Gudummawar Kasar Amurka Wajen Kera Makaman Kare Dangin Kasar Iraki:




Amurka Uwar Munafukai

A bugunta na shekaranjiya (2 ga watan Oktoban nan da muke ciki), jaridar Milliyat ta kasar Turkiyya ta buga wani rahoto da ta buga ta rubuta cewa kasar Amurka ce ta ba wa kasar Iraki makaman kare dangin da take da su.

To dangane da wannan lamari, muna iya cewa wannan bayani na jaridar dai ba wani bakon abu ba ne don kuwa wannan batu na taimaka wa kasar Irakin da Amurkan ta yi da makaman kare dangi don ta yi amfani da su a kan jamhuriyar Musulunci ta Iran a lokacin kallafaffen yaki na shekaru takwas da Irakin ta kallafa wa Iran din wani abu ne da bai buya wa al'ummomin duniya ba tun ma kafin su da kansu jami'an Amurkan su bayyana hakan a fili a 'yan kwanakin baya-bayan nan, duk da cewa wasu daga cikinsu sun ci gaba da kokarin boye wannan lamari.

Sai dai kuma duk da hakan, ita wannan jarida ta kasar Turkiyya ta yi karin bayani sosai kan irin hannun da Amurkan take da shi da kuma irin taimakawa kasar Irakin da ta yi da sinadarai da kuma irin waddannan muggan makamai na kare dangi.

Jaridar dai ta bayyana cewa a shekarar 1982 kasar Amurkan ta hanyar amfani da wani kamfanin da ke samar da irin wadannan sinadarori masu hatsarin gaske ta aika da irin wadannan sinadarori ga jami'ar Bagdad, bayan kasar Irakin ta bukaci hakan. Su dai wadannan sinadarori dai suna iya haifar da wasu cututtuka masu hatsarin gaske irinsu shanyewan jiki da dai sauransu. Kuma ita kanta kasar Irakin ta tabbatar wa Majalisar Dinkin Duniya cewa ta kera makamai daga wadannan sinadarai da Amurkan ta ba ta.

Bayan ga wadannan bayanai na wannan jarida ta kasar Turkiyyan, wasu rahotannin ma dai sun tabbatar da cewa a shekarar 1982, hukumar kula da kuma fada da cututtuka ta kasar Amurka C.D.C a takaice, ta aika da wasu sinadarorin masu hatsarin gaske ga kamfanin AL-MUTHANNA dake kudancin kasar Irakin wanda yake kera makamen kare dangin kasar. Haka nan kuma rahotannin sun bayyana cewa an aika da wadannan sinadarori ne kuwa da izinin mai'akatar kasauwanci ta kasar Amurka. Wannan bayani dai ya fito fili ne lokacin da wani kwamitin bincike na Majalisar Amurkan a shekarar 1994 ya fitar da wani bayani kan yadda wannan lamari ya kasance da kuma inda aka tura wadannan sinadori.

Masu kula da al'amurran yau da kullum dai suna ganin cewa dalilan aikawa da wadannan sinadarori a wannan shekara ta 1982 dai a fili suke, su ne kuwa saboda irin raunin da kuma gazawar da kasar Irakin ta nuna a yayin yakin nata da Iran da kuma irin nasarorin da Iran din ta dinga samu a kan sojojin Irakin masu wuce wuri. A da dai Saddam Husainin da masu daure masa gindi ko kuma mu ce wadanda suka sa shi fadawa kasar Iran din suna tsammanin cikin dan lokaci kadan za su iya gamawa da Iran da kuma jaririyar gwamnatinta ta Musulunci, to amma fa sai wankin hula ya kai su dare. To wannan dalilin yana daga cikin abubuwan da suka sa Amurkan ta aika da wadannan sinadori wa kasar Irakin don yin amfani da su a kan Iran, kuma tarihi ya nuna cewa ya yi amfani da su din.

Don haka dai masu kula da al'amurran suke ganin cewa kasar Amurkan da gangan ta aika wa Irakin wadannan makamai. To amma a halin yanzu kuma ganin cewa bukatarta bata biya ba da kuma tsoron kada Saddam din ko kuma wasu daban su yi amfani da wadannan makamai a kansu da kuma 'yar mowarsu wato Haramtacciyar kasar Isra'ila ya sa suka matsa sai sun lalata su.

A takaice dai babu wani batun kula da hakkokin 'yan'Adam ko kuma tsoron kashe sauran al'ummomi da Amurka ta ke cewa matukar dai shi Saddam yana da wadannan makamai, batun dai shi ne manufar Amurka. Don kuwa idan da tunanin kare hakkokin 'yan'Adam ne to ai babu bukatan a ba wa Irakin awannan lokacin don ta yi amfani da su a kan wasu al'umma, amma a halin yanzu a yi kokarin kwace su don tsoron zai yi amfani da su a kan wasu mtuanen. Shin akwai wani banbanci ne tsakni mutanen da wannan zamanin da na yanzu, da Amurkan ta ke ta kokarin kare wa?

To koma dai mene ne, halin da ake ciki dai ya nuna wa duniya wace ce kuma wata manufa ce Amurka take kokarin karewa, shin manufofin al'ummomin duniya ne take karewa ko kuma manufofinta?

Masu iya magana dai su kan ce wai in za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, don watakila kai za ka fada cikinsa.