Haihuwar Sayyida Fatima al-Ma'asumah (a.s)
Ita dai Sayyida Fatima al-Ma'asumah (s) 'ya ce ga Imam Musa al-Kazim (a.s) Limamin Shi'a na 7,
kuma kanwace ga Imam Ridha (a.s), Limamin Shi'a na 8. To kamar dai sauran Ahlulbaiti (a.s), Fatima al-Ma'asumah, ta fuskanci matsaloli da takuri a rayuwarta da suka sosa mata zuciya da kuma yin tasiri a cikin rayuwarta. Hakan kuwa ya faru ne saboda kasantuwan lokacin Imamancin mahaifinta ya yi daidai da lokacin mulkin azzaluman sarakunan Bani Abbas, wato al-Saffah, al-Mansour al-Dawaniki, al-Haadi, al-Mahdi da kuma Haruna Rashid, wadanda suka gudanar da siyasar zalunci da tursasawa akan Imam Kazim (a.s) da kuma takura masa rayuea bugu da kari kan rufe shi a gidajen yari daban-daban kafin daga karshe su kashe shi. Hakan kuwa ya biyo bayan irin kin shirun da shi Imam din ya yi ne kan irin zaluncin da suke yi da kuma take hakkokin al'umma da suke yi ne a lokacin mulkin nasu. To raba Fatima Ma'asumah da wannan mahaifi na ta, a lokacin kuwa tana karama ya sanya ta cikin halin damuwa da bakin ciki. To a irin wannan lokaci dai kulawa da kuma tarbiyyarta ta koma ga hannun mahaifiyarta da kuma yayanta ne. To bayan shahadar mahaifinta da kuma fara Imamancin dan'uwanta Imam Ridha (a.s), irin wannan yanayi dai ya ci gaba musamman bayan tilasta Imam Ridha hijira daga garin Madina zuwa garin Marwa da sarkin Abbasiyawa na wancan lokacin Ma'amun ya yi masa. Don haka Fatima Ma'asumah ta ci gaba da zama cikin irin wannan yanayi a birnin Madina ita kadai ba tare da yayannata ba har na shekara guda lokacin da ya aiko mata da wasika yana gayyatanta ta zo wajensa a Marwa (kamar yadda wasu ruwayoyi suka nuna). To bayan nan sai Fatima Ma'asumah (a.s) tare da 'yan uwanta Fadhl, Ja'afar, Hadi, Kasim da kuma Zaid suka kama hanya zuwa garin Marwa don ganin wannan yaya na su, to sai dai kuma hakan bai samu ba, inda saboda wahalhalu daban-daban da Fatiman ta fuskanta, ta kamu da rashin lafiya a hanya. Saboda tsananin da wannan rashin lafiya ya yi dai ya tilasta wa Fatima al-Ma'asumah da tawagarta su yada zango a garin Sawa don ci gaba da jinya. A wancan lokacin birnin Kum ya kasance (kamar yadda kuma har yanzu ya ke) wata helkwata ce ta mabiya Ahlulbaiti (a.s), don haka jin labarin rashin lafiyar Fatima Ma'asumah da kuma yada zangon da ta yi a garin Sawa, sai ya sa manyan garin suka nufi Sawan da kuma bukatar Ma'asuman ta dawo garin Kum. Ma'asumah dai ta yarda da wannan bukata ta su, inda ta shirya da tawagar tata suka kama hanyar Kum, inda jama'a suke jiran isowarta. Bayan isowarta birnin Kum din a ranar 23 ga watan Rabi'ul Awwal shekara ta 201 bayan hijira, Fatima Ma'asumah ta zauna ne a gidan wani mutum mai suna Musa bn Khazraj, inda ta ci gaba da jinya da kuma bautan Ubangijinta. To sai dai kuma ba ta jima ba a wannan gari na Kum, inda ta rasu a ranar 10 ga watan Rabius Thani shekara ta 201 bayan hijiran wato kimanin kwanaki sha bakwai zuwa sha takwas kenan a garin, inda aka bisne ta a garin. Har ya zuwa yanzu da hubbarenta ya kasance wajen ziyarar miliyoyin al'umma ne a kowace shekara. Akwai ruwayoyi da daman gaske da suke magana kan wannan hubbare na Fatima Ma'asumah da kuma falalolin ziyararsa. Daga cikin wadannan ruwayoyi, akwai cewa:
![]() ![]() ![]() |