|
|
| |||
![]() ________________________ ![]()
![]() An haifi Allamah Sayyid Muhammad Husaini Fadhlullah a garin Najaf al-Ashraf dake kasar Iraki a ranar Sha tara ga watan Sha'aban shekara ta 1354 bayan hijira, wanda ta yi daidai da shekarar 1935 Miladiyya, a lokacin da mahaifinsa, Ayatullah Sayyid Abdulra'uf Fadhlullah (r.a) ya yi hijira zuwa can (Najaf) don neman ilmin addini. Kasantuwan mahaifin nasa malami ne na addini, don haka Ayatullah Fadhlullah ya sami tarbiyya irin ta addini tun yana karami awajen wannan mahaifi nasa. Allamah Muhammad Husaini Fadhlullah ya fara karatunsa na Hawza ne dai tun yana karamin yaro. Inda ya fara karatun nasa a wajen mahaifinsa, har ya gama marhalan karatun da ake kira Sutuh (wato marhalan farko na karatun hawza). A yayin wannan lokaci dai Allamah Fadhlullah darasin harshen larabci, da suka hada da nahwu, sarfu da dai sauransu, haka nan kuma ya karanci Mandik, Usul da kuma Fikhu. A wannan lokaci dai ba shi da wani malami da ya wuce babansa (Allah Ya yi masa gafara), in ban da darasin juzu'i na biyu na littafin Kifayatul Usul da ya yi a wajen Sheikh Mujtaba Lankarani. To bayan gama wannan marhala na karatu a lokacin yana dan shekara goma sha shida, Allamah Fadhlullah ya koma wajen wasu malumma na daban don karanta marhala na Bahasul Kharij (wato darasin da manyan malumma suke bayarwa ba tare da ayyana wani littafi guda ba). A yayin wannan karatu dai, Allamah ya yi karatu ne a wajen manyan maraja'ai na wancan lokacin irin su Ayatullah Abul Kasim Khu'i, Sayyid Muhsin Hakim, Sayyid Mahmud Shahrudi da kuma Sheikh Husain al-Hilli (r.a). Baya ga hakan kuma Allamah ya kasance ya kan halarci tarurruka na tattaunawa ta ilmi da sauran dalibai da malamai suke shiryawa don karuwa da dimbin ilimin da Allah Ya yi musu. Allamah bai dai takaita da wannan darasi na addini kawai da ya ke dauka a wajen wadannan malumma ba, ya kasance ya kan yi karance-karance kan lamurran siyasa da ke gudana a duniya da kuma karance-karancen littattafan manyan masana kan al'amuuran siyasa da kuma marubuta wake. Bayan shekaru 22 na darasi a garin Najaf a makarantun addini na garin, Allamah Fadhlullah ya koma kasar Labanon a shekara ta 1385 Hijiriyya (1975 Miladiyya) don ayyukan isar da sakon Musulunci, bayan gayyatarsa da wasu muminai na yankin Nab'ah dake gabashin birnin Beirut, wadanda suka assasa wata cibiya ta taimako, suka yi don ya kasance tare da su da kuma shiryar da su kan harkar da suke gudanarwa. A yayin wannan lokaci, Allamah Fadhlullah ya assasa makaranta ta addini don ilmantar da mutane da wayar masu da kai kan a bisa koyarwa ta addinin Musulunci, bugu da kari kan shirya tarurruka na wa'azi a wurare daban-daban na kasar Labanon din don isar da sakon Musulunci.
Sai dai kuma daga baya, Allamah Fadhlullah ya bar wannan yankin na gabashin birnin Beirut din, inda ya koma kudancin birnin saboda yakin da ya faru a kasar da kuma kokarin kashe shi da aka yi da kuma dushe tasirin da ya ke da shi a tsakankanin matasa. Daga cikin wannan kokari na ganin bayansa kuwa shi ne wani harin ta'addanci da aka kai Bi'ir al-Abd, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tamanin da kuma raunana da dama, lamarin da daga baya aka gano cewa kungiyar leken asirin kasar Amurka ta CIA ita ce ta shirya shi. Barkewar wannan yaki na basasa a kasar Labanon ya sa da yawa daga cikin al'umman kasar sun rasa iyalansu, yara sun rasa iyayensu, mata sun rasa mazajensu da dai sauransu. Don haka a wannan lokacin Allamah Fadhlullah ya sake kirkiro wata cibiya ta taimakon marasa galihu, inda ya ci gaba da taimaka wa wadannan bayin Allah da suka rasa masu kula da su din. Baya ga wannan aiki na taimako da kuma koyarwa da muka yi magana a baya, Allamah Fadhlullah ya yi rubuce-rubuce na daga littattafa da kuma makaloli da daman gaske a bangarori daban-daban na rayuwa, wadanda sun kai kimanin saba'in. Wasu daga cikin wadannan littattafa shi ya ke rubutawa da hannunsa, wasu kuma dalibansa ne suke rubuta su, wato su tattaro jawabai da kuma darussan da yake bayarwa sai mu mai da su a matsayin littafi don amfanin al'umma gaba daya. Da yake wadannan littattafa na Allaman suna da yawa, za mu kawo kadan ne kawai daga cikinsu:
|
||||