Imaman Ahlulbaiti (a.s) ba su kasance masu Ijtihadi ko fitar da hukumci ba, sai dai sun kasance masu ruwayar Sunna ne, don haka, duk abin da ya fito daga gare su Sunna ce. Su kan ruwaito Sunnar ce da daga mahaifinsa, daga kakansa….daga Manzon Allah (s.a.w.a.). A saboda haka ne Imam Sadik (a.s.) ya ke cewa:
"Hadisina hadisin babana ne, hadisin babana hadisin kakana ne, hadisin kakana hadisin babansa ne, hadisin babansa kuwa hadisin Aliyu bn Abi Talib ne, hadisin Aliyu kuwa hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) ne, hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) kuwa fadar Allah ce Mai girma da Daukaka(1) ".
Daga Kutaiba, ya ce: "Wani mutum ya tambayi Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) wata mas'ala, sai ya ba shi amsarta, sai mutumin ya ce: mene ne ra'ayinka in ya kasance kaza da kaza, mene ne hukumcinsa? Sai Imam ya ce masa: "Saurara! Abin da na baka jawabinsa, to daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ke, mu ba mu daga cikin wadanda a ke ce da su mene ne ra'ayinka a kowane abu (2)".
A saboda haka ne Shaikh al-Baha'i yake cewa:
"Dukkan hadisanmu idan ba 'yan kadan ba suna komawa ga Imamanmu goma sha biyu (a.s.), daga nan kuma suna komawa zuwa ga Annabi (s.a.w.a). Domin ilminsu abin haskaka ne daga waccar fitilar(3) ".
Da wannan ne Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka zama mabubbugar hadisi da ruwaya da bayanin hukumce-
____________
1- A'ayanu al-Shi'a na Allama Sayyid Muhsin Amin juzu'i na 3 shafi na 34.
2- Usulul Kafi na Shaikh Kulayni, juzu'i na 3, shafi na 34.
3- Mubadi Amma fi Ilmil Hadith na Shaikh Baha'i shafi na 22.
Lalle rayuwarsu mai albarka, rayuwa ce da ke danfare da juna, babu rabewa a cikinta, babu wani bako wanda ba sananne ba da ya shamakance saduwarsu da Manzon Allah (s.a.w.a.), to wannan rayuwa tana zaman wata makaranta ce da kuma gwaji rayayye mai nuna Musulunci da tabbatar da hukumce-hukumcensa da kiyaye tushensa. Dukkan wannan yana karfafa mana amincewa da tsarkin mabubbugar da tsabtar baiwar da kuma cewa abin da ya taho daga gare su (a.s.) mai asali ne.
Yayin da muka san dukkan hakan, za mu iya gane yanayin da mazhabar ilmi wanda mabiyan Ahlulbaiti (a.s) suka taso daga ciki suka kuma dauki iliminsu, sannan za mu gane cewa mazhabarsu na hadisi da tafsiri da ilmin akida da tauhidi da dai sauransu suna da aminci kuma hanya ce tsabtacciya mai sadarwa zuwa ga masaniyar annabci da tsarkin shari'a da asalin tushen Musulunci.
Daga nan ya dace mu fito da daidaikun silsilar nan mai albarka ta Imaman Ahlulbaiti (a.s) maruwaita daga Manzon Allah (s.a.w.a.) sannan kuma mu sanar da al'ummarmu matsayinsu na ilmi a shariance. Su Ahlulbaiti (a.s) yayin da suke zancen silsilarsu ta maruwaita hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.), suna zancen wannan silsilar ne, ga ta nan kuwa:
Mun riga da mun yi magana kan guda uku na farko (wato Aliyu, Hasan da Husaini), mun san matsayi da mukaminsu cikin Alkur'ani da Sunnar Annabi (s.a.w.a),
To yanzu kuma bari mu yi bibiyar zantuttukan malamai dangane da sauran da suka saura daga cikin wadannan taurari masu albarka na gidan Annabci.
4- Imam Aliyu bn Husain (Zainul Abidin) (a.s.):
Shaikh Mufid ya nakalto cikin littafinsa Al-Irshad daga Zuhri cewa: "Ban riski wani mutum daga mutanen wannan gida - wato gidan Annabi (s.a.w.a) - wanda ya fi Aliyu bn Husaini (a.s.) ba(1) ".
An nakalto daga Sa'id bn Musayyab, dangane da Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: "Wannan Shugaban masu ibada, Aliyu dan Husain dan Aliyu dan Abi Talib (a.s.) ne(2) ".
Ibn Hajar cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika ya siffanta Imam Aliyu bn Husain (a.s.) da cewa: "Zainul Abidin shi ne halifan babansa (Imam Husain) wajen ilimi da zuhudu da ibada(3) ".
An samu daga Abi Hazim da Sufyan bn Uyaina, ko wani dayansu yana cewa: "Ban taba ganin wani Bahashime wanda ya fi Aliyu bn Husain daraja ko ilmi ba(4) ".
Hakika irin wadannan mutane daidaiku masu daraja wadanda suke kan mukamin Imamanci su ne malaman al'umma kuma su ne mafifita wajen ilmi, to lallai sun cancanca da malamai su siffantasu da irin wadannan siffofi, kuma sun cancanci karkatowar musulmi zuwa gare su wajen karbar hadisi da fikihu da tafsiri da akida da dai sauran ilmomin shari'a matsarkaki.
Hakika Imam Husaini bn Ali (a.s.) ya yi wa dansa Imam Ali Zainul Abidin alamar imamanci, ya kuma bayyanar da Imamanci da shugabancin addini ga dan
____________
1- Kitabul Irshad na Shaikh Mufid babin falalar Imam Aliyu bn Husain (a.s.).
2- Kamar na sama, shafi na 257.
3- Ahlulbaiti na Abu Ilmi.
4- Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi.
An ruwaito hadisi daga Imam Ja'afar Sadik (a.s.) cewa:
"Lallai yayin da Husaini (a.s.) ya yi tafiya zuwa Iraki ya yi ajiyar littattafai da wasiyya wajen Ummu Salama (r.a.). Da Aliyu bn Husaini ya dawo (daga Iraki bayan shahadar babansa) sai Ummu Salama ta mayar da ajiyar zuwa gare shi(1) ".
5- Imam Muhammad bn Aliyu al-Bakir (a.s.):
Amma dansa, Muhammad bn Ali, wanda ake masa lakabi da al-Bakir saboda fadadawarsa cikin ilmomi da masaniyya, to shi kamar mahaifinsa yake, shi ne mafi shahara da musulmi suka sani da tsantsaini da zuhudu da ilmi da masaniyya, malamai da maruwaita da malaman hadisi sun shaida hakan. Sahabin nan mai daraja Jabir bn Abdullah al-Ansari ya ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ba da labarin cewa shi (Jabir) zai riski dansa Muhammad al-Bakir ya kuma umurce shi da ya isar masa da gaisuwarsa.
Wannan sahabin ya ruwaito cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da shi:
"Za ka rayu har ka hadu da wani da nawa daga Husaini, ana ce da shi Muhammadu, yana tsaga ilimi tsagawa. To idan ka hadu da shi ka isar masa da gaisuwa daga gare ni(2) ".
Wannan sahabi kuwa ya riski Imam Bakir (a.s.) alhali yana yaro, sannan kuma ya isar da wannan gaisuwa ta Manzon Allah (s.a.w.a.) gare shi.
Lallai a cikin wannan shaida ta annabta da wannan
____________
1- A'alamul Wara bi A'alamul Huda na Allama Dabrisi/ Nassosin da suke nuni da Imamancinsa/ shafi 252 da kuma Manakib Aali Abi Dalib/ juzu'i na 3.
2- Kitabul Irshad na Shaikh al-Mufid, Fusulul Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki, Ya'akubi cikin Tarihinsa da Sabalanji cikin Nurul Absar da kuma Ibn Jawzi cikin Tazkiratul Khawas.
Hakika malamai da maruwaita da malaman tafsiri da masu neman ilmummukan Musulunci daban-daban a wancan yanki zamanin suna yi wa Imam Bakir kallon kololuwar da tafi kowacce, kuma ilmin da ba wani ilmin da daukakarsa ta kusaci nasa.
Ibn Ahmad al-Hanbali ya siffanta shi da cewa:
"Abu Ja'afar, Muhammadu al-Bakir ya kasance daga malaman Madina kuma ana ce da shi bakir ne domin ya tsaga ilmi wato ya tsaga shi ya sanar da asalinsa ya kuma fadada cikinsa (1)".
Ibn Jawzi ya nakalto daga wani shugaban Tabi'ai, Ada, wata maganar da ya yi kan Imam Muhammad al-Bakir (a.s.) cewa:
"Ban taba ganin malamai suna kaskantar da kai cikin ilminsu kamar yadda na gani a gaban Abu Ja'afar al-Bakir ba(2) ".
6- Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.):
To batun dansa, Ja'afar al-Sadik (a.s.) kuwa, hakika malamai sun yawaita yabo gare shi da kuma mahaifansa da kuma girmama matsayinsu. Za mu ambaci kadan daga cikin wadannan maganganu, kamar haka:
Allama Muhakkik Sayyid Muhsin Amin ya nakalto cewa:
"Lallai Hafiz bn Akd al-Zaidi a cikin littafinsa na Rijalu, ya kawo mutum dubu arba'in daga magaskatan da
____________
1- Imam Sadik wal Mazahibul Arba' na Asdar Haidar, juzu'i na 2, ya nakalto daga Shazratul Zahab juzu'i na 1, shafi na 149.
2- Siratul A'imma Ithna Ashr na Hashim Ma'aruf al-Hasani, juzu'i na 2, shafi na 198.
Ibn Shahr Ashub ya kawo a cikin littafinsa, Manakib Aali Abi Dalib daga littafin Hilyatul Awliya' na Abu Nu'aim cewa:
"Hakika manyan malamai da shuwagabanni sun karbi hadisi daga Ja'afar al-Sadik, cikinsu har da: Malik bn Anas, Shu'ba bn Hajjaj, Sufyan al-Thawri, Ibn Jarih, Abdullah bn Amru, Ruh bn Kasim, Sufyan bn Uyaina, Sulaiman bn Bilal, Isma'il bn Ja'afar, Hatim bn Isma'il, AbdulAziz bn Mukhtar, Wahb bn Khalid, Ibrahim bn Dahhan da dai sauransu. Ya ce: Muslim ya fitar da hadisi cikin Sahihinsa yana mai kafa hujja da hadisinsa (Imam Sadik). Wasu kuma suka ce: Wadanda suka ruwaito daga gare shi sun hada da Malik, Shafi'i, Hasan bn Salih, Abu Ayyub al-Sajistani, Umar bn Dinar da Ahmad bn Hambal. Malik bn Anas ya ce: Ido bai ga ba, kunne bai jiba, kuma bai fado wa zuciyar wani mutum wanda ya fi Ja'afar Sadik a falala da ilmi da ibada da tsantsaini(2) ".
Uztaz Shaikh Mahmud Abu Zuhra, shaihin malami a Jami'ar Azhar ta kasar Masar ya yi magana kan Imam Sadik (a.s.) a cikin gabatarwar littafinsa mai suna Imam Sadik, ya ce:
"Bayan haka; hakika mun yi niyyar mu yi rubutu kan Imam Ja'afar Sadik, da taimakon Allah da gamo da katar daga gare Shi. Hakika mun yi rubutu kan bakwai daga shuwagabanni masu daraja, ba mu jinkirta rubutu kansa domin ya kasa wani daga garesu ba, a'a, shi yana da fifikon gabatuwa bisa mafiya yawansu. Yana kuma da fifiko makebanci bisa manya-manya daga cikinsu domin Abu Hanifa ya kasance yana ruwaitowa daga gare shi yana kuma daukarsa a matsayin mafi sanin abin da
____________
1- Allama Muhsin Amin ya nakalto shi cikin littafinsa na A'ayanu al-Shi'a, juzu'i na 3, shafi na 34.
2- Manakib Aali Abi Dalib na Ibn Shahr Ashub, juzu'i na 4, shafi na 248.
Amru bn Mukdam ya kasance yana cewa:
"Idan na dubi Ja'afar bn Muhammad na kan gane cewa shi daga tsatson Annabawa ya fito".
Shahararren malamin tarihin nan Ya'akubi ya siffanta Imam Sadik (a.s.) da cewa:
"Ya kasance mafificin mutane, mafi ilmin addinin Allah. Mazowa ilmi wadanda suka ji daga gare shi sun kasance idan za su ruwaici wani abu daga gare shi su kance; 'Malam ya ba mu labari(2) '.
Wannan dan haske ne kadan daga sanarwar malamai da maruwaita da masu hadisi da kuma shaidarsu mai bayyana matsayin Ahlulbaiti (a.s) da bigirensun nan na ilmi da imani madaukaki.
7- Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s.):
Batun kuma Imam Musa bn Ja'afar (a.s.) kuwa, shi ne dan Imam Ja'afar Sadik (a.s.). Ya sami tarbiyya cikin
____________
1- Imam Sadik na Muhammad Abu Zuhra, shafi na 3.
2- Tarikh Ya'akubi, juzu'i na 2, shafi na 381.
Hadisi ya zo daga gare Imam Sadik din yana fadawa wani sahabinsa cewa:
"Lallai wannan da nawa da ka gani, da za ka tambaye shi abin da yake tsakanin bangwayen Littafi guda biyu (Alkur'ani) da ya ba ka amsa da ilmi cikakke(1) ".
Malaman Ilmul Rijal da na tarihi sun siffanta shi da cewa shi malami ne mai gaskiya kuma mai ibada ne wanda ya shahara da tsantsaini da takawa da girman al'amari da madaukakin halin kwarai. Za mu ambaci abin da Hafiz al-Razi ya fadi cikin littafinsa na Ilmul Rijal kan irin wannan shaidar, inda yake cewa:
"Musa dan Ja'afar dan Muhammad dan Ali dan Husain dan Ali dan Abu Dalib ya yi ruwaya ne daga babansa, shi kuma dansa Ali bn Musa da dan'uwansa Ali bn Ja'afar sun ruwaito daga gare shi, ya ce; Na ji babana yana fadawa Abdurrahman cewa: An tambayi babana game da shi sai ya ce: Mai gaskiya ne, mai yawan gaskiya, shugaba daga shuwagabannin musulmi(2) ".
Muhammad bn Ahmad al-Zahabi ya fadi game da shi cewa:
"Musa ya kasance daga masu (gwanayen) hikima kuma daga bayin Allah masu tsoron Allah(3) ".
Kamaluddin Muhammad bn Dalha al-Shafi'i ya ce:
"Shi ne shugaba mai girman alkadari, mai madauka-kin al'amari, babban mujtahidi mai kyautata ijtihadi, wanda ya shahara da ibada, mai dogewa bisa biyayyar
____________
1- Kurbul Asnad, shafi na 193, da kuma Al-Manakib na Shahr Ashub, juzu'i na 3, shafi na 411.
2- AlJurhu wa al-Ta'adil na Razi, juzu'i na 8, babin Jim, shafi na 139.
3- Mizanul I'itidal na Zahabi, juzu'i na 3, shafi na 209.
Mu'umin Shabalanji ya ce:
"Musa al-Kazim (r.a.) ya kasance mafi yawan ibada a zamaninsa kuma mafi ilmi(2) ".
8- Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.):
Amma batun dansa wato Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) kuwa, to hakika ya kasance tamkar mahaifinsa wajen ilmi da tsantsaini da cikar kyawawan halaye. Ya karbi ragamar shugabancin addini da nauyin Imamanci a bayan babansa. Ya kai matsayi mai daukaka da daraja wanda ya tilastawa halifan Abbasiyawa Ma'amun ya nada shi magajinsa a bayansa, duk da gaba da fito-na-fito da ke tsakanin Alawiyyawa da Abbasiyawa.
Hakika malamai sun ba da shaida a majalisun ilmi da muhawara, kan matsayin Imam Ali Ridha wajen ilmi da karimci da siffantuwarsa da tsantsaini da takawa.
Ga wasu daga cikin wadannan maganganu:
Al-Wakidi ya ce: "Ya kasance mai gaskiya, yana ba da fatawa a masallacin Manzon Allah (s.a.w.a.) alhali yana dan shekara ashirin da 'yan kai. Yana daga dabaka ta takwas ta tabi'ai na mutanen Madina(3) ".
Amma babansa Musa bn Ja'afar (a.s.) wanda muka riga da muka san matsayinsa na ilmi da tsantsaini da tsoron Allah, shi ma ya ba da shaidar ilmin Aliyu bn Musa al-Ridha da kuma shiryarwa zuwa ga karbar addini da shiriya daga gare shi, inda yake cewa:
"Wannan dan'uwannaku Ali bn Musa, shi ne mafi sani a duk mutanen gidan Muhammadu, don haka ku
____________
1- Madalibul Su'ul na Kamaluddin al-Shafi'i, shafi na 18.
2- Nurul Absar na Mumin Shabalanji, shafi na 218.
3- Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi, shafi na 198.
9- Imam Muhammad bn Aliyu al-Jawad (a.s.):
Amma Imam Jawad (a.s.), shi ma tamkar mahaifa da magabatansa tsarkaka yake wajen ilmi da zuhudu da kuma tsoron Allah.
Sibd bn Al-Jawzi yana cewa:
"Muhammad al-Jawad shi ne Muhammad bn Ali bn Musa bn Ja'afar bn Muhammad bn Ali bn Husain bn Ali bn Abi Dalib. Sunan kunyarsa shi ne Abu Abdullah, wasu kuma su kan ce masa Abu Ja'afar. An haife shi ne a shekara ta 165 bayan hijira, ya yi shahada kuma a shekara ta 220, ya kasance bisa tafarkin babansa wajen ilmi da takawa da zuhudu da kyauta(2) ".
Muhammad bn Ammar ya ruwaito cewa:
"Na kasance wajen Ali bn Ja'afar(*) bn Muhammad a Madina, na kasance a wajensa har na tsawon shekara biyu ina rubuta abin da na ji daga wajen dan'uwansa (Imam Musa bn Ja'afar Kazim) sai Abu Ja'afar Muhammad bn Ali Ridha ya shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a.), sai Ali bn Ja'afar ya yunkura ya mike ba takalmi ba abaya, sai ya sumbanci hannunsa ya girmama shi.
Sai Abu Ja'afar ya ce da shi: "Ya baffana, zauna mana, Allah Ya yi maka rahama".
Sai ya ce: "Ya shugabana, ya ya zan zauna alhalin kana tsaye?!
____________
1- Kitabul Irshad na Shaikh al-Mufid.
2- Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi, shafi na 202.
(*) Aliyu bn Ja'afar Sadiq shi ne baffan baban Imam Jawad (a.s.), kuma yana daga cikin maruwaita masu gaskiya abin dogara a wajen maruwaitan hadisan musulmi.
Sai ya ce: "Ku saurara - sai ya kama gemunsa - idan Allah Mai girma da Daukaka bai nufi wannan furfurar da cancantar shugabanci ba amma Ya nufi wannan saurayin, Ya kuma ajiye shi inda Ya ajiye shi, shin zan yi inkarin falalarsa ne? Muna neman tsarin Allah daga abin da kuke fadi, kai bari dai ni bawansa ne ma (1)!".
Mahmud bn Wuhaib al-Bagdadi al-Hanafi ya ce:
"Muhammad al-Jawad bn Ali al-Ridha, sunan kunyarsa shi ne Abu Ja'afar", daga nan sai ya ce: "shi ne magajin babansa wajen ilmi da fifiko, ya fi duk 'yan'uwansa daraja da kamala(2) ".
10- Imam Aliyu bn Muhammad al-Hadi (a.s.):
Amma Imam Ali al-Hadi (a.s.) dan Imam Muhammad al-Jawad (a.s.) lallai yana da falala mai girma da daukakar al'amari wajen ilmi da tsantsaini, tamkar abin da Mahaifansa masu kyauta suke da shi. Ana masa alkunya da Abul Hasan.
Mu'min al-Shabalanji ya ce:
"Ya kasance mai yawan munajati (addu'a), an fadi cikin al-Sawa'ik cewa: Abul Hasan ya kasance magajin babansa wajen ilmi da kyautattaki(3) ".
Abdulhayy bn al-Ammad al-Hambali ya ce:
"Abul Hasan, Ali bn Muhammad bn Ali al-Ridha bn al-Kazim, Musa bn Ja'afar al-Sadik, ba'alawiyye, bahusainiyye, wanda aka fi sani al-Hadi, ya kasance fakihi ne kuma shugaba mai yawan ibada(4) ".
Alhafiz Imaduddin Abul Fida, Isma'il bn Umar bn Kathir yana cewa:
"Shi Abul Hasan, Ali al-Hadi, shi ne dan Muhammad
____________
1- Madinatul Ma'ajiz, shafi na 450.
2- Jawharul Kalam , shafi na 147.
3- Nurul Absar, shafi na 149.
4- Shazaratul Zahabi, juzu'i na 2, shafi na 129.
An ruwaito daga Yahya bn Harthama wanda Mutawakkil, sarkin Abbasiyawa, ya aika domin taho da Imam Hadi (a.s.) daga Madina zuwa Samarra, ya ce:
"Sai na tafi Madina, da na shiga garin sai mutanenta suka yi kuwwa mai tsanani wanda ba a taba jin irin ta ba, su na masu tsoron wani abu zai faru da Ali. Suna nuna wannan damuwa ce saboda ya kasance mai kyautata musu, mai lizimtar masallaci, ba ya wata karkata zuwa ga duniya. Sai na fara kwantar musu da hankali, ina rantse musu cewa ba a umurce ni da munana masa ba kuma na zo cutar da shi ba ne. Daga nan sai na binciki gidansa, ban sami kome bai sai Kur'ani da addu'oi da littattafan ilmi, a saboda haka sai na ga girmansa ya daukaka a idanuwana(2) ".
11- Imam Hasan bn Aliyu al-Askari (a.s.):
Imam Hasan al-Askari kuwa shi ne dan Imam Ali al-Hadi (a.s.), shi ma tamkar mahaifansa masu kyautatawa yake wajen ilmi, masaniya, tsantsaini da jihadi. Malamai da ma'abuta tarihi sun ba da shaidar hakan. Za mu ambaci kadan daga cikin wadannan maganganu na masana, kamar haka:
"Darajojin shugabanmu Abu Muhammad Hasan al-Askari suna nuni da cewa shi mai daraja ne dan mai daraja, babu wanda ke shakka ko kokwanton imaman-cinsa. Kuma na san cewa da ana sayar da karimci da waninsa ne mai saye shi kuwa mai sayarwa. Shi tilo ne a zamaninsa ba shi da na biyu, ba a kwatanta shi da kowa, ba shi da kishiya. Shi ne shugaban mutanen lokacinsa, shi ne kuma Imaminsu. Zantuttukansa daidaitattu ne, ayyukansa kuwa abin yabo(2) ".
12- Imam Muhammad bn Hasan al-Mahdi (a.s.):
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ranaku da darare ba za su kare ba har sai Allah Ya tasar da wani mutum cikin Ahlulbaitina sunansa kamar sunana, zai cika kasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya(3) ".
An karbo daga Ali bn Abi Dalib (a.s.) daga Annabi (s.a.w.a) cewa ya ce:
"Da a ce babu abin da ya saura na lokaci face yini guda, to da Allah Ya tasar da wani mutum daga cikin Ahlulbaitina ya cika kasa da adalci bayan an cika ta da zalunci".
Haka Abu Dawud ya kawo hadisin cikin Musnad dinsa. Kuma Abu Dawud din da Tirmidhi sun ruwaito shi cikin Sunan dinsu, kowannensu daga Abu Sa'id Khudri (r.a.) ya ce: "Na ji Ma'aiki (s.a.w.a.) yana cewa:
"Mahdi daga gare ni yake, goshinsa mai fadi, mai dogon hanci, zai cika kasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci".
Abu Dawud ya kara da cewa: "Zai yi mulkin shekaru bakwai, ya kara da cewa hadisi ne tabbatacce mai
____________
1- Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi, shafi na 203.
2- AlFusulul Mihimma fi Ahawalil A'imma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 290.
3- Abu Dawud ya ruwaito cikin Sunan dinsa, juzu'i na 4, shafi na 104, hadisi na 4282, Fusulul Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki.
Hadisan da suka zo ta hanyoyin malaman hadisi da ruwaya daga mazhabobin musulmi daban-daban, suna da yawa ainun, dukkansu sun tafi a kan cewa sunan Mahdi shi ne Muhammadu, kuma shi cikin Ahlulbaitin Annabi (s.a.w.a) yake. Sai dai sun saba kan ko waye shi. Abin da ya tabbata wajen mabiya Ahlulbaiti (a.s) da ma wasu ban da su shi ne; shi Mahdi shi ne Imam Muhammad bn Hasan al-Askari bn Ali Hadi bn Muhammad al-Jawad bn Ali Ridha bn Musa al-Kazim bn Ja'afar Sadik bn Muhammad Bakir bn Ali Zainul Abidin bn Husain bn Ali bn Abi Dalib (a.s.). Kuma an haife shi a tsakiyar watan Sha'aban shekara ta 255 bayan hijira, a garin Samarra. Kuma da ikon Allah, bai gushe ba yana nan a fake, zai bayyana a wani lokaci da kasa za ta cika da zalunci da danniya domin ya cika ta da adalci, kamar yadda hadisai suka nuna. Da kuma cewa Annabi Isa (a.s.) zai yi salla a bayansa.
Wannan shi ne takaitaccen bayani kan Imaman Ahlulbaiti (a.s) da mukaminsu da kuma matsayinsu.
Daga gare su ne aka karbi ilmi fikihu da hadisi da tafsiri da ilmummukan akida da shari'a da dai sauransu.
____________
1- Sunan Abi Dawud na Abu Dawud juzu'i na 4, shafi na 104.
"Farkon addini sanin Allah, cikar saninSa kuwa kadaita Shi, cikar kadaita Shi kuwa tsarkake niyya gare Shi(1) ".
"Allah ba Ya karbar aiki ba tare da an sanShi ba, babu kuma yadda za a sanShi sai da aiki. To wanda ya sani sanin zai shiryar da shi zuwa aiki, wanda kuwa bai yi aiki ba, to ba sani a gare shi. Ku saurara! Lallai shi imani sashinsa daga sashe yake(2) ".
Tauhidi ka'ida ce ta Musulunci, shi ne kuma ginshikin fahimta da tunani, kuma shi ne matattarar ilmi da aiki. Shi ne matakin farko da kuma ka'idar sauya shari'a da ka'idoji da halaye kwarai da kuma tafarkin tunani.
Manufar Tauhidi tana matsayin ginshiki wajen gina wayewa ta Musulunci wacce ta kebanta da rininta na tauhidi; Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
"Rinin Allah! Kuma wane ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, masu bautawa ne". (Surar Bakara, 2: 138)
Rinin nan na tauhidi wanda ya banbanta wayewa irin ta Musulunci daga wata wacce ba ita ba, kuma wanda shi ya ba ta siffofi iyakantattu na aike (daga Allah) shi ya sanya wa rayuwar musulmi da tunaninsa wani zubi kebantacce.
Lallai Alkur'ani mai girma da Sunna mai tsarki su ne tushen tunani na matsalolin akida. Hakika sun ba mu bayani cikakke kan akidar tauhidi, sun bayyana mana samuwar Allah Mahalicci, Mai Girma da Daukaka, sun
____________
1- Imam Ali (a.s.) cikin littafin Nahjul Balagah, huduba ta 1.
2- Hadisi mai tsarki daga Imam Sadik (a.s.).
Addinin Musulunci ya watsu yayin da aka ci kasashe da yaki, al'ummai masu wayewa da falsafar jahiliyya kamar su Farisa da Hindu da Sin, sun shigo Musulunci. Haka nan mutane mabiya karkatattun addinan Kiristanci da Yahudanci wadanda kuma sun sami tasirin falsafa da akidojin Kiristanci da Yahudanci su ma sun shigo Musulunci. A hada da abin da aka debo daga tunani da falsafar Yunaniyawa da masu kama da su. Duk wannan ya tsirar da jayayya da shakku, sannan karairayi da bakin manufofi suka shigo akidar tauhidi, yayin da wannan wayewar mai rusawa ta kutsa kai, sai aka samu cewa akidar tauhidi ta kada ta yi rauni a wajen wadanda suka shagalta da bahasi kan akida da ilmin falsafa. Matsaloli da suka shafi rawar da dan'Adam yake takawa a ayyukansa kamar su Jabr (watau tilastawa) da tafwidh (ba da ikon zabi) da kuma Guluwi (masu wuce gona da iri) da tajsim (kudurta cewa Allah jiki ne) da bayani kan Isra'i da Mi'iraji, duk irin wadannan suka taso, da rudani cikin tunanin mutane. Sakamakon haka sai aka sami mazhabobi da kungiyoyi daban-daban suka tsiro tare da akidoji karkatattu, manisanta daga akidar asali ta tauhidi. Wannan ya sa Imaman Ahlulbaiti (a.s) da malamai masu tunani irin na Musulunci sun shiga fagen fama da masu wadannan karkatattun akidu. Jayayyar da har a wannan zamanin gurbinta bai gushe ba, duk da cewa sashin karkatattun kungiyoyin ya bace. Wannan fama da jayay-ya tsakanin wasu kungiyoyi daban-daban ya wanzar da
Saboda abin da Allah (S.W.T.) Ya yi baiwa da shi ga Ahlulbaiti (a.s) na tsarkakar fahimta da kewayewa ga dukkan ilmomin shari'a da sanin Allah da kiyayewarsu da ilmin Littafin Allah da na Sunnar Annabi (s.a.w.a), lallai su da mazhabarsu sun taka rawar gani wajen warware rikice-rikice da rusa karkatattun ra'ayuyyuka da kuma kare manufar tauhidi da tsare tsarkinta. Muna da muhawarorin Imaman Ahlulbaiti (a.s) da hadisansu da tafsiran ayoyin tauhidi da bayanansu masu gusar da rudani domin fahimtar Musulunci ta gudana bisa tafarkinta na asali ba tare da karkata ba ko mummunan fahimta wa ayoyin da yi musu tafsiri na son zuciya ko bin wata batacciyar falsafa, karkatacciya. Wannan bayani na Imamai kan fahimtar Littafin Allah da saninsu da Allah (S.W.T.) ya haifar da wani tunani hadadde mai riko da akidar tauhidi.
Idan mutum ya yi nazarin al'amarin akidar tauhidi da rassanta da matsalolinta bisa tafarkin Ahlulbaiti (a.s) zai riski tsarkaka da zurfin sha'anin tauhidi, kuma zai gane cewa ginshikin akida da duk wata wayewa shi ne kadaita Allah (S.W.T.). Daga nan za a gane cewa akidar tauhidi ta ginu ne bisa tushen; "Tabbatar da cikakken kamala ga Allah (S.W.T.) da tsarkake Shi daga dukkan tawaya da kuma kore duk wani abokin tarayya ko makamanci ko tamka ko kuma kishiya".
Imam Ali (a.s.) ya kafa tushen wannan mahanga ta tauhidi da cewa:
"Tauhidi shi ne kada ka takaita Allah cikin rayawarka takaitacciya, adalci kuwa shi ne kada ka dora wa Allah tuhuma(1) ".
____________
1- Imam Ali cikin Nahjul Balagah bangaren kalmomin hikima, hikima ta 470.
A nan za mu kawo wani sashe na wadannan asasai na tauhidi wadanda suke nuna akidar Alkur'ani da kuma ayyana tushen ilmi, tunani na tauhidi, tsabtansa da kuma asalinsa.
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito Amirul Muminina (a.s) yana cewa:
"Ku nemi sanin Allah ta hanyar Allah, Manzon Allah kuma ta hanyar sakon (Musulunci), wadanda aka ba su shugabanci (Ulul Amri) kuwa ta wajen umurninsu da kyakkyawa da haninsu ga mummunan aiki da adalci da kyautatawa(1) ".
Alfath bn Yazid ya ruwaito daga Imam Ali bn Musa Ridha (a.s.) cewa:
"Na tambaye shi kan mafi kankantar sanin Allah, sai ya amsa min da cewa:"shi ne yarda da kuma furuci da cewa babu abin bauta koma bayan Allah, babu makamancinSa, babu tamkarSa kuma Shi Dawwamam-me ne ba mai gushewa ba, da kuma cewa babu wani abu tamkarSa (2)".
Nafi'u bn Al-Azrak ya tambayi Imam Abu Ja'afar, Muhammad Bakir (a.s.) cewa:
"Ka ba ni labari yaushe ne Allah Ya kasance?, sai ya ce: "Yaushe ne bai kasance ba har zan ba ka labarin lokacin da Ya kasance? Tsarki ya tabbata wa Wanda bai gushe kuma ba zai gushe ba, Makadaici, Wanda ake nufinSa da bukata, bai riki abokiyar zama ba ko kuma da(3) ".
____________
1- Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, babin tauhidi, shafi na 85.
2- Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, babin tauhidi, shafi na 86.
3- Kamar na sama, shafi na 88.
"Ya Amirul Muminina! Yaushe Ubangijinka Ya kasance? Sai ya ce masa:"Tir da kai, ana 'yaushe ya kasance' ga Wanda ba samamme ba ne? Amma wanda samamme ne ba da wani ba, ba a ce wa 'yaushe ya samu'. Shi Allah samamme ne gaban gabani ba tare da wani 'gabani' ba kuma samamme ne bayan 'baya' ba tare da wani 'baya' ba, kuma babu wai iyakar karshe da za a ce karshenSa ya kai iyaka". Sai malamin ya ce da Imam: "Kai Annabi ne?", Sai Imam (a.s.) ya amsa da cewa: "Kaitonka, ni ba kowa ba ne face bawa cikin bayin Manzon Allah (s.a.w.a.)(1) ".
Imam Bakir (a.s.) ya ce:
"Na hane ku yin tunani kan Allah, sai dai duk yayin da kuke nufin duban buwayar Allah to ku dubi girman halittun Allah(2) ".
Imam Sadik (a.s.) ya yi wasiyya ga wani sahabbinsa (Muhammad bn Muslim) da cewa:
"Ya Muhammad! Su mutane, magana ba za ta gushe gare su ba har sai sun yi magana kan (zatin) Allah. To idan kun ji ana hakan ku ce: 'Babu abin bauta face Allah Makadaici, Wanda babu wani abu tamkarsa (3)'".
Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"Ku yi magana kan kome, kada ku yi magana kan batun zatin Allah(4) ".
Yayin da wani ya tambayi Imam Ali (a.s.) cewa: 'Ina Allah Yake gabannin Ya halicci halitta', sai Imam ya yi masa bayani cewa Allah ba Shi da bukatar bigire, Ya karfafa tsarkakar Mahalicci Madaukaki ga barin wannan, haka nan tsarkakke Ya ke ga barin bukatuwa ya zuwa ga zamani.
____________
1- Kamar na sama, shafi na 90.
2- Kamar na sama, shafi na 93.
3- Kamar na sama, shafi na 92.
4- Kamar na sama.
Yayin da kuma aka tambaye shi kan ganin Allah (S.W.T.) sai ya tsarkake Allah ga barin ganuwa. Ga tambayar:
"Ya Amirul Muminina! Shin ka ga Ubangijinka lokacin da kake bauta masa? Sai ya ce: "Kaitonka! Bana bautar Ubangijin da ban ganshi ba", sai ya ce masa to yaya ka gan shi?, sai Imam (a.s.) ya amsa masa da cewa: "Tir da kai, idanu ba sa riskar Allah da gani irin na ido, sai dai zukata sun gan Shi da matabbatan imani(2) ".
Muhammad bn Hakim ya ce: "Abul Hasan Musa bn Ja'afar (a.s.) ya yi rubutu ya aike wa babana cewa: "Allah (S.W.T.) Ya daukaka, girmanSa ya buwaya ga barin riskar ainihin siffarsa. Ku siffanta Shi da abin da Ya siffanta kanSa da shi, ku kuma kame ga barin koma-ba-yanSa(3) ".
Al-Mufaddal ya ce: 'Na tambayi Abul Hasan wani abu kan sifa, sai ya ce: "Kada ku ketare abin da ya ke cikin Alkur'ani(4) ".
Abdur Rahman bn Atik Alkasir ya ce: 'Na rubuta tambaya zuwa Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ta hannun Abdul Malik bn A'yun cewa:
"Wasu mutane a Iraki suna siffanta Allah da wani yanayi da kuma kama, to idan ka yarda, Allah Ya sanya ni fansarka, ina so ka rubuto min da bayani kan ingantac-cen matsayi kan tauhidi. Sai ya rubuto mini da cewa: "Ka yi tambaya - Allah Ya jikanka - kan tauhidi da kuma abin da wadannan mutane suke fadi. Daukaka ta tabbata ga Allah Wanda babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai ji,
____________
1- Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, babin tauhidi, shafi na 90.
2- Kamar na sama, shafi na 98.
3- Kamar na sama, shafi na 102.
4- Kamar na sama.
Batun dayantuwar zatin da tsarkake shi ga barin kama da halitta kuwa, Hamza bn Muhammad ya ce: 'Na rubuta tambaya ga Abul Hasan Al-Kazim (a.s.) kan jiki da kama (da ake danganawa ga Allah), sai ya rubuto min cewa:
"Tsarki ya tabbata ga Wanda babu wani abu tamkarSa, ba jiki babu kama(2) ".
Haka nan muke karanta tauhidi tsarkakakke, kubutacce na Allah (S.W.T.) a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da karantarwarsu da ke nuna ainihin ruhin Alkur'ani da abubuwan da yake tattare da su, da abin da ayoyinsa suka kunsa. Da wannan ne suka tabbatar da akidar tauhidi, suka kore barnace-barnace da shubuhohi da bata wadanda aka jarrabi tunanin Musulunci a wancan lokacin. Haka kuma wannan bayani yake raddi kan batattu da karkatattun 'yan gulatu(*) (masu wuce gona da iri wajen soyayya), 'yan Mufawwida (masu cewa an bar dan'Adam haka kawai a sake komai yayi daga gare shi
____________
1- Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, babin tauhidi, shafi na 100.
2- Kamar na sama, shafi na 104.
(*). Da yardar Allah a nan gaba za mu yi bayani dangane akidar wannan batacciyar kungiya, wacce ta ke siffanta Imaman Ahlulbaiti (a.s) da siffar Ubangiji, Imamai sun la'ance su da kuma barranta daga gare su.
Haka kuma bayanan Ahlulbaiti (a.s) sun fayyace al'amurra wa wadanda suka shiga rudani suka cudanya tafarkin Ahlulbaiti (a.s), tsarkakakke na gaskiya, wanda bai yarda da karairakin 'yan gulatu da 'yan mufawwida da 'yan hululi ba wadanda suka yi da'awar suna bin Ahlulbaiti (a.s), da wadancan kungiyoyi na bata.
Sau da yawa masu neman raba kan musulmi suna cudanya gaskiya da karairayi, suna karkatar da gaskiya, suna kage da kuma gafalantar da jahilai domin shuka gaba da raba kan al'umma da taimaka wa abokan gaba.
Adalcin Allah Da Sharhi Kan Halayyar Dan'adam:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18)
Adalci siffa ce, cikin siffofin Allah (S.W.T.). Muna iya ganin gurabun adalcinSa a dukkan bangarorin samammu, kamar fagen halitta da samarwa da fagen dabi'a da halittar mutum da dabba da tsiro, haka kuma muna ganin wannan adalcin cikin shari'a da dokokin Ubangiji.
"Lalle Allah Na yin umurni da adalci da kyautatawa". (Surar Nahli, 16: 90)
Haka ma adalcin Ubangiji ya bayyana cikin abin da
"Kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa". (Surar Kahf, 18: 49)
"Sa'an nan kuma a cika wa kowane rai abin da ya sana'anta". (Surar Bakara, 2: 281)
"Allah ba Ya kallafawa rai face ikon yinsa, yana da ladan abin da ya aikata, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatawa....". (Surar Bakara, 2: 286)
Bisa wannan tsarin ne musulmin farko suka tafi wajen fahimtar alakarsu da Allah (S.W.T.) da fahimtar halayyar 'yan Adam da ayyukansu. Daga bisani sai falsafa ta shigo ga kuma ra'ayoyin ilmin tauhidi dukkansu masu sassabawa juna. Hakika wadannan sun tsirar da ra'ayoyi uku kan fassarar ayyukan mutane da alakarsu da iradar (nufi) Allah Madaukakin Sarki.
Wadannan ra'ayoyi kuwa su ne:
Hakika wadansu kungiyoyi da mazhabobi sun yi mummunan fahimta wa zahirin wadansu ayoyin Alkur'ani, kamar fadinSa (S.W.T.) cewa:
"Yana batar da wanda Ya so, Yana kuma shiryar da wanda Ya so".
Ra'ayi na biyu kuwa shi ne mai cewa an sakar wa dan'Adam ikon zabi wajen ayyukansa, da kuma nufinsa babu nufin Allah a cikin ayyukansa. Kai suna ganin ma cewa Allah ba Ya iya hana mutum yin abin da ya yi nufin yi ko sabo ne kamar kisan kai, zalunci, shan giya, ko kuwa ayyukan biyayya ne kamar su adalci, kyautatawa, salla da dai sauransu. To da wannan, dan'Adam yana da 'yanci ga barin Allah (S.W.T.), wannan kuwa shi ne ra'ayin Mu'utalizawa.
To Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi raddi wa wadannan ra'ayoyi guda biyu, sun nuna bacinsu gaba daya. Kowanne daga ra'ayoyin nan biyu sun saba da abin da Alkur'ani ya zo da shi, akidar tauhidi kuwa ta kafu kan tushensa ne. su Imamai (a.s.) sun fayyace mana cewa akwai bayyananniyar alaka tsakanin irin yadda ake fahimtar halayyar mutum da imani da adalcin Allah. Suka ce lallai abin da ra'ayin cewa mutum ba ya mallakar wani nufi ko zabi sai dai shi abin tilastawa ne kurum, yana janyo tuhumtar Mahalicci Mai girma da Daukaka da zalunci da kore adalci daga gare Shi, lallai kuwa Ya girmama daga hakan. Saboda ma'anar wannan shi ne Allah Ya tilastawa mutum aikata sharri sannan kuma Ya yi masa ukuba dominsa, haka nan Ya tilasta masa aikata alheri sannan kuma Ya hana shi ladansa. Domin haka ne Imamai (a.s.) suka kakkabe wannan
"Yana batar da wanda Ya so, Yana kuma shiryar da wanda Ya so".
Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi wa matsalolin shiryarwa da batarwa tafsiri bayyananne mai dacewa da adalcin Allah (S.W.T.). Bayanin wannan yana tafe.
Haka nan kuma Imamai (a.s.) sun yi watsi da ra'ayin masu cewa an sakarwa mutum akala sai yadda ya ga dama zai yi, ba tare da Allah Yana iya hana shi ba. Sun bayyana cewa wannan ra'ayi karkatacce da cewa tuhumar Allah ne da rashin cikakken iko kan bayinSa da gajiyawarSa kan hakan. Alhali kuwa Allah (S.W.T.) Mai cikakken iko ne, kuma Mamallakin dukkan halittunSa.
Imamai (a.s.) suna da matsaya matsakaiciya dangane da al'amarin da ya shafi adalcin Ubangiji. Wannan matsaya tana kore Tilastawa da Sakarwa, tana cewa: (Nufin mutum baya iya rabuwa da nufin Allah). Sun bayyana wannan alakar da take tsakanin nufin mutum da nufin Ubangiji bayani cikakke a akidance. Nan gaba za mu kawo ruwayoyinsu masu nuna wannan ra'ayi.
Kafin mu kawo wadannan ruwayoyi, bari mu yi dan sharhi kan batutuwan da mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bambanta da masu ra'ayoyi kan mas'alar adalcin Allah, bisa abubuwa guda uku na asasi:
Amma Shi Allah, domin tausayinSa da jin kanSa, Yana shiga tsakanin bawan da ya cancanci taimakonSa wajen aikata mummunan aiki, domin jin kai. Haka ma Yana taimaka masa wajen aikata alheri idan ya cancanci taimakon.
Wasu jama'a daga cikin musulmi sun dogara da wannan ayar ne bisa tafsiri na kuskure, suka ce ba ya wajaba kan Allah (S.W.T.) Ya cika alkawarin sakayya da Ya yi a ranar kiyama. Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun mai da martani kan wannan zance da cewa, wannan ya sabawa gaskiyar Allah Ta'ala da adalcinSa.
Wancan ra'ayin yana daidaita mai kyautatawa da mai mummunan aiki, hakan kuwa yana rusa kimar kallafawa bayi da kuma sanya shari'a. Ingantaccen zance dai shi ne babu wani aikin da ba shi da sakamako, ko kuma mai daukar laifin yinsa, kamar yadda aya ta ce:
"Ya Ubangijinmu Kada Ka sanya mu daukar abin da babu iko gare mu da shi". (Surar Bakara, 2: 286)
Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun kore wannan fahimta suna masu bayanin cewa ta saba da adalcin Allah da kuma bayyanannen fadi na Alkur'ani mai girma, cewa:
"Allah ba Ya kallafa wa rai face abin da zai iya dauka". (Surar Bakara, 2: 286)
To yanzu za mu kawo sashen ruwayoyi da tattauna-war Ahlulbaiti (a.s), masu mana sharhin wadannan ginshikai na asali da fassara halayyar mutum da alakar da ke akwai tsakanin nufin mutum da ta Allah (S.W.T.). Wadannan ruwayoyi suna kulla tafsiri da sharhin halay-yar mutum da tushen adalcin Allah domin su karfafa mana dayantaka (ta Ubangiji) fahimta da tunani da kuma i'itikadi cikin sakon Musulunci. A lokaci guda sun bata ra'ayin Jabru da Tafwidhu da ma dukkan sauran tunace-tunace da kirdado wadanda suka fice daga tafarkin Alkur'ani.
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Allah Ya halicci halittu Ya kuma san makomarsu. Ya umarce su (da ayyukan biyayya) Ya hane su
Yayin da Imam Ali bn Abi Dalib (a.s.) ya tafi kasar Sham (Syria), domin yakar Mu'awiyya a Siffin, wani daga sahabbansa ya tambaye shi cewa:
"Ya Amirul Muminina! Ka ba mu labarin wannan tafiya tamu, shin da hukumcin Allah ne ko da kaddararSa?" sai ya amsa masa da cewa: "Saurara dattijo, na rantse da Allah ba kwa hawan wani tudu ko ku gangara cikin wani kwari face bisa hukumcin Allah da kaddararSa".Sai Dattijon ya ce: 'Ga Allah nake neman ladar wahalata, Ya Amirul Muminina'. Sai Imam Ali (a.s.) ya ce da shi:"Kaiconka! Ta yiyu kana zaton hukumci lizimtacce da kaddara yankakkiya! Da haka al'amarin yake da sakamako da horo sun baci, kuma da alkawari da narko sun warware. Allah (S.W.T.) Ya umarci bayinSa bisa zabinsu, Ya hana su domin gargadi, Ya kallafa musu sassauka bai kallafa musu mai tsanani ba, Yana biyan kadan da mai yawa. Ba a saba masa domin rinjaya, ba a tilastawa don a yi maSa biyayya. Bai aiko Annabawa don wasa ba, kuma bai sauko da Littafi wa bayi haka a banza ba. Bai kuwa halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu a banza ba; "Wannan shi ne zaton wadanda suka kafirta. To, bone ya tabbata ga wadanda suka kafirta daga wuta(2) ".
An ruwaito daga Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s.) cewa an ambaci Jabru da Tafwidhu a gabansa, sai ya ce: "Shin ba zan sanar da ku wata ka'idar da ba za ku sassaba a cikinta, kuma duk wanda ya yi jayayya da ku sai kun rinjaye shi ba?Sai muka ce: 'E, a sanar da mu', sai ya ce:"Allah Mai Girma da Daukaka ba a biyayya gare Shi domin tilastawa, ba a saba masa don rinjaya, ba
____________
1- Sahihul Kafi na Bahbudi, juzu'i na , babin Jabru da Kadr.
2- Nahjul Balagah, hikima ta 78.
A cikin littafin Sharh al-Aka'id na Shaikh Mufid an ce:
"An ruwaito daga Abul Hasan na Uku (a.s.) yayin da aka tambaye shi batun ayyukan bayi; shin halittattu ne daga Allah Ta'ala? Sai ya amsa da cewa: "Da Shi Ya halitta su da bai barranta da su ba, alhali Yana cewa: 'Lalle ne Allah Barrantacce ne daga masu shirka'. Barrantan nan ba ta shafar zatinsu, Ya dai barranta ne daga shirkarsu da munanan ayyukansu(2) ".
A cikin littafin Kitabul Tauhid na Muhammad bn Ajlan, ya ce: "Na tambayi Abu Abdullah (a.s.) cewa: 'Shin Allah Ya sakar wa bayi al'amarinsu ne?', sai ya ce: "Karimcin Allah ya wuce gaban Ya saki al'amurransu gare su", sai nace: 'To kenan Allah Ya tilasta wa bayi aikata ayyukansu kenan?, sai ya ce: "Adalcin Allah Ya wuce gaban tilastawa bawa yin wani aiki sannan kuma Ya azabta shi a kan wannan aiki(3) ".
A ruwaito cikin Uyunul Akhbar al-Ridha (a.s.) wajen fadar Allah Ta'ala cewa:
"Kuma Ya (Allah) bar su a cikin duffai, ba su gani". (Surar Bakara, 2: 17)
Abu Abdullah (a.s.) ya ce:
"Ba a siffanta Allah da bari kamar yadda ake siffanta halittunSa, sai dai yayin da Ya san cewa ba su dawowa
____________
1- Kitab al-Tauhid da Uyun Akhbar al-Ridha na Sheikh Saduk da kuma Al-Mizan na Sayyid Tabataba'i, juzu'i na 1, bahasin al-Jabru wat Tafwidh.
2- Al-Mizan na Sayyid Tabataba'i, juzu'i na 1, bahasin al-Jabru wat Tafwidh.
3- Kamar na sama.
Har ila yau ya zo cikin wannan littafin wajen tafsirin Imam Ridha (a.s.) kan fadin Allah (S.W.T.) cewa:
"Allah Ya sa rufi a kan zukatansu".
Sai ya ce: "Abin da ake nufi da 'Khatam' shi ne 'al-Dab'u' watau rufi a kan zukatan kafirai domin yi musu ukuba kan kafircinsu, kamar yadda Allah (S.W.T.) ya ce:
"A'a Allah ne Ya rufe a kansu (zukatansu) saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kadan(2) ". (Surar Nisa', 4: 155)
To haka ne tafarkin Ahlulbaiti (a.s) yake fayyace manufar shiriya da bata da kuma cewa Allah (S.W.T.) bai halicci mutane suna batattu ko shiryayyu ba. Sai dai Ya bar musu zabi, Ya ba su nufi, Ya kuma bayyana musu hanyar alheri tare da gargadi kan hanyar sharri da halaka, Allah Ta'ala Yana cewa:
"Lalle ne Mu, Mun shiryar da shi (mutum) ga hanyar kwarai, ko ya zama mai godiya, ko kuma ya zama mai kafirci". (Surar Insan, 76: 3)
Kuma Yana cewa:
"Kuma Muka shiryar da shi ga hanyoyi biyu". (Surar Balad, 90: 10)
Watau Mun sanar da shi hanyar alheri da ta sharri, zabi kuma na gare shi.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fassara ayar da cewa:
"Su dai hanyoyi ne guda biyu, hanyar alheri da hanyar sharri. Kada hanyar sharri ta fi soyuwa gare ku bisa hanyar alheri(3) ".
____________
1- Al-Mizan na Sayyid Tabataba'i, juzu'i na 1, bahasin al-Jabru wat Tafwidh.
2- Kamar na sama.
3- Majma'ul Bayan fi Tafsir al-Kur'an na Tabrisi, yayin tafsirin wannnan aya.
"Babu Jabru ba tafwidhu, sai dai al'amari ne tsakanin al'amurra biyu, watau mataki tsakanin matakai biyu".
Yayin da aka tambayi daya daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s), shin akwai wani mataki tsakanin tilasta-wa (jabru) da sajarwa (tafwidh)? Sai ya amsa da cewa:
"Abin da yake tsakaninsu ya kai fadin tsakanin sama da kasa".
Wannan shi ne takaitaccen bayanin tafarkin Ahlul-baiti (a.s) kan batun Jabru da Tafwidh, haka ne kuma akidar musulmin da suka yi koyi da tafarkinsu take.
Babu shakka makiya Musulunci sun san cewa Ahlul-baiti (a.s) su ne mabubbuga ta asali da tsarkakar addini mai kwaranye wa musulmi dukkan wahalhalu da bala'u. Su masu daraja ne a zukatan musulmi bai daya.
Kowa yana ganin girman alkadarinsu, yana tsarkake duk abin da ya fito daga gare su ko ya karkare zuwa gare su. Don haka ne masu neman rushe addini da shuka masa dasisa suke fuskantar wannan tushe na Musulunci domin su sami damar shuka barna alhali suna karkashin inuwar Ahlulbaiti (a.s). Suna daukar tutar Ahlulbaiti (a.s) da sunan goyon bayansu domin su sami damar kaidi da rushe akidar tauhidi, alhali Ahlulbaiti (a.s) sun barranta daga gare su da kuma tsine musu albarka. Wadannan irin jama'a sun kirkiri akidun bata da karkatacciyar falsafa mai cewa Allah Yana hululi (wato Ya shiga jikin wata halitta daga cikin halittunSa) cikin Imamai - Allah Ya daukaka ga barin hakan- da cewa Allah Ya sakar wa Imamai (a.s.) al'amurran arzurtawa da tasiri cikin halittar aljanna da wuta.
Ba su tsaya nan ba sai da sashinsu ya dangantawa Imamai (a.s.) allantaka. Duk hakan kuwa sun yi shi ne domin kaidi wa Musulunci da musulmi da rusa akidar tauhidi. Hakika masu wannan aiki sun sami asali ne daga kungiyoyi irin na Majusawa, Manawiyya da Mazdakawa wadanda suka shiga Musulunci a munafurce, ba tare da sun yi imani ba. Haka nan, akwai tunanin kiristoci da
Wadannan mabarnata sun bi wancan hanyar suka rudar da hankula da shuka rikici da kirkirar ruwayoyi da ra'ayoyi fandararru, suka danganta su ga Ahlulbaiti (a.s) bisa karya. Saboda haka manyan malami suka rubuta littattafai kan masu ruwaya wato Ilmul Rijal domin tona asirin makaryata da masu kirkira da masu munanan akida tun zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) har ya zuwa karshen jerin Imamai (a.s.), amintattun maruwaita daga Manzon Allah (s.a.w.a.). Ta hanyar ne suka jefar da duk wata ruwaya ta karya da kuma duk wani maruwaici mai kirkira ake gane shi, kamar yadda Najashi ya yi cikin sanannen littafinsa nan na Rijalul Najashi da Shaikh Dusi cikin littattafansa na Al-Fihrist da kuma Rijalul Dusi da dai sauransu.
Tarihi yana sanar mana samuwar wasu kungiyoyi fandararru wadanda suka danganta kansu da Ahlulbaiti (a.s) kamar 'yan Gullatu da 'yan Mufawwidha, alhali kuwa Ahlulbaiti (a.s) sun barranta da su, sun la'ane su da kuma koransu. Baya ga haka ma, malaman mazhabar Imamiyya (Shi'a) suna hukumta su da cewa su najasa ne.
____________
(*). Hakika rawar da wannan aiki na ruguzawa da wadannan batattun tunanunnuka na shafa wa Ahlulbaiti (a.s) kashin kaza suka taka, ba su takaita kawai gare su ba, face ma dai sun yi kokarin shigar da su ga sauran kungiyoyi da al'ummomin musulmi. A saboda haka ne ma malamai da masana na sauran mazhabobin musulmi suka yi iyakacin kokarinsu wajen kubuta daga gare su, amma duk da haka har ya zuwa yanzu muna ganin da yawa daga cikin irin wadannan dasisi da batattun akidoji cikin littattafan musulmi da abubuwan da suke dogaro da su.
"Amma batun sahabban Abul Khaddab Muhammad bn Abi Zainab al-Ajda al-Asadi da duk wanda yake da ra'ayi irin nasa, to lallai sun watse lokacin da suka ji cewa Imam Sadik (a.s.) ya la'anci Abul Khaddab, ya kuma barranta daga gare shi da sahabbansa".
Har zuwa inda yake cewa:
"Wata kungiya daga cikinsu ta ce Abu Abdullah Ja'afar bn Muhammad Sadik shi ne Allah - Allah Ya daukaka ga barin haka daukaka mai girma - sannan Abul Khaddab kuma Annabi ne mursali.
Wata kungiyar kuwa cewa ta yi: "Ja'afar bn Muhammad shi ne Allah - Wal iyazu billah- kuma Shi Allah (S.W.T.) wani haske ne mai shiga jikkunan wasiyyai ya kuma zauna a cikinsu. Wannan haske sai ya kasance shi ne Ja'afar bn Muhammad Sadik, sannan ya fita daga jikinsa ya shiga jikin Abul Khaddab(1) ".
Bayan al-Nawbakhti ya bijiro da wadannan batattun akidu sai ya ce:
"Wadannan kungiyoyin 'yan Gullatu masu da'awar Shi'a, sun sami asali ne daga addinan Kharmadaniyya(**)
____________
(*). Al-Nawbakhti: shi ne Abu Muhammad al-Hasan bn Musa al-Nawbakhti, yana daga cikin manyan malaman shi'a Imamiyya a karni na uku bayan hijira.
1- Firakhul Shi'a na al-Nawbakhti, shafi na 59.
(**). Kharmadaniyya: Kungiya ce wacce ta fito a karni na biyu bayan kashe Abi Muslim Khorasani da da'awar Jawidan bn Sahl, ta kasance daga cikin sauran kungiyoyin da suke Iran tun kafin Musulunci. Sun halalta dukkan abubuwan haramun da kuma halalta matayensu a tsakaninsu. Dubi al-Firakul Khurmadiniyya na Dr. Shahin Kamiran Mukaddam, shafi na 3.
Al-Nawbakhti ya kara da nakalto fandararrun kungiyoyin da suka riga suka mace, masu fakewa da jingina kansu ga Ahlulbaiti (a.s) kamar haka:
"Wata kungiya ta ce wai Muhammad bn Hanafiyya dan Imam Ali (a.s.) 'shi ne Mahdi, Imam Ali ya kira shi da Mahdi, bai mutu ba kuma ba zai mutu ba, wannan ba ya halatta, sai dai kawai shi ya faku ne, ba a kuma san inda yake ba. Zai dawo ya mallaki kasa, babu wani Imami bayan fakuwarsa har zuwa dawowarsa wajen sahabbansa, su ne kuma sahabban Ibn Karb(2) ".
____________
(*). Mazdakiyya: Su ne mabiyan Mazdak wanda ya bayyana a lokacin babban sarkin Farisawa Kubbad mahaifin Anushiran. Sunan littafin da ya yi ikirarin cewa an saukar masa da shi, shi ne Distaw. Maganganunsu yana kama da tsohon addinin Farisawan nan na Maniwiyya, wajen imani da tushen addininsu na Haske da Duhu. Mazdakawa sun halatta haramtattun abubuwa da kuma cewa mutane suna tarayya cikin dukiya da mata. Dubi karin bayanin da Sayyid Muhammad Sadik Bahrul Ulum yayi wa littafin Nawbakhti na Firakul Shi'a.
(**). Zindikai: Su ne masu kore dukka sha'anin addinin Ubangiji, masu ikirarin 'yancin tunani.
(*** ). Dahriyya: su ne masu cewa duniya tana nan tun fil azal, ba ta gushewa, kuma babu wani Mahalicci, suna daga cikin kungiyoyin kafirai da mulhidai.
1- Firakhul Shi'a na al-Nawbakhti, shafi na 60.
2- Kamar na sama, shafi na 44.
"Hamza bn Ammara al-Barbari cikinsu yake kuma shi mutumin Madina ne, sai ya rabu da su ya yi ikirarin cewa shi Annabi ne, shi kuma Muhammad bn Hanafiyya shi ne Allah - wal iyazu billahi -. Ya kuma ce shi ne Imam sannan kuma wasu abubuwa guda bakwai za su sauko masa daga sama, da su ne zai cinye dukkan kasa ya mallake ta. Ya kuma sami mutane daga Madina da Kufa da suka bi shi kan hakan. Imam Bakir (a.s.) ya tsine masa ya barranta daga gare shi, ya karyata shi, a sanadiyyar hakan ne kuma ya sa 'yan Shi'a suka barranta daga gare shi(1) ".
Haka nan ma Imam Sadik (a.s.) ya la'anci Sa'id al-Nahdi wanda wadannan fandararrun kungiyoyin nan suke bi. Imam din ya kira shi shaidan, wanda ya yi wa Imam karya(2) ".
Ga wasu ruwayoyin malaman Shi'a kan matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da wadannan 'yan Gullatu da kuma fandararrun ra'ayoyinsu. Misalin hakan shi ne abin da Imam din ya ce kan Abul Jarud da mabiyansa kamar yadda Ibnu Nadim ya nakalto cikin Alfihrist.
"Imam Sadik (a.s.) ya la'ance shi ya ce: 'shi makahon zuciya ne da idanu(3) '.
Kamar yadda kuma Imam din ya la'anci Abu Mansur al-Ajli, daya daga cikin 'yan Gullatu, an ruwaito cewa:
'Al-Kishshi ya kawo cikin Rijal dinsa shafi na 300 cewa Imam Sadik ya la'ance shi sau uku. Sannan kuma Yusuf bn Umar al-Thakafi, gwamnan Iraki, ya tsire shi a zamanin Hisham bn Abdul Malik(4) '.
Hakika Imam Sadik (a.s.) ya bayyana matsaya kan wadannan 'yan gullatu, daga nan ya ambaci wasu daga cikinsu, su ne:
____________
1- Firakhul Shi'a na al-Nawbakhti, shafi na 45.
2- Kamar na sama.
3- Alfehrist na al-Nadim, shafi na 227.
4- Almukalat wal firak na Sa'ad bn Abdullah al-Ash'ari , shafi na 47.
"Allah Ya la'ance su, mu dai ba mu rabuwa da makaryata msu yi mana karya ko kuma wani mai gurgun tunani. Allah Ya isar mana ga dukkan makaryaci, Ya kuma dandana musu zafin karfe(1) ".
A wani hadisin kuma Imam Sadik (a.s.) ya barranta daga 'yan Gullatu, inda yake cewa:
"Ya ku jama'ar Shi'a - shi'ar Alu Muhammadu- ku kasance matsakaita, wadanda suka wuce gona da iri (masu guluwi) su dawo gare ku, wadanda kuwa suka yi nawa su risko ku". Sai wani mai suna Sa'id ya ce: 'Allah Ya sanya ni fansarka! Wane ne mai guluwi? Sai Imam ya ce masa:"Wasu mutane ne masu fadi game da mu, abin da mu ba mu fada ba, wadannan ba su daga gare mu, mu ma ba mu daga gare su". Sai mutumin ya ce: 'To wane ne mai nawa? Sai ya amsa masa da cewa: "Shi ne mai bidar (gaskiya) yana nufin alheri, alherin zai same shi kuma za a sakanta masa da shi(2) ".
Daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa yayin da Imam din ya sami labarin cewa Abul Khaddab na wuce gona da iri sai idanunsa suka cika da hawaye yana cewa:
"Ya Ubangiji, na barranta ya zuwa gareKa, daga abin da Al-Ajda yake ikirari a kaina, gashina da fatar jikina sun ji tsoronKa. Ni bawa ne a gare Ka dan bawanKa, makaskanci mai tawali'u".Daga nan sai ya sunku'i da kai na dan lokaci kamar yana ganawa da wani abu, sai ya daga kansa yana cewa:"Haka yake, haka yake! Bawa mai tsoro, makaskanci gaba ga Ubangijinsa, kankani, mai tsananin tsoro. Wallahi ina da Ubangijin da nake
____________
1- Rijal al-Kishshi, shafi na 305.
2- Mishkatul Anwar fi Guraril Akhbar na Dabrisi, shafi na 66.
Sadir ya ce:
'Na ce da Abu Abdullah (a.s.) cewa wasu mutane suna ikirarin cewa ku alloli ne, suna kuma kafa hujja da fadar Allah (S.W.T.) cewa:"Kuma Shi ne Wanda ke abin bautawa a sama, kuma bautawa a kasa"", (Surar Zukhruf aya ta 84),sai ya ce:"Ya kai Sadir! (Ka sani) jina da ganina da fatata da namana da gashina duk sun barranta daga wadannan mutane, Allah ma Ya barranta da ga gare su. Ba kan addinina wadannan suke ba, ba kuma kan na iyayena ba. Na rantse da Allah ba zai tara ni da su ba ranar lahira, kuma ba su zo a wannan rana ba face Allah Na fushi da su(2) ".
Kamar yadda suka yi wa Imam Bakir da Sadik (a.s.) karairayi kuma suka barranta daga gare su, haka nan ma suka yi wa Imam Musa Kazim (a.s.) bayan shahadarsa. Suka ce bai mutu ba, sai dai kawai an daukake shi ne kamar yadda aka daukaki Annabi Isa (a.s.) kuma nan gaba zai dawo. Imam Ridha (a.s.) dan Imam Kazim (a.s.) sai ya barranta daga gare su, ya kuma la'ance su.
Kamar yadda Imam Sadik (a.s.) ya ce ba za a rabu da masu yi wa Ahlulbaiti (a.s) karya ba, domin su rikita tafarkinsu, domin kaidi ga Musulunci, haka nan Ahlulbaiti (a.s) suka bayyana matsayinsu dangane da wadannan masu niyyar ruguza Musulunci.
Yana daga ni'imomin Allah ga Musulunci da musulmi cewa wadannan kungiyoyi sun gushe, ba bu
____________
1- Biharul Anwar na Allama Majlisi, juzu'i na 47, shafi na 378.
2- Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, shafi na 269.
A daya gefen kuma, duk masu bincike suna iya ganin abubuwan da ake danganta su da sauran mazhabobin musulmi na akida, kamar su jabru da cewa Allah jiki ne kuma Yana zama a bisa kujera da cewa fadin kujerarSa taki bakwai ne, da cewa Allah zai shigar da kafarSa cikin wuta a ranar lahira sai Ya bice zafinta, da cewa Shi Yana saukowa nan duniya bisa wani farin jaki da dai sauransu.
Hakika a sarari yake cewa duk wadannan zantuttuka, kamar tatsuniyoyin Gulatu, suna warware akidar tauhidi, addinin Musulunci kuwa yana barranta daga gare su.
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ce:
"Ni ina kin a ce mutum ya mutu alhali akwai wata ta'adar Manzon Allah (s.a.w.a.) da ta rage bai aikata ba(1) ".
Babu shakka Ahlulbaiti (a.s) sun ba da muhimmanci kwarai wajen ilmantarwa da tarbiyyar mabiya da sahab-bansu da kuma shiryar da su zuwa hanya sahihiya ta tabbatar da rayuwa irin ta mai akida da halayen kwarai da biyayya ga hukumce-hukumcen Musulunci. Sun karfafa kan gina tarbiyyar musulmi bisa dacewa da Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) domin samar da gwarzaye masu daukar hasken Musulunci da kira zuwa gare shi ta yadda hasken zai watsu kan sauran jama'a su amfana da ilmi da kuma aiki. Ahlulbaiti (a.s) sun yi hakan ne saboda tabbatar da haraka ta Musulunci cikin al'ummar duniya bayan da muggan manufofin masu neman ruguza addini suka bayyana ko ina. Muna iya ganin wannan kokarin nasu a fili cikin halayensu da wasiyyoyinsu da tarbiyyarsu ga mabiyansu. Daga cikin maganganun Imam Bakir (a.s.) akwai raddi kan masu cewa duk wanda ya kaunaci Ahlulbaiti (a.s) ba ya bukatar lizimtar farilloli Musulunci. Imam ya bayyana musu tafarkin Musulunci na gaskiya wanda Ahlulbaiti (a.s) suke kai, kuma suke kaunar dukkan musulmi ya yi riko da shi. Idan ba ka san shi ba, to shi ne tafarkin ilmi da akida ta gaskiya da aiki da duk abin da Alkur'ani ya zo da shi, Annabi (s.a.w.a) kuma ya iyar da shi ya kuma
____________
1- Makarimul Akhlak na Tabrisi, shafi na 39.
"Wallahi ba mu da wata kubuta daga Allah, babu wata dangantaka tsakaninmu da Allah, ba mu da wata hujja a kan Allah, kuma ba a kusantar Allah sai da biyayya. Wanda ya zama mai biyayya daga cikinku to jibintarmu za ta amfane shi, wanda kuwa yake mai sabo daga cikinku, jibintarmu ba za ta amfane shi ba(1) ".
Amru bn Sa'id bn Hilal ya ce da Abu Ja'afar (a.s.): 'Allah Ya sanya ni fansar ka! Ni da kyar nake saduwa da kai, sai dai bayan shekaru, to ka yi mini wasicci da wani abin da zan rika', sai ya ce masa:"Ina maka wasicci da tsoron Allah da tsantsaini da kokari, ka sani cewa tsantseni ba ya amfani sai tare da kokari(2) ".
Daga cikin abin da Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci da shi ga wani mabiyinsa, Abu Usama ya kuma umurce shi da ya isar da shi ga sauran mabiyansa, shi ne cewa:
"Ku ji tsoron Allah ku kasance ado a gare mu, kada ku zamo abin kyama. Ku janyo mana dukkan soyayya, ku ije mana duk wani mugun abu, domin mu ba kamar yadda aka fada dangane da mu muke ba. Muna da hakki cikin Littafin Allah da dangantaka da Manzon Allah (s.a.w.a.) da tsarkakewa daga Allah, da haifayya tsarkakakkiya, ba mai ikirarin hakan, koma bayanmu, face makaryaci*. Ku yawaita ambaton Allah da tuna mutuwa da karatun Alkur'ani da salatin Annabi (s.a.w.a) domin akwai (ladan) kyawawan aiki goma ga ko wane salati a gare shi(3) ".
Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci wa Isma'il bn Ammar, daya daga cikin sahabbansa, da cewa:
____________
1- Makarimul Akhlak na Tabrisi, shafi na 67.
2- Kamar na sama, shafi na 66
3- Kamar na sama.
(* ). A nan Imam yana nuni da darajar dangantaka da Manzon Allah (s.a.w.a.) da suka samu ta hanyar mahaifiyarsu Nana Fadima (a.s.).
Hisham bn Salim ya ce: 'Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana fada wa Hamran cewa:
"Ka dubi wanda ya kasa ka, kada ka dubi wanda ya fi ka, domin haka ya fi (tabbatar da) wadar zuci ga abin da aka yanka maka, kuma za ka fi cancantar kari daga Allah. Ka sani cewa kadan na dawwamammen aiki wanda aka yi yakini, a wajen Allah, ya fi mai yawa dawwamamme amma babu yakini a cikinsa. Ka sani cewa babu tsantsenin da ya fi nisantar ababen da Allah Ya haramta, da kuma kamewa ga barin cutar da musulmai da yi da su. Babu kuma abin da ya fi kyan hali faranta rai. Kuma babu dukiyar da tafi amfani daga wadatuwa da kadan mai biyan bukata. Babu jahilcin da ya fi jiji da kai daci(2) ".
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.) kan siffofin muminai cewa:
"Wanda ya yi bakin cikin mummunan aikinsa, ya yi farin ciki da kyakkyawan aikinsa, to mumini ne(3) ".
Wadannan bayanai suna nuna siffar mumini mai riko da addini irin wanda Ahlulbaiti (a.s) suka yi kokarin samarwa kuma wannan shi ne tafarkinsu na tarbiyyar al'ummar musulmi. Shi ne kuma kiran da suka yi wa al'ummar Annabi (s.a.w.a) na lizimtar Littafin Allah da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.) da gina rayuwa bisa wannan shiriya da tafarki mai karfi. Babu abin da ya fi dacewa ga musulmi sai bin shiryarwarsu da wasiccinsu da kuma wa'azinsu.
____________
1- Makarimul Akhlak na Tabrisi, shafi na 66.
2- Biharul Anwar na Allama Majlisi, juzu'i na 78, shafi na 198, da kuma Furu'ul Kafi na Kulayni, juzu'i na 8, shafi na 244.
3- Makarimul Akhlak na Dabrisi, shafi na 77.
Babu shakka al'ummar musulmi ta san matsayin Ahlulbaiti (a.s) da hakkinsu a kan wannan al'umma na shugabantarta. Domin haka ne za a iya ganin cewa Ahlulbaiti (a.s) suna matakin kololuwa a fagen siyasa da shugabancin Musulunci, domin su shiryar da al'umma, su tabbatar da gyara da aiwatar da hukumce-hukumcen addini da tsayar da adalci.
Duk wanda ya karanci tarihin Musulunci zai gani a sarari cewa shugabantar al'umma bayan zamanin Khulafa'u al-Rashiduna ta koma mulukiyya mai dora kanta bisa bayin Allah da jan hankulansu da dukiya da mukamai da kuma dankwafe hukumce-hukumcen shari'a da wasa da su. Wannan wasa da shari'a da makomar al'umma ya janyo sassabawa da juyin-juya-hali da jayayya mai tsanani da zubar da jinin kungiyoyi masu sabanin ra'ayoyi da tunace-tunace masu warware juna sun zama sakamakon wannan. Wasunsu suna goya wa sarakuna baya kan zaluncinsu da kuma horar da mutane su mika wuya da hana su bijirewa da warware mubaya'arsu ga azzalumai. Wasu kuma sun yi amfani da wannan damar (ta jayayya tsakanin musulmi) wajen tabbatar da mugun nufinsu na ruguza addini yayin da suka dora kira da halalta dukkan haram da dukiyoyi da mata da rusa wajibai, kungiyoyi irinsu 'yan Karamida, Mazdakiyya da Kharmiyya da dai sauransu. Wasu kuma suka dora kira zuwa ga rudani da rusa dukiyar hukuma da zubar da jini da kafirta kowa da kowa kamar su
Da wannan fantsamar ra'ayoyin siyasa masu sassabawa da fitinu da yake-yake na cikin gida, al'umma ta fuskanci hadari mai munin gaske. Ahlulbaiti (a.s), a matsayinsu na jagororin al'umma, sun kasance mafus-kanta da tushen sakon Musulunci wanda duk wata mishkila ta akida da tunani wacce ta kalubalanci musulmi ana iya warware ta a hannunsu. Domin wannan matsayi nasu na matabbacin tafarkin gaskiya, musulmi suna bin ra'ayinsu da riko da matsayin da suka dauka kan al'amurra. Face wadanda suka damfaru da masu iko, masu kare ayyukansu domin biyan bukatar kansa.
A nan za mu yi dubi cikin tafarkin Ahlulbaiti (a.s) akan abubuwan da suka shafi ayyukan siyasa.
Duk wanda ya bibiyo salon siyasar Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmayarsu ta bayyane da ta boye a tsawon karno-ni biyu da rabi zai iya gano cewa aikin da suka yi na siyasa yana bisa ginshikai kamar haka:
(1). Tarbiyyantar da al'umma kan kin zalunci da tabbatar da manufar adalci da bayyana fikirar imamanci da siyasa da fayyace rukunan hukumci da shugabanci cikin addinin Musulunci. Sun yi haka ne domin karfafa fahimtar siyasa ga al'umma da karfafa kulawarta da kiyayyarta ga azzalumai, da farkar da ita daga barci. Wanda ya yi bitar abin da Ahlulbaiti (a.s) suka ruwaito suka watsa daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da wannan al'amari, zai gane muhimmancin wannan mataki wajen farfado da ruhin siyasa da kiyayewa ta Musulunci. A nan za mu ambaci wasu daga cikin ruwayoyin da suke magana dangane da shugabanci da kuma nauyin da suka hau kan shugaba musulmi, da kuma kyamar da Musulun-ci yake wa zalunci da kuma kira zuwa ga adalci, don mu fahimci fikira da tunanin Ahlulbaiti (a.s) wajen fada da zalunci da kuma kwadaitar da al'umma zuwa ga canji da kuma motsi na siyasa.
An ruwaito daga Imam Muhammad Bakir (a.s.) cewa wani dattijo daga kabilar Nakh'a ya ce:
"Na ce wa Abu Ja'afar (a.s.) cewa: Ni na kasance gwamna ne tun zamanin Hajjaj har yau din nan, shin za a karbi tuba ta? Sai na yi shiru, sannan na sake maimaita wannan tambayar, sai yace min: "A a; har sai ka mai da
Abu Hamza al-Thumali ya ruwaito daga Imam Abu Ja'afar al-Bakir (a.s.) cewa:
"Yayin da Aliyu bn Husaini (a.s.) ya zo cikawa sai ya rungume ni ya zuwa kirginsa sannan ya ce: "Ya dana, ina maka wasicci da abin da babana (a.s.) ya mini wasicci yayin da cikawa ta zo masa, kuma da abin da ya ambata cewa babansa ya yi masa wasicci. Ya ce: Ya dana, na hane ka zaluntar wanda ba shi da mai taimako kanka sai Allah(2) ".
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Babu zaluncin da yafi zaluncin da wanda aka zaluntan ba shi da mai taimakonsa a kan shi sai Allah Mai Girma da Daukaka(3) ".
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ku tsoraci zalunci domin shi duhu ne a ranar lahira(4) ".
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Allah Mai Girma da Daukaka Ya yi wasicci ga wani Annabi da cikin Annabawansa wanda yake cikin masarautar wani jabbarin sarki cewa: 'Ka je wajen wannan azzalumin ka ce da shi; Ni ban shugabantar da kai domin zubar da jini da tara dukiya ba, sai dai kawai na shugabantar da kai ne domin ka raba Ni da sautin (karar) wadanda aka zalunta. Domin Ni ba zan bar zaluncin da aka yi masu ba ko da kafirai ne(5) ".
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Da wanda ya aikata zalunci da mai taimakonsa da kuma wanda ya yarda da shi, to dukkansu ukun masu tarayya ne (cikin zaluncin)(6) ".
Imam Sadik (a.s.) din dai ya ce:
"Duk wanda ya yi uzuri wa zaluncin azzalumi, Allah
____________
1- Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 2, babin zalunci.
2- Kamar na sama.
3- Kamar na sama.
4- Kamar na sama.
5- Kamar na sama.
6- Kamar na sama.
Abu Basir ya ruwaito cewa: "Mutane biyu sun zo wajen Imam Sadik (a.s.) a kan wani lamari na mu'amala tsakaninsu. Yayin da Imam (a.s.) ya ji zancen kowannensu, sai ya ce: "Hakika wanda ya cimma bukatarsa da zalunci bai cimma kome ba. Lallai za a biya wanda aka zalunta da addinin azzalumin fiye da abin da shi ya dauka daga dukiyar wanda aka zalunta", daga nan sai ya ce: "Duk wanda yake aikata wa mutane sharri kada ya yi kyama idan aka yi masa. Hakika babu abin da dan Adam zai girba face abin da ya shuka. Babu wanda zai girbi abu mai dadi baicin ya shuka mai daci, babu kuma wanda zai girbi mai daci baicin ya shuka mai dadi". Sai mutane biyun nan suka yi sulhu kafin ma su tashi daga gare shi(2) ".
A'imman Ahlulbaiti (a.s) sun ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Duk wanda ya tafi tare da azzalumi domin ya taimake shi, alhalin ya san cewa shi azzalumi ne, to, hakika ya fice daga Musulunci(3) ".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Adalci na sa'a guda ya fi ibadar shekaru saba'in na sallar dararensu da azumtar yininsu. Zalunci a hukumci na sa'a guda kuma ya fi tsanani da girma wajen Allah a kan sabon shekara sittin(4) ".
Jabir bn Abdullah al-Ansari (r.a.) ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Wanda ya nemi yardar wani sarki da abin da yake fusata Allah, to ya fita daga addinin Allah(5) ".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Wanda ya shugabanci mutum goma sannan bai yi
____________
1- Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 2, babin zalunci.
2- Kamar na sama.
3- Mishkatul Anwar na Dabrisi, fasalin Zalunci, shafi na 315.
4- Kamar na sama, shafi na 316.
5- Kamar na sama, shafi na 318.
Imam Ali (a.s) ya ce:
"Duk mutumin da ya shugabanci wani al'amari na musulmi, sannan ya rufe kofa (ya ki sauraronsu) to yana cikin azabar Allah Mai Girma da Daukaka da la'anarSa har sai ya bude kofarsa ga mai wata bukata da mai (karar) wani zalunci, sun shigo(2) ".
Kamar haka A'imma (a.s.) suke tarbiyyar mabiyansu da karkato da ra'ayin jama'a zuwa ga canji da gyara da shiga fagen siyasa ta hanyarta ta asali.
(2). Yankewa daga Azzalumai: Bayan shiryarwa da tarbiyya kan munin zalunci, Ahlulbaiti (a.s) sun kara da umurni da yanke hulda da azzalumai, kamar yadda ya zo cikin hadisi cewa:
"Duk wanda ya yi tafiya tare da azzalumai, alhali yana sane da cewa azzaluman ne, to hakika ya fice daga Musulunci" da kuma cewa: "Mai aikata zalunci da mai taimaka masa da mai yarda da shi dukkansu masu tarayya da juna ne".
Haka nan suke kira da yanke hulda da azzalumai da rashin taimaka masu. An ruwaito cikin hadisi cewa:
"Idan ranar alkiyama ta zo mai kira zai yi kira: Ina azzalumai da mataimakansu; wanda ya shirya masu kurtun tawada ko ya daure musu wata jaka ko ya fere musu kan alkalami, ku tara su tare da azzalumai(3) ".
Kyakkyawan misalin yankewa azzalumai shi ne abin da A'imma (a.s.) suka yi da matakan da suka dauka dangane da zalunci da azzaluman mahukuntan Umayya-
____________
1- Mishkatul Anwar na Dabrisi, fasalin Zalunci, shafi na 316.
2- Kamar na sama.
3- Biharul Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 75, shafi na 372.
A wannan lokacin A'imma (a.s.) sun gamu da wahalhalu daban-daban daga mahukunta, kamar cutarwa da kora da sa ido da shiga kurkuku da matsi da tsoratarwa, za mu kawo kadan daga cikin irin wadannan abubuwa a cikin wannan littafi.
A matsayin misali na irin wannan yankewa, shi ne matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da halifan Abbasiyawa Abu Ja'afar Mansur wanda ya shahara da mugun hali da zubar da jini da zalunci ga zuriyar Imam Ali (a.s.). Malaman tarihi sun rubuta cewa, wata rana Mansur ya rubuta wasika zuwa ga Imam Sadik (a.s.) yana neman zama da shi don kokarin sanya shi cikin malaman hukuma. Sai Imam yaki duk kuwa da halin tsoratarwa da kaushin halin da mahukuntan suke nunawa.
Ga abin da Mansur ya rubuta:
"Me zai hana ka ziyarce mu kamar yadda mutane suke ziyartarmu"?, sai Imam (a.s.) ya rubuta masa cewa:
"Babu abin da muke tsoronka dominsa, babu wani abu daga sha'anin lahira a gare ka wanda zai sa mu kaunaci (saduwa da) kai dominsa. Ba ka kuma cikin wata
____________
(*) . Hakika Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) ya yanke wa sarakunan da suka yi zamani da shi face dai sai saboda wani yanayi na musamman da ya sa shi ya karbi wazircin Ma'amun a bisa wasu sharudda da Imam din ya kafa masa.
(**) . Amma Imam Jawad (a.s.) rayuwarsa ba ta yi tsayi ba, duk da cewa kuma Ma'amun ya aurar masa da 'yarsa don samun goyon bayan mabiya Ahlulbaiti (a.s), to amma duk da hakan bai taimaka wa Ma'amun cikin komai ba haka nan kuma bai hada hulda da shi ba.
Haka nan dai matsayar A'imma (a.s.) da raddinsu ya kasance ga mahukuntan da ba sa tsai da shari'a, ba su lizimtar ginshikanta.
To haka nan ma malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bi tafarkin Imamansu wajen yanke hulda da azzaluman mahukunta ta hanyar fatawoyinsu masu haramta taimakawa azzalumai ko karbar aikin hukumominsu. Suna kawo wannan ne galibi a babin makasib wato hanyoyin neman abin masarufi. Bari mu kawo maganar Shahid Muhammad bn Jamal(*) Makki al-Amuli wanda aka fi sani da Shahidul Awwal (Allah Ya rahamshe shi) yayin da yake kawo sana'oi haramtattu cewa: "Da taimakon azzalumai cikin zalunci" (yana daga cikin haramtattun sana'oi), shi kuma mai sharhin littafin ya ce: "Kamar yi musu rubutu da kawo musu wanda suke zaluntarsa da dai makamantansu(2) ".
Malaman sun hana karbar duk wani aiki a hukumar azzalumai sai dai da nufin yi wa Musulunci hidima da tunkude zalunci ga barin bayin Allah, ta yadda dai za a samu wani gyara ko wani amfani ga al'umma.
(3). Gwargwarmaya da abin da ya shafi amfani da karfi: Wajibcin umurni da aiki mai kyau da hana mummuna wani ginshiki ne wanda ya tabbatar da gwagwarmaya domin kawar da zalunci, kuma an lizimta
____________
1- Imam Sadik (a.s) na Mahmud Abu Zuhra, shafi na 139.
(*). Yana daga cikin manyan malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) , ya rayu ne tsakanin shekara ta 734 - 786 bayan hijira.
2- Rawdhatul Bahiya fi sharhil Lum'at al-Damashkiyya lil Shahidil Awwal na Shahidus Thani, juzu'i na 3, shafi na 213.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Shugaban shahidai shi ne Hamza da kuma mutumin da ya mike ya umarci sarki azzalumi (da kyakkyawan aiki) ya hana shi (mummuna) sannan sarki ya kashe shi".
Duk wanda ya bibiyi tsarin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da sabawa zaluncin da suka yi, zai ga cewa hanya ce guda wajen sabawa zalunci da kira zuwa ga gyara da gwagwarmaya. Gwagwarmaya ta faro ne a zamanin mulkin Mu'awiyyah dan Abu Sufyan, yayin da ya dora dansa Yazid a kan wuyar al'ummar musulmi duk da cewa bai cancanci shugabanci ba kuma ya rasa dukkan sharuddansa. Wannan ta'asa ta janyo fasadi da kaucewar al'umma, abin da ya sanya Imam Husaini (a.s.) yin shelar jihadi. Imam (a.s.) ya zauna a Makka na tsawon wata hudu bayan barowarsa birnin Madina, daga bisani sai ya fuskanci kasar Iraki. Can a Karbala ne aka yi gumurzu tsakanin rundunar Yazid da jama'ar Imam Husaini (a.s.) 'yan kalilan, a can tsarkakken jini ya zuba, Imam (a.s.) ya yi shahada. Zubar da jinin Imam Husaini (a.s.) tare da Ahlulbaitinsa da kuma mabiyansa ya girgiza al'umma ya tashe ta daga barcin da take ciki. Wannan kuwa shi ne farkon tawaye wa azzaluman mahukunta masu fakewa da Musulunci don cimma burinsu da warware mubaya'ar jabu da shelar kawar da hukumcin bata-gari mai sabawa rukunan Musulunci. Wannan tawaye wa azzalumai shi ya yaye zanin malaman da suke kiran mutane zuwa kaskanci da mika kai bori ya hau, da gurbata ra'ayin ilahirin jama'a da karfafa cewa sai an lizimci mubaya'ar azzalumi an cika masa alkawari komin lalacewarsa. Wadannan muggan malamai dangin Bal'ama dan Ba'ura sun yi kunnen uwar shegu da fadar Manzon Allah (s.a.w.a.) ce wa:
Da kuma fadinsa (s.a.w.a) cewa:
"Babu biyayya ga halitta cikin sabon Mahalicci".
Suna yin biris da fadin Allah Ta'ala cewa:
"Kuma kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku". (Surar Hud, 11:113)
Shi Shugaban shahidai, Imam Husaini bn Ali (a.s.) ya kaddamar da gwagwarmayarsa ne a shekara ta sittin da daya bayan hijira, kuma a wannan shekarar ne ya yi shahada a can yankin Karbala na kasar Iraki. Da wannan ne kuma ya rushe dukkan kiraye-kirayen muggan malamai na rauni gaban hukumomin zalunci da yarda da su. Hakika sautin shahada da jini ya rinjayi na kwadayi da kaskanci.
Imam Husaini (a.s.) ya bayyana wa mutane dalilan fitowarsa da tsarin da yake tafe bisansa da cewa:
"Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana(1) ".
Sannan ya ayyana wa mutane siffofin shugaba wanda shi ne ja-gora mai jan ragamar musulmi, da wajibcin tsayuwa don gwagwarmayar sauya mai hukumci a yayin da ya karkace ya bar wadannan ginshikin. Ga abin da Imam Husaini (a.s.) ya rubuta wa mutanen Kufa:
"Ina rantsuwa da cewa ba wani ne shugaba ba face mai hukumcin da ya tsayar da adalci, mai riko da addinin gaskiya, mai tsare kansa bisa (umurnin) Zatin Allah(2) ".
Daga cikin abin da ya rubuta wa manyan mutanen
____________
1- Maktal al-Husain na Khawarizmi, juzu'i na 1, shafi 88.
2- Kitabul Irshad na Shiekh Mufid, shafi na 204.
"Ni ina kiranku zuwa ga Littafin Allah da Sunnar AnnabiSa (s.a.w.a), domin an riga an kashe sunna an raya bidi'a. To idan kun saurari fadina kuka bi umurnina zan shiryar da ku tafarkin shiriya. Aminci ya tabbata a gare ku da rahamar Allah(1) ".
Hakan nan Imam Husaini (a.s.) ya tabbatar wa al'umma yadda shari'a ta yi umarni da sabawa azzalumin shugaba, ya kuma yi shelar rukunan jihadi mai tsarki, domin sauya hukumcin azzalumai.
Bayan jihadin Imam Husaini (a.s.) mai albarka, Ahlulbaiti (a.s) sun taimaka wa yunkuri daban-daban da Alawiyyawa suka yi tsawon sama da karni biyu, a fadin kasashen musulmi.
Zaid bn Ali bn Husaini, wato dan Imam Zainul Abidin kuma jikan Imam Husaini (a.s.) ya yi yunkuri a shekara ta 121 bayan hijira. Wannan kuwa ya faru ne a zamanin Imam Sadik (a.s.) wanda kuwa ya goyi bayansa ya kuma yi juyayin shahadar Zaid(*).
Fudhail Rassan ya ce:
"Na shigo wajen Abu Abdullah (a.s.) bayan an kashe Zaid bn Ali, sai aka shigar da ni cikin uwar daki, sai ya ce da ni: "Ya kai Fudhail, an kashe baffana? Sai na ce 'fansar ka nake (e an yi haka), sai ya ce:"Allah Ya jikansa, lallai shi ya kasance mumini mai sani, mai ilmi, mai yawan gaskiya. Lallai da ya yi nasara da ya cika alkawari. Lallai da ya sami mulki da ya san inda zai sanya shi(2) ".
____________
1- Maktal al-Husain na Abdurrazak al-Mukarram, shafi na 141- 142.
(*). Yana da kyau mu ambaci cewa Abu Hanifa, shugaban mazhabar hannafiyya, ya taimaka wa yunkurin Zaid kuma ya yi fatawar a ba shi zakka, domin wannan yunkuri nasa.
2- Biharul Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 47, shafi na 325, daga littafin Rijal al-Kishshi.
Daya daga cikin bayyanannen misalin irin wannan mataki na siyasa kuwa, shi ne matakin da Imam Kazim (a.s.) ya nuna dangane da yunkurin da Husaini bn Ali ya yi a shekara ta 169 a birnin Madina, yunkurin da aka fi sani da Yunkurin Fakh(*) wanda aka yi shi a watan Zulkida na wannan shekarar.
Duk da cewa Imam Kazim (a.s.) ya ga alamun rashin nasarar yunkurin a wancan lokacin, babu shakka magan-ganun da ya yi sun nuna cewa yana goyon bayan ra'ayin jihadi. Ga abin da ya fadi wa shi Husainin yayin da ya ga yayi niyyar fita wannan arangama:
"Za a kashe ka, saboda haka ka tsananta yaki domin mutanen fasikai ne, suna bayyana imani suna boye munafunci da shirka. Lalle ne mu daga Allah muke kuma wajenSa za mu koma! Ga Allah nake neman ladan rashinku(1) ".
Yayin da Husain ya yi shahada aka kawo kawukan wadanda suka yi shahada tare da shi wajen mahukuntan Abbasiyawa, sai aka tambayi Imam Kazim cewa wannan kan Husaini ne? sai ya ce:
"E, lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne mu zuwa gare Shi za mu koma. Na rantse da Allah, ya mutu musulmi ne salihi, mai yawan azumi, mai umurni da
____________
(*). Shi dai wannan yunkuri an yi shi karkashin jagorancin Husain bn Ali bn Hasan bn Hasan bn Imam Hasan bn Imam Ali bn Abi Talib, kuma an yi don fuskantar halifan Abbasiyawa Al-Hadi a Madina, bayan da shi Husain din ya dauki alkawari a kabarin Kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.). A yayin wannan yunkurin, Husain ya yi shahada a hannun Abbasiyawan a kusa da garin Makka. Hakika ana daukan wannan yunkuri na Fakh a matsayin bala'i na biyu da ya fada wa Ahlulbaiti bayan waki'ar Karbala.
1- Makatilul Talibiyyin na Abul Faraj, shafi na 447.
Shi dai Husain ya kasance ne yana kiran mutane da cewa:
"Ina kiranku ne zuwa ga abin da Alu Muhammadu suka yarda da shi, da aiki da Littafin Allah da sunnar Annabi (s.a.w.a) a tsakaninku, da kuma tsayar da adalci a tsakanin jama'a(2) ".
Kiran da Husain ya yi, kira ne zuwa ga biyayya ga mutumin da ya cancanci shugabanci, wanda yake daga Alu Muhammadu, kuma shi ne Imam Kazim (a.s.), kamar yadda Zaid ya yi nufin mai da shugabanci ga Imam Sadik (a.s.) da ya yi nasara.
Hakika halifan Abbasiyawa ya fahimci goyon bayan da Imam Kazim (a.s.) yake yi wa yunkurin Husain a yakin Fakh.
Allamah Majilisi ya ruwaito cewa:
"Sai ya (halifan Abbasiyawa) ci gaba da zagin Dalibiyawa (jikokin Ali bn Abi Talib) har ya ambaci Musa bn Ja'afar (a.s.), sai ya zage shi yana cewa: 'Wallahi Husaini bai yunkura ba sai da umarninsa (Musa bn Ja'afar), ba abin da ya bi face abin da yake so domin shi (Imam Kazim) ne ma'abucin wasiyya a cikin mutanen wannan gidan. Idan na bar shi, Allah Ya kashe ni(2) ".
Imam Jawad, jikan Imam Kazim (a.s.) shi ma ya bayyana tasa matsayar dangane da masu gwagwarmar, inda ya ce:
"Bayan Dif (Karbala), ba a cutar da mu kamar cutarwar Fakh ba(4) ".
Akwai misalai masu yawa na yunkuri da goyon bayan Ahlulbaiti (a.s) gare su, har wannan (yunkurin) ya zama tafarki da salo na aikin siyasa wanda yake da
____________
1- Makatilul Talibiyyin na Abul Faraj, shafi na 445.
2- Kamar na sama, shafi na 450.
3- Bihar al-Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 48, shafi na 151
4- Kamar na sama, shafi na 165.
(4). Gwagwarmaya ta Siyasa: Wannan yana da muhimmancin gaske a rayuwar siyasar al'umma a duk lokacin da azzalumin shugaba ya bayyana ba ya gudanar da hukumce-hukumcen Allah Ta'ala, ba ya kuma tsaifa adalci a tsakanin mutane. Kowane Imami na Ahlulbaiti (a.s) ya shugabanci al'umma a fagen siyasa a zamaninsa, kuma ya kasance shi ne alamar bijirewa azzalumai a zukatan jama'ar musulmi. Wannan kuwa shi ne ya bai wa yunkure-yunkuren da aka yi siffar dacewa da shari'a. Halifofin Banu Umayya da Banu Abbas wadanda tarihi ya yi wa shaidar rashin lizimtar addini da barin adalci sun san irin kimar Ahlulbaiti (a.s) a zukatan musulmi, saboda haka suka bi hanyoyi daban-daban domin su nisantar da kaunar Ahlulbaiti (a.s) daga mutane, hanyoyi kamar su tsoratarwa da kai su kurkuku da kisa da rashawa da mukamai da sauransu.
A matsayin misali, Mu'awiyya ya yi tawaye ga Imam Ali (a.s.) ya yake shi duk da cewa shi ne halaltaccen halifa.
Baya ga haka kuma, bai tsaya ba sai da ya yaki Imam Hasan (a.s.) ya yi tawaye wa halifancinsa, ya kashe shi da guba a shekara ta hamsin, bayan hijira.
Yazid dan Mu'awiyya, shi ma ya dauki mataki irin na ubansa akan Imam Husain (a.s.), ya kashe shi tare da mutanen gidansa, ya ribaci zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a.) yayin da Imam Husaini (a.s.) ya jagoranci yunkurin bijirewa hukumar Banu Umayya ta zalunci da aka tilasta ta a kan al'umman musulmi.
Bayan Imam Husaini (a.s.) ya yi shahada, musulmi sun karkata hankalinsu ga Imam Ali bn Husain, Zainul Abidin (a.s.), suna ganinsa a matsayin wata alama kana kuma makoma gare su, don haka ne masu yunkuri
Imam Bakir (a.s.) dan Imam Zainul Abidin (a.s.) shi ma ya nuna matsayin da yake kai na bijirewar siyasa daga Banu Umayya. Imam ya sha wahala kwarai a hannunsu, musamman ma Hisham bn Abdul Malik mai bayyana kiyayya da gaba ga Alawiyyawa. A zamaninsa ne Zaid bn Ali dan uwan Imam Bakir (a.s.) ya fito jihadi.
Shi dai wannan halifa na Banu Umayya ya tabbatar cewa tushen wannan yunkuri na Zaid daga Imam Bakir da dansa Ja'afar Sadik (a.s.) yake. Don haka sai ya kira su daga Madina zuwa ga helkwatarsa da ke Sham, yayin da Imam Bakir (a.s.) ya shiga fadar Hisham sai ya yi sallama yana nuni zuwa ga mahalarta majalisar, amma
____________
(*) An tara wadannan adduo'i na Imam Zainul Abidin a cikin wani littafi da ake kira Sahifatus Sajjadiyya.
"Ya Muhammad bn Ali, ko yaushe sai an sami wani mutum daga cikinku yana raba kan musulmi, da kiran jama'a don su bi shi, domin wauta da karancin ilmi".
Sai Hisham ya ci gaba da suka, jama'ar da ke fada su ma suka fara sukar Imam din bayan Hisham ya yi shiru. Da ganin wannan ka san cewa an umurce su da hakan ne kafin ma Imam din ya shigo tare da dansa, Imam Sadik (a.s.). Ganin haka ke da wuya, sai Imam Bakir (a.s.) ya mike tsakiyar majalisar yana mai raddi ga sarki da cewa:
"Ya ku mutane! Ina kuke zuwa ne? Ina aka nufa da ku ne? Da mu Allah Ya shiryar da farkonku, da mu kuma Zai cika (shiryar) da na karshenku. Idan kuna da mulki abin gaggautarwa, to mu muna da mulki da aka jikirta, kuma babu wani mulki bayan namu, domin mu ne masu mulkin karshe".
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
"Kuma kyakkyawan karshe tana tabbata ga masu tsoron Allah". (Surar A'araf, 7: 128)
Jin haka, ya sa Hisham ya tsare shi(1) .
To a cikin kurkukun ma Imam Bakir (a.s.) bai yi shiru ba, ya wayar da kan fursunoni kan batutuwan siyasa da jihadi har fursunonin suka sami tasirin wa'azinsa, inda suka tayar da hargowa a cikin kurkukun. Ganin haka, sai shugaban kurkukun ya isar da lamarin zuwa ga Hisham, inda shi kuma ya yi umarni da a fitar da Imam (a.s.) daga kurkukun a mai da shi birnin Madina, a hannun wani dan aiken sarki(2) .
Muhammad bn Jarir Tabari ya rubuta cewa dalilin da
____________
1- Al-Manakib na Ibn Shahru Ashub, juzu'i na 4, mas'alar mai da Imam Bakir (a.s.) zuwa Sham.
2- Kamar na sama.
A wata muhawara da ta gudana tsakanin Hisham bn Abdul Malik da Zaid, a lokacin da labarin yunkurin Zaid din ya isa kunnen Hisham, Hisham ya ce da Zaid:
"Na sami labarin kana ambaton halifanci kuma kana burinsa, alhali kai ba ka cikin mazowansa, kuma kai dan baiwa ne".
Sai Zaid ya mayar masa da martani da cewa, Annabi Isma'il dan baiwa ne kuma Allah Ta'ala Ya ba shi annabta. Sannan Hisham ya dora ambaton Imam (a.s.) da zagi, yana mai tambayan Zaid da cewa:
"Dan'uwanka Bakara kuwa...", sai Zaid ya amsa masa da cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ambace shi da Al-Bakir(*) kai kuma ka kira shi da Bakara (wato saniya), lalle sabaninka da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi yawa kuma za ka saba da shi a ranar lahira kamar yadda ka saba da shi a nan duniya, domin Annabi (s.a.w.a) zai shiga aljanna kai kuwa za ka shiga wuta".
To wannan shi ne matakin da Imam Bakir (a.s.) ya dauka da kuma yunkurinsa na siyasa, har lokacin da ya yi shahada.
To daga nan sai zamanin dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s.), a wannan lokaci na Imam Sadik (a.s.) kuwa bala'i ya yawaita kan al'ummar Annabi (s.a.w.a), ya kuma fi tsanani kan Alayensa (s.a.w.a). Imam Sadik (a.s.) ya
____________
1- Dala'il al-Imamah na Muhammad bn Jarir Tabari, vangaren rayuwar Imam Bakir (a.s.).
(*). A nan yana nuni da fadin Manzon Allah (s.a.w.a.) ga sahabinsa Jabir Abdullah al-Ansari ne cewa: Lalle kai za ka riski daya daga cikin 'ya'yan Husaini, shi zai tsaga ilmi, don haka ka isar da gaisuwa ta gare shi". To a saboda haka ne aka kiran Imam Bakir (a.s.) da wannan suna na Bakir , wato mai tsatstsaga ilmi.
Abul Abbas Saffah ya yi kokarin kashe Imam domin saninsa da mukaminsa na jagoranci da goyon bayansa ga bijirewa mahukunta. To amma Allah Ya kare shi daga sharrinsa, duk kuwa da cewa ya taba kiran Imam din daga Madina zuwa garin Hira da ke kasar Iraki, inda ya tsananta masa da kuma sanya shi karkashin 'yan leken asiri.
Yayin da Abu Ja'afar Mansur ya gaji Al-Saffah, shi ma ya ji tsoron matsayin Imam Sadik (a.s.) kamar yadda magabatansa suka ji, sau da yawa ya kan kira Imam (a.s.) daga Madina zuwa Iraki.
Ga yadda yake siffanta karfin Imam a fagen siyasa da tasirinsa kan masu gwagwarmaya, inda ya ke cewa:
"Wannan bakin cikin (yana nufin Imam Sadik) da rike makoshin halifofi, korarsa ba ta halalta, kisan sa ba ya halalta. Ba don mun hadu da shi a bishiya mai kyakkyawan tushe, mai rassan da suka gabata, mai dadadan 'ya'ya, an kuma albarkaci zuriyarta aka tsarkake ta cikin Littattafai ba, da an sanya shi cikin mummunan karshe, saboda labarin da muka samu na tsananin aibantamu da mummunan magana da yake fada game da mu(1) ".
Wannan shi ne matsayin Imam Sadik (a.s.) da aikin
____________
1- Imam Sadik na Abu Zuhra, shafi na 138.
Daga nan sai zamanin Imam Musa bn Ja'afar Kazim (a.s), dan Imam Sadik (a.s.), a lokacinsa cutar da musulmi da karkata addini da kwadaitar da mutane da dukiya sun tsananta a hannun Abbasiyawa. Don haka ne Imam (a.s.) ya kasance jogora wajen gyaran al'amarin Musulunci.
An sanya Imam (a.s.) karkashin leken asiri a zamanin Mansur wanda shi ya kai matuka wajen zaluntar Alawiyyawa da kwace dukiyoyinsu, da gina turakun gadoji da kadarkai da soraye a kansu da ransu, da azabtar da su cikin kurkuku.
To amma bayan da Muhammad Al-Mahdi ya gaji sarautar Abbasiyyawa sai tsoransa ga Imam Kazim ya yi tsanani, don haka sai ya kirayi Imam (a.s.) daga Madina zuwa Bagadaza domin ya hukunta shi. Al-Mahdi ya sa aka rufe Imam Kazim (a.s.) a kurkuku har zuwa wata rana da halifan ya ga Imam Ali bn Abi Talib (a.s.) a mafarko yana ce da shi:
"Kai Muhammad!
"To, shin, kuna fatan idan kun juya za ku yi barna a cikin kasa, kuma ku yanyanke zumuntarku?" (Surar Muhammadu, 47: 22)
Wannan sai ya tsoratar da Mahdi ya fitar da Imam Kazim (a.s.) daga kurkuku.
A mulkin Al-Hadi, sarkin Abbasiyawa, ne bala'i ya tsananta kan Imam (a.s.) da kuma Alu Ali (a.s.). Ya ci gaba da korarsu da kashe su da neman batar da su gaba daya musamman ma bayan yunkurin Husain bn Ali wanda aka fi sani da waki'ar Fakh. Imam Kazim (a.s.) ya gamu da tsanantarwa da matsarwa har sai da ta kai Al-
Daga nan sai Al-Hadi ya sanya Imam Kazim (a.s.) a kurkuku da hana shi damar gudanar da aikinsa na ilmantarwa da jagoranci a bayyane. Amma mutuwa ba ta bar shi ya aikata mummunan nufinsa, don kuwa ta kawo karshen wannan azzalumi jabberi.
Daga nan sai lokacin Haruna Rashid wanda aka sami jayayya mai tsananin gaske tsakaninsa da Imam Kazim (a.s.). Haruna Rashid ya yi kiran Imam da ya taho daga birnin Madina zuwa Iraki, inda ya ci gaba da tozarta shi da sanya shi a kurkuku da azabtarwa nau'i daban-daban, wadanda suka hada da daure shi da karfe yana daukansa daga wannan kurkukun zuwa wancan. Imam (a.s.) ya zauna a kurkuku tsawon shekaru, daga karshe Haruna Rashid ya ci da shi guba ta hannun shugaban dogarawan-sa mai suna Al-Sandi bn Shahik. Imam (a.s.) ya yi shaha-da ne a ranar 25 ga watan Rajab a shekara ta 183 bayan hijira.
Daga nan sai zamanin Imam Ridha, Aliyu bn Musa bn Ja'afar (a.s.), wanda shugabancinsa na siyasa ya wajabtawa Abbasiyawa la'akari da shi a sakamakon karfin alkadarin Imam (a.s.) da kaunar al'umma gare shi ga kuma tsanantar bijirewa ga Abbasiyawa. Wannan yanayi ya tilastawa halifan Abbasiyawa Ma'amun sanya Imam (a.s.) a matsayin magajinsa. Imam Ridha (a.s.) ya karbi wannan matsayi ba don sonsa ba, kana kuma da
To bayan shahadar Imam Ridha (a.s.), wanda ya karbi jagoranci al'umma da lamarin Imamanci shi ne dansa Imam Muhammad Jawad (a.s.) wanda ya yi zamani da Ma'amun na dan lokaci. Ma'amun ya yi mu'amala da shi da girmamawa a munafunce, ya aurar masa da 'yarsa Ummul Fadhl domin ya sami soyayyar al'umma, yayi hakan ne kuwa domin ya juya hankulan mutane ya karkata ra'ayin masu gaba da shi, wadanda suke ganin Imam (a.s.) a matsayin jagora. Sai dai fa Ma'amun bai tsinana komai ba domin Imam Jawad (a.s.) ya bar Bagadaza ya koma birnin Kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) saboda ci gaba da aikinsa na ilmantarwa da jagorancin al'umma a can.
To bayan da Ma'amun ya mutu sai dansa Al-Mutasim ya hau karagar mulkin Abbasiyawa, sai dai kuma shi Al-Mutasim bai jima a kan mulkin ba, to amma dai shi ma ya kasance yana jin tsoron Imam Jawad (a.s.) da kuma hadarin zamansa a Madina. To shi ma Al-Mutasim bai yi wata-wata ba sai ya kama tafarkin iyayensa yayin da ya dauko Imam daga Madina ya kawo shi helkwatarsa domin ya sanya ido a kansa. Marubuta tarihi sun ce Imam Jawad (a.s.) ya yi shahada ne a hannun Mutasim ta hanyar guban da ya sa masa cikin abinci a shekarar da ya kawo shi Bagadaza a lokacin kuwa hijira tana da shekara dari biyu da ashirin da biyar.
To bayan shahadar Imam Jawad (a.s.) dansa Imam Ali Hadi shi ne ya gaji jagorancin al'umma da Imamanci daga mahaifin nasa. A zamanin Mutawakkil Abbasi ne
Marubuta tarihi sun ambaci dalilan da suka sa Mutawakkil ya ta da Imam Hadi (a.s.) daga Madina. Sibt Al-Jawziyya ya ce:
"Malaman tarihi sun ce: Ya fito da shi daga Madinar Manzon Allah (s.a.w.a.) zuwa Bagadaza ne don yana tsananin kin Aliyu da zuriyarsa sai kuma ya sami labarin irin matsayin Aliyu Hadi a Madina da karkatar mutane zuwa gare shi. Wannan ya sa shi tsoronsa (1)".
Bayan shahadar Imam Hadi (a.s.) garin Samarra a shekara ta 254 bayan hijira, sai dansa Imam Abu Muhammad Hasan Askari (a.s.) ya kasance Imami mai kula da harkar al'umma da kuma shiryar da su. To shi ma dai matsayinsa kan Abbasiyawa tamkar na iyayensa ne, wajen fito-na-fito a fagen siyasa. To shi ma dai mahu-kumtan ba su bar shi don kuwa sun cutar da shi kamar yadda suka cutar da mahaifansa. Al-Muhtadi bn Al-Wasik sarkin Abbasiyawa ya sanya shi a kurkuku a garin Samarra, inda ya mika shi ga hannun gandurobobin kurkukun wadanda suka shahara da mugun hali da
____________
1- Tazkiratul Khawas na Ibn Jawziyya, shafi na 359.
Malaman tarihi sun kiyaye abubuwan da suka sami Imam Hasan Askari (a.s.) na matsanancin bala'i, kamar abin da Ahmad bn Muhammad ya ruwaito, inda ya ce:
"Yayin da Al-Muhtadi da fara kashe magoya bayan Ahlulbaiti (a.s) sai na rubuta wa Abu Muhammad Hasan Askari (a.s.) na ce masa: Ya shugabana, godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya shagaltar da shi (Muhtadi) daga barinka. Hakika na sami labari cewa yana maka barazana da cewa: "Wallahi sai na kore su daga duk sababbin kasashe", sai Abu Muhammad (a.s.) ya rubuta da hannunsa cewa: "Wannan shi zai takaita rayuwarsa(1) ".
An ruwaito cewa, Imam Askari (a.s.) ya kasance cikin kurkuku a zamanin Al-Mutamad har lokacin da ya kira shi don warware wata matsala da ta faru tsakanin musulmi da wani malamin Nasara, a kan shayarwa (ruwan sama). Sai Imam (a.s.) ya warware ta, to a saboda haka Al-Mutamad ya fito da shi daga kurkukun kuma ya nemi a saki mabiyansa da ke tare da shi a kurkuku, hakan kuwa aka yi, wato a ka sake su.
Wannan shi ne kadan daga tarihin Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da fito-na-fiton da suka yi da hukumomin zalunci na lokacinsu wadanda suka doru a kan al'umma. Idan an duba da kyau za a ga cewa, silsilar Imamai goma sha daya mai albarka ta Ahlulbaiti (a.s) ta kasance wani fage ne na jagorantar al'umma da kuma shiryar da su. Don kuwa kowane Imami za a ga shi ne jagorar al'um-mar da ya kasance a cikinta, wanda kuma ya fi kowa ilmi da sanin ya kamata. Irin wannan tsari ba zai yiyu a same shi ba sai da shiri gabatacce daga Allah Ta'ala. Kuma babu makawa wannan bibiya ta jagorancin Ahlulbaiti (a.s) yana sanar da mu mukaminsu da fagensu na shugabancin akida da siyasa a rayuwar wannan al'umma.
____________
1- Al-Fusulul Muhimma na Ibn Sabbag Al-Maliki, babin rayuwar Imam Hasan Askari (a.s.).
A zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) musulmi suna samun hukumce-hukumce da dokoki masu tsara al'amurransu na zamantakewa da ibada, kamar su salla, rabon gado, zaman iyali, kasuwanci, jihadi, aikin hajji da abin da ya shafi kasa da filaye da shari'u da sauransu ne kai tsaye daga Annabi (s.a.w.a), domin shi ne mai isar da sako, mai kira zuwa ga shiriya ta hanyar wahayi.
Bayan da ya koma ga Ubangijinsa Mahalicci, al'ummar musulmi sun koma ga Littafin Allah da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.), suna daukar dokoki da sanin ra'ayin shari'a kan dukkan abubuwan da suka shafe su ta hanyar sahabbai da Ahlulbaiti (a.s), wadanda suka kiyaye Sunna da kuma Littafin Allah. Daga nan al'ummar musulmi ta sami ci gaba cikin salon rayuwa, saboda faruwar sabbin abubuwa cikin rayuwar mutane. Babu shakka wadannan sabbin abubuwa suna bukatar hukumcin Musulunci da sanin dokokin shari'a domin daidaitasu. Wannan fadada-wa cikin shari'a ya fara samuwa kusan a karshen karnin farko a zamanin Imam Muhammad Bakir (a.s.), wanda shi ne malamin Madina, kuma mokamar dukkan malaman zamaninsa. Malaman tarihi da na fikihu sun ruwaito cewa saboda hakan ne ma ake kiransa da Al-Bakir, domin fadadawarsa wajen ilmomi da yada su. A zamanin dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ne fannonin ilmi da fikihu da shari'a suka yi fure, yayin da shugabannin mazhabobi suka yi karatu a wajen Imam Sadik (a.s.) din. Da shi babansa Imam Bakir (a.s.) sun kasance masu ruwaito Sunna ne da kuma bayanin abin da Littafin Allah
A zamanin Imam Sadik ne aka fara samun mazhabobin fikihu kamar masu bin ra'ayi da kiyasi, wato mazhabar Imam Abu Hanifa, wanda ya yi karatu na wani lokacin a wajen Imam Sadik (a.s.) da sauran mazhabobi, wadanda daga baya suka takaitu cikin mazhabobi guda hudu, wato: Mazhabobin Malikiyya, Hannifiyya, Shafi'iyya da kuma Hambaliyya. Wadanda su ma wadannan mazhabobi sun rarrabu a tsakaninsu a wajen tafarkin Ijtihadi da yarda da wata ruwaya, a gefe guda kuma ga mazhabar nassi wacce Imam Sadik (a.s.) yake jagoranta, wacce ta dogara da Littafin Allah da Sunnar Annabi (s.a.w.a) wajen fitar da hukumce-hukumcen Musulunci, sannan kuma take watsi da ra'ayi da kiyasi. A daidai lokacin da kuma sauran mazhabobin suka sanya wasu hanyoyi da gano shari'a bayan Littafin Allah da Sunna, kamar su:
Mazhabobin Ahlussunnan nan guda hudu, Hanafiyya, Malikiyya, Hambaliyya da Shafi'iyya sun sassaba kan karbar wadannan hujjoji, ba su hadu gaba daya akansu ba. Za ka ga wasunsu suna tabbatar da wannan su yi watsi da wancan daga cikin hujjojin (hanyoyin samun hukumci).
A dalilin sassabawa wajen dauka ko watsi da wasu hujjoji mazhabobin fikihu guda hudun nan suka sami sabani tsakaninsu kuma suka saba da mazhabar nassi wacce A'imman Ahlulbaiti (a.s) suke jagoranta. Kuma a dalilin hakan ne mazhabobin nan biyar suka sassaba ka
A sarari yake cewa sabanin da ke tsakanin mazha-bobin Musulunci, sabani ne na ilmi wanda bai kamata ya raba musulmi ba, ko ya nisanta tsakaninsu. Domin abin lura shi ne ana iya magance irin wannan sassabawa ta hanyar muhawara da bincike mai tsabta wanda babu son zuciya ciki. Wajibi ne irin wannan bincike a yi shi karkashin ginshikin ilimi yardaddu ga dukkan musulmi, tare da bude kofar ijtihadi wacce take rufe a wurin wasu mazhabobi. Yana da muhimmanci a gane cewa wannan sabani ba tsakanin Sunna da Shi'a yake ba, sai dai ya wanzu ne tsakanin mazhabobin fikihu kamar guda shida: Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya, Hambaliyya, Ja'afariyya da Zaidiyya, a kara kuma da ra'ayoyi da ijtihadin sashin malaman fikihu ko cikin wadannan mazhabobi ambatattu ko waje da su.
Yayin da aka bude kofar ijtihadi wa dukkan sassan musulmi, malaman fikihu kuma suka karbi aikinsu da aka sansu da shi, to za a iya iyakance ginshikan istinbadi (tsamo hukumci daga Alkur'ani da hadisi ko dai wani tushe na shari'a) da ayyana ko mene ne mabubbugan shari'a da kuma hanyar ciro hukumce-hukumce daga mabubbugar nan na tushe (wato Alkur'ani da Sunna). Domin ta hanyar komawa garesu su biyun da kokkofin ruwayoyi da hadisai da zubar da wadanda ba su inganta
Ga wasu misalan yadda ra'ayoyin malaman fikihu suke dacewa ko sassabawa, ba kuma tare da la'akari da ko daga Shi'a ko Sunna suke ba:
Imamiyya da Hambaliyya sun ce: Tahiyar farko wajiba ce a salla, amma Hanafiyya da shafi'iyya da Malikiyya sun ce mustahabi take ba wajiba ba.
Amma tahiya ta karshe kuwa wajiba ce a ganin Shafi'iyya da Imamiyya da Hambaliyya, amma Malikiyya da Hanafiyya sun ce mustahabi ce .
Batun sallama kuwa, Shafi'awa da Malikawa da Hanbalawa sun ce wajiba ce, Hanafawa kuma suka ce ba wajiba ba ce. To amma Imamiyya kuma sun saba, wasu suna cewa wajiba ce, saura kuwa suka ce mustahabi ce. Daga cikin masu cewa mustahabi ce kawai har da Shaikh Mufid, Shaikh Tusi da Allama Hilli(1) .
Dangane da sallar jam'i kuwa, Hanbalawa sun ce wajiba ce, wajibcin kuwa kan kowane mukallafi ne idan
____________
1- Al-Fikhu ala mazahibil Khamsa na Shaikh Muhammad Jawad Mugniyya, shafi na 114.
Kan cancantar zakka kuwa, shafi'awa da Hanbalawa sun tafi a kana cewa wanda ya mallaki rabin abin da zai ishe shi, ba a sa shi cikin fakirai, ba ya halalta a ba shi zakka. Imamiyya da Malikiyya suka ce fakiri a shar'ance shi ne wanda bai mallaki abin da zai biya bukatunsa da na iyalansa a shekara ba. Saboda haka duk wanda ke da wata gona ko kaddara ko dabbobi amma ba za su biya bukatun iyalansa tsawon shekara ba, to ya halalta a ba shi Zakka.
Imamiyya da Shafi'iyya da Hambaliyya sun ce wanda yake da ikon nema ba ya halalta ya karbi zakka. Hanafawa da Malikawa kuma suka ce ya halalta kuma ana iya ba shi.
Kan kwana a Muzdalifa a yayin aikin hajji kuwa, Hanafiyya da Shafi'iyya da Hanbaliyya sun ce wajibi ne a kwana a can, wanda ya bar shi sai ya yi yanka (haka Al-Mugni ya kawo).
Imamiyya da Malikiyya kuwa suka ce bai wajaba ba, amma shi ya fi.
Wajen jifa a Jamratul Akba kuwa, Malikiyya da Hanafiyya da Hambaliyya da Imamiyya suka ce bai halalta a yi jifa gabannin alfijir ba, idan kuwa aka yi hakan ba da wani uzuri ba, sai an sake. Sai dai sun halalta gabatarwar domin uzurai kamar gajiyawa ko rashin lafiya ko tsoro. Shafi'awa kuwa suka ce babu laifi a yi jifa gabannin alfijir domin lokacin da aka ambata na mustahabbanci ne ba wajibci ba (Al-Tazkira da Bidaya
Kan daurin aure Imamiyya da Hambalawa da Shafi-'awa cewa suka yi ba ya halalta a daura aure da rubutu, watau dole ne a yi da baki. Hanafawa suka ce yana inganta idan mai neman aure da wacce ake nema ba sa guri guda.
Shafi'awa da Malikawa suka ce: waliyi na iya aurar da baliga shiryayya idan budurwa ce ko ba da yardarta ba. Idan kuwa bazawara ce, to sai da yardar ta, ba zai gudanar da daura mata aure shi kadai ba, ita ma haka. Ko da yake wajibi ne shi zai yi siga, ita ba za ta iya siga ba.
Hannafawa kuwa suka ce baliga mai hankali tana iya zabin miji da siga da kanta, budurwa take ko bazawara, ba wanda yake da walicci a kanta ko hakkin sabawa zabinta da sharadin ta zabi mutumin da ya yi daidai da ita, kuma kada ta yi aure da mafi karanci daga sadakin tamkarta.
Mafi yawan malaman Imamiyya sun ce baliga shiryayya tana da mallakar dukkan lamurran da suka shafi kulla wata yarjejeniya har da na aure, budurwa take ko bazawara, hakan kuwa saboda balaga da kuma shiryuwarta ne. Tana iya daura aure wa kanta ko waninta, ko ta yi da kanta ko da wakili, ko ta bayar ko karba. Ita kamar namiji take ba tare da wani bambanci ba .
Batun sakin aure kuwa, Abu Zuhra ya fada cikin littafinsa Ahwalul Shaksiyya shafi na 283 cewa: "A mazhabar Hanafiyya saki yana aukuwa ne daga kowani mutum idan ba yaro ko mahaukaci ko mai raunin hankali ba, saboda haka saki yana aukuwa daga mai wasa ko mai maye daga abin da yake haram, ko wanda aka tilasta".
A shafi na 286 ya ce: "Tabbatacce yake a mazhabar Hanafiyya cewa sakin wanda ya yi kuskure ko mantuwa yana aukuwa".
____________
1- Al-Fikhu ala mazahibil Khamsa na Shaikh Muhammad Jawad Mugniyya, shafi na 466.
Imamiyya sun ruwaito daga Ahlulbaiti (a.s) cewa:
"Babu saki sai ga wanda ya nufi sakin".
Dangane da iddar macen da ta yi zina kuwa: Hanafawa da Shafi'awa da mafiya yawa daga Imamiyya sun ce: Idda ba ta wajaba domin zina, domin ruwan (maniyyin) mazinaci ba shi da wata alhurma (girmama-wa). Saboda haka ya halalta a daura aure wa macen da ta yi zina, da kuma ingancin takar ta ko da tana da ciki. Amma Hanafawa sun haramta takar mai ciki sai ta haihu duk da yake ana iya daura mata aure.
Malikawa kuwa sun ce: Wanda ya yi zina da mace tamkar takan ta ne cikin rashin sani, dole ne ta yi istibra'i gwargwadon idda sai fa idan ana nufin tsayar da haddi kanta ne, a nan kam sai ta yi istibra'i da haila guda.
Hanbalawa kuwa suka ce: Idda wajiba ce kan mazinaciya kamar yadda take kan sakakka (AlMugni, juzu'i na 6 da kuma Majma'ul Anhar)
Kan batun wasiyya ga ciki (wato dan da ke cikin ciki) kuwa, malaman fikihu sun saba kan cewa shin dole ne a samu cikin yayin wasiyyar ko kuma a'a.
Imamiyya da Hanafiyya da Hambaliyya da Shafi'iyya bisa mafi ingancin zantuttukansu sun ce ana shardanta hakan, kuma cikin ba ya gado sai idan an san cewa samamme ne yayin wasiyyar. Ana tabbatar da hakan ne, idan matar ta haihu kafin wata shida bayan an yi wasiyyar idan tana da miji mai iya saduwa da ita. Idan kuwa ta haihu bayan wata shida ko fiye, to ba a bai wa ciki kome daga cikin wasiyyar saboda yiyuwar samuwar sabon ciki. Tushe shi ne rashin samuwar ciki yayin da
Malikawa kuwa sun ce: Wasiyya tana inganta wa cikin da yake samamme ne da wanda zai samu nan gaba, domin suna ganin halalcin wasiyya wa wanda ba samamme ba. (Dubi Tazkiratul Hilli da Fikihu ala Mazahib Al-Arba' da litattafan fikihu na Hanbaliyya da dama a babin wasiyya).
Wadannan misalai ne 'yan kadan daga fikihu idan an kwatanta mazhabobin Musulunci da junansu. Muna iya ganin yadda wasu mazhabobi suka dace ko suka saba da juna a mas'alolin hukumce-hukumce. Za a ga Malikiyya da Shafi'iyya sun dace da Imamiyya, su saba da Hanafiyya da Hambaliyya, ko Hanafiyya ko Hambaliyya su dace da Imamiyya, su saba da sauran mazhabobi Ahlussunna, da dai sauran irin wannan. Saboda haka sassabawa ba ta dogara da kasancewa cikin Sunna ko Shi'a, sassabawar ta ilimi da tunani, ba sabawar Sunna da Shi'a ba ce, ko kusa, sai dai sabawa ce ta tsarin ilmin ciro hukumce-hukumce na mazhabobin nan biyar. Saboda haka ya zama wajibi a kan mu mu tantance dalilai na shari'a ta hanyar tattaunawa ta ilmi domin isa ga dacewa, sabili da hukumcin Allah dai daya ne akan kowace mas'ala.
Masu kokarin nuna cewa sabanin da ke akwai tsakanin Sunna da Shi'a tamkar ya mai da su kishiyoyi masu jayayya tsakanin juna, ba abin da suke yi sai karkata gaskiya da nisantar tsarin kubutaccen tattaunawa ta ilmi. Babu abin da suke yi sai aiki wa abokan gaban musulmi ta hanyar wargaza hadin kan musulmi.
"Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku, a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta, sai Ya tsamar da ku daga gare ta. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku, za ku shiryu # Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma su na hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan su ne masu cin nasara # Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka saba wa juna, bayan hujjoji bayyanannu sun je musu, kuma wadannan suna da azaba mai girma". (Surar Aali Imrana, 3: 103-105)
"Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah, wannan shi ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba # Kuma masu mai da al'amari gare Shi kuma ku bi Shi da takawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai # Watau wadanda suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance kungiya-kungiya, kowace kungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai. (Surar Rum, 30: 30-32)
"Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa da ma'abota al'amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara". (Surar Nisa'i, 4: 59)
"Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Ni, Ubangijinku ce, sai ku bi Ni da takawa". (Surar Mu'uminun, 23: 52)
"Kuma ku yi da'a ga Allah da MazonSa, kuma kada ku yi jayayya har ku raunana kuma karfinku ya kau, kuma ku yi hakuri, lalle ne Allah Yana tare da masu hakuri". (Surar Anfal, 8: 46)
Tun al'ummar musulmi tana jaririya a hannun Manzon Shiriya, Muhammadu (s.a.w.a), abokan gaban musulmi daga masu bautar gumaka da yahudawa da nasara da munafukai da masu neman fadanci domin arzurta kansu, suke kokarin kekketa al'ummar da hura wutar sabani da rarraba. Hakika da'awar Musulunci a karkashin jagorancin Manzon Allah (s.a.w.a.) ta fuskanci
Tarihin yadda Musulunci ya sha kokawa da wadan-nan magabta a zamanin Annabi (s.a.w.a) yana cike da abubuwa masu bayyana mana yadda masu jayayya da Musulunci, magabtan al'umma suka yi aiki da makamin rarrabawa da shuka sabani. Duk wanda ya bibiyi Alkur'ani Mai Girma da Sunnar Annabi (s.a.w.a) da dalilan saukar ayoyin Alkur'anin, sannan kuma ya dubi tarihin farkon sakon Musulunci zai lura da cewa sakon ya yaki wannan ciwon mai neman rusa addini, yakin da ba kakkautawa. Ya kuma gargadi musulmi kan kada su fada cikin sabani da rarraba kamar yadda al'ummar da suka shude suka fada. Alkur'ani ya hori musulmi da hadin kai da riko da juna, ya kuma yi gargadi kan rarraba da sassabawa da jayayya, yana mai suranta irin makomar masu yin hakan da cewa:
"....Kuma kada ku yi jayayya har ku raunana, karfinku kuma ya tafi....".
Hakika Alkur'ani ya yi gargadi kan jayayya da sabani wanda shi yake kai mutane da makoma mai muni da rauni da ragwanci da kasawa da gushewar karfi da daula. Haka nan kuma ya gargade mu kan zamowa kungiyoyi masu gaba da neman halaka juna, sashi na dukan sashi, sashi na la'antar wani sashin tamkar yadda mushirikai da batattun al'ummai masu keta kalmar Allah da wasa da shari'o'inSa suka kasance.
Alkur'ani mai girma yana fuskantar da wannan al'umma da ta hada kai bisa kalmar tauhidi:
"...Saboda haka ka tsayar da fuskarka ga addini... wannan shi ne addini madaidaici".
"Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba...".
Da kuma cewa wannan al'umma guda ce:
"Kuma lalle ne wannan al'ummar ku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku biNi da takawa".
"Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku bauta Mini".
Kamar haka ne Alkur'ani ya sanya matakan hada kan al'umma kamar haka:
"Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri da kuma hani daga abin da ake ki".
An umurci musulmi da wannan aikin a madadin rarraba da sabani da jayayya domin kada su halakar da karfinsu kan kokawan cikin gida har ma su raunana su zamo abin hadiyewa ga abokan gaba.
Alkur'ani mai girma yana kiran hankulanmu domin mu gane dalilan sabani da kuma tabbatar da tushen hanyoyin warware shi:
(a). Sabani kan shari'a da tunani irin na Musulunci
"Idan kun yi jayayya cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa...".
"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah".
Alkur'ani yana hana mu mayar da jayayya ta ilimi da shar'antawa zuwa wata matsala ta rarraba da sabani da gaba da keta al'ummar musulmi, ya ce:
"Kuma kada ku yi jayayya har ku raunan, karfinku ya kau.....".
(b). Mas'alolin da suke da alaka da siyasa ko zamantakewa wadanda shugaban al'umma, na shari'a, shi yake tsara su da gudanar da su, to wajibi ne a yi masa biyayya domin kada ra'ayoyi su yawaita a sassaba. Domin dole ne al'ummar musulmi ta zama tana da matsaya guda kan sha'anin siyasa da zamantakewar al'umma.
"....Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzon Allah da ma'abuta al'amari daga cikinku".
Hakan kuwa matukar su ma'abuta al'amari sun lizimci hukumce-hukumcen shari'a, kuma suna tabbatar da maslahar al'umma.
Musulmi a yau - alhamdu lillahi - suna tare da Littafin Allah, wanda barna ba ta shigo masa ko a farko ko a karshe, duk wani mai jirkitarwa bai iso shi, yana nan kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kawo shi:
"Hakika Mu ne Muka saukar da ambato (Alkur'ani), kuma hakika Mu masu kiyayewa ne a gare shi". (Surar Hijiri, 15: 9)
Na biyu kuma, Musulmi sun hadu kan kubutar Alkur'ani daga dukkan wani ragi ko kari, kana kuma sun yi imani da shi da kuma Wanda Ya saukar da shi, wato
Na uku, musulmi sun hadu kan gaskata Annabi (s.a.w.a), suna da Alkibla guda, sun yarda da farillolin Musulunci kamar su salla, zakka, azumi, hajji, jihadi, umurni da mai kyau da kuma hani da mummuna da dai sauransu.
Musulmi sun hadu kan haramcin manyan laifuffuka, kamar su zina, shan giya, luwadi, sata, kisan kai, karya, cin rashawa da dai makamantansu.
Babu wani sabani tsakanin musulmi cikin ginshikai da tushen imani wadanda suke sanya al'umma ta zama musulma, sun yi ittifaki akan dukkan wadannan gishikai. Saboda haka, wajibi ne a warware mas'alolin ijtihadi da ra'ayoyin ilmi ta hanyar mai da su ga Littafin Allah da tabbatacciyar Sunnar Annabi (s.a.w.a) domin kuwa Annabi (s.a.w.a) ya bar al'ummarsa bisa hanya ma'abu-ciyar haske. Annabi (s.a.w.a) ya ce:
"Na bar ku kan hanya mai haske, darenta tamkar yininta. Babu mai karkace mata a bayana sai halakakke".
Al'ummar musulmi a yau tana cikin wani matsayi na tarihinta mai bukatar lura da yanayi na ci gaba mai hadari domin tun da dadewa makiya Musulunci suka yi ta kai hare-hare gare su, kama tun daga yakukuwan Salibiyya (wadanda kiristocin Turai suka yi da musulmi), kawo ya zuwa yau din da muke ciki.
Su wadannan makiya, kama tun daga su wadannan kiristoci na salibiyya da kuma yahudawan sahyoniya da 'yan korensu, sun fuskanci akidoji da maslahohin musulmi da ruguzawa da kuma makirci, kuma ba su gushe ba tsawon karni na goma sha tara da na ashirin suna babbata wannan al'umma, suna yada rarraba da
Ya wajaba kan 'yan'uwa musulmi da su kiyaye tare da sanin hakikanin masu yada dafin rarraba da sabani cikin musulmi ta hanyar dasisa da karya da kage-kage ko ta hanyar riko da raunana da kagaggun ruwayoyi da suke cikin littattafan hadisai. Irin wadannan hadisai za a samu cewa malamai da masu bincike sun riga da sun fitar da su daga da'irar ilmi, suna ganin sauya su aka yi. Duk musulmi sun san da hakan kamar yadda Manzon Tsira (s.a.w.a) ya gargadi musulmi a hajjinsa na bankwana da cewa:
"Hakika makaryata sun mini yawa kuma za su yawaita. To duk wanda ya yi min karya da gangan ya tanadi mazauninsa a wuta. Idan hadisi ya zo muku, ku
To idan dukkanmu muna sane da wannan, saboda maslahar waye masu neman rusa addini suke rubuta littattafai da mujallu masu yada rarraba da sabani tsakanin musulmi da kafirta juna da shuka gaba cikin zukata? - domin maslahar wa suke wannan mugun aiki, musamman ma a wannan lokacin mai hadari? Alhali Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ba za ku shiga aljanna ba sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba sai kun so juna. Shin in shiryar da ku ga wani abu idan kun yi za ku so juna? Ku yada sallama tsakaninku(2) ".
Irin wadannan kulle-kulle babu shakka aikin manyan azzaluman duniya ne, masu rawar jiki duk san da aka ambaci hadin kan musulmi da gangamin al'ummar Annabi (s.a.w.a), saboda tsantsar karfin ta na mutane da albarkatu da akida mai karfin gaske.
Abin da ya dace da malamai da masu tunani da marubuta da masu wa'azi da duk masu daukan nauyin kula da makomar addinin Musulunci masu kyakyawar niyya shi ne su karkata akalar da'awarsu zuwa kalubalantar barnar masu mugun nufi, su kira al'umma zuwa ga hadin kai da warware matsalolinsu na shari'a da tunani bisa dalilai na ilmi.
An nakalto daga Ibn Shar Ashub cikin littafinsa Munakib Ali Abi Talib cewa:
"Wata mace ta yi wasicci da sulusin dukiyarta don a yi mata sadaka, aikin hajji, a kuma 'yanta bawa, to amma dukiyar ba ta isa dukkan wadannan ayyukan ba. Sai aka tambayi Abu Hanifa da Sufyan Al-Sauri kan hakan, sai
____________
1- Safinatul Bihar na Shaikh Abbas Kummi, babin karya, shafi na 484.
2- Sunan Abi Dawud na Abu Dawud, juzu'i na 4, babin yada sallama, shafi na 350.
Abu Kasim Al-Baggar ya kawo cikin Musnad na Abu Hanifa, cewa Hasan bn Ziyad ya ce: Na ji Abu Hanifa yana ba da amsar wannan tambayar: Wane ne mafi sani cikin wadanda ka gani?
Sai ya ce: Ja'afar bn Muhammad. Yayin da al-Mansur ya kawo shi sai ya kira ni, ya ce: Ya Abu Hanifa, mutane sun fitinu da Ja'afar bn Muhammad, saboda haka ka shirya masa tambayoyi masu tsanani. Sai na shirya masa tambayoyi guda arba'in. Daga nan sai ya kira ni alhali kuwa a lokacin yana Hira ta kasar Iraki, sai na amsa masa wannan kira tasa na isa wajensa a lokacin kuwa Ja'afar bn Muhammad yana zaune a damansa. Yayin da na kalli Ja'afar, sai kwarjininsa ya shige ni, tamkar wannan kwarjinin bai shiga Mansur ba. Sai na yi masa sallama, ya amsa mini, sai na zauna. Sai Mansur ya ce: Ya Aba Abdillah, wannan Abu Hanifa ne, sai ya ce: "E, na san shi", sannan sai ya juya gare ni ya ce: "Ya Aba Hanifa, jefa tambayoyinka ga Abu Abdullah". Sai na rika jefa masa tambaya yana amsa mini, yana cewa: "Ku kuna cewa kaza, mutanen Madina suna cewa kaza, mu kuma muna cewa kaza. Ta yiyu mu dace da ku, ta yiwu kuma mu dace da su, wani lokaci kuma mu saba duka. Haka aka yi sai da na gama tambayoyin nan arba'in. Babu abin da ya gaza daga ciki. Sannan Abu Hanifa ya ce; "Lalle
____________
1- AlManakib na Khawarizmi, juzu'i na 5, shafi na 44.
Wadannan abubuwa biyu da suka faru a tarihi suna nuna yadda ake muhawara ta ilmi bisa tafarki mai tsari, yadda ake bijiro da mas'aloli da binciken hakika da gudanar da muhawara da fito da amsa.
Irin yadda Abu Hanifa ya yi muhawara da Imam Sadik (a.s.) da tafarkin da suka bi wanda Musulunci ya tabbatar shi ya cancanta malamai da masu bincike su bi domin hakan Musulunci ya sanya ya zama ginshikin isa zuwa ga hakikanin gaskiya.
Muna iya ganin misalin bin wannan hanya ta ilmi da tunani kubutacce a guri Shaikh al-Azhar, Shaikh Mahmud Shaltut yayin da ya fitar da fatawa cewa ya halalta wa musulmi masu bin mazhabobin Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya da Hambaliya, su bi mazhabar Shi'a Imamiyya kamar yadda ya halalta a bi sauran mazhabobin Musulunci, kuma aikinsu ingantacce ne karbabbe. Baya ga haka kuma Dokta Muhammad Muha-mmad Fahham, daya daga cikin Shehunan Azhar din shi ma yayi amanna da wannan fatawar.
Don dada tabbatarwa, bari mu kawo dukkan wadannan fatawoyi don amfaninmu gaba daya:
Fatawar mai girma Shaikhul Azhar kan halalcin aiki da Mazhbar Shi'a Ithna Ashariyya:
An tambaye shi cewa: "Wasu mutane suna ganin wajibi ne kan musulmi ya yi taklidi (koyi) da mazhabobin nan guda hudu sanannu, kuma babu mazhabar Shi'a Imamiyya ko Shi'a Zaidiyya a cikinsu, domin aikinsa na ibada da mu'amala ya zama ingantacce, karbabbe. Shin Malam yana muwafaka da wannan ra'ayi,
____________
1- AlManakib na Khawarizmi, juzu'i na 5, shafi na 122.
Sai Mai girma ya amsa da cewa:
(Mahmud Shaltut)
Maganar Dr. Muhammad Muhammad Fahham,
Shehin Jami'ar Azhar dangane da fatatar Shaik Shaltut:
"Allah Ya jikan Shaikh Shaltut wanda ya waiwaici wannan ma'ana mai girma ya dawwamar da ita cikin fatawarsa mabayyaniya mai gwarzantaka, yayin da ya yi
"Kuma ka ce: Ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai".
Kuma karshen kiranmu Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai".
(Muhammad Muhammad Fahham)
In an duba za a ga cewa hanyar hada kan al'umma bude take ga duk mai ikhlasi daga 'yan'uwa musulmi, wajibi ne su hada sahu guda, su jefar da sassabawa da 'yan garanci, su tuge dalilan rarraba, su gurfanar da ra'ayoyin ilmi gaban bincike da tattaunawa domin a gano gaskiya.
Mu muna kiran al'ummar musulmi ko ina suke da su fahimci irin halin kunci da musulmi suke ciki na siyasa da zamantakewar jama'a, su kuma yi aiki kan hada kan musulmi da watsar da rarrabuwa, kuma su gano wanda yake rura wutar sabani da 'yan garanci, domin su nesance shi. Domin ya wajaba mu sani cewa muna fama da kulle-kullen Yahudawa Sahyoniya da 'yan mulkin mallaka na Gabashi da Yammaci da 'yan barandansu.
Daga karshe, muna rokon Allah Mai Daukaka, Mai iko da Ya hada kan al'ummar musulmi, Ya nisantar da masu dasisa da masu rura wutar fitina tsakanin al'ummar musulmi da tozarta masu aikin tabbatar da shari'ar Allah da masu kira zuwa gare Shi. Domin akwai taimakawa abokan gaban Allah da hidima ga azzaluman duniya
"Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9: 105)