wayi gari sai Aliyu (r.a.) ya kama hannun Hasan da Husaini suka nufi gurin Manzon Allah (s.a.w.a.). Yayin da Annabi (s.a.w.a) ya gansu suna karkarwa kamar 'ya'yan tsaki saboda tsananin yunwa, sai ya ce: "Babu abin da zai bakanta mini rai fiye da halin da na ganku a ciki". Sai ya tashi ya tafi tare da su sai ya ga Fadima (a.s.) tana wurin sallarta alhali bayanta ya mannu da cikinta, idanunta sun fada. Ganinta cikin irin wannan hali ya bakanta wa Manzon Allah (s.a.w.a.) rai, sai ga Jibrilu (a.s.) ya sauko ya ce: "Karbi ya Muhammadu, Allah Na tayaka murna batun Ahlulbaitinka", sai ya karanta masa wannan surar(1) .
Hakika ayoyin Alkur'ani masu yawa sun sauka da batun Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s.) wanda aka yi tarbiyyarsa cikin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.) tun yana karami(2) . Ya tashi karkashin kiyayewarsa (s.a.w.a) don haka ya kwaikwayi halayensa. Ya yi imani da shi, gaskanta shi da kuma binsa tun yana dan shekara goma. Sannan kuma Imam Ali (a.s.) ya kasance mai daukar tutar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma shi ne jarumin sojansa wanda ya kere kowa a dukkan yake-yakensa, da suka hada da Badar, Uhud, Hunain, Ahzab, Khaibar,
____________
1- Zamakhshari cikin littafin al-Kashshaf, yayin tafsirin Surar Insan, haka nan kuma Fakhrurrazi shi ma ya kawo wannan ruwaya cikin littafinsa na Tafsir al-Kabir . Haka ma Tabrisi cikin Majma'ul Bayan.
2- Birnin Makka ya fuskanci fari mai tsananin gaske kafin aiko Ma'aiki (s.a.w.a.), don haka sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya dauko Imam Ali (a.s.) daga wajen mahaifinsa Abu Talib (a.s.) zuwa gidansa don yi masa tarbiyya da kuma saukaka wa Baffansa (Abu Talib) wanda ya kasance fakiri ne.
Idan muka yi bincike kan asbabun Nuzul (dalilan saukar ayoyi), za mu samu cewa abin da ya sauka dangane da Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib (a.s.) - ban da abin da muka ambata na Ahlulbaiti (a.s) - suna bayani ne:
Bari mu ambato wasu misalai kamar haka:
Ayar Wilayah:
"Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da ManzonSa da wadanda suka yi imani, wadanda suke tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka alhali suna masu ruku'i. Kuma wanda ya jibinci Allah da ManzonSa da wadanda suka yi imani, to, kungiyar Allah su ne masu rinjaye". (Surar Ma'ida, 5: 55-56)
Zamakhshari cikin tafsirinsa ya bayyana cewa:
"Wannan aya ta sauka ne dangane da Aliyu (Allah Ya karrama fuskarsa) lokacin da wani ya roke shi alhali
Al-Wahidi ya ambata cewa al-Kalbi ya fadi cikin dalilin saukar wannan aya, cewa:
"Lalle karshen wannan aya a kan Aliyu dan Abi Talib (r.a.) take domin ya ba da zobensa ga wani mai bara alhali yana cikin ruku'un salla(2) ".
Littattafan tafsiri da hadisi masu yawa sun ambato cewa wannan aya mai albarka ta sauka ne dangane da Imam Ali (a.s.). Akwai cikakken bayani kan hakan cikin wadannan littattafa ga mai karin bayani(3) .
Ayar Tabligh (Isar da Sako):
íÇ ÃíøõåóÇ ÇáÑøóÓõæáõ ÈóáøöÛú ãó ÃõäúÒöáó Åáóíúßó ãöäú ÑóÈøößó æóÅäú áãú ÊóÝúÚóáú ÝóãóÇ ÈóáøóÛúÊó ÑöÓóÇáóÊóåõ æÇááåõ ÈóÚúÕöãõßó ãöäó ÇáäøóÇÓö..
"Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar maka daga Ubagijinka. Kuma idan baka aikata ba, to, ba ka iyar da sakonSa ba kenan, kuma Allah Zai tsare ka daga mutane....(4)" (Surar Ma'ida: 5:67)
____________
1- Zamakshari cikin al-Kashshaf yayin tafsirin Surar Ma'ida aya ta 55.
2- Al-Wahidi cikin Asbabun Nuzul / Surar Ma'ida aya ta 55.
3- Mai son karin bayani sai ya koma ga.....
4- Hakim al-Haskani cikin littafin Shawahid al-Tanzil juzu'i na 1 shafi na 190 ya ruwaito cewa:
"Daga Abdulla bn Abi Aufa, yana cewa: Na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karanto wannan aya (sai ya karanto ayar Tabligh) a Ranar Ghadir Khum, sai ya daga hannayensa har ana ganin farin hammatansa, ya ce: "Ku sani duk wanda ya zamanto shugabansa, to Aliyu shugabansa ne".
Haka nan ma Al-Wahidi cikin Asbabun Nuzul shafi na 135, da kuma Suyudi cikin Durrul Mansur juzu'i na 2 shafi na 198, daga Abi Sa'id al-Khudri cewa: Wannan aya ta sauka ne dangane da sha'anin Aliyu bn Abi Talib.
An ruwaito cewa, yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake dawowa daga Hajjin Ban Kwana(1) sai wannan aya (da muke magana a kanta) ta sauka a gare shi a rana ta goma sha takwas ga watan Zul Hajji(2).
To sai ya yada zango a Ghadir Khum daga Juhfa(3) , inda a nan ne kuma hanyoyi suka rarrabu zuwa birnin Madina, Masar da kuma Sham. Sai ya tsaya a nan har wadanda suke bayansa suka iso, wadanda suke gaba kuwa suka komo inda yake(4) . Akwai wasu itatuwan kaya a rarrabe, sai aka hana Sahabbai sauka a karkashinsu. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sa aka sare wadannan itatuwa na kaya(5) , sai ya sa aka yi kiran salla(6) , ya sallaci azahar tare da jama'a cikin garjin rana(7) . Daga nan sai ya mike ya gudanar da huduba bayan ya yi godiya ga Allah da kuma tsarkake Shi da kuma yin wa'azi ga al'umma, sai ya ce:
"Hakika an kusa a kira ni kuma in amsa, ni kuma abin tambaya ne ku ma abin tambaya ne, to me za ku ce?
Sai suka amsa: "Za mu ba da shaidar cewa kai ka isar da sako, ka yi nasiha, to Allah Ya saka maka da alheri".
Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Shin ba kwa shaidar cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah ba, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, da cewa aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce"?
Sai suka ce: "Haka ne, mun shaida hakan".
Sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida", sai ya ci gaba da cewa: "Shin ba kwa ji".
Sai suka ce: "Na'am" (watau suna ji).
Sai ya ce: "Ya ku mutane! Ni mai gabata ne ku kuma
____________
1- Majma' al-Zawa'id, juzu'i na 9, shafi na 163-165.
2- Hakim al-Haskani ya ruwaito shi cikin juzu'i na 1, shafi na 192-193.
3- Majma' al-Zawa'id, juzu'i na 9 shafi na 163-165, da kuma Ibn Kathir juzu'i na 5 shafi na 209-213.
4- Tarikh ibn Kathir, juzu'i na 5 shafi na 213.
5- Majma' al-Zawa'id.
6- Musnad Ahmad juzu'i na 4 shafi na 281, Sunan ibn Maja babin falalar Ali, ta Tarikh ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 209 da 210.
7- Musnad Ahmad, juzu'i na 4, shafi na 281, Sunan Ibn Majah, babin falalar Ali, da kuma ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 212.
Sai wani ya yi kira ya ce: "Mene ne wadannan nauyaya biyu, Ya Manzon Allah?
Sai ya ce masa: "Littafin Allah, gefe yana hannun Allah, gefe kuma yana hannunku, to ku yi riko da shi, ba za ku bata ba, ba za ku canjba ba, da kuma iyalina, mutanen gidana. Hakika Mai Tausayawa, Masani, Ya sanar da ni cewa su biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki. Na roka musu wannan wajen Ubagijina, saboda haka kada ku gabace su sai ku halaka, kada ku takaita (ga barinsu), sai ku halaka, kada ku sanar da su domin sun fi ku sani(2) .
Sannan sai ya ce: "ashe ba ni ne nafi cancanta ga kowane mumini a kan kansa ba"?
Sai suka ce: "Haka ne, Ya Manzon Allah(3) ".
Daga nan sai ya kama hannun Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya daga sama har mutane suka ga farin hammatarsa(4) , ya ce:
Ya ku mutane! Allah Shi ne Majibincina, ni kuma ni ne majibincinku(5) . To duk wanda na ke majibincinsa, wannan Aliyun majibincinsa ne. Ya Allah! Ka jibinci wanda ya jibince shi, Ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi(6) , Ka taimaki wanda ya taimake shi, Ka wulakanta wanda ya wulakanta shi(7) , Ka so mai son sa, Ka ki wanda ya ki shi(8) ".
Sannan sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida(9) ".
Ba su (Manzon Allah da Aliyu) rabu ba har sai da Allah Ya saukar da wannan aya:
____________
1- Basra sunan wata alkarya ce da ke kusa da Damaskus, San'a' kuma tana kusa da garin Bagadaza.
2- Majma' al-Zawa'id da wasu kalmominsa daga ruwayar Hakim, juzu'i na 3, shafi na 109-110, da kuma Ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 209.
3- Musnad Ahmad, juzu'i na 1, shafi na 118 da 119, da kuma juzu'i na 4 shafi na 281, da Sunan Ibn Majah, juzu'i na1, shafi na 372, da Ibn Kathir, juzu'i na 5 shafi na 209.
4- A cikin ruwayar Hakim al-Haskani, juzu'i na 1 shafi na 190, cewa ya yi: sai ya daga hannunsa har aka ga farin hammatarsa, sannan a cikin shafi na 93 kuma cewa ya yi: har farin hammatarsa ya fito.
5- Hakim al-Haskani cikin Shawahid al-Tanzil, juzu'i na 1, shafi na 191, da kuma wurin Ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 209 cewa ya yi: ni kuma ni ne majivincin kowane mumini.
6- Musnad Ahmad juzu'i na 1 shafi na 118 da 119 da juzu'i na 4 shafi na 281 da 370 da 372 da 373 da juzu'i na 5 shafi na 347 da 370, da al-Mustadrak na Hakim, juzu'i na 3, shafi na 109, Sunan Ibn Majah da Hakim al-Haskani, juzu'i na 1 shafi na 190 da 191, da Tarikh ibn Kathir, juzu'i na 5 shafi na 209 da 210-213, inda ibn Kathir cikin juzu'i na 5 shafi na 209 ya ce: nace wa Zaid, shin ka ji hakan daga Manzon Allah (s.a.w.a.)? sai yace: Babu wani wanda yake gurin face ya gan shi ko kuma ya ji da kunnuwansa, sai Ibn Kathir ya ce: Malaminmu Abu Abdullah al-Zahabi ya ce: wannan hadisi ingantacce ne.
7- Musnad Ahmad, juzu'i na 1 shafi na 118 da 119, Majma' al-Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 104 da 105 da 107, da Shawahid al-Tanzil juzu'i na 1 shafi na 193, da Tarikh Ibn Kathir juzu'i na 5 shafi na 210 da 211.
8- Shawahid al-Tanzil juzu'i na 1 shafi na 191, da Tarikh Ibn Kathir juzu'i na 5 shafi na 210.
9- Shawahid al-Tanzil, juzu'i na 1 shafi na 190.
"A yau Na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imaTa a kanku, kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku". (Surar Ma'ida, 5:3)
Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Allahu Akbar! Bisa kammalar addini da cikar ni'ima da yardar Ubangiji da Manzancina da walittakan Aliyu(1) ".
Akwai ayoyi masu yawa, wadanda wannan karamin littafi ba zai iya tattaro su ba, da suke magana a kan matsayin Ahlulbaiti (a.s) da karamar su da girman mutanen ciki, wadanda wasu daga cikinsu sun kebanta ne ga Uban wannan itace mai tsarki, wato Imam Ali (a.s.). mai karatu zai iya samun wadannan ayoyi cikin littattafan tafsiri, hadisi, tarihi da kuma masu bayani kan falalolin wadannan taurari da kuma wadanda suka yi magana kan Asbabun Nuzul na wadannan ayoyi. To amma bari mu kawo kadan daga cikin irin wadannan ayoyi, su ne kuwa:
(1). Fadin Allah Madaukakin Sarki:
(ÅäøóãóÇ ÃäúÊó ãõäúÐöÑñ æáößõáøö Þóæúãò åóÇÏò)
"Abin sani kawai kai mai gargadi ne kuma a cikin kowadanne mutane akwai mai shiryarwa". (Surar Ra'ad, 13:7)
Hadisi ya zo cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sanya hannunsa bisa kirjinsa, ya ce:
"Ni mai gargadi ne, ko wadanne mutane kuma suna da mai shiryarwa", sai ya yi nuni da hannunsa zuwa Ali
____________
1- Hakim al-Haskani ya ruwaito shi daga Abu Sa'id al-Khudri, juzu'i na 1 shafi na 157-158, hadisi 211-212, daga Abu Huraira shafi na 158 hadisi na 212, da kuma cikin Tarikh na Ibn Kathir juzu'i na 5 shafi na 214.
(2). Fadar Allah Madaukakin Sarki:
ÃÝóãóäú ßóÇäó ãõÄãöäðÇ ßóãóäú ßóÇäó ÝóÇÓöÞðÇ áÇ íóÓúÊóæõæäó
"Shin wanda ya zama mumini yana kamar wanda ya zama fasiki? Ba za su yi daidai ba". (Surar Sajada, 36: 18)
Wannan mumini kuwa shi ne Aliyu (a.s.), fasikin kuma shi ne Walid bn Ukba (2).
(3). Fadar Allah Madaukakin Sarki:
ÃÝóãóäú ßóÇäó Úáì ÈóÈøöäóÉò ãöäú ÑóÈøöåö æíóÊúáæåõ ÔóÇåÏñ ãöäúåõ
"Shin wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma shaida na binsa daga gare shi...." (Surar Hudu, 11:17)
Manzon Allah (s.a.w.a.) shi ne yake bisa hujja bayyananna a al'amarinsa, shaidan kuwa shi ne Imam Ali (a.s.)(3) .
(4). Fadar Allah Madaukakin Sarki:
(ÝÅäøó Çááåó åõæó ãóæúáÇåõ æÌöÈúÑíáõ æÕóÇáÍõ ÇáãÄãöäíä)
"....to lalle Allah Shi ne Mataimakinsa da Jibrilu da Salihin muminai...." (Surar Tahrim, 66: 4)
Salihin muminai a nan shi ne Aliyu bn Abi Dalib (a.s.)(4) .
(5). Fadar Allah Madaukakin Sarki:
(æÊóÚöíóåÇ ÃõÐõäñ æÇÚöíóÉñ)
____________
1- Al-Mustadrak, juzu'i na 3, shafi na 129, Kanzul Ummal, juzu'i na 6, shafi na 157, Dabari ma ya ambaci haka cikin tafsirinsa da Fakhrurrazi cikin tafsirinsa na Al-Kabir, da kuma Suyudi cikin Durrul Mansur yayin da yake tafsirin wannan aya.
2- Ibn jarir Tabari ya ambaci hakan, da kuma Suyudi cikin Durrul Mansur , da Zamakhshari cikin Al-Kashshaf yayin da yake tafsirin ayar, da kuma Wahidi cikin Asbabun Nuzul shafi na 200, da kuma Tarikh Bagdad da kuma Riyadhun Nadhrah.
3- Suyudi cikin Durrul Mansur, Fakhrurrazi cikin tafsirinsa yayin tafsririn wannan aya, kamar yadda Al-Muntaki Al-Hindi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 1 shafi na 251.
4- Suyudi cikin Durrul Mansur karkashin tafsirin wannan aya, Kanzul Ummal juzu'i na 1 shafi na 237, Askalani cikin Fathul Bari juzu'i na 13 shafi na 27 da kuma Haithami cikin Majma'a juzu'i na 9 shafi na 194.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karanta wannan aya, sai ya juya ga Ali (a.s.), ya ce: "Na roki Allah da ya sanya shi shi ne kunnenka".
Sai Ali (a.s.) ya ce: "Babu wani abu da na ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na manta shi(1) ".
Al-Wahidi ya nakalto cikin Asbabun Nuzul daga maruwaita daga Buraida, cewa:
"Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Allah Ya umurce ni da in kusato da kai, kada kuma in nisantar da kai, cewa kuma in ilmantar da kai, don ka kiyaye, kuma Allah Ya yi alkawarin Zai sa ka kiyaye din. Sai aya ta sauka: "Kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye".
(6). FadinSa Madaukakin Sarki cewa:
(Åäøó ÇáøóÐíäó ÂãóäæÇ æÚóãöáæÇ ÇáÕøóÇáöÍóÇÊö ÓóíóÌúÚóáõ áãõãõ ÇáÑøóÍúãäõ æõÏøðÇ)
"Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na nagari, to (Allah) Mai rahama Zai sanya soyayya a tsakaninsu". (Surar Maryam, 19: 96)
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa:
"Ya Aliyu ka ce: "Ya Allah Ka sanya mini wani alkawari, kuma Ka sanya mini soyayya cikin zukatan muminai". Sai Allah Ya saukar da wannan ayar dangane da Aliyu (a.s.)(2) .
(7). Fadar Allah Ta'ala cewa:
(Åäøó ÇáøóÐíäó ÂãóäæÇ æÚóãöáæÇ ÇáÕøóÇáöÍóÇÊö ÃõæáÆßó åõãú ÎóíúÑõ ÇáÈóÑöíøóÉ)
"Lalle ne wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafifita alherin halitta" (Surar Bayyina, 98:7)
____________
1- Ibn Jarir Dabari ya ruwaito shi cikin tafsirin ayar, da kuma Zamakhshari cikin Al-Kashshaf yayin tafsirin ayar, Suyudi cikin Durrul Mansur yayin tafsirin ayar, haka nan ma Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 408, da kuma Wahidi cikin Asbabun Nuzul.
2- Zamakhshari cikin tafsirin Al-Kashshaf, Suyudi cikin Durrul Mansur yayin tafsirin ayar, Riyadhun Nadhrah juzu'i na 2, shafi na 207 da kuma Ibn Hajar cikin Al-Sawa'ik al-Muhrika shafi na 102.
(8). Fadar Allah Madaukakin Sarki cewa:
( ÃÌóÚóáúÊõã ÓöÞÇíóÉó ÇáÍÇÌøö æÚöãóÇÑóÉó ÇáãóÓúÌöÏö ÇáÍóÑÇãö ßóãóäú Âãóäó ÈÇááåö æÇáíóæãö ÇáÂÎöÑ)
"Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira kuma ya yi jihadi domin Allah?...." (Surar Tauba, 9: 19)
Lalle wadannan su ne Abbas da Dalha, wanda ya yi imani kuwa shi ne Aliyu (a.s.).
Akwai wasu ayoyi da dama a kan wannan lamari da muke magana a kansa, amma za mu takaita saboda takaitawa.
____________
1- Ibn Jarir Dabari cikin tafsirinsa, Suyudi cikin Durrul Mansur ta vangarori daban-daban, ya kara da cewa, a duk lokacin da Aliyu (a.s.) ya nufo wajen sahabban Manzon Allah (s.a.w.a.) sukan ce: Ga mafifitan alherin halitta (Khairul Bariya) ya iso. Haka ma an ruwaito wanda hadisi cikin Sawa'ikul Muhrika shafi na 96 da kuma cikin Nurul Absar na Shabalanji, shafi na 70 da kuma na 101.
Dukkan wanda ya bibiyi sunnar Manzon Allah (s) da tarihinsa na aikace da kuma alakarsa da mutanen gidansa wadanda nassin Alkur'ani ya kawo, sannan shi (Manzo) kuma ayyanasu (Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu ), zai san cewa mutanen wannan gida suna da wata rawar da za su taka a bangaren nauyin rike sako da kuma wayewar wannan al'umma. Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance mai tsare-tsare domin al'ummar tasa da kuma shirya da ita domin ta karbi wannan ni'ima ta Ahlulbaiti (a.s), da umurnin Allah (S.W.T.).
Hakika wannan yanki mai haske na tsare-tsaren Annabi (s.a.w.a), wadanda ya yi da umurnin Allah, ya soma ne da aurar da Fadima (a.s.) ga Imam Ali (a.s.), da dasa wannan itaciya mai albarka, domin rassanta su mamaye sansanin wannan al'umma, tsawon rayuwarta.
An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) yayin da ya aurar masa da Fadima (a.s.) cewa:
"Lalle Allah Madaukakin Sarki Ya umurce ni da in aurar maka da Fadima bisa sadaki gwargwadon nauyin miskalin azurfa dari hudu, shin ka yarda da hakan". Sai Aliyu (a.s.) ya ce: "Lalle na yarda da hakan, Ya Manzon Allah". Anas bin Malik ya ce: Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Allah Ya hada kanku, Ya arzurta kokarinku, Ya albakace ku, Ya kuma fitar da zuriya mai albarka". Sai Anas ya ce: "Wallahi, hakika kuwa Allah Ya fitar da zuriya mai albarka daga gare su ".
An ruwaito cewa yayin da Annabi (s.a.w.a) ya aurar da Fadima ga Aliyu (a.s.), sai ya shiga wajenta ya kira ta
____________
1- Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30.
"Ya Allah! Ni ina nema mata tsarinKa da zuriyarta daga shaidan jefaffe". Sai kuma ya ce wa Ali (a.s.): "Miko min ruwa", sai Aliyu (a.s.) ya kawo masa, sai ya zuba a kansa da kuma tsakanin kafadunsa (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ina nema masa tsarinKa da zuriyarsa daga shaidan jefaffe".
A wata ruwayar kuma cewa aka yi, sai ya bukaci a kawo masa ruwa, bayan ya yi alwala da shi sai ya zuba a kan Aliyu da Fadima (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ka albarkace su cikin zuriyarsu(1) ".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana neman uzuri ga duk wani daga cikin sahabbai da ya zo neman a ba shi Fadima (a.s.), yana mai cewa:
"Hukumci bai sauko ba tukunna(2) ".
Hakika wannan kula ta Ubangiji da AnnabinSa ta aurar da Fadima (a.s.) ga Aliyu (a.s.) ta sanya aurar da ita bai faru ba face da umurni daga Allah (S.W.T.) domin wannan ya yi nuni ga matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kuma alherin al'umma da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake nufi da alakarsa da su. Wannan matsayi na su kuwa shi ne Alkur'ani mai girma ya fassara, haka nan ma sunnar Annabi (s.a.w.a) mai daraja.
Watakila hasken da muke tsinkaya daga ruwayoyi da hadisai Manzon Allah (s.a.w.a.) da Ahlulbaiti (a.s) (wadanda kuwa masu yawa ne) suna riskar da mu ne irin zurfaffar kula ta Allah da ManzonSa (s.a.w.a) wajen gina wannan gida, da yawaita soyayya da albarka da kula gare shi. Domin mutanen wannan gida su zama ja-gororin al'umma cikin rayuwarsu da kuma hanyoyin tsirarsu daga bala'u da kuma kasancewa tsari da makoma t
____________
1- Al-Ithafu bi hubbil Ashraf na Abdullah bn Muhammad bn Amir al-Shabrawi al-Shafi'i, shafi na 21.
2- Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30.
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana danganta zuriyar Aliyu da Fadima (a.s.) da kansa, yana cewa: "Lalle su zuriyata ne 'ya'ya ne, kamar yadda Alkur'ani ya bayyana hakan da cewa:
(Ýóãóäú ÍÇÌøóßó Ýíåö ãöäú ÈóÚúÏö ãóÇ ÌóÇÁßó ß ãöäó ÇáúÚöáúãö ÝóÞõá ÊóÚÇáóæÇ äóÏúÚõ ÃÈúäóÇÁóäóÇ æÃÈúäóÇÁóßõãú æäöÓóÇÁóäóÇ æäöÓóÇÁóßõãú æÃóäúÝõÓóäóÇ ÃäúÝõÓóßõãú )
"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku". (Surar Ali Imrana, 3: 61)
Abin nufi da 'ya'yansa a wannan aya su ne Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda maganganun malaman tafsiri da ma'abuta tarihi suka sanar da mu.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karfafa wannan ma'anar wa al'ummarsa sau da yawa, bari mu ambaci kadan daga cikinsu. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Allah Ya sanya zuriyar kowane Annabi daga tsatsonsa, (ni kuma) Ya sanya zuriyata cikin tsatson wannan", yana nufin Aliyu (a.s.)(1) .
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana rungumar Hasan da Husaini (a.s.), yana cewa:
"Dukkan 'ya'yan wani uba dangantakarsu ta ubansu ce, ban da 'ya'yan Fadima, ni ne ubansu, da ni ake dangantasu". Imam Ahmad ya fito da wannan hadisin cikin al-Manakib(2) .
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) yana karfafa matsa-yin Ahlulbaiti (a.s) a kowani muhimmin lokaci, domin al'umma ta koma gare su, ta lizimci tafarkinsu, ta kuma yi riko da soyayyarsu. A ruwayoyi da dama, muna samun
____________
1- Zakha'irul Ukba na Dabari, shafi na 67.
2- Dabari ya ruwaito wannan hadisi da dan bambancin lafazi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 24, haka nan cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 220, Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba shafi na 121, da Suyudi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 29, da wannan lafazi" "Dabarani ya fitar da shi daga Umar, cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Dukkan wani mutum, to danganta-karsa tana komawa ne ga mahaifinsa, in ban da 'ya'yan Fadima, don dangantakarsu tana komawa ne gare ni, ni ne mahaifinsu".
Littattafan hadisi da tarihi sun taru bisa kawo hadisin Annabi (s.a.w.a) da ake kira da Hadisin Nauyaya Biyu (Hadith al-Thakalain). Musulmi sun ruwaito wannan hadisi duk da bambance-bambancen mazhabobinsu na siyasa da fikihu. Za mu ambace shi a nan tare da sashin isnadinsa (maruwaitan da suka ruwaito shi), kamar yadda masu ruwaya da malaman hadisi suka nakalto
1- Hadisus Sakalain (Nauyaya Biyu):
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Na kusata da a kira ni in kuma amsa, amma ni mai bari muku abubuwa masu nauyi guda biyu ne, su ne kuwa: Littafin Allah Mai girma da Daukaka, da kuma zuriyata. Littafin Allah wata igiya ce da aka sako ta daga sama zuwa kasa, zuriyata kuwa su ne mutanen gidana (Ahlulbaiti). Allah Mai tausasawa Ya ba ni labari cewa su biyun ba za su taba rabuwa ba har abada har sai sun iske ni a bakin tafki. To ku lura da yadda za ku rike su a bayana(1) ".
Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto cikin littafinsa mai suna al-Ithafu bi hubbil Ashraf, cewa:
"Muslim da Tirmizi sun kyautata shi (hadisin), haka ma Hakim shi ma ya ruwaito shi, lafazin Muslim kuwa daga Zaid bn Arkam cewa ya yi: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya mike a cikinmu domin ya yi mana huduba
____________
1- Tirmizi ya ruwaito shi cikin Sahihinsa juzu'i na 2, shafi na 380 da isnadinsa daga Zaid bn Arkam, haka ma Hakim ya ruwaito shi cikin Al-Mustadrak juzu'i na 3 shafi na 109, shi ma daga Zaid bn Arkam, haka nan ma Ahmad bn Hambal ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa daga Abu Sa'id al-Khudri, juzu'i na 3 shafi na 17, kamar yadda kuma Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir juzu'i na 1 shafi 129 ya ruwaito, haka ma Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba daga Ahmad shafi na 16.
"Bayan haka, Ya ku mutane, ni dai mai mutuwa ne, kuma zan amsa kiran manzon Ubangijina. To amma na bar muku wasu nauyayan abubuwa guda biyu tare da ku; na farkonsu Littafin Allah, shiriya da haske na cikinsa, to ku kama Littafin Allah ku yi riko da shi". Sannan sai ya ce: "Da Ahlulbaitina, ina gama ku da Allah dangane da Ahlulbaitina (1)".
Al-Shibrawi din kuma ya nakalto cewa: "A wata ruwayar kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa ya yi: "Ni mai bari muku al'amurra guda biyu , ba za ku bata ba idan har kun bi su, su ne kuwa; Littafin Allah da Ahlulbaitina". A wata ruwayar kuma (aka cika da cewa) "ba za su rabu ba har sai sun iske ni a bakin tafki, to ku kula da yadda za ku rike su a bayana (2)".
Ya kara da cewa: "Ibn Hajar ya fada cikin Sawa'ikul Muhrika cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya ambaci Alkur'ani da zuriyarsa da cewa "Nauyaya Biyu" ne saboda nauyin dukkan wani mutum shi ne abu mafi muhimmanci a gare shi, kuma wadannan guda biyu haka suke. Domin kuwa kowane daga cikinsu taska ce ta ilmummukan addini da sirrorin hankali irin na shari'a, domin haka ne ma aka kwadaitar da koyi da su. Wani kaulin kuma ya ce an ambace su da "Nauyaya Biyu" ne domin wajibcin kiyaye hakkokinsu. Sannan kuma wanda kwadaitarwar ta tabbata a gare su, su ne masana Littafin Allah masu riko da sunnar ManzonSa (s.a.w.a), domin su ne wadanda ba su rabuwa da Littafin har zuwa tabki(3) ".
Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya nakalto cikin tafsirinsa Ala'u al-Rahman fi tafsiril Kur'an cewa:
"Haka nan ma kamar hadisin Sakalain wanda yake
____________
1- Al-Ithafu bi hubbil Ashraf, shafi na 22.
2- Kamar na sama.
3- Kamar na sama, shafi na 22-23.
"Ni mai bari muku Nauyaya guda biyu ko kuma halifofi guda biyu, Littafin Allah da zuriyata, Ahlulbaitina, wadanda idan kun yi riko da su ba za ku bata ba har abada, su ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".
(1). Imam Ali bn Abi Talib (a.s) | (2). Abdullahi bn Abbas. |
(3). Abu Zar Giffari | (4). Jabir al-Ansari. |
(5). Abdullahi bn Umar | (6). Hudhaifa bn Usaid. |
(7). Zaid bn Arkam. | (8). Abdurrahman bn Awf. |
(9). Dhamratul Aslami. | (10). Amir bn Laili. |
(11). Abu Ra'fi'. | (12). Abu Huraira. |
(13). Abdullah bn Handab | (14). Zaid bn Thabit. |
(15). Ummu Salama. | (16). Ummu Hani. |
(17). Khazima bn Thabit. | (18). Sahl bn Sa'ad. |
(19). Adi bn Hatam. | (20). Ukba bn Amir. |
(21). Abu Ayyub Ansari. | (22). Abu Sai'd al-Khudri. |
(23). Abu Shuraih Khuza'i. | (24). Abu Kadama Ansari. |
(25). Abu Laili. | (26). Abu Haitham bn Al-Tayhan. |
Allama al-Balagi ya ci gaba da cewa: Wadannan su ne muka riga muka ambaci sunayensu bayan Ummu Hani. Kowannensu ya ruwaito shi, shi kadai, kamar wadanda suka gabace shi, sun tsaya a dandalin Kufa tare da mutum bakwai Kuraishawa, suka tabbatar da cewa sun ji wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.),
Kuma abu Nu'aim Al-Isfahani ya ruwaito shi cikin littafin Munkabatu al-Mudahharin da isnadi daga Jabir bn Mad'am da kuma wani isnadin daga Anas bn Malik da Al-Barra'u bn Azib, haka nan Muwaffak bn Ahmad ya ruwaito shi daga Amr bn al-As.
Da wuya a sami wani littafin hadisi babba ko karami ko littafin falaloli da Ahlussunna suka rubuta wanda bai kawo wannan hadisin ba, daga farkon wadanda suka kawo hadisin daga hadda da kuma zukatan mahaddata har zuwa takardun malaman hadisi. Kuma bai gushe ba ana ruwaito shi daga sahabbai guda ko masu yawa. Ta yiwu ma a ruwaito shi daga sama da sahabbai ashirin a littafi guda, ko dai a game kamar yadda ya zo cikin littafin Sawa'ikul Muhrika, ko kuma da isnadi rarrabe kamar yadda ya zo cikin littattafan al-Sakhawi da Suyudi da Samhudi da dai sauransu".
Sannan sai ya ce:
"Malaman Imamiyya sun ruwaito shi cikin litattafan-su da isnadinsu masu maimaita juna daga Imam Bakir, Ridha da Kazim da Sadik (a.s.) daga iyayensu (a.s.) daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma wadansu isnadan na daban daga Amirul Muminina (a.s) da Umar da Ubayyu da Jabir da Abu Sa'id da Zaid bn Arkam da Zaid bn Thabit da Huzaifa bn Usaid da Abu Huraira da sauransu, dukkanninsu sun ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.)(1) .
A cikin Musnad na Ahmad bn Hambal, ya ruwaito ta hanyar Abi Sa'id al-Khudri daga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ni na kusanta da a kira ni in amsa, ni kuma mai barin nauyayan abubuwa ne guda biyu tare da ku, Littafin Allah Mai Girma da Daukaka da kuma Ahlulbaitna, shi Littafin Allah igiya ce da aka sako daga
____________
1- Al-Balagi cikin Ala'ur Rahman shafi na 44.
Allama Faiz Abadi ya nakalto cewa: " Muslim ya ruwaito Hadisus Sakalain cikin sahihinsa, haka ma Ahmad bn Hambal cikin Musnad dinsa, juzu'i na 4 shafi na 366, da Baihaki cikin Sunan dinsa, juzu'i na 2 shafi na 148, juzu'i na 7 shafi na 30, haka ma Darimi ya ruwaito shi Sunan dinsa, juzu'i na 2 shafi na 431, Al-Muttaki cikin Kanzul Ummal, juzu'i na 1 shafi na 45, da juzu'i na 7 shafi na 102, haka ma Dahawi cikin Mishkilul Athar juzu'i na 4 shafi na 368, Tirmizi ma ya ruwaito shi cikin Sahihinsa, juzu'i na 3 shafi na 109, haka Nisa'I cikin Khasa'is shafi na 21. Haka nan ma cikin al-Mustadrak na Hakim, juzu'i na 3 shafi na 148.
Haka nan kuma idan muka duba za mu ga kusan dukkan maruwaita sun ruwaito wannan hadisi da ke gwama Ahlulbaiti (a.s) da Littafin Allah Mai Tsarki. Daga wannan ne musulmi za su fahimci cewa Ahlulbaiti (a.s) su ne makoma baicin Littafin Allah kuma su ne aka bar wa amanar Littafin har su isa ga tabki.
2- Hadisus Safina (Hadisin Jirgin Ruwa):
Yayin da Hadisus Sakalain yake gwama Ahlulbaiti (a.s) da Alkur'ani waje guda domin nauyin da aka dora musu na bayyana Alkur'anin da kwaranye boyayyun abubuwansa da asirorinsa da abubuwan da ke kewaye da shi, to wannan hadisi na Safina kuwa yana bayyana wa al'umma ne cewa su Ahlulbaiti (a.s) su ne jirgin tsira, kuma hanyar kubutar wannan al'umma bayan Manzon Allah (s.a.w.a.). Domin haka, lallai rashin riskan wannan jirgin da rashin hawansa, zai ja wadanda suka ki shiga jirgin zuwa ga nutsewa da halaka. Domin kin binsu, kin bin ja-gora zuwa gabar shiriya da tsira ne.
Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto daga Rafi Maulan Abu Zarri, ya ce:
"(Wata rana) Abu Zar (r.a.) ya hau dokin kofar Ka'aba, ya kama marikin kofar ya dogara da shi, sai ya ce: "Ya ku mutane, wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuma bai sanni ba, to ni ne Abu Zar, na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ahlulbaitina tamkar jirgin Nuhu suke, wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya ki hawa ya fada wuta".
____________
1- Musnad Ahmad bn Hambal, juzu'i na 3 shafi na 17.
"Ku sanya Alayena (a gareku) matsayin da kai yake da shi a jiki, kuma matsayin idanu ga kai. Domin shi jiki baya shiryuwa sai da kai, shi kuma kai ba ya shiryuwa sai da idanu(1) ".
Abu Nu'aim(2) ya ruwaito ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin (Annabi) Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawa ya nutse (ya halaka)(3) ".
An ruwaito ta hanyar Anas bn Malik, cewa, ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Abin sani kawai shi ne cewa, misalin Ahlulbaitina a cikinku, kamar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka (4)".
Suyudi ma ya ruwaito wannan hadisin cikin littafinsa Durrul Mansur karkashin tafsirin fadin Allah Madauka-kin Sarki cewa:
(æÅÐ ÞõáäóÇ ÂÏÎõáæÇ åóÐöå ÇáÞóÑúíÉó ÝóßõáõæÇ ãöäúåóÇ ÍóíúËõ ÔöÆúÊõãú ÑóÛóÏÇð æÇÏúÎõáõæÇ ÇáÈÇÈó ÓõÌøóÏÇð æÞõæáæõÇ ÍöØøóÉ äóÛúÝöÑ áßõãú ÎóØÇíÇßõãú)
"Kuma lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alkarya, sa'an nan ku ci daga gare ta, inda kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga kofa kuna masu tawali'u, kuma ku ce: "Kayar da zunubai" Mu gafarta muku laifukanku".
Inda ya ce: "Ibn Abi Shaiba ya fitar da hadisi daga Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya ce:
"Abin sani dai, misalinmu (Ahlulbaiti) cikin wannan al'umma kamar misalin jirgin Nuhu ne, kuma kamar Kofar Yafuwa (Hidda) ce(5) ".
Al-Muttaki ya ruwaito shi cikin littafin Kanzul Ummal (juzu'i na 6 shafi na 216) cewa, Manzon Allah
____________
1- Shabrawi al-Shafi'I cikin littafinsa na al-Ittihaf bi hubbil Ashraf, mukaddimar mawallafi, shafi na 26.
2- Abu Nu'aim cikin littafin Hilliyat al-Awliya juzu'i na 4 shafi na 306, ya nakalto daga Firuz Abadi cikin littafin Fadha'il al-Khamsa min al-Sihah al-Sitta juzu'i na 2 shafi na 64, Ibn Hajar ma ya ambato shi cikin Zawa'id babin Ahlulbaiti wal Azwaj shafi na 277, haka ma Haithami ya nakalto shi daga Ibn al-Bazzar cikin Majma' al-Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163, kamar yadda kuma Dabarani ya kawo cikin Mu'ujamul Kabir juzu'i na 1 shafi na 125, haka ma Dabari cin Zaka'ir shafi na 20, haka ma Hakim cikin al-Mustadrak tare da karin lafuzza, juzu'i na 2 shafi na 343, haka ma cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 216.
3- Hakim cikin al-Mustadrak ya ruwaito wannan hadisi a juzu'i na 2 shafi na 343, inda ya ce: wannan hadisi ne ingantacce a bisa sharadin Muslim, haka ma Al-Muttaki ya ruwaito shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 216, da kuma Haithami cikin Majma'ansa, juzu'i na 9 shafi na 168, haka ma Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir dinsa shafi na 20, haka ma Khadib al-Bagdadi cikin Tarihinsa, juzu'i na 12 shafi na 19.
4- Fadha'il al-Khasa na Firuz Abadi, juzu'i na 2 shafi na 65.
5- Kamar na sama.
"Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka, kuma tamkar kofar Hidda ne ta Bani Isra'ila". Sannan ya ce Dabarani ma ya ruwaito wannan hadisi daga Abu Zarri(1) .
3- Hadisin Aminta Daga Sassabawa:
A cikin wannan hadisin, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) ke takawa a fagen akida da siyasa. Domin mafi hadarin abin da yake samun al'umma shi ne rarraba da sabawa cikin ra'ayi da akida da kuma fuskantarwa ta siyasa. Don haka ne ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana tsoratar da al'ummarsa wannan fitinar, ya kasance yana tsare-tsare saboda hadin kanta da riko da juna ta bangaren tunani da siyasa. Kana kuma yake fuskantar da al'ummar tasa zuwa ga lizimta da riko da Ahlulbaitinsa da komawa gare su. A saboda hakan ne kuma, ya siffanta su da cewa su masu lizimtar Alkur'ani da kiransa ne, kuma ba za su rabu da juna ba har ranar tashin kiyama. Ya kuma siffanta su da cewa su jirgin tsira ne, kuma kofar yafuwar zunubbai. To a nan kuma yana siffanta su ne da cewa su ne mattara, kuma su ne madogara mai hada kan wannan al'umma ta musulmi ne, da kuma cewa riko da su da rayuwa bisa tafarkinsu lamuni ne daga rarraba da sabawa.
Al-Dabarani ya kawo hadisi daga Ibn Abbas (r.a.) cew, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Taurari aminci ne ga mazauna kasa daga nutsewa (halaka), Ahlulbaitina kuwa aminci ne ga mazauna kasa daga sassabawa (rarrabuwa)(2) ".
____________
1- Kamar na sama.
2- Al-Ittihaf bi Hubbil Ashraf na Al-Shabrawi shafi na 20, Hakim ma ya fitar da shi cikin al-Mustadrak, juzu'i na 3 shafi na 149, inda ya ce wannan hadisi ne ingantacce sai dai kuma bai (Muslim) ruwaito shi ba, kamar kuma al-Muttaki ya fitar da shi cikin littafinsa Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 217, haka ma Ibn Hajar ya kawo shi cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika shafi na 140.
"Taurari aminci ne ga mazowa sama, idan taurari suka tafi, mazowa sama sai su tafi, Ahlulbaitina kuwa aminci ne ga mazowa kasa, idan Ahlulbaitina sun tafi, mazowa kasa sai su tafi".
Sai al-Dabarani ya ce: "Ahmad bn Hambal ya ruwaito wannan hadisi cikin al-Manakib(1) .
4- Hadisul Kisa'i (Hadisin Mayafi)(*):
Hadisin Mayafi shi ne hadisin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) yayin da Ayar Tsarkakewa ta sauka. Mun riga da dai mun gabatar da wannan hadisi kuma mun yi magana a kan shi tare da kawo ra'ayuyyukan wasu malaman tafsiri, da kuma ruwayoyin da suka yi batun wadannan wadanda aka tsarkake a cikin babin "Ahlulbaiti (a.s) Cikin Alkur'ani". To amma a nan za mu kawo wasu ruwayoyi ne daban domin karfafa wannan fikirar da kuma kafa wannan manufar da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake da ita wajen yin hakan (wato lullube su da mayafinsa da kuma yi musu addu'a).
Hanyoyin da wannan hadisi ya zo suna da yawan gaske cikin littattafan hadisi da ruwaya da tafsiri, to amma za mu ambaci wasu daga cikinsu ne kawai:
"Dangane da abin da aka ruwaito daga Ummu Salama, matar Annabi (s.a.w.a), Imam Ahmad ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa har ya zuwa ga Ummu Salama, inda ta ce: "Wata rana Manzon Allah (s.a.w.a.)
____________
1- Fadha'il Khamsa, juzu'i na 2 shafi na 68.
(*). An kira wannan hadisi da sunan Hadisin Mayafi ne saboda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tara Ahlulbaitinsa guda hudu (Aliyu, Fatima, Hasan da Husaini) ya rufe su da mayafi.
"Ya Allah! Zuwa gare Ka ba zuwa wuta ba, ni da Ahlulbaitina". Sai Ummu Salama ta ce: 'Da ni ya Manzon Allah', sai ya ce: "Na'am da ke(*)".
Al-Wahidi ya ruwaito cikin littafinsa Asbabun Nuzul marfu'i ta hanyar Ummu Salama (r.a.) ta ce: (Wata rana Annabi (s.a.w.a) ya kasance a dakinta sai Fadima (a.s.) ta zo da tukunya da wani abinci na alkama a ciki, sai ta shiga da shi. Sai yace da ita: "Ki kira mini mijinki da 'ya'yanki biyu". Sai Ali da Hasan da Husaini suka zo, suka shiga suka zauna suna cin abincin, Annabi (s.a.w.a) kuma yana zaune a kan wani benci, a kan wani mayafi wanda aka saka a Khaibara. Sai Ummu Salama ta ce: Ni kuma ina cikin dakin, kusa da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya kama mayafin ya lullube su da shi, sannan ya ce:
"Ya Allah! Mutanen gidana, kebantattuna (kenan), to Ka tafiyar da kazanta daga gare su Ka tsarkake su, tsarkakewa".
Sai ta ce: Sai na shigar da kaina, na ce: "Ni ma ina tare da ku, Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "Ke kina tare da alheri, ke kina tare da alheri". Sai Allah Mai girma da Daukaka Ya saukar da ayar:
____________
1- (*). Ma'ana E kema ba kya zuwa wuta.
"....Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa (1)". (Surar Ahzabi, 33:33)
Mun riga da mun yi magana kan Hadisin Soyayya wajen tafsirin Ayar Soyayya, kuma mun ambaci wasu masu ruwaya da suka ruwaito shi da kuma daga wajen wadanda suka ruwaito shi. A nan za mu sake ambaton hadisin ta hanyoyin daban ne, kuma zai kasance mai amfani mu ambaci sashin abin da ya taho daga Annabi (s.a.w.a) a kan son Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu a wasu ruwayoyin na daban.
(Imam Ahmad da Dabarani duk sun ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da Ayar Soyayya, wato "Ka ce: "Bana tambayarku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka, sai mutane suka ce: Ya Manzon Allah, su wane ne makusanta wadanda soyay-yarsu ta wajaba a kanmu?, sai yace:
"Aliyu da Fadima da 'ya'yansu guda biyu".
Al-Bazzaz da Dabarani sun ruwaito cewa Hasan dan Aliyu (a.s.) yayi huduba wata rana yana cewa:
"Wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuwa bai sanni ba, to ni ne Hasan dan Muhammadu (s.a.w.a). Ni ne dan Mai albishir, ni ne dan Mai gargadi, ni ne dan mutanen gida wadanda Allah Ya farlanta son su a kan kowane musulmi, Ya kuma saukar a kansu (da ayar), "Ka ce: Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau,
____________
1- Al-Fusulul Muhimma fi Ahawalul A'imma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 25-26.
Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa:
"....wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".
Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa:
"...wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".
Inda ya ce: "Soyayyar ta Alayen Muhammadu (s.a.w.a) ce (2)".
Hadisan da suka zo game da so da kaunar Ahlulbaiti (a.s) da kuma yin musu da'a da lizimtarsu, ba za su kirgu ba cikin wannan dan karamin littafi, sai dai mun zabi sashi ne daga cikinsu kawai, don kuwa kowanne daya daga cikinsu (Ahlulbaiti) (a.s.) rana ce mai haske a cikin littattafan hadisi da ruwayoyi.
To amma domin a kara arzurta mai karatu da kara karfafa abin da zai kara masa sanin Ahlulbaiti (a.s) da kuma karfafa dangantaka da su, da mai da shi mai ta'allaka da su, mai rayuwa bisa tafarkinsu, don ya samu nasarar samun cetonsu, bari mu sake ambaton wasu daga cikin hadisan da suka zo game da su:
(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin al-Awsad daga ibn Hajar (r.a.) cewa; "Karshen abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya furta shi ne: "Ku wakilce ni cikin Ahlulbaitina(3) ").
(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin Al-Awsad daga Jabir bn Abdullah (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba, na ji yana cewa:
"Ya ku mutane! (Duk) wanda ya fusata mu, mu Ahlulbaiti, Allah Zai tashe shi ranar kiyama yana bayahude(4) ".
(Muslim da Tirmizi da Nasa'i duka sun ruwaito daga Zaid bn Arkam cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
____________
1- Al-Ithafu bi hubbil Ashraf na Shaikh Shabrawi, shafi na 17-18.
2- Al-Fusulul Muhimma fi Ahawalul A'imma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 29.
3- Suyudi ya ruwaito shi cikin littafin Ihya'ul Mayyiti daga Dabarani daga Umar, shafi na 20, kamar yadda Haithami kuma ya fitar da shi cikin littafin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163, kamar yadda kuma Ibn Hajar ya kawo shi cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika shafi na 90.
4- Suyudi ya ruwaito shi cikin littafin Ihya'ul Mayyiti daga Dabarani daga Jabir bn Abdullah, shafi na 22, kamar yadda Haithami kuma ya fitar da shi cikin littafin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 172.
Alkhatib ya fitar a cikin littafin Tarihinsa daga Aliyu (r.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Cetona ga al'ummata, na ga wanda ya so Ahlulbaitina (2)".
Kamar dai yadda muka bayyana, hadisai da ruwayoyi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) game da Ahlulbaitinsa (a.s.) suna da yawan gaske, kuma ba za su kidayu ba a wannan karamin littafin. Malamai da masu hadisi sun kebance musu litattafai, ko kuma fasulla a littattafan hadisai, ko kuma sun ambata a wuraren da suka dace cikin litattafan tafsiri da ruwaya. Ga kadan daga ciki:
"Mu Ahlulbaiti ba a gwada mu da kowa (3)".
A cikin wannan hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana mukamin Ahlulbaiti (a.s) ne, da kuma matsa-yinsu madayanci, domin ya sanar da al'umma mahal-linsu, ya kuma shiryar da ita zuwa ga riko da su da lizimtar hanyar su a bayansa, domin a auna su da wasu wadanda ba su ba, don a gani.
A cikin wani hadisi na daban kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana magana ne kan Ahlulbaitisa (a.s.), inda yake cewa:
"Mu Ahlulbaiti, Allah Ya zaba mana lahira bisa ga duniya, kuma lalle Ahlulbaitina za a nuna musu son kai da tsanani da kora cikin garuruwa, har wasu mutane za su zo ta nan - sai ya yi nuni da hannunsa ta gabas - ma'abutan bakar tuta, za su tambayi hakki, ba za a ba su ba, za su yi yaki kuma su yi nasara. Za a ba su abin da suka so kuma ba za su karbe shi ba har su mika ta (tutar) ga wani mutum daga Ahlulbaitina, har sai ya cika duniya
____________
1- Muslim ya ruwaito shi cikin littafin Fadha'il al-Sahaba (Falalar Sahabbai) cikin babin falalar Aliyu bn Abi Talib daga Yazid bn Hayyan, juzu'i na 4 shafi na1873, haka ma Ahmad bn Hambal ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa ya yi kuma daidai da abin da Muslim ya ruwaito, juzu'i na 4 shafi na 366-367, kamar yadda kuma Muttaki ya ruwaito cikin Kanzul Ummal juzu'i na farko shafi na 158, da kuma cikin juzu'i na bakwai shafi na 102, haka ma Suyudi ya ruwaito shi cikin tafsirinsa Durrul Mansur juzu'i na 6 shafi na 7, ya ce daga gare shi: Muslim, Tirmizi da Nasa'i sun ruwaito shi daga Zaid bn Arkam, haka ma Suyudi ya ruwaito shi cikin littafinsa Ihya'ul Mayyit shafi na 11.
2- Khadib ya ruwaito shi cikin tarihinsa, juzu'i na 2 shafi na 146 da kari cikin matanin, kamar yadda kuma Al-Muttaki ya kawo hadisin cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 217 karkashin lamba ta 3800, sannan Suyudi ma ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti bi Fadha'il Ahlulbaiti, shafi na 37.
3- Tabari cikin Zakha'irul Ukba shafi na 17.
(Dailami ya kawo hadisi daga Abu Sa'id (r.a.) cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Fushin Allah ya tsananta kan wanda ya cutar da ni dangane da Ahlulbaitina(2) ".
(Daga Aliyu (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ku yi wa 'ya'yanku tarbiyya kan halaye guda uku: son Annabinku da son Ahlulbaitinsa da kuma karatun Alkur'ani, domin mahaddatan Alkur'ani na cikin inuwar Allah a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa, tare da AnnabawanSa da ZababbunSa(3) ").
(Dabarani ya ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Digadigan bawa ba za su gushe ba har sai an tambaye shi abubuwa hudu: Kan rayuwarsa, yadda ya karar da ita; da jikinsa, yadda ya tsufar da shi, da dukiyarsa, yadda ya kashe ta da inda ya same ta da kuma soyayyarmu, Ahlulbaiti(4) ").
A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana shiryar da al'ummarsa zuwa ga Ahlulbaitinsa, yana kuma bayyana matsayinsu na ilmi, da kuma fuskantar da al'ummar zuwa gare su yayin da fitinu suka tsananta, ra'ayoyi kuma suka sassaba. Yana gwama su da Littafin Allah, domin su ne malamai masu bayyana abin da Alkur'ani ya kunsa, masana hakikaninsa da abubuwan da ya tattara.
(Dabarani ya fitar da hadisi daga Al-Mudallabi bn Abdullahi bn Handabi daga babansa, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba a Juhfa, ya ce:
____________
1- Kamar na sama.
2- Suyudi ya fitar da shi cikin Ihya'ul Mayyit daga Dailami daga Abi Sa'id, shafi na 43, haka ma Al-Manawi ya ambace shi cikin Faizul Kabir juzu'i na 1 shafi na 515, ya ce: Dailami ya fitar da shi cikin Firdausi.
3- Suyudi ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 40-41, yana cewa: "Dailmai ya fitar da shi daga Aliyu, kamar yadda kuma Al-Muttaki ya ambato shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 8, shafi na 278, kamar yadda kuma Ibn Hajar ya ambato shi cikin Sawa'ikul Muhrika, shafi na 103.
4- Suyudi ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 39, daga Dabarani daga Ibn Abbas, haka ma Al-Muttaki ya ambato shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 8, shafi na 212, yana cewa: "Dabarani ya nakalto shi daga Ibn Abbas, sannan kuma Haithami ma ya ambace shi cikin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 10 shafi na 346, ya ce: "Dabarani ya ruwaito shi cikin Al-Kabir da Al-Awsad.
"Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika masu kiyayewa ne gare shi". (Surar Hijr, 15: 9)
Alkur'ani littafin Allah ne da wahayinSa abin saukarwa a kan AnnabinSa mai daraja, Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w.a). Littafin da Allah Ya kiyaye shi daga jirkita da gurbata. Wannan wahayin Allah tsarkakakke, wanda hannun mai jirkitawa bai taba shi ba, duk wata barna bata samunsa, ko ta baya ko ta gaba. Shi a yau yana nan kamar yadda ya sauko wa Manzo Amintacce (s.a.w.a), ba tare da wata tawaya ko kari ba. Shi ne mabubbugar shari'a, daga gare shi ake fitar da hukumce-hukumce, shi ne ma'auni sunna, magwajin fahimta da tunani, shi ne mabubbugar wayewar ilmomin Musulunci kana kuma tushen alherin dan'Adam da tsirarsa.
Hakika musulmi sun zazzaga da Alkur'ani tsakanin-su, daga tsara zuwa wata tsarar, suna nakaltar sa da kiyayewa da kula da shi kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya saukar da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.). Wannan kuwa shi ne abin da musulmi suka dace a kai, kamar yadda suka hadu a kan karyata ruwayoyi raunana na karya wadanda suka sabawa wannan ijma'i na malamai kan rashin gurbatan Alkur'ani ta kowane bangare.
Babban malamin tafsirin nan wanda ya rubuta shahararren littafin tafsirin nan na Majma'ul Bayan fi
"Akwai irin wadannan maganganu (marasa tushe) kan kari ko ragi cikin Alkur'ani, da ba sa ma bukatan magana a kansu. To amma dangane da kari, an hadu kan cewa rashin ingancin hakan, amma batun ragi, wasu jama'a daga cikin abokanmu da wasu mutane daga cikin 'yan Sunna sun ruwaito cewa akwai canji ko tawaya a cikin Alkur'ani. To amma ingantacciyar magana a gurinmu ita ce sabanin hakan (wato babu wata tawaya ko ragi a cikin Alkur'ani), hakan kuwa shi ne abin da Murtadha(**) (Allah Ya tsarkake ruhinsa) ya bayyana ya kuma yi bayani a kai. A wurare da dama ya ambata cewa ilimin da ake da shi kan ingancin nakalto Alkur'ani kamar ilmin da ake da shi kan garuruwa, manyan abubuwan da suka faru, shahararrun littattafa da rubutattun wakokin larabawa, lallai an sami kula mai tsanani, bukata kuwa ta tabbata kan nakaltar Alkur'ani da kiyaye shi. Bukatar da kular sun kai matsayin da nakalto shahararrun littattafa da wakokin da muka ambata ba su samu ba, domin Alkur'ani mu'ujizar annabta ne, a nan ake daukar ilmomin shari'a da hukumce-hukumcen addini. Malaman Musulunci sun kai matuka wajen kiyaye shi da kare shi har sukan san duk abin da a ka
____________
(*)- Shaikh Tabrisi yana daga cikin shahararru kana manyan malaman mazhabar Shi'a Imamiyya a qarni na shida hijiriyya.
(**)- Sayyid Murtadha: shi ne Aliyu bn Husain, yana daga cikin manya-manyan malaman Shi'a Imamiyya na qarni na hudu hijiriyya, kuma yana daga cikin daliban Shaikh al-Mufid kuma malamin Shaikh al-Tusi, Mu'assasin Jami'ar birnin Najaf al-Ashraf, ya rasu a shekara ta 437 Hijiriyya.
Ya kuma kara da cewa: "Lalle ilmi a kan tafsirin Alkur'ani da sassaninsa da kuma ingancin nakalto shi kamar ilmi ne a kan jumlarsa, kuma hakan yana bisa tafarkin abubuwan da aka sani ne bisa larura cikin littat-tafai wallafaffu, kamar littafin Sibawaihi da Al-Mazanni. Masu kula da wannan sha'ani (nahawu) sun san littattafan nan a fasalce tamkar sanin da suka yi musu a jumlace, ta yadda da wani zai shigar da wani babi na nahawu cikin littafin Sibawaihi, wanda da baya ciki, to da sun gane da kuma fahimtar cewa an sanya shi ne cikin littafin daga baya, ba daga cikin asalin littafin yake ba, haka nan ma yake game da littafin Al-Mazanni. Kuma sananne abu ne cewa kula da nakalin Alkur'ani da tsare shi, yafi gaskata bisa kula da tsare littafin Sibawaihi da kuma Diwanin mawaka".
Ya kuma sake cewa: "Shi Alkur'ani ya kasance a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) a tare yake a wallafe kamar yadda yake a yau. Ya kafa hujja da cewa Alkur'ani ya kasance ana darasinsa ana kuma haddace shi a wancan zamani har aka ayyana wata jama'a cikin sahabbai da cewa sun haddace shi, da kuma cewa ana bijiro da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) ana karanta masa, sannan kuma wata jama'a daga cikin sahabbai kamar su Abdullahi bn Mas'ud da Ubayyu bn Ka'ab da sauransu, sun sauke Alkur'ani gaba ga Annabi (s.a.w.a) sau da yawa. Duk wannan yana nunawa cewa shi Alkur'ani ya kasance tararre ne jerarre, ba yankakke ba, ba kuma a watse yake ba. Ana riskar wannan hakika kuwa ba tare da bukatar wani dogon tunani ba. Sayyid
Sannan kuma sai ya ce:
"Abin da ya shahara a wajen malaman Shi'a da masu bincikensu, kai ba ma kawai shahara ba har ma babu jayayya a cikinsa, shi ne rashin ragi ko kari cikin Alkur'ani(2) ".
Shaihin malaman hadisi Muhammad bn Ali bn Husain bn Babawaihi al-Kummi, wanda ake wa lakabi da "Saduk" (ya rasu a shekara ta 381), kuma mawallafin littafin Man La Yahdhuruhul Fakih da kuma dimbin muhimmman littattafai, ya fada cikin littafinsa mai suna I'itikadatul Saduk cewa:
"Akidarmu game da Alkur'ani mai girma wanda Allah Ya saukar wa AnnabinSa Muhammadu (s.a.w.a) shi ne abin da yake cikin bangwayen nan biyu, shi ne wanda yake hannun mutane bai wuce wannan ba - har ya zuwa inda yake cewa - kuma duk wanda ya danganta gare mu cewa muna fadin wai Alkur'ani ya fi haka to shi makaryaci ne". Sannan ya shiga kawo hujjoji kan hakan, mai son karin bayani yana iya duba cikamakin maganan tasa(3) .
Shugaban jama'ar Shi'a, Abu Ja'afar Muhammad bn Husain al-Dusi (wanda ya rasu a shekara ta 460 hijiriyya), mawallafin littafin Al-Khilaf da Al-Mabsud da Al-Tahzib da Al-Istibsar da sauransu, ya fada cikin littafinsa na tafsiri mai suna Al-Tibyan cewa(4) :
____________
1- Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an na Shaikh Dabarasi a mukaddimar tafsirin.
2- Kama na sama.
3- Ma'al Khatib fi Khututihi al-Aridha na Shaikh Lutufullah Safi, shafi na 42.
4- Tafsirul Tibyan Shaikh Dusi juzu'i na 1shafi na3.
"Ni mai barin Nauyayan Abubuwa guda Biyu ne tare da ku, wadanda idan kuka yi riko da su ba za ku bata a baya na ba: (su ne) Littafin Allah da Zuriyata, Ahlulbaiti, don ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".
Wannan yana nuni da cewa shi Alkur'ani samamme ne a dukkan zamani, domin ba zai yiwu ya yi umurni da riko da abin da ba za mu iya riko da shi ba, kamar yadda Ahlulbaiti (a.s) da wanda bin fadarsa yake wajibi samammu ne a duk lokaci. To idan wanda yake tare da mu an hadu a kan ingancinsa to ya kamata mu shagaltu da tafsirinsa da bayyana ma'anoninsa, mu bar komawa bayan wannan).
Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya tabbatar da wannan hakika cikin tafsirinsa Ala'ur Rahaman fi Tafsiril Kur'an, wato dawwamar Alkur'ani da kubutarsa daga jirkita da gurbata, inda yace:
"Haka Alkur'ani ya ci gaba a kan wannan gagarumin tafarki daga wannan al'umma zuwa wancan, kana iya ganin duban dubata na littattafa da mahaddatansa, kuma
"Lalle Mu ne Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika, Masu kiyayewa ne a gare shi".
Da kuma fadinSa Ta'ala cikin Surar Kiyamati:
"Lalle ne wajibi ne a gare Mu, Mu tara shi, Mu (tsare maka) karatunsa".
To idan ka ji wani abu kan jirkitar Alkur'ani da bacewar sashensa, daga bakaken ruwayoyi, kada ka ko kula su sannan ka fadi duk abin da ilmi yake yarda da fadinsa na daga sassabawar su da rauninsu da raunin masu ruwaitosu da sabawarsu wa musulmi, da kuma raunin da abin ruwaitowarsu - rusashshe - ya zo da shi(1) ".
Shehin malamin ya ci gaba da cewa cikin tafsirinsa karkashin fasalin: "Maganar Imamiyya Kan Cewa Babu Tawaya Cikin Alkur'ani", inda yace: "Ba a boye yake ba cewa Shaihin masu hadisi wanda aka san shi da kula da abin da yake ruwaitowa, wato Shaikh Saduk (Allah Ya kyautata makwancinsa) ya fada cikin littafinsa al-I'itikad cewa: "Akidarmu ita ce cewa Alkur'anin nan da Allah Ya saukar wa AnnabinSa (s.a.w.a) shi ne dai wanda yake cikin bangwayen nan biyu (wanda kowa ya sani) bai kuma wuce haka ba, wanda kuwa ya danganta mana cewa mun ce ya fi haka, to shi makaryaci ne".
Shaikh al-Mufid a littafinsa na al-Makalat ya kawo cewa wasu jama'a daga cikin Imamiyya sun ce shi
____________
1- Ala'ur Rahaman na Shaikh Al-Balagi, juzu'i na 1 shafi na 18
A cikin littafin Kashful Gida'i fi Kitabil Kur'an, a fasali na takwas, kan tawayar Alkur'ani an ce: Babu shakka cewa an kiyaye shi daga tawaya da kiyayewar Sarki Mai sakamako, kamar yadda Alkur'ani ya yi nuni da hakan a sarari, kuma malamai suka hadu a kai.
Shaikh Baha'i yana cewa: "Kuma haka nan an yi sabani kan aukuwar kari da tawaya cikinsa, abin da ya inganta shi ne shi Alkur'ani mai girma kiyayayye ne daga hakan, kari yake ko ragi, kuma lalle fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "Kuma lalle Mu, hakika Masu kiyayewa ne gare shi" yana nuni da kuma tabbatar da hakan.
Al-Mukaddas al-Bagdadi cikin Sharhin al-Wafiya yana cewa:
"Hakika sanannen zancen Imamiyya kan ragi a cikin Alkur'ani shi ne rashin hakan a cikinsa", har ila yau ya ce an samu daga Shaikh Ali bn Abdul Ali cewa shi ya wallafa littafi na musamman kan kore tawaya cikin Alkur'ani daga hadisai, inda ya ce idan hadisi ya zo bisa sabanin dalili na Littafin Allah da Sunna ingantacciyar ko kuma ijma' (abin da malamai suka hadu a kai amma da sharadin akwai wani Imami a cikinsu), kuma ba zai yiyu a yi masa wani tawili ba ko kuma daukansa da wasu ma'anoni ta wasu fuskoki ba, to wajibi ne a jefar da shi(1) ".
Marigayi Allama kana Mujahidin zamani Shaikh Muhammad Husain Kashif al-Ghida ya fada cikin littafinsa mai suna Aslul Shi'a wa Usuluha cewa:
"Lalle wannan Littafin da yake hannu musulmi shi ne
____________
1- Kamar na sama, Mukaddima.
Sharifi mai kira zuwa ga gyara, Sayyid Abdul Husain Sharafuddin ya fada cikin littafinsa Fusulul Muhimma fi Talifil Umma cewa:
"Alkur'ani mai hikima, barna bata zuwa masa a zamaninsa ko a bayansa. Abin sani dai shi ne a cikin bangwaye biyun nan, shi ne kuma a hannun mutane, ba a kara ko da harafi ko kuma a rage wani ba, babu musayyar kalma da wata, ko harafi da wanin harafin. Kuma ko wani harafi cikin haruffan Alkur'ani tabbatacce ne a kowani zamani tun daga zamanin da aka saukar da shi. Sannan ya kasance a tare a wancan zamani mafi tsarkaka, yana rubuce kamar yadda yake a yau. Mala'ika Jibrilu (a.s.) ya kasance yana kawo shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) sau da yawa, dukkan wannan yana cikin al'amurra sanannu wajen masu bin diddigi cikin malaman Imamiyya. Don haka ba a dogara da maganan 'yan Hashawiyya, domin su ba su da fahimta".
Haka nan kuma malamin nan mai yawan bincike, babban mutum, Sayyid Muhsin Amin Husaini Amili ya fadi cikin littafinsa A'ayanu al-Shi'a cewa:
"Babu wani daga cikin 'yan Imamiyya, dadadde ko na yanzu da yake cewa akwai kari, babba ne ko karami, cikin Alkur'ani, face ma dai dukkansu sun hadu a kan rashin kari, hakika wadanda ake dogaro da maganarsu daga cikin masu bin diddigi sun hadu a kan cewa babu abin da ya ragu daga cikin Alkur'ani".
To wannan dai shi ne Alkur'ani mai girma da kuma ra'ayin Imamiyya dangane da shi, shi ne kuma dai a yanzu yake hannu musulmi, kamar yadda Manzon Allah
Malamai da masu bincike da masu bin diddigi, suna ganin cewar abin da ke yawo tsakanin wasu mutane na ruwayoyi da zantattuka (marasa tushe) da suke maganar tawayar Alkur'ani, cikin da'irar Ahlussunna da Shi'a, ba kome ba ne face sanyawa ce ta makaryata, wacce babu makawa dole a yi jifa da su.
Haka nan ana samun wasu ruwayoyi wadanda ana yiwa zahirinsu wata fahimta ba tare da zurfafa nazari wajen karanta su da fahimtar su ba, wacce kuma ta sa ake cewa da akwai tawaya cikin Alkur'ani ko kuma samuwar wani Mus'hafi daban kamar yadda al'amarin ya rikitar da wasu mutane, masu muzanta Musulunci kuma suka dauki hakan wata dama ce gare su ta musguwa wa Musuluncin da kuma musulmai da kuma kokarin kawo rarrabuwa tsakaninsu. Kamar abin da aka ruwaito daga Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.), ba tare da kula da ingancin ruwayar ko rashin sa ba. Ga abin da ya ce:
"....amma wallahi - sai ya mika hannunsa zuwa kirjinsa - akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da mu, takobinsa da sulkensa, kuma wallahi, muna da Mus'hafin Fadima tare da mu, babu wata ayar Littafin Allah a cikinsa, shi dai shifta ce daga shiftar Manzon Allah (s.a.w.a.) Aliyu kuwa shi ne ya rubuta shi da hannunsa(1) ".
Hakika wasu sun shiga wahami kan cewa Imam Sadik (a.s.) - wal iyazu billahi - yana ba da labarin samuwar wani Alkur'ani ne ban da wannan Alkur'anin da ke hannunmu, sai wadansu suka dauki wannan waha-mi a matsayin wata hujjar shuka barna tsakanin mutane.
____________
1- Biharul Anwar na Allama Majlisi juzu'i na 47, shafi na 271.
Idan muka koma ga kalma Mus'haf cikin harshen larabci zai sa mu fahimci ma'anar wannan magana ta Imam (a.s.).
Ragib al-Isfahani yana cewa:
"Sahifa ita ce duk wani abu shimfidadde, kamar shimfidar kunci, ganye ko wani shafi da ake rubutu a kansa, jam'inta kuwa shi ne Saha'if ko kuma Suhuf. Allah Ta'ala Yana cewa:
"Suhufin Ibrahima da Musa", "Suna karanta Suhufai tsarkakakku, cikinsu akwai litattafai masu kima".
An ce abin da ake nufi da Suhufan shi ne Alkur'ani, sai Ya sanya su takardu da litattafai a cikinsa domin tara wani abu bayan abin da yake cikin sauran littattafan Allah.
Shi kuwa Mus'hafi shi ne abin da aka yi shi mai tattara takardu rubutattu, jam'insa kuwa shi ne Masahif(1) ).
Saboda haka kalmar Mus'haf, a ma'anonin da muke amfani da su a yau, tana nufin littafi ba suna ne wanda ya kebanta da Littafin Allah (Alkur'ani) ba. Shi suna ne na kowane littafi da ya tattara takardu ko fatu (kamar yadda ake rubutu a jikin fata a zamanin da). Ana kiran Alkur'ani da sunan Mus'haf ne domin shi mai tattare ne da takardu.
Alkur'ani mai girma yana da sunaye daban-daban kamar haka: Alkur'ani, al-Zikr, al-Furkan da kuma al-Kitab(2) , wahayi dai bai kira shi (Alkur'ani) da sunan Mus'haf ba, kai dai musulmi su suka ba shi wannan suna
____________
1- Mu'ujam Mufradat Alfaz al-Kur'an na Ragib Isfahani, wajen kalmar Suhuf.
2- Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an na Allama Dabrisi, a mukaddimar littafin.
Saboda haka, lallai tushen rudanin shi ne batun isdilahi (yadda ake amfani da kalmomi) da ma'ana ta lugga a wancan zamanin, wadda ma'anar da mutane suke dauka a cikinsa, yanzu ba a daukar ta a wannan zamanin.
Sannan kuma Imam ya bayyana ma'anar wannan Mus'haf din domin ya kau da rikitarwar da ka iya faruwa, inda ya ce: "Babu wata aya ta Littafin Allah a cikinsa".
Ma'ana, shi ba Alkur'ani ba ne, ba kuma daga Alkur'ani yake ba, ba kuma wahayi ne ba, (shi dai shifta ce ta Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma (rubutun Imam Ali).
Wasu malumma suna cewa wannan Mus'hafin wasu tarin addu'oi da shiryarwa ne wadanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi shiftar su ga Fadima al-Zahra (a.s.) domin tarbiyyarta da kuma ilmantar da ita.
To wannan yana bayyana mana kuskure, rudani da jirkitarwa da wasu daga cikin musulmi suka yarda da shi a dalilin mummunar fahimta da mugun nufi.
Wanda duk ya yi bitar ruwayoyi da hadisan da suka zo ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) ya kuma karanci tarihin rayuwarsu da alakarsu da Littafin Allah, ba zai sami muhimmanci da kulan da Ahlulbaiti (a.s) suke bayarwa fiye da wanda suke bai wa Littafin Allah, Mai Girma da Daukaka ba, ko a yanayin rayuwarsu ko cikin abin da suka ruwaito da maganganunsu ko cikin abin da suka yi wasiyya ko suka tarbiyyantar ko suka fuskantar da mabiyansu da almajiransu da daukacin 'ya'yan musulmi.
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ya ku mutane, lalle kuna gidan dako ne, kuma kuna kan tafiya, tafiyar kuwa tana sauri da ku, kun ko ga dare da yini da rana da wata suna tsufar da kowane sabon abu, suna kuwa kusanto da kowane manisanci suna kawo kowane abin alkawartawa, to ku tanadi shiri wa tafiyar nan mai tsawo".
Ya ce: sai Mikdad bn Aswad ya mike, ya ce: Ya Manzon Allah! Mene ne gidan dako?, sai yace masa:
"Gidan isarwa da yankewa, to idan fitinu kamar yankin dare mai duhu sun rikitar da al'amurra a kanku, na hore ku da Alkur'ani, domin shi, mai ceto ne abin karbawa ceto, mai jayayya abin gaskatawa. Duk wanda ya sanya shi gabansa zai ja-gorance shi zuwa aljanna, wanda ko ya sanya shi a bayansa zai iza shi zuwa wuta. Shi kuwa ja-gora ne mai shiryarwa zuwa mafi alherin
Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
"Mahaddacin Alkur'ani, mai aiki da shi yana tare da Mala'iku Marubuta, Masu daraja, Masu da'a ga Allah(2) ".
Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Wanda Allah Ya ba shi Alkur'ani, sai ya ga cewa an bai wa wani mutum fiye da abin da aka ba shi, to hakika ya rena babban abu, ya kuma girmama karami(3) ".
Ya zo kuma daga wajen Imam Muhammadu Bakir (a.s.) cewa ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ya ku jama'a makarata Alkur'ani! Ku ji tsoron Allah Mai Girma da Daukaka cikin abin da Ya dora muku na LittafinSa domin ni abin tambaye ne, ku ma abin tambaya ne. Ni za a tambaye ni kan isar da sako, ku kuma za a tambaye ku ne kan abin da aka dora muku na Littafin Allah da Sunnata(4) ".
Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
____________
1- Usul Kafi na Shaikh Kulayni juzu'i na 2 shafi na 598.
2- Kamar na sama, shafi na 603.
3- Kamar na sama, shafi na 605
4- Kamar na sama, shafi na 606
Imam Sadik (a.s.) kuma yana cewa:
"Alkur'ani alkawarin Allah ne da bayinSa, to hakika ya kamaci mutum musulmi ya yi dubi cikin alkawarinsa, ya kuma karanta ayoyi hamsin daga ciki a kullum(2) ".
Imam Sadik din dai yana cewa:
"Abubuwa uku za su kai kuka zuwa ga Allah Madau-kakin Sarki: masallacin da aka kaurace masa ba a salla a cikinsa, malamin da ke tsakanin jahilai da kuma Alkur'anin da aka rataye shi kura tana hawa kansa don ba a karanta shi(3) ".
Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
"Lalle Alkur'ani rayayye ne ba matacce ba, kuma yana gudana kamar yadda dare da yini suke gudana, kuma kamar yadda rana da wata suke tafiya. Yana kuma tafe ne kan na karshenmu, kamar yadda yake tafe a kan na farkonmu".
Amirul Muminina (a.s) ya ce:
"Sannan Allah Ya saukar masa da Littafi, haske ne fitilunsa, ba su mutuwa, fitila ce da haskenta ba ya bishewa, kogi ne da ba a risko zurfinsa; tafarki ne wanda salonsa ba ya bacewa; haske ne wanda ba ya yin duhu, mai rarrabewa wanda karfin hujjarsa ba ya raguwa, bayani ne wanda ba a rusa ginshikinsa, waraka ce wadda ba a tsoron cuta a tare da ita, daukaka ce wacce ba a rinjayar masu taimakon ta; gaskiya ce wadda ba a tabar da masu taya ta. Shi ne taskar imani, kuma tsakiyar shi, shi ne mabubbugan ilmi da kogunan shi; shi ne koraman adalci da tabkunan shi; shi ne murhun Musulunci da ginin shi; shi ne kwazazzabon gaskiya da mafakarta; shi tekun ne da masu kwarfa ba sa iya kwarfe shi; idanuwar ruwa ne masu kwarfa ba su iya karar da shi; wuraren sha
____________
1- Usul Kafi na Shaikh Kulayni juzu'i na 2 shafi na 607.
2- Kamar na sama, shafi na 609.
3- Kamar na sama, shafi na 613.
Haka nan dai muke fahimtar kimar Alkur'ani da darajarsa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da kuma tafarkinsu. Ita ce kuwa kima ta hakika wacce Alkur'ani ya yi furuci da ita, wahayi kuma ya siffanta shi da ita
"Hakika wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa hanya da tafi daidai". (Surar Isra'i, 17: 9)
Alkur'ani shi ne hanyar rayuwar al'umma, mabubbu-gar ilmi da shiriya, taskar ma'arifa da wayewa, tafarkin fahimta da tunani, ma'aunin ci gaba da halaye na kwarai, shi ne doka ta ilmi wajen tsara rayuwar dan'Adamtaka, kuma shi ne ma'aji mai tattara al'adun rayuwar mutumtaka da dokokinta.
____________
1- Nahjul Balagah, huduba ta 198.
A cikin abin da ya gabata, mun ambaci yadda tafar-kin Ahlulbaiti (a.s) da mazhabarsu suka tabbatar mana da cewa Littafin Allah madawwami ne, ba jirkitarwar da ta same shi, shi ne kuma kundin dokokin Ubangiji dawwa-mammu, shi ne tushen shari'a, shi ne ma'auni mai hukumci kan ingancin ruwayoyi da hadisai, shi ne kuma hujja wajen tabbatar da kuskure ko dacewar kowane abu. Hadisi ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:
"Idan wani hadisi ya zo muku daga gare ni, ku gwada shi da Littafin Allah, abin da ya dace da shi ku karba, abin da ya saba masa kuwa ku yi jifa da shi(1) ".
Bayan tabbatar wannan da soke dukkan raunanan maganganu na barna, za mu gane cewa tafarkin musulun-ci na asali ya nuna wa musulmi da ma'abuta ilmi da sani hanyar fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da mu'amala da nassin Alkur'ani, ya kuma kayyade mana hanyar. Wannan batu na fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da kuma tawilinsa, batu ne mai tushe, wanda kubutar tunani a Musulunce da ingancin akida da shari'a da masaniyar Musulunci duk sun dogara a kansa ne. Domin duk wani karkata ko takaita ko takaitawa wajen fahimtar Alkur'ani da binciken taskar shari'a da akida da fitar da hukumce-hukumcensa da riskar iliminsa da dokokinsa na zamanta-kewar al'umma da na siyasa, tattalin arziki, tarbiyya, zartar da hukumci da dai sauransu, duk suna kai wa ga karkata da rarrabar musulmi, da kuma yin tawaye ga tsarin asalin addinin Musulunci da tsabtarsa.
____________
1- Majma'ul Bayan na Dabrisi, Mukaddima, juzu'i na 1, shafi na 13.
Tafsiri dai a wajen malaman lugga, shi ne: "Gano ma'anar lafazi da kuma fito da ita(1) ".
Tawili kuwa shi ne: "Mai da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka ya zuwa dacewa da zahirin al'amari(2) ".
Ahmad Ridha ya ce: "Kalmar tafsiri an dauko ta ne daga kalmar "fassara" wacce aka ciro ta daga "assifru", shi ne kuwa fitarwa da bayyanarwa. Ana cewa "asfaras subhu" wato asubahi ya bayyana, ana kuma cewa "asfaratil mar'atu an wajhiha" wato mace ta fito da fuskarta, an yi amfani da kalmar "asfara" wajen fitowa.
Ko kuma ace kalmar tafsiri an dauko ta ne daga "fasara-yafsiru" kamar "daraba-yadribu" ko "nasara-yansuru" "fasara-yafsiru-fasran. Fasru tana nufin bayyana da fito da rufaffen abu. Mutum ya kan ce "fasartu" ga abu idan ya bayyana shi(3) ".
Shaikh Tabrisi (Allah Ya daukaki mukaminsa) ya fadi cikin gabatarwar tafsirinsa mai daraja wato Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an cewa:
"Tafsiri shi ne fito da manufar lafazi mai rikitarwa, tawili kuwa shi ne maidowa da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka, ya zuwa ga dacewa da zahiri. Tafsiri shi ne bayani".
Abul Abbas Mubarrid ya ce: "Tafsiri da tawili da ma'ana duk daya suke. An ce 'fasru' shi ne fitowa da rufaffe, tawili kuwa shi ne karshen abu da makomarsa, da abin da al'amarinsa yake komawa gare shi...(4) ".
Hanyar Da Ake Bi Wajen Tafsirin Alkur'ani:
Yayin da tafsiri yake bayanin ma'anar kalmomin Alkur'ani da jumlolinsu da kuma fito da ma'anoni a
____________
1- Majma'ul Bahrain na Duraihi, kalmar fassara.
2- Majma'ul Bayan na Dabrisi, Mukaddima, juzu'i na 1, shafi na 13.
3- Ahmad Ridha cikin Mukaddimar Majma'ul Bayan, juzu'i na 1, shafi na 13.
4- Gabatarwar Majma'ul Bayan juzu'i na 1 shafi na 13.
Duk wanda ya yi bitar littattafan tafsiri da tafarkin masu tafsiri, zai samu cewa akwai tazara mai fadi da ramuka masu hadari, wadanda sashin masu fassara suka fada, sai suka karkace daga manufar tafsiri domin hanyoyin tafsirin wadanda suka bi da bayanin tawilin da suka yi wa ayoyin Alkur'ani. Wani lokacin a samu sun dogara da raunanan ruwayoyi da aka sossoka, wani loton kuwa a samu sun bi son zuciya sai su tankwarar da Alkur'ani zuwa ra'ayoyin kungiyoyin da suke bi, da kuma son zuciyarsu kebantacciya. Sai ka ga suna kokarin sa ayoyin Alkur'ani su dace da abubuwan da suka auku a tarihi kuma danganta su ga wadansu daidai-kun mutanen da Alkur'anin ba su yake nufi ba. Kai sun ma nemi su sa ayoyin Alkur'ani su dace da girmama ra'ayoyinsu da karkatar su kebantattu.
Misalin karkata cikin tawili shi ne fuskartar da ayoyin Alkur'ani da sashen masu falsafa da ilimin kalami suka yi bayan sun riga sun yi imani da tunani da mazhabobin kalami da falsafa sannan suka tankwara ma'anonin ayoyin zuwa wadannan mazhabobin.
Misali kuma shi ne cewa akwai abin da sashen marubuta da masu tafsiri ke yi na fuskantar da ayoyin
____________
1- Daga cikin misalin tawili, shi ne tawilin da ake yi wa wannan aya: "KujerarSa ta yalwaci sammai da kasa", anan ana yi wa kujera tawili da ilmi da mulki…da dai sauransu, ba wai kujera wacce ake zama a kanta ba kamar yadda aka sani.
Hakika masu tafsiri da yawa sun fada cikin wannan kuskuren, kuma daga mazhabobi daban-daban, na Ahlussunna ne ko na Shi'a ko kuma waninsu. Bayan sun yi wannan kuskuren sai su dora kawo hujjoji da dalilai don kare wadannan ra'ayoyi nasu.
Idan muka koma ga tafarkin Musulunci na asali wajen tafsiri za mu ga cewa ya yi watsi da wannan tafarki da muka fadi a baya da kuma tabbatar da asasai ingantattu na tafsiri.
Don kuwa tafsiri kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi, kuma tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da duk wanda ya bi tafarkinsu ba tare da karkata ba da malaman tafsiri masu lizimta, yana da asasai da ginshikansa wadanda suke shiryar da mai tafsiri da mai bincike zuwa dacewa mayalwaciya.
Bari mu kawo bayanin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da Imamai Masu shiryarwa (a.s.) da malaman al'umma kan batun sanya ginshikai wadanda ba su da wata karkata, domin tafsiri da tabbatar da ma'aunai da kuma dokoki masu kiyaye wannan ilmi mai daraja, domin shi ilmi ya ba da gudummawarsa tare da cikakkiyar kula da kubuta daga karkatarwa. Kuma domin
Allama Dabrisi ya ambata cewa: "Ya inganta daga Annabi (s.a.w.a), ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) cewa: "Tafsirin Alkur'ani ba ya halatta sai da asari (wato hadisi) ingantacce da kuma nassi bayyananne(1) ".
Lalle Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna bin wannan hanyar, suna kuma watsi da yi wa Alkur'ani tafsirin da ya yi nisa daga wadannan ginshikai guda biyu, wato:
Don haka ne ya wajaba cewa dole tafsirin ya lizimci wadannan ginshikai biyu, cikakkiyar lizimta. Sannan kuma wajibi ne kada mu gafala kan cewa hankali yana da fagensa na asasi da ja-goranci wajen fahimtar Alkur'ani da tafsirin ma'anoninsa da fuskantar da zahirinsa, bisa sharadin cewa shi hankali zai lizimci iyakokin Littafin Allah da Sunnan Ma'aiki (s.a.w.a.), ba zai kuma sabawa tsarinsu ba. Hakika Manzo Mai girma ya ba wa hankali fage fitacce wajen tafsirin Alkur'ani, inda ya ce:
"Alkur'ani mai saukin korawa ne, mai fuskoki da yawa; to ku dauki fassarar da ta fi kyau(2) ".
Har ila yau ya ce:
"Ku bayyana Alkur'ani kuma ku nemi kebantattun abubuwansa(3) ".
Alkur'ani mai girma ya bayyana irin rawar da hankali zai taka cikin tafsiri, ya kuma yaba wa ma'abota hankula masu fitar da hukumce-hukumce daga
____________
1- Gabatarwar Majma'ul Bayan na Tabrisi, juzu'i na 1, shafi na 13.
2- Kamar na sama.
3- Kamar na sama.
"Da masu istinbadinsa daga cikinsu sun san shi". (Surar Nisa'i, 4: 83)
Alkur'ani ya yi suka ga wadanda suka bar tunani da lurar hankali cikin ayoyin Alkur'ani mai girma, da gano ma'anoninsa da abubuwa da ya kunsa, da cewa:
"Shin ba su lura da Alkur'ani ne, ko kuwa da kemare ne bisa zukata" (Surar Muhammadu, 47:24)
Daga nan za mu san cewa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) tafsiri yana dogara ne da asasai uku:
Haka nan muke samun cewa tafsiri yana da asasai da dokoki, kuma abin da ya tafo na tafsirai wanda za a cewa ra'ayin mutum ya shige shi, ko kuwa an dauki wasu nazarce-nazarcen ilmi wadanda mai tafsirin ya yi zamani da su, ko ra'ayoyin falsafa da ilmin akida, ko abin da aka danganta shi da ruwayoyi raunana ko ma wadanda sanadinsu yashashshe ne, ko kuwa masu karo da ayoyin Alkur'anin da suke a sarari ko kuma sunna tabbatatta, ko kuwa tafsirin da mai tafsirin ya daidaita shi da ra'ayinsa da karkatarsa da kuma sauran irin wadannan, dukkansu ababan yarfarwa ne a tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da kuma malamai da masu tafsiri wadanda suka bi shiriyarsu. Sau da yawa kuma ana samun cikin tafsiran musulmi, sunna da shi'a, ra'ayoyi da tafsirai wadanda ba su lizimci wannan hanyar ta Musulunci ba, wadanda kuma ba su bayyana ruhin Alkur'ani.
Don haka, ba wa irin wadannan tafsiran kima ba ya
Mai tafsiri kuwa ko wane ne shi, Alkur'ani hujja ce akansa, ba shi ne hujja a kansa ba. Kuma ba zai zamo hujja kan musulmi ba face da gwargwadon abin da ya dace da katari da abin da ya gano na hakika kawai.
Hakika hani ya zo daga wajen Imamai (a.s.) kan magana ba da wani ilimi ko hujja ba. An ruwaito Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"Abin da kuka san shi to ku fade shi, abin da kuwa ba ku sani ba to ku ce "Allah Shi Ya fi sani". Lalle mutum yana tuzgo aya daga Alkur'ani ya fadi cikin tuzgowar da ya yi, faduwar mai nisan fiye da tsakanin sama da kasa(1) ".
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Ko wane abu ana komar da shi zuwa ga Littafin Allah da Sunna(2) ".
____________
1- Sahihul Kafi na Bahbudi, juzu'i na 1, shafi na 5.
2- Kamar na sama, shafi na 11.
"Allah Ya ni'imta bawan da ya ji maganata sannan ya haddace ta ya kiyaye ta ya kuma bayar da ita (ga wasu) kamar yadda ya ji ta. Sau da yawa ana samun mai daukar ilmi, amma ba malami ba, sannan kuma sau da yawa ana samun mai daukar ilmi ya zuwa wanda ya fi shi sani(1) ".
Baicin Littafin Allah, Sunna ita ce mabubbuga ta biyu daga mabubbugan shari'a, wadanda musulmi suke dogara da su wajen fitar da hukumce-hukumce da dokoki da ka'idojin Musulunci. Ita Sunna tana daukar nauyin bayani da faiyacewa da kuma tafsirin Littafin Allah da furuci da abubuwan da ya kunsa da kuma abubuwan da ya tattara na shari'a da tunani da kuma tarbiyya. Shi nassi na Alkur'ani yana dauke da wata wadata da arziki na tunani da shari'a, mai girma kuma dauwamammiya, ita sunna kuwa ta dauki nauyin bayyana wannan arziki da gamar da shi. Lalle hankula ba za su iya riskar Littafin Allah tamkar yadda Sunna take riskar shi tana bayyana shi ba. Manzon Allah (s.a.w.a.) shi aka yi wa zance da wahayi, shi ne kuwa masanin abin da ke cikin Littafin Allah mai girma na daga abin da suka shafi hukumce-hukumce da ababen fahimta daga ciki da kuma manufofin da yake da su.
Don haka ne ita Sunna mabubbuga ce wacce ba ta kafewa, kuma gaskiya ce wacce barna bata taho mata a bayanta ko a gabanta. Sunna ita ce amintacciya mai ayyana dokokin rayuwa da kuma tsarin jin dadin
____________
1- Al-Diraya na Zainuddin al-Amuli, shafi na 113.
æãÇ ÂÊóÇßõãõ ÇáÑøóÓæáõ ÝóÎõÐõæåõ æóãÇ äóåÇßõãú Úóäúåõ ÝóÇäúÊóåõæÇ
"Abin da Manzo ya zo muku da shi, ku karba, abin da kuma ya hane ku, to ku hanu...". (Surar Hashr, 59: 7)
áóÞóÏú ßóÇäó áóßõãú Ýöí ÑóÓõæáö Çááåö ÃõÓúæóÉñ ÍóÓóäóÉñ áöãóäú ßóÇäó íóÑÌõæ Çááåó æóÇáíóæãó ÇáÂÎöÑ
"Hakika abin koyi mai kyau ya kasance muku daga Manzon Allah, da duk wanda yake kaunar Allah da kuma ranar lahira...". (Surar Ahzab, 33: 21)
ÝÅäú ÊóäóÇÒóÚúÊõãú Ýöí ÔóíúÁò ÝóÑõÏøõæåõ Çáì Çááåö æóÇáÑøóÓõæáö
"Idan kuka yi jayayya a wani abu to ku mai da (hukumcinsa) ga Allah da Manzo...". (Surar Nisa'i, 4:59)
Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) da wadanda suka dauki tafarkinsu wajen tafsiri da hadisi da fikhu da shari'a da akida, sun lizimci wannan hanyar, sun kuma yi gwagwarmaya, sadaukarwa, daurewa cutarwa, shiga kurkuku, kisa, azabtarwa da kuma kora duk a dalilin kare sunna mai tsarki da kira zuwa ga dacewarta da Littafin Allah mai girma.
Hakika an bijirar da Sunna tsarkakakkiya ga coge da karkatarwa da jirkitarwa wanda masu yi wa Musulunci dasisa, karya da kiyayya suke yi domin muzanta wannan dawwamammen sako na Ubangiji, domin kuma su karkatar da tafarkin al'ummar Musulunci.
Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna fagen kan gaba wajen kiyaye Sunna tsarkakakkiya da daukar ta da kuma
Don aka ne suka yaki bidi'oi da bata, suka yi kira da a lizimci Littafin Allah da Sunna da sanya Littafin Allah ya zama shi ne ma'aunin Sunnar Annabi (s.a.w.a). Sun yi hakan ne domin Littafin Allah abin kiyayewa ne daga karkatarwa da jirkita - Alhamdu lillahi - kiyayye ne kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya isar da shi ga Annabi Amintacce Muhammadu (s.a.w.a).
"Lalle Mu muka saukar da Ambato (Alkur'ani) kuma lalle Mu Masu kiyaye shi ne".
Saboda haka, babu hannun jirkitawa ko coge ko wasa da ya taba shi. Domin haka ne ma muke samun Amirul Muminina (a.s) yana cewa:
"Ya ku mutane! Farkon aukuwar fitinu (na daga) son zuciya wadanda ake bi da hukumce-hukumce fararru (wato na bidi'a) wadanda ake sabawa Littafin Allah wajen binsu, mutane suna jibintar wasu mutane wajen bin wadannan hukumce-hukumce. Da dai ita bata tsantsarta take, da ba ta buya ba ga mai hankali, da kuma gaskiya tsantsarta take, da sabani bai samu ba. Amma ana daukar wani abu a nan, a dauki wani a can, sai a cudanya su, sannan su zo tare. A nan ne Shaidan ya rinjaye majibantansa, wadanda kuwa kariya ta gabata gare su daga Allah suka tsira(1) ".
Abu Basir, daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa: "Na ce da Abu Abdullahi (a.s.) cewa: Wadansu abubuwa suna taho mana, mu ba mu san su cikin Littafin Allah ko Sunna ba, to za mu dube su? Sai ya ce: "A'a, amma kai ko ka dace ba za a sakanta maka ba, idan kuwa ka yi kuskure to ka yi wa Allah Mai Girma da Daukaka karya(2) ".
____________
1- Sahihul Kafi na Muhammad Bakir Bahbudi, juzu'i na 1 shafi na 8.
2- Kamar na sama, shafi na 9.
"Dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata cikin wuta take".
Abdullah bn Abi Ya'afur ya ce: "Wata rana na tambayi Abu Abdullah (a.s.) game da sassabawar hadisai, wadanda muke amincewa da wadanda ma ba mu amince musu suna ruwaitowa", sai ya ce:
"Idan hadisi ya zo muku kuma kuka sama masa wata shaida daga Littafin Allah ko wata magana ta Manzon Allah (s.a.w.a.), (to ku karba) idan kuwa ba haka ba to wanda ya kawo muku hadisin ya fi cancanta da shi(1) ".
An samu daga Ayyub bn Al-Hurr ya ce: "Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana cewa:
"Duk wani abu ana iya masa raddi in ban da Littafin Allah da Sunna, to duk hadisin da bai dace da Littafin Allah ba, to kyalkyali ne kawai(2) ".
An samu daga Ayyub bn Rashid daga Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ya ce:
"Abin da bai dace da Alkur'ani ba daga cikin hadisai kyalkyali ne kawai(3) ".
An samu daga Imam Sadik (a.s.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Wanda ya yi riko da Sunnata yayin sassabawar al'umma, yana da ladan shahidai dari(4) ".
Wani mutum ya taho wa Amirul Muminina (a.s) ya ce: "Ka ba ni labari (mece ce) Sunna da bidi'a da jama'a da kuma rarraba", sai Amirul Muminina (a.s) ya ce da shi:
"Sunna ita ce abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sunnanta, bidi'a kuma ita ce abin da aka fare shi a bayansa. Jama'a ita ce wadanda suke tare da gaskiya ko da su kadan ne, rarraba kuwa ita ce wadanda suke tare da
____________
1- Sahihul Kafi na Muhammad Bakir Bahbudi, juzu'i na 1 shafi na 11.
2- Kamar na sama.
3- Kamar na sama.
4- Mishkatul Anwar na Tabrisi, babin riki da sunna.
Har ila yau, Imam Ali (a.s) yana cewa:
"Sunna biyu ce: Sunna ta wajibci, riko da ita shiriya ce, barinta kuwa bata ce. Da kuma Sunna cikin abin da ba wajibi ba, riko da ita falala ce, barinta kuwa kure ne(2) ".
Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"Ita Sunna ba a yi mata kiyasi, to ya ya za a yi kiyasin Sunna alhali mace mai haila tana rama azumi, amma ba ta rama salla(3) ".
An samu daga Abu Abdullah, Imam Sadik (a.s.) daga Mahaifansa, daga Imam Ali (a.s.) cewa:
"Kowace gaskiya tana tare da wata hakika, kuma kowace dacewa tana tare da wani haske. To abin da ya dace da Littafin Allah ku karbe shi, abin da kuwa ya saba da Sunnar Manzon Allah, to ku bar shi(4) ".
Sannan kuma yana cewa:
"Allah Ya ji kan mutumin da ya kawo hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ba tare da ya yi masa karya ba, ko da kuwa mutane sun guje shi(5) ".
Sannan Amirul Muminina Ali (a.s) ya ce: "Na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Idan hadisi ya taho muku (sashinsa) yana daidaita, (sashi kuma) yana sassabawa, to abin da sashinsa yake karyata sashe ba daga gare ni yake ba, kuma ban fade shi ba, ko da an ce na fada. Idan kuma hadisi ya taho muku, sashensa yana gaskata sashe, to shi daga gare ni yake, kuma ni na fade shi. Wamda kuwa ya ganni bayan rasuwata, kamar wanda ya ganni a raye ne, wanda kuwa ya ziyarce ni to zan kasance masa mai shaida a ranar kiyama(6) ".
____________
1- Mishkatul Anwar na Tabrisi, babin riki da sunna.
2- Kamar na sama.
3- Kamar na sama.
4- Kamar na sama.
5- Kamar na sama.
6- Kamar na sama.
"Ya Muhammad! Abin da ya taho maka na wata ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya dace da Alkur'ani to ka dauke shi, abin da kuwa ya taho maka na ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya saba da Alkur'ani to kada ka karbe shi(1) ".
Haka nan ake sanya iyakoki wa abin da ake daukarsa Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) ne a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da tafarkinsu da kuma alakar wannan Sunna mai tsarki da Littafin Allah, da kuma rawar da take takawa cikin shari'a da sanya dokoki da gina rayuwar zamantakewa da ta ibada, wa al'ummar Musulmi.
Muna iya tsamo wadansu abubuwa daga wannan tsarin mazhabi kamar haka:
Rabe-Raben Sunnar Annabi (s.a.w.a):
Malamai suna raba Sunnar Annabi (s.a.w.a) zuwa gida uku:
Saboda haka muna iya cewa abin da ya fito daga Ma'aiki (s.a.w.a.) na aiki ya kasu kashi biyu:
Don haka, aikin Manzo (s.a.w.a.) yana bukatar tafsiri domin mu gane wajibi da mustahabi da kuma ja'izi. Malamai wadanda suka kebanta da wannan fannin suna rarrabewa cikin fahimta da tafsirin 'aiki' a cikin Sunna, ta hanyar hujjoji da alamomi da tafarkin bincike na ilmin Usulu.
To kamar haka ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta iyakance yadda ake mu'amala da Sunna mai tsarki da tafarkin tabbatar da ingancinta da tafsirinta.
Tafarkin Bincike da Tabbatarwa:
Malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suna da hanyar bincike da tabbatar da Sunnar Annabi (s.a.w.a) wacce Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka iyakance kuma suka bayyana tushenta da alamominta. Mun riga mun yi nuni ya zuwa ga ruwayoyin da suka zo kan hakan a baya.
Bisa wannan tushen malaman fikhun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka kafa tafarkin gyara (nakdi) cikin aikin bincike na ilmi. Babu wata sunna da suke mika wuya wajen ingancinta tun farko, sai dai su dauki matakin shakka kan ingancin sunnar, sannan su ci gaba da kokkofi da binciken ruwayar da tabbatar da ingancinta, idan har ingancinta ya tabbata sai su yi riko da ita da kuma daukanta a matsayin hujja da kuma fitar da hukumce-hukumce daga cikinta. Idan kuwa rashin
Bisa ga wannan bayani, malaman mazhabar Ahlul-baiti (a.s) ba su yi ikrari da samuwar wasu littattafan hadisai masu inganci, sake ba tare da wani kaidi ba. Sai dai kowane littafi dole ya rusuna wa bincike da gwaji kafin a tabbatar da ingancinsa.
Misalin littattafai mashahurai a ruwaya wadanda suka tattara abin da ya taho ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) su ne:
Da dai sauran littattafan hadisi.
Babu shakka malaman Imamiyya wadanda kuma suke lizimtar tafarkin Ahlulbaiti (a.s) a fikihu da shar'antawa da ilmomin Musulunci sun sanya hadisan da suka zo cikin wadannan littattafa a bisa ma'aunin bincike wanda ya kubuta daga son rai, inda bayan binciken suka zubar da adadi mai yawa na hadisan saboda rashin ingancinsu.
Kamar yadda wadannan malumma suka binciki wadannan littattafa na hadisi, haka kuma suka gudanar da bincike kan wasu littattafan kuma, kamar su Sahih Bukhari, Sahih Muslim, Sunan Abi Dawud, Kanzul Ummal da dai makamantansu daga cikin littattafan hadisai da ruwayoyi, suka kuma auna su da wannan ma'auni na ilmi, kamar dai yadda suka gudanar akan wadancan, suka dauki na dauka da kuma zubar da ba
Su wadannan malamai kuwa, su kan yi wannan bincike nasu ne a bisa wadannan asasai:
(A). Bincike Kan Isnadi: Abin nufi da isnadi kuwa shi ne silsilar maruwaita wadanda suke ruwaito hadisi. A nan malaman su kan tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiyar maruwaitan, suna masu dogaro da ilmul Rijal, wanda yake gabatar musu da sanarwar abin da ya jibinci mutanen da suke maruwaita ne, yana shaidar gaskiya ko rashin gaskiyarsu, ba tare da la'akari da mazhabar da maruwaicin ya fito ba. Idan ya zama abin dogaro kuma gaskiya, sai su karbi ruwayarsa, idan kuwa an yi suka cikin al'amarinsa sai su ture ruwayar tasa. Su ba sa duba kome sai gaskiyar mai ruwaya da kubutarsa a bisa ginshikai tabbatattu.
(B). Binciken Matani: Abin nufi da matani shi ne asalin nassi. A nan malamai suna bincike ne kan luggar matani da ma'anarta, kuma suna bincike domin su tabbatar da cewa abin da ya taho a hadisin bai sabawa Littafin Allah ko tabbatacciyar Sunna ko wata hakika tabbatacciya wacce Mai shar'antawa Matsarkaki (Allah) Ya tabbatar da ita a matsayin tabbatacciyar hakika a hankalce ba.
Yayin da ingancin isnadi da na matani suka tabbata wajen malamai sai su karbi ruwayar, idan kuwa ba haka ba sai su ture ta, ba ruwansu da cewa a wani littafi daga cikin littattafan hadisi ta zo.
Saboda haka a tafarkin malaman fikihu da malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) Imamiyya ba a samun:
Wanda duk yake bitar littattafan Usulu da fikihu da Ilmul Rijal , zai samu wannan hakikar a bayyane.
Da haka ne wannan hanyar bin diddigi ta ilmi ta kiyaye asalin shari'a da tsarkin ta, da kuma hadin kan musulmi da nisantar nuna bangaranci, jahilci da ganin girman wani tun da ba a ba da dama wa wadannan abubuwa a tafarkin bincike, don kuwa a yayin bincike kowa daya ne.
Kuma da wannan tafarkin bincike da ilmin bin diddigi, wanda ya kafu a bisa asasin neman gaskiya da bincike a aikace, da rashin mika wuya da yarda da ingancin kowace ruwaya ba tare da lura da kowane ne maruwaicin ta ba, ko littafin da aka ruwaito ta ba, ne ake gudanar da binciken hadisi.