Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, tsira da Aminci su tabbata ga mafificin halittanSa Annabi
Muhammadu da zuriyarsa tsarkakakku, da sahabansa masu tsarkin niyya da kuma duk wanda ya bi su da
kyakkyawan aiki har zuwa ranar tashin kiyama. Bayan haka: Tun farkon bayyanar addinin Musulunci ya
zuwa yau Musulmai sun yi imani da ingancin abinda Annabi (S.A.W.A.) ya ba albishir da shi game da
bayyanar mutum daga zuriyar gidansa a karshen zamani - wanda ake kira - Mahadi zai cika duniya da
daidaito da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci da ja'irci saboda haka jira da sauraron da
muminai suke yi wa Mahadi (A.S.) ya zama na tsawan karnoni babu wanda ya baude ya kauce musu illa
'yan kalilan daga masu da'awar tajdidi da canji sakamakon tasirantuwar da suka yi da wasu
rubuce-rubucen, masanan Turai 'yan a sani a gurbata, wadanda ba bincike ba ne a kan abu ayyananne.
Irinsu rubuce-rubucen Fan Flatun da Donald Son da Golad Zihar da makamantansu 'yan a sani a gurbata
wadanda suke ganin sun yi nazari da bincike na karya kan akidojin Musulmi hatta su ka kai ga karyata
lamarin bayyanar Mahadi (A.S.) a karshen zamani. Wasu na iya zamantowa sun rudu da salonsu na
kyakkyawar niyya dangane da kira zuwa ga tajdidi da sabunta nazari wajen fahintar al'amuran Musulunci
da kuma kokarin bayyana dacewarsu da zamantowarsu daidai da manufofin zamani da suka farlanta wayewa
irin ta yanzu, suka ga cewa musanta akidar bayyanar Mahdi martani ne kwakkwara ga kiran Addinin kirista
- kuma mai gamsarwa ne ga tafarkin 'yan a sani a gurbata - wadanda suka nufo addinin Musulunci suka
suranta shi a rubuce-rubucensu da cewa wani kwaure ne da rayuwa ba ta bubbuga a cikinsa. Haka nan ne
tasirin darrusan masana Turai 'yan a sani a rusa ya bayyana a kan fahimtar wasu daga cikinmu, wanda
hakan ya samar da baraka daga ciki, inda zaka ga an shiga yin tawilin tabbatattun adubuwa a addini da
kuma sa shakku ga me da wani sashe nasa kamar al'amarin bayyanar Imam Mahadi (A.S.) a karshen zamani
kuma mai yiwuwa za ka ji taraddudi mai gundurarwa daga maganganun 'yan a sani a gurbatan, dangane da
al'amarin bayyanar.
Hakan ba za ta taba yiwuwa ba idan ba don dauka mataki ba, ba tare da kyakkyawan nazari ba daga bangaren irin wannan gurguwar fahimtar da kuma tasirantuwa da ita har zuwa matsayin imani da cewa ita ce hakika da lalle ne a sallama a mika wuya game da ita duk kuwa da irin dattin da take kunshe da shi da kuma son kan da ke tare da ita wajen daldalewa da kuma yanke hukunci, da makirci ga Musulunci da musulmi, ta yaya ba haka ba alhali kuwa ga Gzolad Zihar da Davi Wir, da Mac Donald da Bandaly, Taw Zie suna bayyana cewa Alkur' ani(1) na da tuka da warwara.? Babu mamaki mu sami wani daga cikin masu wa'azin addinin Kirista ya soki akidar Musulmi dangane da
bayyanar Imam Mahadi (A.S.) duk kuwa da cewa wannan akida ta bayyanar ba wai ta kebantu da Musulmi ba ne su kadai dinsu kamar yadda zai zo a bayanan wannan gabatarwar:
Gamewar Duniya da Akidar Mahadi lalle akidar bayyanar babban mai tserarwa wanda zai yada adalci da jin dadi idan ya bayyana a karshen zamani, kuma ya kawar da zalunci da danniya a ko'ina cikin duniya baki daya, ya tabbatar da adalci da daidaito a hukuma mayalwaciya, wannan akida ce da dukkan ma'abuta saukakkun addinai ukun nan suka yi imani da ita kuma mafi yawan al'ummu suka yarda da ita. Yahudawa sun yi imani da ita, kamar kuma yadda Kirista suka yi imani da dawowar Annabi Isa (A.S.) haka kuma mabiya addinin Zordasta sun yi imani da jiran dawowar Brahma Shah kazalika Kiristan Ahbash suna sauraron dawowar mai mulkinsu Tiyu'dur tamkar dai Mahadi a karshen zamani, har ila yau masu addinin Hindu sun yi imani da dawowar Fishino, kamar dai Majusawa dangane da imaninsu game da rayuwar Ushidar. Kazalika zamu iske mabiya addinin Budanci suna jiran bayyanar Ruza kamar yadda Asbaniyawa ke jiran sarkinsu Rusarik da kuma Mangolawa masu jiran jagoransu Jangiz Khan.
An samu wannan akidar a gurin mutanen Masar tun da dadewa kamar kuma yadda aka samu a dadaddun littafan mutanen kasar Sin. Bugu da kari kuma an samu bayanai karara a gurin hazikan yammaci da masana Falsafa kan cewa duniya na jiran babban mai gyara wanda zai jagoranci al'amura ya kuma hade kan kowa da kowa a karkashin tuta da take guda:
Daga cikinsu akwai: Mashahurin masanin Falsafar nan na kasar Ingila Betrand Russel inda ya ce:
"Duniya na jiran wani mai gyara ya hade kan duniya a karkashin tuta guda da take guda."(2)
Daga cikinsu akwai: Allama ANESHTYN mai littafin "An Nazariy Nisbiyya ya ce: "Lalle ranar da sulhu da zaman lafiya za su game duniya baki daya mutane kuma su zama masoyan juna kuna 'yan'uwan juna baki daya ba shi da nisa(3).
Fiye ma da dukkan wannan shi ne abinda Mashahurin Masanin Falsafar kasar Ingila Barnard Show ya zo da shi yayin da ya yi bushara da zuwan wani Mai gyara a littafinsa "Man and Super Man".
Dangane da wannan kuma babban malamin nan Abbas Mahmud Al-Akkad yana cewa a cikin littafinsa "Barnard Show" a karin bayanin cewa: "Ya tabbata gare mu cewa super Man ba abu ne da ba zai yiwu ba kuma lalle kira zuwa gare shi ba zai rasa kanshin gaskiya tabbatacciya(4) ba."
Dangane da Musulmi kuwa dukkaninsa a bisa sabanin mazhobobinsu da kungiyoyinsu sun yi imani da bayyanar Imam Mahadi (A.S.) a karshen zamani a bisa asasin abinda Manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi bushara da shi, babu wata Mazhaba da ta kebantu da wannan imani sabanin wata. Malaman Ahlussunna da dama sun bayyana imaninsu dangane da akida game da Mahadi tun daga Malaman karni na uku hijiriyya har zuwa yau cewa wannan al'amari ne da suka yi ittifaki a kansa, kai yana ma daga cikin akidarsu baki daya. Abu da ya fi wannan
ma shine Fatawar Malamansu kan wajabcin kashe wanda ya karyata bayyanar Mahadi, wasunsu kuma suka ce wajaba ya yi a ladabtar da shi da dukan da zai luguiguita shi ya wulakanta har sai ya dawo ga gaskiya da kuma daidai a bisa tilas -gwargwadan bayani-kamar yadda za mu yi ishara gare shi a bisa asasin fatawoyin da suka fita daga Mazhabobi hudu.
Saboda haka ne ma Ibin Khaldun ya ce yana mai bayanin akidar Musulmi game da bayyanar Mahadi:
"Ka sani cewa abu da yake mashahuri a tsakanin dukkan mabiya Musulunci a bisa shudewar zamani shi ne cewa babu makawar bayyanar wani mutum daga Ahlul Bait a karshen zamani wanda zai taimaka wa addini ya tabbatar da adalci, kuma Musulmi su bi shi, ya shugabanci dukkan kasashen Musulmi kuma ana kiran sa Mahadi (5). Kuma Malam Ahmad Amin na Al-Azhar ta kasar Masar duk kuwa da tsaurin ra'ayin su biyun game da wannan akida, sa'an nan/ Sai ya kara da cewa yana bayyana ra'ayin Ahlussunna., dangane da ita:
"Amma Ahlussunna su ma sun yi imani game da(6) ita." Sa'an nan kuma sai ya ambata ainihin abinda Ibn Khaldun ya(7) ambata sa'an nan kuma yace:
"Ibn Hajr ya kididdige adadin hadisan da aka ruwaito game da Mahadi, ya iske su sun kai wajen hamsin. Sa'an kuma sai ya ambata abinda ya karanta daga Littafan Ahussunna dangane da Mahadi yace: Na karanta Risalar Malam Ahmad bin Muhammad Rinus Sadik a raddin da ya yi wa Ibin Khaldun wadda ya sa wa suna "Ibrazul
Wahm" wato "Bayyana Wahamin da ke akwai daga maganar Ibin Khaldun; ya kare maganar Ibin Khaldun game da sukansa a kan hadisan da suka zo game da Mahadi kuma ya tabbatar da ingancinsu, sa'an nan ya ce: Ai sun kai matsayin tawaturi(8) (hadisi mai Maruwaita da yawan gaske yadda ba'a kokwantosa).
A wani gurin kuma yana cewa: Na karanta wata Risalar kuma dabam dangane da wannan al'amarin wadda kanunta shi ne: "Al-Iza'atu Lima Kana wa ma Yakunu Baina Yadayyis Sa'ati "wato" sanar da abinda ya kasance da kuma wanda zai kasance kafin sa'a (Tashin kiyama), na Abi Tayyib bin Abi Ahmad Bin Abil Hasanil Hasani"(9)
Har ila yau kuma ya ce:
"Lalle Imam Shaukani ya rubuta littafi dangane da ingancin haka ya sa masa suna' At-Taudhiu fi Tawatri Ma Ja'a fil Muntazari wad Dhajjali wal Masihi wato "Bayani game da tawaturancin,(yawan maruwaitan,) abinda ya zo game da wanda ake jira da Dujal da kuma Al-Masihu." Saboda haka babu bambanci tsakanin Shi'a da Ahlussuna game da hadisan imani dangane da bayyanar Mai Tserarwa matukar dai Ahlussunna sun riga sun sami hadisai hamsin game da haka daga tafarkunansu kama sun kidaya bayyanar Mahadi daga cikin alamomin tashin alkiyama, kuma sun tabbatar da bacin maganar Ibin Khaldun wajen raunana wasu hadisai wadanda suka zo dangane da haka da ya yi, sa'an nan kuma sun rubuta Littafai ko sun yi maganganu wajen raddi a kan haka a kai a kai cikin littafai da kuma Risaloli, kai babu ma bambanci
tsakanin dukka Musulmi da sauran mabiya saukakkun addinai da al'ummu dangane da imani da asalin koda kuwa sun sassaba a kan ainihin wane ne a ayyane tare kuma da ittifakin musulmi a kan cewa sunansa Muhammadu ne tamkar sunan Annabi (S.A.W.A.) kuma lakabinsa a gurinsu shi ne Mahadi. Daga nan ne za a sani cewa ittifakin Ma'abuta sauran addinai da yawancin al'ummu da kabilu da hazikan yammaci da Masana Falsafa, tare da bambancin addinai, da sabanin akidu, da rarrabar ra'ayoyi da tunani da al'adu - a kan asalin akidar ba zai yiwu ya zamana haka nan babu madogara ba saboda koruwar tabbatar makamancin wannan haka sarmadan - Idan kuma muka kara a kan ittifakin da mabiya mazhabobin addinin musulunci dabam-dabam suka yi baki daya a kan ingancin imani da bayyanar Imam Mahadi a karshen zamani da kuma cewa daga Ahlil Bait (A.S.) yake - kamar yadda zai zo filla-filla, to daga nan za a san cewa wannan ittifakin babu makawa ya zamanto yana daga cikin ittifakin wannan al'umma wadda ba zai yiwu ta zamana ta yi shi a kan karya ba, kamar yadda yake tabbatacce a gurin bayaninsa yayin nan kuma sabanin ayyana ko wanene shi ba zai cutar da imaninsu da bayyanar Mahadi daga Ahlul Baiti (A.S.) ba , domin akwai yiwuwar sanin hakikaninsa daga littafan musulmi da ake dogaro da su saboda sanin su da aka yi kan bin hanyar kawo hadisai ta hanyar ji da fada da baki da baki da kuma sadarwa zuwa jigon shari'a da kuma abinda babu kini gare shi na daga tarihin rayuwar al'ummun duniya baki daya
Mu kuma duk da haka muna cewa:
Imanin ma'abuta littafi wato Ahlul kitabi da bayyanar wani mai tserarwa a karshen Zamani ba ya zama nesa da kasancewar addinan nasu sun yi bushara da Mahadi daga
Ahlul Bait (A.S.) ba kamar dai bushararsu game da Annabinmu (S.A.W.A.) sai dai kawai sun boye haka ne saboda taurin kai da girman kai sai dai wadanda suka yi imani da Allah daga cikinsu kuma suka ji tsoron Allah.
Abinda ke cikin littafan Attaura game da busharar bayyanar Mahadi a karshen zamani, kamar yadda nassin abinda marubucin nan Abu Muhammad al-Ordan ya rubuta a littafin "Safaru Armiya" ga dai nassinsa kamar haka:"ku hau ya ku dawakai ku motsa ababan hawa domin zaburar da jaruman kausha da kauda masu kamawa... da kuma Diyun mai rike kwari, wannan ranar shugaban rundunoni, ranar narko domin ramuwar gayya a kan makiyansa, sai takobi ya ci ya koshi/... domin shugaban rundunoni da aka yanka a kasar Arewa a tekun yufret"(10) kuma akwai wani abu da ya fi wannan bayyana sosai, Sa'id Ayyub masani mai binciken nan malamin Ahlus suna a littafinsa mai suna al-Masihu Al-Dajjal, ya ce: "Ka'abi ya ce: An rubuta a Asfarul Anbiya' : Mahdi babu wani aibi a aikinsa". Sa'an nan sai ya yi karin bayani a wanan nassin ya ce, "Na shaida cewa na same shi kamar haka a littafan Ahlul kitab suna bin diddigin al'amarin Mahadi (A.S.) kamar yadda suke bin diddigin hadisai game da kakansa (S.A.W.A.). Hadisan sifrur Ru' ya sun yi ishara ga wata mace wadda mazaje goma sha biyu za su fito daga tsatsonta sa'an nan ya yi ishara ga wato matar kuma wata wadda za ta haifi mutum na karshe da tsaton kakarsa, sa'an nan ya ce: Wannan mata ta karshen hadarurruka za su dabaibaye ta kuma sai ya sanya alamar hatsarurrukan da za su gewaye wannan matar da sunan "Tannayu ya ce" Tannayu ya
tsaya a gaban mata da ke hauare har ta haihu kuma za a hadiye dan nata da zarar ta haihu. Sifrur Ru'uya na 3 sakin layi 12, wato dai hukuma na son ta halaka wannan yaron amma bayan haihuwar yaron, Barkli yana cewa a Tafsirinsa, "yayin da hatsarorin suka dumfaro ta sai Allah ya dauke danta ya kare shi." Nassin "Allah ya dauke danta."
Sifru Ru'uya 1215 wato dai Allah ya boye wannan yaron kamar yadda Barkli yake fada.
Sifru ya ce boyuwar wannan yaron za ta kasance kwana dubu da dari biyu da sittin wannan shi ne gwargwadan lokacin da ke da alama a gurin Ahlulkitab. Sa'an nan game da zuriyar matar baki daya sai Barkli ya ce "Lalle Tannayu zai yi yaki mai tsanani da zuriyar matar kamar yadda sifru ya ce:
"Sai Tannayanu ya fushi da matar sa'an nan ya tafi don ya shirya yaki da sauran zuriyar ta wadanda ke kiyaye Wasicin Allah."(11) Sifru Ru'uya na 12 shafi na 13.
Wannan kuma koda yake, bai inganta ba ga Musulmi ya kafa hujja da abinda ke cikin littafan tsoho da saban alkawari saboda irin gurbatawar da kuma musanyawar da aka yi musu saidai kuma duk da haka yana tabbatar da masaniyar Ahlul Kitabi game da Mahadi a sarari, sa'an nan kuma sabaninsu dangane da cewa wane ne shi a ayyane, domin ba dukkan abinda Musulunci ya zo da shi bane ya zama ya kebanta da shi daga addinan da suka gabata, a'a akwai al'amura da dama na asasi wadanda
Musulunci ya zo da su kuma sun kasance a shari'un da suka gabata kafin shi.
Shatibi ya ce: "Ayoyi da dama da aka ba da labari a cikinsu game da hukunce-hukunce na asasi a addinan da suka gabata suna cikin Shari'armu kuma babu bambanci a tsakaninsu."
Idan har haka ya tabbata, to imanin Musulmi game da ingancin abinda Manzo (S.A.W.A.) ya yi bushara dangane da bayyanar wani Mutum daga Zuriyarsa a karshen zamani kuma har ila yau wannan akidar ta kasance a gurin Ahlul kitab (wato Yahudu da Nasara) ko kuma wasunsu da suka gabaci addininsu kuma hakan ba zai fitar da shi daga da'irar addinin Musulunci ba bayan Annabi (S.A.W.A.) ya yi bushara da shi bayan kuma yin imani da cewa shi Annabi (S.A.W.A.) "Ba ya Magana a bisa son rai ba kome ba ne illa wahayi da aka yi.(12)
Amma dangane da imanin al'uummu daban-daban game da ainihin wannan akida kamar yadda ya riga ya gabata za a iya fassara shi a bisa asasin cewa akidar bayyanar Mai tserarwa ba ta saba da dabi'ar mutum da damuwoyinsa da hanga-hangensa ba. Idan da Mutum ya yi tunani koda dan kadan dangane da ittifakin yawancin al'ummu game da ainihin akidar to lalle da ya fahimci cewa akwai hikima mawadaciya wajen tafi da wannan duniyar wadda mutum zai nemi karin karfi daga gare ta wajen tabbata da tsayiwa daidai a gaban fandarewar da yake gani da kuma Zalunci da dagawa, kuma ba zai bar debe tsammaninsa ba ba tare da ya yi guzuri da sa tsammani da kyawun fatan cewa adalci lalle ne ya yi rinjaye ba.
Amma sabanin ma'abuta addinai magabata kuwa da kuma al'ummun da suka gabata wajen tantance sunan wannan Mai tserarwa, babu wata dangantaka da yake da ita a kan musa abinda Annabi (S.A. W.A.) ya yi bushara game da shi. Kuma babu wani abu da zai sa a yi bayanin rashin daidai dinsu game da ayyana wane ne shi wannan Mai tserarwar matukar dai addinin Musulunci ya riga ya dauki nauyin wannan al'amari mai muhimmaci, ya bayyana sunansa, girmansa, zuriyarsa, siffofinsa, rayuwarsa, alamun bayyanarsa da hanyar hukuncinsa
har ma hadisai masu hanyoyi dabam daban dangane da haka suka zo da adadin maruwaitansa daga bangaren Ahlussunna wadanda suka ruwaito hadisan sun kai sama da sahabbai hamsin kamar yadda manyan malamansu da mahaddatansu da masanan fikihunsu da hadisansu suka bayyana kuma za mu kawo hujjoji a kan haka daga bisani.
Amma dangane da sabanin Musulmi kuwa game da ayyana ainihin sunan Mahadi (A.S.) kamar yadda yake sananne tsakanin Ahlussunna da Shi'a, to babu wata hujja kome kankantarta kuwa asbilo da wannan sabani ga masanan Turai da 'Yan Korensu, sai dai ma akasin haka daga dalilai kwarara akan haka. Domin wannan irin sabani shigen sabani ne akan sanin wasu lamurra dangane da wani abinda babu kokonto cikin tabbatarsa. Kamar dai sabaninsu a kan Alkurani game da cewa shi dawwamamme ne ko fararre daga Allah, duk kuwa da cewa sun yi imani da kafircin wanda ya musa shi. To ka kintata wannan a kan sauran sabanin da ke akwai a sauran al'amuran akida ba jigonta ba.
____________
1- Littafn Almustashrikuna wal lslam na Dokta Irfan Abdulhamid shafi na 17 da Dira satun fil Fikril Falsafi al-Islami Dokta Hismuddin Al-Alusi shafi na 68, da Buhusun Fi Kur'anil Karim Dokta Abdul Jabbar Shararab shafi na 52-54, An kawo kamar yadda muka gabatar game da fadin wasu makiya musulunci cewa Kur'ani akwai tuka da warwara a cikinsa, to sai da an karyata wannan zargi a wadannan littattafa da muka ambata.
2-Al-Mahdi Maw'ud wa daf'us shubhat anhu Sayyid Abdur Ridha Shahristani Shafi na 6.
3-Al-Mahdi Maw'ud wa daf us shubhat anhu shafi na 7.
4-Barnard Show: Abbas Mahmud Al-Akkad shafi na 124-125.
5- Tarikhu Ibin Khaldun shafi na 555 fasali na 52.
6- Al-Mahdi wal Mahadawiyya na Ahmad Amin shafi na 41.
7- Al-Mahdi wal Mahadawiyya shafi na: 110.
8 -Almahdi wal Mahdawiyya shafi na 106.
9 -Al-Mahdi wal Mahdawiyya shafi na 109
10- Littafi mai tsrki a karkashin Mahjer Audata Mahawish Abu Muhammad al-Urduni:155, nassin an ciro shi ne daga Safaru Irimiyau na 36 Shafi na 211.
11- Al-Masih Al -Aajal na Sa'id Ayyab bugu na uku, shafi na 379-380. Na ce: Mahadi a gurin Shi'a shi ne Imami na goma sha biyu daga Imaman Ahlul Bait na farkonsu shi ne Ali Ibin Abi Talib (A.S.) kuma hadisi game da Mahadi kuwa gaskiya ne kuma shi daga 'ya'yan Fatima yake kuma akwai tabbacin ingancinsa kuma a bayyane yake an ruwaito shi daga hanyoyi daban-daban daga Ahlussunna kamar yadda za mu kawo maka kuma a gurin Shi'a shi ne wanda aka haife shi daga 'ya'yan Fatima na goma sha biyu, uku daga cikinsu kai tsaye,
wadanda su ne Hasan da Husaini da Muhsin, Tara kuma ba kai tsaye ba kuma su ne Imamai tara daga 'ya'yan Imam Husain (A.S.). Amma 'ya'yan Hasan (A.S) suma daga 'ya'yan Fatima (A.S.) suke sai dai kuma an cire su daga cikin adadi goma sha biyun saboda su ba sa daga cikin Imamai. Kuma wannan ba zai hada da wanda ba Imami ba wato Muhsin domin shi ma Fatima (A.S.) ce ta haife shi kai tsaye,saboda haka ne Malam Sa'id Ayyub ya ce: "Wadannan sune siffofin Mahadi, kuma har ila yau sune siffofinsa a gurin Shi'a Imamiyya masu bin Imamai goma sha biyu." Sa'an sai ya yi karin bayani a gefen shafi na 379 da abinda da ke ishara ga kusancin siffofin. Wannan kuwa koda yake abu ne mai yiwuwa sai dai imanin Shi'a da wasunsu dangane da bayyanar Mahadi (A.S.) a karshen zamani bai zamanto a bisa asasin littafan tsoho da sabon alkawari ba ne kamar yadda za mu gani filla-filla a wannan littafin.
12 -Surar Najmi 53: 3