|
|
| |||
![]() ![]() ________________________
SAKON IMAM KHUMAINI (R.A) YAYIN SHAHADAR AYATULLAH SHAHID MUTAHARI (R.A)
(بسم الله الرحمن الرحيم )
( إنَّا لله و إِنَّ إلَيْهِ راجعون )
Ina taya Musulunci, manyan waliyai madaukaka da sauran al'ummar musulmi musamman jaruman al'ummar Iran juyayi da kuma murnar wannan babban rashi na babban shahidi kuma masani marigayi Alhaji Shaikh Murtadha Mutahari (Allah Ya rahamshe shi); juyayi (na) saboda shahadar wannan mutumin da ya gudanar da dukkanin rayuwarsa madaukakiya wajen ci gabantar
da manufofin Musulunci madaukaka sannan kuma ya yi fada da camfe-camfe da kauce wa hanya; juyayi saboda rashin wannan mutumin wanda da wuya ake samun irinsa a bangaren sanin Musulunci, ilmummukansa da kuma Alkur'ani mai girma. Hakika na rasa dan dake da matsayi a zuciyata kuma a halin yanzu ina cikin juyayin wannan mutum ne wanda na dauke shi a matsayin sanyin zuciyata.
Lalle shahadar wannan madaukakin da ta sanya Musulunci ya rasa wani jigo nasa da cika shi zai yi wuya. Ina farin ciki da taya murna kuma saboda samun irin wannan mutum ma'abucin sadaukarwa wanda a lokacin rayuwarsa da kuma bayanta ya haskaka tafarki kana kuma ya ke ci gaba da hakan. Sannan kuma yayin nuna farin cikina, ina taya madaukakin addinin Musulunci, addinin da
ke tarbiyyantar da dan'Adam, da kuma al'ummar musulmi murnar samun irin wannan da wanda haskensa ya haskaka rayuwar mutane sannan kuma ya haskaka duhhunai. Duk da cewa dai na yi rashin wannan madaukakin da nawa, amma ina alfahari cewa Musulunci ya samu irin wannan da kuma yana da shi.
Mutahari dai, wanda ya kasance ma'abucin tsarkin ruhi da karfin imani da bayani da da wuya ka samu irinsa, ya tafi, zuwa ga madaukakin matsayi, to amma ya kamata magabta su san cewa tafiyarsa ba tana nufin tafiyar shaksiyyarsa ta Musulunci da ilmi ba ne.
'Yan ta'adda ba za su iya kashe dukkanin ma'abuta Musulunci ba. Ya kamata su san cewa, cikin ikon Allah Madaukakin Sarki, al'ummarmu sukan kara samun karfin gwuiwa da tsayin daka sanadiyyar kashe manyan mutanenta a tafarkin fada da fasadi, danniya da mulkin mallaka. Hakika al'ummarmu ta kama tafarkinta sannan kuma ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wajen ganin
bayan rassuna tsohuwar gwamnatin (Shah) da 'yan koranta ba. (Addinin) Musulunci dai ya ci gaba ne ta hanyar sadaukar da magoya bayansa. Shahada da mutumci sun kasance danjuma da danjummai ne a wajen addinin Musulunci tun farko-farkonsa har zuwa yau. Gwagwarmaya a tafarkin Allah da kuma tafarkin ('yanto) marasa galihu na daga cikin tsare-tsaren Musulunci na gaba-gaba.
( (ومَا لَكُمْ لا تقاتلونَ في سَبيل اللهِ والمستضعفين من الرجال والنسا,ِ والولدان) )
"Kuma mene ne ya same ku, ba ku yin yaki a cikin hanyar Allah, da wadanda aka raunanar na daga maza da mata da kuma yara…..".
Su dai wadannan mutane wadanda suka dandani mutuwa da rashin nasara, sannan kuma suke so su dau fansa kan hakan ta hanyar wannan mummunan aiki nasu, ko kuma suke zaton cewa za su iya razana masu jihadi a tafarkin Allah, to fa su san cewa sun yi kuskure. (Su san cewa) dukkan wani gashi ko kuma digon jini na wani shahidi daga cikinmu da zai zuba, to za
a tayar da wani mutum guda ne ma'abucin sadaukarwa da juriya da shi.
Ku sani sai dai idan za ku iya kashe dukkanin wannan jarumar al'umma, idan kuwa ba haka ba, to kashe wani mutum guda komai girmansa kuwa ba wani amfanin da zai muku. Wannan al'umma tamu dai, saboda imaninta da Allah Madaukakin Sarki sannan kuma saboda raya addinin Musulunci ba za ta taba ja da baya ba saboda wannan kisan gilla (naku). Mu mun shirya wa
sadaukarwa da kuma shahada a tafarkin Allah Madaukakin Sarki.
Don haka na sanya ranar Alhamis 13 ga watan Ordebehesht 1358 ta zamanto ranar zaman makoki na gaba daya don girmama ruhin wannan mujahidi ma'abucin sadaukarwa a tafarkin Musulunci, kuma ni ma da kaina zan zauna a makarantar Fa'iziyya a ranakun Alhamis da Juma'a (don juyayi). Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya yi rahama da kuma gafara ga wannan madaukakin da na Musulunci,
sannan kuma ya daukaka addinin Musulunci.
Amincin Allah Ya tabbata ga shahidai a tafarkin gaskiya da 'yanci.
RUHULLLAH AL-MUSAWI AL-KHUMAINI
SAKON IMAM (R.A) YAYIN JUYAYIN SHEKARAR FARKO TA SHAHADAR SHAHID MUTAHARI (R.A)
(بسم الله الرحمن الرحيم )
Duk da cewa dai wannan Juyin Juya Halin Musulunci, baya ga irin makirce-makircen makiya da 'yan amshin shatansu, cikin ikon Allah da yardarSa ya yi nasara sannan kuma cibiyoyi da ma'aikatun (gwamnati Musulunci) daya bayan daya cikin shekara guda sai ci gaba suke ta yi wajen gudanar da ayyukansu, to amma duk da haka munafukai makiya wannan juyi sun haifar da wani gibi da cike shi
zai yi wuya ga al'ummarmu da cibiyoyin ilmi da na Musulunci, hakan kuwa shi ne kisan gillan da suka yi wa marigayi babban masani Hujjatul Islam Hajj Shaikh Murtadha Mutahari, Allah Ya rahamshe shi.
A hakikanin gaskiya, a halin da nake ciki (a daidai lokacin Imam yana fama da jinyar ciwon zuciyar dake damunsa) ba zan iya nuna irin damuwa da matsayi da wannan mutum (Mutahari) yake da shi ba. To sai dai abin da zan ce dangane da shi, shi ne cewa lalle ya yi gagarumar hidima wa Musulunci da ilmi, shi ya sa ma damar da makiya 'yan ta'adda suka samu wajen kawar da wannan bishiya
mai dadin 'ya'ya (Mutahari) daga hannun cibiyoyin ilmi da Musulunci da kuma hana su ci gaba da amfanuwa da ita ya kasance babban abin bakin ciki.
Mutahari dai ya kasance da kana sanyin ido na kuma babbar garkuwa ga cibiyoyin addini da na ilmi sannan babban mai hidima ga al'umma da wannan kasa. Allah Ya rahamshe shi Ya kuma sanya shi cikin manyan masu hidima wa Musulunci.
A halin da ake ciki labari ya zo cewa masu adawa da Musulunci da kuma sauran kungiyoyin dake adawa da Juyin Juya Halin Musulunci, ta hanyar bakar farfagandarsu, suna kokarin raba daliban jami'oinmu daga amfani da litattafan wannan babban malami. Don haka ina kira ga daliban jami'a da sauran masana da kada su bar litattafansa, su mance da kararrakin makiya. Ina rokon Allah Madaukakin
Sarki nasara cikin ayyukanmu.
Amincin Allah ya tabbata ga bayin Allah salihai.
RUHULLAH AL-MUSAWI AL-KHUMAINI
SAKON IMAM (R.A) YAYIN JUYAYIN SHEKARA TA BIYU TA SHAHADAR SHAHID MUTAHARI (R.A)
(بسم الله الرحمن الرحيم )
Yanzu lokaci ne na shahadar Shahid Mutahari wanda a 'yar gajeruyar rayuwarsa ya bar wasu abubuwa masu amfani da suke nuni da irin kauna da soyayyar da yake da ita ga Musulunci. Shi mutum ne da ya yi amfani da alkalami da tunaninsa wajen karin haske kan mas'alolin Musulunci da na falsafa ta yadda al'umma za su fahimta ba tare da wata damuwa ba. Babu shakka dukkan litattafa da jawabansa cike
suke da ilmi kuma masu amfanarwa ne, kamar yadda nasihohi da wa'azuzzukansa, wadanda sun fito ne daga cikin zuciyarsa da take cike da imani da akida, masu amfani ne ga masana da sauran jama'a.
Fatanmu dai ita ce, a samu damar amfanuwa da wannan babbar bishiya mai cike da 'ya'yaye na ilmi da imani. Abin bakin cikin shi ne cewa hannayen 'yan ta'adda ba su ba da wata sanarwa ba sannan kuma sun hana matasanmu amfanuwa da wannan abin amfani mai daukaka, to sai dai muna gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya sanya abubuwan da suka saura na wannan shahidin malami suna cike da abubuwan koyarwa da tarbiyya.
Shahid Mutahari dai ya tafi, muna rokon Allah da Ya tayar da shi tare da WaliyanSa.
RUHULLAH AL-MUSAWI AL-KHUMAINI
WANI SASHI NA JAWABIN IMAM (R.A) A SHEKARA TA UKU DA SHAHADAR SHAHID MUTAHARI (R.A)
....da yake yau yayi daidai da shekarar shahadar Marigayi Shahid Mutahari Allah Ya yi masa rahama, don haka dole ne in ce wani abu kan hakan. Marigayi Shahid Mutahari dai wani mutum ne da ya hada bangarori daban-daban, sannan kuma irin ayyukan da ya yi wa matasa da sauran al'umma da wuya ake samun wani mutum da ya yi irinsu. Dukkanin abubuwan da ya bari (na ilmi) suna da kyau, kuma masu shiryar da
dan'Adam ne, lalle ya yi aiki wa wannan al'umma.
Ya Allah, don ManzonKa, ka tashe shi tare da Manzon Allah (s.a.w.a)....
|
||||