Shi dan Adam a dabi'arsa yana da ikon yin biyayya da kuma sabo. Yana da 'yancin zaban daya daga cikin wadannan hanyoyi matukar dai ba an tilasta shi ba ne.
Sai dai shi mutum ba ya iya fahimtar falala da albarkar da ke cikin yin biyayya, face sai ya kasance ya mika kome nasa ga Allah, yana mai neman taimako da kuma shiriyarSa. Yana mai karban kiran Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma koyi da abubuwan da ya zo da su. Idan har mutum ya yi sa'ar riko da imani (Musulunci) da kuma aikata karantarwar Manzonmu, Muhammadu (a.s.), to zai sami kwan-ciyar hankali da farin ciki duniya da lahira, in kuwa ba haka ba, to zai fuskanci kunci da damuwa.
Hakika za a iya takaitar da damar da dan'Adam yake da ita wajen sabo a duk lokacin da yake riko da dokokin Musulunci, aikata umurnonin Allah da kuma kula da fidiransa (wato irin kyakkyawan yanayi da aka halicci mutum), al'ummar da yake ciki da kuma Ubangijinsa. Hakika wajen aiwatar da wannan muhimmin aiki, Musulunci ya yi matukar kokarinsa wajen shiryar da mutum zuwa ga hanya madaidaiciya kana kuma ya nuna masa yadda zai
Don haka ne, Mu'assasar Al-Balagh a burinta na shiryar da mutane take gabatar muku da wannan littafi, "Sabo da Sakamakonsa", a silsilar littattafan da ake kira da "Fahimtar Musulunci", daidai da koyarwar Musulunci. Manufa da burin yin hakan kuwa shi ne samar da mafita da kwanciyar hankali ga wannan duniya tamu mai cike da fitinu da rikice-rikice.
MU'ASSASAR AL-BALAGH.
"Kuma wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, kuma ya ketare iyakokinsa, Zai shigar da shi wuta". (Surar Nisa'i, 4:14)
Don haka, an bayyana sabo a matsayin abu mai cutarwa, wanda ya saba wa dabi'ar dan'Adam.
Su batattun mutane masu wuce haddi sun kasance suna rasa fahimtar munin wuce haddi, sannan ba sa girmama ma'ana da kimar abubuwa. Don haka ne ba sa yin mu'amala da kyawawan abubuwa, kuma suka saba wa tsarurrukan hankali da kuma mika wuya ga munanan ayyuka. A sabili da haka ne ma, Alkur'ani mai girma ya siffanta shirka - don kuwa ita ce ginshikin duk wani sabo- a matsayin fadowa daga wani waje mai tsawon gaske, inda yake cewa:
"....kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yana kamar abin da ya fado daga sama, sa'an....
A saboda haka, sabo ya kumshi duk wani aiki da ya saba wa dokokin dabi'u na kwarai wanda shari'ar Ubangiji ta zo da shi kana lafiyayyen hankali da tsarkakakkiyar fidira wacce bata ba ta shafe ta ba ta gano shi. a koyarwar Musulunci, sabo yana nufin barin wajibai da kuma aikata abubuwan da aka haramta, sannan da barin ayyukan alheri da aikata sharri da munanan ayyuka.
A wannan zamani namu, 'yan'Adam suna fuskan-tar wahalhalu masu tsanani, saboda nuna halin ko-in-kula da suka yi dangane da abubuwan da suke hara-mun. A saboda haka ne ma, gwamnatoci daban-daban suka ba da muhimmanci mai girman gaske wajen yaki da laifuffuka da munanan ayyuka, ta hanyar amfani da duk wani karfin kimiyya da na dan'Adam da suke da shi wajen gyara al'umma don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar jama'a da kuma kasa baki daya. Bugu da kari kan samar da kyakkyawan yanayi na ci gaban al'umma. To amma duk da wannan kokari da suke yi wajen fada da munanan ayyuka, ba su sami nasarar kawar da laifuffuka da munanan ayyuka ba, face ma dai sai ci gaba suke yi.
Wadannan shirye-shirye da tsarurruka na gyara, ba su sami nasara ba ne saboda kasantuwan an
A dalilin haka, dukkan kwararrun wajajen bincike, dakunan kimiyya da kuma kungiyoyin fada da miya-gun laifuffuka suka gagara aikata wani abin a-zo-a-gani, don kuwa sun gagara fahimtar amfani da tasirin dokokin Ubangiji. Hakika da sun bukaci taimako daga dimbin ilimin Ubangiji kana suka yi amfani da hankali da kuwa sun gano mafita daga da yawa daga cikin matsalolinsu.
Hakika wadannan masu sabo ba su kyauta wa kansu ba ta hanyar bayyanar da kansu ga azaba da kaskanta da kuma fushin Allah.
A bisa tsarin Musulunci, aikata munanan ayyuka kamar kisan kai, sata, cin amana, yaudara, zalunci, cuta, cin kudin ruwa, boye kayayyakin
A saboda wannan dalili ne, al'ummomin da suke karkashin irin wannan tsari suke fuskantar hawa-hawan faruwan muggan laifuffuka da suke haifar da barazana ga salin tushen zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma. Inda kuma aka halalta ayyuka irin zina, luwadi, shan giya, safaran muggan kwayoyi, caca da sauransu, sannan a wasu lokuta ma ake bayyanar da su a matsayin ayyukan da aikata su ba laifi ba ne. Idan har aka yi la'akari da wadannan bayanai, za a ga cewa rundunar shedanci da kuma laifuffuka da ke cikin mutane a sake suke kana al'umma kuma suna fuskantar yaduwar zubar da jini, kashe-kashe, yake-yake da muggan cututtuka. To amma shi Musulunci a nasa bangaren ya yi iyakacin nasa kokarin wajen fadakarwa da kuma tsara al'amur-ran 'yan'Adam da kuma kirkiro shirye-shirye don rage tasirin miyagun ayyuka da kuma gabatar da dokoki da tsare-tsaren gyara wanda zai bai wa mutum da al'ummar da yake ciki damar rayuwa cikin aminci da kwanciyar hankali.
____________
1- A baya-bayan nan wasu tsarurrukan siyasa sun dauki boye kayayaki a matsayin laifi wanda ake hukumta mutane a kai.
2- An fassara tsarin "Sekula" da cewa wasu tsarurruka ne wadanda dan'Adam ya kirkiro ba tare da la'akari da dokokin Allah ba.
"A cikin zukatansu akwai wata cuta; sai Allah Ya kara musu wata cuta, kuma suna da azaba mai radadi, saboda abin da suka kasance suna yi na karya". (Surar Bakara, 2: 10)
"A'a ha! Ba haka ba abin da suka kasance suna aikatawa dai, ya yi tsatsa a cikin zukatansu". (Surar Mudaffifin, 83: 14)
"...to, a lokacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukatansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasikai". (Surar Saff, 61:5)
"To, saboda warwarewarsu ga alkawarinsu, da kafiratarsu da ayoyin Allah, da kisan su ga Anna-bawa ba da hakki ba, da cewarsu, zukatammu suna cikin rufi. A'a, Allah ne Ya yunke a kansu saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kadan". (Surar Nisa'i, 4: 155)
Daga wannan bayani na Alkur'ani, za mu fahimci cewa, an arzurta dan'Adam da hankali, hangen nesa da kuma karfin godiya. A dalilin haka, yake son aika-ta alheri da ayyukan alheri kwarai. Kana kuma yana nesantar munanan ayyuka wadanda suka bar mummunan tasirinsu a kwakwalwarsa, ta yadda bai damu da aikata duk wani laifi ba kana ya zamanto ya dabi'antu da aikata zunubai ba tare da nuna damuwa da yin nadama ba. Sannan ya zamanto wani irin mutum mai kiyayya da duk wani bangare na kyakkyawan rayuwar dan'Adam, kuma ya rasa duk wani irin nau'i na mutunci, karama, tsarkaka da dan'Adamtaka. A takaice dai, zai iya zama kasurgumin mai laifi.
Don haka, Alkur'ani mai girma ya lissafa irin mummunan tasirin da aikata sabo da zunubi da
Saboda haka, daga lokacin da mutum ya saba da aikata zunubai da sabo, to zuciyarsa takan cutu ta yadda za ta katangu daga fahimtar abin da ya dace. Zuciyar mutum takan bakanta ta yadda duk rayuwarsa za ta zamanto cikin aikata sabo da laifuffuka.
Dangane da wannan al'amari, maganganun Imam Sadik (a.s.) sun bayyana irin mummunan tasiri da sabo yake yi a kan mutunci dan'Adam, kana yana mai karin haske kan ma'anonin wadancan ayoyin Alkur'ani da suka gabata. Don haka, aka gargadi musulmi da cewa babu wani bambanci tsakanin karamin zunubi da babba, kana ya ci daga da neman gafarar Ubangiji don ya sami damar gujewa hanyar bata kuma da samun damar rayuwa wacce take cike da tsoron Allah da kuma tsarkaka.
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa:
"Babu wani abin da yake lalata zuciyar mutum kamar zunubi, zuciyarsa takan gurbata da zunubai ta yadda shi zai zamanto bawanta - sai abin da ta so zai aikata -"(1).
____________
1- Usul al-Kafi na Kulayni, juzu'i na biyu, shafi na 268, bugu na uku.
Hakika shi mai laifi (zunubi) ba ya aikata laifin face dai sai akwai wani abu ko kuma wani yanayi da yake tunkuda shi ga aikata hakan. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Shin, to, wanda aka kawata masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yana daidai da waninsa)? Saboda haka, lalle, Allah Yana batar da wanda yake so, saboda haka kada ranka ya halaka a kansu domin bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sana'antawa". (Surar Fadir, 35:8)
Duk da cewa abin da yake aikatawa ba kome ba ne, to amma shi mutum yana mai rudin kansa da cewa abin da yake aikatawa shi ne daidai. Hakika Alkur'ani mai girma ya yi bayanin irin wadannan mujirimai:
"Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi barna a cikin kasa", su kance: "Mu masu kyautatawa kawai ne! To lalle ne su, su ne masu barna, kuma amma ba su sansancewa". (Surar Bakara, 2: 11-12)
"Ka ce, ko mu gaya muku game da mafifita hasara ga ayyuka? wadanda aikinsu ya bace a cikin rayuwar duniya, alhali kuma suna zaton
Hakika, shi mutum a koda yaushe yana neman mafaka ce ga abubuwan da yake aikatawa domin ita fidiran dan'Adam ba ta kaunar mummunan abu. A dalilin haka ne ma, babu yadda za a yi ya yarda cewa abin da yake aikatawa ba daidai ba ne face ma har ya gano munin aikin nasa. Duk kuwa da cewa fidiran dan'Adam ba ta kaunar mummunan aiki, duk kuwa da cewa mummunan ayyukan suna nan, to amma sai da Musulunci ya kirkiro hanyoyi da tsare-tsaren hana aukuwan laifuffuka kana kuma ya tsaro kyawawan yanayi da zai kare dan'Adam da al'ummar da yake ciki daga fadawa cikin ramukan zunubai. A takaice dai, Musulunci ya yi amfani da duk wata hanya da yake da ita wajen ruguza abubuwan da suke haifar da aikata sabo da munanan ayyuka. Wadannan abubuwa kuwa su ne kamar haka:
Jahilci shi ne mafi girman al'amarin da ke hana mutum amfani da kwakwalwa da kuma fidirarsa. Ko shakka babu, duk mutumin da ya rasa cikakken
Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Ko sun riki wadansu abubuwan bautawa, baicinSa? Ka ce (Ya Muhammadu), ku kawo hujjarku. Wannan shi ne ambaton wanda yake tare da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabannina. A'a, mafi yawansu ba su sanin gaskiya, saboda haka su masu bijirewa ne". (Surar Anbiya, 21: 24)
Wannan bayani yana tabbatar da cewa ba kasafai malamai da masana suke aikata munanan ayyuka ba, koda kuwa suna cikin lalatacciyar al'umma ce. Koda yake, yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa kariya ta ainihi daga munanan ayyuka tana samuwa ne ta hanyar mallakar "Ilimi irin na Ubangiji". Domin saboda rasa irin wannan muhimmin al'amari ne, ya sanya da yawa daga cikin malamai da masana suka zamanto masu taimako da kuma shirya barna, zubar da jini, aikata laifuffuka da kuma cutar da dan'Adam. Wadannan munanan dabi'u da kuma son aikata zunubai suna wanzuwa daga wadannan malamai ne, saboda tunani da ilmummukan da babu Allah a ciki ne yake ja-gorantarsu, wanda
Hakika Manzonmu (s.a.w.a) ya yi bayanin irin wannan al'amari, yayin da yake ba da amsar tambayar da aka yi masa cewa su wane ne mafi sharrin mutane? Sai ya amsa da cewa:
"Malamai idan suka lalace"(1) .
A saboda wannan dalili ne, Musulunci ya kuduri aniyar yakan jahilci ta hanyar yada hanyoyin neman ilimi wanda hakan shi ne babban asasin gyara. Wannan babban muhimmanci da Musulunci ya bai wa ilimi ya samo asali ne daga irin i'itikadin da yake da shi na cewa rashin kyakkyawan ilimi na iya taimakawa wajen faruwar mummunan ayyuka da zunubai. Sannan kuma mallakar kyakkyawan ilimi mai amfani zai iya samar wa mutum hasken hikima da fahimta kana kuma ya taimaka masa wajen dasa imani, kaunar juna, tausayi da kyautatawa da kuma nuna rashin amincewa da duk wani nau'i na sabo.
"Ya ce, ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma amma ina ganinku, wasu mutane ne, masu jahiltar gaskiya". (Surar Ahkafi, 46: 23)
"Lalle ne kai, ba ka jiyar da matattu, kuma ba ka sa kurame su ji kiranka, idan sun juya suna masu bayar da baya. Kuma kai ba ka zama mai shiryar da dimammu daga bata ba. Ba ka jiyarwa face wanda yake yin imani da
____________
1- Tuhaf al-Ukul na al-Harani, shafi na 36, bugu na biyar.
"A'a ha! Wadanda suka yi zalunci sun bi son zuciyoyinsu, ba tare da wani ilimi ba. To, wane ne zai shiryar da wanda Allah Ya batar? Kuma ba su da wadansu mataimaka". (Surar Rum, 30:29)
Hakika Alkur'ani mai girma ya siffanta wadanda suka jawo wa kansu fushin Allah da wadanda jahilci ya rufe musu ido.
Idan muka dubi cikin wadannan ayoyi na Alkur'ani, za mu iya fahimtar dalilan aikata munanan ayyuka a mahangar Alkur'ani:
Na farko, an kwatanta jahilci da cewa makanta da kurmanci ne tun da suna hana mutum yarda da gaskiya da kuma adalci.
Na biyu, an siffanta jahilci a matsayin mutuwa don kuwa yana lalata wa mutum rayuwa. Don duk wata alakar mutum da duk wani bangare na tunani da fahimta yakan lalace. Bugu da kari, Musulunci yana kwadaitar da dan'Adam wajen neman ilimi da masaniya wanda yakan bude masa hanyar shiriya da farin ciki. A saboda wannan dalili ne, Allah Ya aiko da Annabawa da Manzanni don su shiryar da mutane, ta hanyar dalilai da ilimi, zuwa ga hanya madaidaiciya.
Babu shakka, irin al'ummar da mutum ya taso a ciki da kuma tarbiyyar da ya samu, suna da matukar tasiri ga rayuwa da dabi'unsa. Domin akan haifi mutum ne a cikin mafi tsarkakakken yanayi, ta haka ne zai ci gaba da girma cikin irin yanayin da ya sami kansa a ciki, wadanda su za su tsara masa yadda halaye da dabi'unsa za su kasance.
Matukar dai mutum ya girma cikin kyakkyawan yanayi da kuma tsarkakan al'umma, to ruhinsa yakan sami wani karfi da kuma kulawa wanda ka iya bashi daman samun daukaka da kuma komawa zuwa ga alheri da kyawawan dabi'u. A takaice dai, zai iya samun damar isa ga babban buri da manufar rayuwarsa, wato biyayya da kuma mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki. A daya bangaren kuma, mutumin da ya rasa tsarkakakken yanayi da kuma tarbiyya mai kyau, yakan wayi gari cikin son kai, munanan ayyuka, rashin da'a da kuma rashin sanin ya kamata, wanda sakamakon hakan shi ne samar da wani irin dimaucaccen mutum wanda bai san ya kamata ba. Inda daga karshe mutum yakan zama bawan kyalkyale-kyalkyalen duniya da son zuciyarsa ta inda zai zamanto ya dabi'antu da aikata kisan kai, sace-sace, zinace-zinace, yaudara, shaye-shaye da kuma nisantar kyawawan dabi'u.
A saboda wannan dalili ne, Alkur'ani mai girma ya yi dubi cikin wadansu masu aikata zunubi kana ya nuna cewa addini, wato Musulunci, shi ne
"Sa'an nan kuma a bayansu Muka aika Musa da Haruna zuwa ga Fir'auna da mashawartansa, tare da ayoyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutane masu laifi". (Surar Yunus, 10: 75)
"A cikin zukatansu akwai wata cuta; sai Allah Ya kara musu wata cutar, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna yi na karya". (Surar Bakara, 2: 10)
"Kuma idan an karanta ayoyinmu a gare shi, sai ya juya baya, yana mai girman kai, kamar dai bai saurare su ba, kamar dai akwai wani danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushara da azaba mai radadi". (Surar Lukman, 31:7)
"Kuma suka yi musunsu, alhali zukatansu, sun natsu da su, domin zalunci da girman kai. To, ka dubi yadda karshen mabarnata ta kasance". (Surar Namli, 27:14)
"Za ni karkatar da wadanda suke yin girman kai a cikin kasa ba da wani hakki ba, daga ayoyiNa, kuma idan sun ga dukkan aya, ba za su yi imani da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiri-ya, ba za su rike ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar bata, sai su rike ta hanya. Wancan ne, domin lalle ne su, sun karyata da ayoyinMu, kuma sun kasance, daga burinsu gafilai". (Surar A'arafi, 7: 146)
Hakika daga wadannan bayanai na Alkur'ani, za mu iya fahimtar wani muhimmin al'amari, shi ne kuwa cewa wadannan batattun mutane, son zuciya da alfahari ne yake rudinsu. Don haka ne zukatansu suka kekashe, ba sa iya tunani mai kyau da fahimtar al'amurra. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
"To, don me masu hankali ba su kasance daga mutanen karnonin da suke a gabanninku ba, suna hani daga barna a cikin kasa? Face kadan daga wanda muka kubutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma wadanda suka yi zalunci suka bi abin da aka ni'imatar da su a cikinsa, suka kasance masu laifi". (Surar Hud, 11: 116)
Hakika Alkur'ani mai girma ya ta kawo wadannan bayanai ne don ya shiryar da dan'Adam zuwa ga hanya madaidaiciya, hakan kuwa don
"Domin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya bata karya, kuma koda masu laifi sun ki). (Surar Anfali, 8: 8)
3. Bukatuwa
Hakika tabbataccen al'amari ne cewa biyan bukatan dan'Adam na duniya ako da yaushe yana daga cikin dalilan da suke kawo kyakkyawa kana tsarkakakkiyar rayuwa. Rahsin hakan kuwa na iya sa mutum ya gagara kare kansa daga fadawa cikin aikata munanan ayyuka da kuma laifuffuka. Don haka ne ma, Musulunci ya ba da gagarumin muhimmanci ga abubuwan bukatuwa na rayuwa ta hanyar tsara dokoki da ka'idoji wadanda za su taimaka wa mutum wajen gudanar da kyakkyawan rayuwa cikin farin ciki da daukaka.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tabbatar da wannan al'amari, yayin da yake cewa:
"Babu abin da yafi taimakawa ikhlasi da gaskiya mutum kamar wadata"(1) .
Sannan kuma yana cewa:
"Wadatar da take kare ka daga aikata zalunci ita ta fi fakircin da ke janka zuwa sabo"(2) .
Kana kuma an ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yayin da yake yabon Ubangiji, yana cewa:
____________
1- Usul al-Kafi na Kulaini, juzu'i na 5, shafi na 71.
2- Kamar na sama, shafi na 72.
Don haka, Musulunci ya ba da matukar muhim-manci ga wannan al'amari ta inda har ya bayyana cewa babu laifi ga mutumin da ya aikata haramun yayin da yake cikin talaucin da rashin aikata wannan aiki zai kai shi ga rasa ransa. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"....to, wanda aka matsa, wanin dan tawaye, kuma banda mai zalunci, to, babu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin kai". (Surar Bakara, 2: 173)
Daga wannan bayani, za mu fahimci cewa wuce haddin dan'Adam ya samo asali ne daga rashin wadata. A takaice dai, a wasu lokuta, mutum yakan aikata zunubai a bisa tilas. A bisa haka, ana iya cewa al'ummomin da ba na Musulunci ba, ba su yi adalci wa dan'Adam ba don kuwa an bar shi ba tare da kare shi daga barazanar talauci, kuma aka raba shi daga ni'imar kyakkyawar rayuwa da kuma ilimi mai amfani. Hakika babu wani dalilin da za a tuhimci mutane kana a yanke musu hukumci kan aikin da suka aikata cikin tilas (ba da son ransu ba).
____________
1- Kamar na sama, shafi na 73.
A duk lokacin da mutum ya rasa shaukin kyawa-wan dabi'u da rashin sanin ya kamata kana ya hadu da rashin imani da Allah da akidar sakamako da azaba bayan mutuwa, to jure wa rashin aikata zunubi zai yi masa wuya. Abu mai muhimmanci a wannnan al'amari, shi ne imani da Allah, Masanin abin da ke boye (gaibi), wanda Shi ne mabubbugar duk wani alheri da albarka kana Mai kula da duk wasu halaye na dan'Adam. Daga karshe, hakika Musulunci ya ba da muhimmanci mai girman gaske kan ilimin akida da kuma wani tsari da zai kula da rayuwar mutum ta bayyane da ta ruhi.
Saboda la'akari da kasantuwan sabo na daga cikin ayyukan da suke ruguza al'umma, Musulunci ya yi amfani da duk wani karfi da yake da shi wajen tsige tushen wannan bala'i, don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin al'umma. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Ya mutanen littafi! Lalle ne, ManzonMu ya je muku, yana bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kuna boyewa da littafi, kuma yana rangwame daga abu mai yawa. Hakika, wani haske da wani littafi mai bayyanawa ya je muku daga Allah. Da shi, Allah Yana shiryar da wanda ya bi yardarSa zuwa ga hanyoyin aminci, kuma Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininSa, kuma yana shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya". (Surar Ma'ida, 5: 15-16)
Musulunci ya yi hakan ne saboda la'akari da ka'idojin da suka dace da ci gaban dan'Adam da al'ummar da yake ciki, don kuwa Musulunci ya kasance addini ne na ilimi da kuma shiryarwa irin ta ruhi. Kana kuma, Alkur'ani a fili ya bayyana cewa manufar Musulunci ita ce shiryar da dan'Adam zuwa ga hanya madaidaiciya ta hanyar fitar da shi daga duhu zuwa ga haske don ya samu damar rayuwa cikin zaman lafiya da kwanciyar
Don ba wa mutum daman kiyaye shu'uri, tunani da mutuncinsa, Musulunci ya jaddada muhimmancin amfani da wa'ayi da kuma kwakwalwa. Alkur'ani mai girma, dangane da hakan, yana cewa:
"….Malamai kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa….". (Surar Fadir, 35: 28)
Dangane da hakan ma, Imam Musa al-Kazim (a.s.) yana cewa:
"Hakika an halicci mutane ne don su yi da'a wa Allah. Ceto ba ya yiyuwa ba tare da biyayya ba, kuma biyayya ba ta yiyuwa sai da ilimi"(1) .
2- Imani Da Adalcin Allah Da Kuma Sakama-kon Lahira.
Wannan al'amari ya kasance daya daga cikin shika-shikan akidar Musulunci, kuma an yi
____________
1- Tuhaful Ukul na Al-Harani, shafi na 289.
"To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra na alheri, zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)
Saboda karfafa wannan tabbatacciyar akida, mumini yakan sadaukar da kansa ga kyawawan dabi'u da kuma guje wa munana. Wadannan ayoyi na Alkur'ani mai girma masu zuwa, sun yi bayanin wannan lamari:
"Kuma ku tsayar da su, lalle su, abin tambaya ne". (Surar Saffati, 37: 24)
"Kuma kowane mutum Mun lazimta masa abin rekodinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a ranar lahira da littafi wanda zai hadu da shi budadde". (Surar Isra', 17: 13)
Hakika daga lokacin da mutum ya damfaru da wannan akida, to zai fahimci dadin da ke cikin biyayya da kuma aiki daidai da dokoki da ka'idojin kyakkyawan rayuwa wacce take cike da farin ciki da daukaka. Ko kuma ana iya cewa, ayyuka da daukakan dan'Adam zai samu tsarkaka.
"….kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku....". (Surar Bakara, 2: 235)
3- Biyan Bukatun Dan'Adam Da Kuma Magance Talauci.
A koda yaushe wannan babban al'amari yana nuna irin kokarin da Musulunci yake yi wajen kawar da tasirin tsananin talauci. Don kuwa, Musulunci ya sanya biya wa dan'Adam bukatunsa na yau da kullum a matsayin daya daga cikin wajibansa, ta hanyar kirkiro da harajoji na wajibi kamar su zakka, khumsi (daya bisa biyar na kudin shigan mutum) don kubutar da 'yan'Adam daga barazanar talauci. Hakika tun farko halittar dan'Adam aka kafa wadannan wajibai. Dangane da hakan Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Lalle ne ka samu, ba za ka ji yunwa ba a cikinta, kuma ba za ka yi tsiraici ba". (Surar D.H., 20: 118)
"Saboda haka, sai su bauta wa Ubangijin wannan gida (Ka'aba). Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsoro". (Surar Kuraish, 106: 3-4)
Daga cikin muhimman siffofin sakon Musulunci shi ne cewa yana daukan kwararan matakan tsaro da kuma kariya daga aikata zunubi kafin hukumta
5- Kange Mutane da Kuma Tsarurrukan Gyara
An siffanta mutum da cewa shi wata halitta ce wanda halaye da mu'amalarsa da sauran 'yan'uwansa yana da wani irin gagarumin tasiri ga dabi'unsa, koda yake irin kaskantar da shi da mutane za su yi a duk lokacin da ya saba wa wata ka'ida ta kyawawan dabi'u za ta iya kaskantar da shi ya zama ba kome ba. A sakamakon haka, zai yi kokarin boye kansa daga mutane don ya tserar da kansa daga cin mutuncin mutane.
Don haka, an halitta wa mutum wannan mika wuya na fidira ce don ya yi daidai da hikimar Ubangiji wacce ta kasance take amfanar da mutum wajen kaunar dokoki da adalci. Bayan da ya wajabta wa mutum aikata kyawawan dabi'u da kuma hana shi aikata munana, Musulunci ya samu nasara wajen ware wadannan mutane (masu sabo) da niyyar sanya su cikin kunci da jin kunya don ya motsar da fidirar alheri da daukaka ta inda za su sami sauyin ra'ayi kan aikata sabo.
"A duk lokacin da wani ya kawo maka zancen wani, to ka ce masa, idan har kana son ka zauna da mu, to dole ne ka bar aikata hakan, idan har bai bari ba, ya zama dole ku kore shi"(1) .
6- Tuba Da Kuma Fatan Gafarar Ubangiji.
Tuba wata hanya ce da Allah, cikin ni'ima da rahamarSa, Ya arzurta bayinSa da ita don su sami mafaka daga zunubansu. Allah Yana gaya wa masu barna cewa:
"Ka ce: (Allah Ya ce), Ya bayiNa wadanda suka yi barna a kan rayukansu! Kada ku yanke kauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Na gafarta zunu-bai gaba daya. Lalle Shi, Shi ne Mai gafara, Mai jin kai". (Surar Zumar, 39: 53)
Daga wannan bayani, za mu fahimci cewa tuba ta kasance tana da tasiri wajen dawo da mutum zuwa ga fidirarsa, kana tana ba shi daman tuntuni cikin zunubansa da suka gabata da kuma daura aniyar aikata alheri da barin sabo. A saboda tunanin gafarar Ubangiji da sabuwar hanyar da ya kama, shi wannan mai tuba, saboda tasirin wannan sabon yanayi da ya samu, zai sami karfin gwuiwa da kyakkyawan rayuwa.
____________
1- Wasa'il al-Shia na Hur al-Amili, juzu'i na 11, shafi na 410, bugu na biyu.
Hakika a fili yake cewa hukumta masu laifi zai kare su daga ci gaba da wannan mummunan aiki nasu don su kare mutuncinsu. Alkur'ani mai girma ya yi bayanin muhimmancin hukumta masu laifi:
"Kuma kuna da rayuwa a cikin kisasi, ya ma'abuta hankula; tsammaninku, za ku yi takawa". (Surar Bakara, 2: 179)
Dangane da wannan al'amari Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Abubuwan da doka (hukuma) za ta iya hanawa ta hanyar mai mulki, ba zai yiyu ga Alkur'ani ya hana ba"(1).
Bayan da aka riga aka gano tasirin hukumci wajen hana aikata laifi, Musulunci ya kirkiro haddi (hukumci) a matsayin wata muhimmiyar hanya wajen hana aikata laifuffuka a lokacin da ilimi da tarbiyya suka gagara samun nasara. Don haka, gudanar da hukumce-hukumce tare da kira ga kyawawan dabi'u sun kasance mafi dacewan al'amari wajen gyaran al'umma.
____________
1- Hadisin Kudsi.
A bisa mahangar Musulunci, ana ganin mutum a matsayin shugaban dukkan halittu duniya. Don haka duk ayyukansa, wadanda suka dace da wadanda ba su dace ba, sun kasance a karkashin tasirin "Ka'idar Zamantakewa", wanda ke nuna cewa ayyuka da dabi'un dan'Adam, kyawawa ko munana, sun cancanci sakamako ku azabar da ta dace da su. Idan har aka rasa wannan ka'ida, wato ka'idar sakamako, to kokari da kuma ayyukan mutum za su rasa wani amfani kana kuma kimar rayuwa za ta kasance cikin rudu, bugu da kari kuma adalcin Ubangiji zai zamanto ba shi da wata ma'ana. Bisa la'akari da cewa dan'Adam halitta ce mai tsananin son kanta, don haka Musulunci sai ya yi amfani da wannan so wajen tsara dokoki da ka'idojin ukuba. Don kuwa wadannan dokoki za su hana shi jin dadi da walwala da kuma sanya shi cikin wahala, to hakan yakan sa shi a wasu lokuta ya nesance su.
Haka nan kuma, Allah Ya tsara azabobi wadanda ayoyin Alkur'ani suka bayyana su a matsayin sakamakon ayyukan dan'Adam da kuma tabbatar da adalci da hikimar Ubangiji. Bisa dubi cikin bayanan Alkur'ani kan azabtarwa, za mu iya gani wadannan abubuwa, kamar haka:
(1)- Azabtarwa a matsayin "Ka'ida ta Dabi'a" wanda suke da alaka ta kurkusa da sauran ka'idoji na ayyukan dan'Adam da na al'umma. Alkur'ani
"...lalle, idan wani mai gargadi ya zo musu, tabbas za su kasance mafi shiryuwa, daga dayan al'ummomi. To, a lokacin da mai gargadi ya je musu, bai kara su da kome ba face gudu. Domin nuna girman kai a cikin kasa da makircin cuta. Kuma makirci na cuta ba ya fadawa face a kan mutanensa. To, shin, suna jiran (wani abu ne) face dai hanyar (kafiran) farko. To, ba za ka sami musanya ba ga hanyar Allah. Kuma ba za ka sami juyarwa ba ga hanyar Allah. Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin kasa, domin su duba yadda karshen wadanda suka gabace su ba? Alhali kuwa sun kasance mafifita karfi daga gare su? Kuma Allah bai kasance wani abu na iya rinjayarsa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kasa. Lalle Shi ne Ya kasance masani, Mai ikon yi". (Surar Fadir, 35: 42-44)
"Kuma, hakika, mun halakar da al'ummomi daga gabanninku, a lokacin da suka yi zalunci, kuma Manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu, amma ba su kasance suna imani ba. Kamar wannan ne, muke sakawa ga mutane masu laifi. Sa'an nan kuma muka sanya ku masu mayewa a cikin kasa daga bayansu, domin mu ga yaya kuke aikatawa". (Surar Yunus,10: 13-14)
"Kuma babu abin da ya hana mutane su yi imani a lokacin da shiriya ta zo musu, kuma su nemi gafara daga Ubangijinsu, face hanyar farko ta je musu ko kuma azaba ta je musu nau'i-nau'i". (Surar Kahfi, 18: 55)
Bisa wadannan kalmomi na Allah, an bayyana azabtarwa a matsayin tabbataccen sakamakon aiki wanda ke tabbatuwa a duk lokacin da aka samar da abubuwan da suke tabbatar da shi, kamar lalacewa, zalunci, cin mutunci da sauransu.
(2)- Sau da dama azabtarwa tana ta'allaka ne da wani takamammen aiki, ba wai kawai wani al'amari ne da aka dora wa raunanan mutane tare da wani dalili ba.
(3)- Azabatarwa tana da alaka ta kurkusa da adalcin Ubangiji wanda hakan yana nuna cewa Allah ba zai bar azzalumai su tafi haka kawai ba tare da yi musu azaba ba. Sannan su kuma wadanda aka zalunta a dauko musu fansa. Alkur'ani mai girma ya na cewa:
"Yana mai karkatar da sashensa domin ya batar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yana da
4- Alkur'ani mai girma ya bayyana nau'o'i hudu na irin azabar Ubangiji:
Wannan ya hada da duk wadansu matakai na hukumce-hukumce, ka'idoji, dokoki da cin tara wadanda ake gudanarwa a dokokin laifuffuka (a kotuna) kamar su hukumcin kisa, tilasta biyan hakki da kuma yanke hukumci.
(B)- Azabtarwa Irin Ta Al'umma.
Irin wannan azabtarwa tana faruwa ne a sakamakon bijirewar mutane ga sakon Ubangiji da kuma aikata ayyukan sabo wanda ke kawo wahalhalu, bakin ciki da bala'i na gaba daya. Wannan tabbatac-cen bala'i yana faruwa ne a sakamakon kauce wa hanya madaidaiciya wacce Ubangiji Ya zaba. Inda daga karshe, azabobi kala-
"Ka ce: Shi ne mai iko a kan ya aika da wata azaba a kanku, daga bisanku, ko kuwa daga karkashin kafafunku, ko kuwa Ya gauraya ku kungiyoyi, kuma Ya dandana wa sashenku masifar sashe. Ka duba yadda Muke sarrafa ayoyi, tsam-maninsu suna fahimta".(Surar An'am, 6: 65)
"Barna ta bayyana a cikin kasa da teku, saboda abin hannayen mutane suka aikata. Domin Allah Ya dandana musu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su komo". (Surar Rum, 30: 41)
"Kuma Allah Ya buga misali, wata alkarya ta kasance amintacciya, natsattsiya, arzikinta yana je mata a wadace daga kowane wuri, sai ta kafirta da ni'imomin Allah saboda haka Allah Ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro, saboda abin da suka kasance suna sana'antawa". (Surar Nahli, 16: 112)
"Kuma lalle ne, hakika, mun kama mutanen Fir'auna da tsananin shekarun fari da nakasa daga 'ya'yan itace, tsammaninsu suna tunawa". (Surar A'arafi, 7: 130)
"Alamar yardar Ubangiji ga bayinSa shi ne adalcin shuwagabanninsu da kuma saukin kayayyaki (a kasuwa), kana kuma rashin yardarSa, ita ce zaluncin shuwagabanninsu da kuma tsadar kayayyaki"(1).
"Duk yadda kuka kasance, za a mulke ku".
Sannan kuma yana cewa:
"A duk lokacin da lalatattun mutane suka zama masu mulki, kuma Dagattansu suka zamanto marasa mutunci, sannan kuma ake girmama fasikai, to su saurari saukar bala'i"(2) .
Sannan kuma yana cewa:
"Muminai suna cikin wahalhalu har sai an gafarta musu dukkan zunubansu".
Imam Ali (a.s.) yayin da yake shawartar 'ya'yansa, yana cewa:
"Kada ku taba barin umurni da kyawawan ayyuka da kuma hani da munana, domin in kuka yi haka, to mafi sharrin al'ummarku za su mulke ku, kuma ba za a amsa muku duk salloli da addu'oinku ba"(3).
An ruwaito Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa:
____________
1- Usul al-Kafi na Kulayni, juzu'i na 5, shafi na 162.
2- Tuhaful Ukul na Alharani, shafi na 25.
3- Kamar na sama, shafi na 136.
Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) din dai yana cewa:
"Hakika wani daga cikinku zai kasance mai yawan tsoron mahukunta, hakan kuwa saboda zunubansa ne, don haka sai ku yi iyakacin kokarinku wajen nisantar aikata zunubi, sannan kuma ku nisanci son zukatanku"(2).
Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) yana cewa:
"A duk lokacin da al'umma suka kirkiro wasu zunubai a cikin rayuwarsu wadanda da ba sa aikatawa, a sakamakon haka, Allah Zai saukar musu da bala'o'in da ba su taba saninsu ba"(3).
____________
1- Usulul Kafi na Kulaini, juzu'i na 2, shafi na 274.
2- Kamar na sama, shafi na 275.
3- Kamar na sama.
Hakika a duk lokacin da mutane suka zamanto sun lalace, kana suka mika wuyansu ga munanan ayyuka, to ba za su taba tsira daga kasancewa a karkashin mulkin zalunci da kuma rayuwa cikin kaskanci saboda yin wofi da suka yi da ka'idojin Musulunci.
(C)- Azabtarwa Irin Ta Ubangiji
Wannan ita ce mafi girman dukkanin azabobi. Alkur'ani mai girma ya yi cikakken bayani kan tarihin mutane da al'ummomi da suka bar hanya kana suka ci gaba da aikata munanan ayyuka da kuma saba wa umurni da koyarwar Annabawa da Manzanni. Inda a sakamakon haka, Allah Ya saukar musu da azabarSa a bangaren guda a matsayin sakamakon abubuwan da suka aikata,
"Barna ta bayyana a cikin kasa da teku, saboda abin da hannayen mutane suka aikata. Domin Allah Ya dandana musu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su komo". (Surar Rum, 30: 41)
"Ka ce: Shi ne mai iko a kan ya aika da wata azaba a kanku, daga bisanku, ko kuwa daga karkashin kafafunku, ko kuwa Ya gauraya ku kungiyoyi, kuma Ya dandana wa sashenku masifar sashe. Ka duba yadda Muke sarrafa ayoyi, tsam-maninsu suna fahimta". (Surar An'am, 6: 65)
(D)- Azabtarwa Irin Ta Lahira
Alkur'ani mai girma bai taba yin cikakke da kuma karin bayani sosai kamar yadda ya yi yayin bayanin rayuwa a ranar lahira ba.
"Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to yana da goma din misalinsa. Kuma wanda ya zo da mugun aiki guda, to ba za a saka masa ba face da misalinsa. Kuma su ba a zaluntar su". (Surar An'am, 6: 160)
"Domin Allah Ya saka wa kowane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah mai gaggawar hisabi ne". (Surar Ibrahim, 14: 51)
"....to, wane ne mafi zalunci daga wanda ya karyata game da ayoyin Allah, kuma ya hinjire daga barinsu? Za mu saka wa wadanda suke hinjirewa daga barin ayoyinmu da mugunyar azaba, saboda abin da suka kasance suna yi na bijerewa". (Surar An'ami, 6: 157)
"Suna da wata shinfida daga jahannama kuma daga samanu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke saka wa azzalumai". (Surar A'arafi,7: 41)
Idan muka yi dubi cikin irin wannan siffantawa, za mu iya fahimtar cewa wannan takaitacciyar duniya wata gada ce ta zuwa lahira. Hakika ma dai lahira wani ci gaba ne na wannan duniya wacce ta kasance rayuwa ce wacce ba ta da karshe. A bisa bayanin Alkur'ani, mutum da ayyukansa a wannan duniya yana wakiltan farkon bangaren rayuwa ne; daya bangaren kuwa rayuwar lahira, wanda yake ci gaba ne na wannan rayuwa, ne yake wakiltarsa.
A bisa wannan bayani, za mu fahimci cewa ranar lahira, ita ce ranar da za a zo da ayyukan mutum don tantancewa da kuma yin sakamako. Dangane da hakan, Sheikh Raghib Isfahani ya na cewa:
"Sakamako yana bukatuwa da abin da ya yi daidai da shi, in alheri to alheri, in kuwa sharri, to sharri, ana cewa an saka masa kan kaza da kaza. Allah Ya na cewa: "Sakamakon mummunan aiki, shi ne mummuna kamar sa""(1) .
Alkur'ani mai girma ya yi cikakken bayani kan akidar sakamako:
"....Kuma wanda ya zo da mugun aiki guda, to ba za a saka masa ba face da misalinsa. Kuma su ba a zaluntar su". (Surar An'am, 6: 160)
Hakika, wannan ka'ida ta sakamako wata babbar alama ce na adalcin Ubangiji da kuma kamalarSa. Daga karshe, ka'idar "Adalcin Ubangiji" ta kumshi tasirin akida, dabi'a da na ruhi ga dan'Adam.
Don haka, bayanin cewa ya kamata dan'Adam ya sanya muhimmancin wadannan ka'idoji a zuciyarsa, ya zamanto wani share fage ne na kokarin dan'Adam na gina kyakkyawa kana tsabtatacciyar rayuwa wacce take cike da kwanciyar hankali da daukaka.
Hakika idan aka rasa sakamako (azabtarwa), to daidaituwar alaka da ke tsakanin aiki da kuma saka-makonsu zai jirkita matukar dai ana aikata sabo, kana kuma za a rasa kimar abubuwa sannan kuma hasken adalci zai bace a cikin rayuwa.