KALMAR MU'ASSASA
Surar Kasas: Aya Ta 5.
|

Ya Allah muna bude yabo da godiya gare Ka kuma Kai mai sa a dace a kan abu da yake daidai da baiwarKa.

Lalle babbar matsala ta asasi wadda dan Adam yake fama da ita a yau ita ce babban gibin akida da gurbatar ruhi, wannan matsala ita ce take fassara mana halin rudu da yamutsi da damuwar da ke akwai a tunani da kuma hankali, kamar kuma yadda take fassara mana halin lalacewar dabi'un kwarai mai ban tsoro da ake fama da su a yawancin kasashen yammaci da kuma wasu daga kasashen Musulmi.

Duniyarmu a yau ta wayi gari tana ganin lalacewa a jejjere dangane da abubuwa dabam-daban da suka shafi ra'ayin siyasa da alakar zamantakewa, hatta ma al'amuran kasa da kasa.

Amfani da karfi da tursasawa a yau sun zamanto su ne kalmar da ke kan gaba, tilastawa da zalunci da matsa lamba kuma alamune na zahiri, barazana da ruda hankali da na ci gaba sun bar alamunsu a kowane bangare yadda har ya zamanto yana bayyana cewa: Lalle duniya ta riga ta fara cika da zalunci da ja'irci da dagawa da kafirci.

Ma'aunai na kyawawan dabi'u da yan Adamtaka kuwa sun kusa a daina hukunci da su ma'aunin adalci kuwa ba a amfani da su sai kalilan, hadafin ilimi da ingantaccan al'amarin hikima kuwa ba a kidaya su a matsayin madogara da madakatu sai dai a kan wasu al'amura kayyadaddu da gurare ayyanannu.

Zahirin wannan alamari ya zama bayyananne a yawan mazaunan dan Adam yadda har ba ya bukatar wata hujja don tabbatar da haka.

A cikin irin wannan yanayi da ke dabaibaye da tsoron abinda zai zo nan gaba da kuma yanayi irin wanda ke kusan ya rufe gaskiya, kuma a cikin inuwar wannan shamakin da ban tsoron wanda mutum musulmi ke rayuwa ciki musamman ma bayan kafofin sadarwar yammaci sun yi ta yakar sa ta hanyar sadarwa da duk wanke kwakwale da gurbata tunani a karkashin miyagun take da sunayen manya yadda har ma sun kusa su janye yanki mai yawa daga cikin masana ilimin zamani daga yayan al'ummar musulmi ko kuma suka yi gaf da fitar da su daga addninsu, dukkaninsa.

Tare da la'akari da wannan dukkaninsa baki daya, da kuma amsa wa babban kalubalen wannan zamani wanda al'ummar musulmi ke fuskanta da kuma son yada gaskiyar musulunci da saninsa da koyarwarsa da ra'ayinsa da matsayinsa dangane da al'amura dabam-daban, da kuma don haskakawa da ganarwa,da kama hannun matasa masana ilimin zamani don kare su daga tarkon masu fakon musulunci, da fitinarsu da makircinsu, saboda haka ne "Cibiyar Arrisala" ke ba da kokari a wannan bangare da aiki na ilimi da wayar da kai domin samun kamala da aikin wayar da kai wanda cibiyoyin Musulunci suke yi tana yadawa a gabashi da yammacin kasa baki daya. Nan take ne Cibiyar Arrisala ta fifita farawa da ayyukanta ta bangaren wayar da kai da wani al'amarin akida daga akidojin Musulunci, da ke kewaye da rikirkitawa kuma ya sha fuskantar shakku da suka a duk tsawon zamani ba tare da dakatawa ba kuma har ila yau yana fuskantar yakayya ta wayarwa mai hatsari, da aka hade kai daga baraden
kafircin Yammacin Duniya, mai adawa da Musulunci kamar yadda muke ganin haka daga yawan littafan koyarwa da suka yi maganganu game da al'amarin "Mahadi da aka yi Alkawari", wadanda suka yi shigar burtu da tufafin ilimi alhali kuma sakaye suke da kibiyar suka da rikitarwa game da akidojinmu da manufarmu ta addini da ta dogara a kan wahayi daga Ubangiji a Alkur'ani da kuma Sunna. Idan wannan har zai iya zamantowa - dalili mai wadatarwa game da fara aikinmu - to za mu yi kokarin wadata dakunan littafan karatu da abinda zai zama mai amfani na sosai Insha Allah. Kuma daga gare Shi Ta'ala muke neman taimako da katartarwa kuma Ya wadace mu kuma madalla da Shi abin dogaro.
Cibiyar Arrisala.