Mece Ce Wayewa? Kuma Wane Ne Wayayye?

Muna amfani da wannan kalma ta "wayewa", mu ce wannan mutum wayayye ne, wannan waye-war ta Musulunci ce.....don haka me muke nufi da wayewa da kuma wayayye?

Abin nufi da wayewa, ita ce jam'in ilmummuka da kuma masaniya ta mutum wadanda mutum yakan samo su kana kuma su kasance masu tasiri cikin tunani, fahimtarsa ga abubuwa, dabi'u da halayensa da kuma alakarsa da Allah, al'umma da kuma rayuwa. Misali ilimin akida, tarihi, fikhu, dokoki, siyasa, kyawawan halaye, tattalin arziki, zamantakewa da dai sauransu.

Sannan kuma wayayyen mutum shi ne wanda ya tsinkaye wani sashi na wadannan ilmummuka da sauran ilmummukan dan'Adam, sannan kuma su yi tasiri cikin halayensa, tasiri mai kyau.

Dan'Adam yana bukatar fahimtar rayuwa ta al'ummance, siyaya, ilmummukan tarihi, hukumce-hukumce, akida, shari'a, dokoki da dai sauransu, don ya samu damar yin mu'amala da al'umma, mu'amala mai kyau, don tsara rayuwa da kuma samun nasara cikin al'amurransa. Don haka wayewa ita ce masaniya da kuma halaye, ko kuma



(6)


ita ce masaniyar da take tsarkake dabi'un dan'Adam. Don kuwa mutum jahili babu yadda za a yi ya fahimci al'amurran masaniyar da ta dace.....

Misali: muna bukatar ilimi da masaniya wajen fayyace matsayinmu dangane da yanayin siyasar da take gudana a kasashenmu, ko kuma tsarin tattalin arzikin da ke gudana, ko kuma tafarkin siyasar da jam'iyya ko kuma wani shugaba na siyasa yake kai.....ko kuma matsalar matsayin mace a rayuwa ta yau da kullum, ko kuma matsalar hijabin mace, ko kuma matsalar 'yanci da hakkokin dan'Adam, ko kuma matsayin Musulunci kan wani abu, da dai sauransu......

Hakika fahimtar wadannan mas'aloli da ma makamantansu da kuma fitar da matsayinmu dangane da su, yana bukatar ilimi da kuma masaniya.

Wayayyen mutum shi ne wanda ya mallaki ilimin da zai ba shi damar fahimtar abubuwa da kuma tsinkayarsu da kuma daukan matsayin da ya dace kan su ba tare da bata lokaci ba. Ko kuma ta hanyar dubi cikin ilmummuka don fahimtar lamarin.

A lokacin da mutum ya kasance mai karancin wayewa, ko kuma mutum maras ilimi, babu yadda zai iya daukan matsayi da matakin da ya dace kan wani lamari yana mai dogaro da fahimta da kuma tsinkayarsa, face dai zai zamanto mai koyi ne da wadansu, wanda akwai hatsarin gaske cikin hakan



(7)


ga yanayi da kuma matsayinsa. A lokuta da dama mutanen da suke da karancin ilimi da wayewa sukan fada cikin hatsari da kuma daukan matakan da ba su dace ba kan wasu lamurra saboda koyi da wasu, ta haka ne mutum yakan zama makaho, wanda yake bin al'amurra ido a rufe ba tare da ilimi da kuma masaniya ba. A lokuta da dama yakan yi kuskure wajen tsai da matsaya, kana daga baya kuma ya kasance cikin nadama.

Wayayyen mutum, shi ne mutumin zamani, wanda ya san ma'anar dan'Adamtaka kuma ya ke girmama ta.....kuma shi ne mutum mai cikakken mutumci, yakan yi mu'amala da abubuwa cikin hankali da kuma ilimi.....

Wayayyen mutum, shi ne wanda ilimi da wayewa suke yin tasiri cikin halaye da kuma dabi'unsa, sannan kuma wayewa ta bayyana cikin maganganunsa yayin da yake magana da sauran mutane, kana kuma ta bayyana cikin mu'amalarsa yayin mu'amalarsa da su ko kuma a lokacin da yake rayuwa da su.

Hakika wayewa takan bayyana cikin yanayin mutum, takan bayyana cikin lafuzza da kuma tufafinsa da kuma tsarin rayuwarsa a cikin gidansa.

Mutum wayayye, shi ne mutum ma'abucin mikakkiyar dabi'a, wanda yake zaban ayyuka, halaye da kuma lafuzzan da zai yi magana da su a bisa asasin fahimta da kuma hankali.

Misali, wayayyen mutum shi ne wanda yake fitar



(8)


da matsayinsa kan wani lamari na siyasa sakama-kon masaniyyarsa da wannan lamari, sannan kuma yake tabbatar da alakarsa da sauran mutane bisa asasin ilimi ba tare da cuta ko cutarwa ba......

Wayayyen mutum, shi ne wanda wayewa ta tabbatar masa da yanayinsa ma'abucin mutumci, kyawawan halaye da kuma dabi'u na kwarai.....

Wayayyen mutum, shi ne wanda yake koyon asasin mu'amala mai kyau tare da iyalansa.

Sannan kuma wayayyen mutum, shi ne mutumin da yake girmama ra'ayoyin sauran mutane, yana kuma mai mu'amala da su cikin girmamawa.



(9)



Banbance-Banbancen Wayewa

Wayewa ta bambanta daga akida zuwa wata akidar ta daban, sannan daga mataki zuwa mataki ta daban......

Wayewar jari-hujjar Turai ta bambanta da na Kwaminisanci, kuma wadannan biyun duk sun bambanta da wayewar Musulunci.....da dai sauransu.

Abin nufi da bambance-bambancen wayewa shi ne nau'in wayewa, misali wayewar Musulunci tana da wasu abubuwa da suka kebanta da ita kawai, ita ce kuwa wayewa wacce ta doru a bisa asasin imani da Allah Madaukakin Sarki, Wahayi, Annabci, Ranar Lahira.....da dai sauransu.

Sannan kuma wayewar abin duniya (madiyya), wayewa ce wacce ta doru a bisa asasin kafirci, inkarin samuwar Ubangiji, addinai da kuma kyawa-wan dabi'u da dai sauransu.

Don haka wayayyen mutum musulmi shi ne mutumin da ya mallaki wayewa da kuma masaniya a bisa asasin Musulunci.....sannan kuma ake ganin tasirin wannan wayewa cikin ayyuka, rubuce-rubucensa, idan ma'abucin rubutu ne, ko kuma cikin maganarsa yayin da yake magana da mutane......

Wayayyen mutum musulmi, shi ne mutumin da



(10)


ya mallaki ilmummukan Musulunci daga Alkur'ani, hadisi, tarihin Annabi (s.a.w.a.), fikhu, akida da kuma tunanin Musulunci, ta yadda zai kasance yana fahimtar dan'Adam da kuma rayuwa a bisa tsari da ra'ayin Musulunci. Misali, zai fahimci lamarin 'yanci, siyasa, kyawawan halaye, alakar mace da namiji da sauran mu'amaloli na yau da kullum a bisa mahangar Musulunci ne, sannan kuma zai dubi lamurra ne da kuma yin tunani kansu a tafarki irin na Musulunci, haka nan kuma zai tsara su ne bisa ma'aunin halal da haram, imani da Allah, tare da kuma dacewarsu da hankali da ingantaccen ilimi.

Kiyaye Yanayin Musulunci

Wajibi ne malamai, 'yan boko, marubuta da 'yan jaridu musulmi su tsaya tsayin daka wajen kare yanayi da kuma mutumcin addinin Musulunci ta hanyar ayyuka da kuma rubuce-rubucensu, kamar yadda hakan kuma wajibi ne na hukuma da kuma gwamnatoci.....

Babu shakka rubuce-rubuce, ayyukan zane, mujjallu da jaridu, shirye-shiryen radiyo da talabijin na malamai da 'yan boko musulmai ya taimaka, zai kuma taimaka nesa ba kusa ba wajen haifar da kuma tabbatar da wayewar Musulunci.....

Don kuwa sun yi rubuce-rubuce kan akidar Musulunci, 'yanci, hakkokin 'yan'Adam, mace a Musulunci, falsafar ibada, ilimin Alkur'ani da hadisan Ma'aiki (s.a.w.a), tsarin siyasa, zamantakewa,



(11)


tattalin arziki da tarbiyya a Musulunci, kamar yadda kuma suka yi hakan kan fikhu, tarihin Annabi (s.a.w.a.), kyawawan dabi'u, kissoshi, tarihin Musulunci da dai sauransu.

A cikin wadannan rubuce-rubuce nasu sun taimaka wajen kare Musulunci da kuma mayar da martani kan wasu shubuhohin da makiya Musulunci suke bijirowa da su. Hakan shi ne ake kiransa kare Musulunci ta hanayar wayewa.



(12)




(13)


Asasan Wayewar Musulunci

Don samar wa kanka asasan wayewar Musulunci, dole ka fara karatu da bincike kan asasan wayewar Musulunci ta hanyar karanta manya-manyan litattafan Musulunci asasai, darussa da kuma tsarin Musulunci..

Muna iya takaita tafarkin da zai samar wa matashi musulmi asasin wayewar Musulunci, kamar haka:

1- Asasin da wayewar Musulunci ta ginu a kai, ita ce akidar Musulunci; akwai kuwa littattafa da dama da aka rubuta kan akidar Musulunci.....

Don tanadar wa kanka asasan wayewar Musulunci, dole ne ka fara da karanta littattafan akidar Musulunci, ko kuma kasetocin radiyo da na bidiyo da aka tanadar a kan hakan, ko kuma ka dinga halartan darussan akida, idan har akwai hakan a kusa da kai.

Hakika kafin mutum ya sami dama da kuma iya amsa shubhohin da makiya suke bijiro da su ga Musulunci, dole ne mutum ya tabbatar da tushen akida a zuciyarsa ta hanyar ilimi da kuma yakini.

Sannan kuma dole ya kasance ya fahimci wasu mas'aloli na akida, kamar su adalcin Ubangiji, kaddara, annabci da kuma mu'ujizar wahayi, gaibi,



(14)


tashin kiyama, sakamako, imamanci.......da dai sauransu, sosai. Kana kuma don ilimin akida ya kasance ingantacce, dole mai karatu ya zabi littattafan akida wadanda suka kubuta daga kura-kura da kuma kauce wa hanya, da kuma daukan Alkur'ani mai girma a matsayin ma'aunin fahimtar akidar da yake karantawa cikin wadannan littattafa.

Imam Sadik (a.s.) yana kiranmu zuwa ga karban ilimin akida ta hanyar Alkur'ani, inda yake cewa:

"Kada ku wuce Alkur'ani, sai ku bata bayan shiriya".

2- Wayewa irin ta fikhu: Ilimin fikhu zai tabbatar mana da masaniya kan hukumce-hukumcen shari'a da kuma dokokinta cikin rayuwarmu, da suka hada da hukumce-hukumcen iyali, gwamnati, dukiya, kasa, kasuwanci, ibada, abubuwan ci da sha, da dai sauransu, musamman ma kan abubuwan da suka zama wajibi mu aikata ko barin su.....

Don samun wayewa irin ta fikhu kuwa, dole ne ka lizimci karanta littattafan fikhun Musulunci da kuma yin darasinsu.

Ko da yake ba wai ma'anar sanin fikhun addini shi ne masaniya kan hukumce-hukumcen fikhu da sauransu kawai ne ba, face dai yana nufin wa'ayi da kuma fahimtar akida, tsari, hukumce-hukumce da kuma ikon ciro hukumce-hukumcen.

3- Don dada fadada wayewarka ta Musulunci, da kuma samar wa kanka asasin wayewar Musulunci,



(15)


dole ne ka lizimci karanta takaitattun littattafa cikin ilimin Usul al- Fikhu, Ulum al-Kur'an, Ulum al-Hadis.....da dai sauransu.

Karanta wadannan littattafa zai tanadar maka da masaniya kan muhimman asasan wayewar Musu-lunci, ko da dai kuwa a matakin farko ne, da suka shafi ijtihadi, yadda ake ciro hukumcin shari'a, ilimin Alkur'ani da kuma hadisi.

4- Wayewarka ta Musulunci ba za ta cika ba ba tare da bincike cikin tarihin Manzon Allah (s.a.w.a.), yadda ya gudanar da rayuwarsa mai albarka, tarihin manyan Musulunci, Ahlulbaiti (a.s.) a kan gaba ba. Irin wadannan bincike da karatu za su tabbatar maka da cikakkiyar wayewar Musulunci a rayuwa; shin cikin dabi'u da halaye ne, ko kuma cikin dokoki da tsarin rayuwa, ko kuma cikin fahimtar shari'ar Musulunci ne. Kamar kuma yadda za ka samu mafi girman darasi da wa'azi da kuma bayanin ma'anar Musulunci a aikace. Akwai littattafa da dama da suka yi magana kan hakan da kuma kan tarihin Annabi (s.a.w.a.).

To amma dole a yi hankali da littattafan da suke dauke da guba da kuma gurbataccen ilimi kan tarihin Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma Ahlulbaitinsa (a.s.).

5- Kyawawan Halaye: Kyawawan dabi'u da kuma wayewa irin ta kyawawan halaye rukuni ne daga cikin rukunan wayewar Musulunci, malamai da 'yan boko musulmai sun wallafa littattafa da



(16)


dama kan ilimin kyawawan halaye. Don samun wayewar kyawawan halaye, dole ne ka karanta littattafan ilimin kyawawan halaye, da kuma gano kyawawan halayen Musulunci ta hanyar Alkur'ani mai girma da kuma sunnan Ma'aiki da Iyalan gidansa (a.s.).

6- Tarihin Musulunci: Tarihi malamin mutum ne kana kuma mai nuna masa hanya, don kuwa cikinsa akwai wa'azi, darussa, ilimin da babu yadda za a yi mutum ya wadatu daga gare su. Hakika mabubbuga ce ta wayewa da masaniya.....

Tarihi yana sanar da mu al'ummarmu da kuma irin girman ilimi da wayewar da suka kasance tare da su a tsakanin sauran al'ummu, da kuma abubuwan da iyaye da kakanninmu suka gudanar kamar bude garuruwa da 'yantar da al'ummu, fada da zalunci, fasadi, mulkin mallaka da dai sauransu. Kamar yadda kuma yake sanar da mu ilimi mai yawan gaske kan al'ummomin da suka gabace mu.

Don haka karantar tarihi yana samar mana da cikakkiyar wayewa da kuma cika mana tamu wayewar, ko da yake hakan yana bukatuwa da ingantattun littattafan tarihi.

7- Sanin yare da kuma adabi: Yaren larabci shi ne yaren Musulunci, Alkur'ani da kuma hadisan Annabi (s.a.w.a.). Shi ne kuma yaren ilimi da masaniya ta Musulunci.....fikhu, akida, Usul al-Fikhu, ilimin hadisi, falsafa, kyawawan halaye da dai sauransu. Sanin hakan kuwa wani asasi ne mai



(17)


muhimmanci na wayewa......

Sannan kuma ana kirga ilimin nahawu daga cikin muhimman ilimin yaren larabci ga mutum mai wayewa, don haka darasin nahawu da sarfu lamari ne da ya zama dole wajen cim ma ingantaccen karatu da kuma kubuta daga kure.

Hakika duk wanda ya jahilci ilimin nahawu, dole a samu kura-kurai cikin maganarsa cikin harshen larabci, hakan kuwa babbar aibi ne gare shi da dole ne ya magance shi. Bugu da kari kan cewa kuskuren nahawu ko sarfu cikin karanta kalma yana iya canza ma'anarta a wasu lokutan.

Wayewa irin ta sanin yare ita ce ma'auni ga mutumcin mutum wayayye, don kuwa magana da kuma kula da ka'idojin yare yana nuni da matsayin wayewar mutum.

Babu shakka duk wanda ba ya kyautata maganarsa, ko kuma yake yawan kure cikin yare yana nuna wa mutane raunin wayewarsa ne. Don haka wajibi ne sanin ma'anar lafuzzan yare, ka'idojin nahawu da sarfu, yadda ake magana a yaren da kuma kokari wajen karfafa adabi ta hanyar karatu da kuma sauraran darussa da kuma tattaunawa ta adabi, bugu da kari kan darasin takaitattun littattafan nahawu.

8- Tunanin Musulunci: Daga cikin ilimin wayewa na asasi shi ne masaniyar tunanin Musulunci a bangaren siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da dai sauransu.....



(18)


Don samar wa kanka asasin wayewa a wannan bangare, wajibi ne ka karanta littattafan wayewar Musulunci wadanda marubuta da 'yan boko musulmi suka rubuta a bangaren tattalin arzikin Musulunci, tsarin siyasa da gwamnati a Musulunci, tsarin zamantakewa, tsarin iyali da tarbiyya, 'yanci da hakkokin 'yan'Adam a Musulunci da dai sauransu.

Hakika karanta wadannan littattafa da kuma sauraran shirye-shiryen telibijin da na radiyo kan tunani, ilimummuka da kuma wayewar Musulunci, zai tabbatar maka da masaniya da kuma wayewar Musulunci na asasi. Kana kuma zai bude maka hanyar wayewa da masaniyar Musulunci da kuma kare tunaninka daga guba......

Don haka wajibi ne ka fara da tabbatar da wayewar Musulunci da farko, sannan kuma a mataki na biyu ka fara bincike kan sauran wayewa wadanda ba na Musulunci ba, don tabbatar da ingantacciyar wayewa ta Musulunci.

Amma matashi musulmin da yake farawa da karance-karance kan wayewar da ba ta Musulunci ba da kuma tabbatar da wayewar da ta yi nisa da ta Musulunci, zai rayu cikin rudu da rashin fahimtar ainihin tunanin Musulunci, face ma dai wannan hanya ta haifar da bacewar da dama daga cikin



(19)


matasa. Hakan kuwa yana da hatsarin gaske, don haka wajibi ne a fara da karantar wayewa da kuma tunani irin na Musulunci, a fahimce su sosai, kafin a shiga bincike kan sauran wayewa.



(20)




(21)


Wayewa Da Ci Gaban Kasa

Babu shakka rayuwar mutum tana tasirantuwa da abubuwan ci gaban rayuwa na zamani wadanda ake amfani da su wajen ci gabantar da rayuwa......

Kamar yadda kuma take tasirantuwa da irin ci gaban kere-kere da ilimi wanda dan'Adam ya cim ma ta hanyar kafafen yada ilmummuka, irin su radiyo, telibijin, komfuta, bidiyo da sinima, da kuma injunan noma da rubutu, likitanci da masana'antu daban-daban da suke samar wa mutum da abubuwan da yake bukatuwa da su a rayuwarsa ta yau da kullum, da kuma yadda ake zama a manyan birane ta hanyar manyan gine-gine, yanayin gine-ginen da kuma kasuwanni da dai sauransu.

Wadannan abubuwa sun canza yanayin rayuwa da kuma mu'amalar mutane, kana kuma sun yi tasirin gaske wajen tabbatar da yanayin mutum da kuma tunaninsa. Suna da mummunan tasiri a cikin rayuwar mutum kamar yadda kuma suke da kyakkyawan tasiri wajen samar da sauki da ci gaban rayuwa.....

Ci gaban masana'antu da kuma yanayin rayuwa a cikinta, ya cutar da yanayin mu'amalar mutane, don kuwa irin alakar da ke tsakanin makwabta da



(22)


dangi a halin yanzu ba irin wacce ta kasance a da ba ne. Saboda a halin yanzu muna iya ganin yadda makwabta sukan iya rayuwa na shekaru ba tare da an sami wata alaka ta makwabtaka tsakaninsu ba, a wasu wuraren ma ba tare da sun san juna ba.....

A da makwabta da 'yan'uwa sun kasance sukan ziyarci junansu, suna masu tattaunawa na sa'oi masu yawa kan matsalolin rayuwa da dai sauransu.....to amma bayan da aka kirkiro telibijin sai ya zamato ya karanta haduwar mutane, don kuwa a ko da yaushe suna zaune a gindin telibijin din ne. Mutane a da kafin bayyanar irin wadannan kayayyakin alatu na zamani, sun kasance masu ba da lokaci wajen karfafa alakoki na zamantakewa, ziyarar 'yan'uwa da abokan arziki, to amma bayan bayyanar wadannan abubuwa da kuma mishkilolin rayuwa, sai aka rasa wadannan kyawawan alakoki. Ta haka ne dan'Adam ya rasa wannan ruhi na zamantakewa mai gina mutum......

To, don samun nasara a kan wannan lamari da ya cutar da rayuwar dan'Adam, dole ne mu fadada da kuma kyautata alakarmu da 'yan'uwa da abokan arziki ta hanyar kafa kungiyoyin taimakon al'umma, halartar sallolin jama'a a masallatai, ziyartarsu a lokutan farin ciki, bakin ciki, hutu, bayar da kyaututtuka da kuma aika wa da gaisuwa ta hanyar wasika ko kuma ta wayar tarho da dai sauransu. Hakan wajibi ne na rayuwa.

Don kuwa mutum wayayye shi ne mutum mai



(23)


sake fuska ga kowa, wanda ya san yadda zai rayu da mutane da kuma yin mu'amala mai kyau da su.....

Saboda muhimmanci da alakar zamantakewa ta ke da shi ne a rayuwa, ya sa shari'ar Musulunci ta jaddada batun fadadawa da kuma karfafa wannan alaka da ke tsakanin 'yan'uwa da abokai da kuma makwabta. Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

"Ya ku mutane! Lalle ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dan-gogi da kabiloli domin ku san juna. Lalle mafi-ficinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa......" (Surar Hujurat, 49: 13)



(24)




(25)


Koyi Irin Na Wayewa

Mutane sun bambanta wajen karbar wayewa da kuma fahimtar ci gaba, da suka hada da tunani, dabi'a, sanya tufafi, cin abinci, mu'amala, yanayin rayuwa da kuma alaka da sauran mutane......

Kashin farko na mutanen sukan karbi hakan ne ta hanyar fahimta da kuma tabbaci, sun san dalilin da ya sa suka yarda da wannan tunani ko kuma wancan, haka nan kuma sun san dalilin da ya sa suka ki yarda da wannan tunani ko wancan.....sun san me yasa suke aikata wani aiki, kana kuma me yasa ba sa aikata wani aikin.

Kashi na biyu kuwa na mutane sun kasance 'yan amshin shata ne kawai (masu koyi ne kawai), ba su da wata fahimta ko masaniya kan lamarin da suka yarda da shi. Su mabiyan dukkan abin da kafafen watsa labarai suka fadi ne kawai wajen tabbatar da tunani da kuma yanayin dabi'a da kuma matsayinsu, Su kan yarda da abubuwa ba tare da masaniya ko fahimta ba.

To irin wadannan mutane su ne mutane ma'abu-ta rauni. Ba su mallaki wani iko ko karfi ba haka kuma ba sa iya daukan matsaya. To irin wadannan mutane ba za mu kira su wayayyu ba, ko da kuwa sun kira kansa wayayyun.



(26)


Da yawa daga cikin mutane sukan kalli telibijin ne, ko kuma abubuwan da jaridu da mujallu suka buga, ko kuma sinima, ko kuma abubuwan da wasu suke aikatawa, sai su tasirantu da su. Babu shakka babbar matsalar da al'umma take fuskanta a wannan duniya tamu ta Musulunci ita ce matsalar koyi da wayewar Turai.

Wasu su kan yi koyi da wayewar Turai a bangaren iyali, 'yanci, jinsi, yanayin mace, dabi'u da kuma akidoji, su kan samo su da kuma yarda da su ta hanyar koyi da mutumin Turai ba tare da wata mujadala ba ko kuma dubin irin mummuna tasirin irin wadannan dabi'u a kasashen Turai ko Amirka ba.

Wasu ma sukan yarda da wasu tunanunnuka marasa tushe dangane da addini, wadanda suke dauke da kararrraki da kuma guba, yana mai imani da su da kuma kokarin kare su. Ba wani kokari da yake yi na ganin ya tsamar da kansa daga gare su ba ko kuma canza su ba.

Hakika mutum wayayye shi ne mutumin da yake gina yardarsa da kuma mahangarsa kan abubuwa da kuma tunani ta hanyar fahimta da kuma masaniya. Hatta ma abubuwan da yake karbansu daga sauran mutane, ba ya yarda da su face sai bayan ya yarda da mutumin da yake nakalto masa wadannan abubuwa, kana kuma ya fahimce su sosai.



(27)


Halayyen Wayayyen Mutum

Daga cikin munanan halayen da suke damun mutum shi ne cutar mummunar dabi'a, kamar ji-ji da kai, girman kai, cuta, son kai, cutar da mutane da dai sauransu.

Don haka daga cikin siffofin mutum wayayye na farko shi ne nesantar siffofi abin ki da kuma cututtukan zuciya.

Mai yiwuwa daga cikin bayyanannun cututtukan zucin da ka iya samun mutum wayayye ita ce wuce gona da iri da kuma neman hawa kan sauran mutane.....

Don wasu sukan ji cewa yanzu sun fi sauran mutane sannan kuma sauran mutane ba su cancanci su girmama su ba; don haka suke mu'amala da su cikin girman kai da neman hawa kansu......

Hakika irin wannan hali yana nuni ne da nakasar wayewar wannan mutumin, da kuma irin cutar da take damunsa a cikin zuciyarsa wacce take hana shi yin mu'amala mai kyau da sauran mutane. Kamar yadda kuma take hana shi samun girmamawar sauran mutane da kuma kai shi ga fushi da kuma azabar Ubangiji Madaukakin Sarki.....

Babu shakka wayayyen mutumin da ya san ma'anar wayewa da kuma ilimi, wajibi ne wayewa



(28)


irin ta kyawawan halaye ta zamanto babban asasin wayewarsa.....don kuwa duk mutumin da bangaren kyawawan halaye na yanayinsa bai cika ba, to ba mutum ne ma'abucin cikakkiyar wayewa ba, face ma dai ba za a kira shi da sunan mutum wayayye ba. Hakan kuwa saboda ana kwatantata dan'Adam-takar mutum ne da kyawawan halayensa, su ne ma'aunin ilimi da cikar mutumtakarsa. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana jaddada wannan lamari cikin fadinsa cewa:

"Lalle an aiko ni don in cika kyawawan halaye".

"Wanda ya fi muminai cikar imani, shi ne wanda ya fi su kyawawan halaye".

Don haka wayayyen mutum shi ne mai kaskan-tar da kai wanda yake girmama sauran mutane da kuma sanin girman wayewar tasa, sannan kuma yana mu'amala da mutane gwargwadon yanayin tunani da wayewarsu. Don kuwa ko da a ce ya san wani abu daga cikin wayewa, to ai ya jahilci abubuwa da dama, kamar yadda wasunsa kuma suka jahilci wayewa da kuma wasu abubuwan da suka kebanta da shi, haka nan shi ma ya jahilci wayewa da kuma wasu abubuwan da suka kebanta da wasunsa. Wannan wata hakika ce da kowa ya santa, kuma ita ce mabubbugar kaskantar da kan mutum. Alkur'ani mai girma yana tabbatar da



(29)


hakan, Allah Madaukakin Sarkin Yana cewa:

"Muna daukaka darajoji ga wanda Muka so, kuma a saman kowane ma'abucin ilimi akwai wani masani". (Surar Yusuf, 12: 76)



(30)




(31)


Tsare-Tsaren Aiki

Kafin ka zamanto wayayyen mutum, dole ne ka tsara wa kanka wayewa.....

Haka kuma kafin ka tsara wa kanka wayewar, dole ne ka tsara wa kanka tafarkin isa ga wayewar.....

Akwai hanyoyi daban-daban na isa ga wayewa, daga cikinsu akwai littafi, mujalla, jarida, radiyo, telibijin, tattaunawa, tambaya, hanyar sadarwa ta internet da dai sauransu......

Don haka wajibi ne ka ribantar da lokacinka wajen samun wayewar da ta dace da aiki da kuma babbar manufarka.

Abin da zai biyo baya wasu muhimman koyarwa ne, wadanda yana da kyau mutum ya yi kokarin ya ga ya amfana da su wajen isa ga wayewar da yake so:

A duk lokacin da ka tashi, yi kokarin ka ga ka karanta wani abu daga cikin Alkur'ani mai girma, haka nan ma gabannin barci. Sannan kuma ka yi kokarin ka ga ka haddace ko da aya guda ce a kowace rana, kana kuma ka ba da himma wajen kiyaye abin da kake karantawa. Haka nan kuma ka



(32)


yi kokarin haddace hadisan Annabi (s.a.w.a.) guda biyu a kowane mako.....

Ka yi kokarin ka ware sa'a guda a kowace rana don karanta wani littafi na ilimin wayewa.....ka karanta jarida a kowace rana, sannan kuma ka saurari labarai da kuma sharhinsu da kuma sauraron shirye-shiryen da suke magana kan wayewa a radiyo da kuma telibijin......

Ka yi kokarin kirkiro wani kulob da kuma wata kungiya ta karatu tare da abokanka don zama kowane mako ko kuma tsakiyar wata don karanta wasu littattafa da suke bayani kan wayewa da kuma tattaunawa a kansu da kuma bijiro da tambayoyi da wasu shubuhohi don samo masu mafita.

Yi kokari ka karanta wata mas'ala daga cikin mas'alolin fikhu a kowace rana, sannan kuma ka yi kokarin fahimtar ma'ana da kuma abin da ta kumsa.....

Ka dauki wani littafi ko kuma wata mujalla tare da kai a lokacin da za ka yi tafiya da kuma karanta shi yayin da ka ke cikin mota ko kuma jirgi ko kuma yayin da ka ke jiran abin hawa a tasha......

Yayin da kake hutawa da rana, yi kokari ka ga ka karanta wani littafi ko kuma mujalla kafin ka yi barci.....

Ka ware wani littafi don rubuta wasu ilmummuka na gaba daya, wadanda kake bukatuwa



(33)


da su yayin da kake karanta wani littafi ko kuma ka ke sauraron radiyo ko telibijin, kana kuma ka rubuta sunan jarida ko mujalla ko kuma littafin da ka samo wannan ilimi da kuma ranar da aka buga.



(34)




(35)


Matsayinmu Dangane Da Wayewar Wasu

Duniyarmu ta yau ta bambanta da sauran zamunna da suka gabata ta hanyar abubuwan wayewa, isar da sako da kuma samuwar abubuwan wayewa.....

Babu shakka samuwar littattafa, jaridu da mujallu, radiyo da telibijin, internet, bidiyo, na'urar fad da dai sauransu, na daga cikin hanyoyin yada wayewa da kuma ilmummuka, suna daga cikin abubuwan da suka samar wa mutum hanyoyin wayewa masu girman gaske kana kuma a cikin karamin lokaci. Wasu ma sukan isa ga mutum kamar kyaftawan ido ba tare da wani cikas ba, sabanin shekaru aru-aru da suka gabata.

Irin wadannan hanyoyi na sadarwa da suka ci gaba, wadanda ake karantawa, ji ko kuma saurare, sun kasance suna nakalto mana nau'oi daban-daban na wayewa da ilmummuka cikin karamin lokaci ba tare da wani bata lokaci ba, saboda irin sauri da kuma yadda aka tsara su.

Wasu daga cikinsu sun ginu a kan ingantacciyar madogara, da ke taimakawa wajen



(36)


shiryar da mutum da kuma kyautata alakarsa da Ubangijinsa, gyara al'umma, fadada tunani, gina mutum da kuma kare mutum daga fasadi da munanan halaye.

A daidai lokacin da wasu kuma suke taimaka-wa wajen yada kafirci, bata da kuma nisanta mutum daga Allah Madaukakin Sarki, Mahaliccin halittu. Sannan kuma suna taimakawa wajen kwadaitar da mutum zuwa ga mummunan tarbiyya da kuma katange shi daga wayewa da kuma ci gaba na Musulunci, bugu da kari kan yada kararraki da sunan Musulunci da dai sauran irin wannan nau'i na lalata da komar da mutum baya zuwa ga lokacin jahiliyya, lokacin da dan'Adam ya rasa duk wata kima ta dan'Adamtaka da kuma kyawawan halayen da ya kamata ya kasance tare da su.

Da yawa daga cikin littattafa da makaloli da tunanunnukan da ake yadawa a halin yanzu suna cutar da tunaninmu na Musulunci da kuma kokarin haifar da shakku cikin zukatanmu kan girman Musulunci, wanda ya tsamar da mutum daga duhun zalunci zuwa ga haske, da kuma bayyanar da Musulunci ta hanyar da ya saba wa koyarwarsa ta hakika.....

Hakika muna fuskantar nau'oi daban-daban na wayewa, wadanda wasunsu ba abin da suke kokarin yi in ban da lalata mana kyawawan dabi'unmu na Musulunci, wadanda a ko da yaushe suke kokarin



(37)


tabbatar da mu a kan tafarkin gaskiya da girmama kai da kuma tabbatar da mu a matsayin 'yan'Adam, to amma fa sai dai ba dole ba ne mu yarda da dukkan wadannan wayewa da suke mana barazana. Dole ne mu bude idanuwanmu da kyau wajen ganin mun tace su, don mu dauki na dauka, mu zubar da zubarwa.

Don kuwa mu muna da asasi da kuma ma'auni na wayewa.....mu muna auna ingancin wayewa ne da akida da kuma shari'ar Musulunci da kuma abin da ilimi da kuma hankali (lafiyayye) ya tafi a kai. Duk abin da ya dace da wadannan abubuwa, ko daga gurin waye ya fito, to wayewa ce ingantacciya kuma abin karbuwa a gare mu, duk kuwa abin da ya saba wa hakan, ko daga wajen waye ya fito, to ba karbabbe ba ne a wajenmu, kuma za mu yi jifa da shi da kuma nesantarsa, nesantar mai tsananin da ba za mu sake waiwayarsa ba.

Don haka mu za mu yi mu'amala da wayewar wasu ne, mu'amala irin ta hanjin jimina, wato akwai na ci akwai na zubarwa. Ma'ana za mu dau wanda yake ingantacce kana kuma mai amfani wanda ya yi daidai da koyarwar Musulunci, sannan kuma mu yi jifa da wanda ya saba wa akida da kuma shari'armu, wanda babu makawa zai cutar da mu ne da kuma al'ummarmu.



(38)


Matsaya Dangane da Masu Ra'ayi na Daban

Hakika muna rayuwa ne cikin fadaddiyar al'umma, ma'abuciyar ra'ayoyi daban-daban na siyasa addini, wayewa da kuma zamantakewa.

Haka ma mutanen da muke tare da su, suna riko ne da mazhabobi daban-daban na Musulunci, da kuma ra'ayoyi da mahanga daban-daban na siyasa da kuma sauran addinoni.....

Don haka dole ne alaka da wadannan mutane, akidoji da ra'ayuyyuka, ta kasance a bisa asasin fahimta da kuma tattaunawa. Hakan kuwa ta hanyar ilimi da sauran hanyoyin tunani ne.....

Dole ne mu san ra'ayoyin wasunmu matukar dai muna son daukan matsayi dangane da su. Ba ya inganta mu dau matsaya kan wani lamari ko kuma wani mutum, ba tare da mun san ra'ayinsa da kuma tattaunawa da shi ba, don hakan babu abin da zai kai mu gare shi face kuskure da zato maras tushe.

Sannan kuma babban kuskure ne a maida sabanin ra'ayin da ke tsakanin al'umman musulmi zuwa ga adawa da kuma kiyayya (wanda hakan kuwa babu inda zai kaimu in ban da raunana kanmu karfinmu da kuma ba wa makiya damar shigowa cikinmu da yi wasan kura da mu). Don kuwa a matsayinmu na musulmi mun yi imani da 'yancin



(39)


fadin albarkacin baki gwargwadon yadda shari'a ta tanadar, kana kuma muna yarda da raddi da kuma bude fage don yaduwar ra'ayuyyuka daban-daban wadanda za su amfanar da mu, sai dai fa dole ne irin wadannan tattaunawa su kasance na ilimi da kokarin tabbatar da hakika. Amma a duk lokacin da aka sami sabanin haka, to da wuya a kai ga manufa da kuma tabbatar da abin da ya dace.