RA'AYOYI DA KALAMOMIN IMAM{R.A.}


Zabi Maudhu'in Da Kake So, Don Ganin Abin Da Ya Kumsa


SANIN ALLAH DA BAUTA ANNABAWAN ALLAH (A.S.)
MA'ASUMAI (A.S.)HADIN KAN MUSULMI
ADDININ MUSULUNCI DA TSARONSAALKUR'ANI MAI GIRMA
SHI'ANCI (MAZHABAR JA'AFARIYYA)GYARA KAI DA YAKIN BIN SON ZUCIYA
DOGARO DA KAIHAKURI


SANIN ALLAH DA BAUTA:
Allah ne hakikanin haske, dukkan wani abu koma bayanSa, duhu ne.
Dukkanmu daga Allah muke; dukkan halittun kasa da sama na Allah ne; kuma wadannan alamu ne na samuwar Allah, kuma duk a zuwa gare shi makoma take.
Allah Ya albarkace mu da ni'imominSa, don haka wajibi ne mu sarrafar da abin da Ya ba mu a tafarkinSa.
Dukkammu daga Allah muke kuma wajibi ne mu kasance a bautarSa.
Ka mai da hankali zuwa ga Allah domin zukata su mai da hankali zuwa gare ka.
Zahirin aiki ba shi ne ma'auni ba, a'a imanin mutum ga aiki shi ne ma'auni.
Dukkan kowane baligi (mukallafi) a bayan kasa na fuskanatar jarrabawa daga Allah (Ubangiji).
Mukami da matsayin da mutum ke da shi, da dukkan wani aikin da ya doru a kansa na a matsayin jarrabawa ce a gare shi.
Yardar Allah ita ce ma'auni a Musulunci, ba mutane ba. Muna kimanta mutane da gaskiya ba gaskiya da mutane ba. Ma'auni shi ne adalci da gaskiya.
Ku farka Ya ku jama'a, Hukuma ki farka , Ku farka dukkanku. Dukkanku gaban Allah kuke, za a kira ku gobe ku ba da bayani a kan abubuwan da kuka aikata da wajibanku.
Halittun kasa da sama a gaban Allah su ke, kada ka aikata zunubi a gaban Allah. Kada ka yi fada domin abubuwa marasa tushe, masu gushewa a gabanka. Ka yi aiki domin Allah.
Mutum na iya boyewa sauran halittu abubuwa, amma dukkan abubuwa game da mu na hannun Allah, kuma zai mayar mana da ayyukammu.
Ka kira Allah Marinjayi, domin kuwa Insha Allahu, zai saukaka maka matsalolinka.
Dukkan abubuwan da suka wajaba a kanmu na addini tausasawar Allah ne, amma muna tsammanin cewa wani nauyi ne.
Dole ne dukkammu, mu zama bayin Allah, kuma mu sani cewa komai daga gare Shi yake.
Mizanin bambance na Allah daga na Shaidan yana a dubin ainihin aiki amma ba wanda yayi aikin ba.
Sa Allah a zuci, hijira daga mutum kansa zuwa ga Allah (wadda ita ce mafi girman hijira), hijira daga son rai (ko kai) zuwa ga gaskiya, da kuma daga wannan duniyan zuwa ga duniya ta boye sun zagaye ka.
Bayan dogara ga Allah, ka dogara ga karfin kanka wanda shi kan sa na Allah ne.
Ina gaya muku cewa, kada ku ji tsoron kowa sai Allah, kuma kada ku dogara da kowa sai Shi.
Komawa ga wanin Allah ya kan gindaya shinge mai duhu ga mutum.
Rashin tuna Allah na kara gurbata zuciya, kuma ya kan sa galabar son zuciya da Shaidan a kan mutum da kara fasadi a kullum. Ambato da tuna Allah na sa wa zuciya sakina da tsaftace ta da mayar da ita madubin ganin hasken Allah. Tana tsarkakar da zuci da kare mutum daga kangin son rai.
Ku sani cewa: babu wutar da tafi fushin Allah zafi.
Kamar yadda yake wajibi a kan mu na kare kan mu, mu fitar da kan mu daga duhu zuwa ga haske, haka kuma yake wajibin mu ne mu kira wasu a kan haka.
Allah samamme ne kada ka gafala da Shi ! Allah Ya na nan, dukkan mu Ya na lura da mu.
Dukkan duniya gurin Allah ne, dukkan abin da ke faruwa na faruwa ne a gurin Allah.
Ka zamo a sane koda yaushe cewa dukkan abin da ka aikata a gaban Allah yake, idanduna dake kiftawa a gabanSa suke, harsuna da ke magana a gabanSa suke, hannuwa da ke aiki a gabanSa suke, kuma gobe, dole ne mu bada amsa a kan su duka.
Ku isar wa zuciyarku cewa dukkan abin da kuka aikata a gaban Allah suke.
Dukkan martabobin da Annabawa da Salihan bayin Allah suka cimma, sun samu ne daga tsinke alakar zukatunsu zuwa ga duk wanin Allah, da kuma allakar da zukatansu ga Allah.
Sa kanka ka yi nitso cikin wannan kogi, kogin Ubangiji Allah, kogin Annabci, kogin Alkur'ani mai girma.
Ka sani cewa, shukura domin rahamomin Allah na boye da na bayyane wani nau'i ne na bauta, kuma wajibi ne na ibada wanda ya wajaba akan kowa, daidai gwargwadon abin da mutum ke iyawa, koda yake, babu wani abin halitta da ke iya wa Allah godiyar da za ta kamance Shi.
Ba wani shakka cewa, soyayya wa Allah, bauta masa da tsarkake Shi na bukatar ilimi da sanin matsayinSa mai maras iyakan girma, kyakkyawan siffofinSa da girmanSa. Idan akwai rashin ilimi da sanin wadannan abubuwa, ba za a taba cimma bin wadannan manufofi ba.
Ka'idojin bauta su ne cewa babu wani karfi ko kudura abin bauta ma sai Allah, da kuma babu abin soyayya sai Allah da waliyansa.
Ainihin yabo na Allah ne kawai kuma bai zama na waninsa ba, koda kuwa yabo ga huren fulawa ko tuffaha kuka yaba to yabo ne wa Allah.
Idan ayyukanka ba saboda Allah ba ne, kuma ka fita daga hadin kan Musulunci, to lalle zaka zama saniyar ware.
Idan har manufarka Ubangiji ne sai kuma abin duniya ya biyo baya ya koma ya zama na Allah. Dukkan abin da kowannen mu ke da shi daga Allah ne, dole ne mu sarrafar da dukkan karfinmu dominSa.

ANNABAWAN ALLAH (A.S.):
Annabawa sun zo ne domin sanya kudurorin da aka tanada zuwa na aiwatarwa da kuma su kai dan'Adam zuwa ga ainihin dan'Adam na gaskiya.
Dukkan kokarin Annabawa ya kadaita ne wajen kiran dan'Adam zuwa ga hanya madaidaiciya (gaskiya) da sa shi ya bi tafarkinta.
An aiko Annabawa ne domin su kubutar da halayen mutane da zukatansu da ruhinsu daga dukkan duhu sannan su maye gurbinsu da haske.
Annabawa sun zo ne domin kiran mutane daga duhu zuwa ga haske.
Sakon Annabawa ya kawo canje-canje na kimiya da irfani, sanin Allah a duniya ya sauya sandararriyar falsafar kasar Girka (Greek) wadda su kansu Girkawa suka kago wadda ta kasance mai muhimmanci har yanzu zuwa wata fahimta ta ilimin irfani da kai wa ga hakika ta gaskiya irin ta manyan masana hakika.
Abin da Annabawa suke bukata shi ne sauya dukkan al'amura na rayuwa da na halitta da kuma mutum su dace da yardar Allah.
Albarkar aiko Mafificin Annabawa albarka ce da tun da, kama daga farkon halitta zuwa karshen lokaci, ba a samu ba kuma ba za a taba samun irin ta ba.
"Zillullah" (wato inuwar Allah) shi ne Shugaban Manzanni wanda shi a kan kansa babu wani abu daga gare shi, duk komai wahayi ne.
Tsira da amincin Allah Mai girma su tabbata ga Annabi Isa dan Maryama (a.s), Ruhullah Manzon Allah Mai girma wanda ya kasance yana tayar da matattu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Mahaifiyarsa tsarkakakkiya Maryama, wacce, ta hanyar hura ruhin Allah, ta haifi wannan irin da mai albarka ga wadanda ke jin kishirwar rahamar Allah.
(Jawabi ga limaman Kirista) Domin samun yardar Allah da aikata abin da Isa (a.s) ya umurta, ku kada kararrawar cocin ku domin kare Iraniyawa raunana da kuma yin tir da zaluncin azzalumai.
Ainihin aikin Annabawa shi ne magance son rai gwargwadon iko kuma su shiryar da zuciya.
Mu masu neman abu mafi alheri ga al'umma ne; mu mabiya Annabawa ne wadanda sun zo domin gyaran al'umma, sun zo ne domin ja-gorancin al'umma zuwa ga sa'ada.
Idan da dukkan Anabawa za su hadu wuri guda, ba za su taba sabawa da juna ba.
Hikimar Annabawa ita ce gallaza wa kafirai da makiya bil adama, da kuma rausasawa ga junansu, wannan gallazawar ita kanta rahama ce.
A farkon kiransu, Annabawa sun fuskanci masu hannu da shunin al'umma ne, Annabi Musa (a.s) ya fuskanci Fir'auna. Masu galihu su ne suka fi cancantar a fuskance su don su shiryu.

MA'ASUMAI:
Wannan mutum (wato Sayyidina Ali (a.s)) shi ne bayyanar gaskiya da adalci, shi ne abin mamaki na dukkan halitta, kuma daga farkon duniya har abada, babu mutum in banda Manzon Allah (s.a.w.a.) ba da ke iya kaiwa matsayi da martabansa.
A bisa asasi sojoji komai sanin sunayensu da aka yi sojojin dogon yaro ne a nan duniya. Mafi shaharar gwarzon soja mai sadaukar da kai ga Musulunci shi ne Ali (a.s), kuma shi ne sojan dogon yaro mafi girma.
Wannan karamin gida na Fatima (a.s) fa, wadanda aka tarbiyyantar a cikinsa, sun kai hudu ko biyar a bisa kidaya, amma a hakika su ne suka bayyanar da dukkan kudurar Ubangij, kuma sun kaddamar da hidimomin da suka sa mu da ku da dukkan bil adama mamaki.
A tafarkin kare dukkan martabar mace abin girmamawa kuma kamar yadda yake Fatimatuz Zahra (a.s) ita ce mace guda abin koyi, wajibi ne kowa ya yi koyi da ita.
Dukkan dabi'u masu kyau, da bayyanar malakutin Ubangiji, da jabarutu da mulku da nasutu duk sun tattara a jikin wannan halittar (wato Fatimatuz Zahra) (a.s).
Babban juyin mutanen Iran shi ne share fage ga babban juyin juya halin na duniyar musulmi a karkashin tutar Hujja (wato Imam Mahdi) (a.s).
Imamuz Zaman (ma'ana Mahdi mai dogon zamani) (a.s) yana kallonmu, yana lura da malamai domin ya ga abin da suke yi a yanzu da Musulunci ke hannunsu kuma duk an yanke musu uzuri.
Mu da muke jiran (Imami na 12 Ma'asumi) bayyanarsa mai albarka, ya wajaba gare mu mu tabbatar da aiwatar da adalcin Ubangji a wannan kasar ta Waliyul Asri (Imam Mahdi).
Shahadar Imam Ali (a.s), Husaini ibn Ali (a.s) da tsarewa da daurewa da kora zuwa gudun hijira da shayar da guba ga Imamai, ya faru ne a tafarkin kalubalen siyasa wanda 'yan shi'a ke yi wa 'yan mulkin kama karya; a takaice dai fafatawar siyasa na cikin muhimman abubuwan da suka wajaba na addini.
Abin ban takaici shi ne cewa ba su bar mai martaba Amirul muminina (Ali (a.s)) ya bayyana Musulunci a sarari kamar yadda ya kamata ba da kuma yadda Musulunci ya so ya zama ba.
Musibar da ta auku a kan Amirul Muminina da Musulunci tafi wadda ta auku wa Sayyidush-Shuhada' (Shugaban Shahidai Imam Husaini (a.s)).
Annabawa ba su sami cikakkiyar nasara wurin aiwatar da manufofinsu ba, amma Allah Ta'ala zai kawo wani (Imam Mahdi) wanda zai aiwatar da al'amurra a karshen zamani.


KAN HADIN KAN MUSULMI:
Na yi kokari da dukkan karfi na kuma zan ci gaba da yin dukkan abin da nake iyawa domin hadin kan dukkan mutanenmu da rokon Allah Ya taimake mu a wannan muhimmiyar matsala wadda ta dogara ga jurewar wannan al'umma.
Wajibi ne mu hada kai, idan muka yi haka, ba za mu ga wani sharri ba.
Wajibi ne musulmai su zama hannu guda wurin fuskantar dukkan girman kai.
Kira zuwa ga Musulunci ainihin kira zuwa ga hadin kai ne.
Muminai 'yan uwan juna ne a dukkan duniya kuma ta umurnin Alkur'ani 'yan uwa duk daya ne.
Na sha fadar cewa a Musulunci abubuwa kamar kabila, harshe, 'yan kasanci da muhalli, ba muhimman al'amurra ba ne, musulmai Ahlussunnansu da Shi'ansu 'yan uwan juna ne, duk daya ne kuma kowa na amfana da damar da Musulunci ya bayar da hakkokinsa.
A Musulunci Bakurde ko Bafarishe, sunni ko shi'a ba abin dubi ne ba, domin dukkansu 'yan uwan juna ne kuma duk daya suke.
Ya hau kan dukkanmu mu hada kai, mu zama 'yan uwan juna,....
Abin da dukkanmu ke bukata a yanzu shi ne kare wannan hadin kan.
Muddin ku ka zama abu guda ba wanda ke iya karya ku.
Hanyar ceton al'umma daga kangin mulkin mallaka shi ne ta hanyar addini wanda ke da zurfi a zuciyar al'umma.
Muddin ku ka rike hadin kan ku, Allah Ya na tare da ku. Hannun Allah yana tare da wannan kungiya.
Ta hanyar hadin kai a kalma guda da dogaro ga Musulunci, al'ummar Iran ta sa harkar ta ci gaba, kuma ba zata yi watsi da wannan sirrin ba.
Dole ne mu fahimci cewa "hadin kai a kalma daya" ne sirrin cin nasara kuma kada ku taba barin ku rasa wannan sirrin.
Yau ranar hadin kai ce da zama abu guda, kuma wannan ma yana daya daga cikin mafi girman rahamomin Allah.
Dukkanmu mun san irin tasirin da hadin kan al'umma ya haifar kuma har wa yau yake da shi, kuma a akasin hakan, irin kuncin da sabani da rashin jituwa suka janyo wa wannan al'umma a tsawon tarihi.
Sirrin cin nasararku, al'umma mai girma, ya kasance hadin kai a kan kalma guda da dogaro da imani.
Saboda kuwarku ga Allah, da kuma taken Allahu Akbar da kuma wannan hadin kai ya sa kuka yi galaba a kan wadannan masu karfin.
Tsaron Musulunci da Jamhuritar Musulunci na cikin muhimman ayyukan da suka hau kan dukkanmu kuma yana bukatar hadin kai.
Ku yi kokari kada ku rasa wannan hadin kai a kalma guda da dogaro ga Allah.
Idan Musulmai suka hada kansu, a hannu guda, babu wanda ke iya tunkararsu.
Idan musulmai suka hada kai, babu gwamnatin da ke iya danne su.
Musulunci ya zo ne domin hada kan dukkan al'ummomin duniya, Larabawa, Ajamawa (wadanda ba Larabawa ba), Turkawa, Farisawa da sauransu. Ya kuma kafa al'umma daya mai girma da sunan al'ummar Musulmi a duniya baki daya.
Mu 'yan shi'a dole ne mu zama 'yan uwan juna da 'yan sunna kuma kada mu bar wasu su zo su kwace dukkan abin da muka mallaka.
Ya wajaba akan dukkan musulmai da su hada kai tare.
Idan al'ummomin musulmi, wadanda sun kai zuwa biliyan guda, suka zama 'yan uwan juna da yin alaka ta 'yan uwantaka, babu wata cutarwa da za ta same su.
Ina kaskantar da kai wurin mika hannu wa dukkan wadanda ke yi wa Musulunci hidima da kuma kiransu da su hada kansu gaba daya ta hanyar cikakken hadin kai su yi aiki domin fadada adalcin Musulunci wanda shi ne kadai hanyar da wannan al'umma za ta cimma sa'ada.
Ku bar fadin "Hadin Kai" a koda yaushe amma bakwa yin komai dominsa. Ku yi aiki tare, ku 'yan uwa juna ne.
Na sha fadin cewa dole ne ku samu hadin kai a kan kalma guda domin ku gudanar da wani abu. Idan kowa ya dauki hanya daban da tafiya a kan hanya daban, bare ('yan kasashen waje) za su amfana da abin da zai zo baya in ma akwai wani.
Idan al'umma na son ta tsira, a farko, dole ne mutanenta su hada kai da kuma yin aiki sosai.
Mu zama 'yan uwan juna, sabani aikin 'yan wuta ne.
Kuna bukatar hadin kai a kan kalma guda, a yau fiye da jiya da gobe fiye da a yau.
Ku samu tabbacin cewa idan al'umma ta hadu a kan wata matsala ta Musulunci, kamar yadda ku ka shaida, babu karfin da ke iya tura ta baya.
Dukkan musulmai 'yan uwan juna ne kuma abu daya ne, babu wani wanda ya bambanta da wani kuma dole ne kowa ya zama karkashin tutar Musulunci da Tauhidi.

ADDININ MUSULUNCI DA KUMA TSARONSA):
Musulunci shi ne addini mafifici kuma shi ne mafi tsarki a cikin dukkan addinan duniya.


Matsa Wannan Alama Don Komawa Sama