AYATULLAH MAHMUD HASHIMI SHAHRUDI
________________________

RAYUWARSA

IJTIHADINSA

RUBUCE-RUBUCENSA

MUKAMAN DA YA RIKE


RAYUWARSA

An haifi Ayatullah Sayyid Mahmud Hashemi Shahrudi ne a birnin Najaf na kasar Iraki a ranar 2 ga watan Dhul Qadah 1367 BH (wato shekara ta 1948 miladiyya), sai dai kuma asalin iyaye da kakanninsa daga garin Shahrud dake gabashin Iran suke.

Mahaifinsa dai shi ne Ayatullah Sayyid Ali Husayn Shahrudi, wanda shi ne mutum na farko da ya tsara da kuma rubuta maganganun Ayatullah Sayyid Abul Qasim Khu'i (r.a) a kan Fikhu da Usul al-Fikh.

Ayatullah Shahroudi dai ya fara karatun addini ne ko kuma abin da ake ce ma karatun Hawza, tun yana karami wato bayan gama makarantar Piramare kenan, inda saboda hazakar da yake da ita ya sami damar kare karatun share fage da kuma ma wanda ya biyo baya cikin karamin lokaci. Abin da ya ba shi daman wucewa gaba da kuma halartar darussan Usul al-Fikh da Bahasul Kharij na Ayatullah Sayyid Bakir Sadr (rahmatullah alaihi). A daidai wannan lokaci kuma ya kasance ya kan halarci wasu darussan da Imam Khumaini (r.a) da kuma Sayyid Khu'i suke gabatarwa, a nan ma dai ya nuna tsananin hazaka da kuma kwazo, ta yadda malaman da kuma daliban da suke karatun tare duk suna jinjina masa.

To wannan a bangaren karatu kenan, to a bangare guda kuma Ayatullah Shahroudi ba wai kawai ya takaita da karatun ba ne, bayan karatun kuma ya hada da gwagwarmaya da kuma goyon bayan harkokin gwagwarmaya. Irin wannan lamarin ne ma ya sa a shekarar 1974 aka daure shi a gidan yari inda aka dinga gana masa azaba kala daban-daban.

Har ila yau bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, al'umman musulmin kasar Iraki da kuma daliban Hawza sun gudanar da zanga-zanga don nuna goyan bayansu ga wannan nasara. To nan take gwamnatin Irakin ta fara nuna yatsa wa shi Ayatullah Shahroudi da cewa shi ne ya shirya wannan zanga-zanga, lamarin da ya sa suka sanya shi a gaba da kuma takura masa. Ganin irin wannan hali ne ya sa Ayatullah Bakir Sadr, wato malaminsa ya umurce shi da ya yi hijira zuwa Iran a matsayin wakilinsa a wajen Imam Khumaini (r.a). Bayan zuwansa Iran ya kasance mai isar da sako tsakanin Imam Khumaini (r.a) da kuma Shahid Ayatullah Sadr (r.a). Ayatullah Shahroudi dai ya dauki nauyin yada ra'ayuyyukan Juyin Juya Halin Musulunci na Iran da kuma Jagoransa Ayatullah Khumaini a matsayin wani nauyi da ya hau kansa, a dai dai lokacin da kuma ya ke kokarin karfafa wannan harka ta gwagwarmayar musulunci a kasar Iraki, da kuma tunzura al'umman Iraki wajen yin tawaye wa gwamnatin kasar da kuma kafa gwamnatin Musulunci.

Baya ga haka kuma Ayatullah Shahroudi ya kan gudanar da jawabai da kuma gabatar da makaloli kan ilmummuka daban-daban da suka shafi fikhu da sauran abubuwan da suka yi kama da haka a tarurruka daban-daban da aka gudanar a Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma ma sauran kasashen duniya.

A shekarar 1981 ne dai Ayatullah Shahrudi ya fara karantar da Bahasul Kharij a kan Usul al-Fikhu a birnin Kum, inda dalibai da dama suke halartar darasin da kuma amfanuwa da wannan dimbin ilimi nasa.

Ayatullah Sharudi ya zamanto alkalin alkalai na Iran ne a watan Augustan 1999 a lokacin da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i ya nada shi a wannan matsayi bayan karewan wa'adin tsohon alkalin alkalan Ayatullah Muhammad Yazdi ya yi.

IJTIHADINSA

Irin wannan kwazo na sa dai ya sa a ranar 27 ga watan Rabi'ul Awwal 1399, ya samu daman isa ga darajar ijtihadi, inda ya karbi satifiket din ijtihadin nasa daga wajen malaminsa Ayatullah Bakir Sadr. A wani bangare na wannan satifiket na ijtihadi, Ayatullahi Sadr din ya rubuta cewa: "A halin yanzu ka zama daya daga cikin Mujtahidai, wanda zai kasance babban buri na Musulunci da kuma musulmi, ina rokon Allah Ya taimaka maka da kuma ba ka nasara.

Don karin bayani, ga cikakkiyar takardar shaidan ijtihadin Ayatullah Shahrudi da Shahid Bakir Sadr (r.a) ya rubuta masa:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Fiyayyen halitta, Manzo Muhammad (s) tare da tsarkakan Mutanen gidansa.

A halin yanzu, mai girma Hujjatul Islam Sayyid Mahmud Hashemi ya gabatar da mafi muhimmanci rayuwarsa wajen karatun Fiqh, Usul -al-Fiqh da kuma Shari'a, kuma Allah Madaukakin Sarki Ya taimaka masa ya ba shi nasara wajen isa ga matsayin Ijtihadi, madalla da wannan ni'ima.

Don haka, a halin yanzu yana da ga cikin mujtahidan da Musulunci da musulmi suke bukatuwa da shi.

Saboda haka, na nada shi a matsayin wakilina akan dukkan abubuwan da suka shafe ni, da suka hada da harkokin kudi da dai sauransu, ta yadda dukkan wakilaina da kuma masu bina suna iya bada dukkan hakkoki na Musulunci gare shi.

Ina rokon Allah, Madaukakin Sarki, da Ya kare shi ga Musulunci da kuma Musulmi baki daya.

Muhammad Baqir Sadr
27th ga watan Rabiul Thani, 1399 (1979)
RUBUCE-RUBUCENSA

Baya ga koyarwa da yake yi, Ayatullah Shahrudi kuma ya yi rubuce-rubucen littattafa da makaloli daban-daban, daga cikinsu akwai:

  1. Buhuth fi ilm al-Usul: (Maganganu ne na Ayatullah Sadr a kan Usul al-Fiqh.
  2. Ka'idatul Farag wa al-Tajawuz.
  3. Buhuth fi al-Fiqh: (Bayanai kan Khumusi).
  4. Al-Nadharat al-Kawniyyah.
  5. Muhadharat fi althawrat alHusainiyyah: (Bayani kan gwagwarmayar Imam Husaini (a.s)
  6. Mu'tiyat ayat al-Mawaddah
  7. Masdar al-Tashri wa nizam al-Hukm fi al-Islam.
  8. Tafsir al-Maudhu'i li Nahj al-Balagah.
  9. Maqalat Fiqhiyyah: (Makaloli kan Fiqh).
  10. As-Sawm Tarbi'ah wa Hidayah: (Makala kan Azumi.
  11. Da dai sauran wasu littattafa da makaloli.
MUKAMAN DA YA RIKE
  1. Alkalin alkalai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
  2. Wakili a majalisar kula da tsarin mulki na Iran.
  3. Wakili a Majalisar Fayyace Maslahar Tsarin Musulunci ta Iran.
  4. Wakili a Majalisar gudanarwa ta Makarantun Hawza ta Kum.
  5. Wakili a Majalisar Koli ta Ahlulbayt (a.s) ta Duniya.
  6. Wakili a Majalisar Hadin Kan Mazhabobin Musulunci.
  7. Shugaban Mu'assar Ilmin Fikhu na Iran.
  8. Wakili a Majalisar Kwararru Mai Zaben Jagora.

Matsa Wannan Alama Don Komawa Sama