بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
اللّهُمّّ إنِّي أسألك بِرَحمَتِكَ الّتي وَسِعَتْ كُلَّ شَيءٍ
Allahumma Inni As'aluka Birahmatikal lati wasi'at kulla shai'in
Ya Allah ni ina rokon Ka da rahamarKa wacce ta game kome da kome,

وَبِقُوَّتِكَ الَّتي قَهَرتَ بِها كُلَّ شيءٍ وخَضَعَ لَها كُلُّ شيءٍ وَذّلَّ لَها كُلُّ شيءٍ
wa bi kuwwatikal lati kaharta biha kulla shai'in wa khadha'a laha kullu shai'in, wa zalla laha kullu shai'in
Da kuma karfinKa wanda ka gallabi kome da shi, Kuma kome ya rusuna gare .shi kuma ya kaskanta gare shi,

وَبِجَبَروتِكَ الَّتي غَلَبتَ بِها كُلَّ شيءٍ
wa bijabarutikal lati galabta biha kulla shai'in
( 2 )
Da fifikonKa wanda Ka rinjayi kome da shi,

وَبِعزَّتِكَ الَّتي لا يَقُومُ لَها شيءٍ
wa bi izzatikal lati la yakumu laha shai'un,
Da daukakarKa wadda babu wani abu da zai iya da ita,

وَبِعَظَمَتِكَ الّتي مَلأتْ كُلَّ شيءٍ
wa bi Azamatikal lati mala' at kulla shai' in
Da girmanKa wanda ya cike kome da kome,

وَبِسُلطانِكَ الّذي عَلا كُلَّ شيءٍ
wa bi sultanikal lazi ala kulla shai
Da ikonka wanda ya daukaka a kan kome,

وَبِوَجهِكَ الباقي بَعدَ فَناءِ كُلِّ شيءٍ
wa bi wajhikal Baki ba'ada fana'i kulli shai'in,
Da Fuskarka mai wanzuwa bayan karewar kome da kome,

وَبِأسمائِكَ الَّتي مَلأَتْ أركانَ كُلِّ شيءٍ
wa bi asma'ikal lati mala'at arkana kulli shai'in
Da Sunayenka wadanda suka cike kome

وَبِعِلمِكَ الَّذي أحاطَ بِكُلِّ شيءٍ
( 3 )
wa bi'ilmikal lazi ahada bi kulli shai'in
Da iliminKa wanda ya kewaye kome da kome,

وَبِنُورِ وَجهِكَ الَّذي أضاءَ لَهُ كُلُّ شَيءٍ
wa bi nuri wajhikallazi adha'a lahu kullu shai'in
Da hasken FuskarKa da ke haskaka wa kome da kome,

يا نُورُ يا قُدُّس يا أوَّلَ الأوَّلينَ ويا آخِرَ الآخَرينَ
ya Nuru ya Kuddusu, ya awwalal awwalin, wa ya akhiral akhirin.
Ya haske, ya tsarki. Ya Farkon fararru ya karshen na karshe,

اللّهُمَّ اغْفِر لِيَ الذُّنُوبَ الّتي تَهتِكُ العِصَمَ
Allahummagfir liyaz zunubal lati tahtikul isama,
Ya Allah Ka gafarta mini zunubban da ke kekketa shamaki,

اللّهُمَّ اغْفِر لِيَ الذُّنوبَ الّتي تُنزِلُ النِّقَمَ
Allahummagfir liyaz zunubal lati tunzilun nikam,
Ya Allah Ka gafarta mini zunubban da ke sauko da azaba

اللَّهُمَّ اغْفِر لِيَ الذُّنوبَ الَّتي تُغَيِّرُ النِّعَمَ
( 4 )
Allahummagfir liyaz zunubal lati tugayyirun ni'ama
Ya Allah Ka gafarta mini zunubban da ke Canja ni'ima,

اللَّهُمَّ اغْفِر لِيَ الذُّنوبَ الَّتي تَحبِسُ الدُّعاءَ
Allahummagfir liyaz zunubal lati tahbisud du'a'a
Ya Allah Ka gafarta mini zunubban da ke tsare addu'a,

اللَّهُمَّ اغْفِر لِيَ الذُّنوبَ الَّتي تُنزِلُ البَلاءَ
Allahummagfir liyaz zunubal lati tunzilul bala'a ,
Ya Allah ka gafarta mini zunubban da ke saukar da bala'i,

اللَّهُمَّ اغْفِر لِيَ الذُّنوبَ الَّتي تَقطَعُ الرَّجاءَ
Allahummagfir liyaz zunubal lati takta'ur raja,
Ya Allah Ka gafarta mini zunubban da ke yanke tsammani,

اللَّهُمَّ اغْفِر لِيَ كُلَّ ذَنْبٍ أذْنَبتُهُ وَكُلَّ خَطيئَةٍ أخْطَأتُها
Allahummagfir li kulla zanbin aznabtuhu, wa kulla khadi' atun akhda' atuha
( 5 )
Ya Allah Ka gafara mini dukkan zunuban da na aikata, da kuma dukkan kuskure da na yi shi,

اللَّهُمَّ إنَّي أَتَقَرَّبُ إلَيكَ بِذِكرِكَ وَأسْتَشْفِعُ بِكَ إلى نَفْسِكَ
Allahumma inni atakarrabu ilaika bi zikrika, waastashfi'u bika ila nafsika,
Ya Allah ni ina neman kusanci da Kai ta hanyar ambatonKa, kuma ina neman cetonKa da Kai daga gareKa,

وَأسْألُكَ بِجودِكَ أنْ تُدْنِيَني مِنْ قُربِكَ وَأنْ تُوزِعَني شُكْرَكَ وَأنْ تُلْهِمَني ذِكْرَكَ
wa as'aluka bijudika an tudniyani min kurbika, wa an tuzi'aniy shukraka, wa an tulhimaniy zikraka.
Kuma ina rokon Ka don yawan baiwarKa Ka kusantar da ni kusa da Kai, Kuma Ka cusa mini godiyarKa, Ka tsiro mini da ambatonKa,

اللَّهُمَّ إنِّي أسْألُكَ سُؤالَ خاضِعٍ مُتَذَلِلٍ خاشِعٍ أن تُسامِحَني وَتَرحَمَني
Allahumma inniy as'aluka su'ala khadhi'in mutazallilin khashi'in, an tusamihani wa tarhamani
( 6 )
Ya Allah ni ina rokon Ka roko irin na Mai rusunawa, mai kankan da kai, Ka yi mini rangwame Ka yi mini rahama,

وَتَجْعَلَني بِقِسْمِكَ راضِياً قانِعاً وفي جَميعِ الأحْوالِ مُتَواضِعاً
wa taja'alani bikismika radhiyan kani'an wa fi j ami' il ahwali mutawadhi'an.
Ka sanya ni mai yarda da kasafinKa ina mai wadatuwar zuci, Mai kankan da kai a kowane hali,

اللَّهُمَّ وَأسألُكَ سُؤالَ مَنْ اشْتَدَّت فاقَتهُُ
Allahumma wa as'aluka su'ala man ishtaddat fakatuhu,
Ya Allah ni ina rokonKa roko irin na wanda bukatarsa ta tsananta,

وَأنْزَلَ بِكَ عِنْدَ الشَدائِدِ حاجَتَهُ وَعَظُمَ في ما عِنْدَكَ رَغْبَتُهُ
wa anzala bika indasshada'idi hajatahu, wa azuma fi ma indaka ragbatuhu,
Wanda ya zo shi gare Ka da bukatarsa yayin tsanani. Kuma kwadayinsa game da abinda ke gurinKa ya tsananta,

اللَّهُمَّ عَظُمَ سُلطانُكَ وَعَلا مَكانُكَ وَخَفِيَ مَكْرُكَ وَظَهَرَ أمرُكَ
( 7 )
Allahumma azuma suldanuka wa ala makanuka, wa khafiya makruka wa zahara amruka,
Ya Allah mulkinKa Ya girmama, MatsayinKa ya daukaka, tanadinKa ya boyu Al'amarinka ya bayyana,

وَغَلَبَ قَهْرُكَ وَجَرَتْ قُدْرَتُكَ وَلا يُمْكِنُ الفِرارُ مِنْ حُكُومَتِكَ
wa galaba kahruka wa jarat kudratuka, wa la yumkinul firaru min hukumatika,
KarfinKa ya yi rinjaye, kudurarKa ta gudana, ba zai yiwa a tsere daga MulkinKa ba,

اللَّهُمَّ لا أجِدُ لِذُنُوبي غافِراً ولا لِقَبائِحي ساتِراً ولا لِشيءٍ مِنْ عَمَلِيَ القَبيحِ بالحَسَنِ مُبَدِّلاً غَيْرُكَ
Allahumma la ajidu li zunubi gafiran wa la likaba'ihi satiran, wa la lishai'in min amaliyal kabihi bil hasani mubaddilan gairaka,
Ya Allah ni ban sami wani wanda zai gafarta mini zunubina ba, da wanda zai suturce miyagun ayyukana ba, da wanda zai musanya mini mummunan aikina da kyakkyawa ba baicin Kai,
( 8 )

لا إلهَ إلاّ أنْتَ سُبْحانَكَ وَبِحَمدِكَ ظَلَمْتُ نَفْسي وَتَجَرَّأتُ بِجَهلي
la ilaha illa anta subhanaka wa bihamdika zalamtu nafsiy, wa tajarra'atu bijahliy,
Buba wani abin bautawa baicin Kai, tsarki ya tabbata gare Ka, dukkan godiya taKa ce. Na zalunci kaina. Na yi wauta da jahilcina,

وَسَكَنْتُ إلى قَدِيمِ ذِكرِكَ لِي وَمَنِّكَ عَلَيَّ
wa sakantu ila kadimi zikrika liy wa mannika alayya,
Na amintu da dadadden ambatonKa gare ni, da baiwarKa a gareni,

اللَّهُمَّ مَوْلايَ كَمْ مِن قَبيحٍ سَتَرتَهُ وَكَمْ مِنْ فادِحٍ مِنَ البَلاءِ أقَلْتَهُ
Allahumma mawlaya kam min kabihin satartahu, ,wa kam min fadihin minal bala'i akaltahu
Ya Allah Ya Majibincina, sau da yawa Ka suturce munanan abubuwa, sau da yawa bala'i mai tsanani Ka tsare shi,

وَكَمْ مِنْ عِثارٍ وَقَيتَهُ وَكَم مِنْ مَكْروهٍ دَفَعتَهُ
( 9 )
wa kam min itharin wakaitahu, wa kam min makruhin dafa'atahu
Sau da yawa tuntube Ka gusar dashi, sau da yawa abu mummuna Ka tunkude shi,

وَكَم مِن ثَناءٍ جَميلٍ لَسْتُ أهْلاً لَهُ نَشَرتَهُ
wa kam min thana'in jamilin lastu ahlan lahu nashartahu,
Kuma sau da yawa yabo mai kyau wanda ba cancance shi ba Ka yada shi.

اللَّهُمَّ عَظُمَ بَلائي وَأفْرَطَ بي سُوءُ حالي وَقَصُرت بِي أعْمالي
Allahumma azuma bala'iy wa afrada biy su'u haliy, wa kasurat biy a'amaliy,
Ya Allah bala'i na ya girmama, mugun halin da nake ciki ya kazanta ni, ayyukana sun gaza mini,

وَقَعَدَتْ بي أغْلالِي وَحَبَسني عَن نَفْعي بُعْدُ آمالِي
wa ka'adat biy aglaliy, wa habasaniy an naf iy bu'udu amaliy
Tarkunana sun kunkume ni, Dogon burina ya hana ni amfanar kaina,

وَخَدَعَتْني الدٌُّنيا بِغُرورِها وِنَفْسي بِخِيانَتِها وَمِطَالِي
( 10 )
wa khada'atniyad duniya bi gururiha, wa nafsiy bikhiyanatiha, wa midaliy,
Duniya kuma ta rude ni da yaudurarta. Zuciyata kuma da laifinta, da kuma bata lokacina,

يا سيِّدي فَأسألُكَ بِعِزَّتِكَ أن لا يَحجُبَ عَنْكَ دُعائِي سُوءُ عَمَلي وَفَعالِي
ya Sayyidiy fa as'aluka bi'izzatika an la yahjuba anka du'aiy su'u amaliy wa fi'aliy,
Ya shugabana don haka ina rokon Ka da daukakarKa Kada mugun aikina da aika-aikata su hana Ka karbar addu'ata,

وَلا تَفْضَحني بَخَفِيِّ ما اطَّلَعْتَ عَلَيهِ مِن سِرِّي
wa la tafdhahaniy bi khafiyyi mad dala'ata alaihi min sirriy,
Kuma kada Ka tozarta ni da boyayyen abinda Ka san shi na daga sirrina,

ولا تُعاجِلْني بالعُقُوبَةِ على ما عَمِلتُهُ في خَلَواتي مِن سُوءِ فِعْلِي وإساءتي ودَوامِ تَفْريطِي وَجَهالَتي وَكَثْرةِ شَهَواتي وَغَفْلَتي
( 11 )
wa la tu'ajilniy bil ukubati ala ma amiltuhu fi khalawatiy min su'i fi'iliy wa isa'atiy, wa dawama tafridiy wa jahalatiy, wa kathrati shahawatiy wa gaflatiy,
Kuma kada Ka gaggauta yi mini ukuba a kan abinda na aikata shi ina kebance ni kadai na daga mummunan aikina, da jahilcina, da yawan sha'awata da gafalata,

وَكُنِ اللَّهُمَّ بِعِزَّتِكَ لِي في الأحْوالِ كُلِّها رَؤوفاً وَعَلَيَّ في جَميعِ الأمُورِ عَطُوفاً
wa kunil lahumma bi'izzatika liy fil ahwali kulliha ra'ufan, wa alayya fijami'il umuri adufan ,
Ya Allah, kuma, Ka zamanto mini mai sassautawa a kowane hali, mai tausasawa a dukan wani hali,

إلهي وَرَبِّي مَنْ لِي غَيْرُكَ أسْألُهُ كَشفَ ضُرِّي وَالنَّظَرَ في أمْري
ilahiy wa rabbiy man liy gayruka as'aluhu kashfa dhurriy wan nazara fiy amriy,
( 12 )
Ya Ubangijina Majibincina wa nake da shi bayan Kai wanda zan roke shi yayewar damuwata da kuma duba al'amarina

إلهي وَمَولايَ أجْرَيتَ عَلَيَّ حُكْماً اتَّبَعْتَ فيه هَوى نَفْسي
ilahiy wa mawlaya ajraita alayya hukman ittaba'atu fihi hawa nafsi
Ya Ubangijina Ya Majibincina ashe za Ka gudanar da hukunci a kaina a kan abinda na bi son raina a cikinsa,

وَلَمْ أحْتَرِس فِيهِ مِنْ تَزيينِ عَدُّي فَغَرَّني بِما أهْوى وَأسْعَدَهُ على ذلِكَ القَضاءُ
wa lam ahtaris fihi min tazyini aduwiy, fagarraniy bima ahwa, wa as'adahu ala zalikal kadha'u
Ban kiyaye sakar abokin gabana a cikinsa ba, har ya yaudare ni da abinda yake so, kuma kaddara ta taimaka masa a kan haka,

فَتَجاوَزْتُ بِما جَرى عَلَيَّ مِن ذلِكَ بَعْضَ حُدودِكَ وَخالَفْتُ بَعْضَ أوامِرِكَ
fa tajawaztu bi majara alayya ba'adha hududika wa khalaftu ba'adha awamirika,
( 13 )
Saboda haka da abinda ya gudana a kaina sai na ketare wasu iyakokinKa, na saba wa wasu umarce-umarcenKa,

فَلَكَ الحَمْدُ عَلَيَّ في جَميعِ ذلِكَ وَلا حُجَّةَ لي في ما جَرى عَلَيَّ فِيهِ قَضاؤُكَ وَألْزَمَني حُكْمُكَ وَبَلاؤُكَ
fa lakal hujjatu alayya fi jami'i zalika, wa la hujjata liy fiy ma jara alayya fihi khadha'uka, wa alzamaniy hukumuka wa bala'uka,
Godiya ta tabbata gare Ka a kan dukkan wannan, ba ni da wata hujja a kan abinda kaddararKa ta gudana a cikinsa a kaina, hukumcinKa kuma ya dora mini tare da bala'inKa,

وَقَدْ أتَيْتُكَ يا إلهي بَعْدَ تَقْصيري وَإسْرافِي على نَفْسي مُعْتَذِراً نادِماً مُنْكَسِراً مُسْتَقيلاً مُسْتَغْفِراً مُنيباً مُقِرَّاً مُذْعِناً مُعتَرِفاً
wa kad ataituka ya Ilahiy ba'ada taksiriy wa Israfiy ala nafsiy mu'utaziran nadiman munkasiran mustakilan mustagfiran muniban mukirran muz'inan mu'utarifan,
( 14 )
Lalle na juyo gareKa ya Ubangijina bayan kwaurona da ketare haddina a kan kaina, ina mai ba da uzuri mai nadama, mai karaya, mai neman afuwa, mai rokon gafara, mai tuba, mai amsa laifi, mai sallamawa ina mai furuci da laifina,

لا أجدُ مَفَرَّاً مِمّا كانَ مِنَّي ولا مَفْزَعاً أتَوَجَّهُ إلَيهِ في أمْري غَيْرَ قُبُولِكَ عُذْري وإدْخالِكَ إيَّايَ في سَعَةِ مِنْ رَحْمَتِكَ
la ajidu mafarran mimma kana minniy wa la mafza'an atawajjahu ilayhi fi amri gaira kabulika uzriy wa idkhalika iyyaya fi sa'atin min rahmatik
Ban sami wata matsera ba daga abinda ya auku daga gurina ba, babu mafakar da zan koma gareta a kan al'amarina ba tare da Ka karbi uzurina ba, kuma Ka shigar da ni cikin yalwar rahamarKa,

اللَّهُمَّ فَاقْبَلْ عُذْري وَارْحَمْ شِدَّةَ ضُرَّي وَفُكَّني مِنْ شَدَّ وَثاقِي
Allahumma fakbal uzriy warham shiddati dhurriy wa fukkaniy min shaddi wathakiy,
( 15 )
Ya Allah Ka karbi uzurina, kuma Ka yi rahama ga tsananin cutuwata, Ka kunce ni daga tsananin daurina,

يا رَبِّ ارْحَمْ ضَعْفَ بَدَني وَرِقَّةَ جِلْدِي وَدِقَّةَ عَظْمِي
ya rabbir ham dha'afa badaniy wa rikkata jildiy wa dikkata azmiy,
Ya Ubangiji Ka ji kan raunin jikina da siririntar fata ta da lage-lagen kashina,

يا مَنْ بَدَءَ خَلْقِي وَذِكْرِي وَتَرْبِيَتي وَبِرِّي وَتَغْذِيَتي
ya man bada'a khalkiy wa zikriy wa tarbiyatiy wa birriy wa tagziyatiy,
Ya wanda ya fari halitta ta da ambatona da tarbiyyata da kyautatawata da ciyarwata,

هَبْني لإِبْتِداءِ كَرَمِكَ وَسالِفِ بِرِّكَ بِي
habniy libtida'i karamika wa salifi birrika biy,
Ka yi mini baiwa saboda farawar karimcinKa gare ni da sauran kyautatawarKa gare ni,

يا إلهي وَسَيِّدي وَرَبِّي أتُراكَ مَعَذِّبي بِنارِكَ بَعْدّ تَوْحيدِكَ
ya ilahiy wa sayyidiy wa rabbiy, a taraka mu'azzibiy bi narika ba'ada tauhidika,
(16 )
Ya Ubangijina, ya Shugabana, Mai lura da ni, shin za Ka yi mini azaba da wutarKa bayan na kadaitaKa,

وَبَعدَ ما انْطَوى عَلَيهِ قَلْبي مِنْ مَعْرِفَتِكَ وَلَهِجَ بِهِ لِسانِي مِنْ ذِكْرِكَ
wa ba'ada man dawa alaihi kalbiy min ma'arifatika, wa lahija bihi lisaniy min zikrika ,
Kuma bayan abinda zuciyata ta kunshe na iliminKa kuma harshena ya shagala da shi na zikirinKa,

وَاعْتَقَدَهُ ضَميرِي مِنْ حُبِّكَ وَبَعدَ صِدْقِ اعْتِرافِي وَدُعائِي خاضِعاً لِرُبُوبِيَّتِكَ
wa'atakadahu dhamiriy min hubbika, wa ba'ada sidki i'itirafiy wa du'a'iy khadhi'an li Rububiyyatika,
Zuciyata kuma ta kudurce soyayyarKa, kuma bayan gaskiyar furacina da du'a'ina ina mai kankan da kai ga shugabancinKa?

هَيْهات أنْتَ أكْرَمُ مِنْ أنْ تُضَيِّعَ مَنْ رَبَّيْتَهُ أو تُبْعِدَ مَنْ أدْنَيْتَهُ
( 17 )
Haihata anta akramu min an tudhayya'a man rabbaitahu, aw tubaida man adnaitahu,
Faufau, har abada Kai Ka wuce tozarta wanda Ka tarbiyyantar, ko kuma Ka nesanta wanda Ka kusantar,

أو تُشَرِّدَ مَنْ آوَيْتَهُ أو تُسَلِّمَ إلى البَلاءِ مَنْ كَفَيْتَهُ وَرَحِمْتَهُ
aw tusharrida man awaitahu, aw tusallima ilal bala' i man kafaitahu, wa rahimtahu,
Ko kuma Ka kori wanda Ka gayyato ko Ka jefa wanda Ka wadace shi, Ka rahamshe shi, zuwa ga bala'i,

وَلَيْتَ شِعْري يا سَيِّدي وإلهي ومَوْلايَ أتُسَلِّطُ النارَ على وُجُوهٍ خَرَّتْ لِعَظَمَتِكَ ساجِدَةً
wa laita shi'riy Ya Sayyidiy wa ilahiy wa Mawlaya, atusallidan nara ala wujuhin kharrat li'azamatika sajidatan
Kaitona, ya Ubangijina, ya Shugabana, ya Majibincina, shin za Ka mamayar da wuta a kan fuskokin da suka kifu suna sujada ga girmanKa,

وعلى ألْسُنٍ نَطَقَتْ بِتَوحِيدِكَ صادِقَةً وبِشُكْرِكَ مادِحَةً
( 18 )
wa ala alsunin nadakat bitawhidika sadikatan, wa bi shukrika madihatan,
Da kuma a kan harshen da ya yi furuci da tauhidinKa yana mai gaskiya, kuma yana mai yabo don godiya gare Ka,

وعلى قُلُوبٍ اعْتَرَفَتْ بإلهِيَّتِكَ مُحَقِّقَةً
wa ala kulubin i'itarafat bi ilahiyyatika muhakkikatan,
Da kuma a kan zukatan da suka hakikance da kasancewarKa Ubangiji suna masu tabbata,

وعلى ضَمائِرَ حَوَتْ مِنَ العِلْمِ بكَ حَتّى صارَتْ خاشِعَةً
wa ala dhama'ira hawat minal ilmi bika hatta sarat khashi'atan
Da kuma kirazan da suka san ilimi game da kai har suka zama suna masu tsoro,

وعلى جَوارِحَ سَعَتْ إلى أوطانِ تَعَبُّدِكَ طائِعَةً وَأشارَت بِاسْتِغْفارِكَ مُذْعِنَةً
wa ala jawariha sa'at ila awdani ta'abbudika da'i'atan, wa asharat bistigfarika muz'inatan
Da kuma a kan gabobin da suka yi tafiya zuwa guraren bauta maKa suna masu da`a, kuma suka dukufa neman gafararKa suna masu sallamawa.

ما هكَذا الظُنُّ بِكَ ولا أُخْبِرْنا بِفَضْلِكَ عَنْكَ يا كَريمُ
ma hakazaz zannu bika wa la ukhbirna bifadhlika anka ya karimu,
Ba haka aka zata game da Kai ba, kuma ba haka aka ba mu labarinKa da falalarKa ba, ya mai karimci,

يا رَبِّ وأنْتَ تَعْلَمُ ضَعْفي عَن قَليلٍ مِن بَلاءِ الدُّنْيا وَعُقُوباتِها
ya Rabbi, wa anta ta'alamu dha'afiy an kalilin min bala' id dunya wa ukubatiha
Ya Ubangiji kuma kai ka riga ka san raunina game da bala`i na duniya, dan kalilan da ukobobinta,

وما يَجْري فيها مِنَ المَكارِهِ على أهْلِها
wa ma yajriy fiha minal makarihi ala ahliha,
Da abinda ke gudana a cikinta na daga munanan abubuwa a kan mutanen cikinta,
( 20 )

على أنَّ ذلِكَ بَلاءٌ وَمَكرُوهٌ قَليلٌ مَكْثُهُ يَسيرٌ بَقاؤُهُ قَصيرٌ مُدَّتُهُ
ala anna zalika bala'un wa makruhun, kalilun makthuhu, yasirun baka'uhu, kasirun muddatuhu
Kan cewa wannan bala`i ne kuma mummunan abu ne da yake kalilan, dorewarsa kuma gajeruwa ce, zamaninsa kuma gajere ne,

فَكَيفَ احتِمالِي لِبَلاءِ الآخِرَةِ وَجَليلِ وُقُوعِ المَكارِهِ فيها
Fa kaifa ihtimaliy li bala`il Akhirati wa jalili wuku`il makarihi fiha
Lahira da girman aukuwar, ta yaya zan iya jure bala'in munanan abubuwa a cikinta,

وَهُوَ بَلاءٌ تَطُولُ مُدَّتُهُ وَيَدومُ مَقامُهُ وَلا يُخَفَّفُ عَن أهلِهِ
Wa huwa balaun tatulu muddatuhu wa yadumu makamuhu, wa la yukhaffafu an ahlihi,
Wannan kuwa bala'i ne wanda zamaninsa yake tsawaita, matsayinsa kuma yake dawwama, kuma ba a sassauta wa ma`abutan sa,

لأنَّهُ لا يَكُونُ إلاّ عَنْ غَضَبِكَ وَانْتِقامِكَ وَسَخَطِكَ وهذا ما لا تَقُومُ لَهُ السَمواتُ والأرضُ
( 21 )
li'annahu la yakunu illa an gadhabika wan tikamika wa sakhadik, wa haza ma la takumu lahus samawatu wal ardhu,
Domin ba ya aukuwa sai daga fushinKa da ramuwarKa, da fushinKa, wannan kuwa abu ne da sammai da kasa ba za su iya jurewa ba.

يا سَيِّدي فَكَيفَ بِي وأنا عَبْدُكَ الضَّعيفُ الذَّليلُ الحَقيرُ المِسكِينُ المُستَكينُ
Ya Sayyidiy fakaifa biy wa ana abdukad Dha'ifuz zalilul hakirul miskinul mustakinu,
Ya Ubangijina to ni kuma ta yaya zan iya, alhali ni bawanKa ne rarrauna, wulakantacce, tozartacce, miskini, wahalalle.

يا إلهي وَرَبِّي وسَيِّدي وَمَولايَ لأيِّ الأمُورِ إلَيْكَ أشْكُو ولِما مِنْها أضِجُّ وَأبْكي
Ya ilahiy wa rabbiy wa sayyidiy wa mawlaya, liayyil umuri ilaika ashku, wa lima minha adhijju wa abki,
Ya Ubangijina, ya Shugabana, ya Majibincina, game da wane al'amari ne zan kai kuka gareKa, kuma game da wanne ne zan yi gunji in yi kuka?
( 22 )

لألِيمِ العَذابِ وشِدَّتِهِ أمْ لِطُولِ البَلاءِ ومُدَّتِهِ
li alimil azabi wa shiddatihi am liduwlil bala'i wa muddatihi,
Game da zafin azaba ne da tsananinta ko kuma game da tsawon bala'i ko kuma dorewar zamaninsa,

فَلَئِنْ صَيَّرتَني لِلْعُقوباتِ مَعَ أعْدائِكِ وَجَمَعْتَ بَينِي وَبَينَ أهْلِ بَلائِكِ
fala'in sayyartaniy lil'ukubabati ma'a a'ada'ika wajama`ata baini wa baina ahli bala`ika,
Idan har Ka sanya ni a cikin ukuba tare da makiyanKa, kuma Ka hada ni da tare da maa'abuta bala'inKa,

وَفَرَّقْتَ بَيْني وَبَينَ أحِبَّائِكَ وأوْلِيائِكِ
wa farrakta bainiy wa baina ahibba'ika wa awliya'ika,
Kuma Ka raba tsakanina da masoyanka,da waliyanka.

فَهَبْني يا إلهي وسَيِّدي وَمَولاي وَرَبِّي صَبَرتُ علي عَذابِكَ فَكَيفَ أصْبِرُ علي فِراقِكَ
( 23 )
fahabniy ya ilahiy wa sayyidiy wa mawlayya wa Rabbiy sabartu ala azabika, fa kaifa asbiru ala firakika,
Da waliyanka, to Ya Ubangijina, Shugabana, Majibincina, Mai kare ni, Ka sanya ni in yi hakuri a kan azabarKa, amma ta yaya zan iya hakuri a kan rabuwa da kai?

وَهَبْني صَبَرْتُ علي حَرِّ نارِكَ فَكَيفَ أصْبِرُ عَنِ النَّظَرِ إلى كَرامَتِكَ
wa habniy sabartu ala harri narika fakaifa asbiru anin nazari ila karamatika,
Kuma idan har na iya jure zafin wutarKa, to ta ya zan iya jure rashin ganin KarimcinKa?

أمْ كَيفَ أسْكُنُ في النّارِ وَرَجائِي عَفْوُكَ
am kaifa askunu fin nari wa raja'iy afwuka,
Ko kuma ta yaya zan zauna a cikin wuta alhali ina sa tsammani da afuwarKa,

فَبِعزَّتِكَ يا سَيَّدي وَمَولاي أقْسِمُ صادِقاً لَئِنْ تَرَكْتَني ناطِقاً لأضِجَّنَ إلَيكَ بَينَ أهْلِها ضَجيجَ الآمِلِينَ
( 24 )
fa bi'izzatika ya Sayyidiy wa mawlaya uksimu sadikan, la'in taraktaniy nadikan la'adhijjana ilaika baina ahliha dhajijal amilin,
Don haka ina mai rantsuwa da gaskiya da dawwamarKa, ya Shugabana ya Majibinci na lalle idan har Ka bar ni ina mai furuci to zan yi ta gunjin kuka a tsakanin Mazaunanta gunji irin na masu jiran tsammani,

ولأصْرُخَنَّ إلَيكَ صُراخَ المُسْتَصْرِخينَ ولأبْكِيَنَّ عَلَيْكَ بُكاءَ الفاقِدِينَ
wa asrukhanna surakhal mustasrikhin, wa la'abkiyanna alaika buka'al fakidin,
Kuma zan yi kururuwa gare Ka kururuwa irinta masu tsananin kururuwa, kuma zanyi maKa kuka, irin na masu rashi,

ولاُنادِيَنَّكَ أيْنَ كُنْتَ يا وَلِيَّ المُؤْمِنِينَ
wa la unadiyannaka aina kunta ya waliyal muminin,
Kuma zan kiraye Ka, ina Kake ne ya Majibincin muminai,
( 25 )

يا غَايَةَ آمالِ العارِفِينَ يا غِياثَ المُسْتَغيثينَ يا حَبيبَ قُلُوبَ الصَّادِقِينَ
ya gayata amalil arifin, Ya giyathal mustagithin Ya habiba kulubis sadikina,
Ya mafificin tsammanin masana, Ya Mataimakin masu neman taimako, Ya masoyin zukatan masu gaskiya,

ويا إلهَ العالَمينَ أفَتُراكَ سُبْحانَكَ يا إلهي وَبِحَمدِكَ تَسْمَعُ فيها صَوْتَ عَبْدٍ سُجِنَ فيها بِمُخالَفَتِهِ
wa ya ilahal alamina afaturaka subhanaka ya ilahiy wa bihamdika tasma'u fiha sauta abdin muslimin sujina fiha bimukhalafatihi,
Ya Ubangijin dukkan halittu. Ashe zai yiwu Kana gani, tsarki ya tabbata gare Ka, Ya Ubangijina, godiya ta tabbata gare Ka, Kana jin muryar bawa musulmi an kulle shi a cikinta a sakamakon sabonsa,

وذَاقَ طَعْمَ عَذابِها بِمَعْصِيَتِهِ وَحُبِسَ بَينَ أطْباقِها بِجُرمِهِ وجَريرَتِهِ
( 26 )
wa zaka da'ama azabiha bima'asiyatihi, wa hubisa baina adbakiha bijurmihi wajariratihi,
Kuma ya dandana azabarta don zunubinsa; an tsare shi a cikin dabakokinta saboda laifinsa da zunubinsa,

وَهُوَ يَضِجُّ إلَيكَ ضَجيجَ مُؤمِّلٍ لِرَحْمَتِكَ
wa huwa yadhijju ilaika dhajija mu'ammilin li rahmatika,
Kuma yana gunjin kuka gareKa, gunji irin na mai sanya tsammani da rahamarKa,

ويُنادِيكَ بِلِسانِ أهْلِ تَوحِيدِكَ وَيَتَوَسَّلُ إلَيْكَ بِرُبُوبِيَّكَ
wa yunadika bilisani ahli tawhidika, wa yatawassalu ilaika birububiyyatika,
Yana kiran Ka da harshen tauhidinKa, kuma yana tawassuli zuwa gare ka da shugabancinka.

يا مَولاي فَكَيفَ يَبْقى في العَذابِ وَهُوَ يَرْجُو ما سَلَفَ مِنْ حِلْمِكَ (ورَأْفَتِكَ وَرَحْمَتِكَ)
ya mawlaya fakaifa yabka fil azabi wa huwa yarju ma salafa min hilmika,
Ya Majibincina to ta yaya zai dore a cikin azaba alhali shi yana kaunar abinda ya gabata na
( 27 )
daga hakurinKa? da tausasawarKa da rahamarKa,

أمْ كَيفَ تُؤْلِمُهُ النّارُ وَهُوَ يَأمَلُ فَظْلَكَ وَرَحْمَتَكَ
am kaifa tu'ulimuhun naru wa huwa ya'amulu fadhlaka wa rahmataka,
Ko kuma ta yaya wuta za ta kona shi alhali yana sa ran falalarKa da rahamarKa,

أمْ كَيفَ يُحْرِقُهُ لَهيبُها وأنْتَ تَسْمَعُ صَوْتَهُ وتَرى مَكانَهُ
am kaifa tuhrikuhu lahibuha wa anta tasma'u sautahu wa tara makanahu,
Ko kuma yaya tartsatsinta zai kona shi alhali Kana ganin gurin da yake?

أمْ كَيفَ يَشْتَمِلُ عَليهِ زَفيرُها وأنْتَ تَعْلَمُ ضَعْفَهُ
am kaifa yashtamilu alaihi zafiyruha wa anta ta'alamu dha'afahu
Ko kuma ta yaya ruguginta zai ritsa shi alhali Ka san rauninsa?

أمْ كَيفَ يَتَقَلْقَلُ بَينَ أطْباقِها وأنْتَ تَعْلَمُ صِدْقَهُ
Am kaifa yatakalkalu baina atbakiha wa anta ta`alamu sidkahu,
( 28 )
Ko kuma yaya zai yi ta makyarkyata a tsakanin dabakokinta alhali Ka san gaskiyarsa?

أمْ كَيفَ تَزْجَرُهُ زَبانِيَتُها وهُوَ يُناديكَ يا رَبَّه
Am kaifa tazjuruhu zabaniyatuha wa huwa yunadika ya rabbah,
Ko kuma yaya zabaniyawanta za su gallaza masa alhali shi yana kiran Ka Ya Ubangiji?

أمْ كَيفَ يَرْجُوا فَضْلَكَ في عِتْقِهِ مِنْها فَتَتْرُكَهُ فيها
Am kaifa yarju fadhlaka fi itkihi minha fatatrukahu fiha,
Ko kuma yaya zai tsammaci falalarKa Kan 'yantar da shi daga cikinta amma Ka bar shi a cikinta?

هَيْهاتَ ما ذلِكَ الظُّنُ بِكَ ولا المَعْروفُ مِنْ فَضْلِكَ
haihata ma zalikaz zannu wa lal ma'arufu min fadhlika,
Har abada ba a taba zaton haka daga gare Ka ba kuma ba a taba sanin haka daga falalarKa ba,

ولا مَشْبِهٌ لِما عامَلْتَ بِهِ المُوَحِّدينَ مِنْ بِرِّكَ وإحْسانِكَ
wa la mushbihun lima amalta bihil muwahhidina min birrika wa ihsanika,
( 29 )
Kuma haka bai taba kama da abinda Ka aikata ga masu kadaita Ka ba, na alherinKa da kyautatawarKa,

فبِاليَقينِ أقْطَعُ لَوْلا ما حَكَمْتَ بِهِ مِن تَعْذيبِ جاحِدِيكَ
fabil yakini akda'u, lawla ma hakamta bihi min ta'azibi jahidika,
Saboda haka na hakikance ina mai cewa idan ba don abinda Ka yi hukunci da shi ba na azabtar da masu karyata Ka ba,

وَقَضَيْتَ بِهِ مِنْ إخْلادِ مُعانِديكَ لَجَعَلْتَ النّارَ كُلَّها بَرْداً وَسَلاماً وَما كَانَ لأحَدٍ فِيها مَقَرَّاً وَلا مُقاماً
wa kadhaita bihi min ikhladi mu'anidika laja'altan nara kullaha bardan wa salaman, wa ma kanat li ahadin fiha makarran wa la makaman,
Kuma Ka yanke na dawwamar da masu maka tsaurin kai gareKa ba to da Ka zamar da wuta baki dayanta ta koma sanyi amintacce kuma da babu wani guri a cikinta da zai kasance mazauni da madawwami,

لكِنَّكَ تَقَدَّسَتْ أسْماؤُكَ أقْسَمْتَ أنْ تَمْلأها مِنَ الكافِرينَ
( 30 )
lakinnaka takaddasat asma'uka aksamta an tamla'aha minal kafirina
Sai dai kuma sunayenKa sun tsarkaka Ka riga ka rantse kan za Ka cika ta da kafirai,

مِنَ الجِنَّةِ والنّاسِ أجْمَعينَ وأنْ تُخَلِّدَ فيها المُعانِدِينَ
minal jinnati wan nasi ajma'in wa an tukhallida fihal mu'anidin
Daga cikin aljannu da mutane baki daya, kuma za Ka dawwamar da masu tsaurin kai a cikinta,

وأنْتَ جَلَّ ثَناؤُكَ قُلْتَ مَبْتَدِءاً وتَطَوَّلْتَ بالإنْعامِ مُتَكَرِّماً
wa anta jalla thana'uka kulta mubtadi'an, wa tadawwalta bil'inami mutakarriman,
Kuma yabonKa ya daukaka Ka fada tun da farko, kuma Ka yawaita ni'ima da karimci

أفَمَنْ كَانَ مُؤْمِناً كَمَنْ كَانَ فاسِقاً لا يَسْتَوونَ
afa man kana muminan kaman kana fasikan la yastawun.
Ashe wanda yake mumini zai zamanto kamar wanda yake fasiki? Sam ba za su zama daya ba,

إلهي وَسَيِّدي فَأسْألُكَ بالقُدْرَةِ الَّتي قَدَّرْتَها
( 31 )
Ilahiy wa sayyidiy, fa'as'aluka bil kudratil latiy kaddartaha,
Ya Ubangijina Ya Shugabana, don haka ina rokon Ka da kudurarKa, wadda Ka kaddara kome da ita,

وبالقَضِيَّةِ الَّتي حَتَمْتَها وَحَكَمْتَها وَغَلَبْتَ مَنْ عَلَيهِ أجْرَيْتَها
wa bil kadhiyyatil latiy hatamtaha wa hakamtaha, wa galabta man alaihi ajraitaha,
Kuma da hukuncinka wanda Kake tabbatarwa Kake hukuntawa kuma Ka rinjayi duk wanda Ka gudanar da shi a kansa,

أنْ تَهَبَ لي في هذِهِ الليلة وفي هذه السّاعَةِ كُلَّ جُرْمٍ أجْرَمْتُهُ
an tahaba liy fiy hazihil lailati wa fi hazihis sa'ati kullajurmin ajramtuhu,
Ka yafe mini, a cikin wannan dare a cikin wannan sa'a duk wani laifi da na aikata,

وكُلَّ ذَنْبٍ أذْنَبْتُهُ وَكُلَّ قَبِيحٍ أسْرَرتُهُ وَكُلَّ جَهْلٍ عَمِلْتُهُ كَتَمْتُهُ أو أعْلَنْتُهُ أخْفَيْتُهُ أو أظْهَرتُهُ
wa kulla zanbin aznabtuhu, wa kulla kabihin asrartuhu wa kulla jahalin amiltuhu katamtuhu aw a'alantuhu, akhfaituhu aw azhartuhu,
( 32 )
Da dukkan wani zunubi da na yi, da dukkan wani mummunan da na yi a boye, da dukan wani jahilci da na aikata, na boye shi ne ko na sanar da shi,

وَكُلَّ سَيِّئَةٍ أمَرتَ بإثْباتِها الكِرامَ الكاتِبينَ الّذينَ وَكَّلْتَهُم بِحِفظِ ما يَكُونُ مِنّي
wa kulla sayyi'atin amarta bi'ithbatihal kiramal katibin, allazina wakkaltahum bi hifzi ma yakunu minniy,
Da kuma dukan wani mummunan aiki wanda Ka umarci marubuta masu girma su rubuce shi. Wadanda Ka wakilta su da su kiyaye duk abinda zai faru daga gurina,

وَجَعَلْتَهُمْ شُهُوداً عَلَيَّ مَعَ جَوارِحي وَكُنْتَ أنْتَ الرَّقيبَ مِنْ وَرائِهِمْ والشّاهِدَ لِما خَفِيَ عَنْهُم وَبِرَحْمَتِكَ أخْفَيتَهُ وبِفَضْلِكَ سَتَرتَهُ
wa ja'altahum shuhudan alayya ma'a jawarihiy, wa kunta antar rakiba alayya min wara'ihim , wa shahida lima khafiya anhum wa bi rahmatika akhfayta, wa bifadhlika satartahu,
( 33 )
Kuma Ka sanya su shaidu a kaina tare da gabobina, kuma Kai Kai ne mai lura da ni baicin su, kuma Kai ne, shaida a kan duk abinda ya boyu daga gare su, don haka Ka rufe Ka suturce da falalar Ka,

وأنْ تُوَفِّرَ حَظِّي مِنْ كُلِّ خَيرٍ تُنْزِلُهُ أو إحْسانٍ تُفَضِّلُهُ
wa an tuwaffira hazziy min kulli khairin tunziluhu, aw ihsanin tufdhiluhu,
Kuma Ka cika mini kasafina daga duk wani alheri da Ka yi baiwa da shi,

أو بِرٍ تَنْشُرُهُ أو رِزْقٍ تَبْسُطُهُ أو ذَنْبٍ تَغْفِرُهُ أو خَطأٍ تَسْتُرُهُ
aw birrin tanshiruhu, aw rizkin tabsiduhu, aw zanbin tagfiruhu, aw khada' in tasturuhu.
Ko kuma kyakkyawan abu da Ka yada shi, ko kuma dukiya da Ka kwarara ta, ko kuma zunubi da Ka gafarta shi, ko kuma kuskure da Ka suturce shi.

يا رَبِّ يا رَبِّ يا رَبِّ يا إلهي وسَيِّدي ومَوْلايَ
Ya Rabbi Ya Rabbi Ya Rabbi, Ya ilahiy wa Sayyidiy wa mawlaya,
Ya Ubangijina, Ya Ubangijina, Ya Ubangijina, Ya abin bautata, Ya Shugabana, Ya Majibincina,
( 34 )

ومَالِكَ رِقِّي يا مَنْ بِيَدِهِ ناصِيَتي
wa malika rikkiy, ya man biyadihi nasiyatiy,
Ya Mamallakin 'yancina, ya wanda makwarkwadata ke hannunSa,

يا عَليماً بِضُرِّي ومَسْكَنَتي يا خَبيراً بِفَقْري وَفاقَتي
ya aliman bi dhurriy wa maskanatiy, ya khabiran bi fakriy wa fakatiy,
Ya Masanin cutata da tsananina, Ya Masanin boyayyen talaucina da tsananin bukatata,

يا رَبِّ يا رَبِّ يا رَبِّ أسألُكَ بِحَقِّكَ وقُدْسِكَ وأعْظَمِ صِفاتِكَ وأسْمائِكَ
Ya Rabbi Ya Rabbi Ya Rabbi, as'aluka bihakkika wa kudsika wa a'azama sifatika wa asma'ika
Ya Ubangijina, Ya Ubangijina, Ya Ubangijina. Ina rokon Ka da hakkinKa da tsarkinKa da mafi girman siffofinKa da sunayenKa,

أنْ تَجْعَلَ أوْقاتِي في اللَّيلِ والنَّهارِ بِذِكْرِكَ مَعْمُورَةً وبِخِدْمَتِكَ مَوصُولَةً
an taj'ala awkatiy fil laili wan nahari bi zikrika ma'amuratan, wa bikhidimatika mawsulatan,
( 35 )
Ka sanya lokutana na dare da rana su zama rayayyu da zikirinKa, kuma sadaddu dahidimarKa,

وأعْمالِي عِنْدَكَ مَقْبُولَةً حَتّى تَكُونَ أعْمالِي وَأوْرادِي كُلُّها وِرْداً واحِداً وَحالِي في خِدْمَتِكَ سَرْمَدا
wa a'amaliy indaka makbulatan, hatta takuna a'amaliy wa awradiy kulluha wirdan wahidan, wa haliy fi khidmatika sarmadan,
Kuma ayyukana da wurudodina su zama bai daya, halina kuma ya zama hidima gare Ka har abada.

يا سَيِّدي يا مَنْ عَلَيهِ مُعَوَّلي يا مَنْ شَكَوْتُ إليهِ أحْوالي
ya sayyidiy ya man alaihi mu'awwaliy, ya man ilaihi shakautu ahwaliy,
Ya shugabana, Ya wanda gare shi nake kai kukan halayen da nake ciki,

يا رَبِّ يا رَبِّ يا رَبِّ قَوِّ على خِدْمَتِكَ جَوارِحي
Ya Rabbi Ya Rabbi Ya kabbi, kawwi ala khidmatika jawarihiy,
Ya Ubangijina Ka karfafa gabobina, wajen hidimarka,
( 36 )

واشْدُدْ على العَزيمَةِ جَوانِحِي
washdud alal azimati jawanihiy,
Ka tsananta kirjina wajen himma,

وَهَبْ لِيَ الجِدَّ في خَشْيَتِكَ وَالدَّوامَ في الإتِّصالِ بِخِدْمَتِكَ
wa hab liyal jidda fr khashyatika, wad dawama fit ,ali bikhidmatika,
Kuma ka ba ni dagewa wajen tsoron Ka da dawwama a sadarwa da Kai,

حَتَّى أسْرَحَ إلَيكَ في مَيادينِ السَّابِقينَ
hatta asraha ilaika fi mayadinis sabikina,
Har na garzaya zuwa gare Ka a ciki masu tserarreniya,

وَأُسْرِعَ إلَيكَ في المُبادِرينَ وأشْتاقَ إلى قُرْبِكَ في المُشْتاقِينَ
wa usri'a ilaika fil mubadirina wa ashtaka ila kurbika fil mushtakina,
Kuma in gaggauta zuwa gare Ka cikin masu zaburowa kuma in yi dokin kusanci gare Ka cikin masu doki,
( 37 )

وأدْنُوَ مِنْكَ دُنُوَّ المُخْلِصينَ وَأخافَكَ مَخافَةَ المُوقِنِينَ وأجْتَمِعَ في جَوارِكَ مَعَ المُؤْمِنينَ
wa adnuwa minka dunuwal mukhlisin, wa akhafaka makhafatal mukinin, wa ajtami'a fi jiwarika ma'al muminin.
Kuma in kusato gare da kusantowa irinta masu tsarkin niyya, kuma in ji tsoronKa tsoro irin na masu yakini kuma in hade a kusace gare Ka tare da muminai.

اللَّهُمَّ وَمَنْ أرادَني بِسُوءٍ فأرِدْهُ وَمَنْ كادَنِي فَكِدْهُ
Allahumma wa man aradaniy bi suw'in fa aridhu waman kada niy fa kid'hu
Ya Allah duk wanda ya nufe ni da mummuna to Ka nufe shi, duk wanda ya yi mini mugun tanadi to Ka yi masa mugun tanadi,

واجْعَلْني مِنْ أحْسَنِ عَبِيدِكَ نَصيباً عِنْدَكَ وأقْرَبِهِمْ مَنْزِلَةً مِنكَ وأخَصِّهِمْ زُلْفَةً لَدَيكَ
waj' alniy min ahsani abiydika nasiban indaka, wa akrabihim manzilatan minka, wa akhassihim zulfatan ladaika,
( 38 )
Kuma Ka sanya ni daga cikin mafifitan bayinKa masu rabo a gurinKa, da kuma mafi
kebantarsu kusantaka gare Ka,

فإنَّهُ لا يُنالُ ذلِكَ إلاّ بِفَضلِكَ
fa'innahu la yanalu zalika illa bi fadhlika
Kuma babu wani mai samun haka sai dai da falalarKa,

وَجُدْ لِي بِجُودِكَ واعْطِف عَلَيَّ بِمَجْدِكَ واحْفَظني بِرَحْمَتِكَ
wa jud liy bi judika, wa'adif alayya bi majdik, wahfazniy bi rahmatik,
Ka yi baiwa gare ni da kyautarKa, kuma Ka tausasa mini da girmanKa, kuma Ka kare ni da rahamarKa,

واجْعَلْ لِسانِي بِذِكْرِكَ لَهِجاً وَقَلْبي بِحُبِّكَ مُتَيَّماً
waj'al lisaniy bi zikrika lahijan, wa kalbiy bihubbika mutayyaman,
Ka sanya harcena ya zama tare da zikirinKa, zuciyata duka ta dulmuye da soyayyarKa,

وَمُنَّ عَلَيَّ بِحُسْنِ إجابَتِكَ وأقِلْنِي عَثْرَتي واغْفِرْ لِي زَلَّتي
wa munna alayya bihusni ijabatika, wa akilni athratiy, wagfir liy
zallatiy,
( 39 )
Ka yi mini baiwa da kyakkyawar amsawarKa, Ka share mini tubatubaina, Ka gafarta tabewata,

فإنَّكَ قَضَيْتَ على عِبادِكَ بِعِبادَتِكَ وأمَرْتَهُمْ بِدُعائِكَ وَضَمِنْتَ لَهُمُ الإجابَةَ
fa'innaka kadhayta ala ibadika bi ibadatika, wa amartahum bi du'a'ika, wa dhaminta lahumul ijabata,
Domin Kai Kai ne ka yi hukunci ga bayinKa da ibadarka kuma Ka umarce su da addu'a rKa,

فَإلَيْكَ يا رَبِّ نَصَبْتُ وَجْهِي وَإلَيْكَ يا رَبِّ مَدَدْتُ يَدِي
fa ilaika ya Rabbi nasabtu wajhiy, wa ilaika ya Rabbi madadtu yadiy,
Don haka gareKa ya Ubangiji nake juya fuskata, kuma gare Ka nake mika hannuna,

فَبِعِزَّتِكَ اسْتَجِبْ لي دُعائِي وبَلِّغْني مُناي
fabi izzatika istajib liy du'a'iy wa balligni munaya,
Don girman daukakarKa Ka amsa mini addu'ata Ka isar mini burina,
( 40 )

ولا تَقْطَعْ مِنْ فَضْلِكَ رَجائِي واكْفِنِي شَرَّ الجِنِّ والإنْسِ مِنْ أعْدائِي
wa la takda'a min fadhlika raja'i wakfiniy sharral jinni wal insi min
a'ada'iy
Kada Ka yanke mini kaunata daga falalarKa, Ka iyar mini sharrin aljanu da mutane daga cikin makiyana.

يا سَريعَ الرِّضا إغْفِر لِمَنْ لا يَمْلِكُ إلاّ الدُّعاءَ فَإنَّكَ فَعَّالٌ لِمَا تَشاءُ
ya sari'arridha, igfir liman la yamliku illad du'a, fa'innaka faalun lima tasha'u
Ya mai saurin yarda, Ka gafarta wa wanda bai mallaki kome ba sai addu'a domin Kai mai aikata abinda Ka so ne.

يا مَنْ اسْمُهُ دَوَاءٌ وَذِكْرُهُ شِفاءٌ وطاعَتُهُ غِنَىً
ya man ismuhu dawa'un, wa zikrihu shifa'un, wa da'atuhu ginan
Ya wanda sunanSa magani ne, kuma zikirinSa waraka ne kuma biyayya gare Shi wadata ce,

ارْحَمْ مَنْ رَأسُ مَالِهِ الرَّجاءُ وَسِلاحُهُ البُكاءُ
( 41 )
irham man ra'asu malihir Raja'u, wa silahuhul buka'u,
Ka yi jin kai ga wanda uwar - kudinsa shi ne sa tsammani, makaminsa kuma shi ne kuka.

يا سابِغَ النِّعَمِ يا دافِعَ النِّقَمِ يا نُورَ المُستَوحِشِينَ في الظُّلَمِ
Ya sabigan ni'am, ya dafi'an nikam, Ya nural mustauhishina fiz zulami,
Ya mai kwarara ni'ima, Ya mai kore wahalbalu Ya hasken masu kewa a cikin duffai,

يا عَالِماً لا يُعَلَّمْ صَلِّ على مُحَمَّدٍ وآلِ مُحَمَّدٍ وافْعَلْ بِي ما أنْتَ أهْلُهُ
Ya Aliman la yu'allam, salli ala Muhammadin wa ali Muhammadin, waf'al biy ma anta ahluhu,
Ya masani wanda ba a sanar da shi, Ka yi dadin tsira ga Muhammadu da zuriyarsa Ka aikata abinda yake kai ma'abucinSa ne da ni,

وَصَلَّى اللَّهُ على رَسُولِهِ والأئِمَّةِ المَيَامِينَ مِنْ آلِهِ وَسَلَّمَ تَسْليماً كَثيراً
Wa sallallahu ala Rasulihi wal a'immatil mayamina min alihi wa sallama tasliman kathiran.
( 42 )
Kuma Allah Ya yi dadin tsira ga Manzonsa, da Imamai masu daraja daga Zuriyarsa kuma Ya ba su aminci, aminci mai yawa.