|
|
| |||
________________________ ![]() Saboda imanin da nake da shi na cewa wannan tafarki na Ahlulbaiti (a.s.) wato Shi'a Ja'afariyya Ithna Ashariyya a matsayin tafarkin gaskiya kana kuma tafarkin tsira wanda duk wanda yayi riko da shi ba zai taba tabewa ba har sai ya riski Ma'aikin Allah Baban Nana Fatsuma, Kakan Hasan da Husain kana kuma Dan uwan Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib, a bakin Tafkin Alkausara, kamar yadda Ma'aiki (s) ya bayyana. Kana kasantuwan cewa abokan gaban Allah da ManzonSa da kuma Muminai sun yi ta kokarin ganin sun dushe haske wadannan Zababbun Allah (Ahlulbait) da kuma hana al'umma tsinkayen shiriyar da ke cikin wannan tafarki na tsira da hana su riko da Shuwagabannin Gaskiya, Limaman Shiriya, wadanda Allah Madaukakin Sarki Ya umurci dukkan Mumini da yayi riko da su matukar dai yana son saduwarsu da Shi tayi kyau ranar gobe kiyama. Sannan kuma bisa la'akari da cewa Imam Khumaini (Allah Ya kara masa rahama) shi ne mutumin da ya fito da wannan tafarki na tsira a fili ga jama'an duniya har ya sanya ni ma nayi riko da wannan "Igiyar Ta Allah Mai Karfi", kana kuma nake rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya tabbatar da ni akan wannan tafarki kana kuma Ya dauki raina a kansa Ya kuma tayar da ni tare da wadannan Bayi naSa abin kaunarSa, kana kuma Ya sanya ni masoyin masoyinsu kana kuma makiyin makiyinsu, 'yan wuta. To a saboda haka, na sadaukar da wannan shafi da kuma dukkan aikin da nayi a cikinsa ga wannan tsarkakakkiya ruhi (Imam Khumaini), ina mai fatan ranar tashin kiyama zai ja hannayena zuwa ga wadannan Tsarkakan Kakanni nasa (a.s.) don in sami cetonsu da kuma shiga inuwarsu. Muhammad Awwal Bauchi! |
||||