SAYYID SHAHID BAQIR AL-HAKIM (R.A)
________________________


An haifi Ayatullah Sayyid Muhammad Bakir Hakim ne a shekarar 1939 a garin Najaf mai tsaki, mahaifinsa dai shi ne babban marja'in shi'a din Ayatullah al-Uzma Muhsin Hakim (r.a) wanda ya kasance babban marja'in shi'a tun daga shekarar 1955 zuwa 1970, kuma Ayatullah Bakir Hakim shi ne dansa na biyar.

Zuriyar al-Hakim dai sananniyar zuriya ce a kasar Iraki da sauran kasashen musulmi musamman mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s), don haka muna iya cewa Ayatullah Bakir Hakim ya taso ne daga gidan malamai ma'abuta addini da kuma gwagwarmaya da fada da zalunci.

Ayatullah Bakir Hakim ya fara harkokinsa na addini da siyasa ne tun yana karami dan shekaru 13 a duniya, inda ya shiga kungiyoyi masu fada da zalunci a kasar Irakin.

Ayatullah Hakim dai yana daga cikin mutanen farko-farko kana na gaba-gaba da suka kafa kungiyar siyasa ta Musulunci tare da Shahid Bakir Sadr tun cikin shekarun 1950, kuma sun ci gaba da kasancewa tare da juna har lokacin da shi Shahid Sadr din ya yi shahada a 1980 a hannun gwamnatin kama karyar kasar Irakin ta wancan lokacin karkashin jagoranci Saddam Husaini.

A shekarar 1972, jami'an tsaron tsohuwar gwamnatin Ba'thawa ta kasar Iraki sun kame Marigayi Sayyid Bakir Hakim inda suka tsare shi da kuma gallaza masa nau'oi daban-daban na azaba, to sai dai daga baya gwamnatin ta sako shi saboda irin boren da al'ummar Iraki suka yi da kuma nuna rashin amincewarsu da hakan.

To sai dai kuma gwamnatin ba ta bar shi ba, don kuwa a shekarar 1977, jami'an tsaron gwamnatin sun sake kame shi saboda boren da al'ummar birnin Najaf mai tsarki suka yi a watan Fabrairun wannan shekara, inda wata kotu ta musamman ta yanke masa hukumci zama gidan maza na rai da rai ba tare da an wata shari'a da aka gudanar ba. To sai dai a wannan karon ma gwamnatin ta sako shi a watan Yulin shekarar 1979 bayan matsin lamban da gwamnatin ta fuskanta daga al'ummar kasar.

Bayan fitowarsa daga gidan yari, Ayatullah Hakim ya ci gaba da wannan gwagwarmaya tasa da kuma akala da Shahid Bakir Sadr har zuwa shekarar 1980 lokacin da gwamnatin kama-karyan Iraki ta kashe Shahid Sadr din.

Jin kadan bayan fara kallafaffen yakin da Iraki ta kallafawa Iran, Marigayi Ayatullah Bakir Hakim ya yanke shawarar barin kasar Irakin a shekarar 1980 da kuma isowa Iran don gudun hijira a can.

Marigayi Ayatullah Bakir Hakim, bayan isowarsa Iran, ya ba da gagarumar gudummawa wajen kirkiro Majalisar Koli ta Juyin Juya Halin Musulunci ta Iraki a shekarar 1982. Kafa wannan kungiya dai ta kasance babbar barazana ga tsohuwar gwamnatin kama karya ta Irakin, don haka gwamnatin ta dirka wa sauran iyalan gidan Hakim din inda ta kame kimanin mutane 125 daga cikin iyalan wannan gida a shekarar 1983, inda daga baya gwamnati ta kashe mutane 29 daga cikin iyalan gidan Hakim din tara daga cikinsu kuwa 'yan'uwa ne shakikai na Marigayi Bakir Hakim din.

Irin wannan zalunci da tsohuwar gwamnatin Irakin ta ke yi wa iyalan gidan Hakim din dai bai sa Marigayi Hakim din yin sassauci kan wannan matsaya tasa akan gwamnatin kama-karyar Saddam Husainin ba, duk ma da kashe dan'uwansa shakiki Sayyid Mahdi al-Hakim da jami'an leken asirin tsohuwar gwamnatin suka yi a kasar Sudan a watan Janairun 1988.

A shekarar 1984, an zabi Marigayi Sayyid Hakim a matsayin shugaban Majalisar Koli ta Juyin Juya Halin Musulunci na Irakin wanda kuma ya ci gaba da kasancewa shugabanta har yau din nan da ya yi shahada.

Marigayi Sayyid Hakim ya ci gaba da ayyukansa na siyasa a Iran din har lokacin da ya koma kasarsa ta haihuwa Iraki a ranar 10 ga watan Mayun wannan shekarar bayan faduwar gwamnatin Irakin, shi kuma bayan ya kwashe shekaru ashirin da uku yana gudun hijira a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Bayan komawarsa gida dai ya samu tarbar al'ummar Iraki daga ko ina cikin fadin kasar da ana iya cewa al'ummar Irakin ba su taba ganin irin taba cikin shekarun nan.

Marigayi Sayyid Hakim, bayan komawarsa gida ya zauna ne a garin Najaf inda ya ci gaba da jagorantar sallar juma'a da kuma sauran nau'oi na mu'amala da mutane da kuma shiryar da su.

Don karin bayani kan Shahid Sayyid Hakim da irin ayyukansa ana iya komawa ga shafinsa na internet wato: www.al-hakim.com