An haifi Imam Sayyid Abdul Husain Sharafuddin ne a garin Kazimiyya dake kasar Iraki a 1290 hijiriyya. Ya fito ne daga gidan ma'abuta ilmi da tsoron Allah. Mahaifinsa dai shi ne Sharif Yusuf dan Sharif Jawad dan Sharif Isma'il, mahaifiyarsa kuwa ita ce al-Zahra bint Sayyid Hadi ibn Sayyid Muhammad Ali.
Allamah Sayyid Sharafuddin dai ya fara karatunsa ne tun shekarunsa ba su yi yawa ba a garuruwan Najaf da Samarra na kasar Iraki, kuma ya yi karatu a wajen malamai irin su: Ayatullah Tabataba'i, Ayatullah Khorasani, Fathullah al-Isfahani, Shaikh Muhammad Taha Najaf, Shaikh Hasan al-Karbala'i da dai sauran manyan malamai da masana ilmummukan addini.
Bayan wasu shekaru na karatu a kasar Iraki a wajen manyan malaman lokacin, Allamah Sayyid Sharafuddin ya koma Jabal Amil na kasar Lebanon a lokacin yana dan shekaru 32 a duniya, inda a can ya zamanto shugaba kana jagoran al'ummar yankin wajen harkokinsu na addini, siyasa da al'amurran yau da kullum, bugu da kari kan shiryar da jama'a da kuma karantar da su.
A zamansa a Lebanon dai, Sayyid Sharafuddin ya kasance mai tsananin nuna adawarsa ga mulkin mallakan faransawa kuma ya tsaya kyam kan wannan akida tasa lamarin da ya sanya 'yan mulkin mallakan suka ta ba da himma wajen ganin sun ga bayansa ta hanyar shirye-shiryen makirce-makircen kashe shi, to sai dai Allah Madaukakin Sarki cikin ikonsa Ya kare shi daga
makircin makiyan. To sai dai duk da haka, makiyan ba su hakura ba don sun ci gaba da makircin nasu har lokacin da suka kore shi tare da iyalansa zuwa garin Damaskus na kasar Siriya, kana kuma sojojin Faransa suka mamaye gida da ofishinsa.
Ayyukan Sayyid Sharafuddin dai ba su tsaya kawai a kasashen Lebanon da Siriya ba, don kuwa ya kan tafi wasu waje ma na daban. Daga cikin irin wadannan kasashe kuwa har da kasar Masar. A shekarar 1329 hijiriyya ne Sayyid Sharafuddin ya tafi Masar inda ya gana da malumman kasar, daga cikin wadanda ya gana da su har da Shaikh Salim al-Bishir al-Maliki, babban shehin jami'ar Al-Azhar ta Masar a wancan lokaci, inda daga baya suka ci gaba da musanyan wasiku tsakaninsu kan lamurran addini da abubuwan da suka shafi akidun
shi'a. Wadannan wasiku nasu ne aka har hada aka mai she su littafin nan da ake kira al-Muraja'at.
Baya ga kasar Masar, Sayyid Sharafuddin ya kai ziyara zuwa kasashen Palastinu, Saudiyya (Madina) da kuma Iran.
To da yake kowace rai ma'abuciyar dandanan dacin mutuwa ne, Sayyid Sharafuddin ya koma ga Mahalaccinsa ne a shekarar 1957 wanda ya yi daidai da 8 ga watan Jimada al-Thani 1377 hijjiriyya, kuma an bisne shi ne a garin Najaf al-Ashraf na kasar Iraki kusa da kabarin kakansa Imam Ali bn Abi Talib (a.s).
Sayyid Sharafuddin tsawon rayuwarsa ya rubuta litattafa da dama, wasu daga cikinsu an buga su wasu kuma ba a buga su ba saboda kona su da makiya suka yi. Daga cikin wadanda aka buga din har da:
- Al-Muraja'at.
- Al-Fusul al-Muhimma fi Ta'alif al-Umma.
- Ajwabat Masa'il Musa Jarullah.
- Al-Kalimat al-Gharra fi Tafdhil al-Zahra (a.s).
- Al-Majalis al-Fakhira fi Ma'atam al-Itrat al-Tahira.
- Abu Hurairah.
- Falsafat al-Mithak wa al-Wilayah.
- Thabt al-Ithbat fi Silsilat al-Ruwat.
To wadannan wadanda aka buga ne, wadanda kuma ba a buga ba suna da yawa su ma, ga kadan daga cikinsu:
- Sabil al-Mu'umin.
- Al-Nusus al-Jaliyya.
- Tanzil al-Ayat al-Bahira.
- Ta'alikat ala Sahih Bukhari.
- Ta'alikat ala Sahih Muslim da dai sauransu.