ALLAMAH SHAHID MURTADHA MUTAHARI
________________________


An haifi Shahid Murtadha Mutahari ne a shekarar 1919 a garin Fariman da ke lardin Khurasan na kasar Iran. A wannan gari ne ya yi karatunsa na firamare daga bisani kuma ya samu zuwa garin Masshad don ci gaba da makarantar gaba da firamare. Ya kuma gama wannan makaranta ne yana dan shekara 18 a duniya. Bayan ya kammala wannan karatu ne ya koma birnin Kum, ya fara harkarsa ta neman ilmin addini.

Isarsa birnin Kum ke da wuya sai ya fara karatu a karkashin manyan malamai kamar su Imam Khumaini da Ayatullah Muhakkik da Agha Mirza Mahdi Ashtiyani da Allama Tabataba'i da kuma Ayatullahil Uzma Burujardi.

A karkashin wadannan malaman ne Ayatullah Mutahari ya zage damtse ya yi ta karatu ba ji ba gani yadda cikin dan karamin lokaci sai ga shi ya yi zurfi cikin fannonin ilimi daban-daban, kamar su Usulul Fikihu da Tarihi da Falsafa da Ilmul Hadis da Ilmul Kalam da Tafsiri da Mandik da dai sauran fannonin ilmin da ake karantar da su a birnin Kum.

Ayatullah Mutahari ya kasance malami ne cikakke, ga shi kuma ma'abucin magana da rubutu. Saboda iya maganarsa ne ma babu inda ba a gayyatarsa ya je don ya yi lakca a dun fadin Iran.

Ban da kuma sanin da Allah Ya hore masa na ilmin addini, idan aka koma ta fannin ilmin zamani kuwa malaman boko ma haka suka ganshi, domin kuwa farfesa ne guda na ilmin falsafa a jami'ar birnin Tehran. Irin wannan kwazo nasa ne ya sa ya karanta da dama daga cikin litattafan da masanan Turai suka rubuta da kuma yi musu raddi.

Abin ban al'ajabi kuma shi ne yadda yake yi wa rubuce-rubucen wadannan mutane fidar kaza ya ware shirmen da ke ciki da kuma kafa hujja akan wadanda suke da kyau.

Mutahari dai kamar yadda kowa ya sani ne malami ne wanda ko da wasa ba ya hari a ci wa Musulunci tuwo a kwarya, domin kuwa duk lokacin da wani marubuci daga Turai alal misali ya yi wata katobara, nan da nan zai nemi littafin ya yi nazari akansa sannan kuma ya yi masa raddi tare da kafa masa hujjoji daga cikin litattafan nasa ya kuma sa shi ala tilas ya janye wannan mummunar ra'ayi nasa. Kamar yadda kuma ko da wani malami ne musulmi ya kauce hanya, nan da nan ya kan yi kokarin dawo da shi ko da kuwa a wace mazhaba ya ke don mutum ne da ya san mazhabobin Musulunci daban daban.

Daya daga cikin gagaruman aikin da Ayatullah Mutahari ya yi shi ne kokarin da ya yi wajen tabbatar da rashin ingancin akidar 'yan kwaminisanci, don kuwa lokacin da 'yan kwaminisancin suka fara barna a jami'ar Tehran, suna ta dulmuyar da yara da sanya su suna ridda daga Musulunci, nan da nan Ayatullah Mutahari ya yi hijira ya baro Kum ya dawo Tehran domin yin jihadin akida da 'yanto da yaran daga fadawa wutar 'yan kwaminisanci. Hakan kuwa aka yi domin ya zo ya toshe bakin 'yan kwaminisancin ya kure su da kuma hana su sakat duk da irin bakin da aka sansu da shi. Bayan dan lokaci kadan sai ga matasan sun dawo taitayinsu, duk sun rabu da malaman karya masu akidar bata sun ko ma ga malamin da ya san Allah da ManzonSa ya kuma san duniya da lahira tare da kyakkyawar sanin zamaninsa. Wadannan dalibai kuwa sun ba da gudummawarsu nesa ba kusa wajen samun nasarar Jagoran Juya Halin Musulunci. Don haka Ayatullah Mutahari ya ci gaba da zama a Tehran din har lokacin da ya yi shahada jin kadan bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musuluncin a shekarar 1979.

Baya ga wannan gagarumin aiki da Ayatullah Mutaharin ya yi, ya kuma rubuta litattafa da yawan gaske, ya kuma bar kaset-kaset na wa'azi bila adadin wadanda ake ta rubuta su ana ta mayarwa littafi kana kuma ana ta fassarawa zuwa harsuna daban-daban na duniya. Daga cikin litattafan nasa kuwa har da Ka'idojin Hikima, Mutum da Kaddara, Gudummawar Iran ga Addinin Musulunci, Lullubin Mata A Musulunci, Nazari Cikin Nahjul Balaga, Dangantakar Mutum da Imani, Wahayi da Annabci, Rayuwa Madawwamiya da kuma Dangantakar Al'umma da Tarihi, da dai sauransu da dama.

Irin wannan kokari da gagarumar gudummawa da Ayatullah Mutahari ya sanya makiya cikin halin damuwa da rashin jin dadi, don haka suka kasance suna ta kulla kulle-kulle ganin bayansa. Hakan kuwa ya faru don sun samu nasarar kashe shi inda ya yi shahada a watan Janairun 1979 jin kadan bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci a Iran.

Dangane da wannan shahada, an ruwaito Imam Khumaini (r.a) yana cewa:

"Na yi rashin da wanda yake tamkar rabin raina. Ina jimamin mutuwar wannan mutumi wanda na dauke shi a matsayin ribar rayuwata. Shahadar wannan babban malami ta bar wani babban gibi wanda babu abin da zai cike shi cikin sauki. Ina mai alfaharin samun irin wadannan bayin Allah masu sadaukar da kai, wadanda ke haskaka hanyar shiriya ga mutane ko da bayan ransu! Ina mai barka ga Musulunci mai limantar da mutane da tarbiyyar irin wadannan gwaraza hazikai masu rayar da matattu (jahilai) suna kuma haskaka dubu da iliminsu".

Matsa nan don ganin sakonnin Imam Khumaini yayin juyayin Shahadar Allamah Mutahari.

Don karin bayani kan Shahid Mutahari da irin ayyukansa ana iya komawa ga wannan shafi na internet wato: www.motahari.org