AYATULLAHI SHAHID BAKIR SADR
________________________


An haifi marigayi, Shahid Ayatullah Bakir Sadr ne a shekarar 1930 a garin Kazimain da ke kasar Iraki. Mahaifinsa shi ne Sayyid Haidar Sadr mashahurin malami wanda ya rasu tun Bakir Sadr yana da shekara goma sha hudu a duniya.

Gidansu dai gida ne na sharifai kuma mahaifansa masu riko ne kam-kam da addinin Musulunci. Zuriyar gidan zuriya ce mai albarka da tarin alheri domin an dade ana samun mashahuran malamai masu gwagwarmaya a tafarkin Allah da kare addininSa.

Daga cikin malaman da wannan gida ya haifar har da Sayyid Sadruddin wanda ya yi zamaninsa da rayuwarsa a birnin Ilmi na Kum da ke Iran, akwai kuma Sayyid Muhammad Sadr da ya yi zamaninsa a Iraki kuma shi ne jagoran gwagwarmayar da ta rike wuyan 'yan mulkin mallakar Birtaniyya a shekarar 1920. Haka nan kuma akwai Sayyid Sharafuddin marubucin littafin nan na Al-Muraja'at da ya rike wa 'yan mulkin mallakan Faransa wuya a kasar Labanon a shekarar 1943 wanda shi ma na daga cikin 'yan wannan gida, sai kuma Imam Musa al-Sadr wanda shi ne ya assasa kungiyar Amal a kasar Labanon wanda ya bace bayan ya halarci wani taro a kasar Libya a shekarar 1978 har ya zuwa yanzu kuwa ba a san inda yake ba. Daga nan kuma sai wannan bawan Allah, wato Sayyid Bakir Sadr.

Bakir Sadr tun yana karami ya fara karatu, kuma bai sha wata wahala ba dangane da kwarammniyar neman inda zai je ya yi karatu illa iyaka dai kawai ya fara karatunsa a gidansu inda kowa ya kan zo ya figi rabonsa. Da yake kuma Allah Ya ba shi wata irin kwanya ta saurin fahimta, yana da shekara goma, kusan duk ya karance litattafan dalibai na sama da shi a tarihi da mukaddamar ilimin shari'a da kuma sauran fannoni daban-daban. Litattafa da dama ma shi kadai dinsa ya karance su ba tare da malami ba.

Kafin ya kai shekaru ashirin dai sai da ya kai matsayin ijtihadi inda zai iya tsamo hukumce-hukumcen Musulunci kai tsaye daga Alkur'ani da hadisi. A lokacin ne kuma ya fahimci wasu kura-kurai da suka kasance a cikin wasu litattafan da aka dade ana karantar da su musamman ma a bangaren mandik. Don haka ya yi ta kokarin bayyana irin nakasar da ke cikin wadannan littattafam hasali ma daga baya sai da ya rubuta littafi shi kansa a mandik mai suna Usus al-Mandikiyyah lil-istikara.

Littafinsa na farko da ya rubuta shi ne wanda ya shafi asasin ilmin fikihu wato Ilmul Usul; lokacin yana da kimanin shekaru ashirin da uku. Daga cikin littattafan da ya rubuta akwai Falsafatuna (Kan falsafa), Iktisaduna (kan tattalin arziki), al-Bank al-Ribawi fil Islam, al-Insan al-Mu'asir awl mushkilatul Ijtima'iyya, Fadak fi al-Tarikh, Wilaya (kan shugabancin Ahlulbaiti), Al-Imamiyyah wa aslafihim minash shi'ah da dai sauransu.

A shekara ta 1958 ya yi kira ga kasashen larabawa da su farka su dubi irin fasadi da lalatar da ke kunno kai cikin kasashensu daga Turai. Ya yi kira kuma da babbar murya kan cewa lalle ne a yi ta maza don tserar da jama'a daga irin wannan annoba. Ya rubuta 'yan kananan litattafa ana raba wa jama'a don su tuna dalilin zuwansu duniya, da kuma inda suka sa gaba da kuma abin da ya kamata su yi wa al'ummarsu tun lokaci bai kure ba.

Ta fannin siyasa kuwa ya dauki wani mataki don kawo gyara a cikin kasar Iraki ita kanta, wanda yake gyara ne cikin ruwan sanyi. Ya hada kan malaman kasar ta hanyar kafa kungiyar malamai a garin Najaf don su magance bambance-bambancen da ke akwai. Ya kuma yi kokarin ganar da jama;a da bayyana musu cewa siyasa da Musulunci tun fil azal a hade su ke domin siyasa ita ce hanyar tafiyar da rayuwar dan'Adam, Musulunci kuwa dama ya zo ne don ya yi jagorancin dan'Adam zuwa ga alherin duniya da na lahira.

Irin wannan kokari dai ya sanya Birtaniyya da kungiyar Ba'athawa da ke mulki a kasar Irakin cikin halin damuwa saboda suna ganin hakan zai sanya kwabarsu ta yi ruwa, don haka suka fara kokarin ganin sun kame shi da ma ganin bayansa. Don haka sai suka shirya wasu 'yan koransu suka kai hari kan dalibansa a inda yake gabatar da lacca, shi ma suka kai masa hari gida suka kama shi da tsare shi a gidan yari. Wannan kamu dai ya janyo zanga-zangogi a kasar lamarin da ya tilasta musu sake shi. Fitowarsa ke da wuya sai ya ba da wata fatawa inda yake cewa:

"Duk wani hada kai da Ba'asawa tamkar hada kai da kafirai ne, azzalumai makiya Musulunci".

Wannan fatawa dai ta sanya mutane suka kaurace wa gwamnatin da jami'anta. Wannan yanayi dai ya tada hankalin mahukunta don haka sai suka fara tunanin samo wata hanya da za su yaudari mutane. Hanyar da suka bi kuwa ita ce ta nuna wa mutane cewa su ma fa suna tare da Musulunci kuma sun yi imani da shi, sannan shi ma shugaban gwamnatin Saddam Husaini shi ma fa yana kokari taimakon Musulunci ne. A lokacin ne suka fara nuno shi a gidajen talabijin yana salla da kuma ziyarar wajaje masu tsarki na kasar, amma ina don kuwa mutane sun riga da sun gano su, sun fahimci cewa suna so su yaudare su ne, amma dai karya suke munafukai ne. Ganin wannan yanayi sai jami'an suka koma kamar yadda a ka sansu inda suka sake ci gaba da kame mutane da sanya su cikin gidajen yari musamman ma dai mabiya Sayyid Bakir Sadr.