SAYYID HASSAN NASRULLAH
________________________


An haifi Sayyid Hasan Nasrallah ne dai a kauyen Karanteena na kasar Labanon, mahaifinsa kuwa dan kasuwa ne mai saida 'ya'yan ita ce don amfanin al'umman yankin tare da yayan Sayyid Nasrallah din, a wasu lokuta kuma Sayyid Hasan shi ma ya kanje wajensa don taimaka masa. A irin wannan zuwa da yake yi ne wata rana ya ga hoton Imam Musa al-Sadr, sanannen malamin nan na kasar Labanon din da ya bace a kasar Libya kuma har ya zuwa yanzu ba a san inda yake ba, wannan hoto dai ya yi tasirin gaske a zuciyar Sayyid Nasrallah inda har ya yi fatan shi ma da a ce wata rana zai zamanto kamar wannan malami da kuma fatan ya kasance daga cikin mabiyansa saboda irin haiba da alamun takawa da ke tattare da shi.

Hasan Nasrallah dai tun yana karami bai kasance kamar sauran yaran kauyen nasu da suke zuwa wasan kwallo, iyo da dai sauransu ba, sabanin haka ya kasance ya kan lizimci zuwa masallaci duk da cewa shi dai ba shi da alaka da wani malami na musamman, amma dai duk da haka ya kasance mai kula da al'amurran addini. Irin wannan yanayi na sa ne ma ya sanya ya kan zauna shi kadai tare da hoton Imam Musa al-Sadr saboda mafi yawan al'ummar garin ba su damu da lamurran addini ba.

Lokacin da ya dan data, wato kimanin shekaru tara a duniya, Sayyid Hasan ya kan je wata 'yar kasuwa da ake sayar da gwanjon litattafa don ya saya da kuma karantawa, musamman ma dai litattafan da suka shafi addini, duk da cewa dai ba ya fahimtar dukkan abin da ya karanta saboda karancin shekaru, to amma dai ya kan ajiye wadannan litattafa da nufin cewa nan gaba zai sake karanta su da kuma fahimtar abin da suka kumsa. A daidai wannan lokaci da Sayyid Nasrallah ya ke ci gaba da wannan bincike yana makarantar elementare ne a makarantar al-Najah da ke yankin nasu. A shekarar 1970 ne dai ya gama wannan makaranta da kuma shiga makaranta ta gaba a Sinelfeel da ke garin Sur. Bai dai samu ya gama wannan makaranta ba saboda barkewar yaki a kasar Labanon din a shekarar 1975, lamarin da ya tilasta wa iyalansa barin wannan gari da komawa kauye.

Sayyid Hasan Nasrallah ya fara shiga wata kungiya ce dai a lokacin da ya koma garin Bazouriya inda ya shiga cikin kungiyar Amal ta Imam Musa al-Sadr saboda irin alaka da kuma kaunar da ya ke wa Imam Musa din a lokacin kuwa yana dan shekara 15 ne a duniya, ita dai wannan kungiyar ta Amal ana mata lakabi da "Kungiyar Marasa Galihu", duk da cewa a wannan gari nasu dai kungiyoyi kwaminisanci da Markisanci ne suka fi samun gindin zama. Bayan zamansa dan kungiyar Amal tare da wansa Sayyid Husain Nasrallah, an ba shi matsayin wakilin kungiyar na wannan gari duk kuwa da karancin shekarun da ya ke da shi.

Bayan dan wani lokaci dai, Sayyid Hasan Nasrallah ya kuduri aniyar tafiya birnin Najaf al-Ashraf na kasar Iraki don karatun addinin Musulunci a lokacin kuwa yana kasa da shekaru 16 ne a duniya. Bayan da ya yi wannan kuduri sai ya tafi garin Sur inda ya sadu da wani malami da ke wakiltar Imam Musa al-Sadr a garin mai suna Sayyid Muhammad al-Garawi don tattaunawa da shi kan yadda zai cimma wannan buri nasa na tafiya garin Najaf din. Jin haka sai Sayyid al-Garawi, wanda daman yana da alaka da kuma sanayya da Shahid Sayyid Muhammad Bakir al-Sadr, babban malamin garin Najaf din na lokacin, sai ya rubuta wa Shahid al-Sadr din wasika da bayyana masa irin kwazon Sayyid Nasrallah don ya ba shi daman karatu a Najaf din.

Bayan 'yan shirye-shirye, sai Hasan Nasrallah ya yi ban kwana da iyalansa ya kama hanyar Najaf, koda ya isa sai ya tafi inda 'yan kasar Labanon su ke da nufin su taimaka masa isar da wasikar da take tare da shi ga Shahid al-Sadr, inda Sayyid Abbas Musawi, wanda daga baya ya zamanto shugaban Hizbullah, ya karbi wasikar da nufin isar da ita zuwa ga mai ita, wannan dai ita ce farkon alakar Sayyid Nasrallah da Sayyid Abbas al-Musawi (r.a). Bayan isar da wannan wasika dai, Shahid al-Sadr ya yi maraba da Hasan Nasrallah, inda ya bukaci Sayyid Abbas al-Musawi da ya sama masa wajen zama da kuma ci gaba da koyar da shi, ta haka ne Sayyid Abbas al-Musawi ya zamanto malami kana kuma mai shiryar da Sayyid Nasrallah, wannan alaka da ta ci gaba da wanzuwa har lokacin da Sayyid Abbas din ya yi shahada lokacin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai masa hari da tarwatsa motar da yake ciki.

Da yake Sayyid Abbas ya yi nisa a karatunsa a lokacin, don haka sai Shahid al-Sadr ya ware masa aji don koyar da kananan dalibai, inda daga cikin daliban har da shi Sayyid Nasrallah. Saboda irin kwazon da Sayyid Abbas ya ke da shi ya sanya daliban nasa sun yi karatu mai yawan gaske cikin dan karamin lokaci.

A shekarar 1978 Sayyid Nasrallah ya gama kashin farko na karatun nasa yana mai shaukin ci gaba da karatunsa a wajen wannan malami nasa da ya kasance masa tamkar uba, to sai dai kuma wani gagarumin al'amari ya faru da ya kusan kawo karshen wannan karatu nasa. Wannan lamari kuwa shi ne faruwar wani gagarumin shiri da gwamnatin Iraki ta wancan lokaci ta fara na korar daliban Hawza 'yan kasashen waje da suke karatu a Irakin suna masu zargin wasu da kasancewa jami'an leken asirin kasar Siriya wasu kuma suna da alaka da wasu kungiyoyi da Musulunci. Wannan lamari ne dai ya sa jami'an tsaron Irakin suka kai hari ga makarantar Hawza ta birnin Najaf da kame wasu dalibai, inda bayan tsare su na wani lokaci suka kore su da dama kuwa daga cikinsu 'yan kasar Labanon ne. A daidai lokacin da jami'an gwamnatin Saddam din suka zo kame daliban kuwa, Sayyid Abbas Musawi ba ya cikin kasar Iraki ya tafi hutu Labanon don haka aka shawarce shi da kada ya dawo don ana nemansa ruwa a jallo. A nasa bangaren shi ma Sayyid Nasrallah ba ya nan a makaranta lokacin da aka zo wannan kame, don haka bayan da ya dawo aka gaya masa labarin kame 'yan'uwansa, sai aka shawarce shi da shi ma ya gudu, inda kafin jami'an tsaron su ankara ya samu damar ficewa daga Irakin da kuma komawa gida.

Bayan komawarsa gida ma, Sayyid Nasrallah ya ci gaba da karatunsa a wajen Sayyid Abbas Musawi a makarantar da ya bude, a daidai lokacin da kuma ya ke karantarwa a ita dai wannan makaranta. Baya ga karatu da kuma karantarwar, Sayyid Nasrallah ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a wannan kungiya ta Amal, inda ma aka zabe shi a matsayin wakilin kungiyar na bangaren siyasa a garin Bikaa.

A shekarar 1982, bayan mamayan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi wa kasar Labanon, an samu kafuwar wasu kungiyoyi masu son fada da wannan mamaya, to sai dai kuma saboda wasu dalilai da suka ta bijirowa ya sanya an samu rabuwar kai tsakanin 'yan wannan kungiya ta Amal, inda wasu daga cikinsu suka fice suka kafa kungiyar Hizbullah daga cikin wadanda suka balle din kuwa har da Sayyid Nasrullah. Babban take da burin kungiyar Hizbullah din dai shi ne kawo karshen wannan mamaya ta yahudawa.

Duk da cewa dai daga farko-farkon lamurra Sayyid Hasan Nasrallah bai kasance daga cikin majalisar gudanarwa ta wannan kungiya ta Hizbullah ba, to sai dai kuma ya rike makamai daban-daban a kungiyar da suka hada da shugaban reshen Ba'alabak daga baya kuma ya zamanto shugaban reshen Bika'a na kungiyar gwagwarmayar. Sannan kuma ya kasance mataimakin shugaban kungiyar reshen birnin Beirut, daga baya ma dai ya zamanto shugaban reshen Beirut din bayan da shugaban reshen Sayyid Ibrahim Ameen Sayyid ya koma bangaren siyasa na kungiyar, hakan ya sanya ya kasance daga cikin manyan jami'an kungiyar na gaba-gaba. Duk da cewa dai Sayyid Hasan na son ci gaba da karatunsa, to sai dai kuma saboda wannan mamaya na yahudawa ya hana shi hakan saboda ayyukan fada da wannan mamaya. To amma a shekarar 1989, bayan samun izini daga kungiyar, Sayyid Nasrallah ya nufi birnin Kum na kasar Iran don ci gaba da karatun nasa. A garin Kum dai Sayyid Nasrallah ya yi karatu a wajen malamai daban-daban inda duk suke yaba masa saboda irin kwazon da ya ke da shi.

To sai dai kuma wannan karatu nasa a Kum bai jima ba saboda kisan gillar da yahudawan sahyoniya suka yi wa Sayyid Abbas al-Musawi, shugaban kungiyar ta Hizbullah a shekarar 1992, wannan danyen aiki dai ya tilasta masa dawowa gida. Bayan jana'iza da zaman makoki dai majalisar gudanarwa ta kungiyar Hizbullah din ta zabi Sayyid Hasan Nasrullah a matsayin shugabanta, saboda irin kwazonsa da kuma kusancin da yake da shi da Shahid Abbas al-Musawi, kuma wannan mukami ne ya ke ci gaba da rikewa har zuwa yau din nan.

Sayyid Hasan Nasrullah dai ya yi aure ne a shekarar 1978, inda ya auri Fatima Yasin wacce ta fito daga garin al-Abbasiya da ke yankin Sur. Ya zuwa yanzu dai Sayyid Nasrallah yana da 'ya'ya hudu, wato Hadi, wanda ya yi shahada a yayin bata kashi da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila a lokacin yana dan shekaru 18 a duniya, sai kuma mai biye masa wato Muhammad al-Jawad, sai kuma Zainab sai kuma na karshensu Muhammad Ali.

Don karin bayani kan Sayyid Nasrullah da irin ayyukansa ana iya komawa ga shafinsa na internet wato: www.nasrallah.net